Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 33
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 33: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 33. Ai kuwa tana sauke idanunta a cikin nasa idanun by mistake, wani irin…
3,358 words
Ai kuwa tana sauke idanunta a cikin nasa idanun by mistake, wani irin mahaukacin ihu ta zunduma, a dubu ?ari ta saki Mahnoor ?in, kada kuso ku ga yadda ta wantsala wa?an nan siraran kafafun nata kamar na shamuwa ko balbela za'a ce ne, wasu sirara da su ga uban tsawo, ai a ?ari ta watsa a guje sai waje tana ihu kamar wata zararriya, sai fa?i take. "Yau na shiga uku na, yau na yi ido hu?u da aljani shikenan zan rasa hankalina da ganina, shikenan zan dawo aljana nima". Ai bata zame ko'ina ba sai gidan Ar?o, sai ihu take a kan hanya, ta ja matasa da dama suka rufa mata baya da nufin su kamata, dan a tunaninsu ta rasa hankalinta ne take wannan ihun a kan hanya, shiyasa suka bita dan su ji me yake faruwa.
Ita kuwa Mahnoor tana ganin Nennen ta saketa ta yi waje da gudu ne yasa ta fara waige waige tana son ganin me ya sanya Nennen ta saketa? Ita dai tasan idan Nenne ta fara dukanta sai ta gaji take rabuwa da ita, komai magiyar da zata yi mata bata ha?ura har sai san da ta gaji, to yau me ya faru ta saketa?. Ai kuwa unexpect ita ma ta ha?a ido da shi, yana tsaye, yadda yake bin su Gimbiya Sarina da kallon wala?anci haka yake binsu da irin wannan kallon, irin wannan kallon nasa yana mugun karyawa mutun zuciya, dan kallo ne mai kama da mugun harara, ta gefen ido yake wurgawa mutun irin kallo, ko ya kake idan aka yi maka irin wannan kallon wala?ancin sai ka ji ka shiga wani irin yanayi, sai ka zargi kanka ko baka da gaskiya ko kuma ka yi laifi ne, irin wannan kallo wlh sam bashi da da?i idan aka yi wa mutun, duk sai yasa gaji kai ba komai bane a duniya, to haka dama yake kallon su Sarina, ya kware a iya irin wannan kallon wala?ancin, kuma Sarina da Fanan yafi yi wa irin kallon, dan ya tsane yaran nan bare ma Fanan da ake son ?a?aba mashi ita, ya tsaneta, tsanar kuma ta samo asaline daga kan Mammiensu, tsanar da ya yi mata ne ya shafesu suma.
Ai kuwa suna ha?a ido ta kwala ihu, a guje ta nufi waje. Karaf suka ci karo da bappa dake shigowa cikin gidan hannunsa ?auke da ?an ?aramin buhu da ya zuba kayan fruits a ciki. Baya baya ta yi ta fa?i ?asa.
"Subhanallah Mahnoor lafiya kika fito a guje haka?". Cewar bappa. Kasa iya amsa mashi ta yi, fuskarta jaga jaga da hawayen dukan da Nenne ta yi mata.
Mahreen dake biye da shi a baya ne ta yi kan Mahnoor ?in tana fa?in. "Adda Mahnoor meyasameki? Naje gonar bappa ne fa na gaya mashi Nenne ta saki zuwa wajen aljani, dukanki Nennen ta yi ne?".
Kai ta girgiza alamar a'a Nenne bata daketa ba. Kama hannunta Mahreen ?in ta yi a in da ta taimaka mata ta mi?e tsaye. Hannu tasa tana goge mata hawaye. "To waye ya dakeki?". Ta sake jefa mata tambaya.
Da kyar ta iya saita nutsuwarta tare da cewa. "Babu wanda ya dakeni, aljanin ne ya tashi ya fito waje shi ne ya bani tsoro".
Da sauri bappa ya ce. "Yauwa masha Allah to mu koma ciki bari naje na bashi abinci, dan nasan yanzu abincin kawai zai bu?ata, saboda yasha maganin cin abinci".
Ba musu suka wuce gaba ri?e da hannun junansu, ya rufa masu baya. Jaish dai yana tsaye a in da yake, bai motsa ba, ya kasa iya komawa ciki ne saboda rashin karfi, dama da kyar da su?in goshi ya iya fitowa wajen, yanzu kuma ya kasa motsawa ma daga in da yake, ga wani irin azabbabben yunwa da yake ji, ji yake tamkar ana yayyanke mashi ?a?an hanjinsa saboda azabar yunwa, a wannan yanayi da yake ciki wlh kome ya samu zai iya ci bawan Allah, maganin cin abincin bappa ta fara aiki gadan gadan.
Suna shigowa ya bawa Mahnoor buhun hannunsa a kan ta je ta wanke fruits ?in ta kawo mashi. Shi kuma ya matso ya kama Jaish ?in yana yi mashi fa?a a kan ya dai'na tashi kada ya je ya fa?i ya jiwa kansa ciwo, ya bari zuwa gobe ko jibi idan ya ?ara samun karfi sai ya rin?a fita. Ko kallonsa bai yi ba, hasalima ba jin yarensu yake yi ba, dan haka bai ji me bappan ya ce ba, shi dama yare biyu ya iya, daga larabci yaren iyayensa sai kuma turanci yaren masu jajayen kunnuwa.
A wannan karon sam Jaish ?in bai yi wani yunkuri ture bappa ko wani abin magamancin hakan ba, saboda bashi da wani karfi, yana ji yana gani bappa ya ?an rungumosa suka koma cikin ?akin, zaunar da shi bappan a saman tabarma ya yi, sannan ya janyo mashi kwaryar namar da Mahreen ta kawo cikin ?akin ta ajiye da suka gama suya, bayan ya janyo mashi kwaryar namar ne ya sake janyo mashi kwaryar dake shake da ruwan sha mai sanyi na randar ta?o, ya kuma yi sanyi tamkar a fridge aka ?auko shi. Bu?e mashi paipain dake rufe da kwaryar namar ya yi tare da tura mashi gabansa. Habawa azababben yunwar da yake ji yasa ya mance da cewa ma ana yin brush a duniya, ai hannu kawai yasa ya fara ?aukar namar, ya mance da cewa yana jin kyamarsu. Haba ai yunwa ba kanwar uwar kowa bace bare ta tausayawa bawa, kowa ta kama kifar da shi take yi ta nukurkushesa har sai ya zama abin tausayi, duk wani iyashegen mutun da tsiyarsa duk sai yana ?oshe yake yi, komai ji da kan mutun yunwa tana sanya shi ya yi ladab ya mi?a wuya, to yau dai ga Prince Jaish yunwa ta kifar da shi ta nukurkushesa har ya zama tamkar ba shi ba....... Allah mai iko yau Jaish ne a Nigeria, a Nigeria ma a Adamawa, a Adamawan a rugar fulani zaune yana cin abincin da suka girka da hannunsu, rayuwa kenan ba ta yadda bata juyawa bawa, ina son ku kara tunawa da cewa yau idan kai ne gobe ba kai bane, duniyar ma gaba?aya nawa take? Wuni guda ?aya fa take a wajen mahaliccinmu, Allah kasa mu cika da kyau da imani ha?e da kalmar shahada!!.
A bakin kofa Mahnoor ta tsaya ta mi?awa Mahreen kwayar fruits ?in da ta wankosu tas, sun yi fresh da su. ?an satar kallon Jaish ?in ta yi yadda yake cusa namar nan a bakinsa tamkar wani ya ce zai kwace mashi, bawan Allah yadda kuka san shi da wasu zakunar da suka shekara basu ci abinci ba yake ci, sai cusawa yake yi a cikin bakinsa, irin kada su cinye su barshin nan, bai gama cinye na bakinsa ba zai sake ?auki wani ya cusa a bakin masa, shi da yake cin abinci cikin class mai ?aukar hankali, cikin nutsuwa da jan aji, yau sai ga shi yana cin abinci tamkar almajirin da ya kwana uku bai ga idanun abinci ba, har ya karyar mun da zuciya, shi ma aya ce mai zaman kanta a garemu, yau da gobe sai Allah, yau da gobe ta wuci wasa, dan haka kada ki ga Allah ya baki wani matsayi a rayuwarki ki ce zaki wala?an wasu, a kowani lokaci Allah na iya canza abubuwa ba tare da ya nemi shawarar kowa ba, Allah na iya kwace abinsa ba tare da neman shawararki ba, dan kuwa lokacin da ya baki ma ai bai nemi shawararki ba, dan haka ina fatan Jaish ya zamar mana aya ku ?auki darasi........ Ni dai bari na le?a wani ?angaren.
___________________________????
KHADIJAH ????
A hankali ta juyo dan ganin wanene?. Wani matashi ne da ba zai wuci shekaru 25 zuwa 27 ba. ?arisowa in da take ya yi, murmushi ya sakar mata yana ?o?arin bu?e baki ya yi magana ta rigasa da cewa. "Ina wuni malam?".
"Lafiya lou Alhdulillah Khadija Ahmad, ya gida yasu mama?". A takaice ta amsa mashi da lafiya lou Alhdulillah.
Shiru suka ?an yi, shi ?in malaminsu ne na islamiya ?insu. Katse masu shirun ya yi da cewa. "Khadijah Ahmad duk abin da ya faru da ku na samu labari, Allah ya ji?an baba da rahma ya kuma sanya mama ta iya cin wannan jarabawar tata".
Shiru ta yi ta kasa iya amsawa da Amin ?in, saboda wani irin tukukin bakinciki da ya taso mata, yanzu kenan labarin abin da mamarsu ta aikata ya baza ko'ina? Yanzu duk in da zasu wuce nunasu za'ana yi kenan ana cewa ga wa?an da mamarsu ta kashe babansu? Innalillahi wainnailayhir rajiun! Hasbunallahu wani'imal, wannan wace iriyar musifa ce?!.
"Kiyi hakuri Khadija komai mai wucewa ne, sannan ko wani bawa da irin tasa ?addara da jarabarwar, fatana dai Ubangiji Allah ya baku ikon cin jarabawarku, ki cigaba da addu'a". ?an dakatawa ya yi da maganar yana kallon face ?inta, duk da ba wani hasken kirki ne a wajen ba amma suna iya ganin juna, shi da kansa yasan ta yi ki?a kuma ta yi haske, ta ?ara kyau sosai, dama kun san Zainab ta fita haske, to yanzu har ta kusa ?ara Zainab ?in a hasken fata.
Cigaba ya yi da cewa. "Dama naga kun jima baku zo islamiyya bane yasa na ce bari na zo na duba meyasa baku zo ?in ba? Allah yasa dai kuna lafiya?". Daga yadda yake magana da ita cikin mutunci da girmama juna zaku iya fahimtar kaunarta yake yi, ba shakka akwai soyayyarta a zuciyarsa ga kwayar idanunsa ma ya nuna hakan.
Wani irin wahalallen ajiyar zuciya ta sau?e, murya a karaye kamar zata sa kuka ta ce. "Malam muna nan lafiya, sai dai islamiyyar ce ba zamu iya cigaba da zuwa ba, duk fa yanzu kowa yasan abin da ya faru da mu, kasan dama can ?an islamiyyan namu ba kaunarmu suke yi ba saboda bamu kula kowa muna yin rayuwarmu ne kawai, yanzu idan mun je islamiyya ai kanmu muka jawa bakinciki, dan dai babu wanda zai hana yaran islamiyyar nan tsokanarmu a kan mamarmu ta kashe babanmu, dan haka mu ba zamu sake zuwa ko'ina ba". Ta kai karshen maganar siraran zafafan hawaye na bin kuncinta.
Hakika shi kansa yasan da haka, kuma yana matu?ar tausaya masu, saboda zasu zama abin tsangwama a cikin mutane, amma hakan ba shi ne zai sa su ki neman imili ba, a zamanin yanzun nan ka nemi ilimin ma idan aka ?unsa maka wani bakinciki in ba ka kai zuciya nesa ba sai ka aikata sa?on Allah bare ace kuma baka nemi ilimi ba ai sai abin ya kwa?e maka, amma hakika ya matu?ar tausaya masu na irin rayuwar da zasu fara fuskanta a wajen al'umma a yanzu.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Nasan da haka Khadijah, amma ba hakance zata sa ku ?i neman ilimi ba, kin san da cewa ilimi yana da matu?ar mahimmanci sosai, dan haka ku kawar da kanku a kan duk abin da zaku gani kuma zaku ji, ku daure ku nemi ilimi, kada ki manta babanku bashi da burin da ya wuce ya ga kun yi karatu mai zurfi, to meyasa ba zaku kokarta ku cika mashi burinsa ba? Ki yi tunani a kan hakan mana". Ya kai karshen maganar yana mai da kallonsa a kan mutumin da yake fitowa daga cikin shagon da ta fito a yanzu.
"Tom shikenan malam zamu yi shawara da ?ar uwata da kuma kawunmu Sadiq, kowani hukunci ya yanke mana shi zamu kar?a tun da shi ne mamarmu kuma babanmu a yanzu". Tana magana zafafan hawaye ne suke cigaba da bin ?uncinta.
"Dan Allah Khadeejerh ki daina kukan nan haka ya isa, addu'a kawai zaki rin?a yi, addu'a makamin mumini, kada ki zama kamar baki da tawakkali sannan wadda bata yarda da ?addara ba mana! Dan Allah kukan ya isa haka, Allah ya gani ba zan iya jurar ganin kukanki ba........."
Wani irin ?augo kai ha?e da kallonta a kansa ta yi na jin kalamansa na karshe in da yace ba zai iya jurar kukanta ba. ?an kawar da kallonsa daga kanta ya yi ya mayar da kallon nasa a kan mutumin da ?azun ya fito daga cikin shagon, so ya tsaya ne a ta bakin shagon yana making call.
"Kamar yadda kika ji na fa?a ne Khadeejerh, ba zan iya jurar ganin kukanki ba, zuciyata tana sosuwa sosai saboda ba zan ?oye maki ba ina sonki, ba kuma tun yau na fara sonki ba, ya kai shekara biyu ina dakon sonki, ban samu damar furta maki bane sai yanzu, ki sani aurenki nake son yi".
Wani irin zaro idanu waje ta yi, kirjinta ta ji ya bada dukan uku uku, bata ta?a zaton hakan daga garesa ba. A dai'dai wannan lokacin kuma wannan mutumin da ya fito daga shagon tun ?azun yake tsaye yake waya ya zo wucesa ta kusa da su.
A ?ari ta wani irin toshe hancinta da hannunta saboda wani irin bala'in warin da kamshin turaren bawan Allahn nan ya yi mata, duk da ta toshe hancinta nan take cikinta ya mur?a zuciyarta ya fara tashi, kan ta yi wani yunkuri amai mai karfin gaske ya kwace mata....... Tashin sense.
Bata iya matsawa daga in da take tsaye ba ta fara tikar aman, hakan yasa ta ?atawa malamin nata jikinsa da aman, da yake yana kusa da ita ne. ?asa ta tsugunna ta cigaba da sharara amanta. A ru?e shi ma ya tsugunna yana tambayarta lafiya me yake damunta. Ina ai bata iya bashi amsa ba amai kawai take yi.
Sosai ta yi aman har ta galabaita, idanunta suka yi jajir kamar jini, ta sha wahala sosai. Ganin aman ya dakata ne yasa malamin nasu ya yi saurin nufar shagon mai provision ?in na bayansu ya kar?o mata ruwa. A harzarce ya zo ya fasa ruwan ya bata. Da kyar ta iya kar?a ta fara wanke bakinta da shi, da kyar ta iya mi?ewa tsaye, bata sake ce da shi ko uppan ba ta nufi hanyar gida, tana tafiya tamkar wadda ta sha wani abin, sai layi take yi kamar zata fa?i ?asa. Bin bayanta ya yi yana yi mata sannu har suka isa bakin titi, sai tambayarta yake yi dama bata da lafiya ne? Me yake damunta? Har da ?arawa da an kaita asibiti ne ko ba'a kaita ba?.
Ita dai ko sannu bata sake ce mashi ba, haka ta samu da kyar ta tsallaka titin ta nufi hanyar gida. Binta ya yi yana cigaba da yi mata magana bata kula shi ba har ta shiga cikin gida ta barshi tsaye a waje.
Hauwa kawai ta isko a parlourn, tamkar bata ganta ba ta wuce ta nufi ?akin nasu, har lokacin kuma tana layi kamar wadda ta sha wani abin.
"Ke Khadeejerh lafiya kike kuwa?". Cewar Hauwa uwar shisshigi a lamuran mutane. Ai yadda kuka san da bango take magana haka Khadeejerh bata kulata ba, cigaba da tafiyarta kawai ta yi har izuwa cikin ?akin nasu, ta banko kofa ta murza key.
Tana shiga bata kula Zainab bama ta wuce cikin toilet ?insu. Wani aman ta je ta sakeyi saboda yadda cikinta yake mur?a mata sosai, har lokacin tana jin warin turaren mutumin yaki sakar mata hanci, shiyasa ta sake zuba wani aman. A ru?e Zee dake kwance a saman gado ta diro ?asa, ita ma ba wani karfin kirki bane a jikinta amma haka ta bi bayan Khadeejerh ?in da gudu izuwa cikin toilet ?in.
Ganin tana ta amai ne yasa ta ?ara ru?ewa, a rikice take tambayarta meyasameta, ta yi maganar tare da ?arisowa ciki ta ri?eta. Bata iya amsa mata ba sai amanta da take yi, sai da ta yi mai isarta, sai da zuciyarta ya ?anyi sanyi sosai sannan ta wanke bakinta tare da cewa Zee ta saketa ta fita bari ta yi wanka.
Cikin kuka Zee ta ce. "Amma Aunty Khadeejerh ki gaya mun me yake damunki tukun nan in fita".
"Kije ?aki idan na fito zamu yi magana". Ta fa?a da kyar. Tana kuka ta nufi wajen ba tare da ta sake yin wata magana ba.
Wanka ta yi tare da ?auro towel ta fito. A zaune a bakin gado ta isko Zee ?in, wucewa ta yi ta nufi wajen jakar kayan da Zee ?in ta dawo da su daga asibiti, dukkansu basu da kaya sai wanda Sadiq ya kwasowa Zee ?in daga tsohon gidansu ya kai mata asibiti lokacin da take kwance, kayansu duk yana tsohon gida.
Wata doguwar riga ta ciro ta sanya a jikinta, tsawon bai kai mata har ?asa ba kam, amma ba laifi ya ?an yi mata daidai, sai dai ya matseta sosai, dan ta fi Zee ?iba ka?an.
Gadon ta zo ta haye ta kwanta, zannin gadon ta ?angaren da take ta yaye ta lullu?a da shi, nan take ta fara rawan sanyi alamar zazza?i. Ganin haka sai yasa Zee bata iya sake tambayarta me yake damunta ba, sai ta yi shiru kawai, daga karshe ma lalla?awa ta yi ta dawo kusa da ita suka kwanta a tare, kafin wani ?an lokaci barci ya yi awon gaba da su ba tare da sun ci abinci ba bayin Allah, ga Zainab bata sha magungunarta ba, basu yi waya da Sadiq ba haka barci ya yi awon gaba da su.
______________________????
KINGDOM OF POWER.
Dai'dai Gimbiya Chuchu zata shiga bedroom na Akka ta ji an rufe mata idanu ta baya. Murya a sanyaye ta ce. "Yah Jawad me haka ne wai?". Zame hannayen nasa ya yi tare da cewa. "Waye ya ce maki ni ne?".
Juyowa ta yi suna fuskantar juna tare da ciro wayarta daga kunnenta. "Ba wanda ya gaya mun kai ne face kamshin perfume ?inka".
Kashe mata ido ?aya ya yi tare da cewa. "Da waye ake waya to? Naga kina kan call". Dawo da kallonta kan screen ?in wayar ta yi. "Yah Rizwan ne". Jinjina kai yayi ba tare da ya sake yin magana ba, gera kawai ya ?aga mata alamar ta cigaba da yin wayarta mana.
Mayar da wayar kunenta ta yi tare da cewa. "Yah Rizwan zamu yi magana anjuma, zan yi hira da Yah Jawad yanzu". Bata jira amsarsa ba ta katse kiran.
Tana katse kiran ta ?ago da kallonta a kansa, while shima kallonta yake yi, suna ha?a idanu suka sakarwa da juma murmushi. Sunkuyar da kanta ?asa ta yi tana cigaba da murmushi.
"Me kuke tattaunawa ne da Yah Rizwan ?in namu?". Ya jefa mata tambayar yana ?ago ha?arta, dan ta sunkuyar da kai ?asa. Ha?i?a ya ji matu?ar da?in yadda ta bashi mahimmanci, ta bar abin da take yi ta ce wannan lokaci nata nashi ne yanzu bana yin magana da kowa ba ne, ya ji matu?ar da?in hakan, bawan Allah bai san soyayya take yi da yayan nasu ba!. Hmmm akwai gagarumin matsala ranar da ?aya ya fahimci ?aya yana sonta, sai Allah ne ka?ai yasan irin bala'in tashin hankalin da bayin Allahn nan zasu shiga, waye zai hakura ya barwa ?an uwansa? Ko dai dukkansu biyu hakura zasu yi ne? Anya ma a cikinsu akwai wanda zai iya hakura kuwa? Dan fa dukkansu suna yi mata zazzafar so ne fiye da tunaninku!! Gaskiya Mammaiensu nan bakar azzaluma ce, zata azabtar da su cikin ruwan sanyi ta hanyar sanya masu ciwon zuciya, bayin Allah marayun Allah masu kaunar junansu zata shiga tsakaninsu ta rabasu, wato idan Allah ya ha?aka da mai bakar zuciya fa kai kam ka shiga uku wlh, Allah dai ya kyauta ya shiga tsakanin nagari da mugu!.
"Hira kawai muke yi da shi, ya ce mun zai zo a satin nan saboda Akka sannan kuma saboda au........." Wani irin kunya ne ya rufeta ta kasa iya ?arisa gaya mashi sannan kuma saboda aurensu, kasa karisa maganar ta yi, ta yi shiru.
"Awww sai a zauna ayi ta hira da su Yah Rizwan ni ba za'a zo ?akina a tayani yin hiran ba ko?". Cikin zolaya ya yi maganar.
A ?an shagwa?e ta ce. "Kai Yah Jawad kai fa Momma ta hanani zuwa room ?inka, ta ce kada na sake shiga ciki, ko naje kai maka wani abin na tsaya a iya parlour kawai".