Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 19
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 19: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 19. Dukkansu an rasa mai bakin magana a cikinsu, Floria da Ronnie sun shagala da…
3,302 words
Dukkansu an rasa mai bakin magana a cikinsu, Floria da Ronnie sun shagala da kallonta, ta tafi da imaninsu, ita kuma jira take yi ta ji me zasu sake ce mata.........
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 2/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??STEP TWO....??????
E_____________14
Dukkansu an rasa mai bakin magana a cikinsu, Floris da Ronnie sun shagala da kallonta, ta tafi da imaninsu, ita kuma jira take yi ta ji me zasu sake ce mata.
Floris ce ta ?atsesu da cewa. "Am ki cire kayan jikin nan naki akwai kaya a clothes set dake cikin room glass ?in can, ki je ki za?i wanda kike so sai ki sanya, kayan jikin nan naki sun yi datti ai".
Wani irin dogon numfashi Ronnie ya ja tare da sau?ewa a hankali, ko me ya tuna sai ya saki cool murmushin mai wuyar fassaruwa, sannan ya ?ariso in da suke a tsaye. Hannu yasa ya tattarewa Sweetien gashin kanta tare da cewa Floris ta ha?a mashi hair dryer bari ya busarwa da Sweetien gashin kanta.
Okey ta amsa mashi da shi tare da ?auko luxurious dryer ta juna mashi, sannan ta wuce ta ?aukowa da Sweetien kayan da take ganin sun dace da ita ta kawo mata saman bed ?in ta ajiye. Kaya ne irin nasu shigar ta wannan birni, sket ce mai bala'in kyau kasarta kamar umbrella launin blue black, sai riga t-shirt mai karamar hannu launin white, a iya west ?inta rigar ya tsaya mata, shi kuwa sket har ?asa ya kai mata, ya fito mata da shape ?inta kamar dai mutanen cikin birnin.
A takaice dai Ronnie shi ya busar mata da gashin kanta, ba ?arya gashin kan nata ya tafi da imaninsa, ta burge shi sosai da sosai, yana busar mata yana shafawa. Ya kuma iya gyaran sosai, dan gashin nata ya yi matu?ar kyau sosai, da ya gama sai ya ciro pil daga nasa kan ya ?aure mata nata gashin da shi, ta yi kyau sosai.
Bayan sun kammaka floris ta taimaka mata ta sanya kayan a jikinta, Ronnie ya ri?o hannunta a kan ta zo su je ganin wasa. Abin mamaki sam bata yi mashi musu ba, ta bi su kawai suka tafi.
Tun da suka nufo waje ta saki baki tana kallon hanya, mamaki da al'ajabi sun hanata magana, floris da Ronnie sai hira suke zubawa, ita kuma sai kalle kalle take yi.
A haka suka nufi stair case. Nan fa ta ce ba zata hau wannan electric stair case ?in ba, ya tsoratata sosai, gani take yi kamar zata fa?i. Da dai Ronnie yaga da gaske ta tsorata da ganin stair case ?in sai ya sa?eta a saman shoulder ?insa suka sau?o ?asa. Ita dai ta datse idanunta gam bata son sake ganin komai, dan gaba?aya gidan tsoro da al'ajabi yake bata.
Sai ha?uwa da ?an'matan da samari suke yi a hanya, kowannensu cikin girmamawa yake gaishe da Ronnie, dan shi ne shugabansu a nan, saboda yafi kusanci da Black Tiger.
?an'matan kuwa duk wacce suka ha?u da ita sai ta ?allawa Floris and Sweetie da ya ?auko a saman shoulder ?insa harara, sai harararsu suke yi, da alama ?ishi suke ji, dan fa kowacce bata da burin da ya wuce ta mallaki zuciyar Ronnien da bai ma san suna yi ba.
Kai tsaye wani katafaren waje suka nufa, girman wajen nan ya wuce tunaninku, yanayin tsarin ginin wajen kamar football stadium aka tsara shi, wajajen wasanni daban daban ne a cikin wajen, filin da aka tanada dan zaman al'umma suga wasa an ?awata wajen da luntsuma luntsuman kujeru masu shegen laushi kamar a gidan gwamnati, kowani kujera kuma akwai wani luxury glass table a gaban kujerun, sun ?awatu iya ?awatuwa kamar ba na ?an kallo bane, yadda kuka san manyan sarakuna aka tanadawa saboda ha?uwarsu, gaba?aya kujerun launin ash colors ne masu haske.
Daga wani ?angare na musamman a cikin wajen kuwa wasu shegun kujeru ne wa?anda tsarinsu ya fita daban da kowacce sofa dake wajen, daga ganin zaka shaida na musamman ne, suna da yawa a wajen, dukkan kuma one one seaters ne, kai an fa zuba kayan alatu a wajen, ga girman stadium ?in zai iya kwashe rabi da kwantan mutanen cikin birnin DARK WORLD.
Daga ta ?angaren hagu kuwa waje ne mafi ha?ari, wato wajen da ake datse kan duk wanda ya fa?i gasar, shi ma wajen tsabar mugunta irin na Black Tiger har da ?awata wajen kamar wajen abin kirki ne, shar?a shar?an wu?a?e masu bala'in kaifi ya tanada a wajen, sannan ga head lock da aka ?awata shi sosai, waje ne da mutun zai sanya kansa sai a rufe, iya kan nasa kawai wajen da za'a datse zai saka a wajen, daga nan sai mai datsewa ya sanya wu?a ya cire mashi kan nasa shikenan an kashe shi. Haka suke yi gaban jama'ar birnin ba tausayi bare inami, ba kalmar da black tiger ya tsana irin kalmar fa?uwa, sam baya son wannan kalma, nasara kawai yake so, coz baya ha?a hanya da wanda ya ta?a fa?uwa ma, nasara a jininsa take!!!.
Saman wa?an nan kujeru na musamman ?in Ronnie ya zaunar da Sweetie, a gefenta Floris ta zauna, shi kuma Ronnie ya zauna kusa da Floris ?in, sai banka masu harara Delisha dake gefe guda take yi, ita ma ta halarci wajen, ji take yi kamar ta sha?o Sweetien nan ta na?a mata ?an banzan duka, ita tun ainahi jininsu bai ha?u ba, ita kuwa Floris tana kaunar Sweetie sosai, tun ganinta da ita na farko ta ji yarinyar ta burgeta ta shiga ranta.
Sweetien dai ta yi shiru tana bin uban dubbannin jama'ar da suke cikin wajen da kallo, mamaki ne duk ya bi ya isheta, ga tsoron da ya mamayeta, bata ta?a ganin jama'a haka ba, kunsan Kamran da Pretty sai mum ?insu kawai ta sani, to yau dai gata ga jama'ar birnin Dark world!!.
Wajen da ?an wasan zasu yi wasa an ?awata shi over, sannan wajen a kewaye yake ta yadda zasu yi wasansu cikin aminci, kun dai san yadda wajen ?an wasan Wrestling yake ai, to haka aka kawata masu nasu wajen ma.
Wani irin ihu da fito da jama'ar wajen suka fara yi ne yasa Sweetien yi wani irin razana tana ?o?arin guduwa, a garin ?o?arinta na mi?ewa ta gudu ne idanunta suka sau?a a kan Devil dake gefenta yana zaune saman nasa sofar. Habawa ai bata san lokacin da ta kurma ihu ba, saboda ba karya Devil ya tsoratata fiye da tunaninku, kun dai san yadda jikin ?an Wrestling yake ko? Suna cike, damatsan hannun nan nasu kamar zai fashe, ga uban tattoo da suke zanawa a jiki, su tara gashin kai mai tsawo wanda wannan kuma dama al'adar birnin Dark world ne, sannan abu na biyu da ya kara tsorata Sweetien shi ne Devil fuskarsa a tur?une kamar an aiko mashi da cewa uwarsa ta mutu, daga ganin wannan fuska babu imani a tattare da shi, ga idanu manya sai muzurai yake yi, shararren ?an Wrestling ne wanda shi ne master dake basu horo a kan Wrestling ?in, shi ya koyar da Ronnie ma, amma shi yanzu baya wasa, dan babu mai yin winning ?insa, har yanzu ba'a samu wanda zai iya dokesa ba, shiyasa ya daina shiga wasan yana cigaba da horar da masu tasowa kawai, a yanzu dai Ronnie shi ne zakara a cikin duk ?an wasan dake cikin empeir ?in, da yake shi Ronnie yana da siririn jiki kalar nasu na Koreans sai ya zamana shi duk horon Wrestling ?in da ya samu wajen Devil damatsan hannunsa basu wani cika sosai ba, bai da wani cika, idan ka gansa sai ka yi zaton ba zai iya ta?uka komai ba, sai an ha?u a filli wasa kaga in da yake zubar da maza yana ?agawa yana wurgi da su kamar yasamu kwalaye.
Sannan shi Ronnie bai wani ?ata jikinsa da tattoo sosai kamar na master Devil ba, tattoo ?an daidai ya zana na zanen bakar damisa, shi kam Devil duk ya zane ko'ina na jikinsa, ganinsa da ido sai ya baka tsoro, ba'a banza Sweetien ta tsorata ba, rashin mutuncinsa ya yi yawa, kowa tsoronsa yake yi a cikin birnin except Ronnie, ga shi kullum cikin wando three cuters and riga mai gajeran hannu yake, duk ya saki damatsan hannu duk tattoo nasu kunama, damisa da sauransu yana kara razana zu?atan bayin Allah dan iskaci ya yi mashi yawa.
Ihun da ta zunduma ya janyo hankalin mutane dayawa a kanta har shi Devil ?in, idanu suka yo kanta. Da sauri Ronnie ya mi?e ya dawo kusa da ita ta ?ayan bangaren da Master Devil yake kenan. Ri?o hannayenta a cikin nasa ya yi tare da tambayarta lafiya?.
Nan take jama'a suka tsareta da ido, sun ga kyau iya kyau, sai suka kasa tantance ita da king of beautyn nasu wato Ronnie ma wanene ya fi kyau?.
Ita ma Floris matsawo ta yi suka fara tambayarta me yake faruwa?. Da kyar ta iya ce masu. "I'm afraid". Ta yi maganar kamar zata yi kuka.
"I'm here to take care of you, don't be scared of anything, nothing will happen, just watch the game let me watch your beautifull face like television". Cewar Ronnie, ya kai karshen maganar yana ?an murmushi.
?an?ame hannunsa ta yi tana tunanin Kamran and Pretty, zuciyarta tamkar zata fashe saboda tsoro, daga karshe ma kwantar da kanta a saman shoulder ?insa ta yi tana cigaba da tunaninta.
Shigowar wani ?a??arfan matashi cikin wajen wasan ne yasa jama'ar wajen suka sake saka fito tare da ihu, wasu suna sakin tafi da hannunsu rap, rap, rap.
Matashi ne ?a??arfa madaki katti, shi ma jikinsa duk zanen tattoo na Black Tiger, chocolate guy ne, jikinsa duk jijiyoyi a tsaitsaye, karfi kam ba'a magana, ga shi kuma kyakkyawa sosai, gashin kansa bai da tsawo sosai, a iya wuya ya tsaya mashi, sannan ya watsa gashin nasa kamar dambun rama bai ?aure ba.
Sai tafi ake yi ana jiran wanda zai iya gwabzawa da shi ya fito. Almost 10 mins da shigowarsa cikin filin kafin wani ha?a??en matashi ya shigo, na gaya maku mutanen birnin Dark world fa ni har yanzu banga mummuna ba, kyawawa ne sosai kamar su suka yi kansu, ga cikar duk wata halinta na mata da maza, abin dai ba'a magana, sai dai kash ba musulmi ko guda ?aya a cikinsu, dukkansu abu ?aya suke bautawa, Christian's ne...... Fata na dai Allah ya kawo maku shiriya ku gane gaskiya wata kila zaku daina zalincin da kuke yi, dan musulunci rahmace babba da babu irinta a duniya.
Wani irin fito mai sauti Ronnie ya yi shigowan wannan guy na biyun, bayan ya yi fiton ne ya ce da Floris. "Our Oxil ne zai yi winning".
Delisha ce ta amsa da cewa. "No Feros ne winner". Har ta yanke hukunci.
Harara ya wurga mata da ido tare da cewa zamu gani.
Ita dai Sweetie da bata ma san me za'ayi a wajen ba ta kwanta shiru a saman shoulder ?insa abinta, bata san wani irin wasa za'a gudanar ba, ita dai tana ta ganin ?osassu kuma lafiyayyun maza sai tururuwan zuwa wajen suke yi. Ga ?an'mata ma nan birjin, kowacce tana ta kallon wanda take burin aura.
Hannu ?an wasan suka ha?a suka gaisa da juna, dama a ?aidar wasan kenan, sai an gaisa an rungumi juna kafin a fara. Suna gaisawa jama'a suka sanya ihu ha?e da fito, kowa ka ?aga idanu ka kallah a cikin jama'ar zaka gansa da murmushi a face ?insa, da alama suna cikin annasuwa, tabbas mutanen birnin nan suka jin da?in ganin wannan wasa, sai murna suke yi.
Master Devil da yake a matsayi commissioner wasannin ne ya mi?e tsaye, yana da tsawo sosai ga fa?i, taku ya fara yi cikin jarumta ya isa cikin tsakiyar filin wasan, Sweetie tana ganin ya mi?e ta ?ara ?an?ame Ronnie, dama tun ?azun sai satar kallonsa take yi ya tsoratata ya kuma bata mamaki, bata ta?a ganin mutun irin haka ba a rayuwarta, ko Kamran da yake da damatsan hannu manya saboda horon da Mamma ke bashi bai kai rabin Devil ba, shiyasa ta ru?e baiwar Allah.
Hand gloves na wasan master Devil ya ?ar?a a waje rappern wasannin, irin hands gloves ?insu masu kauri sosai ?in nan, shi ya kar?a ya sanya masu a hannu tare da ?aura masu maroon ?in handkerchief a gaban goshinsu, sannan ya sanya hannu a tsakiyansu ya yi counting from 1 to 10 kafin ya furta start. Yana fa?in hakan ya bar wajen.
Wasa aka fara bugawa, mazan nan kowannensu ya zage dantse, bugun juna suke yi babu wasa, kowa yana son ya rayuwa, wannan wasa ce tsakanin mutuwa da rayuwa, duk wanda ya fa?i shikenan ya bar duniya, kuma a haka suke yarda su yi, dama murnarsu suke shiga cikin wasan.
Jama'a sai fito suke yi, su dama kun san ?an karawa abu armashi ne, ai kuwa sai yi suke yi. Wasa ya fara ?aukar zafi, wasu maza dake zaune a saman nasu sofar sai kace da su ake fa?ar, sai wani wuwwurga hannu suke yi, idan ?an wasan ?aya ya ?aga ?aga zai buga da ?asa sai kagansu su sanya hannu kamar zasu tare shi, yadda kuka san da su ake yi, ?an karawa abu armashi wato masu ihu da fitoma suna yin nasu, yanzu almost karfe 11 na dare amma babu alamar zasu je su kwanta su yi barci, ita ma Sweetie yanzu ta ware idanunta tana ganin wannan wasa mai abin al'ajabi a gareta, sai dai kuma tausayi ne cike taf a ranta, dan yadda suke jibgar juna tsakaninsu da Allah sai da idanunta suka kawo kwallah, abin ya ?aga mata hankali sosai, amma ba yadda zata yi dole ta hakura ta kallah.
Wasa ta ?auki zafi, Feros ya fasawa Oxil baki, nan take Ronnie ya ?ata rai, dan Oxil mutuminsa ne, ita kuwa Delisha murmushi ta fara yi dan ita tana backing na Feros ne, Floris da dama bata bin bayan kowa wasa kawai ta zo gani hankalinta a kwance yake abinta, duk wanda aka daka shi ya sani.
Wasa fa ta yi tsamari sosai, Feros ya sake fasawa Oxil hanci, nan fa hankalin masoya Oxil suka tashi, ciki kuma harda Ronnie wanda yake jin kamar ya je ya kar?awa Oxil ?in, ransa ya ?aci, shi gani yake naushi ?aya ya ishe shi ya gama da Feros, fa?i yake yi a ransa in dai Feros ya yi winning ya ja aka kashe Oxil to tabbas next wasa da shi zasu buga ya ?aukarwa Oxil fansa....... Babbar magana, yau dai ake yinta, wato wasan ma wasu suna shiga ne dan ?aukar fansan ?an uwansu kamar dai yadda Ronnie ya kurta a ransa yanzu! E lallai black tiger kafi kowa tara makiya a duniyar nan, dan kai ne silar komai, tab da mutanen birnin nan zasu samu dama ina ga cinyeka ?anya zasu yi, dan dai kawai ba wanda ya san kai mutun ne ko aljani, amma fa my people's akwai matsala babba a wannan birnin, Allah ka dawwamar da mu a cikin addinin musulunci addinin ni'ima, yo idan ba rashin musulmar zuciya ba zasu yi irin wannan wasa da ransu haka ne? Sun ?auki rai ba'a bakin komai ba! Allah yasa su samu dai su musulunta ko a rage zalinci kam in ba haka ba akwai babbar matsala.
A hankali tausayi yasa Sweetien ta fara kuka da hawayenta, musamman yadda taga sai jibgar Oxil Feros yake yi, abin ya yi matu?ar ?aga mata hankali, kamar ba jini da tsoka bane a jikunansu, sun zage sai jibgar juna suke yi kamar basu jin zafin jikinsu?.
Wani irin naushi da Feros ya kaiwa Oxil ne yasa shi ya yi baya baya yana ?o?arin fa?uwa, cikin zafin jini Feros ?in ya sake binsa da nufin ya ?arisa shi kawai ya cinye gasar.
Rai a matu?ar ?ace Ronnie ya kurma ihu da sunan Oxil ?in wanda hakan ya yi sanadiyar sanya Oxil ?in ya farga tare da dawowa cikin hayyacinsa, cikin fusata ya sanya hannusa ya kare naushin da Feros ya kawo mashi, da karfin gaske ya mur?e hannun Feros ?in baya tare da mi?ewa tsaye da kyau ya fara ?o?arin kwatar kansa.
Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya Ronnie ya sauke tare da yin fito da bakinsa, ita dai Sweetie sai kuka take yi ba tare da kowa ya lura da ita ba, duk hankulansu na kan wasa.
Ronnie ji yake yi tamkar ya tashi ya taya Oxil fa?ar nan, har wani tsuma jikinsa yake yi, sai ciza lallausan la??ansa yake yi, shi ala dole bugun da Oxil yake yi wa Feros ta yi mashi ka?an........... Kash ana ?an iska a cikin birnin Dark world wlh, kun ji mun Ronnie fisabilillahi my people's wai jibgar da ake yi wa Feros ta yi mashi ka?an, Allah gamu gareka, Allah ka shirya mutanen birnin nan........??
An gwabza wasa iya wasa, sun jibgi juna iya jibga, daga karshe Oxil ya yi nasarar kayar da Feros kasa a in da ya kasa tashi har commissionern wasannin wato master Devil ya ?irga daga ?aya zuwa goma bai mi?e ba, ya sha jibga ba ka?an ba, shi ma Oxil ?in dai da kyar ya sha, da kyar da su?in goshi ya iya yin galaba, ya ci wuya, shi ma sai ya yi jinyar kansa, dan ya daku.
Ganin bai tashi bane yasa commissionern ya kama hannun Oxil tare da ?agata sama a zuwan shi ya yi nasara. Nan take masoyansa suka fara ihu suna fito kamar zasu tashi wajen. Ronnie har da mi?ewa da sauri ya raba Sweetie da jikinsa, cikin sauri ba tare da ya bi ta kanta ba ya wuce ya shiga wajen wasa, rungumar Oxil ?in ya yi kafin ya sakesa suka fara taka rawa kamar me.......... Ashe dai Ronnie ya iya rawa.
Rawa sosai suka taka kamar west ?insu zai ?alle shi da master Devil, da alama master ma yana team na Oxil ne, shi ko Oxil girgiza kai kawai ya tayasu, dan ba zai iya rawa ba, jiki duk ta yi tsami. Ki?a mai dukan sautin gaske Dj Jack ya sakar masu, ba karya sun taka rawa, suna yi Ronnie yana fito da karfin gaske, da alama wannan winning ?in da Oxil ya yi fa ya yi masu matu?ar sugar. Suma masoyansa sun takarawan nasarar da ya samu.
Sai da suka taka rawansu mai isarsu jama'a suna yi masu fito sannan ne Ronnie ya dawo wajen zamansa, sai a lokacin ya lura da Sweetie ta sha kuka har ta ?oshi, ?azun duk bai gani ba hankalinsa na'a kan wasan, burinsa kawai Oxil ?insa ya yi nasara. Rarrashin ta ya hau yi tare da tambayar meya sameta me aka yi mata take kuka?.
Shi kuwa master umarni ya baiwa wasu jaruman maya?a da su ?auki Feros su sanya shi a wajen da suke datse wuyar wanda ya fa?i wasan wato head lock kenan. Ai kuwa basu yi ?asa a gwiwa ba wajen aiwatar da hakan, bayan sun kaisa wajen ne master ya ce Oxil ya je ya ?arisa aikinsa, Allah sarki Feros da bai gama dawowa cikin hayyacinsa daga dukan da ya sha a hannun Oxil ?in ba zai bakunci lahira.......Abin ya ta?a mun zuciya sosai.
Babu imani bare tausayi Oxil ya ?aga wu?a ya datse mashi wuya da ita, habawa sai jini ke feshi kamar fanfo. Fito jama'a suka sanya suna jinjinawa Oxil a zuwan ya yi jarumta ya yi abin kirki.