Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 26
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 26: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 26. "Yauwa ginnaji amin a fini ko? (yauwa alajinmu ka tashi ko)?". Yadda ta yi…
3,363 words
"Yauwa ginnaji amin a fini ko? (yauwa alajinmu ka tashi ko)?". Yadda ta yi maganar tana haki zaka fahimci ta saba dallawa a guje, ma'ana ta saba yin gudu, dan bata wani wahala ba, ita kuwa Mahnoor wannan gudun da ta yi sai wani irin haki take yi kamar numfashinta ba zai dai'dai tu ba, amma Mahreen ai shar, wannan da za'a saka gasar gudu a kauye na tabbata sai ta fi kowa, ita zata zo na ?aya, gata ?ar siririya, haba my people's karku ga yadda take pella kafafu idan ta arce a gujen.
Sarai ya ji anyi magana, amma bai san da wani yare bane, dan haka bai gane me aka fa?a ba, kuma dai yaki ?ago kai ya kalli wace aljana ce take a gabansa, dan ma Allah ya rufa mashi asiri yau kwalliya ka?an ta ?an yi kafin su tafi karatu da suka yi wanka, sai dai ta cika powder nan nata da ta saba a fuska, amma ba'a lapka janbaki sosai ba, dan Mahnoor ta ce mata idan tasa ka?an ta fi kyau, sannan yau bata ?ata fuskar da bakin kwalli sosai ba.
Ganin bai amsa mata bane yasa ta ?ago da kallonta a kansa, sai a lokacin ta zaro idanun tana kallon tsawonsa da ya fi bappanta, kun san tun jiya a kwance yake, sai yanzu ta gansa da kyau. Ai a ?ari ta ?aga kanta sama ta kai kallonta saman fuskarsa. Da yake kan nasa tana du?e ?asa sai bata wani iya tantance face ?insa da kyau sosai ba, amma dai taga kumatunsa da yake jajir saboda mulmula mashi da ta rin?a yi.
Saboda rashin tsoro irin na yarinyar nan hannu tasa ta ?an ta?a plat tummynsa, dan a iya nan taawonta ya tsaya, ba zata iya ta?a shi a sama da haka ba. Ta?a shi ta yi tare da cewa. "An kam a wala volwa na? (Kai kam baka magana ne?)".
Daga hannun nata da ta ta?a shi ya fara bi da kallo kafin ya kai kallonsa saman face ?inta. A lokacin ita ma tana kallon face ?in nasa da kyau, ai kuwa suka yi four eyes. ?an zaro idanu ya yi da ganin face nata da ya yi, ba komai yasa ya zaro idanu ba face kwalliyar dake saman face ?inta.
Ai kuwa yana zaro idanun nasa da suke ja ta sakesa tare da kurma ihu ta yi baya baya ta fa?i ?asa, dan kuwa ya bata tsoro, ga idanu manya manya, sannan gasu jajir kamar jini, duk yadda aka yi akwai abin da ya samu idanunsa wlh, dole akwai abin da aka sanya mashi a cikinsu ko kuma ya sanyawa kansa, dan sun yi wani irin ja mai ban tsoro, duk wanda ya kalli cikin idanun nasa sai ya tsorata sosai. Dani da ku dai mun san idanunsa farare ne.
Tana fa?uwa ?asa numfashinta ya ?auke diff, shi kuwa yana ganinta ta zube ?asa bai taimaka mata ba, sai ma hannunsa da ya cire daga saman goshinsa ya dafe cikinsa da shi, dan wani irin mur?a mashi da cikin nasa ya yi da karfi, wani irin zafi ya ji shiyasa ya dafeta. Wani irin kwa?e fuska ya yi saboda kyama, shi Mahreen kyama sosai ta bashi, a ganinsa ta yi datti over, bai san nan ta sha wankarta ba, kayan nata ne kawai suke ko?e kamar masu datti, amma ba wani datti, dan suna da tsabta sosai.
Shi kuwa mugun kyama ta bashi, barema gidan nasu da ya kallah, dama tun da ya bu?e idanu ya kalli in da yake cikinsa ta fara mur?a mashi, wannan dalilin yasa ya fito waje ko zai samu sassauci. Ai kuwa yana fitowa ya ci karo da su bukka gidan ?asa nan take kansa ya fara sara mashi, hakan yasa ya dafe kan nasa ga cikinsa na juyawa.
Wani irin amai ne ta kwace mashi. Da kyar ya iya jan kafafunsa ya matsa daga bakin kofar, a tsakar gidan ya dakata ya fara tikar amai mai sautin gaske, kamar zai amayar da ?a?an hanjinsa.
A wannan hali bappa ya shigo ya samesa, ga Mahreen a sume kwance a ?asa. Ganin yana ta amai yana ?o?arin fa?uwa ?asa dan jikinsa babu kuzari ko ka?an ne yasa bappa bai bi ta kan Mahreen ba ya yi kansa yana yi mashi sannu da harshen fillanci.
Hannu yasa ya ?an ri?osa dan kada ya fa?i, sai layi yake yi kamar wanda ya sha wani abin na maye, a hakan ma kuma wai ya yi ta maza ya rike kansa da ?an sauran karfin da ya rage mashi. Bawan Allah sai Allah ne ka?ai yasan kwanansa nawa rabonsa da abinci........... Tab akwai cakwakiya, anya Jaish zai iya cin abincinsu kuwa? Anya zai iya yarda ya ?ara minti ?aya a cikin gidan kuwa? Akwai matsala, already kun san shi da muguwar kyankyani dama, ga shegen izza da suna isa, akwai dai matsala babba!!.
A hanzarce bappa ya ri?esa, a lokacin amai ?in yake ti?awa da gasken gaske, bai ma san an ri?esa ba, duk in ya tuna kwalliyar kan fuskar yarinyar da ya kallah yanzu wato Mahreen sai cikinsa ta sake mur?a mashi, aman nasa ma banda zallar ruwa dake fita ka?an ka?an babu komai, dan babu komai a cikinsa, bai ci abinci ba, sai uban kakari da karfi da yake yi ba wani aman kirki.
Ya ?an jima a sunkuye a wajen kafin ya fara sassauta mashi, wlh ba karya ya wahala matu?a, dan wannan kakari da yake yi duk ta ?ara nukurkushe mashi ?an karfin da ya rage mashi, ba dan bappa da yake rike da shi ba da ya jima da zubewa ?asa, amma Allah yasa bappa ya ri?esa, ya wahala idanunsa sun ?ara yin jajir kamar wuta, wasu siraran jijiyo ne suka fito mashi a forehead ?insa, ga wani uban zufar wahala dake tsastsafo mashi a face ?insa, harta zara zaran eyelashes ?insa sun ji?e da gumin da ta wanke mashi face ?in nasa, red lips ?insa sai kerma suke yi alamar yana jin sanyi kuma babu kuzari a tattare da shi, arab hairn nan nasa ya watse caka caka kamar bai ta?a sanin menene gyara ba.
Lokacin da ya ?an dawo dai'dai aman ya tsaya, a hankali ya ?ago idanunsa da suka yi mashi nauyin ?agawa, kai kallonsa ya yi ta gefen da bappa yake dan yaga waye ya ri?esa?.
A dai'dai lokacin kuma bappan ya ce. "Allah sarki a yari bone sosai, sannu, jo?u bari mi wandina ma diyam a lota hundukoma be ?anduma, (Allah sarki ka sha wahala sosai, sannu, ka zauna bari na kawo maka ruwa ka wanke jikinka da bakinka..........."
Ai bai ?arisa maganar ba ya dakata sakamakon turesa da Jaish ?in ya yi gefe guda har sai da ya fa?i ?asa. Tattare dukkan sauran karfi da suka rage mashi ya yi ya ture bappan tare da zubewa ?asa a saman gwiwowinsa ya cigaba da yin kakarin amansa, sai dai aman taki fitowa, da alama ruwan dake cikin nasa ne ya ?ara.
Ba komai yasa ya ture bappa ba kuma face kyama, a cewarsa bappa na wari, sannan ya ji kyamar kayan jikinsa......... Ni kam nace zan ga wannan cakwakiyar ya zata ?are, yo idan bappa yana maka wari zanga mai yi maka magani, kai in short ma zan ga wanda zai taimaka maka ka tashi daga wajen da kake yin aman ma kafin aje ga batun magani, gaskiya da babbar matsala!!!.
Bappa dattijon kirki mi?ewa ya yi tsaye, sam shi bai kawowa ransa kyamansa yasa Jaish ?in ya turesa ba, ya yi tunanin ma ko dai Jaish ?in ya ?an samu wata matsala a ?wa?walwarsa ne, dan haka sai bai damu ba ya ka?e jikinsa tare da sake matsowa ya ri?e kafa?un Jaish ?in ya yi mashi sannu cikin sanyin murya, ga Mahreen kuwa a sume kwance a ?asa, duk yadda bappa yake kaunar yarinyar nan amma ya nufi Jaish dan ya karrama kalmar nan ta bakonka annabinka, sarai kuma ya ga Mahreen ?in, amma saboda kyan zuciya irin nasa sai ya za?i ya fara taimakawa bakon nan nasa, bai san cewa bakon nasa iyashegensa in ji Yah Jawad tana da yawa ba, i really like Yah Jawad, musamman yadda yake fa?arwa Jaish ?in gaskiya, ga shi ya gaya mana gaskiya rashin kunya yake damun Yah Jaish ba kunya ba...........??
Ko ya zai yi a karo na biyu idan ya ?ago ya ga still bappa da yake kyama ne ya ri?esa?...... To ni dai bari na le?a Dubai mu gani.
DUBAI.......ABU ABDUSSALAM EMPIRE??
Kamar yadda ?an tahalikan nan suka fa?a haka kuwa a kayi a gidan suka sake kwana. Washegari da safe tun karfe biyar da suka tashi suka yi sallar asuba basu mayar da barci ba.
Misalin karfe 5:30 suka tsala wanka, Obaid ne ya fara yin wankar bayan ya fito Omaid ya shiga. Da yake su a dukkannin gidajen uncles ?in nasu suna da kaya a rooms ?insu sai suka shiga dressing room ?in suka fara shiri.
Wando three cuter na ?aya daga cikin uniform nasu na swat suka sanya a jikinsu, sai farar t-shirt mai karamar hannu mai laushi sosai. Wow arab hairn nan nasu ya sha gyara na ?in ?arawa, sun yi kyau sosai, bafa zaku ta?a iya rabesu ba.
Komai nasu gwanin birgewa da ban sha'awa, suna kaunar junansu over, ga su da shegen son wasa da juna, yanzu haka da suka shiga yin brush bayan tashin su daga barci sai da suka yi ta tsokanar juna, Obaid na goge bakinsa yana wani lumshe ido irin barci bai isheshi ba, ya ratayo karamar towel a wuyarsa yana goge bakin kamar yana jin tsoron ta?a hakwaran nasa. Da gangan Omaid ya shigo cikin toilet ?in ya salalla?o a hankali ya zo ya kwace brush ?in da yake goge bakin nasa da shi ya sanya a nasa bakin ya fara goge nasa fararen hakwaran.
A kule Obaid ya bu?e baki zai yi magana, ruwa Omaid ?in ya tarfo daga pampom dake wajen wash hand base ?in ya watsa mashi a fuska, shi ma a fusace ya tari ruwan ya fara watsa mashi ba dakatawa har sai da Omaid ?in ya gudu ya fita daga toilet ?in da brush ?in a bakinsa, ?auko wata brush ?in Obaid ?in ya yi tare da ha?a wani tsadaddun mayukan goge bakin nasu, sannan ya cigaba da goge bakinsa, haka zaku gansu suna wasa gwanin birgewa, amma kada kuso ku gansu suna shiryawa wani mugunta, a wannan part ?in sam sam basu da da?in kallo.
Bayan sun kammala shirinsu Obaid ne ya fara ficewa waje daga ?akin. Omaid ya rufa mashi baya, sai dai shi Omaid yana fitowa part ?in brothers ?insu ya nufa, domin ya gaishesu ya duba jikin Ramish, shi kuwa Obaid da hannunsa take ta faman yi mashi kaikayi na ya je ya jibgi wa?an can criminals ?in ai waje gaba?aya ya nufa.
A ?angaren Leesharh kuwa, tasata a gaba Sharifat ta yi a kan lallai ta zo su je ta gaishe da Yah Ramish ?inta. Sosai Leesharh ta tsorata, tana tsoron shiga ta gansu, dan da yake bata da gaskiya sai taga kamar idan suka ganta zasu gane abin da ta zo yi, wannan dalilin yasa bata son zuwa in da suke ko da Sharifat ta bu?aci hakan. Amma da yake yau rashin lafiya ne sai ta ce to su je ta gaishe da su ?in.
Wanka ta yi ta shirya cikin arab abaya mai shegen kyau launin maroon color, ta yi matu?ar kyau sosai da sosai, ta yafa gyalen kayan a kanta, ba make up sai natural beautynta.
Fitowa suka yi suka nufi part na su Ramish ?in, zuciyarta sai dukan uku uku yake yi, fargabarta ?aya me zata je ta tarar? Wannan shi ne fargabar da take yi.
Baki a ?auke da sallama suka shiga room da Ramish ?in yake kwance, gaba?aya family suna a tare da shi except Obaid da yake ?akin horo yana aikin da ba'a sanya shi ba. Omaid kuwa yana tsaye a kusa da Guyson yana latsa wayarsa, hankalinsa ma baya a tare da su, sai magana Abu Abdussalam yake yi mashi hankalinsa ya yi nisa, chatting yake yi da wata class mate ?insu da ta kasance kawar Obaid, Obaid suna shiri da yarinyar, sabuwar zuwa school ?in ce, ni da ku dai mun san sai hali yazo ?aya ake abota, to dai da walakin goro a miya a kan wannan yarinyar. Chatting yake yi da ita in da take gaya masu yanzu daddynta zai mayar da ita school su kuma sai yaushe zasu dawo?....... Nikam nace baban wannan yarinya da kasada yake, yarinya mace da aikin swat fisabilillahi, gaskiya bai kyauta mata ba, daga gani ita ma bata jin magana a gida kamar dai su ?in.
Wani irin muguwar fa?uwar gaba Leesharh ta ji lokacin da ta sauke idanunta a kan ?a?an King Zuhair, musamman ma Bilal da yake tsaye a kan Ramish dake kwance kamar gawa, ha?i?a Bilal ya shiga tashin hankali sosai, idan ka gansa gaba?aya a hargitse yake saboda tashin hankali, sai ka tausaya mashi.
Tun da suka shigo ta tsaresa da idanu tana ?o?arin tuna a ina ta ta?a ganin face ?in nan, tabbas ta ta?a ganin face ?in Bilal a wani waje, to a ina ne? Ta mance, amma tabbas daga fitanta a gidan AAJ zuwa yau akwai in da ta ta?a ganinsa. Sai dai kuma da ta sauke kallonta a kan Dr Raj sai ta kasa iya banbancesa da Bilal ?in kuma, sai ta shiga ru?anin waye ta ta?a gani a cikinsu? Kuma basu wani kama sosai, kawai dai jini ba wasa ba, sannan kuma kowani ?an adam da yadda yake kallon mutun, kai zaka iya ganin kamannin wane da wane amma ba lallai wani kuma ya ga kamannin ba.
Bata ?ara shiga fargaba da faduwar gaba ba sai da ta sauke idanunta a kan Ramish dake kwance, Allah ya gani tana tsoron wannan bawan Allah, ba komai ya ja mata wannan tsoro ba kuma face rashin gaskiyarta, yanzu a jikinta tana jin cewa tabbas cutar da shi masu nikaf suke son yi, amma duk da haka bata tunanin kin taimaka masu saboda tana son babanta sama da kowa a rayuwarta.
Shiru ta tsaya tsoro da fargaba ya hanata yin magana kuma ta kasa ?arisawa cikin ?akin. Omaid ne ya nufo hanyar fita daga ?akin yana latsa waya, hankalinsa ya yi nisa wajen chat da wancan yarinyar. Yana can yana ta?a waya har ya ?ariso tsakiyar ?akin, bai ankara ba ya bangaji Leesharh dake ?o?arin kauce mashi hanya da ta gansa ya nufo in da take tsaye.
Ai kuwa yana bangazarta wayar hannunsa ta fa?i ?asa. A ?ari ya ?ago kansa tare da zare idanu, ganin itace bai yi wata wata ba ya cire hannu ya dalla mata mari mai sautin gaske wanda yaja gaba?aya ?akin suka ?ago idanu suna kallonsa.
Ita kuwa a ?ari ta sanya hannun ta dafe ?uncinta, wani irin azaban zafin marin da ta ji ne yasa ta fara ruwan zafafan hawaye ba tare da ta sani ba. Shi kuwa dama haushinta yake ji saboda suna zargin bata da gaskiya Guyson ya ce su rabu da ita kada su sake dangantata da mutanen banza, haushin hanasu bincike da ?aukar mataki a kanta da Guyson ya yi ne gaja suka tsaneta sosai. Haushinta da yake ji yasa ya sake ?aga hannu zai kara dalla mata mari a karo na biyu. Da gudu Sharifat ta ?ariso wajen ta ri?e hannun nasa tare da saka mashi kuka, kafin ta iso wajen ta ri?e hannunsa ma Dr Raj da Rizwan har suna ha?a baki wajen cewa kada ya yarda ya kara mata mari, yanzu ma wannan da ya yi mata bata gama dawowa cikin hanyacinta ba, idan ya kara mata ai sai ta sume.
Abbie ne ya kalli Omaid ?in. "Jeka abinka my son". Ya fa?a. Wucewa ya yi ba tare da ya ?auki wayar tasa da ta fa?i ?asan ba, a cewarsa wlh shi ba zai du?a ya ?auki wayar ba, idan kuma ya ce lallai sai Leesharh ta du?a ta ?auko mashi wayar ba zasu wanye lafiya da brothers ?in nan nasa ba, bare ma yadda ya ji har suna ha?a baki wajen hana shi kara mata mari lallai ya tabbata ba zasu wanye lafiya ba, hakan yasa ransa a ?ace ya fice daga ?akin ya kyale wayar a ?asa tare da fisge hannunsa daga ri?on da Sharifat ta yi mashi......... Ran maza ya ?ac!!.
Sharifat ?in ce ta tsugunna ta ?auka mashi wayarsa tare da ri?o hannun Leesharh ?in tana hawaye ta nufi waje. Bata kai ga fita ba Abbie ya dakatar da ita a in da ya ce ta zo. Ba musu ta juya ta dawo garesa, gefensa ya nuna mata ta zauna, hannu yasa ya kwantar da kanta a saman laps ?insa har lokacin tana ri?e da hannun Leesharh ?in bata saki ba.
Goge mata hawaye Abbie ?in ya fara yi tare da tambayarta me abin kukan to, shi ma Yah Rizwan tamyar da ya gefa mata kenan. Cikin kuka ta ce. "Abbie Yah Rizwan wlh I really like Leesharh, because she's so silent innocent and good girl, and marainiya ce, no dad no mum, bata da kowa sai Allah sai kuma ni, meyasa Omaid zai mareta dan sun bugi juna? Jiya Obaid ya mareta bata yi mashi komai ba, su idan basu son mutun sai su yi ta yi mashi mugunta, to ni ina son Leesharh sosai........". Da kyar ta ?arisa maganar saboda ta tuna cewa Leesharh bata da iyaye.
Shi kansa Abbie sai da ya ji wani irin tausayin maraicinta ya soki zuciyarsa, bayin Allah suna da zuciya mai kyau suna kuma da zuciyar kaunar marayu, nan take suka ji kaunar Leesharh ?in ya kamasu, shi kuma Bilal da hankalinsa baya kan hiran nasu sai bai ji komai ba, gaba?aya hankalinsa kacokam yana kan Ramish.
Ri?o hannun Leesharh ?in Abbie ya yi tare da zaunar da ita a ?ayan gefen nasa, wlh Abu Abdussalam sarkin kaunar yara ne, duk ?a?an King Zuhair da ya tattare suka dawo gidansa bai ishe shi ba, har Auta Zunaira son ?auketa yake yi King yaki yarda, shi fa bai ki ace gidansan nan a cike yake da ?a?ansa ba, sai kuma Allah bai bashi aihuwa dayawa ba, ?a?ansa uku ne kawai a duniya, shiyasa ya kwaso ?a?an King, bai ma ki a ?ara mashi wasu ba.
"Rizwan bani handkerchief a wajen kan nan". Cewar Abbien. A hanzarce ya ciro daga aljihunsa ya mi?a mashi, gogewa Leesharh ?in hawaye ya kar?a ya fara yi yana bata hakuri, nan take ya ji yana kaunar yarinyar, ji ya yi gaskiyar saboda maraicinta shi zai maye mata gurbin mahaifinta, dan gaskiya yana son ?a?a mata sosai, amma Sharifat kawai Allah ya bashi, dan haka yanzu a ransa ji yake bayan Sharifat ya samu Leesharh.
A ?angaren Ummie kuwa haka kawai ta ji wani irin tsanar Leesharh ?in ya kamata, ko me dalilinta Allah ka?ai masani komai da komai na fili da na ?oye. Shi ma Rizwan da yake yana da saukin kai sosai sai ya ji yana kaunar Leesharhn, sai ya ji ta bashi tausayi sosai, ?ar yarinya da ita ta rasa iyayenta, Allah sarki ita da ya kamata a ce yanzu tana tare da iyayenta tana jin ?umin jikinsu, amma saboda babu su gata a in da ma bata sani ba ta zo aikatau, to daga yau gaskiya ta bar yin aikin komai duk da dama ba wani aikin kirki take yi ba, amma daga yau ta zama ?ar gida ita ma, kuma zai ri?eta matsayin kanwa kamar yadda ya ri?i Sharifat, haka yake tunani a cikin ransa.
Shi kuwa Guyson da ya fisu zuciyar tausayi sosai har da hawaye ya yi mata, shi dama already tausayi take bashi, tun da ya ganta an kawota gidansu da sunan aiki tun kafin ma yasan ita marainiya ce yake tausaya mata, dan a cewarsa ?aramar yarinya kamar wannan ta zo aiki ai akwai tausayi.
Shi kuwa Omaid sarki bakar zuciya yana fita waje harabar gidan ya nufa, kai tsaye in da Obaid yake ya nufa, haushin da ya ji a cikin gida zai je ya sauke a kan criminals ?in nan......... Tab ni kam na ce criminals kunga ta kanku.