Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 25
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 25: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 25. Ta ?ebo abincin kenan sai ga bappa, Nenne da kuma Mahnoor ?in, bappa ya je ya…
3,292 words
Ta ?ebo abincin kenan sai ga bappa, Nenne da kuma Mahnoor ?in, bappa ya je ya tasosu a gaba, amma da kyar suka yarda suka biyosa, sai da Ar?o ya ?ata rai, shi ma fa Ar?on ganin kyan Jaish yake yi kamar aljani ko rafani haka, dan kuwa shi ma bai ta?a ganin mutun irinsa ba, kawai dai ya daure ne ya ce Nenne ta bi mijinta ita kuma Mahnoor ta bi babanta tun da ya zo da kansa a karo na biyu.
Habawa suna shigowa Nenne ta yi maza ta shige ?akinta da gudu, wai dan ma kada aljanin yasan ta dawo da daddare ya shigo ?akinta ya sha?eta. Ita kuwa Mahnoor ta kan?ame bappa tana zare idanu.
"Gajin bappa me zaki yi da abincin da kika ?ebon nan? Ko dai baki ?oshi bane zaki kara?". Cewar Bappan. "A'a bappa na ?oshi, wancan aljanin zai je na bawa rabonsa a baki, shi kaga bai ci abincin ba".
Zaro idanu Mahnoor ta yi tare da cewa. "Ke Mahreen baki da hankali ko? Ke baki tsoro ko? Wlh yanzu dare ne sai kin je ya shakeki kin mutu ai". Ko a jikinta ta ce. "Adda Mahnoor kin cika tsoro, bappa ya ce aljani baya komai, kawai kune kuke tsoronsa, amma baya komai, to ni ko yana komai ma sai na je wajensa tun da yana burgeni". Tana kai karshen maganar ta yi maza ta afka cikin ?akin.
Da sauri bappa ya saki hannun Mahnoor ya bi bayanta dan kada ta je ta yiwa bawan Allah Jaish ?uren abincin dole, yasan ka?an daga aikinta kenan.
Ita kuwa Mahnoor juyawa da sauri ta yi zata gudu cikin ?akinsu saboda tsoro sai ji ta yi Hamma Faisal ya kirata daga ta kofar gida.
Dakatawa ta yi tare da juyowa. Da yake akwai hasken wata tankar sai ta iya gajinsa. "Hamma Faisal kai ne a daren nan?". A sanyayye ta yi maganar.
"Ni ne, na zo gidan nan kafa uku bana samunki sai bappa kawai, ni kuma na kasa iya komawa gida ba tare da na ganki ba". Ya kai karshen maganar tare da shigowa cikin gidan.
Kujera ta ?auko mashi daga cikin kitchen ya zauna a tsakar gidan, sannan ta ?auko mashi rabon abincinta daga cikin kitchen ?in ta kawo mashi, ta koma ta ?ebo mashi ruwa a cikin kwarya, ta rufe kwaryar da pai pai, baiwar Allah bata sanar da shi rabon abincinta bane, saboda kyan zuciya irin nata sai ta hakura ta bashi. Ta ci abinci a gidan Ar?o wajen kakanta Inna.
Da yake gidan kawunsa ne sai bai nuna wani pulako ba, da alama ya saba cin abinci a gidan, dan haka sai ya bu?e abincin ya fara ci, ?akinsu ta shige dan ita bata yarda ta yi hira da shi a cikin gida, kai ko a idanun Mahreen bata yarda su yi hira, Mahreen ?in ma kunyarta take ji, in kunga ta sake tana hira da shi to sun ha?u a wajen kiwo ne ya sameta ita ka?ai tana zaune, daga lokacin da Mahreen ta bayyana a wajen to hiranta da shi ya ?are, dan ko zai yi magana sau dubu ba zata amsa shi ba, sai Mahreen ta tafi, bare kuma ace bappa ko Nenne suna kusa, ai nunawa take kamar bata ta?a saninsa ba, kullum dare idan ya zo hira to shi da bappa suke hiran, ita dai idan ta kawo mashi abinci sai ta shige ?aki, idan ya gama hiransa da bappa sai ya tafi sai da safe in sun ha?u a daji, haka ake soyayyar gwanin ban dariya.
Tana shiga ta haye gado ta kwanta, already ta yi sallah a gidan Ar?o, kwanciya ta yi ta takure waje guda, dan tana tsoron gidan a yanzu, gani take yi kamar Jaish aljani zai zo ya sha?eta, sai tunani take yi a kan ita ta ganshi ma ta sa bappa ya kawo shi gidan, idan ma kashewa ne ita zai fara kashewa kenan, tuna haka yasa ta kara takurewa waje guda ta dunkule kamar maggi star.
Mahreen kuwa da kyar Bappa ya hanata ?urawa Jaish abinci, sun sha fama kafin ta hakura, zama ta yi kusa da bappan suka fara hira yana biyewa shirmenta da tambayoyinta marasa kan gado a kan Jaish ?in ko in ce aljanin nasu, haka bappa ya rin?a biye mata har san da barci ya ?auketa, sannan ne ya ji iskar duniya tana ka?awa, haka ya mi?e ya ?auketa sai ?akinsu, a kusa da Mahnoor ya kwantar da ita, hasken farin wata na haska masu har cikin ?akin nasu.
Yana kai ta ciki ya fito tare da zama kusa da Faisal saman kujera da ya ?auko daga kitchen, hira suka fara yi da Faisal ?in, kun san fulanin daji da iya hiran dare kamar rana, tsakar dare, zaka samesu zaune suna hira kamar wasu aljanu, ko tsoro basa ji, dare tamkar rana yake a wajensu. Haka bappa da Faisal suka yi ta hira har almost 11:40pm. Sannan ne suka yi sallama, Faisal dai ya cinye rabon abin Mahnoor tas ba tare da yasan rabonta ya ci ba. Dayawan lokuta rabonta take bashi ita ta hakura, dan Nenne kam bata bashi abin.
Bayan tafiyarsa ne Bappa ya koma cikin ?akinsa tare da ?auko wani tsummar rigarsa ya fito ya ji?ata da ruwa, ?akin ya koma ya gogewa Jaish ?in miyar kukan da take saman kumatunsa wanda Mahreen ta shafe shi da shi, tas ya goge mashi kafin ya kwanta a gefensa tare da yin addu'ar barci..ASUBA TA GARI IYALAN BAPPA KWAIRAGA.
Washegari da safe kamar yadda suka saba ne, bayan sun yi sallar asuba Mahnoor ta fito ta share gidan tsab, sannan ta je bakin kogi ta ?ebo ruwa kafa uku ta cikasa randunar dake cikin kitchen, bayan ta gama ta hura wuta ta sanya ruwan wankanta ita da Mahreen, da ruwan ya yi zafi ta juye a bakiti ta ?aura ruwan turo, already suna da ragowar miyan jiya, dama idan zasu yi miyar dare ha?e da na safe suke yi, da safe sai su yi sabon two su dumama miyar su ci da shi.
Da yake wutar tana ci sai da ta yi talge kafin ta shiga wanka, ita ka?ai a tsakar gida kamar aljana, tun karfe biyar take wannan aiki, ita kam Mahreen kafin bappa ya samu ta tashi ta yi sallar asuban ma ai sai an kai ruwa rana, wani lokaci da kuka take tashi har ta yi sallah tana kuka, tana idarwa a wajen zata baje ta cigaba da yin barcinta, bata tashi sai an tasheta su tafi karatu, nan ma wani lokaci da kuka take tashi.
Nenne kuwa sarauniya uwar mugaye, bata firowa sai karfe bakwai kafin nan Mahnoor ta gama girki ta gama komai, wani lokaci ma har sun tafi karatu.
Haka ta kammala duk wani aiki da kuka san mace tana yi a gidanta, kamar matar aure baiwar Allah, ta yi shirinta sannan ta tashi Mahreen a kan ta tashi ta je ta yi wanka su wuce karatu. Da kyar ta yarda ta tashi, tana turo baki ga shegen iya shagwa?a ta nufi cikin toilet ?in, ruwan wankan nata har ya huce, dan ma da zafi sosai Mahnoor ta surka mata, ya huce ya zama ba sosai zafin, haka ta yi wankan ta fito, kaya iri ?aya suka sanya doguwar riga ta atamfa ko?ad?iya.
Alqur'aninsu da bappa ya saya masu time da ya je Niger suka ?auka suka nufi ?akin bappa, a bakin kofa Mahnoor ta tsaya taki shiga, Mahreen kam tuni ta afka cikin da sauri ta je ta fara ta?a kumatun Jaish, wlh har ja kumatun nasa suka yi saboda ta?asu da Mahreen take yi, sun yi jajir da su, Bappa yana tsoron hanata kada ta tsayar mashi da kukan da ba karewa, rufin asirinsa ya rabu da ita, Mahreen ba kowa yake ta?ata ya zauna lafiya ba.
Gaishe da bappa Mahnoor ta yi sannan ta ?aura da cewa. "Bappa zamu tafi karatu".
"To Mahnoor ku kula sosai, sai kun dawo". Cewar bappan.
"To bappa, Mahreen zo ki wuce mu tafi". Da kyar ta fito daga cikin ?akin, wai ita a dole a barta ta zauna tare da aljaninta....... (Wayyo Jaish yana ganin rayuwa wai aljaninta kai jama'a maman Yasmin Mahreen bata da kirki sam sam??)
Suna fitowa Nenne na fitowa daga nata ?akin, nan ta fara surfa masifa a kan ina awakin ta? Ai Mahnoor bata isa ta bar gidan nan ba idan bata je ta kamo awakin nan ta zo ta ?auresu a cikin walden dake kusa da kitchen wanda aka ?an kewayesa da ?an gajeran matanga sannan aka yi runfa da zana daga ta sama, sai tirken awakai da aka kafa a wajen.
Mi?awa Mahreen Alqur'anin hannunta ta yi tare da cewa. "Mahreen ki je karatun kada ki yi lattin bari na kamo awakan nasan suna cikin awakan bappa ne, bari na kamosu na dawo da su sai in sameki a karatun".
Kar?ar Alqur'anin ta yi ta shige ?akunsu ta ajiye ta fito. "Muje mu kamosu tare, ke ka?ai zasu wahalar dake, kuma zasu sanya ki watsa awakin bappa su baki aiki, muje in tare maki".
"Wuce ki ?auki littafinki ki wuce karatu ba zaki tayata ?in ba". Cewar Nennen.
Ai a take ta tur?une fuska zata saka kuka, ganin haka yasa Nennen ta ce. "Sai ki wuce ki bita ?in ai chewing gum". Wannan shi ne biyayyar dole, idan aka ki yi mata biyayya taja asiri ya tonu wajen bappa, kai Mahreen duniya ce, yanzu zata yi wa Nenne hauka mai lasisi, rufin asirinta kawai ta barsu su tafi tare.
Bappa kuwa yana fama da Jaish da ya ?an motsa ka?an, sam hankalinsa baya a kansu bare ya jiyo hayaniyar da suke yi.
A tare suka fita, suna fita Mahreen ta ce. "Baga irinta nan ba, ai dama nace maki ki rabu da Nennen nan ta yi ta zama a gidan Ar?o, amma ke gaki mai tsoron Allah, to wlh Nenne ba zata barmu mu zauna lafiya ba da batun shegun awakin nan nata, ni watarana sai na kashesu dukka ma mu huta da masifar safe".
Ita dai Mahnoor shiru bata ce ko uppan ba, cikin garken awakin bappa suka nufa. Wata yarinya ce ta zo wucewa ta ce. "Ku ba zaku tafi karatu bako? Lokaci ya yi, sai Inna Rabi ta yi maku shegen duka ai, ku kullum baku gajiya da zuwa a makare, ko da yake baku gajiya da shan duka ne shiyasa".
Dakatawa Mahreen ta yi da tafiya tare da ri?e west ?inta, cikin tsiwa da masifa ta ce. "Ke Abu da su waye kike yi?". Ganin Mahreen ce ta amsa mata yasa a hanzarce ta ce. "Ni ba daku nake yi ba". A tsorace ta yi maganar, da alama tun farko bata lura da Mahreen ?in a wajen bane, yarinya ?ar karama ta zama zakanya a cikin kauyen, duk ?an mata tsoron masifar ta dana Nennenta suke yi.
"Da mu kike yi nafikijo (munafuka) ai mune kawai a nan wajen, zo nan munafuka!!". Cewar zakanya Mahreen, cikin tsawa ta yi maganar, irin ba wasa a tattare da itan nan.
Ai a ?ari da hamshin Abu ta watsa, gudu take yi da iya karfinta. ?age rigarta sama Mahreen ?in ta yi zata rufa mata baya. Da sauri Mahnoor ta ri?ota tana fa?in. "To Allah ya yi dare gari ya waye, rikicin duniya dukka sun tashi, wuce mu tafi ki rabu da ita, ke kowace safiyarki da fa?a take farawa, haba Mahreen yakamata ace yanzu kam kin rage jibgar ?a?an mutane".
Sai wani cija la??a take yi, taso ne ta bi yarinyar ta lallasa mata jiki, har da wani ?age riga zata yi gudu dan iya balai. Kwafa ta yi tare da cewa. "Wlh idan muka ha?u da ita a karatu sai na cire mata hakwaran bakinta na gaba, gobe ba zata sake kulamu ba, ?an banza duka zan yi mata sai dai Inna Rabi yau ma ta dakeni, amma sai na gwada mata na fita rashin ji".
"To na dai ji, zo ki wuce mu kama awakin nan mu mayar da su mu wuce karatun". Da kyar ta jata suka shiga cikin garken awakin. Awakin Nennen ?anana ne guda biyar da take kiwatasu a cikin gida, ita sune arzikinta, ji da su take yi, da daddare tana kwamcesu su sha iska, su shiga gidan mutane su yi ta ?arna a kitchen suna kalitan ?anzo a tukunya, idan sun gama ne sai su shiga cikin awakan bappa su kwanta, da safe kullum sai Mahnoor ta kamosu ta zo ta ?aure mata su. Ita kuma Nennen idan ta tashi ko sallar asuba ne taga awakin wasu a kitchen ?inta ta rin?a surfa masifa kenan ba ?aga kafa, ta kama akuya ta yi ta jibga dan ba nata bane....... Allah dai ya shiri Nenne, amma akwaita da son zuciya kam.
?aure awakin suka dawo suka yi kafin su ?auki Alqur'aninsu suka wuce makaranta.
Bayin Allan da suka je sai da suka sha bilala bibbiyu na latti. Ana tashi karatun kuma Mahreen ta capke Abu da duka kamar an aikota, kafin Inna Rabi ta zo ta rabasu fa?ar Abu ta sha ?an banza duka da cizo ha?e da yagushi, ta ji mata ciwo a fuska da yagushi. Ai Inna Rabi na dososu ta saki Abu ta watsa a ?ari sai hanyar gida, wlh duk iya shegen Mahreen bata tsayawa a daketa, kaunar lafiyar jikinta take yi amma ta iya jibgar jikin wasu ta yagushesu.
Hanyar gida ta nufa sai taga ai Inna Rabi zata iya biyota gida, dan haka sai ta nufi hanyar wajen kiwonsu, saboda izuwa yanzu tasan bappa ya tafi kiwo, a wajen kiwo kuma ko Inna Rabi ta zo hakuri bappa zai bata ta tafi, ba zai ta?a bari a dakar mashi autarsa ba, kafin zuwa gobe su je karatun kuma bappa ya je ya bada hakuri haka ake fama da ita kullum.
Ai kuwa hasashenta gaskiya ne, a can ta isko bappa yana zaune ?asan bishiya. Ita kuwa Mahnoor gida ta nufa dan ta mayar da qur'anansu kafin ta wuce wajen kiwon nasu. Inna Rabi kuma ta ?auko bayafi tare da ri?o hannun Abu suka bi bayan Mahreen dan ta je ta ha?esu ta ji me ya ha?asu fa?a, bata yanke hukunci ba tare da ta ji ta bakin kowa ba, sai ta ha?esu ma take tambayarsu ta yadda ?aya na zai cuci ?aya ba.
Ko da Mahnoor ta shigo gidan babu kowa, Nennensu ta shiga ma?ota, kun san fulanin daji da shegen iya zuwa ma?ota, suna ?aukar kamar gida ?aya suke, yanzu yanzu zakaga wannan ta shiga ma?ota wannan ma ta shiga nan, rayuwarsu dai akwai ban sha'awa yadda suke kamar ahali ?aya. Ganin Nenne bata nan ne yasa ta wuce ?akinsu ta ajiye Alqur'anan, tana fitowa shi ma Jaish yana fitowa daga ?akin bappa, ya dafe kansa dake barazanar tarwatse mashi da hannu ?aya, jiri ne yake ?ebarsa, ya dafe jikin kofar fitowa
Ai a ?ari ta..............
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 7/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
E_________17
Ai a ?ari ta kurma ihu tare da nufar waje da gudu. Ko kallon in da take ma bai yi ba, shi gidan ma yake bi da kallon kyama da ?askanci, daga sama har ?asa yake karewa gidan kallo, har wa yau idanunsa suna nan jajir kamar jini, da alama akwai abin da ya sami idanun nasa.
Mahnoor kuwa bata zame ko'ina ba sai wajen bappa, tana zuwa ta iskosa ya gama case da su Inna Rabi na jibgar Abu da Mahreen ta yi, ya shiga cikin dabbobinsa yana raba wasu shanu guda biyu fa?a.
Da kyar ta iya ?arisawa wajensa a cikin tsakiyar dabbobin, sai haki take yi tana numfashi sama sama. Sam bai lura da ita ta zo da gudu ba, hankalinsa yana kan dabbobin, ita kuma Mahreen tana zaune tana cin gwaiva da bappa ya tsinko mata dan ya yi mata nasiha. Idan kana son zaman lafiya ka yi mata nasiha kuma ku zauna lafiya sai ka bata wani abin.
Haka bappa yake yi mata, sai ya bata gwaiva ko rake ta nutsu tana sha sai ya yi mata nasiha a nutse, a haka sai kuga ta ?auki maganarsa in ta yi niyya, tafa san daidai yarinyar nan, kawai dai idan anyi mata ba daidai bane take mantawa da wani daidai ta rama abinta, amma sarai ta san me take yi.
Ganin ta ?ariso wajensa tana ta zuba uban haki ga numfashinta na fita sama sama ne yasa ya yi saurin ri?ota yana fa?in. "Mahnoor lafiya kuwa?".
Kasa amsa mashi ta yi, saboda uban gudun da ta sha, numfashinta bai dai'dai ta ba bare ta iya yin magana. Hannunta ya ri?o suka fito daga cikin dabbobin, in da Mahreen ke zaune suka nufa. Gorar ruwansa dake wajen ya ?auko ya bata tare da zaunar da ita a kan ta zauna ta nutsu ta sha.
Ba musu ta kar?a ta sha sosai, gaba?aya a rikice take, sai zare idanu take yi kamar wadda taga wani abin da babu irinsa a duniya, ko da yake a wajensu babu irin Jaish a duniya, dan basu ta?a ganin mai kyau irinsa ba, dole su ?aukesa kamar babu irinsa a duniya........ Ni kam na ce dan ma ba kuga Guyson nawa and Auta Zunaira ba, ai da kun mace saboda kyau.
Sai bayan ta samu nutsuwa ne Bappan ya ce. "Me ya faru Mahnoor?".
A matu?ar tsorace take ta amsa mashi da. "Wannan aljanin da ka kawo ne ya fito daga ?akinka". Yadda ta yi maganar a ru?e take.
Ai bata ?arisa maganar ba ya yi saurin wucewa yana ce masu. "Ku jirani ina zuwa, ai abin da muketa tsumayi kenan tun jiya, farkawarsa kawai muke fata dama".
Kallon Mahreen dake ta sabgar gabanta hankalinta baya a kansu ta yi tare da cewa. "Ke gaji aljaninki ya tashi har ya fito waje". Ta yi maganar tsoro na kara bayyana a saman face dinta. Ai kuwa ita kam Mahreen tsalle ta buga tare da mi?ewa tsaye ta ce. "Dan Allah? Wayyo Allah bari na yi sauri na je na gansa". Tana kai karshen maganar ta watsa a guje sai hanyar gida kamar ba yanzu bappa ya ce su jira shi yana zuwa ba.
Kafin Mahnoor ta bu?e baki ta dakatar da ita tuni ta wuce kamar wata walkiya, fiw ta wuce kamar iska tsabar iya gudu, daga karshe ma ta riga Bappan nasu isa gidan, a hanya ta wuce shi, kamar bata gansa ba, shi kuwa da ya ganta kafin ya bu?e baki ya kirata tuni ta wucewa ganinsa, yadda kuka san iska haka take da gudu.
A dubu sittin ta shiga gidan babu ko sallama. Yana tsaye a in da Mahnoor ta barosa, yana dafe da bango da hannu ?aya, hannunsa ?aya ya dafe kansa yana kallon ?asa ya sunkuyar da kansa.
Kai tsaye gabansa ta nufa a kuje, da kyar ma ta iya taka birki ta kama kanta bata afka jikinsa ba, tsabar yadda ta shigo gidan a guje, gudu ta yi da iya powerta dukka.
Sarai ya ji motsinta kuma ya ji gudun da ta yi har ya zamana da kyar ta kama birki a gabansa, amma yadda kuka san babu shi a wajen, sam bai motsa ba bare a yi tunanin ya ji shigowar mutum, da ni da ku dai mun san halin kayanmu daman, mun san ya yake, su Mahreen ne baki a sanin halinsa.