Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 37
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 37: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 37. Daddynsa dai musulmi ne cikakken mahaddacin Alqur'anin mai girma, ya yi wa…
3,332 words
Daddynsa dai musulmi ne cikakken mahaddacin Alqur'anin mai girma, ya yi wa addini hidima da karfinsa da kuma dukiyarsa, kusan halinsu ?aya da Smart ?in, mum ce taki musulunta, tana da kirki da farar zuciya sosai, kuma tana balain kaunar ?an nata da mijinta, kawai musulunta ne ba zata yi ba, gaba?aya familyn nasu christian ne, amma shi da dad ?in ranar jumma'a tun karfe 10 suke masallaci har izuwa 1:30 ayi sallar jumma'a, suna sauraro hu?ubar liman, kun san manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce duk wanda ya riga liman zuwa masallacin jumma'a ya zauna yana addu'oi ha?e da kararun Alqur'anin mai girma har liman yazo su yi sallah, kuma ya saurari hu?uba, to kamar yadda jariri yake zuwa duniya babu zunubin ko miskala zarratin to haka wannan bawa zai zama kafin ya fita daga cikin masallacin nan, Ubangiji ya shafe komai na daga laifukan da ya yi a baya, haba ?an uwa me kuke jira, ai duk abin da kuke yi ranar jumma'a kam a daure a bada awa uku zuwa hu?un nan domin samun wannan gara?asa.
To shi dai Smart and dad musulmai ne cikakku masu kaunar Allah da Manzonsa, kuma dan mum taki musulunta bai sa basu zaman da?i ba, zaman farinciki sosai suke yi, kullum basu gajiya da yi mata nasiha da nuna mata girman Allah dan ta musulunta........ Fatana dai Allah yasa tana da rabon musuluntar.
Ya ?an ?auki lokaci ka?an yana latsa laptop ?in nasa kafin daga bisani ya kashe laptop ?in ya mi?e tsaye. Kai tsaye ha?a??iyar bedroom ?insa ya nufa. Wanka ya sake yi ya fito........... (Wai ni kam my people's ba Smart ?in nan aka kira a waya a kan roket ta kwace masu ba? Ga shi ba'a gama ha?ata ba bare a shigar mata da control ?? amma yana zaune ko a jikinsa?? da alama guy ?in nan zai azabtar da ni ?? ka ji mun ?an abin da babana ya hanani fa?a.)
Shiri ya tsake yi cikin ?ananan kaya, ko da ya gama shiri ya dawo cikin room ?in sai ya isko Tigersa kwance a kan gadonsa, a takaice ya ce mashi ya tafi. Da farko damisan ya so binsa, hana shi ya yi ya ?auki wayarsa kawai ya fito waje, sai gurnanni damisan yake yi amma bai kula shi ba ya wuce kawai.
Wani irin ha?a??en mota ya ?auko ba wanda suka zo da shi ba, wannan mota da ya ?auko motace mai tu?a kanta da kanta, ba sai ka wahala wajen tu?ata ba, da zarar ka shigar mata da location ?in in da zaka je a map ?inta zata bi komai a sannu ta kaika in da ka bu?ata, idan gudunta bai yi maka ba kana da damar cewa ta ?ara gudu kuma zata ?ara sosai, haka zalika idan kana son ta kara gudun Ac ma zata kara maka, abin dai ba'a magana, shegiyar tsada ce da motar nan fiye da tunanin ku, billions of dollars ne. (Kun san ni bana son kiran sunan ku?in abubuwan dan kada mu sume da jin ku?insu?? wlh ban san meyasa ba ban son fa?an ku?in duk abin da na rubuta?? ya fi mun in ce yana da tsada kawai, kuma wlh ku?insu na gaskiya ne, kiran ne kawai ban son yi.)
To billions of dollars motar nan take, ta ha?u ta gaji da ha?uwa, ita ya ?auko ya shiga, gidan baya ya shiga, kai tsaye ya shigarwa motar in da yake son zuwa. Securitys ?insa sun so su raka shi ya hanasu, dama dan kada ya rin?a yawo da kowa a bayan idanun daddynsa ne yasa ya sayi wannan motar, sannan baya son driving da kansa, kunga a saukake motar zata kaisa in da yake da bu?ata.
Haka shi ka?ai ya bar gida, duk wannan uban tsaro da dad ya ha?a mashi kullum a nan yake zuwa ya jibgesu ya yi fitarsa shi ka?ai, dad yana can ya saki baki a kan ya bawa ?ansa tsaro na musamman, bai san jibge tsaron ?an nasa yake yi a gida ya yi fitarsa shi ka?ai ba...........
Kai tsaye bayan gari ya nufa, wato daji kenan, gaba?aya wajen ?an?anra ne, ice palace kenan, motar tasa ma ba dan ta amsa sunanta mota ba bata isa ta keta wannan hanya ba, wajen akwai sanyi sosai da sosai, dusar ?an?ara sai zuba take yi kamar ruwan sama.
Ya yi tafiya mai nisa a cikin ?an?aran nan kafin ya dakatar da motar, sannan ya ?auko wani jibgegen jacket mai bala'in kyau ya sanya a jikinsa, dan ba karya akwai sanyi kam, komai sabonka da sanyin ?asar idan kazo wannan wajen sai ka ha?awa kanka kayan sanyi ko kuma sanyi ya busar da kai. Already dama kun san ?asar France ba dai sanyi ba, suna da ita sosai, to amma dole wajen da za'a ha?a boma bomai irin wa?an nan ya kasance da sanyi, shiyasa suka nemi in da yake da matu?ar sanyi, dan idan baku manta ba nuclear bom's fa wuta ne, wuta kam mai rai da lafiya ma kuwa, kunga dole a nemi waje mai sanyi domin ha?a su, idan ba haka ba in waje mai zafi ne sai ma'aikatan su yi ta mutuwa, zafin sai ya yi masu illah over, kai bama zai yiwu a waje mai zafi bane.
Fitowa daga cikin motar ya yi bayan ya sanya jacket ?in, nufa kofar shiga underground ?in ya yi.............. Kana sako kafarka a cikin wannan katafaren wajen nasu gaba?aya warin chimical na ha?a nuclear bom's irin su, Uranium-235 U-235, Plutonium-239, Pu-239, Deuterium D2, Tritium T2, Lithium-6 Li-6 zaka ci karo. Dukkansu is for atomic Bombs Fission, gaba?aya wajen idan baku saba ba kuka shiga sai mutun ya mutu har lahira, cikin tamkar engine bread, saboda zafi, ga wasu chimical ?in yadda suke tafarfasa kamar wuta, kai abin dai sai wanda ya gani.
Yana sanya kafarsa a wajen wani katon ?osasshen bature fari tas mai rai da lafiya dake tsaye a wajen bakin kofar shiga ya yi hanzarin ?auko mashi wani irin riga mai ?an tsawo zuwa gwiwowinsa da kuma face mask and katon glass mai haske. Sanya rigar a saman kayan jikinsa ya yi tare da ?ar?ar glass ?in ha?e da mask ?in ya sanya a face dinsa.
Yana yin tsarin wajen fili ne mai matu?ar tsaro wadda wane mutun ya iya gane me ake yi a wajen, duk munarfurci wata ?asa bata isa ta iya gane abin da ake yi a wajen shagon ba, ga wajen underground, sannan ga uban tsaro da aka yi amfani da na'urori wajen sanya mata mahaukatan mata?an tsaro na ban mamaki.
Wasu irin jiga jigan fararen turawa ne birjik a cikin wajen, kowanne da aikin da yake yi, yadda kuka san wani irin katafaren Company ne a wajen, ko da yake wannan ya ci uban company ma, dollars suna kuka a wajen nan, dan ana cin uban ku?i kam, ku?in da ake zubawa a wajen nan wane budget ?in Nigeria.
Gaba?aya cikin wajen tiles ne a kasan floor, ga wasu irin engines masu matu?ar girma, side da suke ha?a chemicals kala kala har su sarrafa shi su mai da shi wuta filin ?an adam bai isa ya tunkara ba idan ba aikinsa bane, daga jefe guda ga wasu irin na'urori wanda da wuya ka iya samun irinsu a ko wace iriyar ?asa, dan kuwa Smart shi ya kyara kayansa, a cikin wajen ta can gefe akwai wani part da aka ware na daban, system ne birjik a wajen, duk wasu irin nau'in abin da ya shafi system irin su laptop, desktop computer, kai duk dai abin da ya shafi system akwai shi a wannan wajen
Duk in da ya sanya kafarsa zai wuce sai wa?an nan jaruman ma'aikatan nasa sun bar abin da suke yi sun ?aga hannu sun sara mashi.
Kai tsaye wajen system ?in ya nufa, har ya kai tsakiyar wajen sai kuma ya juyo ya nufi wajen chemicals ?in da suka ha?asu cikin wani irin jibgegen engine da yake bu?e kamar baf, a nan suke zuba chemicals ?in sai engine ya yi masu mixing ?insa, sai ya ha?u sosai kafin su tura shi izuwa wajen da zai narkasu kuma.
Ma'aikata sama da guda biyar ne tsaye a gaban chemicals ?in suna aikinsu, yana dososu suka bu?a mashi hanya tare da ?aga hannu suka sara mashi. ?aya daga cikinsu ne ya yi hanzarin ?auko hand gloves ya sanya mashi a hannunsa, ?urawa chemical ?in idanu ya yi na ?an sakanni. Chemicals ne irinsu Deuterium-Tritium D-T, Fusion fuel, Lithium Deuteride LiD. Slowly ya dawo da kallonsa a kan ma'aikatan nasa, shiru ya yi yana kallonsu kamar ba zai yi magana ba, can sai kuma ya ce. "This chemicals is it not for Hydrogen Bombs?".
A hanzarce suka amsa mashi da e sune cikin girmamawa. Juyawa ya yi ya nufi wajen systems ?in nan. Binshi da kallon mamaki suka yi, kai guy ?in nan ba dai ?wa?walwa ba, an caku?e chemicals ?in waje guda ma amma ya iya tantance na wani irin nuclear bom ne, kuma chemicals ?in kusan kala ?aya suke a kamanni, amma a haka yana iya tace kowanne koda kuwa zasu ha?a da na nau'in boma bomai daban daban su caku?a ba'a gabansa ba yana zuwa kallo ?aya zai yi masu ya ce masu ya suka ha?a na kaza da kaza? Tun suna mamakinsa har sun hakurar da zuciyarsu sun dai'na, dan sun gane baiwa ce daga Allah ke garesa.
Yana isa wajen systems ?in wani katon bature mai rai da lafiya a hanzarce ya cire mashi hand gloves da wa?an can suka sanya nashi, bayan ya cire sai ya cire mashi glass dake face ?insa ma, wani wajen ya nufa dan ya je ya ajiyesu, shi kuma Smart ?in wata black glass ya ?auko daga cikin drawers da wasu daga cikin nau'i na laptop suke ?aure a kai. Sanya glass ?in ya yi tare da shiga cikin na'urar da kyau ya fara ?o?arin control na nuclears da suka tattasa sama ?asun dan gwaji, harta nuclear da ya kwacewa ma'aikatan nasa ma ya iya sarrafata, saboda already ya shigar mata da control su ne basu sani ba, dama ?azun lokacin da yake gidansa ma'aikatar nasa sun gwada wasu nuclears abin da ya duba kenan a laptop ?insa da ya ?auka a lokacin da ya haura sama a gidansa, to information da ya samu kenan shiyasa ya taso ya zo wajen dan ya ga ya nasarar aikin ya yake da idanunsa.
Abin da kuma masu karatu baku sani ba, idan baku manta ba na ce maku yana da aikinsa na daban, to shi ?in jami'in Secret Intelligence Service, the most powerful Jami'an sirrine in the whole kasar France, haka zalika ma'aikatansa dake wajen nan dukka aikinsu ?aya, yaransa ne, dukka wa?an da kuka gani a cikin wajen za?a?uran masu kishin ?asarsu ne, basu da wasa ko ka?an, da ka shiga hannun wa?an nan gara maka mutuwa, ko da yake ba sai na ?ata bakina ba wajen dogon bayani, mutanen da suke cikin irin wannan waje mafi ha?ari a duniya ai bama sai an ce maku komai ba, wajen da in suka yi mistake ka?an gaba?aya birnin Paris zata bambame da wuta ne, babu abin da zai rage, dan kuwa ba ?ananan boma bomai ake ha?awa a wannan wajen ba, yadda suke ha?a chemicals suke tafasa suna ci da wuta haka zu?atansu yake.
Kowani jami'i aikin dake gabansa kawai yake yi, sai ku rantse da Allah basu san juna ba, babu irin hiran nan na sanayya bare raha, tamkar ma basu san da junansu a wajen ba, kowa ka gani fuska a tur?une tamkar wa?an da aka cewa wutar jahannama zasu shiga, kunga kuwa ai karshen ?aure fuska kenan zasu yi.
Ya ?auki almost 1h a cikin na'urorin nan, yana tsaye a kan kafafunsa ko ?ar na gajiya baiyi ba, tamkar wani sa?agon da aka sassa?a. Yawan ringing da wayarsa ta yi ta yi ne yasa ya ciccire duk wasu na'ura dake jikinsa ya fita daga wajen, sai kaga tamkar ma'aikatan nasa basu ganin komai face aikin dake gabansu, amma da zarar ya dososu zai wuce sai kuga sun ?aga hannu sun sara mashi kamar wasu masu idanu a bayan wuya.
Wani hanya mai ?an tsawo ya bi, duk a cikin wajen ne, wani katafaren luxurious parlour ya shiga, yadda kuka san ba'a underground suke ba, ga wani irin dadda?ar kamshin da sanyi dake tashi a wajen, ba abin da ya fi bani mamaki ma irin furnitures dake cikin parlourn, sun ha?u kam, luntsuma luntsuma da su.
Jami'ai biyu ne ke gadin room door ?in, yana dososu suka kame waje guda tare da sara mashi, bai tankasu ba, tamkar ma bai gansu ba ya sa kai zai shiga ciki. A hanzarce ?aya daga cikinsu ya tsugunna ya ri?e ?asan takalmarsa hakan yasa takalmar suka fita daga kafafunsa, ?aukarsu ya yi ya sanyasu a cikin shoe dryer dake ta bakin door ?in ta ciki.
?ayan jami'in kuma ya yi saurin sanya hannu ya zame mashi rigar dake jikinsa da jami'an farko suka sanya mashi a yayin shigowarsa wajen, yana cire mashi ya fice da rigar daga wajen...... Kai kaga wani isa da iko!! Takalma da rigar ma sai an cire mashi?!! Wannan guy daga gani akwai girman kai!!.
Shi kuwa Smart ?in toilet ?insa dake cikin parlourn ya nufa, akwai socks a kafafunsa, a haka ya zura toilet shoe ?insa ya shige ciki. Kai tsaye wash hand base ya nufa, wash hand sanitizer mai kyau da tsada ya ?auko, wanke hannunsa tas ya yi da shi, yana da tsabta sosai, komai nasa very clean gwanin ban sha'awa.
Waje ya fito bayan ya kammala, a saman sofa ya zauna, kafin ya fito wannan jami'in nasa da ya cire mashi takalma yasata a dryer ya ?auko mashi ruwa mai sanyi and glass cup ya kawo mashi saman table kusa da sofar da ya zauna, su dai wa?an nan jami'ai guda biyun nan aikinsu kenan su hidimta mashi!.
Yana zama ya ciro wayar tasa, gayyar miss calls dayawa ya samu, mum ?insa kawai ta yi mashi 10 miss calls kamar ba ?azun ba jimawa suka rabu ba. Miss calls na dad ?insa ya kai 20, ?an girgiza kai ya yi tare da furzar da iska mai ?an zafi daga bakinsa. A hankali ya jingina bayansa a jikin sofar tare da fara kiran number mum ?in nasa, da alama yafi sonta sosai sama da dad.
Bugu ?aya ta ?auka, tana daga zaune a office nata ta ?aura kafa ?aya bisa ?aya ga sanyin Ac na bugata, sannan ga kamshi mai kwantar da hankali a gauraye a cikin office ?in ta ko'ina, securitys biyu suna gadin kofar shigowa, hannunsu ?auke da manya manyan guns masu lafiya ba sa?a saiti.
Cike da tsananin so da kaunarsa ta ce. "Hello my baby".
Wani dadda?ar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Mum.........." Katse shi ta yi da cewa. "I hope you get to the office safely?".
?aga kai ya yi yana kallon cikin parlourn nasa, wato ita mum duk a tunaninta wajen aikinsa ya tafi, har da tambayar ya isa lafiya? Bata san yana nan yana aiki daddynsa da suka ?oye mata ba, lallai akwai kura ran da ta gane gaskiya kuwa.
"My baby". Ta sake kiran sunansa jin bai amsa mata ba, bata san ya aka duniyar tunaninta a kan idan ta ganosu daddynsa yana ruwa tsundum bane, dan kuwa zai sha hukunci a hannunta ba ka?an ba. (Ni kam na ce idan ma bata ce ta saki daddyn ba???? e mana su ai kunsan mata tana saki a wajensu?? ba wani cikakken hankali ne ya ishi wasun su ba, amma ba ruwana na yi nan kada Smart ya ji abin da nace.)
"Mum everything is going well like the way you think". Ya fa?a a sanyaye, yana magana yana bin parlourn da kallo kamar bai san komai da yake ciki ba.
"How's your work? Hope you're enjoying the day?". Ta sake jefa mashi tambaya. "My mum". "My baby". "My mum". "My baby". Shiru ya yi tare da ?aura hannunsa a saman forehead
Mum da dad ?insa suna yi mashi son ransu, sai ya kira sunansu suma su kira nasa, sun saba mashi da wannan abin tun yana ?an shekara bakwai, sai ya ce mum ta ce baby, idan ya ce dad ya ce son, abin gwanin ban dariya.
Call ?in dad ne ya shigo wayarsa, dukka fa a kan abu ?aya suke son tambayarsa, shi ne kuma ya isa office lafiya sannan ya aiki, a kan wannan tambayar fa suka tara mashi miss calls har haka, kullum haka suke yi mashi, sai sun ji ya isa lafiya kuma yana cikin aminci sannan suke kama nasu aikin, wannan ?an nasu mugun ji da shi suke yi, suna kaunarsa fiye da kansu,....... Ni kam nace ai dole su so shi, dan kuwa shi ka?ai kamar rai ne ke garesu, ga shi sun tsufa, dan shi kansa Smart ?in ya kai 30 years a duniya, kunga kuwa ai sun fara tsufa, basu ma sanya rai a kan samun wani yaron ba, dan a tunaninsu ba samu zasu yi ba, shiyasa suke bashi kulawa fiye da kansu, one in billions yake a garesu.
"Mum dad is call me let me pick his call". Ya fa?a a kasale.
Da okey ta amsa mashi kafin ta jero mashi jawaban da ta saba a kan lallai ya yi breakfast mai kyau tun da yaki ya yi a gida, sannan lallai idan ya yi aiki na awa ?aya ya kwanta ya yi barci na awa biyu dan ya huta, kada ya yi wani tunani idan ba nata ita da dad ?insa ba, ya kula masu da kansa sosai, haka dai ta rin?a jeramasa su kamar yadda ta saba, kullum haka take yi mashi. Wani irin ha?a??en sumbata ta mannawa wayar tata a zuwan shi ta sumbata.
Okey kawai ya ce tare da katse kiran, dan in ya biyewa mum sai su kai yamma basu yi sallama ba, jawabinta baya karewa, idan ya ce mata shi fa yanzu ba yaro bane, sai ta ce mashi har gobe shi babynta ne, a baby take kallonsa, hakan bata yi mashi da?i sam sam, mum ta ki yarda ya girma.........??
Yana ?aukar call ?in daddyn ma abin da mum ta fa?a shi ya sake nanata mashi, okey nan dai ita ta raba shi da su. Yana katse kiran ya ajiye wayar, sam bai bi sauran miss calls ?in ya kira ba, dan dama shi idan ba mum and dad ba baya bin miss calls na kowa ya kira, duk mai bu?atarsa sai dai ya Kiransa.
Shiru ya ?an kwantar da kansa yana kallon sama kamar mai nazarin wani abin, Allah ya gani yana kaunar iyayen nan nasa, yana jinsu a ransa tamkar ya yi masu numfashi.
Wayar tasa ce ta fara ringing again, ?aukota ya yi ya kawota dai'dai saitin face ?insa. Ganin sunan dake yawo a saman screen ?in ne ya sanya shi yin hanzarin picking tare da mi?ewa ya nufi waje, dukkan nutsuwarsa ya tattara waje guda dan yin magana da wanda ya kirasa ?in, da alama mutum ne mai muhimmanci a garesa.
Kai tsaye wajen ya nufa, yana waya yana tafiya har ya je ya shige cikin motarsa. Da gudun gaske motar ta tashi ya bar wajen. Office ?insa ya nufa wato ma'aikatansu na jami'an Secret Intelligence Service. ______________________??????
DARK WORLD??
Idanun Ronnie cika suka yi tab da kwallah a lokacin da Sweetie ta kammala bashi labarinta, sosai ya ji tausayinta ya kamashi, bai ta?a jin tausayin wani ba a rayuwarsa sai yau, ajiyar zuciya ya sauke tare da sanya hannu ya ciro handkerchief daga aljihunsa, goge kwallan da suka cika mashi idanu ya yi, sannan ya matso kusa da ita sosai, sai kuka take yi hawaye duk sun wanke mata fuska, da alama labarinta ba mai da?in saurara bane, handkerchief ?in ya sanya ya fara goge mata hawayen nata da shi........ Abin da mamaki, ashe Sweetie ta san labarinsu kenan? Ta san su waye su?! Tab?ijam!. Amma yarinyar nan akwai basira da nutsuwa.