Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 32

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 32

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 32: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 32. Lallai akwai cakwakiya, wannan guy ?in gaskiya bana ce komai ba, ace maka…

3,357 words

Lallai akwai cakwakiya, wannan guy ?in gaskiya bana ce komai ba, ace maka nuclear ta kwace ta fita amma yana zaune yana sharholiyarsa??? Akwai matsa in dai haka ne, ni dai bari na hau jirgi sai ?asar Nigeria cikin birnin jimeta Yola mu dubasu mu gani, kila kafin mu dawo ya farka daga barci, dan ni ban yarda cewa baya barci ba, nuclear bom fa ake magana amma yana zaune, kuma shi ka?ai zai iya shawo kan matsalar, to ni dai kada nuclear nan ta yo Nigeria ato, ta tsaya a ?asar tasu ko kuma ta yi ta yawo a sararin samaniyarsu, na dai gudu abina.

_________________________??????

JIMETA??

Duk wani karfi dake tattare da shi ne ya kare sakamakon wannan aman, kan kace me ya zube ?asa ya kwanta, sama sama yake numfashin tamkar ba zai rayu ba.

Bappa dai bai karaya ba kuma bai ji komai ba ya matso ya fara yi mashi sannu. Wani irin fita da karfi karfi numfashinsa ta fara yi tamkar zai sume, bawan Allah dama bashi da lafiya ya zo kuma ya ?arisar da ?an karfin da yake da shi a wajen yin amai. A ru?e bappa ya mi?e tsaye ya nufi waje har yana ha?awa da gudu.

Matasa ya nemo a kan su zo su taimaka mashi ya kai Jaish ?in ?aki ya taimaka mashi da agajin gaggawa kada ya mutu.........

My people's ina son ?aukar hutu, kuma ina son in bari sai mun kai ?arshen book 2 ko tsakiya sai na ?auki hutun, wanne kuke ganin ya fi? In ?auki hutu yanzu ne ko sai na kai tsaki ko kuma karshen book 2? Ina son in ?an huta kwakwal ta yi fresh ta ?aro wala?anci, ?? ku tayani da addu'a.......??

??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????

??RAWANIN ?? ZALINCI ????

????????????????

FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????

?????????? 11/10/2024.....??????

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????

??ZANGO NA BIYU....??????

E20

Matasa ya nemo a kan su zo su taimaka mashi ya kai Jaish ?in ?aki ya taimaka mashi da agajin gaggawa kada ya mutu.

Kama shi suka zo suka yi izuwa cikin ?akin, a saman gado bappa ya ce su kwantar mashi da shi. Duk kyakkyamin nan nasa yana ji yana gani suka kamashi izuwa cikin ?akin, kamar ba zai rayu ba! Sai ma da suka kama shi ne jikin nasa ya ?ara tsananta ciwo, dan kuwa da alama wannan uban kyakkyamin nasa a jini take, shiyasa yake fama bawan Allah, kun san akwai wa?an da abin a jininsu yake, akwai wa?an da kuma tsabta ce ta ja masu hakan, idan kana da tsabta sosai tana iya ja maka hakan, to shi bayan tsabta ma a jininsa take abin, shiyasa ko ya ce zai bari ma zai sha bakar wahala ne a banza, dan ba abu bane da za'a iya barinta kamar yadda kuke tunanin nan.

Datse idanunsa gam ya yi baya son ganin cikin ?akin bappan, saboda kyama, ga shi bashi da wani za?in da ya wuce ya kwanta shiru, saboda ko motsawar kirki baya iya yi, cikinsa ne yake bala'in mur?a mashi kamar zai mutu.

Magunguna bappa ya hau ji?a mashi tare da yi wa mutane da suka taimaka suka kamashi izuwa cikin ?akin godiya. Idanunsa a datse gam yana numfashi sama sama har bappa ya kammala ji?a magungunar, su kuma samarin suka yo waje, ?aya daga cikinsu ya ?auki Mahreen izuwa cikin ?akin ya kwantar da ita a gefen Jaish ?in, sannan suka fice daga gidan.

Idanunsa a datse bappa ya fara ?ura mashi magunguna masu uban ?aci kamar me, abin da bai ta?a sha ba, ko a mafarki bai ta?a mafarkin zai sha irinsu ba, ga shi bashi da za?in da ya wuce ya ha?iye a cikin cikinsa dan dolensa, dan kuwa kansa yana ?age da pillow ne, yadda bappa ya sanya mashi bakin kwaryar a ?an bakinsa dan dole ya ha?iye, dan bashi da karfim da zai iya ture maganin ko kuma ya iya ture bappa or ya yunkura ya ce zai fitar da maganin, bashi da kuzarin iya motsa kansa ma bare iya amayar da maganin, haka ya ?ara datse idanunsa ya jin maganin tana ratsa ma?ogwaronsa izuwa cikinsa, wani irin takaici da yake ji kamar zai mutu, ji yake yi kamar ya tashi ya sha?e bappan har sai ya mutu, amma dukka babu halin yin hakan.

Tsab bappa ya yi mashi duk abin da ya dace, sannan daga karshe ya ?ara mashi da maganin cin abinci na gargajiya, a lissafin bappan idan ya bashi maganin da zata sanya shi cin abinci zai ci abinci sosai dan ya samu kuzarin jikinsa.......... Ni kam na ce lallai ba shakka bappa ya gama da Jaish tab?ijam, yanzu yunwa da ba kanwar kowa bace zata nukurkushe mana Jaish na mu ta yadda dan dolensa ya nemi abinci ko dan ya rayu. Akwai matsala gaskiya, bappa dai bai kyauta ba da wannan magani na cin abincin gaskiya .......????

Cin abincin ruga ya kama Jaish Innalillahi. Ko da yake Mahreen zata yi mashi gata wajen bashi a baki, idan ya ki ci ma zata iya yi mashi ?ure wannan yarinyar kam........ Duk kuma cikin gata ne!.??

Barci mai nauyin gaske ne ta ?aukesa. Fitowa waje bappa ya yi, ruwa ya ?ebo ya zo ya yayyafawa Mahreen, abin mamaki a nutse ta farfa?o, tana farfa?owa kuma ta fara rambayar bappan nata ina aljaninta yake?. Da hannu bappan ya nuna mata shi, sannan ya ce. "Jeki ki kira mun hammanku Faisal kin ji?".

Turo baki ta yi, a shagwa?e kamar zata yi kuka ta ce. "Amma bappa kasan dai bana son hamma Faisal ?in nan ko?".

"Yi hakuri gajina jeki ki kira mun shi kin ji ko? Daga yau na yarda baki son shi". Mi?ewa ta yi tana turo baki ta nufi waje. Kai tsaye gidansu Faisal ?in ta nufa. Tana shiga ta gaida Innarsu, sannan ta ce bappa na kiran hamma Faisal, bata jira amsar Innar ba ta wuce ta fice abinta.

Gida ta koma, a lokacin bappa yana hura wuta a kitchen, Nenne kam har yanzu bata dawo ba. Wuta ya hura ya ?aurawa Jaish ruwan wanka, bayan ya ?aura ya fito waje, Mahreen kuwa ?akinsa ta shiga, a kusa da Jaish ta zauna ta tsare shi da idanu, ita dai a duniya aljanin nan nata yana matu?ar burgeta, ya yi mata kyau sosai, bata gajiya da kallonsa, sannan bata son kawar da kallonta a kansa, sai dai yau bata ta?a mashi kumatu ba, domin shakkarsa ya ?an shiga ranta, ta ji tana ?an shakkarsa.

Sallama cikin nutsuwa Faisal ya yi a bakin kofar gidan kafin ya shigo ciki. Har ?asa ya du?a ya ?agawa bappa gaisuwa, cikin so da kauna bappa ya amsa mashi tare da ce mashi. "Yau Shehu ne ya tafi kiwon shanun bappanku ko?". Kai ya gya?a mashi alamar e.

"Tom dama so nake ka je ka kar?awa Mahnoor kiwon nan ta dawo gida, ta zo ta yi mana girki, ni yau ba zan samu fita ba".

Da to ya amsa mashi tare da mi?ewa tsaye ya nufi waje. Ruwan albarka bappa ya fara sanya mashi, da amin amin ya yi ta amsawa har ya fita, bappa yana kaunar Faisal sosai, a yanzu bashi da burin da ya wuce yaga ya ?aura mashi aure da Mahnoor, ha?i?a Faisal yaron kirki ne sosai, ga girmama manya da sanyin hali sosai da sosai, baya son yanayina kuma baya yi, bashi da fa?a kamar na sauran matasan ?a?an fulani, ko takalarsa fa?a kayi baya kula mutun, yana da hakuri sosai da kawaici ha?e da kunya, idan kunji yana magana ma to sun ha?u da abokiyar fa?arsa ce wato Mahreen wanda dama can ita bata zaman lafiya da kowa, duk wanda ya ce mata kule sai ta ce cas, to da ita kawai zaku ji yana magana mai sauti, sai masoyiyarsa abar kaunarsa wato Mahnoor.

Yana fita ba jimawa sosai sai ga Mahnoor ?in ta dawo, tana shigowa Nenne na shigowa tamkar a tare suke. Ai Nennen tana shigowa nata ?akin ta nufa da sauri saboda tsoron Jaish, tana bala'in tsoronsa sosai. Ita ma Mahnoor akwai tsoron nasa dai, amma haka ta nufi kofar ?akin bappan jiki na kerma, kirjinta sai dukan uku uku yake yi.

A bakin kofa ta tsugunna tare da cewa bappan. "Bappa jam?andu?. (Bappa ina wuni?)". Yana daga cikin ?akin zaune a kusa da Jaish da kuma Mahreen ya amsa mata gaisuwar tata sannan ya ?aura mata da cewa abinci zata girkawa bakonsa mai da?in gaske.

?an zaro idanu ta yi kafin ta ce. "Bappa dama aljanu ma suna cin abinci ne?". Kyakkyawar murmushi ya sakar mata kafin ya bata amsa da. "Mahnoor baki yarda da bappanki bane?".

Girgiza kai ta yi tare da cewa. "A'a bappa na yarda da kai". "To idan har kin yarda dani kuma zan yi magana ki ji to na gaya maki wannan bawan Allahn ba aljani bane, mutun ne kamar kowa, ku dai'na ?aukarsa a matsayin aljani, sannan batun kyansa da kuka damu sosai a kansa ku sani akwai mutane kyawawa sosai a duniya, ba yadda Allah baya halittar bawa, amma na maku alkawari ke da Mahreen in zan sake fita Nigeria zan tafi daku, ko Cameroon kuka je akwai turawa mazauna can sosai bama sai a Nigeria ba, akwai larabawa, to wannan bawan Allahn yana ?aya daga cikinsu, ko bature ko balarabe, ni nasaba ganin irinsu shiyasa ban damuba, dole ma idan zan sake tafiya in tafi daku dan ku kalli irinsu saboda ku rage tsoro". Ya kai karshen maganar yana kallonta.

?an karkatawa ta yi ta le?o fuskar Jaish ?in kafin ta sake dawo da kallon nata a kan bappan. "Tom shikenan bappa, na yarda ba aljani bane, amma ni dai ina jin tsoronsa har yanzu, bari na je na dafa mashi tuwo dawa da miyar zogale".

A hanzarce bappan ya fara girgiza mata kai tare da cewa. "A'a Mahnoor ba zai iya cin irin abincinmu ba ai, su basa cin tuwo, kinga yanayinsa ya yi maki kama da wanda zai iya cin tuwo ne?".

Kai ta girgiza mashi alamar a'a.

"Yauwa ai ba zai iya cin irin namu abincin ba, yanzu dai zan yanka mashi zabbi da kaji ko guda goma ko ashirin haka, sai ku gyara ku soya mashi, nasan nama kam zai iya ci tun da suna ci, sai a rin?a dama mashi fura yana ha?awa kafin ya samu sauki ya koma garinsu".

"Tom bappa, bari na sanya ruwa a wuta dan gyara kajin". Da to ya amsa mata, mi?ewa ta yi ta nufi kitchen, shi ma bappa ya mi?e ya fito waje, wajen kajinsu da zabbin nasa ya nufa, haka ya za?o manya manya guda ashiri, kaji goma zabo goma, ?osassu ya za?o, sannan ya tsinto kwan zabi dayawa ya dawo da su cikin gidan.

Mahreen ce ta ri?e mashi wuyar kajin ya yankesu dukkansu, Mahnoor bata ta?a yarda ta ri?e mashi kaji ya yanka, saboda tsoro irin nata, sannan tana da raunin zuciya sosai, idan ana yanka kaji tana wajenma har kuka take yi, dan tausayi suke bata, ba zata iya ganin ana yankasu ba, sai ma idan ransu ya zo fita, a wannan lokacin kuka sosai take yi, shiyasa bata tsayawa a wajen da ake yankan, ita kuwa Mahreen sarkin taurin zuciya da rashin tsoro, ai tuni take ri?ewa bappa ya yanka, ita ko wukar aka bata tsab zata kar?a ta yanka da kanta, ai wannan yarinya special ?in specials ce.

Dukka ya yankasu, da shi da Mahreen suka ha?u suka taya Mahnoor gyara kajin, Nenne dai taki fitowa daga cikin ?akinta, tana kwance tana tunanin wani irin mugunta zata ?ullawa Mahnoor wanda zai sanya bappa ya tsaneta ya dai'na sonta, ya jima tamkar ya kasheta idan ya ganta, abin da kawai ta kwanta take tunani kenan.

Baiwar Allah Mahnoor kuwa tana can tana aikin farantawa mahaifinta rai tana samun lada ba tare da tasan me Nenne ke shirin kullah mata ba.

Sai misalin karfe 3 ta gama soya kajin nan dukka, dan ma Bappa da Mahreen sun tayata sosai, ta gama bappa ya ce ta dafawa Jaish ?in kwan zabbi bari ya duba gonarsa ko akwai nunannun kaya itatuwa ya taho mashi da su a ha?a mashi a kayan abincin nasa kila zai ?an iya ci.

To suka ce mashi, wucewa ya yi ya fita ita kuma Mahnoor ta juye ruwan zafin dake saman wuta ta je ta yi wanka. Mahreen kuma ta kwashe namar ta kai shi cikin ?akin bappa.

Mahnoor bayan ta fito daga wanka shirin zuwa Islamiya ta yi fes abinta ta fito, sannan ta ce da Mahreen ta fito daga ?akin bappan nan ta wuce tazo ta yi wanka ta yi shirin zuwa Islamiya bari ita kuma ta tattare gidan ta share kafin lokacin yin sallar la'asar ta yi sai su yi sallah su wuce islamiya, sam basa jin yunwa dan sun ci namar kajin sosai sun ?oshi, da yake su kam ma ba bakin nama bane, kullum Friday bappa yana tanka masu ?aton rago ?osasshe guda ?aya, kaji kuwa duk lokacin da yaga dama yana yanka masu, so su nama baja baja suna da shi.

Tsintsiya ta ?auko da nufin ta fara share gidan, dai'dai lokacin Nenne da ta tashi a barci yanzu ta fito waje.

"Ke Mahnoor ?auko mun jakar littattafan bappankun nan bari na duba wani littafin addu'oi a ciki zan kai wa gwaggona". Cewar Nennen, tana maganar tana jefawa Mahnoor ?in wani irin kallon tsana.

Narai narai baiwar Allah ta yi da idanu, tamkar zata rushe da kuka ta ce. "Nenne dan Allah ki yi hakuri Mahreen ta ?auko maki, wlh ina bala'in tsoron wannan mutumin da bappa ya kawo, dan Allah Nennen ki yi hakuri, Mahreen ce bata jin tsoronsa, zata iya..........". Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon wani irin matsiyacin kallo da Nennen ta wurga mata, shiru ta ha?iye sauran maganar tata, nan take idanunta suka ciko da kwallah.

"Lallai Mahnoor kin girma, yanzu ni ce zan aikeki ki ce mun in aiki Mahreen? E lallai kuwa, yanzu ai da uwarki ce ta aikeki ba zaki ce mata hakan ba ko? Shekiyar idanunki manya manya kamar na mayun nan kina kallona da su in zo in kwakwale maki su in zubar, wlh tun wuri ki wuce ki je ki ?auko mun jakar nan ko in zo wajen in shakeki sai kin mutu"............ Hasbunallahu wani'imal wakil. Wai menene amfanin mugunta ga ?an uwankan a duniya my people's? Kun ga dai wannan zallar madarar mugunta ce Nenne take ji da shi, idan ba mugunta ba fisabilillahi ita da kanta tana bala'in tsoron Jaish ?in nan, dalilin tsoronsa har ta koma gidan babanta, amma tsabar mugunta zata ce Mahnoor ta shiga in da yake ta ?auko mata jaka fisabilillahi, ai wannan zalinci ne, meyasa ita ba zata iya shiga ba hegiya.

Mahreen da take jiyo duk abin da suke fa?a ne ta fito ri?e da jakan bappan a hannunta tana fa?in. "Nenne Adda Mahnoor fa tsoron aljaninna ?in nan take yi, ni ne kawai bana jin tsoronsa, ga jakar nan na kawo maki......" Wani irin uban harara da ta wurga mata ne yasa ta tsaya ta kasa ?arisowa in da take da jakar.

"Wuce ki mayar da jakar nan ta shiga ita ta je ta ?auko mun, ai Mahnoor na ce ta ?auko mun jaka ba Mahreen ba uwar goninta".

Tur?une fuska ta yi tamkar zata sanya mata kuka.

"Ko kukan jini zaki yi yau sai dai ki yi, kuma idan baki wuce kin mayar da jakar nan ba wlh in na damkeki a cikin gidan nan sai buzunki".

Sanin cewa bappansu bayanan kuma tasan halin Nenne nasu sarai ne yasa ta juya tana turo baki ta wuce mayar da jakar.

"Sai na sake gaya maki abin da zaki yi ne?". Ta jefawa Mahnoor dake tsaye idanunta cike tab da kwallah tambaya. Allah ya sani my people's kun sani Mahnoor tana bala'in tsoron Jaish, tsabar tsoronsa da take ji ma ko bappanta yana cikin ?akin bata shiga, amma saboda bakin mugunta irin na Nenne wai sai ta shiga, ga shi Bappa baya nan ma bare ta ji confidence na shiga. Wasu zafafan hawaye ne suka fara bin ?uncinta, ji take yi kamar shikenan yau ta mutu, abin gwanin ban tausayi sosai. Jikinta har kerma ya fara yi, Allah sarki haka ta nufi cikin ?akin tana karanto duk addu'ar da ya zo bakinta saboda tsoro.

Wani irin shu'umin murmushi na mugunta Nenne ta saki, cikin ranta ta furta. "Ai tun da na gano kina jin tsoron wannan aljani wlh kullum sai na ha?aki hanya da shi, shegiya shi ne ma zai zama ajalinki, ko bani da aika cikin ?akin bappanku sai na ?a?alo ko na karya ne na aike ki ciki sai dai ki mutu in zaki mutu, dama ni fatana kenan ki mutu kowa ma ya huta annoba kawai".

Dai'dai zata shiga ?akin bappan Mahreen ta fito ta nufi waje tana turo baki alamar ta ji haushin Nenne, Mahnoor tana son cewa Mahreen ?in ta juya ta koma ciki dan ta rakata, amma ba hali, dan Nenne na tsaye ta tsareta da ido.

Ciki ta shiga tana kuka, kamar ranta zai fita, har zufar dole ta fara ha?awa. Ganin idanun Jaish ?in a rufe alamar yana barci ne yasa ta yi saurin ?arisawa wajen da jakar yake a in da yake ma?ale a jikin wata itace da ya sanya a jikin bangon wajen. Jakunkuna kala uku ne a wajen. Hannunta nata kerma da kyar ta iya ciro wanda Nenne ta aiketa, juyawar da zata yi caraf suka yi ido hu?u da shi, yanzu ya farka daga nannauyar barcin da ta ?aukesa tun safe.

Ai a dubu ?ari ta kwala ihu tare da jefar da jakar a ?asa ta fasa waje a guje tana ihu.

Tana fitowa Nenne ta damkota ta hau jibga da bata ga jakar a hannunta ba, dama kiris take jira ta na?a mata duka, dan kwana biyu bata daketa ba, saboda Mahnoor yarinya ce mai kiyaye dokoki, komai a nutse take yi, da wuya ka samu ta yi wa wani laifi, tana taka tsantsan da komai, komai aka sanyata a hanzarce take yi, hakan yasa Nennen bata samu ta rin?a jibgarta, dan bata yi mata laifi, shiyasa take ta neman laifinta komai ?an?antarsa ta ci zalin yarinya ta zalunceta a banza.

Ai kuwa jibgarta ta fara yi da karfi, kuka ta fara yi tana fa?in. "Dan Allah Nenne ki yi hakuri, wlh ya bu?e idanunsa ne yasa na gudo, wayyo Allah!". Gwanin ban tausayi.

Ina ai Nenne bata saurareta ba, kai mata duka da hannun take yi ta ko'ina tana fa?in. "Har na aikeki ki ki yi mun abin da nace, dan kinga ina yi maki dariya ko? Ni sa'ar wasarki ce? Yau sai kin gaya mun na haifeki ko ban haifeki ba?". Tana magana tana haki saboda muguntar da take yi.

"Wlh Nenne kin haifeni, dama ni a uwa na ?aukeki, dan Allah ki yi hakuri".

Ina ai cigaba da dukanta Nennen ta yi tana fa?in. "A'a baki ?aukeni a uwa ba, da kin ?aukeni a uwa ai da kin yi mun abin da nace, kuma wlh ko zaki mutu yau sai kin je kin ?auko mun jakar nan, ki wuce ki ?auko mun jakar nan in ba haka ba wlh sai na takaki har hancin cikinki sai sun zubo waje".

Kamar daga sama tana tsaka da jibgarta ta ?ago idanunta sai a kan kofar ?akin bappan, hakan yasa suka yi ido cikin ido da Jaish ?in da yake tsaye ya dafa bango da hannu ?aya ya kuma ?an rage tsawonsa saboda ciwo da cikinsa yake yi mashi. Ya ?aura hannunsa ?ayan a saman cikinsa alamar cikin yana yi mashi tsananin ciwo, ihun da Mahnoor ?in take yi ne yasa shi lalla?awa ya fito waje, dan sun takura mashi, sun toshe mashi kunne, ya fito ne yaga su wanenen suke matsawa rayuwarsa?.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull