Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 17

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 17

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 17: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 17. ?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ?????…

3,351 words

?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????

??STEP TWO....??????

E______________13 and 14

FOREST??

Mamma ta shiga tashin hankali da damuwa sosai na ganin halin da Kamran ya shiga, yau tsawon kwana bakwai kenan ya ki ya yarda ya ci komai, tun yana rashin lafiya ka?an ka?an har abin tazo ta fi karfin sa, yunwa ba wasa ba, tuni ya fita daga hayyacinsa ga shi da kafiyar bala'in, ya fi mammar tasa iya kafewa a kan abu, komai wuya komai da?i idan ?an tahalikin nan ya yi magana baya canzawa, shi burinsa kawai ya mutu ya huta, Allah mun gode maka da kayomu a musulmai, muka taso cikin ni'ima mai girman da babu wanda yake da shi sai musulmai, Alhamdulillah.

Mamma fa da taga da gaske Kamran zai yi wa kansa illah, dan a halin da ake ciki yanzu yana zube ne ko magana bayayi, gaba?aya ya fita hayyacinsa, ga idanunsa a datse gam yaki bu?e su ma bare suyi four eyes da mamman zuciyarsa ta karaya, suna rufe ruf, yanzu fa sai idan mammar ta ?aga shi ko ta kwantar, duk wani karfi na jikinsa ya kare.

Da taga da gaske zai iya mutuwa sai tsoro ya shigeta, ta tsorata sosai ta yadda ta fara nemanwa kanta mafita, tana ganin kamar idan ta kyaleshi ya je nemansu Pretty or mahaifinsa fa to kamar ta sallama shi ne, gani take yi kamar sai dai ta nemi wani ?an ba dai shi ba, kaunarsa yasa bata son ya fita, tana jin tsoron rabuwa da shi kamar hauka.

A kusa da shi ta shigo ta zauna hannunta ?auke da kayan abinci kamar yadda ta saba kawo mashi, wuka tasa ta yanke igiyar da ta ?aure shi da shi ?in. Duk in da ta ?aure shi wajen igiyar ta shata layi, da yake yana da hasken fata, sai zanen igiyar ta fito ?aro ?aro kamar menene, ya yi ba kyan gani, wani wajen kam ma ya ji mashi ciwo har da jini.

Ganin yadda igiyar ta lallata mashi jiki ne yasa mammar ta fara nadamar meyasa ta ?aure shi? Gaskiya bai cancanci irin wannan hukuncin daga garetaba, duk da su ba musulmai bane, a irin renon da ta yi mashi na rashin imani ma duk ya danne ya yi mata biyayya a matsayinta na mahaifiyarsa, abin da mamaki gaskiya, ita kanta ta jinjina mashi sosai, duk yadda ya kai ga kaunar Pretty kuma yana da damar da a lokacin zai iya kwace kansa ya gudu ya je nemanta ?in, amma bai yi hakan ba, ya daure ya bi mammar tasa dan baya son zuwa ko'ina ba tare da izininta ba. Tuna hakan yasa ta fara tunanin bata kyauta mashi ba, tsawon shekaru yana bin umarninta bai ta?a sa?awa ba, duk abin da ta ce shi yake yi, yanzu ya nuna abin da yake so meyasa ba zata bi ra'ayinsa ba? Ai a yanzu ya kawo karfi, ko ya bu?aci soyayyar mace shi ma ai bai yi laifi ba.

?augo shi ta yi ta zaunar, ya kasa iya zama sai langwa?ewa yake yi yana ?o?arin sulalewa ya kwanta against, dan bashi da karfi ko na miskala zarratin. Cikin azama ta jinginasa da jikin bangon dutsen, murya a sanyaye ta fara ?o?arin rarrashinsa, dan tasan yana jinta, sai dai bata san cewa baya cikin hayyacinsa ba, kunnuwansa dai suna jin komai.

Ta yi magana mai ?an tsawo ko motsawa daga in da yake bai yi ba bare a sa ran ya ji abin da ta ce. Ganin hakan yasa ta ?auko tea mai zafi na green tea leaf ta fara ?o?arin ?ura mashi, dan tasan yunwa ce ta yi mashi over.

Wajen ?ura mashi sai da suka kusa kokawa, dan kuwa baya cikin hayyacinsa, yana jin abu mai zafi a bakinsa ya fara ?o?arin furzarwa ya kwaci kansa, bashi da karfi ko ka?an, hakan yasa Mammar ta danne shi ta fara ?ura mashi da gasken gaske kamar yaro, dan dole ya fara ha?iyewa ba dan ya so ba, ta toshe mashi hanci ne kungakuwa dole ya ha?iye.

Sai dai ko da ta samu ya sha ba dayawa ba tana cire cup ?in ya fara tikar amai kamar zai amayar da ?a?an hanjinsa, bata wani damu da hakan ba, dan tasan fin hakan ma zai aikata, ai ya ji yunwa over.

Basket ?in magungunanta na gargajiya ta ?auko, cikin zafi jini ta fara ha?a mashi magani babu wasa, jikinta har wani irin tsuma yake yi. Haka ta rin?a ?ura mashi ha?e ha?en nata babu kama hannun yaro, yanzu dai burinta ta ga ya warke ya koma kamar da.

In short sai da ta ?auki kwanaki uku tana ta faman jinyarsa, ta wahala shi ma ya wahala, banda tarin danasani babu wani abin da yake cikin ranta, duk ta shiga damuwa na wuce misali, da kyar da su?in goshi ta iya samu ta shawo kan matsalar tasa ya dawo daidai. Sai dai kuma ko da ya dawo dai'dai ?in baya magana, dama can kun san ba yawan magana ne da shi ba, yanzu da ya yi ciwon sai abin ya kara tsananta, abinci ma a baki take bashi, yana kar?a ya ci sai dai baya ce mata ko uppan, abin da yasa yake kar?ar abincin ma dan ya ga tashiga damuwa ne sosai, har rama ta yi sosai, yana kaunar mammar tasa sosai, kuma yana yi mata biyayya sosai da sosai, son da yake yi mata ya kai ya iya sadaukar da komai nasa dan ita, hakan yasa ya hakura yake ?o?arin cire duk wani tunanin su Pretty a ransa, dan Mamma ita ce duniyarsa, ita ce komai nasa, tun bai san kansa ba take kula da shi fiye da kanta, komai wuyar da zai sha ya gwammaci ya tabbata cikin wannan wuya amma bai sa?a maganarta ko ?aya ba, ba zai gaji da yi mata biyayya ba, badan ta kula da shi ta rainesa ba yaushe zai girma har ya san da su Pretty a duniya? Da ta yi watsi da rayuwarsa ya makomarsa kenan? So Mamma ita ce gaba da komai kafin sauran abubuwa su biyo baya.

Allah sarki, da ni da ku dukka mun san mantawa da su Pretty a rayuwarsa ba abu bane mai yiwuwa, sun zame mashi wani ?angare na rayuwarsa, zai azabtar da zuciyarsa ne kawai a banza, amma mantawa da su ba abu bane da zai yiwu mashi.

Ganin ya kara samun sauki sosai ne yasa ita ma Mamma ta samu sukuni har ta ?an fara mai da jikinta. Sai dai rashin maganar nan tasa ya dameta sosai, ba um bare uh uhm, ko ta yi mashi magana sai dai ya ?aga mata gera ko kai, abin yana damunta sosai da sosai.

Kamar kullum zaune yake a saman gadonsa ya ha?a kai da gwiwa yana aikin tunani, ba tunanin kowa yake yi ba face na su Pretty and mahaifinsa, yana son sanin wanenen babansa? Wannan itace burinsa a yanzu.

Har Mamma ta shigo cikin ?akin bai ji shigowarta ba yana can yana tunani, kafin ta shigo kuma sai da ta tsaya almost 10 mins a bakin kofa tana kallonsa, ganin bashi da niyar ?ago kai ya kalleta ne yasa ta ?ariso ciki.

A bakin bed ?in ta zauna tare da kai hannu ta ?an shafi wannan tulin uban gashin kan nasa. Yana jinta amma bai ?ago kai ba, dan kwata kwata baya son motsawa komai ?an?antarta daga in da yake, a yadda yake zaunen nan ba ?aramin da?in zaman ya ji ba.

"Kamran lafiya kake kuwa?" Ta fa?a a sanyaye.

Kai kawai ya gya?a mata alamar e yana lafiya ba tare da ya ?ago ba. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sake cewa. "Tashi ka je ka yi wanka". Nan ma girgiza mata kai ya yi alamar a'a ba yanzu ba. Wannan hali da yake yi mata na rashin magana sai dai girgiza kai yana matu?ar damunta, sannan halin da yake ciki yana matu?ar ?aga mata hankali ba ka?an ba, kawai dannewa take yi.

"Kamran meyasa kake mun haka ne? Kasan dai duk abin da zan yi a duniya ina yinsa ne domin kai ko? Domin farincikinka nake yin komai! A takaice ma dominka nake zaune a cikin wannan dajin na tsawon shekaru, meyasa ka kasa gane hakan? Meyasa ka kasa gane cewa uwa tana sadaukar da komai domin ?a?anta? Meyasa ka kasa gane cewa uwa ba zata ta?a cutar da ?a?an da ta haifa ba? Meyasa a yanzu zuciyarka take ?o?arin za?ar wasu da ka ha?u da su daga baya ka manta da wadda ta haifeka ta sha wahala a kanka? Ni nasan da a ce in ka tafi babu wata ha?ari to da ba wanda zai kai ni murnar da ?aukin ganin cewa ka nemo Prettyn taka, amma ka kasa gane hakan, why my son, why?". Ta dagata da maganar tana mayar da numfashi tare da kura mashi idanu.

Ba tare da ya ?ago kan nasa ba ?asa ?asa muryarsa bata fita sosai ya fara magana. "Mamma ki bar maganar su Pretty, saboda ke na hakura da su, saboda farincikinki na mance da su, ki sani Mamma kin fiye mun su, kin fiye mun komai a rayuwata, sai da kika kula da ni na girma na zama mutun sannan na ha?u da su, da baki kula da ni ba a ina zan girma har na san su na kaunace su, dan haka ki dai'na zancensu, ki manta da su kawai, ni ma na ciresu a raina....."

Kasa ?arisa maganar ya yi sakamakon kuka da ya kubce mashi mai karfin gaske, Allah ya gani tilastawa zuciyarsa da yake yi a kan ya manta da su Pretty yana cutuwa sosai kuma ba abu bane da zai yiwu gaskiya, kawai dai mahaifiyarsa ta wuci wasa kuma ta wuci tunanin duk wani mai tunani a ransa ne yasa yake ?o?arin yi mata wannan sadaukarwan da in ya cigaba da matsawa yana iya rasa ransa.

Ita kuwa Mamma tana son ganin farincikin ?an nata ?aya tilo a duniya amma kuma fargabar rasa shi yasa ta gwammaci ganinsa a cikin bakinciki.

Wani irin tausayinsa ne ya kamata, ita tasan zafin so, kuma tabbas soyayya ta gaskiya kamran yake yi wa Pretty, taga hakan a cikin idanunsa tun ranar, tun da take bata ta?a jin zuciyarta ta karaya ko ta ji tausayin wani abin ba sai yau a kan ?an nata, musamman yadda ya ce ya hakura da first love ?insa yarinyar da yake matu?ar kauna saboda farincikinta, tsabar zuciyarsa na son Prettyn ma da kuka ya kai karshen maganar ya hakura da ita, nan take zuciyarta ta ji in ta yi mashi haka ta rabasu magana ta gaskiya bata yi mashi adalci ba, ta cutar da shi sosai, in dai har zai iya sadaukar da soyayyarsa saboda farincikinta meyasa ita kuma ba zata so ta cika mashi burinsa dan ya yi farinciki ba? Abubuwa nawa ya yi ta sadaukarwa wa?an da yake kauna saboda ita? Ba zasu kirgu ba, ya sha hakura da abu saboda ita, ya sha danne zuciya ya yi mata biyayya koda baya so, meyasa ita yanzu ba zata hakura ta mashi abu ?ayan nan ba? Meyasa?. Haka ta rin?a fa?a a cikin zuciyarta.

Shesshekar kukansa ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka. Matsowa kusa da shi ta yi cikin karayar zuciya tare da raunin murya ta fara magana. "Sam ba zaka hakura da Prettynka ba, ka je ka ?aukota a koma inane, ka dai'na kuka ya isa haka, yau ina maka izinin ka je ka ?aukota, nasara tana tare da kai my son". Ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka.

Sai a lokacin ya ?ago kansa, idanunsa a datse gam, hawaye sun wanke mashi fuska, gefe da gefen kunnensa dukka ya jike sharkaf da gumi, ga kuma wani zufar tana cigaba da tsasstsafo mashi, in ka gansa a haka sai ya baka tausayi sosai, mai saurin kuka ma sai ya zubar mashi da kwallah.

Girgiza kai ya shiga yi hawaye na cigaba da gangarowa da gudu daga idanunsa zuwa saman face ?insa, tamkar am bu?ewa ruwa hanya.

Saboda kuka da ya ci karfinsa da kyar ya iya bu?e baki zai yi magana. "Bana da bu?ata Mamma, no need, saboda nasan Pretty ta mutu, ta mutu Mamma, nima mutuwa kawai nake son yi a yanzu, dan nasan na rasa Pretty, babu wani amfanin fita nemanta". Yadda yake magana sai ya baka tausayi, yana maganar ne kawai amma babu wani kuzari ko sanyi a muryarsa, bawan Allah ya zama kaman zararre, ga idanu a datse yaki bu?e su.

Nisawa ta yi tare da furzar da iska mai zafi daga bakinta. "Bata mutu ba, kuma ba zata mutu ba, saboda bazaka ta?a fa?uwa ba my son, komai kasa a gaba sai ka yi nasara, kai ?in jinin nasara ne yake gudu a jikinka, nasara a jininka yake, babu fa?uwa a jininka, mahaifinka bai ta?a fa?uwa ?asa ba a komai da ya sanya a gaba, mahaifinka wuta ne mai balbali, jarumi ne, daga ni har mahaifinka nasara muka sani kuma a jininmu take, dan haka zaka yi nasara, ka dai'na tunanin fa?uwa, idan ka nuna sarewa da gazawa hakan yana nuni da cewa kai ba jinin damisa bane! Dan damisa bai san sarewa ba!".

Wani irin bu?e idanunsa ya yi a ?ari jin cewa yau da bakinta ta ambaci cewa yana da mahaifi! Abin ya ru?ar da shi ya kuma bashi mamaki.

Cigaba da magana ta yi. "Ban so na sake yin magana a kan mahaifinka ba a rayuwata, amma yau kasa na yi magana a kansa saboda Pretty, ka je yarona, kaje zaka yi nasara dawo da Pretty, na yarjema kaje ka kawo mun ita nan".

Wani irin nisawa ya yi tare da furzar da iska, nan take hawayen dake zarya a saman face ?insa suka dakata cak, wani irin wasai ya ji a jikinsa, harshensa da yake ji ta yi mashi nauyi yin magana a ?azun ne ya ji yanzu ta sake shi wasai, cikin tsantsar ?aguwa da son jin wanenen mahaifinsa ya ce. "Mamma ki bani labarin babana, and please ki barni na je garesa ko da sau daya ne na gansa da idanuna kinji?".

?an daure fuska ta yi kafin ta ce. " kamran ba zan baka labarin babanka a yanzu ba, ni dai Pretty zaka je ka ?auko mana a yanzu".

A take ya ri?o hannayenta a cikin nasa, muryarsa har sarkewa yake yi saboda saurin magana ya furta. "Please Mamma na ji ba zaki bani labarinsa ba, to please ki gaya mun in da yake na je na gansa, na yi maki alkawarin ba zan yin mashi magana ba ganinsa kawai zan yi na dawo".

Wani irin canzawa fuskarta ya yi daga annuri izuwa zunzurutun ba?inciki, idanunta a take suka yi jajir, ji take kamar ta fashe da kuka. Amma sai ta danne ta ce. "Shikenan Kamran, zan barka ka je neman nasa, amma ba zan ta?a gaya maka in da yake ba, ka nemosa da kanka, idan har jinin damisa ce take gudu a jikinka to tabbas ba makawa zaka kai kanka in da yake, dan damisa baya sanya kai a waje bai cinma in da yake da burin zuwa ba, dan haka ka kaikanka gare shi".

Cike da zumu?i ya ce. "Mamma ni kuma na yi maki alkawarin tabbas zan kai kaina gare shi, tabbas zan nemo babana". Ya yi maganar tare da sake fuskarsa kamar ba shi yake kuka a yanzu ba, farincikin jin cewa yana da uba kuma Mamma ta bashi izinin isa ga babban nasa yasa ya mance da duk wata ?unci da yake ciki, Allah sarki iyaye kenan.

"Mamma in je in shirya in tafi?". Ya yi maganar yana kallon face ?inta.

Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a kafin ta ce. "Kamran ka nutsu, mahaifinka ba yadda kake tunani yake ba, ya wuci tunaninka, zan barka kaje neman nasa ne ma domin ka matsa mun kuma ina son farincikinka, tabbas nasan zaka iya isa garesa, sai dai kuma kafin na barka ka tafi ina da shara?i guda ?aya".

Da sauri ya ce. "Wani irin shara?i ne Mamma? Ki fa?i koma menene zan yi na yarda".

Nisawa ta yi kafin ta fara magana. "Shara?in shi ne zaka yi ?addakama, ba zaka tafi a haka ba, ba zaka tafi da kamanninka ba, dan bana son kowa ha ga face naka".

"Mamma why to?". Ya fa?a da alamar mamaki a saman face ?insa.

"Because duk wanda ya san babanka idan ya ganka zai gane cewa kai ?in ?ansa ne, kuma kaga alkawari muka yi da kai a kan ba zaka bari kowa ya san kai ?an damisa bane, sannan kuma kusantar hanyar in da babanka yake da ainahin kamanninka ba abu bane mai yiwuwa, dan kafin ma ka kai garesa za'a iya hallakaka, wannan dalilin yasa na ?oye maka wanenen kai, kuma saboda haka yasa nake koya maka fa?a dan watarana ko bananan ka kwaci kanka a koma inane, nasan da cewa ko ba jima ko ba da?e mutanen mahaifinka zasu cinmana, in ma su ganmu a tare ko kai ka ?ai, shiyasa na ke koya maka kare kanka da kuma kwatar kanka a koma inane, dan haka dole sai ka yi ?at da kama idan kana son na yarda ka tafi neman babanka".

Shiru ya yi yana jinjina wannan al'amari, Mamma ta gindayar da shi ta kuma ru?ar da shi, shi yarasa to wani irin family ne da shi........ gaskiya nima narasa wani irin rikitarwa ne wannan.

"Mamma na yarda da shara?inki, amma taya za'ayi na ?oye kamaninna kuma?".

A takaice ta ce. "Kai dai jeka ka yi shirin tafiya ninzan ?atar maka da kamannin naka". Tana kai karshen maganar ta mi?e da sauri ta bar ?akin dan bata son yaga hawayen da take ?o?arin dannewa. Allah sarki bata son rabuwa da shi, tsawon shekaru 26 kenan yanzu kullum ba dare ba rana suna a tare, bai ta?a matsawa daga kusa da ita ba, duk in da zai je a fa?in dajin nan dai zai dawo wajenta, ba dan su Pretty bama shi baya zuwa ko'ina, bayyanar su Pretty suka koya mashi fita har ya je wajensu ya yi awa ?aya zuwa biyu.

Kuka ne sosai mai karfi ya zo mata, ?akinta ta shiga ta fara murzan kuka sosai, rabuwar uwa da ?a babu da?i ko ka?an. Shi kuwa tashi ya yi ya fara shiri, har wani karfi ya ji ya zo mashi.

Duk wani abin da su Pretty suka bashi sai da ya ?auka, ya ?auki wukarsa sannan ya ?auki al'qura'ani mai girma da Sweetie ta bashi. Ya dai gama shirinsa tsab abinsa bai san cewa Mamma tana can tana kuka ba.

Bayan ya kammala duk abin da zai yi ya fito ya nufi in da take. Jin motsin yana nufo wajenta yasa ta yi saurin goge hawayenta tare da fara fito da wasu abubuwa nata dan ta ?atar mashi da kamanni.

Cike da murna ya shigo cikin ?akin nata, sai zumu?i yake yi zai je ya duba su Pretty daga nan ya ?aukesu su je neman babansa, a lissafinsa ba zai iya tafiya ya barsu a dajin ba, zai je ya ?auki Sweetie ya kawota wajen Mamma ?in tun da ita bata gani, ita kuma Pretty ya tafi da ita neman babansa.......... Tab da kuwa akwai cakwakiya in dai da Pretty zaka tafi neman baban naka.

Zaunar da shi a bakin gadonta ta yi tare da ?auko abubuwan nata ta fara aikin ?atar mashi da kamanni. Tas ta yanke mashi dogon gashin kansa sa?anin kullum da take rage mashi tsawon, yau dukka ta yanke, sannan ta aske mashi sajensa ma tas da wani irin ?an ?aramin wu?a na gold mai kama da aska sai kaifin bala'i, tun da yake da ita bai ta?a ganinta da irin wa?an nan abubuwa ba, ko daga ina ta samosu yau kuma? Ya tambayi kansa, gudun kada ya yi mata laifi ta ce ta fasa ya zauna a gida yasa ya ja bakinsa ya yi shiru bai tambayi daga ina ta samo wa?an nan abubuwa ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull