Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 30

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 30

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 30: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 30. Luxury bed room ne fiye da tunaninku a cikin wannan parlourn, tun daga kan…

3,283 words

Luxury bed room ne fiye da tunaninku a cikin wannan parlourn, tun daga kan gado zuwa labulaye har zuwa kan chandelier izuwa kan tiles ?in ?akin, glass na dressing room and bath pan na toilet, komai da komai white and milk colour ne, komai na cikin room ?in nan the most effective thing ne, tamkar ba za'a mutu ba, komai ya ji a room ?in, su kansu furnitures da aka zuba a part ?in zaka san e lallai wannan part na musamman ?in na musamman ne, furnitures ne da a wannan part ?in kawai zaka iya samun irinsu, dan gaba?aya furnitures ?in ha?e suke da computers ha?e da na'urori, ko drawers na room ?in baka isa ka bu?esu ba sai da izinin mai shi, da alama koma waye mai wannan part ?in mutun ne da ake kauna over, dan tun daga kan matakan tsaron da suke kewaye da wannan part ?in zaka fahimci e lallai ba ?aramin kai bane a wajen, ku dubi yadda gidan yake da uban tsaro amma a haka aka gargame wannan part ?in da uban tsaro har haka. Alkalamina bai isa ya zayyana maku ha?uwar part ?in nan ba, kawai dai abin da zan ce maku shi ne wannan part ?in karshe ne wajen ha?uwa.

Wani irin fitinannen kamshi mai kwantar da hankalin mai sha?a ne yake tashi a gaba?aya arear part ?in, kana dosowa wajen zaka ji hankalinka ya kwanta a lokacin da ka sha?i kamshi, shi yake fara yiwa kowani kofar hanci bawa welcome a duk lokacin da ka doso, kana saka kafarka a ciki kuma wani irin sanyin Ac mai ha?e da kamshin ne zai yi maka welcome. Komai na cikin part ?in tsabar tsabta tamkar yanzu aka bu?esu a leda, kar kar suke!!.

Kwance yake a saman wani irin ha?a??en King bed mai bala'in kyau da tsada, shin fi?e yake da zannuwar gado masu bala'in kyau, laushi da kuma tsada, ya lume cikin bargo ya kuma rufe gaba?aya jikinsa gar zuwa wuyarsa da ha?a??en bargonsa mai bala'in laushi, jikin bargon tamkar jikin mage, idanunsa a rufe da eyes care mai shegen kyau, gashin kansa ta sauko mashi har gaban goshinsa, baka iya ganin face ?insa, saboda gaba?aya room ?in duhu ne, ko light ?in wajen drawers ba'a kunne suke ba bare a je kan sauran bulbs ?in.

Sai dai akwai light mai bada haske ?an ka?an a jikin na'urar dake jikin bed side drawers ?in dake kamar waya.

Wani mutun ne ya shigo cikin room ?in, kai tsaye wajen drawer ya nufa, kasancewar room ?in babu haske sosai sai yasa ba'a iya ganin wanenen ya shigo. Remote ya ?auko a cikin drawers ?in bayan ya sanya fingerprint ?insa, a saman drawers ?in ta side guda akwai wani wajen da yake tamkar waya da glass a jikinsa, akwai password sannan akwai fingerprint a jiki duka, haka dukka furnitures na part ?in suke, shiyasa nace maku idan bada izinin mai part ?in ba ko tsinke ba mai iya ta?awa a ciki!.

Kunna wutar ?akin ya yi da wannan remote da ya ?auko, iya wutar chandelier dake tsakiyar room ?in ya kunna, nan take wani irin haske ya gauraye cikin room ?in gaba?aya, a haka ma bai kunna wutar ?akin gaba?aya ba, iya chandelier kawai ya kunna.

Hasken da gauraye room ?in ne yasa wanda yake kwance a saman wannan King bed ?in ya ?an matse idanunsa alamar baya son hasken......... Wow duk da bai bu?e idanunsa ba ni dai nasan ban ta?a ganin kyakkyawan guy irinsa ba, ban san ma ya zan gaya maku ha?uwar guy ?in nan ba........

(Saura na ji kun ce na juyawa Romeo baya?? yo na ga kyau iya kyau, ni fa ina son kyau sosai. ?? Domin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana matu?ar kaunar kyau, yana matu?ar son kyau da kuma kamshi, kunga a matsayinmu na masu koyi da shi ai dole mu so kyau mu kuma so kamshi???? sai dai fa babu mummuna a halittar Allah, komai na Ubangiji mai kyau ne sosai, duk wanda ya ga cewa yana kallo wani mummuma a cikin halittar Allah to maza ya yi saurin korar shai?anin dake kusa da shi, dan shai?an ne yake son zugasa ya kaisa ga halaka, dan babu mummuna a halittar Allah, komai na Ubangijinmu mai kyau and tsabta ne sosai.)

My people's guy ?in nan ya ha?u ma?urar ha?uwa, skin ?insa yadda kuka san Korean guy, tamkar madara, a kwance luf, ya ji hutu har ya gaji, hancin nan nasa masha Allah kawai zan iya cewa, wayyo ?an bakinsa ?an ?arami da shi, lips ?insa na ?asa yana da ?an kauri ka?an, na sama kuma ?an pelem pelem design of heard, yawancin maza zaka ga lips ?insu yakasance red color, amma shi wannan guy ?in nasa pink color ne kamar na mata, kun san mata aka fi sani da pink lips, to shi nasa gaskiya pick ne mai matu?ar ?aukar hankali sosai, yadda gashin kansa yake kwance mashi a gaban goshinsa ba'a magana, bakin kirin da shi yana wani shaki, ba ?aramin kyau ta ?ara mashi ba, face ?insa ta fita ras, kumatunsa ?ul ?ul dai'dai da su, tamkar bai ta?a fita waje ba, hasken fatarsa yana da matu?ar ?aukar hankali, gashin gerarsa tana nan yadda kuka san zana mashi ita aka yi, tana kwance luf sosai, garasan wajen sajensa basu da yawa sosai, ?an dai'dai suke a kwance luf, kai guy ?in nan fa kyansa ya zarce tunaninku, ga wasu zara zaran eyelashes kamar wanda ya sanya na kanti. Kyakkyawar lallausan wuyarsa tana da tsawo ?an dai'dai, gata a cike da tsoka, sai wani ?an jijiyo da suka ?arawa wuyar kyau, sun mashi kamar kwalliya.

?an tsuke fuska ya yi sosai kafin ya fara motsawa a hankali, da alama baya son haske a lokacin barcinsa.

Idanunsa a rufe ruf ya ?an motsa lips ?insa ka?an, nan take wasu ha?a??un dimples masu matu?ar ?aukar hankali suka lotsa a kumatunsa gefe dukka biyun, saura ka?an na sume saboda wani irin kyan da fuskarsa ta ?ara yi. A hankali kamar baya son motsa bakinsa ya furta. "Why dad?". Ha?i?a da?in muryarsa zai iya sanya mutun ya yi shekara yana sauraron maganarsa, in dai ba zai gaji da yin magana ba to ha?i?a jama'a ba zasu gaji da sauraransa ba saboda tsananin da?i da kuma laushin muryarsa, gata a sanyaye. Sai dai a kaifafe voice ?in take, lion voice ke garesa, harshensa da kaifi sosai.

Wani irin cool murmushi daddyn nasa ya saki, shi kansa dad ?in abin kallo ne, hada??e ne sosai duk da tsufa ta fara bayyana a tattare da shi, jajir yake tamkar ka ta?a jini ya fita, fatarsa luwai luwai. "Wake up, now is our time".

"Dad". "Son". "Dad". "Son" "Dad". "Son". Idan ya ce dad sai dad ?in ya ce son, abin nasu gwanin ban dariya. Ganin daddyn nasa ba zai amsa masa bane sai dai ya ce mashi son sai ya fara ?o?arin waro idanunsa dan ya ga daddyn su fuskanci juna.

Tamkar baya son bu?e idanun nasa haka ya warosu waje, da alama barci bai ishesa ba............. Subhanallah!! Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu, shin kunga irin wannan ha?uwa kuwa my people's? Idanun guy ?in nan wani irin idanu ne kaifafa masu cike da gwarjini, tamkar eagle eyes, ga wani shining da suke yi, farin cikin idanun nasa bai yi fari tas ba, ya yi milk milk haka, kwayar idanun nasa kuma hazel ne masu matu?ar kyau da ?aukar hankali, idanun nasa kaifafa ne sosai da sosai, ba kowa zai iya juriyar ganinsa ido cikin ido ba, da wuya a samu mai kure mashi kallo cikin idanun su ga juna kenan, ga idanun nasa dara dara, kila idan baya kallon mutun mutumin yakan iya kallon cikin idanun nasa, amma su kalli juna ido cikin ido abu ne mawuyaci gaskiya, saboda kaifin idanun da kuma gwarjininsa.

Yana bu?e idanun nasa sai kan daddyn nasa dake zuba mashi murmushi mai kwantar da hankali. "Dad why are you always d........." Hannu dad ?in ya ?aura mashi a saman bakinsa tare da cewa. "Your mum is waiting for you, zata fita office ne".

Wani irin kallon kauna ya wurgawa daddyn nasa kafin ya ?an kawar da kallonsa yana ?aure tiger face ?insa, dama fuskar a ?aure, sai ya ?ara ?aureta.

Hannu daddyn ya mi?a mashi. Ya gane nufinsa ya kama hannun nasa ya mi?e kenan. "Daddy now ba zaka iya ba". Ya fa?a yana ?o?arin yin ?asa da bargon jikinsa alamar zai mi?e...... Kada ku mance da English suke magana.

Hannun nasa dad ya sanya ya kama kumatunsa tare da cewa. "Before na zama president am a general of SSS".

Shiru ya yi bai sake yin magana ba, dan yasan magana kawai daddy yake nema da shi, wai general na SSS! Shi da tun da ya taso siyasa yake bugawa amma wai general ko a ina ya zama general ?in? Idan dad da mum basu ja shi da magana ba a gidan sam basu jin da?i, ga shi shi kuma magana wahala take yi mashi!.

Mi?ewa zaune ya yi..... Ya subhanallah! Iya single da short farare ne kawai a jikinsa, yana da kyan jiki kamar madara, sai dai yana da zanen tattoo a hannunsa ta sama sai kuma a bayansa in da a bayan nasa ya yi zanen eagle mai ?an girma, ya yi wannan zanen ne kuma saboda da sunan da wasu da dama suke kiransa kenan wato mikiya, shi ?in tamkar mikiya yake, dan kuwa idan ya doso waje sai ?ananun tsuntsaye sun gudu, tamkar zaki a fa?in dokar dawa yake, shiyasa ya yi zanenta a bayansa, a damatsan hannunsa kuma zanen Tiger ya yi, tattoo ya fito sosai, saboda hasken fatarsa da ta ha?u da bakin zane ai kunga dole ta fito ta yi kyau sosai.

Cikakken namiji ne da a shekaru zai iya kai 30 haka, very very smart guy ne na gasken gaske, idan ka gansa ko kai makiyinsa ne sai ka yarda ya ci sunansa na smart gentle guy. Kwakwalwa garesa sosai, yana da baiwa matu?a, ?asashe da dama sun so ?aukarsa aiki amma daddynsa yaki yarda, yana da ?wa?walwar matu?a, idan ya yi wani abin in ba ka yarda Allah ba yadda baya yin mutun ba ba zaka yarda da shi ya yi ba, sai mai imani da Allah yake iya yarda da baiwar guy ?in nan, sai kana da imani ka yarda Allah na iya yi wa duk wanda ya so baiwa na musamman a lokacin da yake so ne zaka iya yarda cewa ?an adam ne ya yi wannan abin da guy ?in yake yi kuma da ?wa?walwarsa yake yinta,

wane computer idan ya yi wani abin, scientist wato ilimin kimiya ne da shi ?in matu?a.

Ga bala'in ilimin ha?a makamai da yake da shi, wannan dalilin yasa America, England, Russia, south Korea, China duk suke bala'in son ?aukarsa aiki, amma daddynsa yaki. Sai dai kuma fa shi da daddyn nan nasa da kuke ganinsu ku gansu ne kawai ku barsu a yadda suke, abin ba'a magana, sun munafurci sauran kasashen duniya da suke ?awance da su irinsu England da sauransu, sun munafurci ?asan a in da suke ha?a muggayen makamai a ?oye dan kariya ga ?asarsu, a matsayin dad ?insa na president sai ya yi amfani da wannan dama suke mallakar manya manyan makaman ?are dangi, duk ?asar da ta yadda ta takalosu da yaki, to wlh sunan wannan ?asa shafaffiya a doron duniya, domin kuwa sai Allah ne ka?ai yasan iya adadin mugayen makaman da guy ?in nan ya jagoranci yaransa suka ha?awa ?asarsa, wajen da suke ha?a makaman waje ne na sirrri da yake under grawn, daddynsa ya ?addamar masa da wannan wajen dan kawai su rin?a ha?a mugayen makamai, kai guy ?in akwai basira fiye da tunaninku, irin makaman da yake jagoranta su ha?a sam sam babu wata ?asa da ta mallaki irinsu, manya manya ne sosai, mugayen makamai ne fiye da tunajinku, ga wasu makaman masu karfi da ya ha?awa kasarsa wadda ake kira da defense system, makami ne mai iya tare makamai masu linzami komai karfinsu, ga shi da shegen sani dan gane da computer kamar wani aljani, Allah ya bashi in dai ?wa?walwa ne. Yana da kishin ?asa sosai da sosai.

Sai dai wannan batu na makaman iya shi da daddynsa ne kawai suka sani, sai kuma yaran team nasa da suke su hu?u, mum ?insa bata san da hakan ba, da ta sani ba zata ta?a yarda ba, dan tasan yaronta zai zama abin farautar manya shugabannin manya kasashen duniya, tasan kowa zai farauci ransa ne, dan ku dai kunsan manyan ?asashen nan basu son ace kowacce ?asa ta fisu, suna son su zama su ne a kan gaba da kowa, shiyasa zasu nuna suna tare da ku suna sonku dan su le?i asirinku su rin?a ganin me ake ciki, amma da yake daddyn nasa shi ma ba baya ba wajen kaifin ?wa?walwa ga iya siyasa, sai ya zamana yana yarda ya yi abota da kowace ?asa a baki, amma a ?ar?ashin ?asa munafurtarsu yake yi, baya ta?a yarda kowa yasan halin da yake ciki, ya iya siyasarsa ne fiye da tunaninku, yasan takunsa, akwai shi da shegen wayo sosai.

Mum dai sun barta a duhu bata san komai ba, kuma saboda sun san zata hana ?an nata ne yasa basu bari ta sani ba, in takaice maku dai daddyn nasa ne ya ?ata shi kuma ya mayar da shi haka, saboda ha?a wa?an nan makamai ?in ya zana wannan tattoon a jikinsa, sannan saboda ha?a wannan makaman ya yi abubuwa da dama kuma ya koyi abubuwa da dama, lokuta da dama yana cikin chemical kala kala na ha?a booma boomai da su roket, ga uban tarin computers a gabansa kamar ba gobe, hakan yasa yake da shegiyar zafin rai kamar zaki, ga shegen saurin fusata kamar me.

Zuro kyawawan fararen ?afafunsa ?asan bed ?in ya yi, mi?ewa ya yi ya nufi toilet ba tare da ya sake yiwa dad ?in nasa magana ba. Yana mi?ewa wani dogo da shi ga cikar halitta ta jaruman maza, yana da Lion chest faffa?a sosai.

Da kallo kauna daddyn nasa ya bisa har ya shige cikin toilet ?in, suna kaunar juna shi da dad ?in nan nasa over, sannan haka suke rayuwa kamar abokai, idan ka gansu zaka rantse abokai ne, shi ka?ai ne ?ansu a duniya, sai ?ar kanwar mum ?insu da suka ?auko suka ri?e, da alama suna son ?a?a Allah ne bai basu ba, suna bala'in kaunarsa fiye da tunaninku, yadda kuka san zasu yi mashi numfashi saboda kauna.

Izuwa yanzu my people's nasan kun fahimci dalilan da yasa matakan tsaro suka yawaita a part ?insa sosai ko? Idan ma baku fahimtar bari na yi maku bayani, abin da yasa duk da yawan matakan tsaron da suke tun daga farkon unguwar har izuwa cikin gidansu, ta ko'ina tsaro ne amma duk da haka sai da aka kara jibge mashi tsaro ta ko'ina sosai, to ba komai bane yasa hakan face haukar bu?atarsa da manyan ?asashen duniya suke yi, kowacce ?asa tana son ?aukarsa saboda kaifin ?wa?walwarsa ba ?aramin cigaba zai kawo masu ba, America ta yi ta yi ta ?aukesa amma ta rasa damar samun hakan, duk yadda England take ?awance da France ?in amma dad ?insa yaki yarda su raba shi da ?ansa ?aya tilo, kuma bama dan shi ka?ai suka haifa bane yasa yaki yarda ya basu shi, kawai saboda shi ma kunga abin da yake yi shi da ?an nasa, shi ma gina ?asarsa yake son yi ya fi kowa, wayo ne da shi shima kamar me, kuma mum ?insa ma ba zata ta?a yarda ba, ta ce komai zai faru tana kusa da ?anta.

Coz yanzu dai haukar rububinsa da ?asashen duniya suke yi ne yasa daddyn nasa yake matu?ar kula da shi sosai, tsaro ta ko'ina tana tare da shi, dan kuwa shi dad ?in nasa yasan su waye ne ?asashen da suke neman nasa, suna nan suna shirya duk ta yadda zasu yi su ?aukesa su sanya shi dole ya koyar da mutanensu ha?a abubuwan da ya iya, kuma matsalar a nan shi ne misali ko da ya koya masu ?in da wuya su barshi ya rayu, dan basu son cigaban kowace ?asa sai ?asarsu kawai, idan sun barshi ya rayu bayan ya koyar da su ma sun san zai yi wa ?asarsu makaman da ya fi nasu ne dan ai ?wa?walwar tasa ce ba tasu ba, dan haka fasa ?wa?walwar tasa zasu yi da bindiga, hasada ziryan, sai dai fa sun makaro, dan shi ?in zaki ne na gasken gaske, basu isa su kama shi kuma su tursasa shi yin abin da bai yi niya ba, ba zai yiwu ba, guru ne shi ma sosai, kamar yadda yake ha?a makaman boom masu tafasa haka jininsa yake a tafashe, sannan kuma shi mutun ne da baya yafiya, in dai ka yi mashi laifi to tabbas sai ya hukuntaka, baya yafiya, amma kuma baya kula kowa bare ya shiga harkar mutun, sai in kai ka ta?osa. ?ar autar sarkin England ake son a aura mashi, manyan ?asashe da dama suna son aura mashi ?a?ansu mata duk dan saboda baiwar ?wa?walwar da Allah ya yi mashi da kuma jarumtarsa, in yasa kai a abu fa sai ya aikatasa komai wahalarsa, duk yarinyar da mahaifinta ya yi wa dad ?insa magana a kanta sai dad ?in ya ce baya so, shi guy ?in ma bai san da wannan zance ba, dan basu isa su tunkaresa da maganar ba, daddynsa suke yi wa maganar, shi ma dad ?in a siyasance suke yi mashi maganar ba wai zahiriya ba, kowa dai farautarsa yake yi shi kuma basu isheshi kallo ba.

Ha?i?a idan mace zata so guy ?in nan sai dai dan baiwarsa, ku?insa, mu?amin gidansu, ko kuma kyan da Allah ya yi masa, yana da ?inbin dukiya fiye da tunaninku, dan ba ha?a makamai bane kawai aikinsa, ha?a makamai aikin daddynsa ne wannan, kuma shi baya ta?ama da matsayin dad ?insa na president, sannan baya ta?ama da ku?in dad ?insa, yama fi dad ?in ku?i. Mum ?insa prime Minister ce fa, sannan ?a ce ga tsohon shugaban ?asa da ya sau?a kafin dad ?insa ya hau, in short ma mahaifin mum ?in nasa shi ya tsayar da dad ?insa takara ma, kunga kuwa dan dai dukiya basa magana ne da sun ce sun yi uban yawa a gidan nan a kaisu gaba.

Zama daddyn nasa ya yi yana jiransa har ya yi wanka ya fito ?aure da towel launin milk color a west ?insa, ya subhanallah my people's guy ?in nan ya ha?u iya ha?uwa, ga tsawo da cikar halitta.

Ganin dad ?insa a room ?in bai fita bane yasa ya nufi dressing room ?insa. Da sauri dad ?in ya mi?e ya ?arisa wajensa, yana ?o?arin sanya yatsarsa a jikin glass door na dressing room ?in dan ya bu?eta ya shiga ne dad ?in ya ri?o hannun nasa, kusan tsawonsu ?aya da dad ?in, sai dai ya ?an fi dad ?in nasa ka?an.

Jan hannunsa ya yi suka isa wajen gaban luxury mirror ?in nasa. Zaunar da shi a saman wata ha?a??iyar chair ya yi kafin ya fara kwaso lotion masu tsada yana bubbu?esu, tsab ya shafa mashi kamar wani ?aramin yaro.

Shiru bai yi wa dad ?in magana ba har ya kammala. "Let's go in let me dreass you well".

Wani irin kallo da ya wurgawa daddyn ba tare da ya yi magana bane yasa dad ?in cewa. "My smart sarkin fa?a, go and do it by yourself".

Bai ce ko uppan ba dai ya wuce ya nufi room ?in, shi kuma dad waje ya nufa, da alama office zai je, dan shirin suit masu bala'in tsada ce a jikinsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull