Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 22
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 22: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 22. "Bari na yi sallah sai na gaya maki me ya faru". Nan take idanun Khadija suka…
3,359 words
"Bari na yi sallah sai na gaya maki me ya faru". Nan take idanun Khadija suka ciko da kwallah, rayuwa kenan, yau sun dawo yin rayuwa su biyunsu Allah sarki gwanin ban tausayi.
Sallah Zee ta yi, bayan ta idar ne ta yi addu'a sosai, ta ?auki lokaci mai tsawo a wajen jero addu'oin nata kafin nan ta shafa, sannan ta mi?e ta dawo saman gadon ta zauna. Khadija da ta ?ura mata idanu tun ?azun tana kallonta cike da tausayi ne ta ce. "Dan Allah Zee kada zuciyata ta fashe ki sanar da ni meyake faruwa? Ke ka?ai nake jira, a ?age nake wlh".
Ajiyar zuciya ta sauke tare da ?arisa hayewa saman gadon da kyau, sannan ta ri?o hannun ?ar uwar tata, nan ta fara bata labarin abin da ya faru tun fitar ta gida lokaci da mamarsu ta cakawa babansu wu?a har izuwa yanzu da suke zaune.
Ya ilahi ya lilliahi, kuka Khadijan take yi sosai da sosai, hawaye a saman face nata gudu suke yi kamar ba gobe, jikinta har rawa ya fara yi saboda tsananin tashin hankali, babanta ya rasu, mamarta ta ci life in prison, innalillahi wainna ilaihir rajuun, wannan masifa ko makiyin ka ba zaka so ka yi mashi fatan shiga makamancinsa ba.
Rungume juna suka yi suka hau murzan kukansu, wannan hawaye nasu Allah ne ka?ai yasan ranar da zata dakata daga zuba a idanunsu, ya ilahi ya lilliahi. Allah sarki babu mai rarrashinsu, haka suka ci kukansu har ya ishesu suka rarrashi kansu da kansu, Zainab sarkin zuciya sai shessheka ha?i da ajiyar zuciya take ta faman saukewa.
Sai da suka ?an ji dama dama ne Zainab ta ce. "Ina ke kuma kika je? Ina kika tafi kika barni ni ka?ai na rin?a fa?a tsakanin rayuwa da mutuwa? Na sha wahala! Na rasa wa zan yi wa kuka, babu mai rarrashina, babu wanda zan gani na ji sanyi a rai'na, ta ko'ina na juya zafi ne kamar wuta a gareni, sam babu wani sassauci, na ce kawu Sadiq ya kaini wajen mama ya ce shi ma ya je an hana shi ganinta, zuciyata zafi take mun kamar zan mutu, shiyasa kika ga maganin zuciya a cikin magungunana, wlh Aunty Khadija gara mun mutuwa akan azabar nan da na shiga, irin wannan tashin hankali bana fatan ko makiyina ya shiga cikinsa". Ta kai karshen maganar wasu zafafan hawaye suna ganganro mata a saman kumatunta.
Matsowa Khadija ?in ta yi ta fara goge mata hawaye tana fa?in. "Kiyi hakuri Zainab, na tabbata Allah bai mance da mu ba, na tabbata yana sane da mu kuma zai yi mana sakayya, sannan shi ne kawai zai share mana hawaye, ina son ki sani duk halin da zaki shiga kada ki manta Allah yana tare da ke, kuma shi ka?ai ne zai kawo maki sauyi a lokacin da baki ta?a zato ba, dan haka ki goge hawayenki, addu'a baba yake da bu?ata, mama kuma da izinin Allah Ubangijinmu zai dubeta da idon rahama tun da ba da gangan ta kashe baba ba, ban ta?a yankewa daga fatan samun nasara daga wajen Ubangiji ba, nasan shi ?in mai rahma ne a kan bayinsa, da izininsa zai saukar mana da rahmansa, kuma baya mantawa da bawa ko guda ?aya, Allah zai kawo mana mafita".
Maganganun Khadija sun ratsata sosai, hakan yasa ta goge hawayenta tare da yin alkawarin zata yi ?o?arin ta dai'na zubda hawaye duk da tasan abu ne mai wuya a gareta, dan kuwa wani lokacin idan ta yi kukan ne take samun sauki a zuciyarta.
"Aunty Khadija ina kika je har tsawon wata biyu to?". Ta yi tambayar tana kallonta har cikin ido.
A takaice ta ce "Russia!". Zaro idanu sosai waje Zee ta yi tare da maimaita sunan Russia ?in. Jinjina mata kai Khadija ?in ta yi kafin ta ce. "Yeah kamar yadda kika ji hakan ce ?asar Russia aka kai ni".
"Waye ya kaiki can? And me kika yi a can?".
"Saceni suka yi suka kaini can, ni ban san na yi wata biyu da tafiya bama sai da kika fa?a mun yanzu, dan tun da naje ina ga na ?auki kwanaki ko satuttuka a sume, ni ban san komai da ya faru ba".
?ara zaro idanu waje Zee ta yi. "Na shiga uku ni Zainab! To amma ya aka yi kika dawo? Sannan kuma basu yi maki komai ba ko?".
Tana ?o?arin firfito da magungunar Zee ?in da ta mayar ?azun ta amsa mata da. "Wa?an da suka ?aukeni su suka dawo da ni har kofar gida, kuma ni ba abin da suka yi mun, ban ga alamar sun cutar da ni ko wani abin makamancin haka ba, kamar yadda suka ?aukeni a kofar gida haka suka dawo da ni, sannan suka bani wancan jakar mai cike da ku?i suka ce na tafi gida wai na rin?a cin abubuwa masu kyau da ku?in da suka bani".
Shiru Zainab ta yi tana tunanin anya hakan zai yiwu kuwa?........ Ni ma dai nace anya hakan zai yiwu kuwa? Su zo har kofar gida su ?auketa su tafi da ita ?asa mai nisa haka, sannan su ri?eta na tsawon sati bakwai ace sun sake dawo da ita da kansu kamar yadda suka ?auketa? Sannan su bata ma?udan daloli ma ba nairori ba su ce ta tafi ba tare da sun yi mata komai ba! Anya hakan abu ne mai yiwuwa kuwa? Kai akwai dai abin da ya sa?a wanda ita bata sani ba. Hmm akwai dai wata a ?asa, haka kawai ba zasu yi abin da suka yin nan ba.
Katse mata tunani Khadija ?in ta yi ta hanyar cewa. "Zo ki sha magani, dan ina fargabar wani abin ya saman mun ke, ke ka?ai kika rage mun sai Allah da ya haliccimu sai kuma kawu Sadiq, dan haka ba zan barki ki yi wasa da magani ba, zo maza ki sha bari na nemo waya mu kira Kawu Sadiq mu ji ina yake kuma me ya faru ya fita asibiti da sauri haka?". Ta kai karshen maganar tare da turo mata tulin kwalin magungunar a gabanta.
"Aunty Khadija ban fa ci abinci ba, magungunar nan kuma suna da karfi in ji Dr, dole na ci wani abin kafin na sha su". "E haka ne, to ki jirani bari na nemo maki abin da zaki ci, daga nan na nemo mana waya". Tana kai karshen maganar ta zuro kafafunta kasan gadon ta sau?a.
Kai tsaye wajen jakar ku?in nata da taho da shi ta nufa, dala ?aya ta zara, wannan shi ne dare ?aya Allah kan yi bature, yau dai ga Khadija da dukinyar da babanta ma bai mallaki ko kwatansa ba, wannan ma?udan dukiya da yake cikin jakar nata duk familynsu daga ?angaren mamarta har na babanta babu mai kwatan wannan dukiya, dan zallar dollars ne a ciki, gasu da uban yawa, Allah sarki a kan dukiya aka kashe babanta kuma Hauwar take son kashesu, dukiyar baban nasu ma da bai wani taka kara ya karya ba, to ita gata da dukiyar da zai isheta rayuwa ita da familyn nata gaba?aya ba tare da sun juya shi bama ma, su ajiye suyi ta zara kawai zai ishesu har su mutu....... Hmmm tab yau ake yinta, wannan uban ku?in dukka da suka bata kuma ace basu yi mata komai ba? Kai ina akwai ayar tambaya gaskiya.
Da yake su basu ?auki dollars da mahimmanci ba, kai bama su san banbancinsa da ku?in Nigeria ba, ita dai da taga dubu ?aya a rubuce a jiki sai ta yi tunanin ko irin dubu ?ayan Nigeria ne, bata san wajen miliyan ?aya da rabi ake magana a kan dollar dubu ?aya ba. Dan haka rashin sani yasa ta sake zarar dubu ?aya ta nufi waje abinta bayan ta ?auki hijabi Zee ?in ta sanya a jikinta.
Har lokacin su maman Haidar suna parlourn. Maman Haidar ce ta ce. "Khadija ina zaki je a daren nan?". Cikin halin ko in kula ta ce. "Abu zan saya a waje gwaggo".
"To amma kada ki jima kuma ki kula kin ga dare ya yi"...... Kash wato a duniya idan ba ka nunawa wasu kai ma ?an iska bane fa bazaku zauna lafita ba, yanzu dai ga shi maman Haidar ta fara yin biyayyar dole gasu Khadija, ta fara tausaya masu dan dole ba dan tana so ba sai dan gudun kada Khadija ta daketa, wannan shi ne maganin shege sai ?an iska, maganin biri karen maguzawa.
"A daren nan ne zaki fita?". Cewar Hauwa da bata gajiya da shegen shisshigin tsiya.
Ko sannu Khadija ?in bata ce mata ba, bama ta kalli in da take ba, dan wani irin haushin Hauwa da take ji kamar ta shake shegiya ta kashe, idan ta ce zata kulata to wlh za'a sake tabka irin kuskuren da aka yi sati bakwai da suka wuce, dan wlh yadda Zainab ta bata labarin abin da ya farun nan ji take ta kashe Hauwar kawai ta huta.
"Khadija ba dake nake magana bane? Nace kada ki fita da daddaren nan ko?". Hauwa ta sake fa?a kamar wata uwarsu, hegiya bata gajiya da shisshigi a lamuran mutane.
Yadda kuka san da mutun mutumi take magana ba Khadija ba, ko juyowa bata yi ba bare ta ganta, ta sanya kai ta yi waje abinta, dan wlh in ta juyo zata iya sumar da Hauwa da duk abin da ta gani a gabanta ?auka zata yi ta bugawa hegiya, amma gudun kada shai?an ya yi galaba a kanta ne yasa taki juyowa, addu'a take yi Allah yasa tafi karfin zuciyarta, da haka ta nufi waje.
Kai tsaye shagon mai sayar da provision ta nufa. Kayan tea masu inganci ta sayawa Zainab ?in, bayan mai shagon ya ha?a mata komai sai ta bashi wannan dalar da ta ?auko.
Zaro idanu ya yi yana kallon ku?in, ya kasa iya gaya mata cewa a shagon nan nasu basu da ku?in da zasu iya bata canjin wannan ku?in nata. Ya saki baki yana ta kallon ku?in har ta kwashi abubuwan da ta saya ta ?ara gaba abinta, bata tsaya neman canji ba, bama ta san tana da canji ba, dan abubuwan dubu ?aya dai'dai a ku?in Nigeria ta kar?a, na gaya maku ganin ku?in take yi kamar dai'dai yake da ku?in Nigeria, ita dama ba shiga media take yi ba bare ta iya sanin farashin dollar, ba waya ne da ita ba, idan kunga ta ri?e wayar mamarta ma to game take bugawa da wayar, so bata san komai dan gane da fashin ku?in ba.
Hanyar gida ta nufa sai sauri take yi, kamar daga sama daga bayanta ta ji ance. Khadija................. A hankali ta juyo domin taga wanenen da ?o?ari ya iya ganeta a daren nan, hanyar ba wani haske ne sosai da shi ba, bugu da ?ari sabuwar unguwa suke, bata san kowa a unguwar ba to waye ya ambaci sunanta?
Tana juyowa sai taga......................??????
___________________________????
KINGDOM OF POWER ??????
Gimbiya Zunaira??
Ihu sosai take kurmawa da iya karfinta na karshe, wani ?osasshen doki da ya yi kanta a guje ne yasa ta san?are waje guda tare da kurma ihu mai sautin gaske, ga shi dai dokin da babanta yake yawan hawa ne, amma saboda rashin mutunci irin na dokin nan bai ji tausayinta ba ya yi kanta da nufin ya murkusheta, ko tsayawa bai yi ya ga kamanninta da King Zuhair ba bare ya tausaya mata...........?? (Wai doki bai san kamanni bane??? Meyasa ba zai tsaya ya fahimci tana kama da King Zuhair kuma jininsa bace???)
Kanta kawai ya yi da nufin ya tattaketa, haba tsabar tsorata har sai da numfashinta ya ?auke cak, tana ?o?arin zubewa ?asa Hoorain ya tareta da hannu ?aya ta fa?a saman faffa?ar chest ?insa, hannunsa ?ayan kuma da yake ri?e da yellow da jan kyallen ne ya fara ?a?awa dokin a face ?insa. Ai da gudu dokin ya juya ya bar wajen a in da ya bazama cikin sauran dabbobin, dukkan sauran dawakan sun watse sun bazama cikin gonar.
Jefar da kyallen ya yi tare da ri?ota da kyau yana kallon face ?inta, kamar dai kullum kayan warriors ne a jikinsa. Dama kun san tsakaninsa da Auta akwai amana sosai, to tun fitowarta daga family part ya hangota, yana tsaye da abokansa suna hira suna nisha?i ya hangota, tun daga kan yadda yaga tana tafiya ?ar tsan?o ya fahimci bata da gaskiya, ya fahimci akwai abin da take son aikatawa na rashin gaskiya, hakan yasa ya ce da abokan nasa yana zuwa.
Bai jira amsarsu ba ya bar wajen cikin takun jarumta, a hankali ya bi bayanta ba tare da ya bari ta sani ba, duk in taga maya?a sai ta ?uya, shi ma sai ya dakata da binta, idan ta cigaba da tafiya sai ya bi bayanta, idan yaga zata juyo sai ya ?uya, haka suka rin?a tafiya har izuwa bakin gonar. Lokacin da ya ga ta yi wa maya?an bakin gate ?in wayo ta saki tattabarun nan sun tashi sama sai da ta kusa sanya shi murmushi, ?ar karama da ita wai ita ma ta yi wayo, ta yi wa manyan warriors wayo, bata san cewa ba wayo ta yi masu ba, kawai dai a matsayinta na Gimbiya ne basu isa su ki bin umarninta ba shiyasa suka bi tattabaru, bugu da ?ari ta kasance Auta a cikin family, sannan ita ?in sanyin idaniyar kowa na cikin family ne, wannan dalilan yasa suka yi hakuri suka bi tattabaru.
Hoorain dai saura ka?an ta sanya shi murmushi, haka ya la?e ya zuba mata idanu yana ganinta har ta yi dabara ta bu?e kofar gate ?in ta shiga. Cikin tafasar jini ya rufa mata baya, sai dai yana zuwa ya tarar da ta kulle gate ?in ta ciki.
Ganin haka yasa bai yi ?asa a gwiwa ba ya yi zafin naman haurawa ta dogon kakkarfan katangar wajen, dan gudun kada wani abin ya sameta, shi yasan me a cikin gonar, sannan idan wani abin ya sameta ya shiga tara ba uku ba, dan shi King Zuhair zai hukunta, saboda alhakin kula da ita a wuyarsa yake, shi aka dam?awa kula da duk wata motsinta, so ko ciwo ta ji shi za'a hukunta, hakan yasa ya haura ta gini ya bi bayanta dan gudun kada babansa commander ya jibgesa, kunsan commander shi ne mai hukunta duk wani mai laifi, kuma gara mashi ace wani ya hukuntasa a kan Abbu ?insa, dan in ya kama shi mantawa yake yi da shi ?ansa ne, sai ya lallasashi idan sun je part nasu ya yi jinyarsa.........??
Commander namu baya wasa kuma baya son kai, aiki yake gudanarwa dai'dai tsakani da Allah.
Sosai ya ?urawa face ?inta ido yana kallo, ta tafi da tunaninsa, ga kuma tumatunta luwai luwai irin na Jaish in ji Mahreen kamar bread........??
Ya shagaltu da kallon kyanta ya fara jin ihun wasu daga cikin dabbobin wajen, gonar yana ?o?arin ru?ewa da kukan dabbobi daban daban, ba komai bane ya ja hakan kuma face ?allewan da dawakan nan suka yi, sun bazama cikin gonar, so sun watsa wasu daga cikin dabbobin ma. Kafin ya yi wani yunkuri sai ganin wasu daga cikin dabbobin ya yi suna ta watsewa, Auta ta ja komai na ?o?arin rikicewa.
?ago kai ya yi yana tunanin yadda zai yi da ita ya samu ya ka?a dawakan nan ya mayar da su wajensu, tunani yake yi a ina zai kwantar da ita, ga shi ta suma. Yana tsaka da tunani wani ?osasshen doki ya yo kansu a haukace.
Ai kuwa bai san lokacin da ya kwantar da Autar a ?asa a wajen ya mi?e ya tinkari dokin gadan gadan ba. Cikin jarumta ya yi nasarar kama linzamin dokin tare da daka wani uban tsalle ya haye bayanta. Haba wani irin haniniya dokin ya yi tare da ?aga kafafunsa biyu na gaban nan sama yana cigaba da yin haniniya, jan linzaminsa ya yi da karfi nan take ya ka?ashi suka nufi wajen da suke dama. Da gudun gaske dokin ya nufi wajen. Ciki ya mayar da dokin kafin ya dawo ya sa?i Autar a saman shoulder ?insa, kai tsaye ya nufi wajen da King yake zama idan ya kawowa gonar ziyara, akwai waje na musamman da aka tanada, ya sha kayan alatu da luntsuma luntsumar kujeru, an ?awata wajen matu?a da kayayyaki masu ?aukar hankali, sannan ga shinfi?u na alfarma irin na gidan sarauta masu kwalliyar gashin jimmina. Ga throw pillows da aka zuba a saman shinfi?un.
A saman doguwar sofa ya kwantar da ita ya juya, yadda yake tafiya a bu?e zaka gane yana da jarumta sosai, babu tsoro ko ka?an a tattare da shi, ko da yake assistant commander ne shi ?in, dole ya yi namijin jarumta sosai.
Wannan kyalle yellow and red ?in ya ?auko ya nufi dawakan dake ta gudu a cikin gonar, ha?a kansu ya fara yi yana ka?asu dan ya mayar da su in da suka fito.
A lokacin kuma warriors dake gadin gate ?in suka fara knocking na gate ?in ta waje cikin tashin hankali, dan kuwa sun san King ya hana kowa shiga wajen ba tare da izininsa ba, so idan suka yi wasa yau sai sun shiga hannun commander!....... Tab lallai kuna tsaka mai wuya, shiga hannun commander ai ba alkhari bane, kowa baya kaunar hakan!!.
Hoorain yana jinsu amma bai tanka masu ba, sai da ya mayar da dabbobin dukka, sannan ya nufi in da take kwance. Ruwa ya ?auko a cikin freezer dake wajen ya ?ariso wajen nata.
Cike da fargaba ya tarbo ruwan a hannunsa, hannun nasa na karma kamar wanda zai ta?a wuta ya nufi face ?inta da ruwan. Sarai yasan dokar masarautar ce, idan aka kamaka wani warriors ya ta?a ko da yatsar gimbiya ce to zaka fiskanci mummunar hukunci, akwai wani warriors da suka ta?a yin karo da Gimbiya Sarina, hukuncin yanke mashi hannu commander ya yanke mashi, sannan ya watsa shi prison na masarautar har na tsawon shekara ?aya, shi ne hukuncin ta?a jikin Gimbiya Sarina da ya yi. Amma ba'a yanke mashi hannun ba, uncle Abbas ya hana a in da da kyar ya shawo kan King Zuhair ya yarda ya yafe mashi aka mashi hukuncin shiga yarin masarautar na shekara ?aya.
So shi Hoorain yasan da wannan hukuncin shiyasa yake fargabar ta?a jikinta, ?azun da ya kamata bai bari ta ?arisa zubawa ?asa bama bai san ta ya aka yi ya rumgumota haka ba, bai san ina hankalinsa ya shiga ba har ya ri?ota haka, shi bai ma san ya aka yi ya iso gareta da zafi da kuma sauri haka ba, shi dai kawai yaga ya rumgomota bata isa ?asa ba, yanzu kuma da yake ya dawo cikin hayyacinsa shiyasa ya tuna da wannan hukunci yake kuma fargabar ta?ata.
Amma da yake babu kowa a gonar sai ya daure ya shafa mata ruwan a lallausan kumatun, yana yi kamar maras gaskiya ko kamar wani yana yi mashi la?e in ya ta?ata za'a gansa, bawan Allah sai waige waige yake yi.
Da kuka ta farka daga sumar tata, dan a tsorace ta sune, hakan kuma ya yi dai'dai da shigowar warriors dake bakin gate ?in cikin gonar, ta saman ginin suma suka hauro, dan suna zargin akwai mutum a ciki, saboda rufe kofar ta ciki da aka yi, kuma sun fi zargin Autar ce, dan ita ka?ai ce ta zo garesu yau.
Ganin warriors ?in sun shigo wajen yasa bai san lokacin da ya yi saurin kai hannunsa ya toshe mata baki ba, duk da yake matsayin assistant commander yasan ya karya doka, kuma duk da yake gaba da wa?an nan warriors da suka shigo, in fact umarninsa ma suke bi dan shi ya basu horo, amma dole ba zasu rufa mashi asiri ba, shi ya shigo aikinsu, a tsarin masarautar babu rufawa kowa asiri idan ya yi laifi, koda gaba yake da kai ya yi ba dai'dai ba dole ka fa?a, idan aka kama ku da wannan laifi na rufawa juna asiri a kan laifi dukkanku zaku fiskanci mummunar hukunci a hannun commander, coz su ma basa yarda su rufawa juna asiri gaskiya, suna da kula da doka basa karyawa.
Kewaye warriors ?in suka fara yi a cikin gonar suna neman wanene a ciki?.