Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 20

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 20

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 20: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 20. Wani irin azabbabbe kuma razanannen ihu Sweetien ta kurma na ganin ya fillewa…

3,225 words

Wani irin azabbabbe kuma razanannen ihu Sweetien ta kurma na ganin ya fillewa ?an uwansa wuya da wu?a a gaban dubbannin jama'ar birni kuma sai jinjina mashi suke yi babu wanda ya ce ya yi ba dai'dai ba. Ihu ta kurma saboda razana kan kace me numfashinta ya ?auke diff, bata ta?a ganin irin wannan bala'i ba a rayuwarta, a kullum fatanta idanunta su bu?e taga Kamran, ga idanun sun bu?e kuma ta fara cin karo da tashin hankalin da ta gwammaci makantarta ma ya fiye mata alkhari.

Ganin ta kurma ihu kuma ta sume ne yasa Ronnie ya kalli Floris kafin ya dawo da kallonsa kan Delisha. "Wai me yake damun yarinyar nan ne? ?azun na ganta tana kuka, yanzu kuma ta suma, to me aka yi mata?". Ronnie ya tambaya da mamaki a saman face ?insa, wato dai shi wannan tashin hankali duk ko a jikinsa, kun ji ma wai tambaya yake yi me aka yi wa Sweetie ta suma?. Allah mai iko.

Jama'a sai ihu suke yi suna murna, su kuma team na Feros idanunsu sun yi jajir masu saurin kuka har sun fara yi, abin nasu dai babu tsari sam, ina laifin wanda ya fa?i wasan a bashi horo na mai tsanani, amma a kashe shi abin ya munana, ku duba kuga Feros fa ko dawowa cikin hayyacinsa bai yi ba suka cire mashi wuya, a gaskiya Black Tiger bakin azzalumi ne na karshen kasasheshe, irin wannan zalinci haka, Allah dai ya kawo karshen wannan irin mulki taka ta zalinci, Allah ya kawo wanda zai cire wannan RAWANIN ZALINCI ya ?aura CROWN OF JUSTICE, PEACEFUL AND FREEDOM.

Ganin da gaske ta sume ne yasa Ronnien ya mi?e ya ?auketa cak, da alama Ronnie shi aka bawa gadin Sweetie, da alama ya ro?in alfarman a barsa ya kar?o Spender daga hannunta cikin sauki, dan yadda yake yi matan nan da biyu, dole akwai abin da suka shirya mata na dabara.

Kai tsaye ?akinta ya mayar da ita, da kansa ya ?auko ruwa ya yayyafa mata. A haukace baiwar Allah ta farka, ihu take tana fa?in shikenan ya mutu, ya mutu, sun cire mashi kai. Rungumota Ronnien ya yi tare da hawa rarrashinta.

Cigaba da sambatunta ta yi da alama ta fita a hayyacinta. A cikin sambatun nata ne ta yi su?ul da baka ta ce. "A irin wannan ?anyar zalincin da kuka aiwatarwa ne kuke tunanin zan gaya maku in da spender yake har ku mulki duniya? Da kuwa Allah ya kamani, da karshena ba zai ta?a yin kyau ba, tun da ni zan taimaka a azabtar da bayin Allah, wlh ko ina tare da ainahin Spender ba.........." Dakatawa da maganar ta yi sakamakon wani irin azabbabben mari da ta ji saukarsa a ?uncinta.

Ai tuni ta dawo cikin hayyacinta, kwalalo idanu waje ta yi dan taga waye ya mareta, ina idanunta sun ?asa iya gane mata komai da kowa, face ?akin empty babu kowa, tabbas ta jita a jikin mutun, amma ta ?asa iya ganin fuskarsa, kuma ba makancewa ta yi ba, kawai fuskar ne ya ?acewa ganinta saboda marin da ta sha ?in.

Tsoro iya tsoro ne ya dira a ranta, hawaye kuwa yadda kuka san an bu?ewa ruwa hanya haka suke gudu a saman face ?inta, jikinta nan take ya fara kerma ya kuma ?au zafi sosai, addu'oi ta fara jerowa wanda ita kanta bata san wasu iri take yi ba, sai a lokacin kuma ta tuna da cewa bata yi sallah ba.

Wani irin banko kofar ?akin da aka yi aka shigo ne yasa ta ?ara tsorata, ji take kamar bugawa zuciyarta zata yi ta mutu kawai. Fa?i take yi a ranta koma me zai faru ko kasheta zasu yi wlh ba zata ta?a gaya masu in da spender yake ba, dan wannan alkawari ta ?auka, (ta ?aukawa waye?) a wani ?angare na zuciyarta kuma addu'a take yi Ubangiji Allah yasa Kamran ya ri?e kayan da suka bashi da amana, Allah kuma yasa kada su kama Kamran ?in and Pretty, in dai basu kamosu ba, to wlh ba zata gaya masu in da spender yake ba, idan kuma sun kamosu ko dan Pretty dole ta fa?a........... Ni kam nace akwai tashin hankali kenan, wato dama Sweetie tasa abin da suke nema kenan? Tab lallai yarinyar nan ta wuci tunanin mai tunani, gata makauniya, ?ar karama kuma shiru shiru ashe ta san abubuwa da dama! Lallai yau ake yinta kuwa, fatanmu dai shi ne Allah yasa kada su azabtar da ita baiwar Allah, ko me da me ta sani baiwar Allah, tabbas tun da tasan labari a kan Spender ta kuma san da cewa yana da karfi iko na musamman, sannan tasan ana nemansa ruwa a jallo to tabbas da wuya idan bata san tarihinsu ba. Allah dai yasa kada ta ji wahala ta basu spender su cigaba da zalunci, karfin ikon Black Tiger ya ?aru, yanzu ma yaya bare ya samu Spender?. Tab akwai cakwakiya.

Amma ina da tambaya, ya aka yi Sweetien tasan abubuwa da dama Pretty bata sani ba? Ko dai ita ma Prettyn ta sani ne? Waye ya sanar da Sweetien dukka wannan abin?. And meyasa duk yadda da suke da Kamran bata sanar da shi komai dangane da hakan ba? Kuma dai ta yarda da shi sannan tana sonsa! Sannan meyasa kai tsaye mun ?insu ta bawa Kamran auren Pretty ba Sweetie da take babba mai hankali da nutsuwa ba? Daga karshe a tsakanin su ukun nan wato Sweetien, Pretty and Kamran a hannun wanenen Spender yake takamaime? Waye yasan hakikanin in da yake? Akwai babban buhun bala'i kam a cikin wannan birnin tab.

Ba kowa bace ta banko wannan kofa ta shigo face Delisha, sai wani huci take yi, daga ganin yadda take tafiya zaka fahimci sam bata ?ullo mutunci ba, rashin mutunci ne cike a face nata ha?e da mugunta.

Tana zuwa ta fimciko Sweetien daga jikin Ronnie da tun ?azun da ya zabga mata mari ya kasa motsawa daga in da yake...... Me dalilinsa na zabga mata mari to?.

Ya kasa yin wani kata?us har Delisha ta fincikota tare da janta kamar kayan wanki ta nufi waje da ita. Sai bayan sun fita ne Ronnie ya iya sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin muryar ya furta. "Kin yi kuskure". Ya kai karshen maganar tare da mi?ewa ya sauko ?asa daga saman gadon....... To fa ta yi kuskure? Wacece ta yi kuskure? Kuma kuskuren me? Mu je dai zuwa.

Waje ya nufa wato ya bi bayan Delishan kenan, da alama duk jikinsa ta yi sanyi, tafiya yake yi kamar wadda aka zarewa la?a.

Kai tsaye sama ya sake haurawa yana tafiya kamar zai fa?i ?asa.............

___________________________????

GIDANSU KHADIJAH.????

Satin Zainab guda a asirbiti tana fama da jinya, yanzu Alhdulillah jiki ya fara kyau, ita kuwa Hauwa da maman Haidar sai cin karensu suke yi babu ?a??aka.

Yau ta kama ranar jumma'a satin baban Zainab bakwai kenan da rasuwa, Hauwa da Maman Haidar suna zaune a parlour suna hira kamar wasu ?awaye, a yanzu suna shiri sosai, Hauwa ta yi masu mage mai kwanciyar ?aukar rai, da biyu ta yi shiri da su, akwai abin da take hara ne yasa ta kwantar masu da kai suna zaman lafiya.

Hajiyarsu kuma tana cikin ?aki tana kwance, fama take yi da ciwon zuciya, ga hawan jininta ya taso, so bata da lafiya sosai, ko magana bata iya yi, sai an kwantar sai an tayar, rasuwar baban Zainab ya jefata cikin wani halin da baki ya yi ka?an ya fa?esa, Hauwa da maman Haidar basu wani damuwa da halin da Hajiyar take ciki, maman Haidar dama sai abin da Hauwa ta ce take yi, shiyasa bata kula da mahaifiyar tasu, kullum maman Hanif ce take zuwa tana jinyarta, a gida likita yake zuwa ya dubata, maman Hanif ita take zuwa ta bata magani da duk abin da ya dace.

Har yau Hauwa da Maman Haidar basu nemi Khadija ba, Hajiyarsu kuma bata magana a yanzu bare ta ce ina yaran suke, Maman Hanif kam ta san komai, dan har asibitin da Zainab ?in take kwance ta je wajen ta dubata yafi sau a ?irga, yadda aka yi tasan komai kuwa shi ne, tun ranar da suka yi kaca kaca da maman Haidar ta tafi bata sake zuwa gidan ba har sai da Hajiyarsu ta kwanta jinya, a ranar ta zo suka je asibiti dan a lokacin jikin ya tsananta sai suma Hajiyar take yi tana farfa?owa, shiyasa suka je hospital. Bayan sun je anyi duk gwaje gwajen da zasu yi ne aka basu magunguna ha?i da nurse guda ?aya suka dawo gidan, a nan ne ta shiga ?akin su Zainab da nufin ta dubasu, sai bata gansu ba dukkansu biyu.

Hankali a tashe ta fito ta tambayi Maman Haidar ina su Khadijah? Maman Haidar ta ce bata sani ba tun da dama ba'a bata ajiyarsu ba. Nan fa ta shiga tashin hankali ta fara tunanin waye zata kira ta tambaya ina suke?.

Can sai Sadiq ya fa?o mata cikin tunaninta, shi ne ta nemi numbersa ta kirasa, da farko har ya ?oye mata gaskiya, daga baya kuma sai ya tuna cewa ita da maman Haidar akwai banbanci, dan haka sai ya gaya mata gaskiyar abin da yake faruwa.

Tsabar shiga tashin hankali jikinta har kerma yake yi, nan take ta ce ya bata address na hospital ?in gata nan zuwa, to kunji yadda aka yi tasan batun ?atar Khadija da rashin lafiyar Zainab, ita kam maman Haidar ko nemansu ma bata yi ba ita da take da alhakin kula da su ma bare Hauwa gayyar tso?i.

Sai hira Hauwa da Maman Haidar suke zubawa maman Hanif ta koma gidanta, kamar daga sama suka ga an banko labule an shigo masu cikin parlourn.

Saboda sun tsorata mi?ewa tsaye suka yi cikin sauri. Ganin Haidar ne yasa mamar tasa ta ce. "Kai lafiyarka zaka shigowa mutane ?aki babu sallama? Daga ina ma kake ke? Ina ka fito? Yau fa wajen wata biyu ban sanyaka a idanu na ba, ina kaje!".

A maimakon ya amsa mata maganar da ta yi ?in sai ya ce. "Ni mama ba wannan ba, ina Khadijah? Kin san cewa lokacin aurenmu ya yi ko? Satin nan za'a ?aura auren".

"Ina kaje tukun nan? Fa?a mun naji kafin na gaya maka in da Khadijah take".

?aure fuska sosai ya yi. "Wani waje na je ni da abokaina da nufin mu yi sati biyu, shi ne muka yi wata biyu, dan wajen ta yi da?in, to ina Khadija da kawu suke? Kawu ya zo yau idan an sauko daga sallar jumma'a ya ?aura mana auren kawai". Yana magana kamar yana baiwa mamar tasa umarni.

"Haidar maman Zainab ta kashe maka kawunka, Khadija kuma ina jin cewa tana ?akinsu".

Wani irin ihu ya kurma irin na ?an daban nan, muryarsa ?ato ya ce. "Kutumar ubancan, lallai yau akwai durun uwa, A'isha ce ta kashe kawu? To akan me? Meyayi mata? Tukun nan ma kisan gaske ko ma wasa?".

Charap Hauwa ta ca?e zancen da cewa. "Tsabar mugunta ce kawai, ta kasheshi mana shi har lahira". Ta kai karshen maganar tare da fashewa da kukan kinibibi da munafurci.

Wani irin kallon rainin wayo ya wurga mata kafin ya ce. "Ke kuma daga ina gayyar so?i? Kaji munafuka, kina da wani ha?i da kawun ne da zaki tsaya wani ?a?alo kukan munafurci? Ke daga ganinki fuskar bakaken munafukai ne da ke, ni mama ki bani amsata me yake faruwa ne?". Cikin bokarewa ya yi maganar babu respect ko ka?a.

Tsit Hauwa ta yi, ta ha?iye kukan gulmarta, dan Haidar dai bata ga alamar mutunci a tattare da shi ba, jahilci cike da kai yanzu zai yi mata mummunar aiki, tasan matasa irinsu sarai, dan haka sai ta kama bakinta ta yi shiru.

Mamarsa bata ?oye mashi komai ba ta zayyana mashi yadda abin ya faru kamar yadda makira Hauwa ta zayyana masu, da karya da gaskiya duk ta kwasa dama ta gaya masu, dan haka ita ma Maman Haidar haka ta kwasa ta gaya mashi.

Wani irin buga center table na tsakiyar parlourn ya yi da karfi, cikin fusata da ?aga murya ya fara zazzaga jajjagen masifa. "Kutumar uban can, wlh in na yarda Allah ya tsinemun, kamar yadda A'isha ta kashe kawu nima sai na kasheta, wai wace shegiya ko shegen ne ma ya kaita kotu? Ai barin mun ita zasu yi na zo na fe?e shegiya, wlh na rantse da Allah sai ta fito daga prison ?in nan na yi mata yankar rago, su ma su Khadijah ?in ba barinsu zan yi ba, ?an iskan banza, su ma mugun iri ne sosai, basu da amfani a cikin al'umma, kashe su shi yafi". Yana kai karshen maganar ya nufi ?akunan gidan yana tambayar ina su Khadijah zai kashesu dan basu da amfani, ya fasa batun aure.

Kun ga ka?an daga cikin aikin jahilci kenan, Allah da kansa baya hukunta wani da laifin wani, laifin wani baya shafar wani, amma shi Haidar saboda jahilci da ya yi mashi katutu shi ne yake neman su Khadija ya kashe su dan mahaifiyarsu ta yi laifi bisa kuskure. Kai Allah ka bu?a mana ?wa?walwarmu ka bamu ikon neman ilimi ka rabamu da jahilci.

Sai kiransa mamarsa take yi a kan yazo kada ya ta?a su Khadija, amma ina ya yi gaba sai faman banke kofofi yake yi yana shiga cikin ?akuna shi a dole sai ya fito da su ya kashesu.

Ganin basu cikin ?akun nan sai kakarsu dake kwance kamar gawa ne yasa ya fito ya dawo parlourn ya fara tambayar mamar tasa me ya samu kakarsu kuma?.

Nan fa ta sake gaya mashi ai saboda mutuwar baban Zainab ne yasa hawan jini da ciwon zuciya suka kamata. Sake haukace masu ya yi yana fa?in ai ga irinta nan, wlh ba zai bar gaba?aya dangin maman Zainab ba, duk sai ya kashe su kamar shi ne dama ya kawosu duniya.

Sai tausarsa mamar tasa take yi, amma ina sai kara haukace masu yake yi, har da wani cewa zai kwashi abokansa su tafi Kaduna su je su farwa maman maman Zainab ?in su kasheta, sannan ya kashe Sadiq kafin ya san ta yadda zai yi ya fito da maman Zainab daga prison ita ma ya kasheta.

Hauwa kam abin nema ya samu, da?i kamar ta zuba ruwa a ?asa ta sha, ita gani take yi idan ya kashe mata Khadija and Zainab shikenan ta ci dukiya, ita dai matsalarta abin duniya.

Suna tsaka da wannan hayaniya kwatsam ba zato ba tsammani suka ji sallama a bakin kofa. A tare suka kai kallonsu wajen, ba kowa bace face Khadija.

Binta da kallo suka fara yi, dama can su basu san bata nan ba, basu san da ta ?ace ba bare su yi mamakin dawowarta, kallon tuhumama suke binta da shi, tuhumanta suke yi a kan ina kuma ta je? Da a tunaninsu ai suna ?aki basu fitowa sai in zasu girka abin da zasu ci ko makancin haka ne suke fitowa, kuma basu ha?uwa da su ko a kitchen amma basu damu da su san wani hali suke ciki ba bare har su je ?akinsu su dubasu.

Sanye take da doguwar riga abaya maroon color mai matu?ar kyau da tsada, riga ce mai tsadar gaske, takalmar dake kafafunta ma masu tsadar gaske ne, ta yafa gyalen rigar a kanta, hannunta na ri?e da irin school bags ?in nan mai matukar kyau, bata goya a back ?inta ba sai ta ri?e a hannunta, ta ?ara kyau ta kuma yi haske sosai, ta yi ?iba matu?a, kamar ba Khadija ba, gaba?aya ta canza.

Kanta Haidar ?in ya yi da nufin ya aiwatar da kudurinsa na kashesu dukka, da sauri mamar tasa ta yi ?o?arin ri?esa dan kada ya ?allo masu ruwa, ba hankali ne da shi ba, kada ya jajumo masu abin da ba zasu iya ba.

Hauwa kuwa cewa take Maman Haidar ?in ta kyalesa ai gaskiya ya fa?a, su Khadijah mugun iri ne, sun tsotsa a nono, dan haka su rabu da shi.

Maman kuwa ta ce a'a bata shirya ?anta ya tafi prison ba, dan haka ita bata yarda ya kashe kowa ba.

Kin yarda ya yi shi kuwa, ya kafe sai ya kashe su, marika ya fara kaiwa Khadija ?in kamar an aikosa, bata ko motsa daga in da take tsaye ba, da alama zuciyarta ya rigada ya bushe, da alama ita ma mutuwar take da mura?in ta yi.

Dukan gaske ya fara kai mata tana tsaye tana kallonsa ko gezau, sai ?o?arin ri?esa mamarsa take yi. Kwashe kafafun Khadija ?in ya yi da nasa kafafun ta zube ?asa, still dai kallon face ?insa take yi ba tare da ta ce mashi ko uppan ba, kuma bata motsa ba, sai dai ruwan hawaye da take yi saboda zafin dukan da yake yi mata.

Allah sarki ko daga ina ta dawo? Suwaye suka ?auketa? Daga dawowa kuma ta hau kar?ar dukan mahaukaci Haidar, baiwar Allah daga ganin face ?inta cike take tab da damuwa, idanunta sun sha kuka har sun gaji, ga dukkan alamu koma daga ina ta fito bata yi zaman da?i a wajen ba, sai dai kuma jikinta ya nuna ta samu kula sosai duba da yadda ta yi ?iba ta kuma yi haske, da alama wlh zuciyar Khadija a yanzu ya bushe bata jin tausayin komai.

Ganin da gaske zai iya hallaka ?ar mutane yasa mamar tasa ta fara ihun neman taimako, a guje ta yi waje dan ta nemo mai agaza mata. Haniyarsu dake kwance rai a hannun Allah ne ta ji Haidar zai kashe mata jika Khadija da duka, nan take jikinta ya tsananta ciwo, tana kaunar jikokin nata a yanzu kam, dan ta yi nadama, su Khadijah ?in zata gani ta tuna babansu, kuma ace Haidar zai kashesu ai ba zaman lafiya.

Nan take jininta ya sake haurawa sosai, jiki ya tsananta ciwo, suna can su kuma suna hauka babu wanda ma yasan ciwon nata ya tashi, sai numfashi sama sama take yi tamkar rai zai yi halinsa.

Sadiq dake asibiti yana ?o?arin ha?awa Zainab tea ta sha kafin a kawo masu takardar sallama ne ya ji wayarsa tana ringing, yau dama za'a sallami Zainab ?in, dan ta ji sauki sosai, sai dai rashin maganar ne har yanzu dai shiru ba wani cigaba, komai kace mata sai dai ta ?aga maka kai sama kawai alamar ta ji.

Ha?a mata tea ?in ya yi ya mi?a mata tare da ciro wayar tasa daga aljihunsa, my friend shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ?in wayar. Picking ya yi ?o?arin yi call ?in ta katse, dama call ?in farko ta katse saboda yana ha?a tea, hakan yasa bai samu damar ?auka ba.

Cire password na wayar ya yi tare da fara ?o?arin kiran abokin nasa sai ga kiran ya sake shigowa. Picking na call ?in ya yi tare da kara wayar a kunnensa.

Tun kafin ya yi magana ya tsinkayo muryar abokin nasa cikin tsananin tashin hankali yana fa?in. "Sadiq duk in da kake ka yi maza kazo, kome kake yi ka yi maza ka bari mama ta fa?i yanzu zamu kaita asibiti".

A ru?e ya ce. "Meyasameta ta fa?i?".

"Nima dai ban sani ba, na zo gaisheta ne na sameta tana waya, ina ga a wayar ne aka gaya mata wani magana mai ?aga hankali da har yasa ta fa?i, ka yi sauri kazo".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull