Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 21
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 21: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 21. Bawan Allah tsabar ru?ewa da shiga tashin hankali bai san lokacin da ya fice…
3,344 words
Bawan Allah tsabar ru?ewa da shiga tashin hankali bai san lokacin da ya fice daga ?akin ba, sai ya mashi kamar a Kaduna yake ba Kano ba, ko katse kiran bai iya samun dama ya yi ba, shima abokin nasa bai katse kiran ba ya tura wayar a aljihu suka ?auki maman zuwa asibiti, shima Sadiq ?in haka ya tura wayar a aljihunsa ya fice daga hospital ?in, tashin hankali yasa ya mance da Zainab a asibitin ya tafi, wlh Sadiq yana da karfin imani da tawakkali, da wani ne irin wannan tashin hankali daga wannan jarabawa sai wannan wlh da wani ne da ya jima da ha?iyar zuciya ya mutu, wannan bala'i sai kace ba lafiya ba, ko da yake Ubangiji ya fi jarabtar wanda yake kauna, Allah dai ya baku ikon cin wannan jarabawa, amma gaskiya wannan family na Baban Zainab kuna ganin rayuwa, Allah dai ya saka maku da mafificin alkhrinsa bayan kunyi hakuri da juriya kun cinye jarabarwarku.
Haka Sadiq ya tafi ya barta kwance a asibitin, Dr ya kawo mata takardan sallama, zaman jiran kawun nata ta yi har dare bai dawo ba, hakan yasa ta fara tunanin ko dai ta koma gida ne? Wani zuciya kuma ya ce mata idan ta koma gida ya dawo bai sameta bafa? Tun da rana wannan tunani na idan ta tafi ya dawo bai sameta bafa ?in nan shiyasa ta zauna a asibitin har dare ta kasa tsayar da hukuncin da ya dace da ita.
Sai da ta ji ana sallar isha ne ta ce bari dai ta lalla?a ta tafi gida in yaso idan ya zo gida sai ta bashi hakuri. Wannan shawara da ta yanke shi ta bi a in da ta tashi ta ha?a komai nasu, da kyar take tafiya har ta fita daga asibitin, bata da ko naira biyar haka ta tari abin hawa ta hau da nufin ya kaita gida.
A ?angaren Khadija da Haidar kuwa, kafin mamarsa ta samo maza su kama mata shi har ya jiwa Khadija rauni, ya fasa mata baki sai jini yake yi. Da kyar aka iya kama shi, sai huci yake yi yana fa?in wlh sai ya kashesu kamar shi ya kawosu duniya. Haka matasa suka jashi izuwa waje, jin yana ambatar sai ya yi kisan kai ne yasa matasan basu yi ?asa a gwiwa wajen mi?ashi ga hukuma ba, dan kar ya jajumo masu masifa irin na sati bakwai da suka wuce da mmn Zee ta kashe bbn Zainab, ranar sun ga tashin hankali a unguwar, so gudun kada Haidar ?in ya kara jaju?o masu wata bala'in yasa suka wuce station kai tsaye da shi......
_________________________??
A bakin kofar gida mai mashin da Zainab ta tara ya kawota.
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 3/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??STEP TWO....??????
E_______15
A bakin kofar gida mai mashin da Zainab ta tara ya kawota.
Sau?a ta yi tare da kayan nata, nan fa ta tsaya shiru tana tunanin waye zai bata ku?i ta biyasa hakkinsa? Ita dai tasan bata da ko sisi, sannan mamarta bata gidan bare ta yi tunanin shiga ciki ta kar?a, to ya zata yi kenan?.
Ta jima a tsaye a wajen tana tunane tunane har sai da mai mashin ?in ya ce mata. "Malama sallame ni in tafi". Dogon numfashi ta ja tare da sau?ewa a hankali. Murya a sanyaye ta furta. "Ka yi hakuri bawan Allah, wlh bani da ko naira biyar, dan Allah ka yafe mun ku?in".
?ago idanu ya yi ya kalleta da kyau, sannan ya mayar da kallonsa kan gidan nasu, ?an ta?e baki ya yi, ko ba'a gaya mashi ba ya gane Zainab ?ar matar da ya ?auka zuwa bayan gari wajen boka ne ranar, dan har yau kamannin maman zainab ?in yana face ?insa ya kasa mancewa da ita, dan abin da ya jiyo da kunnuwansa a gidan bokan ya tsaya mashi a rai, sannan yasan a unguwar nan ya ?auki mamarta ya kuma kaita ya dawo da ita, dan haka a cikin zuciyarsa ya furta. "Tun da uwarki tana da ku?in zuwa wajen boka to wlh ba zan yafe ku?ina ba sai an biyani, dama ku mutanen arziki ne sai na iya yafe maki".
"Ke malama bani ku?ina kawai, ni ba wai na fito dan na ?auki mutane irinku na kuma yafe masu ku?i bane, nema na fito yi! Dan haka biyani hakkina kawai na wuce".
Shiru ta yi tana tunanin ya zata yi ta biya wannan bawan Allah. Tsawa ya daka mata a kan ta bashi ku?insa shi yana son ya tafi.
Narai narai ta yi mashi da idanu, babanta ne kawai ya fa?o mata a ranta, da yanzu yana nan waye ya isa ya yi mata wala?anci irin haka, da yanzu yana raye ai ko mashin ?in haya ma ba zata hau ba bare har ta rasa ku?in biya, baiwar Allah tasan gayyar shai?anu ne kawai a cikin gidan nasu, ko ta shiga ma babu wanda zai ?aga idanu ya kalleta bare har ya taimaka mata da ko sisi.
Can kuma tunanin maman Hanif ya fa?o mata, nan take ta fara addu'ar Allah yasa maman Hanif ?in tana gidan nasu, tasan ita ce kawai zata iya taimaka mata, a lokacin kuma mai mashin ?in ya fara surfa mata ruwan balai a kan lallai ta bashi ku?insa.
"Kayi hakuri malam, bari na shiga cikin gida na kar?o maka ku?in". Da kyar ta iya idasa maganar saboda tsananin nauyi da tongue ?inta ya yi mata, maganar tata ma bata fita sosai saboda wahala, ga bakin nata babu ?an?ano ?aci rok kamar shuwaka.
"Wlh ba zai yiwu ba, babu in da zaki shiga, a nan zaki bani ku?ina, salon ki shiga ki gudu ki barni, wlh ba zai yiwu ba, kawai fito da ku?i ki bani kayana hakkina".
Wasu zafafan hawayene suka cika mata idanu a in da suka fara ganganrowa da ?a?an da ka?an.
"Ke ko kukan jini zaki yi yau sai kin bani ha??ina, ai ba irinku musrikai mutanen banza ake yafewa ku?i ba!!"
Jin ya dangantasu da musrikai ne yasa ta ?ago da idanu cikin sauri ta wani wurga mashi wani irin kallo wanda yasa sai da ya ha?iyi yawu ba shiri, dama fa kun san ita Zainab ruwa ne ya daki babban zakara, badan haka ba mafa?aciyace number ?aya, dan haka ranta a ?ace dama ga ciwo ga bakinciki tana neman in da zata amayar da bakincikin dake cikinta ko abu zai ragu mata. Cikin fusata ta ce. "Musrikai kuma mutanen banza? Su waye kenan?". Ta yi maganar tana goge hawayen dake fita daga idanunta.
"Gaku kuwa, wlh tun da kuna da ku?in zuwa wajen boka sai an biyani hakkina makiya Allah da Manzonsa kawai".
Ai tsabar haushi bata san lokacin da ta cire hannu zata zabga mashi mari ba, duk ta saki abubuwan hannunta har flask ?in da Sadiq ya saya mata na sanya ruwan zafi a asirbiti ya fashe saboda sakinsa da ta yi, ranta ya sosu da jin maganarsa, bata san cewa yana da gaskiya shi ne nan ya kai mamanta har wajen boka ba, sai dai ya yi kuskure tun da ba tare da su ya kai maman nasu ba, ta kan iya yiwuwa su bama su san ta je ba, ya zo ya ha?esu ya yi masu ku?in goro.
Bata kai ga sauke hannunta a saman face ?insa ba ta dakata, ba komai kuma yasa ta dakata ba face ta gansa babban mutun ne har da furfura a gemunsa, da yara matasane babu abin da zai hana ta maresu sai dai duk abin da zai faru ya faru, amma a irin tarbiyar da iyayenta suka bata ba zata iya marin wanda ya haifeta ba, dan haka sai ta juya cikin fushi zata wuce cikin gida, ranta a matu?ar ?ace ta fasa marin nasa.
Da sauri ya sau?a daga kan mashin ?in ya sha gabanta yana fa?in. "Aww dama marina kenan zaki yi dan nace ku makiya Allah ne? Karya na fa?ana ne? Ni malama ki bani ku?ina! Babu in da zaki motsa ba tare da kin biyani hakkikana ba! Da kuma kin mareni da daga yau baki sake marin wani ba!!". Cikin fa?a ya yi maganar.
Datse idanunta gam ta yi kafin ta ce. "Ka matsa mun a hanya malam, ina ganin mutuncinka, idan ka cigaba da yin abin da kake yi wlh zan yi maka rashin mutuncin da har ka mutu ba zaka mance da shi ba, ku?in naka kuma na cinye ba zan biya ba kayi duk abin da zaka yi!!". Da kyar ta yi maganar kamar wadda aka sanya dole.
Ai kuwa shi ma ransa a ?ace wai ta yi mashi rashin kunya, cikin jin haushi ya cire hannu zai mareta. Kaucewa marin nasa ta yi tare da ja da baya tana wani layi kamar zata fa?i, bata da kuzari ne a jikinta ko ka?an.
Wasu matasa da suka zo wucewa ne suka ga abin da yake faruwa, nan fa suka tsaya suka tambayi me yake faruwa, mai mashin ?in ne ya amsa masu da cewa. "Wannan yarinya zata raina mun hankali, na ?aukota daga hospital zuwa gida ta bani ku?ina wai ba zata bayarba bata da ku?i, tasan bata da ku?i ne ta hau abin hawana? Da nace ba in da zata je sai ta biyani shi ne ta tsaya tana zagina ni kuma zan ?auki mataki, ba zai yiwu ace yarinya kamar wannan wadda na haifa ace tana gaya mun magana ban zaneta ba!".
Ita dai shiru ta bishi da ido tana jin sharrin da yake yi mata, ita burinta ma kawai ta shiga cikin gida ta kwanta, dan jiri take gani yana ?ebarta.
Nan fa matasan suka ce zasu biya ku?in nawa ne ya yi hakuri. Ana cikin hakan sai ga Khadija da hayaniyarsu ya isheta ta taso ta fito dan ta ga su wanenen? Dama tun da yamma take neman Zainab ?in, ga jikinta da yake yi mata ciwo na dukan Haidar da ta sha, bakin nata ma in da ya fasa mata har ya ?an kumbura.
Ganin hayaniyar da Zainab ake yi yasa ta yi saurin ?arisawa wajen tana tambayar lafiya me yake faruwa?. Zainab da take begen ganinta ne ta bu?i baki da karfi ta furta sunanta Khadija. Nan take ta ji jikinta ya watsake, a ru?e ta rungumeta tana fa?in.
"Ina kika je? Ina kika tafi kika barni? Meyasa kika tafi kuma? Kin san wahalar da na sha da baki nan? Babu mama babu baba, kema babu ke! Iya kawu Sadiq ne kawai ya rage mun a duniya! Dan Allah ina kika je?......" Da kyar ta iya kai karshen maganar saboda kuka da ya ci karfinta.
Ita ma Khadijan kuka take yi sosai ta ce. "Ba tafiya na yi ba, ?aukata aka yi aka rabani dake, nayi kewarki sosai, na yi kuka rashinki tun hawaye na zuba daga idanuna har suka daina zuba, ina kaunarki ?ar uwata, ina mama take?".
Daga mai mashin ?in har matasan dake gefe zuba masu idanu suka yi suna kallonsu, a yanzu fa gaba?aya unguwar su Zainab ?in zagin gidansu ake yi ana tsine masu albarka wai su ?in annoba ne, daga dawuwarsu unguwa sai masifu kala kala yake faruwa, har da kisan kai aka yi a gidansu, maganganu dai kala kala marasa da?in ji ake jefansu da shi.
Sai murna da ganin juna suke yi. "Me ya tsayar dake a waje? Daga ina ma kike haka tun ?azun ina nemanki? Ya na ganki duk a firgice and ina mama?". Dukka Khadija ce ta jero mata wa?an nan tambayoyin.
Fuska duk a ji?e da hawaye ta amsa mata da. "Daga asibiti nake, mai mashin ?in da ya dawo da ni ne ya tsayar da ni wai na bashi ku?insa kafin na shiga cikin gida, ni kuma bani da ku?i, kawu Sadiq bai bar mun ku?i ba". Ta kai karshen maganar hawayenta na ?ara tsananta gudu a saman face ?inta.
"Meya kai ki asibiti? Amma dai bari mu shiga ciki sai ki gaya mun, yanzu jirani bari na ?aukowa mai mashin ?in ku?insa". Tana kai karshen maganar ta raba jikinsu dana juna tare da sa kai da sauri ta wuce cikin gidan.
Matasan da suka ce zasu biya mata ku?in ?in jin cewa Khadija zata ?auko ku?in ne yasa suka hakura suka wuce abinsu, dama kawai dai dan sun ga macece yasa zasu biya mata ba wai suna da wani ishasshen ku?i a jikinsu ba, kun san mu a arewacin Nigeria Allah ya horewa matasanmu zuciyar taimakon mata a duk lokacin da suka ga za'a ci zarafinsu, basu bari a ci zarafin mace koma ya take, in ma matar aure ko budurwa or bazawara, su dai koma wace iriyar macece zasu taimaka mata matu?ar suka ga za'a ci zarafinta musamman ma kanawa suna da wannan dabi'a, sai dai muce Allah ya ?arawa zuciyarsu taimako da tausayi.
Mai mashin ?in kuwa yana tsaye yana bankawa Zainab da hankalinta baya a kansa harara, hankalinta na'a kan kofar gidansu tana jiran fitowar ?ar uwarta Khadija, ta yi kewarta sosai, badan bata son masifaba da ta bi Khadija ?in cikin gida, amma idan ta ce zata bita mai mashin ?in nan zai sake tsayar masu da tijara, so gara mata ta daure kawai ta jirata har zuwa ta fito.
Da sauri Khadija ?in ta fito har kamar zata kifa ?asa, Allah sarki duk dan kewar ?ar uwarta, hannunta na ri?e da dala ba naira ba, tana zuwa ta mi?awa mai mashin ?in dollar dubu ?aya sabuwa kal sai kyalli take yi.
Ai wannan mai mashin ?in bai san lokacin da ya sauko ?asa daga saman mashin ?in nasa ba, zaro idanu waje ya yi yana kallon ku?i ya kuma ?ago ya kalli Khadija da ta tsugunna ?asa tana kwashe kayan da Zainab ta zubar, ita sam bata ma san yana kallonta ba, ita kuwa Zainab ta tsaya sai banka mashi harara take yi na yana kallon mata ?ar uwa, bata san shi al'ajabi da mamakin ku?in da ya fito daga hannunsu ma yake yi ba, dala dubu ?aya a yanzu wajen million ?aya da dubu ?ari shidda kenan take, amma Khadija ta zo ta mi?a mashi ta kama harkar gabanta tamkar wadda ta bashi naira ?ari ko ?ari biyu, ko a jikinta, ko daga ina ta samo dala sabuwa kal haka?.
Kwashe kayan tsab ta yi tare da mi?ewa tana fa?in. "Zainab mu shiga ciki dan Allah ki gaya mun ina mama kuma me kika je yi a hospital?".
Wucewa suka yi ba tare da Khadija ta sake bi ta kan mai mashin ?in ba, ko kallon in da yake ma ba ta sake yi ba ta ja hannun yar uwarta suka nufi ciki.
Shi kuwa mai mashin sai Allah Allah yake yi su shiga ciki basu tambayi canji ba ya samu ya gudu da ku?in ya ci bulus a ganinsa, e mana a ganinsa ne ya ci bulus ya samu ku?i a sama, da ni daku kuma duk mun san cin hakkin wani dai ba cin bulus bane, akwai ranar biya, dan Allah baya yafe hakkin wani a kan wani, dole sai mai shi ya yafe maka, laifi tsakaninka da Allah ne wannan idan ka tuba Ubangiji gafurur rahim zai yafe maka, amma tsakaninka da wani, dole sai ka nemo shi ya yafe maka tukun nan, in ba haka ba Allah ya bi mashi hakkinsa.
Ai kuwa suna shiga gida ya yi maza ya haye mashin ?insa, jikinsa har yana kerma wajen yin saurin kunna mashin ?in, da gudun gaske ya bugata ya bar unguwar, sai murna yake yi ya samu ku?i har naira miliyan ?aya da ?auri.
Suna shiga cikin parlour suka isko Hauwa da maman Haidar suna zaune suna aikin da suka saba wato hira, maman Haidar ta ce a rufe Haidar na kwana biyu a cell sai ya nutsu a sako mata shi, ita kanta bata iyawa da haukarsa, ita da ta haife shi ma kenan, amma dan tsabar son zuciya da mugunta a haka take son a ?a?abawa Khadijah ?ar marainiyar Allah shi, kai wlh jama'a mu rage son kai da son zuciya, ba in da hakan zai kaimu face halaka, Allah mun tuba ka yafe mana zunubanmu, a yawaita tuba jama'a, dan babu wanda yasan a ina karshensa zata zo, yawaita tuba zai sa koda kana da zunubi mutuwa ta riskeka zunubin naka su ragu koma Allah ya yafe maka gabaki?aya, dan haka mu yawaita tuba kafin mutuwarmu, Allah kasa mu dace.
"Ku zo nan munafukai! Ina kuka fito?". Cewar maman Haidar. Khadija ce ta amsa mata da. "Daga waje muke gwaggo". Zainab sai aikin binsu da wani matsiyacin kallo take yi, da yake akwai solar a gidan haske ya gauraye parlourn sai ya zamana suna ganin juna sosai, hakan yasa Hauwa taga irin kallon rainin wayon da Zee take binsu da shi.
"Ke rasa kunya ?erar tanka uban waye kike harara? Ko akwai sa'an ki a cikin nan ne?". Cewar Hauwar.
Khadija ce ta amsa mata da. "Kina ji ko Hauwa kike ko wa? Koma ya sunanki dai ina son ki tsaya a iya matsayinki, kada ki sake ki shiga harkarmu wlh, idan kuma kika ki wlh sai na sa kin gane Annbi isa ba ?an Allah bane manzon Allah ne". Tana kai karshen maganar ta ja hannun Zee suka wuce cikin ?akin.
"E lallai Khadija kin girma, wuyarki ya yi kwari ya isa yanka kenan!". Cewar Hauwa.
Zee ce ta capki zance da cewa. "Tun da ya isa yanka ai sai kizo ki yanka ai!".
Daga hanka suka banko masu kofa da karfin gaske, irin su suka sani nan. Ta?e baki maman Haidar sarkin tsoro ta yi, dan ita fa tsoron masifaffu take yi kada su na?a mata duka ato, ta ji da?i ma da Khadija ?in ta amsa mata magana cikin mutunci har ta ce mata gwaggo, dan haka gara ta kama girmanta ta cigaba da samun suna ce mata gwaggon, dan yanzu ta lura yaran nan suna ji da tashen girman, tsab zasu dakata ta yi laushi, gara ta shafawa kanta lafita ta ja mutuncinta.
Hauwa kuwa da yake ?ar balaja'u ce sai ta fara surfa masu masifa, a can ?ar?ashin zuciyarta kuwa tana tunanin ta yadda zata yi ta yi maganin yaran nan, dan ita ma ta lura Khadija tana ji da tashe girma a yanzu, tsab zata iya cewa zata yi fa?a da ita, idan kuma fa?ar zasu yi wlh tsab Khadija zata laka?a mata shegen duka, dan Khadija fa sai dai muce masha Allah, Zainab akwai rashin kunya ba karfin kirki, Khadija kuwa shiru shiru amma in ka kureta karfi ne da ita sosai, haka suke, dama kunsan mai hakuri fa kada ka kuskura ka kuresa wlh, in ka kuresa abin baya kyau sam sam.
Suna shiga ?aki Khadija ta ce. "Zainab kin yi sallah ne?". Kai ta girgiza mata alamar a'a. "Okey yi alwala ki yi sallah kizo ki gaya mun me yake faruwa ne a gidan nan?". Da okey ta amsa mata tare da wucewa cikin toilet, wanka ta fara yi da ruwa mai zafi sosai kafin ta ?auro alwala ta fito.
A saman gado ta isko Khadija ?in tana duba magungunar da aka bata a asibiti. "Zainab wannan uban tulin magunguna kuma na waye? Naga har da na zuciya duk na waye haka?".
Kamar zata yi kuka ta ce. "Magunguna na ne, yanzu ma zan zo in hau shan su".
Zaro idanu ta yi kafin ta ce. "Dukka uban magungunar nan? Ji wannan manya manyan kamar shanu ce zata sha? Dukka kuma zaki sha?". Ta yi tambayar fuskarta ?auke da mamaki.
Kai ta gya?a mata alamar e, abin gwanin ban tausayi.
"To me ya sameki har zaki zuba wa?an nan magunguna a cikinki? Meyake damunki?"