Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 36
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 36: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 36. Mahreen dake zaune shiru ne ta ce. "Aljanina cikinka ne yake ciwo?". A yanzu…
3,353 words
Mahreen dake zaune shiru ne ta ce. "Aljanina cikinka ne yake ciwo?". A yanzu Mahreen tana tsoron ta?a shi, yi mashi magana ma a yanzu tana jin shakkar hakan, sosai take shakkarsa, kuma kunsan yadda ta yi shiru har ya gama cin namar bata ce zata bashi namar a baki ko kuma ta ce su ci tare ba ai daga nan zaku gane lallai tana shakkarsa ko ma tsoronsa.
Jin maganar Mahreen ?in yasa ya ?aga idanu ya kalleta ba tare da ya yi magana ba, hasalima bai san me ta fa?a ba, kawai dai ya ?ago ya kalleta ne. Bappa ne ya ce mata. "Mahreen aljaninki baya magana, ina tunanin shi ?in bebene". ?an zaro idanu ta yi tare da cewa. "Bappa shikenan shi haka zai zauna?". Kai bappan ya gya?a mata alamar e.
Marairace fuska tayi tamkar zata rushe mashi da kuka ta furta. "Allah sarki ya bani tausayi, yanzu kowa yana magana ban da shi? To bappa ka samun mashi magani mana, dan dai ni ina son jin ya muryar aljanu suke?".
Mahnoor dake tsakar gida tana zaune ta buga uban tagumi tana jiyosu ne ta ?an ta?e baki tana mamakin hali irin na Mahreen, yarinya ne baka ta?a gane mata, bata san cewa ita kanta aljana bace ba iya Jaish ba, in za'a cewa Jaish aljana to tabbas ita kam itace sarkin aljanu, ban da nemanwa kai masifa me na yi wa kai fatan jin sautin muryan aljani fisabilillah? Tana zaune ?alau zata jazawa kanta masifa, ai idan tana son jin muryan aljani sai ta saurari nata muryan, dan ita ma aljana aljana mutun mutun ce.
"Mahreen ban tabbatar da cewa yana magana ko baya yi ba bare na bashi magani, amma bari na gwada mugani ko zai iya amsa maganata". Cewar bappan. Ya yi maganar tare da matsowa kusa da shi sosai.
?an zuba mashi idanu sosai ya yi yana kallonsa yadda yake kwance ya datse idanu gam, shi kansa bappan a yanzu ya fahimci dalilan da yasa dole a kirasa da aljani, wani irin shape mai bala'in kyau face ?insa take da shi, hancinsa ta zauna ta kuma tsaru dai'dai da face ?insa, ga gurbin idanunsa da girma, duk da idanun suke a rufe zaka iya gane cewa manya manya ne sosai, ?an bakin nan nasa ba'a magana sai dai shiru, dole mutane su kirashi da aljani, shi ma yanzu ya ?an ji wani irin yanayi a tattare da shi daya kurawa face ?insa idanu, da duk bai lura da hakan ba. Amma sai ya yi shiru bai ce komai dan gane da kyansa ba, ya dai matso kusa da kunnensa a ina ya fara yi mashi magana da fullanci a kan cewa ya dubi girman Allah kada ya wahalar da su ya sanar da su idan yana iya yin magana ko kuma idan yana jinsu.
Sarai ya ji sun yi magana amma bai san me suka ce ba, dan haka sai bai motsa daga in da yake ba, shiru bappa ya yi yana tunani, da yake tattijon kirki ne ga tunani mai nisa, sai ya yi tunanin to taya ma za'ayi Jaish ya ji fulatanci tun da shi ba a ruga yake ba, ?an cikin rugarma gudunsa suke yi hakan ya nuna bashi da wata ala?a da fulani, duk yadda aka yi shi ?in ?aya daga cikin biyu nan ne, wato ko bature ko balarabe, hakan yasa bappan da ya tuna hakan sai ya sake matsowa kusa da kunnensa cikin dattaku ya ce mashi. "Kanajin larabci?". Cikin harshen larabcin ya yi mashi magana.
A hankali ya ?an motsa idanunsa kafin ya warosu a hankali izuwa kan face ?in bappan! Sake mayar da su ya yi ya datsesu ba tare da ya ce ko uppan ba. Bappan ya lura da cewa tabbas yana jin larabci, dan tun da suka yi ta yi mashi magana bai motsa ba sai da suka yi mashi larabci, hakan na nufin yana ji sai dai kamar ba zai iya bu?e baki ya yi magana ba.
Sake ce mashi bappan ya yi. "Dan girman Allah idan har kana jin larabcin ka nuna mana alamar hakan ko ka amsa mana, dan Allah kada ka wahalar da mu ka ji?".
Shiru ya yi nan ma bai motsa ba, sai dai tsab ya ji me bappan ya ce. Ya ?auki a kallah tsawon 2mins har bappa ya cire ran zai tanka masu, yama cire rai a kan yana iya magana, sai kuma ya ga ya ?an bu?e idanu ka?an tare da gya?a mashi kai alamar e yana jin larabcin, amma bai bu?i baki ya yi magana. Wani irin da?i na musamman bappan ya fara ji na ganin cewa an samo yaren da bakon nasa yake ji, abin ya yi mashi da?i sosai, bai damu da rashin amsa mashi da bakinsa da bai yi ba, saboda dama yana son ya san cewa bakon nasa yana jinsu shi ne burinsa, dan ko baya magana in dai yana jinsu to Alhdulillah zai iya yi mashi bayani kuma su fahimci juna, dan shi yana da baiwar iya yin magana da kurame, ya iya maganarsu da ?atsun hannunsa, dan haka bashi da damuwa a kan wannan!!.
Gyara zama da kyau bappan ya yi a in da ya shiga yi mashi bayanin halin da yake ciki da abin da ya faru da shi na tsintarsa a cikin ruwa da suka yi, ya yi mashi hakan ne kuma dan ya samu Jaish ?in ya saki jiki da su ya san su ba cutar da shi zasu yi ba, dan ya fahimci sarai Jaish ?in yana gudunsu, bai kawowa ransa cewa saboda kyamarsu yake ji yasa yake gudunsu ba, ya ?auka saboda yana tsoron kada su cutar da shi ne yasa yake guduwa! Basu san dalilinsa daban ba, ai duk yaran King Zuhair babu matsoraci a cikinsu bare ace yana jin tsoronsu kada su cutar da shi ne!.
Duk abin da bappan ya fa?a yana jinsa sarai, ya ji dukkanin bayanansa, sai dai sam bai motsa daga in da yake ba, sai ka yi zaton bai ji me aka ce ba. Mahreen dai ta ji bappanta yana wani yare daban da bata ta?a ji ba, sai ta zaro idanu tana kallonsa. Bayan ya gama yi wa Jaish bayani ne ta ce. "Bappana dama kaima ka iya yaren aljanu ne?".
Kai kawai ya gya?a mata alamar e. "To bappa dan Allah ka koya mun, kaga dai shi ?in aljanina ne, zan rin?a yin magana da shi". Shiru ya ?an yi mata kafin ya ce. "Ba shi ne idan nace ki nutsu ki karanta NAHHU a islamiya zaki iya larabci sosai sai ki ce mun yana da wahala Nahhu nawa hore ba? (Nahhu ciwon kai take cewa) To ai a cikin Nahhu nima na koyi yarensu". Da sauri ta ?ara zaro idanu waje. "Bappa kenan aljanu yarensu shi ne larabci?".
Girgiza kai ya yi. "Larabci yaren kowa ne, aljanun gaske ma akwai masu jinsa kuma suna magana da shi, yaren annabinmu ne, da shi za'ayi magana a lahira". Shiru ta yi kamar mai nazari a kan maganganun bappan nata, can kuma ta ce. "Bappa daga yau zan fara koyan yaren, kuma zan fara karatun Nahhu har da mu?alaa da malumat, duk zan rin?a karatunsu, kaima ka rin?a ?ara mun da naka karatun a gida yadda zan iya yaren sosai". Jinjina mata kai ya yi alamar to shikenan babu damuwa. Ita dai Mahnoor tana jin larabci dai'dai gwargwado, dan tana mayar da hankalinta sosai a kan karatun islamiyar, bata wasa da shi haka zalika bata fashin zuwa sai idan bappan nasu ya yi tafiya, in baya nan bala'in Nenne yake hanata zuwa, sai ta yi ta sanyata aiki har lokaci ya ?ure bata samun zuwa, amma idan bappansu yana nan lafiya lou take zuwa, sai dai fa bappan idan ya tafi yana kai irin wata biyar haka bai dawo ba, idan kuma ya dawo baya wuce yin wata uku zuwa hu?u ya sake tafiya, bappa yana jin yaruka da ?an dama, ciki har da yarabanci, dan yana zuwa har kudu a wajen yawonsa, yana jin broken English sosai, haka yaren ibo sosai, yana jin Hausa sosai, yana da baiwa ta iya yarika daban daban, kun san mutun mai yawo irin haka ba yaren da ba zai iya ba, sannan kun san akwai fulani irin bappa sosai masu yawan fita yawata ?asashe da dabbobinsu, wani lokaci ma idan suka bar gida sai sufi shekaru 2 basu dawo ba, sai ka manta da su ma rana tsaka sai kaga kiwo ya juyo da su ta wajenku kwatsam sai ka gansu, kamar wasu aljanu ta bakin Mahreen ?in. Sai dai shi bappa baya jimawa sosai, idan ya yi nisa ne wata biyar, ko dan saboda Mahnoor yana dawowa gida!.
Kuma sanadiyar wannan kiwon da yake tafiya wurare daban daban Allah ya albarkace shi da samun shanu dayawa gasu suna ?oshe ?ul ?ul sosai gwanin ban sha'awa.
In short wannan labarin da bappa ya bawa Jaish ne yasa shi ya ?an yi sanyi ya kuma daure ya dai'na nuna masu cewa yana kyamarsu, dan kuwa jinin King wlh basu manta alkhari ko mai ?an?antar idan aka yi masu, haka zalika komai ?an?antar sharri idan ka yi masu basa mantuwa, kar suke ba wata kwana kwana, yanzu yasan bappa ya taimakesa sosai, dan haka sai shi ma ya kudurta a ransa zai yi ?o?arin dai'na nuna masu kyama ya kaunacesu.
In short sai da ya shafi wata biyu dai'dai a tare da su kafin ya fara sakin jiki da su, a wata biyun da suka shu?en sam baya yarda ya yi kusa da su, dan kada ya yi amai a gabansu su ji babu da?i, baya son ya ?untata masu hakan yasa yake daurewa yana dannewa ya kawar da kai, haka zalika bai ta?a yin magana ba a tsawon wata biyun nan, sai dai bappa ya yi mashi magana kuma yana jinsu, ko meyasa baya amsa masu?.
Mahreen ta zage sai koyan larabci take yi dan ta rin?a hira da shi, bata san shi kam ba abin da ya tsana a rayuwarsa kamar surutu ba, ita kuma Mahnoor har yau har gobe ita da Nenne suna tsoronsa, sai dai Nenne ta fi jin tsoronsa sosai, Mahnoor tsoron ya ragu, ba komai kuma yasa ta rage tsoronsa ba face muguntar Nenne, Nennen tana yawan aikanta cikin ?akin na bappa dan tsabar mugunta, tana jin tsoronsa shi ne take aikata wai dan kawai taga Mahnoor ?in tana zubar da kwallah, da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai yasa Mahnoor ?in ta fara sabawa da shi, ta rage jin tsoronsa, yanzu ta san ba cutar da su zai yi ba, dan a koda yaushe idan ta shigo ?akin bappan ma har ta ?auki abin da zata ?auka ta fito yana kwance ko kallon in da take bayani, yana dai jin motsin shigowarta a koda yaushe, baya ?agowa ne ya kalli wace? Kun dai san halinsa dama, akwai miskilanci da shege izza. Amma fa har yanzu a matsayin aljani yake a idanunta, ta ?asa yarda cewa mutun ne!!.
Har yau har gobe wannan kunyan na Jaish tana tare da shi, wlh baya ta?a yarda ya ha?a idanu da bappa sai idan by mistake, amma kunyar ha?a idanu da bappan yake yi, tsawon wata biyu suna kwana a ?aki ?aya amma baya yarda su ha?a idanu, kunya gareshi sosai, halittarsa ce a haka. Sarai bappa ya lura da cewa yana da kunya sosai, hakan bai yi mashi da?i sosai ba, saboda yaso ya saki jiki da shi su saba sosai, amma ina kunya ta hana shi, ga rashin yin magana da yake fama da shi, lokacin da ya samu lafiya sosai tsakaninsa da bappan ya bashi hannu kawai su gaisa, shikenan ko hira bappa yake yi mashi baya cewa ko uppan ko kuma ya nuna alamar ya ji me bappan ya ce.
Mahreen tana shakkarsa sosai, bata yi mashi magana idan bappa baya nan, yanzu ta ja baya da shi dan tun ranar da ta shigo ta same shi babu riga a jikinsa saboda zafi da ta kusa haukata shi bawan Allah abin da bai ta?a ji ba bai saba ba, da zafin ta isheshi ne ya cire riga, to tun da ta shigo ta same shi a haka ta fita a guje daga ranar ta ja baya sosai da shi, tsoron shi ma take ji dan taga kirar karfi.
?an kauye har cincirindon suke yi suna zuwa le?ensa idan bappa ya tafi kiwo, dan izuwa yanzu labari ya baza ko'ina a kauye cewa akwai wani aljani kyakkyawan gaske a cikin gidansu Mahnoor, hakan yasa ake zuwa le?ansa, shi kuwa yana kwance yana ganin masu zuwa le?an nasa. Ita kuwa Nenne bata ta?a yarda ta wuni a gidan saboda shi ?in, dan taki yarda cewa mutun ne har yanzu, tuni ta je ta kai wa gwaggonta labarinsa, tsabar mugunta irin na gwaggon sai ta ce ai wlh kada ta bar Mahnoor ta huta, lallai dole ta rin?a turata wajensa yana bata tsoro dan su kuntata mata........ ?an adam kenan, ko me ribarsu idan sun ?untata wa baiwar Allah? Allah kasa mu fi karfin zuciyarmu, dan wannan duk ka?an ne daga sharrin zuciya idan ka yi sake tafi karfinka, duk bala'in da za'ayi gara ka yi gwagwarmaya ka fi karfin zuciyarka, hakance kawai zata sanya ka ji da?i duniya da lahira.
Yau ma kamar kullum duk sun tafi kiwo, sun bi bappa, Nenne da ta dawo wuni gidan Ar?o bata nan, ta wuce gidan Ar?on, a gidan take zama sai yamma idan bappa ya dawo daga kiwo sai ita ma ta dawo. Kamar kullum Jaish ?in ka?ai suka bari a gida yana kwance, ya ta?a zuwa wajen ciwo bappan sau ?aya, lokacin tun bai jima sosai da su ba, bai wuce sati 2 da su ba lokacin, daga nan bai sake zuwa ba, saboda aman da ya rin?a yi kamar zai mutu, wai wajen akwai datti, hakan yasa bappa ya fahimci yana da kyakkyani sosai, shi ne yasa bai sake yarda ya bisu ba, gara su bar shi a gida kada kyama ta yi mashi illar.
Gajiya ya yi da kwamciyar da yake, hakan yasa ya mi?e tsaye, yau yana sanye cikin kayan fulani da bappa ya saya mashi, har yau ya kasa iya bu?e baki ya yi magana, yana jin duk abin da suke fa?a kuma, maganarce dai shiru har yau. Waje ya nufa, kayan fulanin sun yi mashi kyau sosai, saboda launin navy blue ne ba farar ba, kasancewar yana da hasken fata sosai sai kayan suka yi mashi kyau sosai. Waje ya nufo, cikin nutsuwa yake tafiya. Wasu takalmar bappa dake bakin kofa ya sanya a kafafunsa, takalmar sun yi mashi yawa ka?an, amma haka yasa ya nufi hanyar fita daga gidan.
Ya subhanallah, ai yana fitowa waje gaba?aya matasan da suke yawan zama a ?ar?ashin bishiyar dake kofar gidan suka watse da gudu, dan tsoronsa.
Ko kallon in da suke bai yi ba yasa kai ya nufi hanyar wajen kiwon su bappa, sau ?aya ya ta?a zuwa amma saboda kaifin ?wa?walwarsa bai manta hanyar ba.
A kan hanyarsa na tafiya ya ha?u da Mahreen and Mahnoor sun ?ebo itace zasu koma gida Mahnoor ta yi masu abinci, ita kuma Mahreen ta tayata da ?an aikace aikace, idan sun gama girki sun ci sun ?oshi sai su ?auki na bappa su koma mashi da shi wajen, su taya shi hira har zuwa lokacin tafiya islamiyya su dawo gida, kafin a tashi islamiyyar kuma bappa ya dawo gida, haka suke yi yanzu tun da Jaish ya zo, Nenne ta dai'na zama a gida bare ta yi girkin rana, dama ita take yin na rana idan bappa yana nan, zata yi na rana ta kai masu wajen kiwo, Mahnoor kuma zata yi na safe da dare ha?e da sauran aikace aikace!.
Kallo ?aya ya yi masu ya kawar da kansa, dan ya ganesu, ?an gidansu ne. (Yanzu sun zama ?an gida ?aya kuma jini ?aya?? Allah sarki Prince Jaish namu na amana??)
Mahnoor ce ta ce mashi ina wuni da larabci. Mahreen kuwa duk da tana shakkarsa bai hana ta ce mashi. "Aljani ina zaka je? Kasan hanya ne? Ko dai garinku na aljanu zaka koma?". Da fulatanci ta yi maganar, dan har yanzu ba'a ?arisa iya larabcin ba.
Cigaba da tafiyarsa ya yi har ya ?urewa ganinsu, su kuma tsayuwa Mahreen ta yi tana ganinsa har ya wuce, ita Mahnoor dan dole ta tsaya tana jiran Mahreen ta gama kallonsa, dan tasan ko ta ce mata ta zo su tafi ba zata zo ba har sai ya wuce, dan haka sai ta tsaya kallonsu kawai.
Sai da ya kure masu ne Mahreeh ta juyo suka cigaba da tafiya tana fa?in. "Aljanin nan ban san yaushe zai fara yin magana ba, bappa kuma ya ce shi ba kurma bane, amma ya ki ya yi magana".
Shiru Mahnoor ta yi mata bata amsa taba, dan tasan in ta biye mata zasu kwana su wuni Mahreen tana sanyata magana, ba zata kyaleka ba............
Kai tsaye wajen bappa Jaish ya nufa.............
____________________??????
SMART TIGER.
Sai da ya sha daidai cikinsa ya ajiye cup ?in, sannan ne ya mi?e ya nufi stair case. Haurawa hawa na sama mai gaba?aya ya yi, yana sanya kafarsa a saman wani ha?a??en white Tiger ya yi kansa da gudu, irin foreas Tiger nan ne, ya ji kiwo ya ?oshi sosai, ga shi fari tas da shi, idanunsa ba kamar na sauran damisoshi da kuka sani bane, na shi ligh blue ne, kun san dama su haka idanunsu yake. Tiger ta yi kyau sosai ba karya.
Rungumar damisan ya yi yana shafa jikinsa, saman gaba?aya grass carpet ne a wajen, a nan damisan yake yin rayuwarsa, bai cika fita da shi ba kuma bai cika barinsa ya sau?a ?asa harabar gidan ba, time to time dai yana sau?a da shi zuwa harabar gidan, amma fa ?aki ?aya suke kwana, da daddare idan har zai kwana a gidan, idan kuma ya koma gidansu to a sama Tiger yake kwana.
Da kyar damisan ya yarda ya sake shi suka ?arisa cikin fillin, akwai pool mai girma a saman, sannan akwai Librarynsa na karatu a wajen mai shake da litattafai daban daban a ciki, sai wajen hutawa dake gefe mai shake da kayan alatu iri iri dan more da?in rayuwa.
Kai tsaye wajen hutawarsa ya nufa, wajen an kewaye shi da transparent glass, sannan an ?awata shi da luxurious furnitures masu ?aukar hankali, wajen dai ya tsaru iya tsaruwa.
Wani ha?a??en laptop MJ SWAROVSKI ne a saman center table dake tsakiyar kujerun. A kallah ku?in wannan laptop ?in ya kai dala miliyan uku da rabi, biliyoyin ku?i ake magana.
Daga ganin laptop ?in a ido ma kawai kasan ta ci ku?inta. Yana zama ya jawo laptop ?in, Tigersa kuma ya kwanta a kusa da shi........... One thing about him, shi fa bisa ?aida sannan ta halattacciyar hanya yake ha?a makamansa, kowace ?asa tana iya nemanwa kanta abin da zata iya kare kanta da shi idan aka zo yakarsu su iya kare kansu. Ga shi kuma ya ci karo da tsawon shekaru familynsa ke mulkar ?asar.
Yana da ilimin addini sosai, mahaddacin Alqur'ani ne, yasan duk wasu dokokin Allah dan haka ba zai yi abin da ya sa?awa Allah ba, yana da kula da taka tsantsan, ya riki addininsa da muhimmanci fiye da tunaninku, a kan addininsa ma yana iya sadaukar da ransa. Nasan yanzu zaku yi matu?ar mamakin jin cewa mahaddaci ne shi ?in bayan kuma kun san iyayensa christians ne, to ku saurara kuji labarinsa.
Daddynsa d............. Na manta sai typing nake na bako long page sosai, dole na dakata a nan.??
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 15/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
E22