Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 31

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 31

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 31: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 31. Kai tsaye dining room dad ya koma. Zaune ya isko wata kyakkyawar farar mace…

3,331 words

Kai tsaye dining room dad ya koma. Zaune ya isko wata kyakkyawar farar mace mai gashi har karshen gadon baya, tana sanye cikin wani ha?a??en wandon jeans blue mai bala'in tsadar gaske, ta ciki kuma farar long sleeve t-shirt ce a jikinta, sai ta ?aura wani ha?a??en long coat launin blue kalar wandonta a sama, ta sanya kular malafa fara kal kalar t-shirt ?in cikin a kanta, kyakkyawar gaske ce sosai, sannan daga ganinta ?ar wanka ce ta musamman, dan tundaga sama har ?asa kayan ?an gayu ne a jikinta, matar ta ha?u sosai, takalamar kafarta kawai ya ishi mutun jari.

?an rungumarta dad ya yi tare da manna mata sumbata a kumatu kafin ya wuce ya zauna saman chairs kusa da ita, bodyguards manya manyan guda shidda ne suke wajen table ?in dan serving mutane abinci.

Wata ?ar siririryar matashiyar budurwa ce ta shigo cikin room ?in, sanye take da wani ?an iskan crazy jeans dogo har ?asa da kuma t-shirt ?an figalalle.

Ta saki gashin nan har gadon baya, gashin nata launin dark brown ne mai kyau, kyakkyawa ce sosai ita ma, kamarta ?aya da mum ?in smart eagle, ko ku ce mashi smart Tiger. Kamanninsu ?aya da mum ?in. Shi kuwa smart Tiger ya fi kama da daddynsa, sai dai basa wani kama sosai can can, amma akwai kamar jini, da gani ba tambaya zaka san daddynsa ne.

Tana da zanen tattoo na kunama a saman wuyarta ta gefen hagu, sannan tana da wani zanen a kafa?arta na flowers, zanen ya fito sosai saboda hasken fatarta. Siririn wuyarta sanye yake da wani diamond chain mai ?auke da tambarin cross a gaba, hakan yana nuna cewa ba musulma bace ba.

"Mum I want to go to office". Cewar matashinyar yarinyar, a shekaru zata iya kai 23 to 25 haka. Da yake su jikinsu baya nuna girma sai ka rantse shekarunta 17 to 18 haka.

"You didn't eat your breakfast Heleena". Cewar mum ?in, tana da sanyin murya sosai, mutuniyar kirkice sosai mum ?in nan.

Girgiza kai ta yi tare da cewa. "Am okey mum". Muryarta akwai tsiwa a ciki sosai, da alama mafa?aciya ce sosai.

"No I don't agree! Come and have your breakfast before you go out". Cewar daddy.

"No dad I can't eat anything now, am late". Tana magana tana kallon ?an siririn diamond watch dake manne a hannunta, ga wani ha?a??en diamond earrings ?anana a kunnenta.

"No, sit down and have your breakfast". Cewar daddyn, ya yi maganar tare da juyar da kallonsa a kan bodyguards dake tsaye. Umarni ya yi masu a kan su zuba mata abincin nata.

?o?arin tirjewa take yi a kan ita ba zata ci abinci a gida ba dan ta yi latti, ta bu?e baki zata yi mashi tirjiya kenan ta ja burki babu shiri sakamakon kamshin perfume ?insa da ya daki kofofin hancinsu. Gaba?ayansu harta bodyguards ?in kai kallonsu a kan kofar shigowa cikin room ?in suka yi. Nan take bodyguards ?in suka kara nutsuwa tun bai ?ariso ba, ita kuwa wannan figaggiyar masifaffiyar yarinyar a hanzarce ta haye saman chair ta zauna tare da ?ara nutsuwa, da ta tsaya zata yi wa dad musu saboda ba shi ya haifeta ba, na gaya maku ?a ce ga kanwar mum, shi ne ta tsaya zata gwada mashi bai isa ya sanyata yin abin da bata yi niya ba, ko da yake su turawan nan dama can ko iyayensu da suka haifesu ba jin maganarsu suke yi ba, saboda su suna ganin da zarar sun kawo karfi shikenan sun sami ?anci, iyayensu basu isa da su ba, amma dai ba'a rasa masu natsuwa kamar yadda a ko ina akwai na gari kuma akwai na banza, sai dai su gaskiya gwammatinsu ne ma ta bawa kowa ?anci, iyayensu kuma suka kara lallatasu, dan tun farko iyayen ne ke biye masu suna yin abin da suka ga dama har su zo su fi karfin iyayen ya zama sune suke komawa kamar su ne iyayen........ Na kara jin sanyi a rai da Allah yasa ni musulmace da na san darajar duk wani babban mutun ba ma iyayena kawai ba!!.

A hankali yake takowa tamkar baya son taka ?asa. Yana isowa wajen kofar ta bu?e mashi kanta, dan da na'ura take amfani, da zarar ka dosota zata bu?e kanta, kofofin gidan dukka suna da tsaro sosai, kun dai san yadda gidan his excellency mr President yake ba sai na tsaya ?ata bakina wajen yin dogon bayani ba.

Yana shigowa ?aya daga cikin bodyguards ?in dake wajen ne ya janyo mashi chair baya ya zauna. Shirye yake cikin wandon jeans white color, rigar jikinsa round neck t-shirt ce milk color, kasancewar akwai sanyi matu?a sai ya ?aura wata ha?a??iyar white jacket, ya sanya hular jacket ?in a kansa, kyawawan fararen ?afafunsa suna cikin black socks and luxury booth mai kyau fari, wuyarsa da wani ?an siririn chain mai bala'in tsada, hannayensa ?aya ?aure yake da dan?areren agogo diamond, ?ayan kuma ?aure yake da chains na hannu na zallar madarar zinari masu bala'in tsada, kai guy ?in nan ?an wanka ne na bugawa a jarida, akwai iya ?aukar wanka ga shegen tsabta kamar me, ya ha?u iya ha?uwa. Kara ?aure tiger face ?in nan nasa ya yi kafin ya ?an motsa lips ?insa a hankali furta. "Good morning mum".

Ta tsare shi da kallo kamar zata mayar da shi cikin cikinta saboda tsananin so da kauna, kai daga ganin yadda take kallonsa zaka san tana bala'in kaunar ?an nata fiye da tunaninku.

"Morning my baby, how was your night?".

Shiru ya yi bai sake amsawa ba. Umarni dad ya bawa bodyguards a kan su zuba mashi abinci. Abincin gidan nan fa idan aka girka shi kafin a kawo shi saman dining table sai an yi scanning ?insa, sai na'ura ta tace shi an tabbatar babu wani abin cutarwa a cikinsa, duk dan saboda tsaro, ga shi abincin different kala suke dafawa, sai ayi girki sama da kala 10 lokaci guda........ Ni kam nace koma me zaku yi da zarar wa'adin da Allah ya ?ebawa bawa ya cika dai mutuwa dole ce babu tantama kuma babu wanda ya isa yasa a fasa mutuwa.......... Irin wannan tsaro haka! Dama kunsan shuwagabannin ?asa fa haka suke, komai nasu daban ne, komai zasu ci kuma sai an bincikesa tsab.

Hannu ?aya ya ?aga masu alamar baya bu?atar cin komai tare da mi?e tsaye. Wata black zazzafar luxury glass ya ciro daga aljihunsa ya sanya a idanunsa, nan take ya kara wani masifaffen kyau.

Tun da ya shigo wajen Heleena ta tsare shi da ido, da alama tana tsoronsa sosai, dan yadda ta zauna ta nutsu daga jin kamshin perfume ?insa ya nuna basa shiri sam sam, dan kuwa ita ?in bata da kunya ko ka?an, idan ta tashi rashin kunyarta bata ragawa kowa a cikin gidan sai shi ?in, idanunta a tsai tsaye a tsakar ka na rashin kunya, ko daddy bata raga mashi, duk abin da ya zo bakinta take fa?a masu ba tace magana, shi ka?ai take mahaukacin tsoro, kuma tun da yake da ita sau ?aya ya ta?a dallah mata wani marin da yasa sai da ta sume aka kaita gadon asibiti, daga nan take bala'in tsoron ma su ha?a hanya, dan kuwa ya sauke mata aljanun iskancin da suke kanta na rashin kunya, duk abin da take yi idan ta gansa zata bari ta nutsu sai ya wuce.

Mum ce ta ce ina zai je bai yi breakfast ba?. A takaice ya ce mata yana da meeting ne da wasu yaransa. Daga haka ya sanya kai zai wuce. Mi?ewa mum ?inma ta yi ta bi bayansa. ?aure fuska sosai Heleena ta yi, da kallo ta bisu. Riko hannunsa mum ta yi suka fice daga room ?in kamar wadda zata je ta gaya mashi wani abin, amma nan raka shi wajen motarsa zata yi kafin ita ma ta wuce nata office ?in, tun da ba zai yi breakfast ba ita ma ba zata yi ba kenan, akwai sha?uwa da kauna sosai a tsakaninsu.

Suna futa a filli Heleena ta furta. "I already knew that you didn't love me at all". Ta kai karshen maganar tare da mi?ewa tsaye cikin ?acin rai, ba komai ya ?ata mata rai ba kuma face yadda suke a gidan, shi Smart idan ya yi magana ?aya iyayen nasa basa jayayya da shi, ita kuma idan ta yi magana sai sun ja da ita, yanzu ta ce ba zatayi breakfast a gida ba sun ce basu yarda ba dole ta yi a gida, shi kuma daga ya ce ba zai ci a gida ba sun yi shiru basu kara magana ba, sai ma fasa yin breakfast ?in su ma da suka yi, to hakan ne yake ?ata mata rai, sai ta rin?a ganin kamar suna nuna mata banbanci da shi......... Ni kam na ce Heleenar nan yadda take jin haushin nan tsab idan aka kawo mata contract na kashe smat zata kar?a, gaji yarinya ai sonki ma akeyi da aka matsa maki ki ci abinci amma baki gane ba.

Kai tsaye harabar gidan mum ta fita tana ri?e da hannunsa. Suna fitowa ji kake dip! Dip! Dip gudun manya manyan jami'ai ?osassu masu ji da lafiya kuma madaka katti, dukkansu jami'an dake gidan fararen turawa ne masu jajayen kunnuwa.

Da hannu ya nunawa jami'ai guda biyu su fito mashi da motocinsa fita zai yi ba tare da ya yi magana ba, da alama magana tana yi mashi wahala. Ko da yake irin wannan kyau da Allah ya yi mashi dole ya ja aji sosai, dan yasan shi ?in one in million ne.

Hira mum ?insa take yi mashi ba tare da ya amsa mata ba, yana dai jinta kawai, sai bashi labari a kan wajen aikinta take yi, daga karshe ta ce mashi ko dai zai kaita wajen aiki ne yau?. A takaice ya ce mata no mum. Bata ja da shi ba kawai ta ce a fito mata da jerin gwanon nata motocin.

Haka kuwa aka yi, wata dankareriyar mota aka fito mashi da shi, motocin jami'ai kala hu?u ne suka take mashi baya, mota ?aya na swat ne, mota ta biyu na special emergency unit wato SEU ne, su ?in tamkar wuta suke, aiki da cikawa, baku ji sunansu bane? Emergency suke, abu yana faruwa faka faka zasu dira a wajen su yi handle na komai and they solve everything, so motarsu ce ma a gaba kafin nasa, dan su tabbatar mashi da tsaro, jama'ai ne da suke na musamman. Mota na uku kuma jami'an SSS ne a ciki, suma jami'ai ne masu zafi, duk wa?an nan jami'an sun take sojoji a iya aiki, jarumta, ilimi ha?e da zafin nama, jami'ai ne na musamman masu aiki da ?wa?walwa mamar computer, sannan suna aiki da karfin damtse kamar me.

Smart Tiger a da can baya baya ta?a yarda a take mashi baya, dan a cewarsa ai shi ya fi sojoji da ?an'sanda power to bai ga abin da zai sa su take mashi baya ba tun da ko wani abin ya faru ma sai dai shi ya karesu ba dai su karesa ba, sai dai ya agaza masu, dan haka shi bai ga amfanin su take mashi baya ba, ragwaye ne a cewarsa, wannan dalilin yasa daddynsa a matsayinsa na president ya ?addamar mashi da jami'ansu na musamman wa?an da suka take sojoji da ?an'sanda a tafasar jini da iya aiki, shi ne yasa ya yarda suna take mashi baya, dan ba kananan jarumai bane, nan ma fa sai da mum ?insa ta saka baki ne ya yarda su rin?a take mashi baya su ?in ma, idan ba haka ba yaki yarda, ya ce suma ?ananan kwari ne, daddynsa kuma yana jin tsoron kada wata ?asa ta yi kwantan ?auna ta sace mashi yaro shiyasa bai yarda yana barinsa ya fita shi ka?ai ba. Duk da hakan kuma wlh smart sai ya fita shi ka?ai ?in, shi fa gani yake shi ?in zaki ne a cikin namun dawa, gani yake yi babu wanda ya isa ya ce zai kawo mashi wargi, kuma haka ne, yasan abin da ya taka, ba ?aramin kwaro bane shi ?in.

Mota ta hu?un kuma jami'an NDLEA, motocin biyu suka yi gaba, sannan nasa a tsakiya, sai biyu suka rufa mashi baya.

Juyowa ya yi ya ?an yi hugging na mum ?in tasa, sannan ya manna mata sumbata a kumatu bayan ya raba jikinsu, ita ma sumbatar kumatun nasa ta yi tare da ?aga kafafunta tana son shafa kansa, sai dai bata iya yin hakan ba, dan ya fita tsawo sosai. ?an sunkuyo mata ka?an ya yi ta shafa kan nasa. Sannan suka yi sallama tana sakar mashi lallausar murmushi.

Motar tasa ya nufa, ita ma ta nufi nata jerin gwanon motocin ta shiga. Da gudu securitys suka bu?e masu kofofin motocin nasu, gidan baya ya shiga, ita ma mum a nata motar hakance, gidan baya ta shiga.

Wani katon bature fari tas ne yake tu?a nasa motar, ita ma mum haka. Jerin motocinsa ne suka fara dallawa waje a tsananin guje, sun ?an jima da tafiya kafin motocin mum ya tashi, dan ta tsayar da su tana waya da dad da ta barosa a cikin gida, sai da ta gama da shi sannan ta ce su wuce.

Gudu suke shararawa da motocin nasu kamar zasu tashi sama har suka fita arear Elysee palace dake jibge da securitys ta ko'ina kamar zasu tashi arear, duk in da suka gifta da sunan zasu wuce sai securitys ?in wajen sun ?aga hannu sun sara masu cikin girmamawa.

Kai tsaye Avenue Montaigne Suka nufa, unguwa ce ta manya manyan kai bana ?ananun kwari ba. Duk gidajen dake arear sun amsa sunansu gidajen gaske. Manya manyan luxurious highrise buildings ne kawai a arear, idan ka shiga wannan arear kauyanci ma kawai zai hanaka motsawa daga in da kake

Ya ilahi ya lillahi, my people's ku zo ku ga aljannar duniyar da babu irinta a nan, tun daga kan titin da zata sadaka da cikin gidan wasu irin mahaukatan securitys aka suba a wajen, securitys ne wanda ko giftawarsu ka gani a cikin Tv sai hantar cikinka ya ka?a, jiga jigai ne masu lafiya, sai safa da marwa suke yi a wajen, ga wani uban zare jajayen idanunsu da suke yi suna muzurai kamar mutun ya ruga a guje, yadda suke tsaye suna kewaye ko'ina a wajen bana jin kamar zasu iya barin ko tsuntsuwa ne ta gifta ta tsakar sararin samaniyar harabar wannan gida.

Babban gida ne sosai mai matu?ar girma da ?aukan hankali. Daga yanayin tsarin gidan mutum zai tabbatar da ma?udan kudin da aka zubar wajan tsara shi ba zai ?irgu ba. Ta ko wani ?angare gidan ya ha?u sosai da sosai. Daga wajan gidan akwai wasu flowers da masu kyau da aka ?awata wajan da su, sai babban gate ?in gidan mai matu?ar girma da ?aukar hankali, ga securities ta ko ina da suke shawagi hannayensu ?auke da bindigu, har zuwa second gate ?in da yake wajan, wanda tazaran sa da f?rst gate ?in mutum sai yayi kusan 5 minutes a hanya .

Daga harabar gidan babban fili ne me ?auke da shuke shuke masu kyau da ?aukar hankali, sai babban titin da zai kai mutum har zuwa main building. In short wannan gida ya kai filli girman plot 50. Parking space na wannan gida kawai ya kai girman fili plot 10, tsab zai iya kwasan motoci sama da guda hamsin, a haka kuma cike yake tab da zafafan moto. Pentin gidan gaba?aya ya kasance white color ne, my people's wannan gidan ya ha?u, Allah ya bamu aljannatul firdaus my people's, ku ce amin!.

Da electric stair case suke amfani, amma akwai elevator ma, sai dai sun fi yawaita yin amfani da electric stair case ?in, komai na cikin gidan nan ba ?ananan ?u?a?e aka zuba wajen sayansu ba, lallai ba shakka dollars sun yi kuka kuma sun yi mubaya'a a wannan ginin.

Tampatsa tampatsan gate ?in gidan dukka biyu wasu irin jiga jigan securitys ne suke tsaronsu. Suna dakatawa a parking space na gidan, gaba?aya jami'an suka sau?o ?asa. Bai bi ta kan kowa ba suna bu?e mashi kofar motar yasa kai ya nufi cikin gida.

Wani irin azabbabben dadda?ar kamshi ne yake tashi tun daga ?an nesa da hanyar nufa cikin parlourn gidan, idan nace zan tsaya zayyana maku ha?uwar wannan gida sai mu kwana mu wuni bamu kammala ba, dan haka ku ?awata shi a ranku, ni na yi gaba na je na le?o maku ciki ba zan ?ata lokacina a wajen harabar gida ba.

Shi ka?ai ya shige cikin parlourn, duk sauran securitys da suka rakosa sun tsaya a waje wajen securitys da suka samu a gidan.

Yana shigewa cikin parlourn ya nufi luxurious dining room ?insa, wannan gida dai ba gidan kowa bane face gidansa, bashi da mata, bashi da budurwa, hasali ma bai ta?a yin soyayya ba, kuma bashi da niyar yin matar amma yana da tampatsetsan gida irin wanna, bama wannan ne kawai ba, yana da gidaje sosai, sannan shi mutun ne mai yawan kyauta sosai, yana sadaka fiye da tunaninku, idan zai yi kyauta kuma baya za?ar wa zai bawa, duk wanda ta fa?a kansa kawai bashi zai yi, duk da bashi da sau?in kai da tausayi amma yana da zuciya mai kyau, ga taimakawa gajiyayyu, ku?insa basa tafiya a banza.

Yana zama saman table ?in sai ga wani na'ura mai siffar ?an adam ya shigo wajen. A gabansa na'uran ya tsaya yana jiran umarni.

Ya ?auki tsawon lokaci yana latsar wayarsa wadda shi ka?ai company ta kerawa irinsa, shi ya bada design da duk wasu abubuwan da yake bu?ata da yadda yake so wayar ta kasance, wane mutun ya iya bibiyarsa ta wannan waya, a gar?ame take da matakan tsaro na ban mamakin gaske, komai maitancinka a iya computer baka isa ka datsi tsaron dake tattare da wannan waya ba har ka shiga cikinta, dan shi ma guy ?in shegene a fagen iya computer

So ya jima yana latsa wayarsa kafin nan ya bawa na'uran umarni ya kawo mashi breakfast da ya fi kauna, ya ha?a mashi da Espresso strong coffee...... Ko meyasa yaki yin breakfast a gida ya zo gidansa?.

Da sauri na'urar ya juya ya bar wajen. Cigaba da latsa wayarsa shi kuma ya yi.

A hankali sautin ringing ?in wayarsa ta fara tashi, shiru ya zubawa wayar sexy eyes ?in nan nasa masu shegen shining kamar me.

Har wayar ta katse bai ?auka ba, ?ira na biyu ne ya sake shigowa, a dai'dai lokacin kuma wannan na'ura mai yi mashi aikin ya dawo hannunsa ?auke da wani jibgegen glass tray mai bala'in kyau. Kayan abinci kala kala ne a saman wannan ha?a??en tray ?in tare da spoon, knife da sauransu.

Saman table ?in ya ?aura trayn, sannan ya tsaya a gefe yana jiran umarnin ya hau yin serving.

Kira na uku ne ya sake shigowa, a lokacin ne ya yi pick tare da sanya wayar a hand-free ya ?aura saman table ?in a kusa da shi tare da ?auko tsadaddiyar cup dake cikin tray ?in mai sha?e da Espresso strong. A hankali ya kai ?an bakinsa, lips ?in nan nasa ba'a magana, yana ?aukar hankali matu?a.

Ka?an ya ?an kur?a ya cire, a nutse yake bin komai daki daki, cikin class mai jan hankali.

Daga cikin wayar tasa wata ?atuwar fasashiyar murya ta furta. "Sir the RS52-nuclear was mistakly feared". Cikin tashin hankali mai maganar ya yi ta, yadda yake maganar har word ?insa suna ha?ewa.

Shiru ya yi bai yi magana ba, kuma bai nuna alamar kamar ya shiga tashin hankali ba duk da ya ji cewa sun yi mistake sun saki nuclear bom ?in, basu yi setting ?inta ba aka samu akasi suka saketa, amma hankalinsa a kwance, cigaba da shan espresso strong ?insa ma ya yi. Daga cikin wayar wanda ya yi maganar ya sake cewa. "Hello sir I said the RS.........". Bai bari ya ?arisa sake fa?a ba ya sanya kyakyawan hannunsa ya katse kiran.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull