Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 16
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 16: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 16. A ?angaren Obaid and Omaid kuwa, suna cikin room ?insu dake part na su Ramish…
3,348 words
A ?angaren Obaid and Omaid kuwa, suna cikin room ?insu dake part na su Ramish ?in, dama idan sun zo gidan a nan suke zama, ko a jikinsu suka yi shirin kwanciya Obaid kafa ta dai'na zogi, shirin kwanciya abinsu suka yi, dan a cewarsu ai ragonta ne dan an harbi mutun da bindiga su wani tsaya ?aga hankalinsu, Yah Ramish ai jarumi ne, ba rago bane, sun tabbata da Yah Bilal aka harba haka Yah Ramish ba zai tashi hankalinsa har haka ba, dan shi ?in jarumi ne baya son harkar ragonta, dan haka su basu ga wani abin ?aga hankali ba, Allah ne yake ri?e da ransa, idan ya tashi fine, idan ma bai tashi ba fine, kowa ma zai mutu, su basu son shirmen banza, ba zuciyar mata ne a kirazansu ba da zasu tsaya yin kuka ko su hana kansu barci, dakakkun maza suke shiyasa suka yi kwanciyarsu basu sake le?awa wajen Ramish ?in ba!.
Yo su dama ta ya za'ayi su damu? Kada ku manta suna da tsama tsakaninsu da Ramish ?in da kuma Mama, duk cikin kingdom of power Ramish ?in ne kawai yake iya nutsar da su su nutsu, shi ne mai ci masu ?aniya dai'dai gwargwado, ba wanda suke shakka da tsoro sai shi, shiyasa ba wani kaunarsa suke yi ba, kunga kuwa fin haka ma zasu fa?a, ga maman Ramish ?in ta sako Mommarsu a gaba, ta takura mata, kunga ai dole su ce su ba ragwaye bane. Amma fa da yake jini ba wasa ba har cikin ransu abin ya yi masu zafi, sun ji babu da?i, kuma sun ji a ransu da zasu kama wanda ya harbesa tsab zasu kashe banza, yaran nan baka iya gane masu sam sam.
Haka suka yi shirin kwanciya suka kwanta abinsu, kafin su yi barci ma sai da suka sha hira tare da cewa gobe da safe zasu bar gidan nan dan basu son wani koke koken da shirmen banza, jibi zasu wuce school, zasu koma gidam King Badeen su ?arisa shirinsu a can.
Obaid ne ya fara yin barci ya bar Omaid, shi kuwa Omaid ?in har wajen karfe 3 yana latsa waya bai kwanta ba.
Washegari da safe, shiryawa sosai suka yi kafin su fito, kai tsaye palace na Abu Abdussalam suka nufa, dan su yi mashi sallama. Sai dai ko da suka je baya nan, hakan yasa suka dawo wajen Ramish. A nan suka sami family gaba?aya.
Allah sarki Sharifat idanu sun kunbura luhu luhu sun yi jajir kamar mai ciwon ido saboda kuka da ta kwana yi, shi ma Guyson idanu sun kumbura saboda kuka da rashin samun barci, yau gaba?aya kowa da yake cikin gidan Abu Abdussalam sai da yasan ba lafiya, jami'an special weapons sun yi tururuwa zuwa gidan, kaki sun ?aru a cikin gidan sosai, tamkar ba lafiya ba, sai kai komo manya manyan motocin kaki suke yi, wa?an nan su shigo wa?an nan su fita, babu wanda ya sami damar ganin Ramish ?in.
Harta air force, wato ma'aikatan Bilal sun cika gidan, sai up and down suke yi suna wani muzurai kamar zasu cinye mutun ?anye, ga su mafiya yawancinsu idanunsu jajir, sannan ga wasu jiga jigan bindigu a hannunsu wanda ko baka yi laifiba ka fito tsakar gidan nan ka gansu sai ka razana ka ru?e ka rasa ina zaka sanya ranka, idan ma kana da zuciya a kusa yanzun nan zaka ha?iya ka mutu saboda razanar da zaka yi da ganinsu.
Yadda kuka san ?arayi ne suka hauro gidan suka yi ?arna, sai wani kaiwa suke yi suna komowa ha?e da gyara bindigunsu kamar masu jiran kiris su saki wuta.
Abu Abdussalam suka fara gaisarwa kafin su gaida Ummie, sannan suka bi sauran ?an uwan nasu dukka suka ?aga masu gaisuwa. Da yake yau kowa yana cikin tashin hankali sama sama suka amsa gaisuwar tasu. Cikin girmamawa suka ce da Abu Abdussalam zasu koma gidan King Badeen dan gobe zasu koma school.
Ba musu Abu Abdussalam ya ce okey Rizwan ya rakasu waje yasa a ?aukesu a cikin motan jami'ai, sannan jami'ai kamar guda 10 su rakasu har gida dan tabbatar da tsaro.
Da okey Rizwan ya amsa kafin ya wuce gaba su rufa mashi baya. Kowa dake cikin ?akin banda Ummie duk suna tsaitsaye ne cirko cirko sun zubawa Ramish dake kwance kamar gawa idanu. Ummie kuma tana zaune a bakin bed ?in da yake kwance ta tsare shi da kallo, Guyson kam ya kifa kansa a jikin bangon ?akin yana ruwan hawaye.
Kai tsaye Rizwan ya je ya fa?awa securitys dake bakin gate umarnin Abbie, yana gaya masu kuma ya juya izuwa cikin gida, dan suna tsaka da aiki ne.
Nan take jami'ai 10 cif kamar yadda minister Abu Abdussalam ya fa?a suka shirya tare da fito da mota har izuwa gabansu in da su?e tsaye, sannan suka bu?e masu kofar motar a kan su shiga a mayar da su.
Obaid ne ya fara ?o?arin shiga. Basu kai ga shiga cikin motarba jiniya ya ?ara?e ko'ina a cikin gidan.
Dakatawa daga shiga suka yi, Obaid ya ce su jira bari yaga su waye kuma suka zo? Ba yadda jami'an suka iya dole su jira, haka suka tsaya cirko cirko suna jiransu, yarana kanana sai sakawa manyan mutane ciwon kai.
Wasu daga cikin Jami'an Swat ne suka danno hancin motocinsu guda uku cikin gidan, yau gidan minister ya zamana tamkar filin yake, ko'ina ka juya kaki daban daban ne suke kai komo.
Wasu jiga jigan jami'ai guda biyu ne suka fito daga cikin mota ta tsakiya, suna fitowa wasu matasa guda biyu suka fito suma. Damko matasan suka yi suka nufi hanyar discipline room dake cikin gidan ta kusa da apartment na jami'an dake cikin gidan gaba?aya, a nan ?akin discipline room ?in nasu yake, wannan ?aki wlh da'a kai mutun ciki gwara mashi su harbe shi da bindiga kawai ya mutu ya huta.
Wlh idan suka shiga da mutun wannan ?akin da wuya uwar da ta haife shi ma ta iya ganesa a lokacin da zasu fito da shi. ?aki ne katafare gaske, babu kalar nau'in azaba da babu a cikinta, kayan azabtar da bawa birjin suka tara a ciki, ko ?an'sanda or soja ko dai swat or wani kaki dai idan ya yi laifi, shi da yake da horo a jikinsa ma kuka yake yi idan aka ce a kaisa wannan ?akin a bashi punishment bare kuma wanda bai da kaki bai da horo a jiki, sam babu imani a wannan ?akin.
Dama tun da motocin suka shigo cikin gidan Obaid and Omaid ?in suka nufesu dan su ga su wanenen? Su da zasu tafi amma sun tsaya ganin gulma, jami'an da zasu raka sun ?in kuma sun tsaya kamar wasu tsa?aguna suna jiransu.
Sun zo dai'dai tsakiyar harabar gidan suka ci karo da jami'an swat ?in guda biyu suna ri?e da mutane guda biyun da suka fito dasu daga cikin motan, sun ri?e masu kunkumin wandunansu kamar dai yadda suke damke criminal.
Kallon Omaid Obaid ya yi kafin ya furta. "They looks like a criminals". Jinjina kai Omaid ?in ya yi alamar e zancen Obaid dutse tamkar wani babban mutun. Ga ?an rakiyansu a can suna jiransu sun zo yin abin da ba'a aikesu ba.
Da sauri Obaid ?in ya dakatar da jami'an tare da tambayarsu me wa?an nan kuma suka yi? And su waye su?.
Cikin girmamawa ?aya daga cikin jami'an ya bu?e fasasshiyar voice ?in nan nasa kamar na adawa ya furta. "They're criminals, we're suspect that they are one of those who shot sir Ramish with gun, Sir Bilal told us to bring them home because he cannot go out today".
Da sauri suka juyo suka kalli juna kamar abin ha?in baki, zaro idanu suka yi a tare, da alama yaran nan sun saba magana ?ar kurma kurma da ido ha?e da ?an motsa lips ?in bakunansu, duk wata kafa ta munafurci sun santa kusfa kusfa, kana zaune ka saki baki zasu yi cinikinka su saidaka ko su ha?ama boom da zata yi maka mummunar fashewa ta hanyar yin magana da ido baka sani ba.
Ha?a ido kawai suka yi wajen kallon juna, basu furta ko uppan wa junansu ba, amma haka suka sake juyo da kallonsu izuwa kan jami'an, a tare suka kai wa criminal ?in mutun ?aya wani irin bahagon naushi a baki, Obaid ta gefen hagu ya naushi shi, shi kuma Omaid ta gefen dama kamar an aikosu.
Nan take bakinsa ya fashe hakwara biyu suka fita, da alama hakwaran a mace suke, sun ji busar sigari har sun gaji. Sake kaiwa ?ayan ma naushi suka yi a tare. Tsabar iya mugunta har da na?e jallabiyar jikinsu zuwa gwigwa zasu fara labta masu duka kamar su aka kawowa su basu horo.
?o?arin janye criminals ?in jami'an suka yi, aikuwa Obaid ya ce. "Kai ku dakata mu basu a jikinsu tukun nan, yau saboda su ma a gidan nan zamu sake kwana, da safe zanzo in ?an yi Wrestling a jikinsu ko na 30 mins ne haka, naga sun ru?e da shaye shaye, ba su da kuzarin da zasu iya jurar azabata na 1h".
(Ni kam na ce ko ba su ru?e bama yaushe zasu juri azabanku? Ai ku wlh ko mai lafiya kuka kama sai abin da hali ya yi, Hmmmm jikokin Akka waye ya ce ba ku ba? Yanzu duk rikicin da kuka rin?a yi a cikin gida bai isheku ba sai kun karawa wasu ma? Kai my twin's sai shiriyar Allah.)
Omaid ne ya amsa da. "Sure, ni ma da safe ina zuwa, kune kuka harbi yayanmu ko? To ku shirya kar?ar azabanmu".
Wucewa da su jami'an suka yi, amma sai da Obaid ya kara masu naushi ?aya a ciki. Juyawa suka yi tare da cewa ?an rakiyan nasu su koma bakin aikinsu su sun fasa komawa yau, sai gobe da sassafe zasu koma bayan sun ci ?aniyar wa?an can criminals ?in, daga haka suka wuce cikin gida abinsu, abin nema ya samu, dama ba'a ta?asu ba ma sun iya mugunta bare kuma Allah ya kawo masu mai laifi? Ai shikenan kuma.
Tun daren jiya Dr Raj yake fama a kan Ramish amma har yanzu shiru, waya ya yi wa hospital ?insa a in da ya ?u?aci da a kwararrun Dr's guda biyu and nurses uku su zo gida dan su taya shi aiki, ya dai yi nasarar cire bullet ?in dukka biyu, amma dai har yanzu bai iya shawo kan matsalar ba, basu ma ta tabbacin Ramish ?in yana raye ko ya mutu. Tun jiya Dr yake ?o?arin gano wani abu, yana zargin kamar a cikin jinin Ramish ?in da akwai wata kwaya ta ruwa da ya sha kafin faruwar abin, dan tabbas alamu sun nuna jinin jikinsa a gauraye take, hakan tana ?aya daga cikin dalilan da yasa Dr Raj ?in ya kasa shawo kan matsalar, dan jinin jikin Ramish ?in akwai matsala a tattare da ita kuma jinin tayi sanyi over ta yadda Dr ya kasa iya aikinsa, duk wani allura da ya yi mashi jinin taki ?ar?a sai ta fara ?o?arin canza mashi position na aikinsa, kamar jinin matatce.... Tashin sense.
Nasan kun ?agu ku ji me ya faru, to ku saurara, bayan fitansa gida da nufin ya halarci meeting da zai yi shi da ?an cikin team ?insa. Shi da wani jami'in swat mai tu?a motar tasa kawai suka fita, bai ?auki wasu jami'ai ba, ya fita shi ka?ai, dan yana tunanin meeting ne na sirrin, a ganinsa babu wanda ya san da batun, kuma kunga babu wanda ya san da batun sai Leesharh da ta yi mashi la?e sai kuma ?an uwansa.
Yana kan hanyar tafiya ne Bilal ya kirasa a waya, a nan ne yake sanar da Bilal ?in yana hanyar zuwa guest house ?insa domin yin meeting da yaransa kafin su wuce ?asar Tunisia gobe. Okey Bilal ya amsa mashi da shi tare da ce mashi gashi nan biyo bayansa, daga haka suka yi sallama.
Sun ?an yi tafiya mai nisa tsakaninsa da kiran da Bilal ya yi mashi, kwatsam ba zato ba tsammani wata mota ta tari gaban motarsu, da kyar driver nasa ya iya taka birki, saura ka?an su yi karo da motan da ta shiga gaban nasu.
Jin cewa Ramish ?in bai yi magana bane yasa drivern bayan ya dai'dai ta nutsuwarsa ya juyo tare da cewa. "Sorry sir". Ya yi saurin ce mashi sorryn ne kuma saboda sun san halin Ramish ?in yana da zafi, yanzu zai iya hukuntasa a kan haka, dan zai ce tu?in ganganci ne, ba zai yi la'akari da cewa wata mota ce ta sha gabansu ba, zai hukunta shi ne kawai, shiyasa ya yi saurin cewa sorry.
Sai dai ga mamakinsa Ramish ?in bai amsa mashi ba, yasan cewa dama ba wani amsa masu magana yake yi ba, amma abin ya ?aure mashi kai yadda suka kusa yin accident kuma bai yi magana ba. Juyowa ga Ramish ?in da kyau ya yi da nufin ya sake yin magana, sai ji ya yi anyi knocking na glass ?in motar.
Zuge glass ?in ?asa ya yi da nufin ya yi magana, dama so yake yi ya gama da Ramish ?in kafin ya fita ya ci uban koma waye mai wannan mota da ya shiga gabansu, sai ga mai motan ma ya kawo kansa yana yi masu knocking na glass ?in.
A fusace ya zuge glass ?in, har da ?aure fuska sosai irin ba wasan nan, dan kudirin cin uban komawaye mai motan ya yi a ransa. Bai kai ga bu?e baki ba sai ganin ya yi mai motan ya sanya mashi bindigar silent gun a kai, cike da bada umarni ya ce ya yi maza ya yi waje. Ramish kuwa yana zaune kaman gunki, yadda kuka san an sassa?asa a wajen, idanunsa kuma a bu?e garau yana ganin komai, sai dai ko yatsa daga jikinsa ba zai iya motsawa ba, tamkar ba shi ya yi waya da Bilal ba jimawa ba, in short bayan idanun babu wani abin da yake amfani a jikinsa a halin yanzu, sai kallo kawai, ga kuma wayarsa a hannunsa yana kame kam.
Ba musu wannan jami'in ya fito, saboda babu bindiga a hannunsa, ita kuma bindiga fa kunsan idan tana waje to umarninta ake bi, dan haka wannan jami'in ya bi umarnin bindigar dake kansa dan dole ya fito daga cikin motar. Sai dai akwai kudirin in ya fito ya samu sarari ya ci uban mai motar ya kwaci bindigar a ransa.
Yana fitowa mai motan dake sanye da mask baka a face ?insa, ga hand gloves ita ma baka, takalmar kafarsa Booth ce baka, a takaice baka iya ganin komai na jikinsa face ido, ?ara sanya mashi bindigar da kyau ya yi a kai, da alama ya san halin jami'ai zasu yi ?o?arin kwatar kansu, sai ya kara sanya mashi bincigar da kyau, abinku da babban gari kuma cikin yankin manyan kai na ?asar ko'ina shiru tsit, dan dare ne kowa ya wuce gida, dama su manyan nan ba wani fita suke yi ba, suna cikin gida abinsu, to me zasu fita su nema?.
Wani irin fito mai motar ya yi sai ga wasu maza guda uku masu irin shigarsa sun fito daga cikin motar tasa. Kai tsaye gidan baya na motar su Ramish ?in suka bu?e, kamar sun san ba zai iya ta?uka komai ba, da zafinsu suka ?alle kofar motar. Janyo shi suka yi suka fito da shi, har lokacin idanunsa a bu?e suna kallon komai ba zai dai iya motsawa ba.
Fito da shi suka yi da nufin su sanya shi a cikin motarsu su tafi da shi, a dai'dai lokacin Bilal ya iso tare da motar sojoji guda ?aya, shi baya kasada da rayuwarsa wajen tafiya shi ka?ai, duk in da zai je da ?an rakiya dan tsaro ba dan tsoro ba, inma sojoji or ?an'sanda ko kuma jami'ansa wato air force su take mashi baya, baya dai fita shi ka?ai, shi da ma ba farautar rayuwarsa ake yi ba yana kula sosai, amma shi Ramish yasan nemansa ake kamar hauka, yasan da cewa yana da tarin makiya gaba da baya amma sai kuga ya yi fitowansa shi ka?ai, wani lokaci ma da kansa yake jan motar shi ka?ai, ba ya wani damuwa da ?an rakiya, yana kasada da rayuwansa, sai ya ce shi ba rago bane, zai iya kwatar kansa a koma inane.
Isowar su Bilal wajen yasa mutanen suka yi azama tare da kara zafin nama wajen ganin sun tura Ramish ?in cikin motarsu sun gudu da shi. Ai kuwa drivernsa ya ?aga murya wajen gayawa su Bilal ?in abin da yake faruwa. Da farkoma wucewa motocin su Bilal ?in zasu yi, sai kuma yaga kamar ba gaskiya ake ?ullawa a wajen ba, a matsayinsa na Jami'i sai ya ce su dakata su ga menene yake faruwa a wajen?. Suna dakawata ne mutanen suka fara saurin tura Ramish cikin mota su gudu da shi dan sun ga wasu sun dakata a wajen ga jiniya.
Shi kuwa drivern Ramish da yake yasan cewa motar gidansu ne sai ya yi saurin sanar da su da su yi sauri su zo kar wa?an can su tafi da Ramish, Allah sarki bai gama ihun gaya masu ba mai motan da ya sha gaban nasu ya ciro bindiga ya harbesa. Ganin haka yasa Bilal ya ?auko nasa bindigar tare da fitowa da sauri.
Kan kace me sauran da suka ?auki Ramish ?in suka sauke shi ?asa suka ciro nasu bindigar. Musayan wuta suka fara yi Bilal ya harbi ?aya saura suka gudu, sojojin suka rufa masu baya. ?arisowa wajen Bilal ?in ya yi yana bin Ramish da kallo.
A gabansa ya tsugunna yana yi mashi magana, amma bayan wannan ido da yake binsa da kallo bai iya amsawa ba. Ganin hakan yasa Bilal ?in ya yi tunanin ko dai sun yi mashi wani abin ne? Dan haka sai ya mi?e ya sa?e shi sai saman shoulder ?insa. Yana juyawa da shi da nufin ya kaishi cikin motarsa sai suka ji harbi from nowhere, ba kowa aka harba ba kuma face Ramish ?in, kafin Bilal ya juyo sun ?ara mashi wani harbin, so suke kada wannan dama da suka samu ta ?ubce masu, so suke su kashe shi ta kowacce hali tun da ?aukarsa su tafi da shi ya gagaresu, harbi biyu suka yi mashi, wannan harbin ya ja hankalin sojojin da suka bi masu motan nan, hakan yasa suka dawo a guje suka bi in da harbin ya fito.
Shi kuwa Bilal da karfin hali kai shi cikin mota ya yi, zuciyarsa na tafasa, yana son bin ?an ta'addan ya kamosu dan yana ganin kamar yaran nasa ba zasu iya kamasu ba, yana son binsu ya kamosu amma ran ?an uwansa yafi mashi mahimmanci, hakan yasa ya ja motar kawai da wani mahaukacin gudu ya nufi hanyar komawa gida. A lokacin kuma wani daga cikin sojojin ya yi waya gida a kan wasu jami'an su taho akwai matsala, a hanya Bilal ya ci karo da motocin jami'an gidan nasu wajen motoci goma, umarni ya yi masu a kan su juya ba wasu ?an ta'addan azo a gani bane.
Ba musu suka juya suka takewa Bilal ?in baya suka nufi gida. Wannan shi ne abin da ya faru da Ramish ?in.
To bari mu le?a wani part ?in kuma mu ga wani hali suke ciki. Amma kafin nan meyasa suke son kafin su kashe Ramish sai sun kamashi sun kai shi in da suke? Da suka gagara kamashi ?in ne suka fara yun?urin kasheshi kada damar ta wucesu, sun fa san kama Ramish yana cikin hayyacinsa ba abu bane mai yuwuwa ina ga shiyasa suka ?ullo mashi ta wata hanyar, to fatana dai ni kam Allah yasa RAMISH ?in yana raye, bari mu le?a wani part ?in dai mu gani.
_________________________________????
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 1/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.