Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 34

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 34

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 34: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 34. ?an le?o face ?inta ya yi. "Eyeee momma zata shiga tsakaninmu kenan? Ni ba…

3,339 words

?an le?o face ?inta ya yi. "Eyeee momma zata shiga tsakaninmu kenan? Ni ba zan yarda ba gaskiya, ni dai ki rin?a zuwa ko a parlourn ne ma mu zauna ki yi mun hira dan ki rage mun kewa". ?an zaro idanu ta yi tare da cewa. "Yah Jawad kai kuma wani irin kewa zaka ji? Kana ganin yadda face ?inka take wani shining daga gani kullum hira kake yi a waya da Auntynmu da zaka auro......" Ta kai karshen maganar tare da sanya hannu ta toshe bakin nata tana ?an murmushin.

Damko west ?inta ya yi yana fa?in. "Waye ya gaya maki ina da budurwa da nake yin hira da ita?". Wage baki ta yi da karfi ta furta. "Akka ga Yah Jawad nan zai......" Ai bai bari ta ?arisar ba ya toshe mata bakin nata da hannun ?aya, sanin cewa in dai Akka tana cikin room ?inta to ba abin da zai hanata fitowa ne yasa ya yi saurin zame hannunsa daga bakin nata ya fara ?o?arin cicci?arta sama su bar wajen.

Tsabar tsiya irin nata sake cewa. "Akka ki zo ki ceceni a hannun Yah........." Ai dan dole ?aniyarta ta dakata bata ?arisa maganar ba saboda abin da ya yi mata a wannan karon, ya ?auketa cak da hannayensa, ga shi tana son ?ira mashi ruwa hakan yasa ya rufe mata baki da ?an bakinsa tun da ba hannu.

Dama ta ce tun da ta gane baya son Akka ta gansu a tare ta ce zata fara rama abin da ya yi mata, to ga shi ta fara ramawa kuma ta samu kyautar sumbata, karon farko kenan a rayuwarta, dan ma Allah ya taimaketa mutumin kirki ne ai da kiss ma mai gaba?aya zai yi mata ba iya sumbata ba, to na dai yi shiru.

Nutsuwa tsit ta yi tare da datse idanunta gam, kai tsaye room ?inta dake kusa da na Akka ya shiga da ita, a tsakiyar ?akin ya sauketa yana kawar da kallonsa daga kanta izuwa kofar shigowa, dan ya ji motsi a waje wanda yake kyautata zaton Akkar ce, dan yasan dama in dai tana nan wannan ihun sunanta da Chuchun ta yi zata jiyota shi, idan ta ji kuma tabbas zata fito waje, haka kuwa aka yi, ita ?ince ta fito duba waye ya kirata...... Yah Jawad yana wasa sosai, Momma ta ce ya ?oye soyayyarsa kada ya bari kowa ya sani, amma yana wasa da hakan sosai, har ?aukar Chuchun yake yi a tsakar rana ido na ganin ido, sam baya gudun ya ha?u da wani a cikin family.

A hanzarce ita kuma Chuchun ta ra?a gefensa zata wuce ta gudu ta bar ?akin. Riko hannunta ya yi tare da dawo da kallonsa a kanta. A hanzarce ta yi ?asa da kanta, dan wani irin kunyarsa ta ji, sunbatar tasa ta tsaya mata a rai, ga shi unexpect ya yi mata shi, a lokacin idanunta suna a kan face ?insa, sun ga juna ido cikin ido a yayin da ya sauke ?an bakinsa a saman nata, duk abin ya tsaya mata a rai, yanzu ba zata iya ha?a ido da shi ba.

"Ina zaki je kuma Jannat?". Yana magana yana kallon face ?inta, shi ko kunyar abin da ya aikata ma bai ji ba. ?asa ?asa kamar wadda bata son yin magana ta ce. "Wajen Mommana".

?an ?ago habarta ya yi dan su kalli juna, sai dai taki yarda ta ?ago idanunta su ga junan. "Fa?a mun waye ya gaya maki ina da budurwa kafin ki tafi?". A hankali ya yi maganar kamar wani mai fa?awa wani gulmar wani.

?an turo baki ta yi. "Su Aunty Sarina naji suna fa?a ita da Aunty Fanan wai kana da budurwa saboda ranar ta jika kana waya da budurwar taka". ?an zaro idanu ya yi yana mamakin ko shi a yaushe ya yi waya da wata? Amma yaran nan sun iya sharri da shegen sa ido, kawai dan sun ji yana waya sai aka ce masu da budurwarsa yake waya?.

"Yah Jawad Mammie ma fa ta aiko naje na manta, ka sakeni na tafi wajenta". Ta fa?a tana ?an ?agowa ta saci kallonsa.

"Jannat yanzu ni dan na yi waya da mutun sai nace da budurwa nake waya?". ?asa ta ?ara yi da kai kafin ta bashi amsa da cewa. "A'a da Aunty Fanan ta ce baka da budurwa sai Aunty Sarina ta ce ta jika ka yi ?asa da murya sosai kana gaya mata kalamai na soyayya masu da?i, wai in ba budurwarka ba ba zaka gaya mata hakan ba". Innalillahi Chuchu ta bu?e aiki, dama zama suke yi suna yin gulmarsa kenan, yau ta tona asiri.

Zaro idanu ya yi sosai. "Dama zama kuke yi kuna magana a kai'na ko Jannat?". Yadda ya yi maganar murya a kausashe ne yasa ta ?ago ba shiri ta kallesa. Ganin ya ?aure fuska ne yasa ta fara bashi hakuri tana gaya mashi wlh ita bata yi gulmansa ba, Sarina da Fanan and Aneesa ne suka yi.

Sosai ya ji babu da?in abin da suka yi mashi, ya kuma yi alkawarin sai ya hukuntasu tun da zama suke yi suna gulmarsa. Ganin yadda ta ?an tsorata tana bashi hakuri ne yasa ya saki face ?insa tare da ce mata ta je ta amsa kiran Mammie ?in ta dawo ta same shi a room ?insa. Ya kai ?arshen maganar tare da sakin hannun nata. A hanzarce ta amsa da okey tare da sanya kai ta wuce, da kallo ya bita har ta kurewa ganinsa. Sai da ta kurewa ganin nasa ne ya rufa mata baya a in da ya nufi part ?in su Sarina dan hukuntasu, haka kawai zasu sanya beb ?insa ta fara tunanin yana da burdurwa ta yadda ko ya bayyana mata soyayyarsa taki yarda ta ce yana da wata, lallai basu nemi zaman lafiya ba dole su sha hukunci.

Kai tsaye part ?in uncle Abbas ta nufa ita kum, zaune kamar kullum ta isko Mammien a saman sofa tana wani shan kamshi kamar ita ce Princess na kingdom ?in. Har ?asa Chuchu ta tsugunna ta gaisheta, sai sakin wani irin murmushin mai wuyar fassaruwa take yi tun lokacin da Chuchun ta shigo, dan haka fuska ?auke da murmushi ta amsa gaisuwar tata tare da ce mata ta zauna a saman sofa...... Kai yaran King Zuhair sun samu tarbiya, ji yadda Chuchu ta gaisheta cikin girmamawa, da wata ce yadda take ji da ita ?ar sarki ce ai ba zata zube a ?asa dan gaishe da Mammie ba, amma su babu ruwansu suna girmama Mammien.

Zama ta yi a saman sofan ba musu, wani kwalban turare Mammien ta ?auko daga in da ta ajiye saman hannun sofan, mi?a mata shi ta yi tana fa?in. "Ga wannan turare ne da nasa aka ha?a maki, na sanki da shegen son gayu kakar Guyson ?inmu, shiyasa na saya maki wannan zazzafar perfume ?in, ke ka?ai zaki yi amfani da abinki kada ki tsamma kowa......."

A hanzarce ta tari numfashinta da cewa. "Mammien har da Auta ma kada na bata ta sanya a jikinta?". Kai ta gya?a mata alamar e sannan ta cigaba da cewa. "Ke ka?ai na sayawa, dan nafi kaunarki fiye da kowa, dan haka kar?a abinki". Ta kai karshen maganar tare da mi?o mata. Hannu tasa ta kar?a jikinta duk ya yi sanyi, dan ance kada ta tsamma Auta sai ta ji jikinta ya mutu, amma haka ta kar?a ta mi?e ta nufi waje bayan ta zuba mata godiya.

Da wani irin shu'umin kallo ta bita da shi har ta fice waje, murmushi mai wuyar fassaruwa ta saki. Ita kuwa Chuchun tunani take yi a kan babu wanda ya isa yasa ta hana Auta wannan perfume ?in, a tare zasu yi amfani da shi sai dai mutun ya mutu, yo ita in za'a bata abu a bawa Auta bama ba gara a hanata kawai ba, dan in dai aka bata sai ta bawa Autar......... Cakwakiya kenan, anya turaren Allah da annabi Mammie ta bata kuwa? To ga shi dai ta ce tare zasu yi amfani da shi ita da Auta bayan ance nata ne ita ka?ai, tab akwai rugugin aradu kam.

Aftar some hours.??

___________________????

AUTA AND HOORAIN?????

Zaune take a saman kujera, gari ya yi duhu, amma wajen nasu haske ne tamkar rana, saboda kwayayen bulbs dake ta ko'ina a wajen. Ta tada kai da laps ?in Hoorain dan ta ce mashi tana tsoron wajen, dan dole ya matso kusa da ita, sun yi shiru kowannensu da abin da yake tunani, shi ya jingina kansa da jikin kujeran ya ?aga kai sama, ita kuma tana kwance shiru ta ha?a hannayenta waje guda tamkar mai jin sanyi.

Tamkar a mafarki sadauki Hoorain ya ji busar yaki, a wani irin zabure ya furta Hasbunallahu wani'imal wakil, yaki kuma a masarautarsu da daddaren nan? Innalillahi wainnailayhir rajiun!.

Kafin ya yi wani yunkuri tuni masarautar ta gauraye da busoshin yaki, ta ko'ina buga bososhin yaki ake yi, daga in da suke suna iya jiyo gudun dakarun yaki gaba?aya suna hallara a harabar kingdom ?in.......... Tashin hankali! Yaki unexpect kenan, kuma da daddare fisabilillah?! Subhanallah, ko suwaye da wannan ?anyar aikin na kawo masu farmaki da daren nan?!.

??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????

??RAWANIN ?? ZALINCI ????

????????????????

FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????

?????????? 14/10/2024.....??????

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????

??ZANGO NA BIYU....??????

E21

Kafin ya yi wani yunkuri tuni gaba?aya masarautar ta gauraye da busoshin yaki, ta ko'ina buga bososhin yaki ake yi, daga in da suke suna iya jiyo gudun dakarun yaki gaba?aya suna hallara a harabar kingdom ?in.

Jin irin yadda ya furta Hasbunallahu wani'imal wakil ?in ne yasa Auta ?ago kai ha?e da kallonta a kansa. "Hoorain lafiya kuwa?". A sanyaye ta fa?i hakan. Kallon face nata ya yi tare da jan doguwar numfashi, a gaskiya Kingdom of power ta jima rabonta da yaki, tun Zunaira na jaririya, shiyasa ta kasance bata san ya busoshin yaki ma yake ba, tana dai jin labarin yadda masarautar tasu ta sha gwagwarmaya a baya, ta san yadda suka shiga filin daga a can baya, sun fafata da makiya ba ka?an ba, dan a caf fa?in ?asar Tunisia kujeran mulkin babanta gaba yake dana kowa, wannan dalilin yasa kowa yake farautar kujerar yake neman samun damar mallakarta.

Sai dai kuma basu iya samun damar mallakar ba, dan fa gaba?aya ?a?ansa su Ramish da kuke ganin nan ba baya ba wajen tsayawa mahaifin nasu tsayin daka, a lokacin suna Dubai, amma sun tasowa su zo a duk lokacin da aka kawowa mahaifin nasu farmaki, basu ?aga kafa har sai sun rama sun mayar da martani, commander Zafar and Hoorain ba karya sun hidimtawa masarautar nan tamkar nasu ne, akwai yakin da aka ta?a gwabzawa a masarautar wanda a lokacin an kashe mutane da dama shekarun baya da suka wuce, to jama'a suna kyautata zaton cewa a wannan lokacin aka kashe Mahaifiyar Hoorain, dan tun daga wannan yakin ba'a sake ganinta ba, a lokacin da aka kawo masu hari bata nan ta fita daga cikin masarautar ita da wasu kuyangu, ba'a sake jin ?uriarsu ba har yau, commander ya sha kuka da hawayensa tamkar karamin yaro, da alama suna son juna sosai, shi ma Hoorain ya sha kuka sosai, a lokacin yana ?arami ma.

A can cikin gida kuwa gaba?aya ?an'matan King suna part ?in Akka, duk cikinsu babu wadda ta ji tsoron busar yakin da ya kara?e masarautar, dan fa wlh jinin Modarawa basu da tsoro ko ?igo, abin a jininsu yake tun zamanin jahiliyyah kafin zuwan addinin musulunci haka suke, ka ta?osu ka shiga ?ari uku bama uku ba, komai tsawon shekaru suka samu dama sai sun rama babu yafiya a cikin lamuransu!! In dai baka ta?osu ba basa zalunci zaku zauna lafiya! Ka ta?osu su rama ba ?aga kafa!.

Yah Jawad and uncle Taheer kanin mama ne suka fito daga cikin part ?insu a zafafe, kowannensu da abin da yake tunawa, shi Yah Jawad kai tsaye part na King ya nufa, dan kaunar da yake yi wa dad ?in nasa, a cewarsa bari ya fara da tsare ubansa kafin kowa. Shi kuma uncle da yake shima ya ta?a renon Commander Zafar yana ji da karfi kai tsaye waje harabar gidan ya nufa, ko'ina yau a cikin kingdom ?in zaratan zakunan warriors na masarautar ne wa?an da ake kira da dangerous warriors. Wasu warriors ?in sai ha?a kan mata bayi suke yi izuwa wajen da ya dace su ?oyesu dan basu tsaro, wasu kuma sai shirin yaki suke yi, wasu suna shirya zafafan makaman yaki, Allah yasa ma a ko da yaushe da shirin yakinsu suke, saboda sun san su ?in kowani sarki farautar kujerar King Zuhair yake yi, sun san a koda yaushe zasu iya afkawa yaki ba tare da saka time ko date ba, ba yau suka fara samun harin yaki unexpect irin wannan ba, an jima ana yi masu irin wannan shammatar Allah yana basu nasara a kan makiya.

Habawa ai a ?ari commander Zafar ya fito daga part ?insa, ban da Hoorain babu wanda yake nema, nemansa yake kamar hauka a kan ya zo ya jagoranci ?angaren da suke kula da makamai bari shi kuma ya kula da zakunar mayakansu da zasu fara yin gaba wato masu harbi da kifiya kenan, akwai abokin Hoorain ?in wanda kuke ganinsu kullum a tare mai suna Ansar, shi kuma commander ya ce mashi ya ha?a kan dakarun da zasu fita da dawakai, ya ce su ha?a dawakai guda 400 ma ya isa, dan ma sun ga ba ?ananan mayaka bane suka kawo masu hari, sannan kuma suna dayawa sosai suma, gasu da manya manyan kayan yaki sosai.

Kan kace me masarauta ta ru?e, dan ma suna da tsari sosai.

Yah Jawad yana ?o?arin shiga part ?in King Aunty MieMie tana shigowa, a tare suka ?arisa ciki, ba wanda ya iya yi wa ?an uwansa magana, saboda dukkansu hankalinsu baya jikinsu, yana wajen mahaifin nasu. Ba komai ya ja haka ba face sun san dayawan lokuta idan aka kawowa masarauta hari fa mayakan kwantan ?auna suke yi su nufi in da sarki yake, shi suke fara kashewa kafin su yi ?o?arin ruguje komai, shi ya ?aga masu hankali sosai, sannan abu na biyu sun san kafin a kawowa masarauta hari fa dole sai an santa ciki da waje, dole akwai ?an le?en asirin wasu masarautun a cikinsu ba tare da sun sani ba, so sun san da wuya idan wa?an da suka kawo masu harin a yanzun nan ba'a gaya masu in da King Zuhair yake ba ta yadda kai tsaye zasu hari wajen da yake ?in dan su fara kashe shi.

Ai kuwa suna shiga suka wani irin jan burki ba shiri, dukkansu zaro idanu waje suka yi tamkar idanun nasu zai fa?i ?asa. Ba komai suka gani ya sanyasu jan wannan birki ba face yadda suka sami King a tsaye cikin uniform na maya?a, ya yi tsayuwar jarumta tamkar wani zaki, ga Momma a tsaye kusa da shi tana ?o?arin taya shi shiryawa, da alama ita ta sanya mashi kayan, sai jan mashi gemu take yi tana yaba shi tare da yi mashi kirari a kan ba'a ta?a samun wanda ya ci nasara a kan modarawa ba tun farkonsu har izuwa yau, su ?in jarumai ne na bugawa a jarida, dan haka ta sani da izinin Allah koma su waye suka kawo masu hari da izinin Allah sune zasu yi nasara, sai kara kuranta mijin nata take yi, ko a jikinta, babu karaya ko tsoro a tattare da ita, tsabar zafin zuciya da karfin hali irin nata ta yarda mijinta ya shiga filin daga duk da yake sarki, dan ita gani take in bai shiga filin dagar nan ba za'ayi nasara a kansu tun da ?a?an cikinsu basa nan, ita fa Momma ta yarda da jarumta King, tasan sarai zai iya, su Mama dai sun ki yarda a kan ya shiga fili, tun ?azun suke yi mashi magiya a kan ya hakura a matsayinsa na sarki ya haura sama ya kalli yakin daga sama, momma ta ce a'a dole ya fita saboda al'ummarsa, shi ma ya ce a matsayinsa na adalin sarki dole ya fita saboda al'ummarsa, ya ce kowa dake cikin kingdom ?in nan mutun ne kamar shi kuma kowa yana son ransa kamar yadda shi ma yake son nasa, dan haka kamar yadda yake son kansa da lafiyarsa, matansa da ?a?ansa suke sonsa suma al'ummarsa haka suke son kansu da kuma matansu da ?a?ansu suke sonsu, dan haka dole ya fita ya gwabza dan ya samu hujjar kare kansa a gaban Allah a kan amanar talakawa da ya bashi....... Gaskiya King Zuhair adalin sarki ne over wanda samun irin sa zai yi matu?ar wahala a duniyar yanzu!!.

Akka ma tace ya fita ta bashi goyon baya, kun san jinin Modarawa yake gudu a jikin Akka, ita da Momma ba sarewa ko karaya a lamuransu, basu san menene ja da baya ba, akwaisu da taurin zuciya kam sosai da sosai.

Tun ?asun suka rin?a dragging da su mama and Mummy a kan sun ce su basu son ya fita, hankalinsu a tashe har kuka Mummyn Gimbiya Chuchu ta yi, amma daga karshe ma ce masu ya yi su fice mashi a ?aki fita babu fashi tun da su basu san hakkin bayin Allah da yake rataye a kansa ba, dan haka su fice mashi a part, shi ne yasa suka fita Akka ma tace tana zuwa ta wuce part ?inta, ya rage daga shi sai momma dake ta kara mashi kwarin gwiwa shi kuma yana ta bata wasiya a kan koma bai dawo a raye ba, sam bata wani ?auki wasiyar tasa da mahimmanci ba, dan tana ji a jikinta zai dawo garesu, su fa Modarawa wlh basa ta?a yin tunanin fa?uwa, kullum tunanin sune da nasara suke yi.

Da sauri Yah Jawad ya ?ariso wajen nasu da nufin shima ya dakatar da daddyn nasu daga fita filin, ita kuwa Aunty MieMie da yake jinin King ?in ne a jikinta habawa juyawa ta yi sai part ?inta ta fara shirin yaki ita ma, dan na gaya maku mayakiya ce sosai a baya, har mutunmutuminta aka sassa?a a kofar masarautar tasu, so jaruma ce sosai da sosai, haka ta hau shiryawa dan ta takewa babanta baya zuwa wajen yakin, a nan ta sami mijinta ma yana shirin yakin, kai kingdom of power gaba?aya babu ragwaye, gaba?ayansu a shirye suke, a koyaushe suna shirye su afkawa yaki bayin Allah, jininsu a tafashe yake!!.

Kallon Momma dake ta zubawa King kirarin kara mashi kwarin gwiwa fuskarta ba yabo ba fallasa Yah Jawad ya yi kafin ya ce. "Momma ba zaki hana dad fita ba?". A ru?e ya yi maganar!!. Bawan Allah bai ta?a ganin dad ?insu a filin yaki ba, dan lokacin da ake gwabza yaki shi da Jaish suna Dubai basu dawo ba, shiyasa hankalinsa ya tashi sosai.

"A kan me zan hana shi Jawad?". Ta jefa mashi tambayar tare da ?auke hannunta daga kan gemun King ?in tana dawo da kallonta a kan Jawad ?in, while shi ma King kallonsa yake yi da wa?an nan idanun nasa kamar shi ya arawa gimbiya Zunaira su.

"Momma yaki fa? Haba bai kamata dad ya fita yaki ba! Duk yawan mayakan da muke da su basu isa ba sai dad ya fita?".

"Jawad ina son ku sani su kansu maya?an dake cikin kingdom ?in nan nauyinsu ya ratayane a kan daddynku, matsawar daddynku adalin sarki ne to fa dole hankalinsa ya tashi ya shiga filin daga domin kare al'ummarsa, duk wasu adalan sarakuna haka suke, kuma mu jininmu basu san sarewar gwiwa ba! Dan haka ka kawo wata zancen ba wannan ba!!". Cewar Momma, murya a ?an kausashe ta ?arisa maganar.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull