Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 23
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 23: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 23. Ita kuwa Auta ganin shi yasa ta ?ara tsorata, dan bata yi expecting ?in…
3,368 words
Ita kuwa Auta ganin shi yasa ta ?ara tsorata, dan bata yi expecting ?in ganinsa a wajen ba, ga face ?insa dake cikin hular yakin nan ya ?ara tsoratata. Ya toshe mata baki yaki yarda kuma su ha?a ido dan baya son ganin yanayin dake saman face ?inta, yasan zata sha madarar mamaki na ganin ya ta?a jikinta, dan hakan abu ne da ko da sunan wasa bai ta?a kwatantawa ba.
Ta yi ?asa?e tana kallonsa, ga ragowar guntun hawaye a face ?inta. Dalilai biyu yasa ya rufe mata baki kuma yake ?o?arin ?uyanwa wa?an nan warriors ?in, na farko ita kanta Autar zata fuskanci fa?a a wajen King na ya hanasu zuwa wajen ita saboda rashin ji sai da ta zo, so sai ya yi mata fa?a, domin gudun gobe kada ta sake zuwa ta shiga wata muguwar dabba ta yi mata illa, so dalilinsa na farko Autar baya son ayi mata fa?a, dalili na biyu kuma shi kansa, shi ma ya karya doka ya shiga cikin wajen, sannan kuma ya ta?a mata jiki laifi mafi girma ma kenan ya aikata.
Ganin warriors ?in suna rinkaro ta in da suke ne yasa ya yi saurin zame hannunsa daga bakin nata ya mi?e tsaye, a hanzarce ya sa?eta a saman shoulder ?insa suka ?uya a bayan wasu dogaye kuma cunkusassun flowers dake ?an nesa da wajen da King ?in yake zama. Ita kam ta kasa iya ko motsawa, abin ya yi mugun bata mamaki, bata ta?a tunanin zai ta?a jikinta ko da sunan wasa ba.
Ko da suka ?uya a bayan flowers ?in bai sauketa daga jikinsa ba, da alama baya son ta ta?a ?asan wajen, dan ba takalma a kafafunta, ta zubar da su a garin gudunwa dawakai, kuma fa yaki yarda ya juyo su ha?a ido ko da sunan wasa, duk da a takure suke a bayan flowers ?in dan ba fa?i ne da wajen ba, sai ya mannata da faffa?ar kirjinsa ya juya mata face ta wani ?angaren.
Ita kuwa da bata da burin da ya wuce daga face ?insa dama sai ta kai hannunta saman face ?insa, juyo da face ?insa ta yi ya zamana suna fuskantar juna, ?asa ya yi da idonsa yaki yarda su kalli juna, ?ayan hannunta ta kai zata cire hular yakin nasa dan yau kam ta ga face ?insa.
____________________________??
CHUCHU AND JAWAD
A can cikin gida kuwa bayan sun kammala cin abincin nasu ne ya ce ta tashi su je wajen Momma, daga nan sai ta yi wanka ta cire kayan barcin jikin nan nata.
Da okey ta amsa mashi. Ko sallamar Aunty MieMie basu yi ba, su Yah Jawad bu?ata ta biya masoyiya ta dai'na zarginsa ko neman Aunty MieMie ba za'ayi ba, Aunty MieMie kam tana nan zaku zo ku sameta ne, zata yi maganinku ne.
Kai tsaye cikin gida suka nufa, ya ri?o hannunta suna tafe suna hira kamar wasu abokai, sai rigima take yi mashi yana biye mata, yau dan dolensa ya koyi rarrashi dan kada ta sake gudunsa kamar na baya.
Dai'dai tsakanin part nan mummyrta da hanyar zuwa part ?in King, hanyoyin sun rabu uku ne a wajen, akwai wanda zai sadaka da parlourn King, ?ayan kuma part na mummynta da yake itace uwargida ran gida, ?ayan kuma hanyar zuwa part na momman Auta, to a jikin na mommar ce na Maman Gimbiya Aneesa yake.
To a dai'dai tsakiyar hanyar ne suka hango Akka tana nufar parlourn King, sai ka?a kai take yi a cikin alkyabbarta, daga gani wani ya yi mata ba dai'dai bane zata kai shi ?ara wajen King, wlh Akka duniya ce, ka sake ka shiga gonarta ka shiga uku, yanzu fa wai kwana biyu bata ga Jaish bane take wannan sababin, za ta je ta kai kararsa wajen King a kan baya zuwa gaisheta ne, idan kuma suka je wajenta nan ma rigimace, in basu je ba laifi, kai wannan tsohuwa ba mai iya mata sai su Guyson.
Cike da murna Chuchu ta wage baki ta ce. "Akka ina zaki je?........".
Ai bata ?arisa maganar ba ya toshe mata baki tare da fisgota ta fa?a jikinsa, kafin Akka ta juyo ya yi baya baya ya shige hanyar ?akin Mummynta.
Shiru Akka ta tsaya tana jin kamar dai an kira sunanta, juyowa ta yi sai taga hanyar wayam babu kowa, girgiza kai ta yi tare da cewa tabbas ta ji an kirata, amma bari ta duba ko su waye ne?.
Ita kuwa Chuchu yanzu ta fahimci cewa Yah Jawad yana gudunwa Akka ne a duk lokacin da suke tare, dan haka sai ta ?udurta a ranta wlh sai ta rin?a yi mashi tsiya a duk lokacin da suke tare suka ha?u da Akka, ba zata kyale shi ba, lokacin ?aukar fansar wahalar da ya rin?a bata a baya ya yi.
Motsin alamar kamar mutun na zuwa ta part na mummyn nata ne yasa suka mayar da kallonsu wajen, ga kuma Akka tana zuwa duba waye ya ?irata?..............................Fata na dai Allah yasa Akka ta kamasu ta yi wa Yah Jawad ihun kwarto?? dan wlh ka?an daga aikin Akka ta ce lalata mata jika zai yi, dama suna da jikakkiya a ?asa, ta ce su yi aure sun kai karanta wajen yayanta King Badeen wai ta saka masu ido, shiyasa kuka ga ake ta wannan ?ar tsaman tsakaninta da su, dan kuwa sun kai karant an yi mata fa?a a kan ta kyalesu su ?ara girma kafin su yi aure ne?? wlh King Badeen ma ya iya goya masu baya, shiyasa fa Akka bata raga masu, dan suma basu raga mata wajen kaita kara, gaba da gabanta ne, to su sun ri?e can ?ololuwa sun fita iko, ita kuma ta ri?e iyayensu tana sanyasu yin abu dole?? ana show a wannan kingdom ?in wlh.
Na yi maku long page a tashi Kaina da ruwan Comments dan gobe na yi maku fin haka yawa, ga shi gobe zamu shiga weekend, so a zage ayi comments kila na baku update weekend din ma idan kun farantan.
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 4/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??STEP TWO....??????
E__________16
KINGDOM OF POWER ??????
Motsin alamar kamar mutun na zuwa ta part na mummyn nata ne yasa suka mayar da kallonsu wajen, ga kuma Akka tana zuwa duba waye ya ?irata?.
Rasa mafita Yah Jawad ya yi, tunani yake yi ya zai yi da Akka? Dan da Mummyn Chuchun ta kama shi da ?arta gara mashi Akka ta kamashi, yana jin kunyar mummy sosai, Akka kuma gobara ce daga kogi, sai Allah ne ka?ai zai iya kashe ta, idan ta fara bala'i ba mai iya mata sai yayanta su King.
Da alama mai nufosu ta part ?in mummyn waya yake yi, dan yana irin ya je gaba ya dawo bayan nan alamar waya tana da?i. Shiru ya ?an yi yana sauraron takun tafiyar mai nufosun, sai ji ya yi kamar Gimbiya Sarina ce, wato sistersa ?ar Mammie kenan, hakan yasa ya ?ara ?aure fuska sosai, dan in ta gansu a tare da Chuchu raini ne zai shiga tsakaninsu.
Bashi da mafita dai a yanzu, ita kam Chuchu ko a jikinta, sai ma tsiya da take son yi mashi idan Akka ta ?ariso wajen. ?an raba jikinsa da nata ya yi tare da zuwa hannun a aljihun wandonsa. Handkerchief fara tas mai shegen kamshi ya ciro, sannan ya matso bakin hanyar.
Haba wa Akka na isowa wajen saboda tsiya irin nasa sai ya ware handkerchief ?in nasa ya rufe mata fuska da shi tare da toshe mata baki dan kada ta yi mashi ihu. Da ido ya nunawa Chuchun hanyar part ?in momma a kan ta tafi.
Ita kuwa dan tsiya sai ma kara jingina da jikin bangon wajen ta yi alamar ba zata tafi ba, baya son bu?e baki kada Akka ta ji voice ?insa, yasan tsohuwar nan sarai ta haddace voice ?in kowa a gidan nan except voice na twins Obaid and Omaid, ai wa?an nan twins ?in wlh ko Jaish baya rabe voice nasu, ko King baya rabesu, mommarsu ce kawai take rabesu, ita ka?ai ce ko a duhu ta lalu?asu zata rabe Obaid ta cire Omaid.
Yanzu yana yin magana zata gane voice ?insa. Dan haka sai ya sake nunawa Chuchun hanya a kan ta gudu, ai kuwa make mashi kafa?a ta yi a kan ita gaskiya ba zata tafi ba. Kamar zai yi kuka, ga Akka kuwa tana ta ?o?arin kwace kanta ya toshe mata baki ga rufe mata ido da ya yi, sai ?o?arin ta?a jikinsa take yi dan ta tantance jikin waye ne ya yi mata wannan ?anyar aiki, tab wlh idan ya kuskure Akka ta kwaci kanta ya shiga ?ari biyar ba uku ba.
Chuchu da tsiya taki tafiya, kamar zai yi kuka ya marai rai ce mata fuska yana bata hakuri ta hanyar motsa lips ?insa, kin yarda ta yi ta make kafa?a tana toshe baki da hannunta saboda dariyar mugunta da ke son cubce mata.
Sai da ya wahala, Akka ta kusa kwatar kanta sannan Chuchu ta fara tafiyar yanga dan iya shege, har da wani murgu?a bashi good bye ?inta tana tafiya cikin sai?i kamar hawainiya, ji yake kamar ya jawota ya kifa mata mari, amma ba hali, zaman lafiya yake so da ita, haka ya hakura ya toshewa Akka baki yana kallonta har ta wuce ta hanyar part ?in momma ta kurewa ganinsa.
Sai da ya tabbatar ta yi nisa sosai, sannan ya ja Akka har parlourn King, yana zuwa ya turata saman sofar King ya juya da gudun gaske ya bar parlourn.
Ai kuwa a ?ari Akka ta mi?e ta fara surfa bala'i wai tasan wlh ?aya daga cikin jikokinta ne suka yi mata hakan, ko Jaish ko Jawad, dan sun fi kowa rainata a gidan nan, wlh ?aya daga cikinsu ne ya yi mata hakan, dan haka ba zata kyalesu ba, dole King Zuhair da uncle Abbas su zo su ?auka mata fansa, wlh ba zata yafe ba, har da cewa ita dai bata yi sa'an jikoki ba, har da karawa da cewa jikokin nata kamar masu kar?ar hu?ubar shai?an..........??
King dake ?akinsa yana shirin fita fada ne ya jiyota sai surfa masifa take yi. Hakan yasa ya fito da sauri. A zaune saman sofa ya sameta. A hanzarce ya kariso wajenta yana tambayarta lafiya?.
Ai ina a fusace ta ce ya kira mata Abbas da Jahiz a waya duk su bar abin da suke yi su bi jirgin safe su zo, sai sun zo sun ha?u zata fa?i abin da aka yi mata.......... Kai wannan mata akwai rikici, rikitacciyar tsohuwa ce, uncle Jahiz dake ?asar Brazil, shi kuma uncle Abbas ya tafi ?asar China baya nan, amma dan balai saboda ta nunawa su Jawad ita take da su shi ne sai an ha?o mata kan iyayen nasu dukka, kai Akka duniya ce, kar ka sake ?atacciya ta ha?oku, ba zata kyaleka ba, iyayenka zata sa a gaba, kana ji kana gani ranka na kuna ta zagesu tsab shi ne ta ?auki fansa.........??
King dai bashi da za?in da ya wuce ya bi umarninta, dan sai surfa masifa take yi, ?aki ya koma ya ?auki wayarsa, yau Yah Jawad ya ?allo ruwa, kingdom of power yau ba zaman lafiya.
Number uncle Jahiz king ya fara kira. A lokacin da kiran ta shigo wayarsa yana zaune a saman wata iriyar luxury sofa wadda babu irinta ma a yankin Africa, ku?i ta zauna mashi, tsayawa zayyana maku Daular guy ?in nan ma ba zai yiwu ba, domin kuwa babu irin wannan ginin a Africa ma gaba?aya, dollars ta yi kuka ta kuma yi mubaya'a, kun fa san manyan ?an kwallon nan ba ?aramin dukiya ne da su ba, bare shi Jahiz da yake shararren ?an kwallo da kowacce team ke son sayansa ya buga mata kwallo, dan kuwa in ya shiga filli fa jama'a har wani irin ihu da fito na musamman suke yi, idan ya ri?i kwallo ba mai iya kwata ta da?i a hannunsa. Sai dai fa shi ?in jinin mulki ne ke gudana a jininsa, akwai shi da izza ga shegen iya shariya, baya kula masoyansa ko ka?an, ko ?aga idanu baya yi ya gansu, amma a haka kuma suke haukar kaunarsa, idan ba wasan team nasu ba ma dayawan jama'a basu son zuwa. A baya Manchester united yake bugawa kwallo daga baya real Madrid suka saye shi da, billions suka sayesa, dan yana da tsada sosai, ?an kwallo ne mafi haza?a.
A gaskiya ma shi ya fi King Zuhair ma ku?i ba uncle Abbas ba tukun nan, ya samu duniya kam iya duniya saura lahira.
Zaune yake a saman sofa daga shi sai short jessy trouser zuwa gwiwa, ta sama kuma single ce fara tas, jessyn jikinsa ma ba ?aramin dukiya aka narka wajen sayansa ba, ga su da shegen kyau.
Guy ne iya guy, da ka gansa ka ga King Zuhair, babu banbanci kamar shi yake binsa wajen haihuwa, amma bashi bane, uncle Abbas ne, arab guy, fari tas da shi, ga hanci har baka, dollars ta zauna sosai, jikinsa har wani kyalli yake yi, cikakken namiji ne sosai, da ka gansa ka san ?an kwallo ne na gasken gasken. Kafafunsa na sanye da sillpers na cikin gida masu bala'in laushi, ya yi crossing leg ?insa, hannunsa na ri?e da tsadaddiyar cup na cappuccino ha?a??iya yana sha cike da class. Tsadaddun wayoyinsa ne a saman luxury glass table dake gabansa, ga wata tsadaddiyar laptop a gefe guda saman table ?in, wannan parlourn nasa kamar ba'a duniya kake ba zaka ji idan ka shiga, su kansu sofas ?in nasa kamar wasu jirage luntsuma luntsuma da su.
Wani irin dadda?ar kamshin mai kwantar da hankali ne yake yashi a ko'ina cikin parlourn, ga sanyi Ac mai ratsa zuciya. Sai dai kash dukka wannan alatun nasa bashi da mata, katan gwauro ne bai cika cikakken namiji ba.
Picking call ?in ya yi cikin nutsuwa, da alama yana da nutsuwa sosai da sosai, komai cike da class yake yi.
"Good morning bro!". Ya fa?a kamar baya son motsa baki, voice ?insa sak na King Zuhair, sun yi kama sosai gaskiya, jini ba wasa ba.
Daga can King ya ce. "Akka ta ce ku bar duk abin da kuke yi tana son ganinku yau".
Shiru ya ?an yi kafin ya ce. "Bro I have something very important to do, but me yake faruwa take son ganin mu? Ina da wasa champions league gobe fa".
Nisawa King ya yi. "Kai da ita ne wannan, ni dai na isar da sa?o, ka kira Abbas ka sanar da shi". Daga haka King ya katse kiran.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mayar da wayar ya ajiye.
Shi kuwa King komowa parlourn ya yi ya hau rarrashin Akka a kan tazo su je ciki ta gaya mashi me aka yi mata?. Shi kam Yah Jawad bin bayan Chuchun ya yi izuwa part na Momma abinsa, bai san Akka ta tada balli ba.
A parlourn ya iskota tana tsaye, ai tana ganinsa ta watsa a guje ta nufin ?akin Momma, sai dai kafin ta shiga shi ma ya tako da gudu ya ri?ota, ashe tasan ta yi mashi laifi, tasa shi ya kusa yin kuka.
Ri?o west ?inta ya yi, wage baki ta yi zata yi mashi ihu ya yi saurin rufe mata baki.
"Yau sai kin gaya mun idan ni sa'an wasan ki ne? Nace ki tafi sai kika tsaya kina ganina ko? Wlh saura ki gayawa Akka ni na rufe mata ido zaki ga yadda zamu ?are". Ya fa?a yana ?aure fuska kamar ba shi ne ?azun ya marairace mata fuska kamar zai yi kuka ba, yanzu kuma da ya samu ya ku?uta daga ha?uwa da Akka shi ne zai nuna mata jan ido.
Fitowar Momma daga room nata zuwa parlourn ne yasa ya saketa tare da juyawa zai bar part ?in.
"Zo nan Jawad". Momma ta fa?a tana nufar saman sofa. Da gudu Chuchun kuwa ta nufi cikin room ?in abinta, ta samu Momma ta kwaceta. Tana shiga ta fa?a saman sofa dake cikin room ?in ta hau ti?ar dariya kamar zararriya, sai ta yi dariya sosai sai ta ?an tsaya shiru, idan ta tuna yadda ya marairace mata fuska kamar zai yi kuka ?azun sai ta sake watsewa da dariya kamar ba lafiya ba.
Shi kuwa Momma ta zaunar da shi ta shiga gaya mashi ya kula sosai, dan yana da tarin makiya a tarayyarsa da chuchu, dan haka ya ?uye soyayyarsa, kada ya bari ma a rin?a ganinsu a tare, ya yi kamar ya mance da ita ko sun rabu, dan wanda ya yi ?o?arin rabasu ?in ya ji da?i ya kuma ciresu a ransa kada ya kara ha?a masu wani tuggun, idan ta samu lokaci ta zauna da king zata gaya mashi batunsu, sai a sanya masu rana ayi bikin kowa ya huta, amma yanzu ya kula ya kuma ?oye batun, sannan ya tsananta addu'a sosai, dan abu ne da ya ha?u da mushirikai, so ya kula sosai.
Sosai ya ji da?in maganganunta, addu'a ya yi ta zuba mata, sannan ya ce mata ta yi mashi izini gobe yana son zai bi bayan Jaish ya duba shi. Shiru ta ?an yi kafin ta ce. "Bin bayan Jaish ba zai yiwu ba, zan kira yayansa ya bi bayansa, amma kai kam ba zai yiwu ba, dan kasan cewa baya nan kai ma baka nan daddynku ba zai yarda ba, dole zai san akwai matsala, dan haka kai ka tsaya a nan kana ?ebe masa kewa kuma kasan yadda zaka yi da shi idan ya tambayi ina Jaish ?in, zan sanar da yayanku ya nemo Jaish ?in a koma ina yake".
Jinjina kai ya yi, ya gamsu da maganarta, amma kuma yana tunanin anya zai iya hakuri bai je ya duba ?an uwansa da kansa ba kuwa? Kai abin akwai wahala.
_________________________??
Auta.
Hannu ta kai zata cire mashi hular, a hanzarce ya ri?e hannun nata da nashi hannun ?aya, sannan ya ?ago idanu yana kallonta.
?an turo baki ta yi kafin ta ce. "Fuskarka nake son gani fa! Kullum kana tare da ni amma ban ta?a ganin kamanninka ba, to ni ba zan yarda ba, kai ba ka kalli face ?ina ba?".
Mai da kallonsa kan warriors dake nufar gate ?in fita dan basu ga kowa ba ya yi, sun hakura zasu fita daga wajen kawai. Zuba masu ido ya yi har suka fice a wajen, sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Sake hannunta ya yi tare da mi?ewa tsaye da ita, sauketa daga jikinsa ya yi, sannan ya nufi hanyar ficewa daga wajen ba tare da ya yi magana ba, da alama magana tana yi mashi wahala.
Tafiya yake yi yana tunanin ta ina zasu fita wajen nan ba tare da angansu ba? In dai suna son fita salum alum to dole sai dare, fitarsu da rana ba zai yiwu ba.
"Hoorain". Ta ambaci sunansa tana kumbura kumatu.
Tsayawa cak daga tafiyar da yake yi ya yi, a hankali ya juyo gareta, sai kuma ya kawar da kallonsa a kanta, da alama yana ?o?arin hana idanunsa kallonta ne dan tsaro ba dan tsoro ba.
"Na'am ranki ya da?e". Ya amsa yana mayar da hannayensa baya ya har?esu.
"Meyasa baka son na kallin face ?inka?". Ta fa?a tana ?aure fuska. ?an risinar da kansa ?asa ya yi. "Sorry ranki ya da?e baya daga cikin aiki na ne shiyasa".
Hannu tasa ta ri?o west ?inta tare da ?aure fuska. "Dama aikin da kake yi ma akwai wanda yake ce maka ga abin da zaka yi ne? Ai na ?auka kawai aiki zaka yi".
Jinjina mata kai ya yi alamar e umarni yake kar?ar kuma ganin fuskarsa bata daga cikin umarnin da aka bashi a wajen aiki.
"To ni yanzu na baka umarni ina son ganin face ?inka". Ta yi maganar tana nufo shi.