Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 24
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 24: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 24. ?an juya idanunsa ya yi yana kallon hanyar da take takawa, da alama shi ma…
3,342 words
?an juya idanunsa ya yi yana kallon hanyar da take takawa, da alama shi ma baya son ta ga face ?in nasa, ko me dalilinsa? Wannan sai al?awarina.
?asa ?asa yake satar kallon yadda take tafiya cikin nutsuwa sosai har ta ?ariso gabansa. "Please remove this thing let me see your face".
"Sorry ranki ya da?e, why are you want to see my face?". Still yana kallon ?asa ya yi maganar.
"Because you're the only person da ban san yaya face ?insa yake ba a cikin warriors mafi kusa damu, kuma i want to see it now".
Dawo da kallonsa cikin idanunta ya yi, wani irin fa?uwar gaba ya ji da ganinta cikin idonta da ya yi, bai san meyasa yake jin fa?uwar gaba a duk lokacin da suka ha?a ido ba, shiyasa baya son ha?a ido da ita, yana jin wani irin shock a jikinsa duk lokacin da ya ga face ?inta, ko daga nesa ya ganta sai ya ji zuciyarsa ta amsa.
"Please ranki ya da?e kada ki sanya na karya dokar aikina, kinga yau a dalilinki na aikata abinda King ya hana, na aikata laifi, yanzu haka ni mai laifine sosai, and am sorry to say please ki daina yi mun magana kada ki ja wani lokaci ?an uwanki su yi maki fa?a, kinga gaba?aya ?an uwanki basu son kina yi mun magana, a gaban idanunki ranar Prince Jaish ya daka mun warning a kanki, and kin ji abinda Prince Ramish ya gayawa Abbuna a waya wancan karon, a gaban idanunki dukka aka yi hakan, ni bawa ne kawai mai baki kariya, ko ba haka Prince Jaish ya ce mun wacan ranar a gabanki ba? Please ki bari kin ji? Bana son Abbona ya ?ata rai saboda hakan, ba zai ji da?i ace ya hanani yin abu kuma ina yi ba, ke yarinya ce mai zuciyar zinari, amma am sorry to say ?an uwanki ba haka suke ba, ke baki banbanta bayi da kanki ko maya?a da kanki dan kina kallon darajan ?an adam, amma ?an uwanki ba haka suke ba, bayi ko maya?a daban suke a gabansu..........".
Dakatawa da yin maganar ya yi sakamakon ido da ta zaro mashi, ta ?an bashi tsoro kuma ta ?ara yi mashi kyau.
"Yanzu Hoorain ?an uwana kake zagi a gabana?". Tana fa?ar haka ta fara ruwan hawaye.
Dukar da kansa ?asa ya yi yana fa?in. "Am so sorry princess, na yi kuskure ina neman ki mun afuwa".
Kin kula shi ta yi, kuka ta cigaba da yi har da cewa sai ta gayawa Abbonsa abin da ya yi mata, ya ci mutuncin ?an uwanta a gabanta. Hakuri ya fara bata yana fa?in ta yi mashi duk abin da zata yi mashi na hukumci, amma dan Allah kada ta gayawa Abbonsa, baya son ?atawa mahaifinsa rai.
Wucewa ta yi ta nufi cikin wasu bishiyoyin lemu dake ?an nesa da in da suke. Cikin takun jarumta ya rufa mata baya yana cigaba da bata hakuri.
A jikin bishiya ?aya ta jingina tana cigaba da kukanta. Gabanta ya ?ariso, cikin girmamawa yake bata hakuri. Rufe idanu gam ta yi taki kallon in da yake ma bare yasa ta dai'na kuma.
Zubawa face ?inta idanu ya yi yana kallon yadda zara zara eyelashes ?inta da suka jike da hawaye, ga hawayen a saman kumatunta, ji yake yi kamar ya sanya hannu ya goge mata hawayen nata, baya son ganinsu a face ?inta, amma yana tsoron ?ara laifi kan laifi dan haka sai ya shafawa kansa ruwan sanyi ya ha?ura.
Yana ?ago idanu sai kan wani katon kunama a jikin bishiyar da ta jingina ?in yana nufota, ga shi ya ?ana ?arinsa zai yi harbi. Ai bai san lokacin da ya matso dab da ita ya sanya hannu ya kamo kunamar ba.
Ita kuwa jin mutun ya matso kusa da ita yasa ta waro idanun nata waje, ganin shi ne ya matso dab da ita yasa ta yi ?asa ka?an ta matsa gefe guda sosai. Tana yin gefe ta ga ya kama kunama, ai ?ar kara ta saki tare da barin wajen a guje ta nufi wajen da King yake zama in da ya kwantar da ita ?azun kenan.
Shi kuwa ya yi saurin kaiwa kunamar hannu, ga shi ta ?ana zata yi harbi, aikuwa yana sanya hannu ta sake mashi harbi, sam bai damu ba tun ya kamata bata harbi gimbiyarsa ba. Sakinta a ?asa ya yi ya taketa da wannan kakkarfan takalmar nasa ya kasheta. Nan take hannunsa ta fara yi mashi zogi ta kuma kumbura sosai. Da yake jarumin gaske ne sai ya juya ya bi bayanta ba tare da ya damu da zogin da hannun nasa take yi mashi ba.
A saman shinfi?ar carpet ?in dake wajen ya zauna. Tun da ya nufota ta zubawa hannunsa da ya kama kunamar idanu tana ganin yadda wajen ya kumbura sosai, zaro idanu ta yi tana cigaba da kallonsa har ya ?ariso ya zauna. Nan take ta dakatar da kukan da take yi.
Yana zama ta sauko ?asa kusa da shi, duk da tana tsoron kunamar hakan bai hana ta kama hannun nasa dan ta gani ba. Wash ya ?an furta saboda ri?o hannun da ta yi. Cikin sauri da raunanniyar murya ta ce mashi sorry, ta yi maganar kamar zata yi kuka.
Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai ma so da yake yi ya kwaci hannunsa daga ri?on da ta yi mashi. "Me zan kawo maka ka shafa a wajen?". Still kamar zata yi kuka ta yi maganar.
?ago da kallonsa izuwa kanta ya yi da nufin ya ce mata ta bari amma sai ya kasa, da suka ha?a idanu sai ya kasa iya ce mata ta sake mashi hannu, shiru ya zuba mata idanu, ita ma kallonsa take yi tana begen ganin face ?insa, bata san meyasa yake mugun burgeta ba, ko dan yana bada ransa dan kula da ita ne?
Sun shagaltu da ganin juna, a hankali ta ?ago ?ayan hannunta ta kawo saman face nasa da nufin ta shammacesa ta cire mashi wannan hular, ita dai ta matsa sai ta kalli face ?insa.
Ai kuwa shima ?ago ?ayan hannunsa ya yi ya ri?o hannun nata ya hanata. Turo baki ta yi tare da fara ?o?arin kwace hannunta daga nashi.
Ba musu ya saketa, yana saketa ta sake kai hannun nata ita a dole yau sai ta cire taga face ?insa. Ai kuwa wannan karon da karfi ya damko hannun nata tare da janyota ta fa?a jikinsa, matso da face ?insa dab da tata ya yi da nufin ya yi mata magana yadda zata fahimtar ta daina ?o?arin cire mashi hular, amma suna ha?a ido sai ya kasa yin magana, zubawa juna idanu kawai suka yi, sai kallonsa take yi tana mamakin irin idanunsa, suna burgeta sosai da sosai, ita gaba?ayansa ma daga sama har ?asa burgeta yake yi. She love everything about him.
Da kyar muryarsa ta iya fita, sai sarkewa yake yi ya furta. "Please ranki ya da?e ki yi hakuri, dan Allah kada ki ja mun aiki babba da ba zan iya ?auka........." Dakatawa da maganar ya yi sakamakon gera ?aya da ta ?aga mashi. "Ka bu?e mun face naka na gani, daga nan ba zan sake abin da nake yi maka ba".
Bai san lokacin da ya ce mata. "Waye kuma ya koya maki ?aga gera ?aya?". "Yah JAISH". Ta bashi amsa bata kawar da kallonta daga kansa ba.
"Kuma ya yi maki kyau sosai". A sanyaye ya fa?i hakan.
Mamakin jin abin da ya fa?a ta yi, bai ta?a yi mata magana haka ba, shi daga kar?ar umarni sai aiwatarwa ya iya.
"Kin barni? Kin hakura da cire mun hula?". Ya fa?a ?asa ?asa. Kai ta girgiza mashi alamar a'a bata hakura ba idanuta a tsaye kyam a cikin nasa.
"But why?". Yadda ya yi maganar zaka fahimci ya yi nisa, baya tare da ita, da alama ya mance da wanda yake tare magana kawai yake yi.
Mamaki ne ya kara kamata, tunani ta fara yi a kan anya Hoorain ?inta ne wannan? Guy shiru shiru baya magana, yau tana son ?ata shi da magana, har tunani take yi dama yana magana bayan e da a'a kenan? Yau maganar tasa ma ta musamman yake yinta kamar ba shi ba.
"Hoorain to please meyasa kake ?uye mun face naka?". Kamar zata saka mashi kuka ta yi maganar. "Babu komai, kawai dai baya a tsarin aiki na ne".
"Tom shikenan sai wace rana zaka nuna mun?". A takaice ya ce mata. "Sai ranar da Abbona ya yarda na yi hakan".
Sai yanzu ta fahimci cewa shi yana aiki ne bisa umarnin babansa, Allah sarki, sai ta ji ya ?ara burgeta, baya son ?ata ran babansa "Amma kai kyakkyawa ne ko?". Da alama ta mance cewa a jikinsa take kwance. Shi ma da alama ya mance.
"A'a bani da kyau, ai babu wani kyau da kyansa zata yi tasiri a waje idan kina nan". Ya bata amsa yana cigaba da kallon face ?inta, daga karshe ma sai ya sanya hannu yana goge mata hawayen face ?inta na kukan da ta sha.
"Yanzu kana nufin kamar yadda Yah Jaish yake cewa nafi kowa kyau a gidan nan da gaske ne?". Jinjina mata kai ya yi alamar e da gaske ne tare da lumshe idanunsa.
Cool murmushi ta saki wanda ya ?ara mata kyau dimple ?inta suka lotsa sosai kafin ta ce. "To bari naje naga madubi".
Cikin sauri ya ce "Ai bamu ba fita daga nan sai dare, dan ba hanya". Zaro idanu sosai ta yi har sai da tasa ya kawar da nasa kallon daga kanta. "To ni yanzu me zan ci? And idan uncle na islamiyanmu ya zo karantar da mu ya zan yi? Wanka da sallama dukka a ina zan yi?".
?an shafa kumatun nata ya yi bayan ya gama goge mata hawayen nata. "Nima ban san me zaki cewa uncle naku ba, amma dai zan nemo maki abin da zaki ci, sannan zaki yi sallah a nan, kamar yadda na gaya maki sai dare zamu fita daga nan to hakan ne, dan dole fita zamu yi a sace ba tare da kowa ya ganmu ba".
Ta fahimci me yake nufi, sai dai tsoro ya kamata, me zata ce wa Mommarta da uncle ?in islamiyarsu and Gimbiya Chuchu, sannan idan Yah Jaish ko Yah Omar suka kira Momma zasu yi waya da ita ya zata yi?.
Katse mata tunanin nata ya yi ta hanyar ta?a mata lips ?inta a garin shafa kumatunta da yake yi, shi kansa bai san ya yi hakan ba sai da ta zaro ido tana kallonsa ya farga, dan yana shafa kumatun nata ne ya afka duniyar tunani wani abin da bai bayyanar mana ba ya barwa zuciyarsa.
Sorry ya furta mata tare da sauketa daga jikinsa ya mi?e tsaye, sai zogi wajen wannan cizon kunama yake yi mashi. Wucewa ya yi ya nufi wajen bishiyoyin dake wajen dan ya nemi maganin da zai saukaka mashi wannan zogin ya kuma cire dafin kunamar tare da ce mata yana zuwa.
Da kallo ta bishi da shi har ya kurewa ganinta, yana tafiya cike da jarumta sosai. Yana kurewa ganinta ta koma saman sofar ta kwanta tare da lumshe idanu, kafin wani dan lokaci barci ya ?auketa.
Ko da ya dawo sai ya samu ta yi barci. Tsayuwa ya yi ya zuba mata idanu yana ta kallonta, tsabar shagala da kallonta har ya mance da zogin da hannunsa ke yi mashi, hankalinsa ya bar jikinsa.
________________________????
A can cikin gida kuwa. Wanka Chuchu ta yi ta canza kayan jikinta, kwalliya sosai ta canca?a, kun san ta da shegen iya kwalliya dama, ta yi kyau sosai cikin riga da wando Pakistan dress, ta yafo gyalen kayan a kanta kamar wata amayar, ga shi kalar kayan pink and black sun yi mata kyau sosai.
Waje ta nufa bayan ta zuba perfume masu kamshi sosai. Room ?inta ta nufa. Wayarta ta je ta ?auko, a bakin bed ?inta ta zauna ta fara lalau?ar number Yah Rizwan, tana kewarsa sosai da sosai.
Bugu ?aya ya katse kiran ya kirata, shima yana kewarta sosai, sai kiranta yake tun ?azun bata ?agawa, yanzu da ya ga call ?inta ba ?aramin da?i ya ji ba, duk da suna tare da Ramish da har yanzu bai motsa ba hakan bai hana shi fitowa waje ya kirata ba, dan yana kewar voice ?inta sosai.
Hira suka fara yi cikin nisha?i, rigima ta sanya mashi wai ta yi kewarsa kuma tana son ya zo gaskiya ta ganshi ai dama ya ce mata zai zo, hakuri ya shiga bata tare da gaya mata zuwansu ba zai yiwu ba, sai dai wani lokaci. Sam yaki gaya mata saboda an harbi Ramish da bindiga yasa ba zasu zo ba, sai ya ?oye mata ya ce mata dai sun fasa zuwa wannan karon sai wani lokacin.
Kuka ta sanya mashi a kan ita lallai tana son ganinsa, shi ma da yake ya iya sai ya sanya mata rigima a kan to su yi video call su ga juna, kukan shagwa?a ta sanya mashi a kan ita a zahiri take son ganinsa. Sai da ya rarrasheta sannan ya ce mata dole zai zo ko dan aurensu, yana zuwa kuma ba ?ata lokaci za'a ?aura aurensu ya wuce da ita Dubai, jin hakan ne yasa ta hakura ta dai'na kukan.
Part ?in Akka ta nufa tana tafiya tana waya, a hanya ta ci karo da Gimbiya Fanan. "Chuchu Mammie na kiranki, wai ki zo yanzu". Cewar Fanan ?in.
"To Aunty Fanan ina nan zuwa yanzu bari na gaishe da Akka tun safe bamu gaisa ba". Da okey Fanan ta amsa mata tare da wucewa room ?in Momma......... Hmmm Fanan tana son zuwa part ?in Momma, kuma Mammien ?in tasu ce ta ce ta rin?a zuwa dan ta rin?a yi wa Momma abun kirki tana nuna mata halin kirki ta yadda ko sun samu sun shawo kan Jaish ya yarda zai aureta kada Momma taki yarda, kunga Mammie ta yi dabara, Momma zata ce Fanan yarinyar kirkice mai kyan zuciya, a wayo zasu saye zuciyar Momma, amma kam Mammie ta iya basaja.
Amma my people's me kuke tunani game da kiran da Mammien ta yi wa Chuchun? Menzata ce mata?.................
____________________????
NIGERIA...............JIMETA ????
Har dare can wuraren 9 bappa yaga su Mahreen basu dawo ba, ya san dai basa kwana a gidan Ar?o, kome za'ayi masu basa yarda su kwana, dan bai koya masu hakan ba.
Shi kuwa Jaish tun da ya bu?e idanu ya sake rufewa bai sake bu?ewa ba, wannan abokin bappan shi ma ya bada nashi gudumawar magungunar kafin ya wuce nasa gidan.
Bappa bayan son fita ya bar Jaish ?in shi ka?ai, dan haka sai ya le?a waje ya kira wani matashi dake zaune cikin matasan da suke kofar gidan suna hira. Ko da matashin ya zo sai ya ce mashi jeka gidan Ar?o ka kira mun su Mahreen, and ku taho tare fa.
Da to matashin ya amsa sannan ya wuce. Shi kuma Bappan ya koma cikin gida, ya ?auki abincinsa da Mahnoor ta zuba mashi a kwanonsa ya zauna kusa da Jaish ?in ya fara ci.
Wannan matashi kuwa ko da ya je Mahnoor dai ta ce yau a gidan Ar?o zata kwana saboda tsoron aljani Jaish, Mahreeh kuwa da yake bata da wani tsoro, dama yadda Jaish ?in ya waro idanunsa ne yasa ta tsorata sosai, hakan yasa ta bi bayan matashin suka komo gida, in takaice maku ma Mahreen kam ta mance ma da idanun Jaish sun bata tsoro, tuni ta shiga shargallen duniya.
Tana shiga ?akin Bappan ta hau gaya mashi ?azun aljanin nan da ya kawo ya bu?e idanu, ba ko sallama fa ta fara bashi labari, shi kam matashin nan ya juya ya koma abinsa.
Mamaki ne ya kama bappa a in da ya ce. "Mahreen kema yanzu kin yarda wannan bawan Allahn aljani ne? Kece ka?ai dama a kauyen nan baki yarda da cewa aljani bane, ko bappa ge?e da ya zo yanzu ya duba shi shi ma ya tsorata da ganinsa, ya dai daure ne kawai ya yi mashi magani, amma ya tsorata da ganinsa"
Zama ta yi tare da sanya hannu suka fara cin girkin Mahnoor a tare. "Bappa aljani ne nima na yarda, saboda idanunsa wlh sun kai ukun na Adda Mahnoor da ya bu?esu, suna da girma sosai gasu jajir kamar jini, amma fa ni bana tsoronsa koma aljanin ne, ai ina da karfi, kuma wlh ko aljani ne sai na ta?a kumatunsa, yanzu ma bari mu gama cin abinci nazo na ta?a, ni inaruwa ya je ya yi ta aljanancinsa a can ni dai kumatunsa yana mun da?in ta?awa, amma bappa wai daman menene aikin aljani ne da kowa yake tsoronsa?". Ta kai karshen maganar tare da ?age kai sama kamar mai tunanin wani abin, irin bari ta tuna wai shin menene ma aljanin?...... Mahreen manyan ?asa, wato ita fa dama bata ma san meyasa ake gudun aljani ba, in fact bama tasan me aljani yake nufi ba, wato dai ko Jaish aljani ne sai ta ta?a kumatunsa, gaskiya justice for kumatun Jaish, ya shiga uku da Mahreen, kai wannan yarinya sai shirin Allah.
"Mahreen ?in Bappanta, babu abin da aljani yake yi, kawai dai mutane ne suke tsaronsu, ina Mahnoor take? Taki shigowa saboda tsoron bakon nawa ko?". Cewar Bappa kwairaga.
"A'a bappa Mahnoor tana gidan Ar?o, wai a can zata kwana ba zata dawo gida ba dan tana tsoron wannan aljanin". Tana magana tana kai loma abinci bakinta.
"Kai kai kai aikuwa ba zai yiwu ba, bari na gama cin abincin nan ki zauna tare da bakon nan nawa in je in ?aukota". Da to ta amsa mashi ba ko tsoro.
Haka suka cigaba da cin abincin suna zuba hira har suka kammala, Bappan ya mi?e ya fito. Wanke hannunsa ya yi ya fice daga gidan zuwa gidan Ar?o.
Ita kuwa yana fita ta yi tsalle sai kusa da Jaish, hannunta duk miyar kuka ta rin?a shafe mashi a kumatunsa mai kama da madara saboda haske, duk da haka bai isheta ba sai da ta lakato ragowar miya daga cikin kwanon nasu, ta sanya ?ayan hannunta ta matse mashi ?an red lips ?insa ta tura mashi miyar da ta ?ebo a cikin baki tana fa?in. "Aljani kai ma yau ka ci abincin da Adda Mahnoor ta girka, wlh Adda Mahnoor ta iya girki sosai, idan ka ci sai kace a ?ara maka, sai ma idan ta dama fura ka ji shegen da?i". Tana magana tana tura mashi miyar a bakinsa............. Tab ina ga wlh idan Jaish ya kama Mahreen ba mai kar?arta, rayuwa kenan yau Prince Jaish da kansa ne yake shan miyar kuka a hannun Mahreen, wai lallai kuwa wani abin sai ciwo, shi da yake da shegen kyankyani, kuma tsabar iskanci irin na Mahreen miyar da suka ci suka rage take cusa mashi a baki, Innalillahi wannan yarinya ta gama da Jaish kaca kaca, subhanahu ni dai kam kome zata yi ina team ?inta iya wuya......??
Duk ta shafe mashi kumatunsa da miya, bayan ta gama ne ta zo ta zauna ta nutsu a gabasa tare da kura mashi idanu kamar mai tunanin wani abin a kansa. Can kuma ko me ta tuna ta hau zuba mashi surutu. "Aljani ka tashi mana, ko dai ku a garinku na aljanu baku tashi daga barci ne? Ka tashi muje kaga masarana a gonar bappa sun fara girma, kullum ina addu'a ruwan sama dayawa ya zo dan masarana ya nuna, zan tsamma idan ya nuna, ka tashi ka ci abinci dayawa, ko dai in ?ebo maka zaka ci ne?". Sam yarinyar nan bata da tsoro.
Shi dai yana kwance ko motsawa bai yi ba, yana dai numfashi da take nuna yana raye, bayan haka ba wani abin da zata tabbatar maka da a wani hali yake ciki.
Mi?ewa ta yi kamar wadda aka mintsina ta fito waje, kitchen ta shige wai zata ?ebo mashi abinci ta zo ta ciyar da shi....... Allah sarki bawan Allah ya samu gata har ciyar da shi za'ayi........??