Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 15
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 15: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 15. Ganin suna magana a tsakaninsu yasa Leesharh cikin dabara ta tsugunna ?asa, a…
3,267 words
Ganin suna magana a tsakaninsu yasa Leesharh cikin dabara ta tsugunna ?asa, a cikin wannan duhu babu tsoro tasa hannunta ta fara lalu?ar kwalaben sauri sauri tana tattaresu. Fargaba da fa?uwar gaba saura ka?an yasa zuciyar ?ar tahali?ar nan ta buga, sai bada bugun dum dum yake yi, jikinta na kerma, kun san idan mutun yana aikata rashin gaskiya yana kuma tsoron a kama shi haka zaku ga jikinsa har wani kerma yake yi yana tsuma, to da yake ita kamma kun san akwai ta da karfin hali na gasken gaske, in ta sa kai zata yi abu to fa bata jin shakkar kwatantawa koda kuwa tasan ba zata yi nasara ba, irinsu ne wlh idan suka samu karatu mai kyau ha?e da kula ba kananan mutane masu kaifin ?wa?walwa za'ayi ba, akwai ta da jajircewa sosai, ga kaifin ?wa?walwa sai dai kash bata da kaifin hangen nesa, kunsan hangen nesa daban ne da kaifin ?wa?walwa, shi wannan baiwa ne da ba kowa yake da shi ba sai wanda Allah ya za?a ya baiwa, zaku iya samun yaro karami mai kaifin hangen nesa irin na manya, za kuma ku iya samun babba mai hankali amma ba hangen nesa.
So ita akwai kaifin ?wa?walwa babu hangen nesa sosai, tunaninta ko yaushe a iya yadda take yake, bata tuna makomarta gobe ko anjuma.
Ganin ya kunna hasken wayarsa ne yasa ta zabura ta yi wani irin mi?ewa tsaye, kai jama'a Leesharh ba dai karfin hali ba, ko da yake tana da gaskiya iyaye ba wasa ba, dole ta ceci ran mahaifinta tun da tana da dama, kuma da alama akwai matu?ar sha?uwa a tsakaninta da mahaifin nata.
Allah yasa da ya kunna hasken wayar kafafunsa kawai ya nufa da hasken ba ta kanta ya bi ba, shiyasa basu ga ta tsugunna ba.
Sai magana Guyson da Shafita suke yi mashi dama bai amsa ba, yana kunna hasken wayar a ?afafunsa suka ga jini jajir da shi na lafiyayyen mutun yana zuba daga ?afan nasa.
Ai a ?ari suka yi kansa suna rige rigen tambayarsa me yake faruwa? Meyasame shi a wajen?. A take suka ru?e, Guyson har idanunsa sun kawo kwallah, dan fa shi rago ne a fanni ciwo, amma ban da fannin karatu, a fannin karatu guru ne shi ?in, amma in bashi da lafiya ina ga duk duniya yafi kowa ragonta, kuka yake yi sosai wani lokaci harda ha?awa da cewa shikenan zai mutu ya dai'na kallonsu Yah Ramish, bawan Allah yana kaunarsu sosai.
Duk sun ru?e sai tambayarsa suke yi, ko uppan bai ce masu ba ya sauke yatsun kafafunsa a ?asa da nufin ya taka izuwa cikin parlourn dan ya zauna kafin su kira Dr Raj a san me ya ji mashi ciwon.
Haba tuni Guyson ya sa hannu ya ?auke shi cak, dan fa bashi da ragonta ta fannin karfi ma, kuna ganinsa haka har gym nasu Ramish yana zuwa kullum safiya, shi dai da ya fara ciwo ne ya zama jariri, sai kuma idan yana son abu wajen ?an uwan nasa, yauwa to a nan zaku ga shagwa?a dan su biya mashi bu?atarsa.
Cak ya ?auki Obaid, da yake Obaid ?in ma yana motsa jiki bashi da wani nauyin kirki. Bai zame da shi ko'ina ba sai part ?in su Dr Raj. Da gudu Sharifat ta bi bayansu tana ruwan hawaye.
Leesharh abin nema ya samu, jiki na kerma ta tsugunna ta hau tattare kwalaben da suka yi saura, dama ?azun ta tattare wasu, tana yi tana dafe saitin zuciyarta, dan ji take saboda tsabar bugawar da zuciyar take yi mata tamkar zata fasa kashin kirjinta ta fito waje, Allah sarki, wlh ko da iya wannan fargaba da fa?uwar gaba masu nikaf suka barta mutuwa zata yi baiwar Allah.
Tattare komai ta yi da sauri ta nufi ?akinta, tana zuwa ta wuce toilet ta zuba kwalaben a cikin wc sannan ta bishi da ruwa ya tafi.
Tana yi ta dawo ?akinta da gudu kamar wadda wani abin ya biyota, a saman gadonta ta fa?a tare da sake kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, yau Allah ya taimaketa ta sha a hannunsu da kyar, ya iyahi ya lillahi, sai dai fa?uwar gaba yana gab da kasheta kuwa.
Kuka take wanda duk mai zuciyar imani idan ya jita sai ya tausaya mata, duk wanda ya ji irin kukan nan sai ya san zuciyarta ta zo har wuya.
Tana tsaka da wannan kuka ta tsinkayo vibrate na wayarta a kunnenta, ko bata duba ba tasan masu nikaf ne, hakan yasa ta sanya hannunta dukka biyu a kanta tare da fara birgima a saman gadon tamkar wata zararriya, Allah sarki suna neman haukata yarinya, kuka take yi sosai da sosai har tana wani irin shessheka mai matu?ar ban tausayi.
Har wayar tata ta katse kira na biyu ya sake shigowa, a ?age masu nikaf ?in suke da ta ?auki wayar su ji cewa ta zuba maganin, ita kuma fargabar ?aukar kiran take yi dan tsoron abin da zasu sake ce mata kuma.
Ta jima a haka tana juyi tana kuka sosai, su kuma sai kiranta suke yi basu fasa ba, almost miss calls 15 suka yi mata. Can kuma ta zabura ta mi?e zaune a tsakiyar gadon, jikinta na tsananta kerma sosai, gashin idanunta sun yi sharkaf da hawaye, saboda birgiman da ta rin?a yi har ?an kwalin kanta ya fita, yadda kuka san zararriya haka ta zama. A ?ari ta janyo wayar tata, tsabar yadda jikinta yake kerma da kyar ta iya ri?e wayar. A hanzarce ta yi picking call ?in da ya shigo yanzu.
Voice ?inta har ya canza saboda kuka, da kyar ta iya furta. "Hello".
Daga ?ayan ?angaren aka ce. "Leesharh lafiya kike kuka? Meyasameki?". Babu komai ta amsa masu da shi. Shiru matar ta ?an yi kafin ta sake cewa. "Ina kika jefar da wayarki na yi ta kira baki ?auka ba".
A takaice ta ce. "Bana kusa ne ina waje wayar na ?aki". "Okey kin aiwatar da aikinki ne?". Kai ta gya?a kamar tana a gabansu tare da amsa masu da e. Tana ?o?arin ce masu ina baban nata su ha?ata da shi tun da ta yi masu aikin. Bata kai ga gaya masu hakan ba kawai ta ji diff sun katse kiran, bukatarsu ta biya sun ji ta aiwatar da aikin.
Ciro wayar daga kunnenta ta yi ta fara bin screenshot ?in da jajayen idanun nan nata tana kallo, tunani ta fara yi a kan me hakan yake nufi kenan? Sun kashe waya basu ji uzurinta ba, anya kuwa ba ayar tambaya a kansu?.
A ?angaren su Sharifat kuwa, kai tsaye emagency room dake cikin part na su Ramish suka wuce da Obaid da yake ta faman cewa Guyson ya sauke shi zai iya takawa da kafafunsa, ai shi ba rago bane, dan haka ya sauke shi. Ina ko sauraronsa Guyson ?in bai yi ba, sai da ya kwantar da shi a saman ?aya daga cikin katafaren beds dake cikin emergency room ?in, sannan ya ?ago yana kallon face ?in.
"Sharifat go and call Yah Raj, he has a patient here". Cewar Guyson. Da sauri ta juya ta fice daga room ?in.
Hararar wasa ya wurgawa Obaid tare da fa?in. "Ji wani ?an bakinka a wajen kamar in saukeka kai jarumi ne, you're not a hero at all, because hero never treat a woman like the way your doing, hero never beat woman's or shout for them, if you're a hero go and fight with strong man not small innocent girl".
"Yah Omar stop it, i don't want, am a hero, and who tall you that am fighting with her? Am not her mate, about beating she did a wrong think to me that's why i teach her a lesson". Ya kai karshen maganar yana ?aure fuska sosai.
Cigaba da harararsa Guyson ya yi ba tare da ya yi magana ba, dan yawan magana sam shi ba nasa ba ne, bata a tsarinsa.
Dr Raj ne suka shigo a tare da Sharifat cikin sauri, daga shi sai jallabiya a jikinsa, da alama daga masallaci sallar isha ya dawo. Cikin zafin nama ya zo ya kama kafan Obaid ?in tare da ?urawa jinin dake zuba ?in idanu.
"What happened to him?". Ya jefa masu tambaya. Guyson ya amsa da suna tsaye a wajen wannan ?an hanyar kawai sukaga ya haska hasken wayarsa sai jini suka gani a kafar tasa.
Tambayarsa Dr Raj ?in ya sake yi a kan meyasame shi?. Bai ?oye mashi ba ya gaya mashi gaskiya. Wani irin ?aure fuska sosai Dr ya yi, rai a matu?ar ?ace ya fara fa?a a kan cewa duk laifin masu aikin gidan ne da basu goge komai yadda ya dace da har za'a sami wani abin da zai ji ma wani ciwo a wannan wajen, gaskiya dole duk wata mai aiki dake cikin gidan yau sai sun kar?i hukunci na gaske ma kuwa, sai fa?a yake yi sosai ya ?ata rai. Shi kuwa Guyson binsu da ido kawai yake yi, yana jin tamkar jikinsa wannan kwalba ta fasa, Sharifat dake tsaye a gefe ne ta fara cewa yayan nata ya yi hakuri.
Ransa a ?ace ya fara duba kafan ?anin nasa. Da gudu Omaid ya fa?o masu cikin ?akin har yana haki, tun ?azun yake ta neman Obaid ?in.
Haka Dr Raj ya gyara mashi kafar tasa tare da yi mashi abin da ya dace, sannan ya ce Sharifat ta gayawa Ummie ta tara mashi duk masu aikin gidan nan ta mi?asu ga Discipline master ya basu ajikinsu, dan gobe su ?auki aikinsu da mahimmanci, shi fa wannan discipline master ?in wani shirgegen jami'in Special weapons ne, ya kware a iya casa mutane, duk wanda ya yi laifi a ma'aikatan gidan shi ake damkawa ya yi mashi hukunci, duk ma'aikatan gidan suna matu?ar tsoronsa kamar menene, saboda bashi da mutunci, bakin mugu ne, ya iya tabka ba karya, ga wata shegiyar zabgegiyar bulalarsa wadda aka yi ta da fatar macijin mesa, duk in ya hukunta yarinya ko wani ma'aikaci to fa sai wan da aka hukunta ya yi jinya sosai, saboda bulalar bata wasa bace, akwai shiga jiki.
Sosai Sharifat ta shiga bashi hakuri a kan ya hakura ayiwa ma'aikatan fa?a dai, ayi masu afuwa na yau kawai.
Rai a ?ace Omaid ya ce. "Aunty Sharifat kin san me kike fa?a kuwa? Sakacinsu fa ya ja jinin Obaid ya fita, gaskiya ba zan iya yafe blood na ?an uwana da ya fita ya tafi a banza ba, i can't, dole a hukuntasu, ai wannan basu san aikinsu bane, wai ma manene suka bari a kan tiles ?in har ya ji maka ciwo haka Obaid? Kuma a ina ne?".
Guyson da yake shiru tun ?azun ne ya ce. "Yah Raj please and please for give them kamar yadda Sharifat ta nema masu alfarma, and Omaid I don't want to hear your voice here again, ka mun shiru".
Wani irin kallo mai wuyar fassaruwa Omaid ?in ya wurgawa Guyson ?in kafin ya ce. "Yah Omar my Obaid fa! Blood ?in Obaid fa suka zubar mun, am sorry to say i can't for give them wlh". Yana kai ?arshen maganar ya juya da nufin ya fice daga ?ankin, dan ya lura basu san irin tafarfasar da zuciyarsa take yi mashi a kan zubarwa da ?an uwansa jini da aka yi ba, da shi suka sanya jininsa ya zuba zai iya yafe masu, amma Obaid gaskiya ba zai iya hakura ba, ransa ya ?aci sosai, zuciyarsa na ?una.
Yana juyawa Obaid ?in ya ri?o hannunsa yana fa?in. "Don't go anywhere my blood, please stay with me".
"I want to talk to Abbie ne, zan dawo yanzu, you know i can't stay in other place without you".
Da ido suke binsu, Guyson bai sake cewa ko uppan ba, dan yasan a kan Obaid Omaid zai iya haukacewa, shi ma Obaid a kan Omaid ba abin da ba zai iya aikatawa ba, su ?in kamar chewing gum suke, idan ka ta?a ?aya ka shiga uku, ?aya baya hakura ya yafe ?acin ran ?aya, sun san kome zasu yi yanzu Omaid ba zai hakura ba, ko da kuwa duka zasu yi mashi bafa zai hakura ba, shi ne yasa kawai suka bishi da ido.
Dr Raj da yake ya yi masu farin sani, dan ya fi kowa daga cikin ?an uwan nasu kai masu ziyara a makaranta, kullum kuma ya je complain kala daban daban malaman makaranta suke bashi a kan wa?an nan ?an albarka, so sanin su in and out yasa ya ce da Omaid ?in. "Ba sai ka ?auki wani mataki ba, just leave the case in my hand, I will handle the case".
Juyawa Guyson ya yi ya fice daga ?akin, da kallo Dr ya bisa, tabbas ya fahimci ransa bai so ba, Obaid kaninsa ne, ba zai zo wani abin ya cutar da shi ba, amma duk da haka bai kamata a hukunta wa?an da basu da laifi ba, a ha?a masu aiki dukka a hukunta a kan haka ai bai dace ba, wasu ai suna aikinsu da kyau.
Bin bayan Guyson ?in Sharifat ta yi da sauri, dan ita ma ta lura ransa ya ?an ?aci, Dr Raj kuwa ya tsaya da su Obaid yana kara yi masu nasiha. Sai huci Omaid yake yi shi a dole ba zai hakura ya yafe jinin ?an uwansa da ya zuba ba.
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 30/9/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??STEP TWO....??????
After some minutes.
Da misalin karfe 8:10pm. Wani irin jiniyace ta fara tashi tun daga farkon shinfi?a??iyar titin da ta keto har cikin gidan Abu Abdussalam, jiniya ce ta daban, ba kamar yadda suka saba jin jiniyar ba, ta yau yadda kuka san filin yaki suka dinfara, kaki ne kala kala har wajen kala hu?u, dukkansu sun saki jiniya, mitocin jami'ai ne gaba da bayan, a tsakiya kuma familys car's ne. Gudu suke shararawa na gasken gaske tamkar zasu tashi sama.
Tun daga nesa suke danna horn tamkar zasu tashi unguwar gaba?aya. A ?ari securitys dake tsaron gate ?in suka wangaleta. Yadda suka taho a haukace suna gudu haka suka danna hancin motocin ciki.
Leesharh dake kwance a saman bed ?inta tana aikin kuka ne ta zabura ta mi?e zaune, tun da Allah ya kawota wannan gida bata ta?a jin jiniya irin haka ba, tamkar zasu tashi garin, sannan bata ta?a jin motocin gidan sun shigo a haukace haka ba. Hakan yasa ta diro ?asa daga saman gadon nata, da gudu ta nufi wajen windown ?akin nata domin ta le?a taga su wanene?.
Dai'dai lokacin da ta le?a dai'dai lokacin Bilal ya zo wucewa ta tsakar harabar gidan ?auke da Ramish a saman shoulder ?insa ga jini na zuba kamar an bu?ewa ruwa hanya, ko motsi Ramish ?in baya yi, manya manyan jami'an special weapons uku ne suka takewa Bilal ?in baya suka nufi cikin gida.
Dafe saitin zuciyarta dake barazanar tarwatsewa ta yi da hannu, salati ta fara sakawa tare da tambayar to me ya sami Ramish ?in kuma? Ya mutu ne?. Babu mai bata amsa, hakan yasa ta yi ?asa?e a wajen jiki ba kwari, yadda kuka san wadda aka zarewa laka.
Ta ?auki a kallah 20 mins a wajen tana tsaye, kukan da ta ji yana tinkaro room ?in nata ne ya dawo da ita daga duniyar da ta afka. Da kyar ta iya janyo kafafunta ta koma wajen bed ?inta, ta kasa iya zama, zuciyarta ce ke bugawa da sauri da sauri, tsoronta dai kada ace ya mutu, tunani ta fara yi a kan to meyasame shi?.
Sharifat ce ta afko cikin ?akin nata tana kuka wiwiwi hawaye bibbiyu kamar ?aramar yarinya. Tana zuwa ta fa?a jikin Leesharh tare da ?ara sautin kukan nata.
A ru?e Leesharh ?in ta ce. "Sharifat lafiya me yake faruwa?". Cikin kuka ta amsa da. "Harbin Yah Ramish da bindiga aka yi, kuma ni ina ganin kamar ya mutu, wayyo yau na shiga uku na, in ya mutu ya zan yi ni kuma?".
Bu?e baki ta yi da nufin ta fara rarrashinta kenan Guyson ya fa?o cikin ?akin yana kiran sunan Sharifat ?in, sahunta ya biyo, tun daga emergency room yake ta aikin rarrashinta amma taki yin shiru, Ummie ma ta saka baki, amma taki ta yi shiru, gaba?aya family sun taru a cikin room ?in, ba wanda bai ce ta yi shiru ba, amma taki ta yi shirun, da suka matsa mata da rarrashin ne ma ta fito ta basu waje.
Jin abin da Sharifat ?in ta ce yasa Leesharh sake shiga tsananin tashin hankali, amsa ?aya take son sani shi ne ya mutu ko yana raye? Shi ne abin da kawai take son ji.
Ri?o hannun Sharifat ?in Guyson ya yi da nufin su tafi. Yah Rizwan ne ya shigo cikin ?akin, ya biyo bayanta ne shi ma, hannunta ya ri?o suka fice dan su je su rarrasheta, shi Yah Rizwan sarai yasan Sharifat tana son Ramish, dan in baku manta ba a baya na gaya maku tafi sha?uwa da shi a kan sauran ?an uwan nata, Rizwan abokinta ne sosai kamar dai Guyson, so saboda kusanci da suke da shi yasa ya fahimci tana son Ramish, amma bai gaya mata ya gane hakan ba, ya dai rabu da ita tana dakon kauna.
Yau dai gaba?aya hankalin kowa a matu?ar tashe yake, Guyson ma ya sha kuka, da yake shi da Sharifat akwai saurin kuka, Obaid and Omaid kuwa idanunsu a bushe, shi Obaid ma cewa ya yi bari ya je ya yi wanka da kafar ciwon nasa, yaran nan sam sam babu wani tausayin kirki a ransu, abin kirkinsu ?aya dai shi ne kaunar juna da suke yi, amma kome zai faru zuciyarsu bata karaya sam sam.
A haka dai yau gidan ta kwana hankali a matu?ar tashe, kowa yana cikin damuwa, amma King Zuhair bai da kabari, sun ki sanar mashi abin da ya faru.
Da Abu Abdussalam, Rizwan, Bilal sai Dr Raj sune suka kasance a tare da Ramish ?in, sai fama Dr Raj yake yi a kansa dan shawo kan matsalar, Guyson ma ya kasa iya yin barci, sai shige da fice yake yi daga room nasa zuwa wajen ?an uwan nasa.
Ba yadda su Rizwan basu ro?i Abu Abdussalam ba a kan ya yi hakuri ya je ya kwanta dare ya yi, amma ina ya kafe ya ce in sunga ya fita daga ?akin nan to fa ya san a wani hali Ramish yake ciki, dan yanzu su dukkansu har Dr Raj ?in basu san a wani mataki yake ba.
Sharifat da ta tare a saman dadduma tun karfe 10 sallah take yi tana kuka, addu'a take yi Allah yasa kada ya mutu, bata damu da son jin meyafaru har aka harbesa ba, ita dai burinta kawai ya farka. Ita ma Leesharh ta ji tausayinsa sosai, kuma tasha kuka, duk sai ta ji tamkar ?an uwanta aka harba, ta shiga damuwa sosai, hakan yasa ta yi mashi addu'a sosai kafin ta kwanta, sai dai ko da ta kwanta bata iya yin barci ba, tunani ya hana ta rintsawa, sai kuka take yi masu nikaf basu ha?ata da babanta ba, bama su sake kiran ta ba, tun da suka yanke call ?in ?azun, basu cika alkawari ba.