Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 18

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 18

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 18: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 18. Bayan ta aske mashi sajensa sai ta aske gashin gera ma, ta sanya mashi wani…

3,367 words

Bayan ta aske mashi sajensa sai ta aske gashin gera ma, ta sanya mashi wani irin powder a wajen da ta aske gashin, wlh sai ya canza kamanni gaba?aya, kun san idan aka cirewa mutun gashin gera yadda yake canzawa kamar ba shi ba. Haka dai ta zage ta canza mashi kamanni, wlh ba zaka ta?a zaton shi bane. Ta ?auko wani dogon towel da ta sa?a ta na?a mashi rawani da shi, ya fito kamar irin larabawan ?asar Iraq ?in nan, ba zaka ta?a cewa shi bane.

Fatan nasara da fatan alkhairi ta yi mashi, sannan ta bashi umarnin tafiya. Duk zumun?in da yake yi na son tafiya sai ya ji jikinsa ta mutu da ta ce ya tafi, nan take ya ji idanunsa sun cika da kwallah, damuwa ce ta bayyana a saman fuskarsa. Juyowa ya yi suka kalli juna, ganin idanun Mammar tasa ms a cike da kwallah yasa na sa hawayen da suka cika mashi idanu suka fara zubowa.

"No Kamran no, kada ka yi kuka, ka tafi kawai, sai dai ina son ka mun alkawarin zaka dawo gareni! Ina zaune ina jiranka".

Matsowa ya yi tare da ri?o hannayenta. "Mamma zan dawo gareki, duk wuya duk da?i zan kasance da tunaninki a duk in da nake, please Mamma kema kada ki yi kuka kin ji?".

Hug na juna suka yi, hawayen da take ?o?arin dannewa ne suka fara zubo mata, tana jin kamar kada ta barshi ya tafi, dan tana ganin kamar za'a gane shi ?an cikin damisa ne a kashe shi, tana jin kamar zasu rabu rabuwa ta har abada kenan.

Sun jima rungume da juna suna kuka kafin daga karshe ta yi ta maza ta raba jikinsu tare da ri?o hannunsa ta fito da shi waje. A wajen ma tsayawa suka yi tana goge mashi hawaye shi ma yana goge mata nata, da kyar suka iya rabuwa bayan ta bawa Rocky amanarsa.

Da gudu ta juya ta koma cikin gida shi kuma ya nufi kasa har lokacin ya ?asa dai'na kuka, Rocky ya rufa mashi baya suka tafi a tare. Rocky da Kamran akwai amana, wannan rashin lafiya da Kamran ya yi Rocky ma har ?ar rama ya yi, saboda baya fita ya fatauci nama sosai, koda yaushe yana zaune a bakin kogon nasu yana dakon jiran fitowar Kamran ?in tun da ba halin shiga ciki.

Kai tsaye wajensu Pretty ya nufa cike da kaguwa na son ganinsu.

TO KAMRAN ALLAH YA TSARE HANYA YA KUMA HA?AKA DA CIKAN BURINKA NI DAI SHI NE FATANA????

_____________________________?????????

DARK WORLD???????

Saboda kuka da wahalar da ta sha yasa ta yi barci mai nauyi wanda bata farka ba sai can wuraren karfi 9 na dare. Tana farkawa kuma abin mamakin da bata ta?a zato ba a rayuwarta shi ne ta farka idanunta suna gani, tamkar a mafarki ta ji kuma take ganin abin.

Tana farkawa kuma da kyakkyawar fuskar Ronnie ta fara cin karo, yana tsaye a gaban gadon nata hannunsa ri?e da wani allura da ya ha?a yake son yi mata, ko alluran menene oho masu, idanunta dai ba aiki suka yi mata suka bu?e mata su ba, su ka?ai suka san me suka yi mata idanun suka bu?e. One thing about Ronnie shi student ne. Har yanzu bai kammala karatu ba, kuma yana zuwa school, sannan yana ?aya daga jikin ?aliban likitoci da Dark world suke alfahari da su, yana da kwazo ta fanni karatu sosai, ya kerewa tsaransa. So duk lokacin da yake da class yana zuwa school, suna da babban university da black tiger yasa aka gina masu, ga manya manyan asibitoci da dai sauransu, shi fa black tiger kullum burinsa ?asarsa ta zamana tana da komai na more rayuwa, ta zama number ?aya, sai dai akwai ?an banzan zalinci kuma kamar kafurin farkon zamani.

So Ronnie kwararrene a fannin nan na likitanci, ri?e yake da allura zai yi mata.

A duniya Sweetie bata da burin da ya wuce idanunta su bu?e ta yi tozali da Kamran, sai ga shi yau sun bu?e ta yi tozali da madarar kyau da ya take na Kamran, sai dai kallon kamar idon sani ta yi wa Ronnie ?in, ta ji kamar ta sansa.

Mamaki da al'ajabi ya hanata motsawa daga in da take kwance, wai yau itace idanunta suka bu?e tana gani? Kai abin da mamaki, Pretty and Kamran ne kawai a cikin tunaninta, sai ayyana yadda zata kalli Kamran take yi, Pretty kam already ta san ya kamanninta yake, Kamran take mararin gani. Shekara bakwai tana tare da Pretty idanunta suna gani, so tasa kamanninta saura Kamra

Tuna cewa ga fa in da take yasa idanunta suka ciko da kwallah, zuciyarta na sanar da ita cewa shikenan ba zata sake ganin Pretty and Kamran ba. Kan kace me hawaye sun fara zuba daga idanun nata.

Ronnie bai lura da hawayen nata ba bai ma lura da ta farka ba, hankalinsa naa kan wanna kyakkyawar yarinya mai kula da Sweetien da ta shigo yanzu. Jikinta na sanye da wani guntun wandon jeans baki da t-shirt mai laushi pink color wanda ya tsaya mata a iya kunkuminta, ta ?aure gashin kanta ta zuba jelar a baya, ta bar wani guntun gashi a gaban goshinta wanda ya ?ara mata kyau sosai, fara ce tas amma bata kai Ronnie ba, a gaskiya ma idan tana gabansa za'a iya ce mata bakar fata, dan shi fa koreans ne, jikinsa kamar madara, tas yake.

?arisowa kusa da shi yarinyar ta yi, ?an rungumar juna suka yi irin welcome ?in nan kafin ya sumbaci kumatunta, ita ma sumbatar nasa lallausan kumatun ta yi. A shekaru wannan yarinya ba zata wuci 12 years ba, sai shegen kyau irin na mutanen cikin Dark world ?in.

"Beb go and bring food for her, ina ga yanzu zata iya farkawa......." Bai kai karshen ba idanunsa suka sau?a a kanta tana hawaye.

A hanzarce ya ce. "Kash beautiful Queen why are you crying? Baki san kuka a yanzu isn't ur own bane? Kina son kuka ya yi affecting na idanun naki su sake rufewa ki daina kallo ne? Please stop this crying because bana son ki dai'na kallo". Ya kai karshen maganar tare da zama a kusa da ita ya ajiye alluran hannunsa a gefe ya hau goge mata kwallah.

Juyawa Floria ta yi ta nufi room door ba tare da ta yi magana ba. Shi kuma bayan ya goge mata hawaye ya ?ago ta dan ya ?ara rarrashinta da kyau. A kirjinsa ya mannata yana ce mata sorry, sannan ya ?auko injection ?in da ya ajiye a gefen, cikin wannan sanyayyar voice ?in nasa ya fara yin magana tare da matso da bakinsa dab da kunnenta, dan a hankali ya yi magana. "Bari na yi maki injection a jijiyar hannunki ko?"

Ita dai har yanzu gani take yi mafarki fa take yi ba gaskiya ba, gani take yi kamar idan ta farka zata ga idanunta sun rufe, haka yasa ta kafe shi da idanu tana kallonsa, dan ya yi mata mugun kyau, bata son ta yi missing wannan kyau bata gani da kyau ba ta tashi daga mafarki da take zaton shi take yi taga ta koma makauniya.

Sosai take ta kallon kyansa bata ce ko uppanba, shi kuma kallon kalar idanunta da suka burge shi yake ta yi, ya ji kamar ta bashi idanun nata ya ?ara kyau kan kyau.

Shigowar Floria cikin ?akin ne yasa Ronnie kawar da kallonsa daga kanta tare da ?auko alluran ya gyara hannunta da nufin ya yi mata. Tana ta kallon shi ita kuma bata ankara ba bata ji time ?in da ya ?aure hannunta ya nemi jijiya ba sai ji ta yi zafin tsira alluran ya ziyarceta.

Wani irin ?an?anme shi ta yi tare da fasa kuka. Zare injection ?in ya yi a hankali tare da fara ce mata sorry. Ita kuma Floria ta ?aura katon glass tray ?in abincin a saman carpet ta haye saman gadon ita ma. Ha?uwa suka yi ita da Ronnie suka rarrashi Sweetien har sai da suka tabbatar ta yi shiru. Sannan ne Ronnie ya rabata da jikinsa ya sauko ?asan gadon.

"Beb ki kula da ita ta ci abinci sai ta yi wanka ku zo mu je muga wasan su Ovil". Yana gama magana bai jira amsarta ba ya nufi waje.

A kowace Daula akwai jarumi da yake gaba da kowa. To a Daular Dark World dai Ronnie ne jarumin da yake cinye duk wata gasar da black Tiger zai sanya, yana da karfi sosai da kuma dabara, ga ilimi, idan suna Wrestling in dai ya shiga shi zai yi nasara, kasancewar suna cikin ?ata ba musulmai bane yasa a duk lokacin da ya yi nasara zai kashe wanda ya fa?in kamar yadda yake a dokance ba tare da ya ji wani ?ar ?ar ba. Kakkaifar wu?a yake ?auka ya datsewa wanda ya fa?i ?in wuya ba tare da tausayi ko makamancinsa ba, sai dai bai cika shiga gasar ba, dama dan ra'ayin kansa yake shiga, sai ranar da yake cikin nisha?i yake shiga kuma ya yi nasara. Duk ?an'matan cikin birnin Dark world suna mahaukacin son suga zai yi wasa, suna son ganin wasan sa, domin idan ba'a wasa ba ba sa samun damar ganinsa, baya fita, ko school kaisa ake yi a mota mai tinted, kowa tana santin kyansa kuma tana kaunarsa, sannan suna son ganin wasan sa ne dan suka ga jarumta, jarumin gaske ne wanda yake da karfi.

Yana fitowa daga cikin ?akin suka ci karo da Delisha a kusa da ?akin ta nufo wajen. Harara ta wurga mashi ba tare da ta ce mashi uppanba.

Wani irin ?ayatatcen murmushi ya sakar mata har sai da dimples ?insa suka lotsa sannan ya kashe mata ido ?aya kamar wani tsohon kwarto. Hannunta ya ri?o tare da jawota jikinsa, a kunne ya ra?a mata cewa. "Sarkin fa?a sai ina kuma?".

Sake banka mashi harara ta yi, shi ko ya sake sakar mata wani lallausan murmushi, shi fa har da?i yake ji idan tana wannan hararar tasa, kyau take karawa.

"Sake ni in tafi ka ji?'. Ta fa?a a sanyaye kamar ba ita ce mai shegen tsiwa da fa?a ba.

"Haba mana beb kafin na sake ki gaya mun in da zaki je tukun nan". Yana magana yana wani lumshe idanu kamar wanda yake cikin yanayi.

"Wai kai meyasa a rayuwarka ka cika neman fa?a ne? Yanzu ina ruwanka da in da zanje?".

Matso da face ?insa dab da tata ya yi kafin ya ce mata. "Saboda haka nake, kuma ai ke da kanki kinsan ni jarumi ne dole na takali fa?a dan nasan zan kare kai'na na kuma kwaci kaina".

Cigaba da banka mashi harara ta yi tare da fa?in. "Wajen wannan yarinyar zanje".

"Dama ai na sani, kin ?ebo zafinki zaki je ki sauke a kanta ko? To zo mu je ki bani abinci a baki yunwa nake ji ka fin ki dawo ki je ki zalinci ?ar mutane". Yana kai karshen maganar bai bari ta yi magana ba ya sa?eta a saman shoulder ?insa ya nufi downstairs da ita.

Shi fa Ronnie idan ba su Delisha dake cikin Daular black Tiger ba baya kula kowa, a waje cikin birnin ?aukin ganinsa da ido ma kawai suke yi, bege jin zazza?ar voice nasa suke yi, saboda kowa yasan shi ne mafi kusanci da black Tiger, black tiger yana kaunarsa kamar me, kowa yana son ganinsa da ido, shi kuwa yana nan yana biyewa su Delisha ko a jikinsa, bai ma san ana haukar son ganinsa a cikin birnin ba. Idan ya fita wajen gasa ya zama cikakken jarumi da babu biyunsa a kaf fa?in birnin, idan kuma ya dawo cikin Daular ka gansa tare da su Delisha sai ya zama kamar na mata wanda bai da karfi ko ka?an haka yake.

?angaren su Sweetie kuwa

Sosai Floria ta hau lalla?a Sweetien a kan taci abinci, amma ta kafe a kan ba zata ci ba har sai taga Pretty and Kamran. Da kyar ta iya shawo kanta ta yarda zata ci, sai da ta yi mata karyar gobe da safe za'a kawo mata Pretty and Kamran ?in nata, sannan ne ta yarda ta ci.

Mandi rice Floria ta zuba mata ?an dai'dai a plate, sannan ta zuba mata watermelon juice a wani ha?a??en kuma tsadadden cup. ?an ka?an ta ci abincin saboda yunwar ta rigada ta yi mata yawa, ka?an ?in nan da ta ci ma har wani mur?awa cikinta yake yi saboda yunwar.

Bayan ta ci ta sha ne Floria ta ce taje ta yi wanka. ?asa iya mi?ewa ta yi har sai da ta taimaka mata ta ri?eta. Bayan ta mi?ema sai da ta taimaka mata izuwa bakin toilet ?in.

A bakin ta saketa ta juya ta dawo, ta barta da nufin ta ?arisa shiga cikin toilet?in, sai kallon ?akin take yi, komai ya ru?ar da ita, dan Allah yasa tana da nutsuwa sosai ne yasa ta danne tsoronta da kauyancinta ha?e da al'ajabinta tana dai bin ?akin dakallo, da Pretty ce ai da ta yi masu hauka, dan bata ta?a ganin irin wanna ?aki ba.

A hankali ta ja kafafunta da suka yi mata nauyi ta ?arisa shiga cikin toilet ?in. Tsantsar tsoro ne cike fal a cikin ranta, gani take kamar ?akinma gaba?aya zai ruguzo mata a kanta, gani take kamar zata fa?i ?asa ta ?asa ganewa. Amma dai ta yi jarumtar danne tsoronta.

Tana shiga cikin toilet ?in Tv dake manne a bango yana magana ya haukatata. Ga wata kyakkyawar ?ar tsana dake ta kusa da kofar shigowa wadda take amfani da battery ta yi mata welcome ta hanyar furta hakan da turanci. ?ar tsanan ?ar babbace da zata kusa kaita tsawo, kawai ta ce mata welcome, unexpected ta ji maganar.

Ai a wanna karon tsoron nata yaki dannuwa, da gudun gaske ta juya ta nufo waje tare da kurma ihu wandan sai da ta tsorata Floria tasa ta ta kusa rugawa a guje. Kai tsaye Florian ta nufa tana ihu.

Da yake mutanen birnin Dark World ba dai jarumta ba sai Floria ta tsaya tare da tambayarta me ya faru take wannan ihu.

?asa yin magana ta yi sai nuna mata toilet da hannu take yi tana kuka. Ri?ota ta yi, dan ta fahimci Sweetie fa ?ar kauyece bata san komai ba shiyasa ta tsorata. Hakan yasa ta kama hannunta tana gaya mata ta yi shiru ba komai, haka ta rakata har cikin toilet ?in. Gane cewa bata san komai bane yasa ta tsaya ta hau nunnuna mata abubuwan da yadda zata yi amfani da su.

Ai ina Sweetie ta ce bata san wannan ba, Floria ba zata bar wannan toilet ?in ta barta ita ka?ai a ciki ba, sai dai ta hakura da yin wankan su fita a tare. Da yake suna son ta yi wankan sai Floria ?in ta ce to ta yi wankan bari ta jirata.

Nan ma kuma sai ta ma?e mata kafa?a a kan a'a ita ba ta yarda ba, ba zata iya cire kaya a gaban kowa ta yi wanka ba, ko da take makauniya idan Pretty ta rakata wajen da zata yi wanka tafiya take yi ta bata waje, dan haka ita ba zata cire kayanta a gaban Floria ba. Nan ta ta fara sakawa Floria ciwon kai, zata fita ta ce ba haka ba, zata zauna nan ma ta ce ba zata cire kaya a gabanta ba, to wani irin masifa ce wannan?.

Dafe kai ta yi tana tunanin ya zata yi da wannan yarinya? Ga shi dai shekarunsu kusan ?aya, da ?an watanni ?alilan Floria zata fita, amma ta kafe ita fa ba zata cire kaya a gabanta ba, abin ya bawa Floria mamaki sosai, dan ita dai tasan a tsakar gida ma mamanta tana yi mata wanka kafin Ronnie ya ?aukota ya dawo da ita cikin Daular black Tiger, kuma da dawowarta cikin Daular bai wuce 1 year ba, so da girmanta ma a tsakar gida ake yi mata wanka, kowa ya shigo zai ganta kuma ba abin da ya dameta, yau taga sabon salo wajen Sweetie mai kunyar nuna jikinta a gani. Floria fa ba marainiya bace, da mamanta da babanta a raye, kuma suna cikin birnin Dark World, Ronnie ne kawai ya ga ta burgesa ya ro?i alfarman da black Tiger ya sanya a ?aukota ta dawo cikin Daular da zama, shi ne sanadiyar dawowarta cikin Empire ?in.

Da kyar da su?in goshi Sweetie ta yarda Floria ta fita ta barta a ciki. A gaggauce ta yi wankar, ruwa ta kwarara kawai, ba wani fitan da ta yi, sam bata yarda ta kunna shower ko wani abin ba, fanfo ta kunna ta tari ruwa a borket ?in da ta gani a cikin toilet ?in, ruwan da sanyi haka ta zuba a jikinta daga kai bata surka da na zafi ba, jikinta duk dau?a, da yake tana tsoro sosai ne yasa ta kwara ruwa bata wanke dau?ar ba ko soso ma bata nema ba.

A gurguje ta sanya kayanta ta fito. Sai muzurai take yi, a tsorace take da komai na ?akin sosai.

A zaune saman gadon ta isko Floria, ganinta yasa ta mi?e ta sau?o ?asa tana binta da kallo.

"Har kin yi wankar?". Ta fa?a tana mai da kallonta kan yatsun kafar Sweetien wa?an da suke dogaye ba sosai ba, ga su farare tas suna kyalli gwanin birgewa, yana yin yatsun nata masu ?aukar hankali, ita kanta Floria ?in da take mace sai da ta ji Sweetie ta yi mata, ta tafi da imaninta, a hakan ma wai dan cikin wahala suka taso, da sun samu hutu kamar na wannan Daula ai da anyi kyau na ban mamaki. Ga gashin kanta da yake golden white ta ji?a shi da ruwa ya kwanto a hayanta wasu sun zubo mata ta gaba, wayyo abin ba'a magana, sai ta ?ara tafiya da imannin mutane, sai ma ta ?an zaro idanu, wannan gurun wuyar tasu ita da Pretty yana matu?ar ?aukar hankalin duk wata idanu da zata sauka a kansu, suna rikita mutane sosai. Sweetie hasken fatarta ita da Pretty ya kai na Ronnie ko ma ya ?an ?ara shi ?a?an. A duk cikin birnin Dark world kuma ba wanda ya kai Ronnie ?in haske, to ku kwatanta ya hasken su Pretty yake kenan a ranku.

Katse su Ronnie ya yi ta hanyar shigowa cikin ?akin. Wani irin fa?uwar gaba ya ji lokacin da ya sauke idanunsa a kanta, tun da yake ganinta a kwance ko a zaune yake ganinta, yanzu dai tana tsaye a kan kafafunta, ga shi gashin kanta a wargaje bata tara shi ba saboda tsoro, ta fito ne kawai a guje dan kada wani abin ya kamata. Yanayin kayan jikinta kuma kayan sakar da Kamran ya basu ne, kun san yadda kayan yake idan baku manta ba, kuma bashi da ?an'kwali dama.

Sosai Ronnie ya zaro idanu yana kallonta, bai ta?a tunanin haka take da kyau ba. Kamo gashin kansa ya yi a in da ya dawo da shi ta gaba yana kallon na kanta. Nata gashin golden white mai matu?ar kyau ga sheki mai daukar idanu, nasa gashin kuma up white ne wanda ya fi nata haske sosai, sai abin ya ?ara burgesa sosai. Dama tun da ya sauke idanunsa a kan nata idanun ya kamu da kaunar idanun nata, sun burgesa idanun sosai har ya ji kamar ya kwacesu.

Ita kuma a ru?e take binsu da kallo while su kuma suna binta da kallon mamaki, ita Floria kallon mamaki na ta yi saurin gama wanka take binta da shi, shi kuma Ronnie kallon mamakin haka take da tsantsar kyau dama yake yi mata. ?ar karama da ita sai cikar halittar good bye, kamar ita ta bawa kanta su, ga tsokar gurun wuyar nan nata ba'a magana.

A hankali ya dawo da kallonsa kan tsala tsalan cinyoyinta dasu da matu?ar ?aukar hankali, ?ul ?ul da su, ga sket ?in nata dama ?an gajere. Ronnie fa ya ru?e da alama.

(Mumcy, Ummu Sudies and Maman Sultan yau dai black Tiger ya yi maku abin arziki ya bu?ewa Sweetie idanunta ?? Allah yasa ba ya bu?e mata bane dan ya tasata a gaba ta kaisu ga Spender ???? idan ta ki tasha bugu hannunsu Davil?? ina daga gefa??)

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull