Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 35

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 35

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 35: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 35. Tana rufe baki King bai bari Yah Jawad ?in ya sake yin magana ba ya ce mashi.…

3,372 words

Tana rufe baki King bai bari Yah Jawad ?in ya sake yin magana ba ya ce mashi. "Kaje ka ha?a mun kan ?a?ana dukka ka sauke mun su izuwa under ground, sannan umarni ne ka tsaya da su a wajen, duk da mayakan da zasu basu tsaro ban yarda ba, dan mutun bare ba abin yarda bane, ana iya ha?a baki dasu ko a sayesu a cutar mun da family, dan haka ka tsaya da su kada kaje ko'ina,". Fuska a ?aure ya yi maganar, hakan yasa Yah Jawad bai ja da maganar ba, dan kuwa bai ga alamar wasa a tattare da dad ?in nasu ba, in a serious note ya yi maganar, dan haka sai ya kar?i umarni ya juya ya fita kawai.

Shi da Jaish mafa sun ta?a renon Commander Zafar, jarumta a jininsu yake, suna da karfi sosai, amma su wajen Ramish and Bilal suka koyi wannan training ?in kafin commander!.

Yana fita ya nufi part ?in Akka, a nan ya samesu gaba?ayansu except Auta, harta Mammiensu da su Mummy sun ha?u a wajen.

Yana zuwa ya ce da su su tashi su tafi, Chuchu na ganinsa ta taso da gudu ta nufesa tana fa?in. "Yah Jawad Aunty Sarina ta ce mun yaki za'ayi kuma Auta ban ganta ba, na shiga uku dan Allah Yah Jawad ka nemo mun ita, na je part na Momma bata nan, na je ?akinta bata nan, na duba ko'ina ban ganta ba, kuma ni yau since morning fa bamu ha?u da ita ba". Wani irin zaro idanu ya yi tare da mayar da kallonsa kan su Fanan ?in. Tabbas bata cikinsu, a ?ari ya fara tambayarsu ina take?.

Cikin girmamawa su Fanan ?in da suka sha duka a hannunsa ?azun suka amsa mashi da suma basu ganta ba, ?azun sun ci duka sosai a hannunsa, lilis ya yi masu kamar an aiko shi, su Sarina iyayen rashin kunya sai da idanu ya rena fata, an daku, shiyasa suka nutsu suka kara bashi girma suna girmamashi dan dole ?an ?aniya.

Jin cewa kowa ya ce bai ganta bane yasa ya ce yana zuwa bari ya dubata ko tana barci a wani ?akin. Da sauri Chuchun ta ce. "Yah Jawad zan bika". Girgiza kai ya yi. "A'a Jannat ki zauna a cikin ?an uwanmu, dan kinga yadda Kingdom ?in nan yake a rikice ban lamunta ki bini ba, ki zauna ina zuwa yanzu zan tambayo Hoorain ko ya ganta ne, in dai bata cikin nan kinga ta fita waje kenan, idan ta fita kuma dole Hoorain zamu nema, dan shi ne mai alhakin kula da ita a duk lokacin da ta fita". Ya kai karshen maganar tare da nufar waje.

Kuka ta sanya mashi tana yi mashi magiya a kan dan Allah ya tafi da ita, tana son ta raka shi ta riga kowa ganin ?ar uwarta autansu. Tsawar da Mammie ta daka mata a kan ba zata bishi ba ta wuce ta dawo ne yasa ya juyowa tare da dakatawa daga tafiyar da yake yi. Da farko bai da niyar juyowa ya saurareta saboda baya son fita waje da ita, amma da Mammie ta yi magana sai ya ji yana son fita da ita, dan haka da ya juyo sai ya mi?a mata hannu kawai.

A guje ta nufesa, a hanzarce ya ri?o hannunta kafin Mammie ta yi wani magana ya fice waje abinsa. Kai tsaye part part na kowa suka fara shiga suna nemanta.

A can cikin gonar kuwa, cemata Hoorain ya yi ta tashi a kafarsa yana zuwa, tashi ta yi tana mai cigaba da tambayarsa lafiya kuwa?. Bai iya amsa mata ba ya yunkura zai tashi domin ya nemo masu hanyar fita daga wajen nan.

A hanzarce ta ri?o hannunsa tare da cewa. "Hoorain kasan dai ina tsoro shi ne zaka tafi wani wajen ka barni ko?". Kamar zata yi kuka ta yi maganar, ta yi maganar kuma cikin shagwa?a tana turo baki. Ita sam bata san bala'in da yake faruwa a cikin masarautar ba.

?an kawar da kallonsa daga kanta ya yi, wannan yarinya ta rantse sai ta jefa shi cikin wani hali, shi idan tana irin wannan magana tana sawa ya ji tamkar yana a sararin samaniya, irin wannan shagwa?a ta rin?a yi mashi ?azun har tasa ya yarda ta kwanta a saman laps ?insa ba tare da ya sani ba. Hannunta ya ri?e ba tare da ya yi mata magana ba. Mi?ewa tsaye ta yi suka fara kewaye a cikin gonar suna neman hanyar da zasu iya fita ba tare da sanin masu gadin bakin gate ba. Tafiya ka?an ya yi ta fara yi mashi shagwa?a a kan ita ta gaji da tafiya sai dai su koma su zauna. Da yake shi yasan me yake faruwa baya son gaya mata ne yasan halinta sarai, yanzu idan ya gaya mata me yake faruwa a cikin kingdom ?in in ta fara yi mashi kuka sai tasa ya ru?e ya fita hayyacinsa, dan zata yi kuka ta ce sam ya mayar da ita cikin gida taga ?an uwanta suna lafiya ne, sanin hakan ne yasa ya saki hannunta tare da tsugunnawa a gabanta ya bata baya almar ta hau tun da ta gaji da tafiya.

Da sauri ta haye bayan nasa ya mi?e da ita. Cigaba da tafiya ya yi ba tare da ya ce mata ko uppan ba, sai jero mashi tambayoyi ta rin?a yi kamar wata ?ar jarida. Shi kam sai tafiya yake yi cikin jarunta, jikinsa har tsuma yake yi saboda bala'in dake faruwa a cikin kingdom ?in. Wajen kusa da gate ?in suka nufa, sun kusa isa bakin gate ?in ya ce mata ta sauko bari ya yi wani abin, make mashi kafa?a ta yi tana fa?in. "Ni wlh tsoro nake ji ba zan iya saukowa ba sai ka mayar da ni cikin gida". Wannan ma bai sanar da ita abin da yake faruwa ba ta makalemashi wai tana jin tsoro, ina kuma ace ya gaya mata, ai ya shiga uku ko nan da nan ba zata yarda ya kara motsawa ba.

"Ranki ya da?e duba mana hanyar fita fa zanyi". Cikin wannan sanyayyar kuma dadda?ar voice ?in nasa ya yi maganar, kuma ?asa ?asa kamar mai jin tsoron yin maganar ya yi ta.

"Ni dai a'a muje koma inane a tare". Ta fa?a a shagwa?e. Sh dai Allah ya gani wannan shagwa?a tata tana kashe mashi jiki.

Lallashinta ya fara yi yana lalla?ata a kan ta sau?a yana son ya lalla?a a hankali ya le?a securitys dake wajen gate ?in suna nan ne ko dai sun nufi wajen sauran warriors dake cikin kingdom ?in?.

Kafewa ta yi taki yarda ta sau?o, shi kuma sauri yake yi saboda yadda busar yakin nan take tashi ta ko'ina ya ?aga mashi hankali sosai, hakan yasa ya damko hannunta tare da fisgota ya dawo da ita ta gabansa da nufin ya sauketa tun da ta baya ba zai iya sauketa ba ta ri?e mashi wuya, har sai idan ita ta sakesa zai iya sauketa, shiyasa ya dawo da ita ta gaba. Wani irin zaro mashi wa?an nan dara daran idanuwan nata ta yi, an kuma yi sa'a shima face ?in nata yake kallah, hakan yasa ya ji ba zai iya abin da ya yi niya ba, ?an kawar da kallonsa daga kanta ya yi yana bata hakuri. Hakika ta lura da cewa Hoorain baya son kallon cikin idonta, in dai tana kallonsa baya ta?a yarda ya kalli cikin nata idanun, kawar da kansa yake yi.

Modarawa sarakan zuciya sake shi ta yi tana ?o?arin sauka daga jikin nasa, ta yi fushi ne saboda ya yi yunkurin sauketa daga jikinsa ta karfin tsiya, bawan Allah bata san abin da yake gabansa ya fi wuta zafi ba, ba laifinsa bane, hankalinsa ne a matu?ar tashe, Abbonsa kawai yake tunawa, yasan yanzu yana can yana nemansa, idan aka fara yakin nan bai kai kansa ga mahaifinsa ya taimaka mashi ba baya jin zai iya yafewa kansa, yana cikin tashin hankali da tsaka mai wuya shiyasa ya yi mata hakan!.

Ganin alamar tayi fushi zata sauka daga jikin nasa ne yasa ya yi saurin ?an?ameta, har yanzu duk tashin hankali da yake ciki ba zaka ga hakan a kan face ?insa ba, cikin tausasawa ha?e da rarrashi ga voice ?asa ?asa ya ce. "Am so so sorryyyyyyy ranki ya da?e".

Bata yi mashi magana ba, hasali ma bata ?ago ta sake kallonsa ba, sai ?o?arin barin jikin nasa kawai take yi. Shi kuma yaki saketa sai bata hakuri yake yi, wlh sam taki kulasa, ashe ita ma tana da zuciya ta iya fushi. Ba yadda bai yi da ita a kan ta yi hakuri ba taki, ko magana ma bata sake yi mashi ba, dan gani take ma ya yi mata karshen wala?anci a duniya, dan ya samu ma ta hau bayansa saboda tsoro shi ne zai yi ?o?arin sauketa ta karfi? Lallai ba laifinsa bane, laifinta ne da take sakar mashi fuska. Baiwar Allah baki san shi ma ba laifinsa bane, tashin hankali ne ya kai tashin hankali shiyasa ya yi maki hakan, ita ma dan bata san me yake faruwa bane, da ta sani ba zata yi fushi da shi ba.

Bashi da za?in da ya wuce ya saketa ta sau?a, dan ta fara yi mashi kuka tana ture shi, ga shi taki ta yi magana, hakan yasa sai ya saketa kawai, dan baya son ganin kukanta. Yana sauketa ta nufi gate ?in kai tsaye zata fita.

Cikin zafin nama ya ri?o hannunta, dan kuwa idan ta fita sun shiga uku, zargine ma zai hau kansu sosai, za'a ce tun safe me suke yi a cikin goner su biyu kawai? A cikin gida kuma ba'a nemeta ba tun safen, saboda suna da parts dayawa, kowa zai yi tunanin tana wani part ?in ko tana wajen Mammiensu Sarina ko part na Aunty MieMie, shiyasa ba wanda ya ce ina take sai yanzu da abin nan ya faru aka fara nemanta.

Juyowa ta yi a fusace zata yi mashi magana sai gani ta yi yana ?o?arin zube gwiwowinsa a ?asa dan ya bata hakuri tun da taki yarda da kalaman bakinsa. Cikin sauri ta yi ?o?arin hana shi, sai dai kafin ta kaiga yin magana har ya aiwatar da hakan. A hanzarce ita ma ta zube nata gwiwon a ?asa tana fa?in. "Dan Allah ka yi hakuri ka tashi ka ji? Kuma ai ranar nace kada ka ?ara tsugunnawa ka bani hakuri ko?". Tana magana tana cigaba da hawayenta tun na ?azun da yaki sauketa.

"Sai kin amsa da kin ha?ura zan tashi". Ya fa?a yana kawar da kallonsa daga kan face ?inta, saboda kukan da take yi baya son gani.

"Na hakura Allah kuwa". Ta kai karshen maganar tare da fa?awa jikinsa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sanya hannunsa ?aya ya fara goge mata hawayen da yake jin zafin zubowarsu. Hannunta ta zura ta bayansa ta ?an rungumosa tana ?an shesshekar kuka............ Ni kam nace Auta yanzu fa kada ki manta kin fara girma sai a dai'na rungumar kowa, dan an fara zama ?an'matan.......????

Da yake hankalinsa duk yana wajen Abbonsa sai ya yi mata dabara suka mi?e tsaye, haka ya nufi bakin gate ?in ri?e da hannunta.

Kash an rufe gate ?in ta waje, da alama warriors dake wajen sun tafi cikin kingdom suma. Dafe kansa ya yi tare da fara tunanin ta yadda zai hau gini da ita a bayansa, dan dole ya nemo hanyar fita idan ba haka ba yana cikin bala'i ba ka?an ba, rashinsa ma zai iya sanyawa makiya su yi galaba a kan Abbonsa, domin kuwa idan har Abbo bai gansa ba zai shiga tashin hankalin da zai sa ba zai iya ta?u?a komai a filin yakin ba, hakan zai sanya makiya su iya kai mashi hari har su yi nasara, ya shiga tashin hankali iya tashin hankali bawan Allah.

A can cikin gida kuwa tsab aka ha?a kan maya?a sannan aka umarce masu ri?e da kwari da baka da su fara fita waje, dan a dokar kingdom of power basu yarda yaki ta zo cikin masarauta ta samesu, sai dai su su tunkareta su tareta a waje su gwabza, hakan kuwa aka yi suka tunkareta. Wasu tsirarun warriors da ba zasu wuci guda ?ari bane suka kukkunna wuta a jikin itace suka rufa masu baya da shi domin ganin haske yadda zasu ji da?in gwabza yakin da kyau. Sai dai abin da basu sani ba mayakan da suka kawo masu hari fa sun kewaye masarautar gabas da yamma kudu da arewa, kwantar ?auna suka yi masu, sun kasa kansu wajen kaso biyar duk dan cinwa burinsu....... Tashin hankali!!.

Mayakan commander Zafar kaso na farko da suka fara fitowa wato masu kwari da baka a can kusa da mayakan da suka kawo masu harin suka dakata, a nan commander ya umarcesu da su tsaya su kuma shirya yadda ya kamata, da yake ba yau suka fara yakin ba sai ya zamana sun jera kansu da kansu ba tare da wani ya basu umarni ba, sun yi tsayuwar mazajen gaske, kudai kun san duk wata jarumta to ta biyo bayan mayaka, baku jin ko kwatance za'ayi da namiji jarumi to da sadaukan yaki ake kwatantashi bane? Da mayaka ake kwatance dan an san sune jarumtarsu ta kai jarumta babu wani mix ko ka?an. Na?e kafafunsu suka yi tamkar wa?an da suka yi kneel down, sannan suka lankwashe kafa ?aya baya ya yin da suke ?ago kwari da bakarsu suna saitata yadda ya dace, ga dakaru masu ri?e da wuta a tsakiyarsu dan su samu haske. Daga cikin kingdom ?in ma fa akwai manya manyan makamai na kwari da baka wadda daga can za'a iya yi wa abokan hamayyar nasu ruwan kibau, kowani makami kuma yana iya ?aukar kifiya sama da ?ari, yanzu haka wasu maya?an suna ciki suna zubawa makamin kifitoyi sosai a cikinsa tare da jerasu da kyau ta yadda zasu ji da?in yi masu ruwan kibau.

Daga in da suke suna iya gani da kuma jiyo maganganun mayakan da suka kawo masu harin. Babban cikinsu ne ya ce da su. "Get ready is time to fight now, kuje!! Kada ku kuskura ku dawo ba tare da kun dawowa da Queen ZARINA spender ba, dole ku kwato mata shi domin ta yaki duniya!!".......... Tashin hankali, spender kuma?. To me ha?in King Zuhair da Spender? Dama yana wajensa ne ko yaya? Gaskiya akwai sarkakiya ha?e da cakwakiya!! Me ha?in kingdom of power da spender? To fah wata sabuwar cakwakiya kenan!!. Shi BLACK TIGER ya ce yana son ya kar?i Spender dan ya mulki duniya, ita kuma wannan QUEEN ZARINA ?in ko wacece ita? Kun ji ita kuma tana neman SPENDER ne dan ta yaki duniya, tab?ijam! To wai shin menene ma wannan Spender ?in? Ainahinsa mallakin wanenen? Sannan a yanzu takamaime yana hannun waye? Lallai akwai gagarumin matsala, akwai gagarumin rugugin aradu da cakwakiya mai matu?ar sarkakiya, KING ZUHAIR kuma da Spender?! Tab?ijam!!

Commander Zafar dake tsaye a tsakiyar warriors dake ri?e da kwari da bakan ne ya ?aga murya da karfi ya ce masu. "Ready!!". Nan take suka ja kifiya da karfi suna jiran umarninsa na gaba kuma. Commander dai duk hankalinsa wlh bata jikinsa, ?ansa ?aya tilo a duniya kawai yake tunawa, ya nemesa kamar hauka bai gansa ba, sai dai kasancewar bai ji fargaba ko fa?uwar gaba ba yasa ya ji a ransa koma a ina ?an nasa yake yana cikin ?oshin lafiya, sai dai damuwarsa ?aya, yasan halin ?ansa da zafin nama ha?e da tafasar jini ga zafin rai, sannan yasan shi da bakar kishi, yana kishin masarautar sun nan over, kuma yana matu?ar kaunarsa, amma ace ya ji an buga busoshin yaki kuma duk in da yake duk abin da yake yi bai bari ya hallara a gaban baban nasa ba? Kai abin da ?aure kai sosai, abin ya damu commander a cikin zuciyarsa, sai waige waige yake yi yana duba ta ina zai ga ?ullowan zakin nasa, hazikin jamumin mayaki abin alfaharin KINGDOM OF POWER!. Sai dai har yanzu shiru ko alamarsa bai gani ba.

Suma maya?an can ri?e suke da sandar wuta a hannayensu, hakan ya bawa su Commander damar ganinsu da kyau, da kallo ?aya commander ya yi masu ya gane daga wace masarauta suke, dan haka sai ya ?ara gayawa dakarunsu a kan irin kisan wala?anci zasu yi masu, sannan su ?ara jajircewa tare da fito da jarumtarsu su baje basirarsu a fili, dan wannan shi ne karo na uku kenan suna gwabza yaki da wannan masarauta, dole wannan karo su yi masu mai kankat.

Masarautar Queen Zarina hatsabibin masarauta ne wanda ya?arsa ba abu bane mai sauki, karfinsu kusan ?aya ne da kingdom of power ?in, amma su sun ha?a ne da karfin sihiri ba iya karfinsu bane kawai, shiyasa karfin nasu yake kusan ?aya da kingdom of power, duk fa?an da suka yi a baya sai dai su gwabza su gaji su hakura, ?aya baya cin galaba a kan ?aya..... Babban magana, akwai matsala fa, da alama KINGDOM OF QUEEN ZARINA nan wannan karon da gagarumin shiri suka taho, dan kunga unexpect suka kawowa su commander hari, idan har basu yi gagarumin shiri ba kunga ba zasu fara ba, dan sun ta?a yakin ai, kowanne yasan karfin ?an uwansa, dan su gwabza a baya sosai!!.

A saman dawakai gaba?aya mayakan masarautar Queen Zarina suke, hakan yasa commandersu suma yana ce masu ku afka suka ka?a kan dawakan nasu suka nufo su commander Zafar da gudun gaske. Habawa shi kuma commander da karfi ya ?aga murya ya furta. "Fire!!". A ?ari dangerous warriors suka kara jan kifiyoyinsu kan kace me sai ganin ruwan kifiyoyi suna shawagi a sararin samaniya, commander yasa sun saki wuta....................

To fa babban aiki. Ina Chuchu and Jawad? Sun koma cikin gida ko yaya? King ya fito kuwa? Babban tashin hankalin ma shi ne, Uncle Jahiz, Yah Rizwan, Guyson suna hanyar dawowa, daga yanzu izuwa kowani lokaci jirginsu zai iya sauka, tashin hankali! Zasu shigo su tadda yakin da basu san da shi ba, fatan mu dai Allah yasa kada su yi wannan mummunar gamon, Allah yasa wani abin ya ri?esu a airport har izuwa a gama yakin, dan ba da shirin yaki suka fito ba.

Ga shi a yanzu yadda ake cikin tashin hankalin nan duk cikin family ba wanda yake da nutsuwar tunawa da su bare har ya kirasu a waya ya ce kada su nufo gida ana yaki, yanzu hankalin kowa a tashe yake, Innalillahi wainna ilaihir rajuun akwai matsala babba kuwa! Ya su Auta zasu yi su fito? Idan sun fito zai iya kaita a cikin family part kuwa? Yana da kwarin gwiwar yin hakan kuwa? Zasu rayu ma tukun nan? Dan dai kunga mayakan can sun kewaye ko'ina na kingdom ?in ba tare da su King sun sani na, shigar dare suka yi masu, da alama kuma sai da suka kewaye ko'ina suka gama shirinsu kafin su busa masu busar isar da sa?on ga mayaka sun kawo masu hari, idan Auta ta samu ta koma cikin gida ya za'ayi ta gane ?an uwanta suna part na ?ar?ashin ?asa an ?oyesu? Akwai matsala babba, shin su Mummy zasu rayu kuwa? Dan kunga an kewayesu ta ko'ina!! To ni dai bari na le?a wani wajen na dawo daga baya in ?auko maku rahoton me ya faru a wannan yakin!!.

_______________________??????

JIMETA.................NIGERIA.

Sosai ya ci namar nan kamar ba gobe, dan ya ji yunwa sosai matu?a, sai kallonsa suke yi, tsananin tausayinsa ne cike fal a ran bappa, bayan ya ci ya ji cikinsa ya ?auka ne ya mi?e ya kwanta a wajen, saboda yadda cikinsa yake tsananin mur?a mashi, dan ya jima bai sanyawa cikin nasa komai ba, dole dama ta yi mashi ciwo. Bappa ne ya ce mashi ya tashi ya hau gado cikin harshen fillanci. Sam bai gane me suka fa?a ba, in takaice maku labarima shi Jaish yana jin duk abin da suke fa?a duk da bai san wani yare ko me suke nufi a kalaman nasu ba, amma bai kurmance ba yana jinsu, yaren ne kawai bai sani ba.

Da bappa ya lura da yana jinsu magana ce baya yi ko baya son amsa masu, sai ya yi tunanin ko dai tun ainahi dama bebene?.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull