Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 28
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 28: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 28. Ba karamin mamaki ya ji ba lokacin da ya kalli delisha ta shiga ainahin…
3,351 words
Ba karamin mamaki ya ji ba lokacin da ya kalli delisha ta shiga ainahin babbar parlourn black tiger da babu wanda ya ta?a shiga sai shi Ronnie, bayan shi a gaba?aya masarautar babu wanda ya ya?a shiga cikinta, yau Delisha ta ja Sweetie har ciki.... Tashin sense...........
Meyasa aka kai ta can? Me zasu yi mata?.
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 8/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
E18
DARK WORLD??????
Bayan Delisha Ronnie ya bi, jikinsa duk a mace kamar wanda aka yi wa dukar tsiya, da kyar yake iya jan kafarsa ya nufi sama.
Ba karamin mamaki ya ji ba lokacin da ya kalli Delisha ta shiga ainahin babbar parlourn black tiger da babu wanda ya ta?a shiga sai shi Ronnie, bayan shi a gaba?aya masarautar babu wanda ya ya?a shiga cikinta, yau Delisha ta ja Sweetie har ciki.... Tashin sense...........
Meyasa aka kai ta can? Me zasu yi mata?.
Da yake shi ya saba shiga cikin part ?in, ba bakon bane a part ?in sai ya bi bayanta har zuwa ciki, Delisha ?in ita ce ma bakuwa da bata ta?a shiga part ?in ba sai yau a dalilin Sweetien. Ya yi matu?ar mamaki a kan meyasa yau Black Tiger zai sanya Delisha irin aikin da shi ka?ai yake sakawa ya yi mashi? Meyasa ya yi hakan? Yau da kansa ya bar wata ta shiga part ?insa da ba wanda ya ta?a shiga sai shi Ronnie! Lallai akwai matsala.
Da wannan tambaya da mamakin cike a ransa ya shiga gold parlourn......... Hmmmm al?alamina ya yi ka?an ya iya zayyano maku yadda ha?uwar wannan gold parlourn yake, al?alamina ba zai iya ba, dan karshen ha?uwa ne, abin da zan ce maku kawai a nan shi ne four in one ne parlour, parlours har kala hu?u ne a cikin guda ?aya, dukkansu kuma an ?awatasu a luntsuma luntsumar kujesu wanda aka yi su da gold, kun sansu arziki mafi yawaita a cikin birnin gold ne, dan haka akwai shi wadatatce, kusan komai na Daularsa da gold aka yi ta....... Babban kai kenan.
Ha?uwar parlourn nan ya wuci tunaninku, ga shi gari guda a girma, kofofin shiga sauran ?ananan parlourn guda ukun manya manyan luxurious glasses ne, center table dake tsakiyar kowani sofa set ma kawai abin kallo ne, ha?i?a idan ka shiga wannan parlourn zaka yi zaton ba'a duniyar nan kake ba, babu hasken rana dake shigowa wajen, luxury curtains ?in parlourn masu kauri ne sosai da sosai, gaba?aya parlourn kuwa gauraye yake da white light na flourescent bulbs, shi babban parlourn ma flourescent bulbs ?insa yana da tsayi sosai, duk da ya kasance ginin yana da tsawo sosai, amma flourescent bulb ?in centern parlourn ta sauko dai'dai, and design na flourescent bulb ?in tamkar wasu kyawawan flowers haka aka yi su, sun ha?u har sun gaji da ha?uwa, haske ne da su sosai da sosai ta yadda su ka?ai ne a kunne a parlourn amma sun haske ko'ina duk girman parlourn, gasu golden color sai suka kara fito da gold parlourn. Irin wannan parlour sai dai baki ta yi shiru kawai, wani irin makeken Tvn dake cikin gold parlourn nan idan yana kunne sai kaga mutanen ciki kamar ka kirasu su amsa saboda girma, jiga jigan manyan Ac's kam ba'a magana, Daula iya Daula sai bakin zalinci.
Har tsakiyar gold parlourn Delisha ta jata, sai kuka take yi babu wanda ya saurareta. Dakatawa ta yi a tsakiyar parlourn tana binta da wani irin matsiyacin kallo, ta ji haushi ne da ya zama bata ta?a zuwa wannan part ?in ba sai a dalilin Sweetien yau, bata so ace hakan ta faru ba, ta so ace ta shigo ba ta dalilin kowa ba, isarta yasa ta shigo kawai ba wani ya yi mata alfarma ba, ba dai yadda ta iya ne kawai, sai dai ita kanta tana tunanin meyasa Black Tiger bai sanya Ronnie wannan aiki ba ya sanyata ta je ta ?auko mashi Sweetien? Bayan kuma da Ronnie kawai ya aminta a cikin Empeir ?in, abin dai ya bata mamaki. Haka zalika duk da ta kasance wayayyiya yar boko kuma ?ar cikin empeir ?in, sannan ta saba ganin kayan alatu na more rayuwa very expensive ones, amma da ta shigo cikin gold parlourn nan sai da ta zama cikakkiyar ?ar kauye babu mix, sai satar kallon ko'ina da ina take yi, bare kuma ita Sweetie da take girman forest! Ai kauyanci dole!.
Shi ma Ronnie ya shiga ru?ani da har ya fara zargin kansa ko dan ya mari Sweetien ne yasa yau Black Tiger ya sharesa? Sai a lokacin kuma ya tuna cewa shi ma ya yi kuskure ba iya Sweetie kawai ba, dan kuwa ya san duk abin da suke yi a kan idanun Black Tiger ?in suke yinsa, a tafi hannunsa suke, duk wani motsinsu yana sani kamar wani aljani, dole mutanen birnin su ce shi ?in ba mutun bane, yana ganin komai da ake yi a fa?in birnin, shi kuma a lokacin ransa ne ya yi mummunar ?aci da har ya kasa control ?in tempersa har ya mareta, shi kansa bai san dalilin wannan marin ba, abin ne ya zo mashi unexpect kawai.
Wani irin tsawa Delisha ?in ta daka mata wadda ya sanyata kara ru?ewa, dama can ba ta cikin hayyacinta sosai, tsawa ta daka mata a kan ta gaya mata in da Spender yake ko kuma ta kasheta a nan.
Har?e hannayensa a bakin kofar shiwo gold parlourn ya yi, shi kansa kofar shigowar abin gani ne, na farko kofar bullet proof ce, babu bullet ?in da zata iya fasashi, sannan water proof ce, design of the most expensive door in the world, kai kofar ta ha?u ta gaji da ha?uwa, sannan da gold aka yi ta.
Zubawa Delisha wa?an nan kyawawan idanun nasa ya yi yana kallonta, ji yake yi tamkar ya yi kuka, shi bai ta?a jin tausayin wani abin ba a rayuwarsa kamar yadda Sweetie ta bashi tausayi a yau, idan kaga tashin hankalin da yake kan face ?in yarinyar nan wlh sai zuciyarka ta karaya, a tsananin tsorace take, sai dai kuma babu alamar zata amsa masu tambayar da suke yi mata a tattare da ita, sam bata nuna alamar kamar ta san abin da suke tambaya ?in bama.
Shiru bata yi magana ba sai kerma da jikinta yake yi, hakan ba ?aramin kara fusata Delisha ya yi ba, wani irin mari da ta dallamata ne yasa sai da baiwar Allahn nan ta yi wani ni irin juyawa tare da kifawa ?asa.
Idan ran Ronnie ya yi dubu a kan wannan marin to ran nasa ya ?aci, cikin fusata ya tako ya ?ariso in da suke, daga ganin yadda yake tafiya kai kasan ba rago bane, jarumin gaske ne.
Dai'dai lokacin da ya ?ariso wajen ita kuma Delisha ta ?agota da dogon gashin kanta tana ?o?arin dalla mata wani marin a karo na biyu, ga shi ta damke mata gashi tana ja da karfi. Yana zuwa ya ri?e hannunta ta baya, a fusace ta juyo dan taga wanene? Ai kuwa tana juyowa ya ?auketa da nasa marin mai do?ar da jin bawa.
Wani irin jiri ta gani ya ?ebeta da karfi, ta ji hannun maza, dan fa marin Ronnie ba wasa, wurgi da hannunta da ya ri?e ya yi da nufin ya kama Sweetien dake ?o?arin zubewa ?asa saboda marin da ya ?auke Delisha ?in da shi yasa Delishan ta saki gashin kan Sweetien da ta ri?e ba shiri. Tana sakinta kuma ta tafi zata fa?i ?asa, shi ne ya yi wurgi da hannun nata zai taro Sweetien.
Yana ?o?arin kama Sweetien Delisha da ta dawo dai'dai ta cire hannu zata dallah mashi mari ita ma ko tsoro babu, ta fa san wanene shi sarai, amma take ?o?arin rama marin da ya yi mata dan nemanwa kai rugugin balai. Ai kuwa cap ya capke hannun nata da hannunsa ?aya tare da ?ara dallah mata wani gigitattacen marin mai karfin gaske da ?ayan hannunsa, sannan ya ri?o Sweetie da hannun da ya mareta ?in, cikin ?acin rai ya kwashe kafafunta ta zube ?asa, abin da yasa ya yi mata hakan kuma ba komai bane face renin da take ?o?arin kawowa a tsakaninsu, a iya saninsa yasan cewa ko master Devil ya mara bai isa ya ce zai rama ba bare ita, saboda shi ?in kowa yana girmamasa kamar yadda suke girmama Black Tiger, sanin Black Tiger ?in ya fifita shi sama da kowa a cikin birnin, dan dole ake yi mashi biyayya, da yara da manya wa?an da suka fisa, kai har dattawa suna yi mashi biyayya, dan ya mareta shi ne ita sarkin bala'i zata rama? Tab dan ma ta samu hankalinsa na kan Sweetie ne, ai da ya yi mata one blow seven die.
A fusace ta mi?e tsaye, kansa ta yi da iya karfinta a dole ba zata kyalesa ba, gani take yi yanzu ta kawo karfi ita ma, ji take kamar zata iya dukansa, mutumin da tun yana ?an shekara biyar ya fara koyan Wrestling shi ne wai take tunanin zata iya dukansa.
Ai kuwa sake Sweetien ya yi ya juya kanta kamar wani zaki, kan kace me suka fara gwabza fa?a kamar wasu zakuna. Ronnie yana da karfi sosai, wani irin dam?a ya yi mata a gashin kanta wanda sai da yasa ta yi ihu, da karfi ya ja gashin kan nata tare da ce mata ta ji yadda Sweetien ma ta ji lokacin da ta ja mata nata gashin, ashe ba da?i? Ashe da zafi?, yana yi mata magana yana ?ara fisgar gashin nata da karfin gaske.
Azaban da ta ji ne yasa cikin dabara ta juya tare da damko dogon wuyar nan nasa da karfi ita ma, hakan yasa ya saki gashin kan nata da sauri, yana sakinta ta juyo da kyau tare da shake mashi wuya da karfin gaske. Sweetie kam kara tsorara sosai ta yi, musamman yadda taga suna fa?a cikin rashin tausayin juna, kamar basu ta?a sanin juna ba, duka sosai Ronnie ya yi mata tamkar bai ta?a saninta ba, duk da hakan kuma ta kasa daddara a cewarta ba zata barshi ya sha a banza ba, kenan ya daketa ya daki banza? Ba zai yiwu ba, ga shi sai kara cin jibga take yi.
Da dai yaga dan yana yi mata a hankali ne take ?ara za?ewa, sai ya cire duk wata sanaiya ya kama hannunta dake wuyarsa ya ?an?arota, da karfi ya mur?e hannun nata ta baya, ji kake ?ad ya ?alle mata ?ashin hannu. Bai barta ta yi ihun hannun ba ya jajumota sama cikin fusata zai yi wurgi da ita saman glass table dake kusa da su.
Ihun da Sweetie ta kurma tare da rufe idanu ne yasa ya farga da kisan kai da yake son yi, dan kuwa in dai ya yi wurgi da ita a wajen sai dai wata ba ita ba, ba zata yi saura ba, dan babu abin da zai hana ?ashin bayanta ballewa sai dai wani ikon Allahn. Jin ihun Sweetien yasa ya wurgata saman sofa tare da matsowa ya ri?o hannun Sweetien wanda ta ?aura a saman face ?inta ta rufe idanunta da shi dan kada taga yadda zai yi kisan kai.
Yana ri?e hannunta ya mi?ar da ita tsaye kenan kwatsam sai ji ya yi Delisha ?in ta buka mashi wani abin saka flowers a ciki, wadda ya kasance shi ma da gold aka yi shi, haka ta daddage ta ?aga shi da hannunta ?aya ta buga mashi a bayan ?eyansa, tana buga mashi kuma ta fara layi kamar zata fa?i ?asa, ga bakin azaba da hannunta da ya karya mata yake yi mata.
Ai kuwa sakin hannun Sweetien ya yi tare da juyowa ya capki wuyarta, da karfi ya sha?eta, ga kansa in da ta buga mashi abin zafi yake yi mashi over, kamar yadda yake jin ra?a?in wajen haka yake ?ara shake mata wuya da karfin gaske, nan take idanunta suka firfito waje ta fara ?o?arin fa?a tsakanin rai da mutuwa, ?o?arin shakar numfashi take yi, amma ina ta kasa, dan ba ri?on wasa ya yi mata ba. Ta kasa iya kwatar kanta.
Sai da ya tabbatar ta dai'na numfashi, sannan ne ya hanka?ata da karfi da kuma hannun ?aya, gaba?aya ta tafi ta kifa a ?asa kamar gawa, ko motsi bata yi kamar ta mutu.
?aga idanunsa ya yi yana kallon ?an siririn gold stair case dake cikin gold parlourn kusa da dining room, stairs case ne mai design of indomie ?an siriri na wucewar mutun ?aya, na haurawa ne sama in da ainahin room ?in Black Tiger yake. Ajiyar zuciya ya sauke, dan yasan duk abin da suke yi tsab Black Tiger yana kallonsu, yasan komai, kawai dai bai tanka masu bane, ya barsu suka gwabza abinsu.
Stair case ?in ya nufa kai tsaye, babu ko tsoro bare shakka, haka ya bar Sweetie a wajen tana zaune ta rasa madafa, ga dukkan alamu ya saba haurawa wajen.
A can wajen wasa kuwa, sai ra?ashewa suke yi, an saki sauti sai rawa suke yi, master Devil ma fa ashe ya iya taka rawa over, Floris ma rawa ta taka sosai kamar babu ?ashi a jikinta yarinyar nan, suna chashewa son ransu, sharholiya iya sharholiya, dama haka suke yi duk idan aka gudanar da gasa.
Makudan kyauta masu tsada Black Tiger ya aikowa Oxil da shi kamar yadda yake a dokar gasar, ba'a karya doka sam sam, ko ma waye ya ci ko ya fa?i a gasar doka zata hau kansa.
Almost 1 hour Ronnie ya ?auka a saman kafin ya sau?o, yadda ya shiga ba'a haka ya sau?o ba, daga ganin yadda face ?insa take a yanzu zaka san yana cikin tashin hankali da damuwa, idanunsa sun yi jajir sosai, alamar ran maza ya ?aci. Ga dukkan alamu ya yi katari da abin da bata yi mashi da?i ba a saman!!.
Kai tsaye waje ya nufa bai sake bin ta kan Sweetien ba, yadda yake tafiya cikin jarumta zaka fahimci lallai ransa a ?ace, ya fusata sosai.
Da kallo Sweetien ta bishi har ya kurewa ganinta. Zama ta yi a ?asa a wajen gwanin ban tausayi, kallon Delisha dake baje a ?asa kamar gawa ta yi kafin ta mayar da kanta ta kifa a saman gwiwowinta, shiru ta yi tana tunanin yadda za'ayi ta gudu ta bar wannan Daula. A hankali voice ?in mummynta ya fara ratsa kunnuwanta, tana tunano zantukan da suka yi kafin mum ?in ta ?ace masu.
"Sweetie duk wuya duk da?i kada ki yarda ki bawa wani mahaluki wannan abin, ki kasance mai dauriya a duk halin da zaki shiga, in dai kika bada wannan abin to tamkar ki sadaukar da ran mahaifinki ne, ni nasan ba zan ta?a kai labari ba, shiyasa na za?i na baku shi ?in, dan ba kowa zai yi zaton abin yana hannunku ba, ki kula da Pretty sosai, magana ta karshe a nan shi ne ki sani wannan abin yana da matu?ar ha?ari sosai, manya manyan sarakuna na sama da masarautu biyar ne suke neman wannan abin idanu a rufe, zasu iya aikata komai dan su same shi, nasan rayuwarku zata iya shiga ha?ari a dalilin wannan abin, amma bani da wani za?in da ya wuce in damka maku shi kamar yadda mahaifinku ya bani shi amana, ki sani wannan makulli ne na rayuwa ko mutuwa na mahaifinku".
Ajiyar zuciya ta sauke tare da sake waigawa ta fara tunanin yadda suka yi da Pretty a kan Spender ?in bayan ?atar mum ?insu.
"Pretty kin san yadda zamu yi da wannan abin da mummy ta bamu ?in?".
Pretty dake zaune saman gado ta buga uban tagumi ta amsa mata da a'a bata sani ba. "To ni dai wannan abin ni zan baki ki ri?esa, saboda ke kina da ido ni bani da shi, dan haka ke zaki fi kula da shi, sannan ki kula sosai kin dai ji abin da mum ta ce a kansa ko?".
Kai ta gya?a mata tare da amsa mata da e. Hakan yasa Sweetien ta cire abin ta bawa Prettyn a kan ta ajiye shi, dan haka yanzu Spender dai yana hannun Pretty ba hannun Sweetien ba, in dai har Sweetie tana son rayuwarta kuma tana son barin wannan Daula to dole sai Pretty ta zo, dan ita ke rike da Spender, ita tasan in da ta ajiye shi..... Tashin hankali gaskiya Sweetie tana tsaka mai wuya, yanzu ma shin ina Prettyn take? Sannan a ina ta ajiye Spender ?in? Lallai ya tabbata ita ma Pretty tana da shegen wayau, duk yadda suke da Kamran bata ta?a gaya mashi ba ko da sunan wasa, amma ni tambayata a nan shi ne, ta ya aka yi Black Tiger yasan mum ?insu Sweetie ta bawa Spender ba Pretty ba? Dan kunga dai kai tsaye Sweetien suka nufa, and shin sun san su twin's masu kama ?aya ne ma ko dai basu sani ba kawai sun kama Sweetien ne? Wa ma ya gaya masu Spender na hannunsu? Anya basu kama mum ?insu ba kuwa? To idan ba ita ba ai babu wanda yasan ta bawa Sweetie abin, ko ita mum ?in kuma bata san da cewa Sweetien ta baiwa Pretty abin ba, ita dai tasan Sweetie ta bawa ba Pretty ba, akwai cakwakiya babba kuwa, ta ina za'a nemo Pretty ta zo ta ku?utar da ?ar uwarta daga RAWANIN ZALINCI? Dan kuwa sai ta zo kam, saboda ko ita Sweetien bata san a ina Prettyn ta ?oye shi ba..... Wannan shi ne babbar magana!!!.
Tunanika kala kala take ta faman yi a ranta, kamar ance ta ?aga kanta sama ta ?aga. Tana ?agawa ta kalli flourescent bulb da take a zaune saitinsa yana ?o?arin fa?o mata a kanta, sai wani jijjiga yake yi da karfi kamar zai ?allo.
Ihu ta kurma tare da fara ?o?arin tashi ta bar wajen dan kada ya fa?o mata a kanta, sai dai ta kasa iya motsawa daga wajen, ihu ta rin?a yi tare da datse idanunta gam ta kuma takure jikinta waje guda, sai ?o?arin mi?ewa take yi amma ta kasa.
Ganganrowa ?asa flourescent ?in ya yi har gabanta, ihu ta rin?a kurmawa, kuma ihun nata baya fita, ga dai ?an bakinta ta wagesa tana kurmawa, sai dai ba wani sautin da yake fita daga cikin bakin nata, abin da ?aure kai sosai........ Ni ma dai ya ?aure mun kai sosai gaskiya.
Nan take ta ji kamar ana juyata, a ?ari ta bu?e idanunta, me zata gani? Sai ganin parlourn ta yi yana wani irin jujjuyawa kamar fanka, komai na cikin parlourn juyawa yake yi, gaba?aya light na cikin wajen bulbs sun fi gida 30 suka fara kawo light suna mutuwa lokaci guda, bulbs dake cikin gold parlourn sun kai guda 20 sai kawowa suke yi suna ?aukewa suma, lokaci guda suke ?aukewa su sake kawowa kamar ba lafiya ba, idan suka ?auke kuma wani irin duhu mai ban tsoro ne yake sake bayyana a gaba?aya gold parlourn, sai ta rin?a ganin wasu irin halittu da bata ta?a ganin irinsu ba a cikin duhun kafin hasken ya sake dawowa, idan haske ya dawo kuma sai ta ga komai normal babu wa?an nan halittu.
Kanta ne ya fara juya mata ta fara fita daga cikin hayyacinta saboda bala'in tashin hankali, jikinta sai kerma yake yi. Da alama sun lura Sweetien fa bata da niyar basu Spender ne yasa suka fara azabtar da ita da tashin hankali kala kala ha?e da yi mata gizo, a tunaninsu idan ta sha azaba dole ma zata gaya masu in da yake,.........Babbar magana!!.
Tun tana iya gane in da take, tun tana iya ganin hasken light dake ?aukewa yana sake dawowa har ta dai'na gani, idanunta suka rufe ruf ta sulale ?asa ta kwanta a wajen.