Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 38
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 38: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 38. Rarrashinta ya fara yi a kan ta yi shiru. Da kyar ya samu ta dai'na kukan,…
3,322 words
Rarrashinta ya fara yi a kan ta yi shiru. Da kyar ya samu ta dai'na kukan, ruwa ya ?auko mata ta kar?a ta sha. Shiru ya zuba mata idanu yana kallonta, ita kuma ta du?ar da kanta ?asa tana ?an shesshekar kuka...... Abin da mamaki sosai gaskiya, Ronnie da yake irin wannan masarauta mai cike da zalinci kala kala, azaba kala kala mai ta?a zuciya bai ta?a zubar da kwallah wai dan an zalintar wani ko kuma yaga zalincin da ta ?aga mashi hankali ba sai a kan labarin Sweetie, wannan wani irin labari ne to? Kada ku manta ?azun fa aka datsewa wani wuya a gabansa amma rawa ma ya rin?a ti?a shi da master Devil ko a jikinsu, yanzu sai ga shi kwatsam yana yi wa labarin Sweetie kwallah, kai da mamaki sosai abin, shi fa bai ta?a zubar da kwallah a kan wani abin ba, tab?ijam lallai da matsala in kuwa hakan ne, ko me ta gaya mashi?.
Zuciyarsa ta karaya matu?a yau a karon farko a rayuwarsa, bai ta?a jin karaya ko wani rauni na sai yau, duk sai ya jikinsa ya yi sanyi, har wani guntun ciwon kai ya ji.
Hannu ya kai ya ri?o nata hannayen, hakan yasa ta ?ago kanta tare da sauke idanunta a cikin nasa. "Where's your mum now?". A hankali ya fa?i maganar. "I don't know where is she". Ta bashi amsa.
Sake sauke ajiyar zuciya ya yi kafin ya matso da bakinsa dab da kunnuwanta, ?asa sosai ya yi da murya tamkar munafukin da zai kai gulmar kishiya ga kishiyarta, a haka ya fara yi mata ra?a a kunne kamar haka. "Ya isa haka kukan please, I promised you that ba zan ta?a bari ki sake yin kuka ba, kuma na yi maki alkawarin tabbas duk yadda za'ayi zan ku?utar dake daga gidan nan, ba zan ta?a bari yaya ya azabtar dake kamar yadda ya yi wa wasu a baya ba, ya sha kashe mutane a kan neman Spender, ya sha wahala kafin ya iya nemo in da kike, ya ta?a kama wata yarinya ta so ta yi kama da ke, kai kuna ma kama sosai da ita, a tunaninsa lokacin kece ya kama, ya bu?aci Spender daga hannunta sai ta ce bata san menene bane ma, haka ya kasheta da azaba ha?e da razanarwa, sai da ta haukace kafin ta mutu saboda razanata da yake yi, na yi maki alwarin zaki gudu daga gidan nan, sai dai ki mun al?awarin ko da yaya ya kamaki ba zaki ce da sa hannuna ba?". Dakatawa da maganar ya yi yana jiran ya ji me zata ce! Ya kurawa face ?inta idanu kamar zai cinyeta ?anya.
A hanzarce ta gya?a mashi kai alamar ta yarda ba zata ce da sa hannunsa ba ko da an kamata. Nisawa ya yi tare da sanya hannu ya kwantar da kanta a saman kirjinsa. Cigaba da magana ya yi a cikin kunnenta. "Queen of beauty tun kafin a kawo ki nan wajen na san labarinki". A hanzarce ta ?ago da kanta. Mayar da ita ya yi tare da cigaba da maganarsa. "Bawai labarin tarihin rayuwarki na sani ba, no, labarin cewa Spender yana hannunki na sani, sau da dama na bu?aci ganin hotonki yaya yana hanani, dan ya ce har ni a wannan karon bai yarda da ni ba, saboda ya sha nemo hotunan mutanen da yake samun labarin Spender yana hannunsu, zai sha wahala ya nemo hotunansu, sai dai kafin ya kai ga isa garesu wasu sun rigasa, hakan yasa yake tunanin ko ni nake gayawa mutane, dan yasan ni ka?ai yake gayawa rahoton, amma magana ta gaskiya bana gayawa kowa, kawai dai abin da na lura da shi shi ne masu neman Spender suna da yawa ne". ?an dakatawa ya yi da yin maganar yana mayar da numfashi a hankali hankali.
Shiru ta kwanta tana sauraronsa, ?wa?walwarta sai sa?a mata waye shi wannan yayan nasu? Meyasa ya zama bakin azzalumi har haka?.
"Yanzu kin san me nake so da ke?". Ya katse mata tunanin nata. Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a.
Nisawa ya yi kafin ya ce. "Dole ki saki jikinki a gidan nan, domin kada wani ya gane shirina, sannan ki nuna tamkar baki cikin damuwa, ki yi rayuwa tamkar yadda kike yi a forest ?inku, ki ?ir?iro farincikin dole domin mu cinma burinmu, lastly kada ki ?ara mun zancen Kamran a nan, zancen Pretty is okey for me". Mamakin kalamansa na karshe ne ya kamata, dama tun ?azun ta lura da shi ya canza fuska, tun lokacin da ta gama bashi labarin mum ?insu ta shigo labarinta ita da Kamran and Pretty a forest, tun daga nan ya canza fuska ya ?ata rai kamar ba shi ba, bare ma da ta ce mashi bata da wani burin da ya wuce ta bu?e idanu ta fara kallon Kamran lokacin da suke Forest kenan, ta ?ara mashi da cewa bata yi farincikin bu?ewar idanunta ba tun da bada shi ta fara yin tozali ba, tana kewarsa tamkar hauka, daga nan face ?insa ta sauya ya ?ata rai, ji yake yi kamar ya tashi ya tafiya ya barta Black Tiger ya cinyeta ?anye ma idan yana so, ya ji kamar kada ya taimaka mata, amma sai ya daure, ko me dalilinsa oho dai.
Okey ta ce mashi tare da cewa ba zata sake ba. Hannu ya kai saman gashin kanta. "Beautiful Queen gashinki ya so ya yi kama da nawa, amma naki ya fi nawa kyau sosai".
Rasa me zata ce mashi ta yi, dan ita ba wani hira ta iya ba, kun san dama da Pretty kawai take hira, ko Kamran sai dai gaisuwa ce take ha?asu, so bawani iya dogon magana ta yi ba.
"Baki ce komai ba". Ya sake fa?an. "Nakama yana da kyau". Da kyar ta iya fa?an hakan.
"Golden white ya fi up white kyau fa, i really like yours, and see this your eyes is very very sexy nice and........" Sai ya ?arisa mata sauran maganar a cikin kunne kamar wani maras gaskiya.......... Ya yi maganar ta yadda ban ji me ya ce ba!!. Kuma yana zuba mata kalaman yana wani lumshe idanu kamar ba lafiya yake ba!!.
Ba wani abin da ta gane da kalamansa, ita dai bayan cewa da ya yi nata ya fi nasa kyau, sai kuma kalmansa na karshe da ya ce ita ?in kyakkyawace ta karshe sannan kuma tana da sexy body kakar babbar mace, daga haka bata san ma'anar sauran kalaman nasa ba, shi dai ya sani! Kuma sexy kalamai ya rin?a gaya mata a cikin munnen nata, to ita da take girman forest dama ta ina zata gane wannan karatun nasa fisabilillah? Ai sai shi ?in zai gane.
(Summy princess zan yi wa Ronnienki ihun kwarto fa, ta ya zai wani zauna yana gayawa baiwar Allah irin wa?anga kalamai? Aisha baita jidda Maman Sultan Ronnie zai ?ata maku tarbiyar da kuka yi mata, ku kama sumayya ku jibgeta zata ja mashi kunne in ta ji wuya)
Shiru ta yi bata bashi amsa ba, dan ita bata san me zata ce ba. Jin ta yi shirun ne yasa ya ?an lankwasa dogon wuyar nan nasa ya le?o face ?inta. "Queen of beauty why kika yi shiru? Give me my amsa mana, i said why are you so beautiful like that, do you look like mom or dad?".
A sanyaye ta amsa da. "I don't know what to say, that's why am silent, but ka manta na ce maka we don't know our dad?".
?an shafa gashin kan nata ya yi tare da cewa. "Oh oh eyya na manta ne, zaku ga dad ?inku nan ba da jimawa ba, in dai na samu na ku?utar dake daga hannun yaya to ba shakka nima zan biyo bayanki daga baya, zan tayaki neman dad and mum with our Pretty". Yana magana kamar wanda yake jin barci ko maras lafiya.
Godiya ta yi mashi sosai, daga haka bata sake yin magana ba ta yi shiru. Sarai ya lura da bata iya magana bama bare ajega sexy words masu da?i, daga e sai a'a ta iya.
"Ronnie". Ta ambaci sunansa ?asa ?asa. Mi?ar da wuyarsa ya yi kafin ya amsa. "Ina son sanin wanenen ya kawo ni nan? And me zai yi da Spender? Waye wannan yayan naku? Sannan ina su mamanku ku kuma suke?".
Wani irin yanayi ne ya bayyana a saman face ?insa jin tambayar da ta yi na wanenen Black Tiger? Alamar tsoro ha?e da tashin hankali ne suka bayyana a saman face ?in nasa, nan take ya shiga taitayinsa, idan da da?in hira da ita yasa ya mance in da yake, to yanzu ta tuna mashi dalilin wannan tambaya tata, fuskarsa ta canza daga annuri izuwa tashin hankali. Rabata da jikinsa ya yi tare da yun?urawa zai mi?e ba tare da ya bata amsa ba. ?ago idanu ta yi ta kallesa da kyau, tabbas ta lura da canzawar da ya yi lokaci guda, sai dai bata kawo wani banzan tunani a ranta ba, ta yi tunanin ko kawai zai tafi ne babu dalili.
Ha?i?a ya ji babu da?i sosai a ransa, ba komai yasa hakan ba kuma face ta yi mashi tambayar da ba zai iya amsa mata ba, bai isa ma ya amsa mata ?in ba, bai so kuma ace ta nemi wani abin a wajensa ta rasa ba, amma ko zai mutu ba zai iya gaya mata wanenen Black Tiger ba! Da alama shi yasan Black Tiger ?in sosai, kawai dai ya nuna kamar bai san shi ba ne, idan kuka yi duba da yadda yake shiga har cikin bedroom ?insa kunga da wuya idan bai san ya kamanninsa suke ba.
"Zan ro?i yaya da ya bar Floris ta rin?a zuwa kuna yin hira idan na tafi school, zan so ace tana koya maki wasu abubuwa, ko ba komai idan kika bar gidan nan zasu amfaneki......". Da kyar ya iya ?arisa maganar, daga jin yadda yake magana zaka fahimci ransa a ?ace yake.
Yana gama maganar ya nufi waje da sauri ba tare da ya sake kallonta ba. Yana fitowa ya shiga bedroom ?in Black Tiger dan ya ro?esa a kan Floris ta zo ta rin?a zama da Sweetie.
Ya ?auki tsawon 20 mins a ciki kafin ya fito ya nufi ?akin da aka kwantar da Delisha tana jinya, duba lafiyar jikinta ya je ya yi tare da fitowa. Nasa room ?in ya shiga, wanka ya fara yi kafin ya shirya cikin sport wears masu tsada, ya yi wa kayan kyau sosai. ?asa ya sau?o da nufin ya ci abinci ya je buga ball, zakarar Dark world kenan, a komai shi ne a gaba, ball ?in ma ba'a barshi a baya na, ga shi yau ba zuwa church, dan pastor ya fa?i bashi da lafiya yana kwance a hospital, yanzu shigarsa wajen yayan nasu ya samu labarin hakan.
A parlourn ya isko Floris na zaune a saman sofa tana jera abubuwan game ?inta dake saman trayn wasan. Ta bayanta ya lalla?o ya zo ya sanya hannu ya watsa mata cubs ?in da ta sha wahala ta jera. A dubu ta juyo domin taga wanene?.
Tana ganin shi ne ta ha?e rai tare da ajiye tray ?in, cikin dabara ta ?auki pillow ta harbesa a fuska da shi. Kamar ya san zata yi hakan ya yi carap ya capke pillown ba tare da ta ta?a fuskar tasa ba. Haushi ne ya kamata ta nufesa gadan gadan irin ta zuciyan nan.
Sai da ya bari ta iso in da yake ta ?aga ?an hannun nan nata kamar bulala zata kai mashi naushi a ciki ne ya ri?e hannun nata, wurgi da pillown hannunsa ya yi ya ha?e ?an hannayen nata ya ri?e da hannunsa ?aya. Sumbata ya manna mata a dogon wuyar nan nata yana fa?in. "I really missed you my beb, yaushe kika dawo daga school?". ?o?arin kwace kanta take yi dan ta samu ko naushi ?aya ne ta yi mashi. ?agata sama ya yi sai saman kirjinsa, a kunne ya ra?a mata. "Tsaya ki ji wani magana" kin yarda ta yi tana ?o?arin barin jikin nasa. Cigaba da gaya mata magana a kunnen ya yi kan kace wani abin har ta fara dariya kamar zararriya. Dining room ya nufa da ita sai dariya take yi, ko me ya gaya mata yasata dariya? Oho mashi. Wato shi Ronnie har da sarrafa mata ya iya, daga ya sanya wannan dariya sai ya sanya wancan kuka, kai anyi ?an duniya da babu biyunsa a Dark world ?in nan wato Ronnie, shi dai babu ruwansa, bashi da wata matsalar rayuwa.
Zama suka yi ya ce ta bashi abinci a baki, ai kwana biyu bata bashi ba. Make mashi kafa?a ta yi tare da cewa a'a ba zata bashi ba. Marairace mata ya yi tare da shagwa?e fuska kamar ba shi ne zakin Dark world ?in ba, kamar zai yi kuka ya ce mata please ta yi hakuri ta bashi mana.
Jan mashi aji ta fara yi. Hannu ?aya yasa ya damko wuyar rigarta zai jawota jikinsa, dama mini sket and vest ce kawai a jikinta. Ganin ya damkota ne yasa ta fara ihun wasa tana fa?in zata bashi abincin. Kashe mata ido ?aya ya yi, ya yi ?asa da murya sosai. "Da baki amsa ba yau da kinga aiki da cikawa".
Harara ta wurga mashi, ido ya sake kashe mata yana sakin cool murmushi dimple nasa mai tafiya da imani maza da mata yana lotsawa. "Zero tension kawai". Ta fa?a ha?e da murgu?a baki. Kwaikwayan yadda ta murgu?a bakin shi ma ya yi sai dai bai iya ba, daga karshe ma sai dogon harshensa ya fitar ya lashe lips ?insa wai shi ma a dole ya murgu?a baki. Su dai robbot suna tsaye suna kallonsu har sai da ya ce su zuba mashi abinci.
Da farko Sweetie ya so ta bashi abincin a baki shi ma ya bata dan yasan bata ci komai ba, shiyasa yana dawowa daga school ya nufi wajenta dan ta ciyar da shi, amma ta zo ta ?ata komai ta hanyar kawo mashi zancen wanenen Black Tiger? Tana son kasheshi tun kwanansa bai ?are ba, zata ja mashi rugugin bala'i ai gara mashi ya kama kansa shiyasa ya bar ?akin.
Wai ni kam to menene dalilin Black Tiger na ?oye kansa? Dole akwai wani ?wa??waran dalili kam, ba haka kawai banza zai boye kansa yana wanzar da zalinci ba!!.
Ciyarda shi a baki ta yi har sai da ya ?oshi, sannan ya mi?e ya ?auketa cak suka nufi wajen buga kwallo. Jama'a sun cika stadium ?in tab, komai ya kankama shi ka?ai ?an team ?insa suke jira. Yana sako kafarsa a fili jama'a suka hau tafi da ihun murnar zakinsu ya shigo fili. ?aure fuskar nan tamau ya yi tamkar ba yanzu ya gama wasa da Sweetie and Floris a cikin gida ba, shi fa Ronnie ?an rai'nin wayo ne na bugawa a jarida, mata kawai ne suke ganin murmushinsa, kuma su ka?ai ne yake sakarwa fuska, matan ma dama da Floris ce sai Delisha, to yanzu sun yi fa?a ya kakkarya Delisha sai ya maye gurbinta da Sweetie, su biyu yanzu yake sakarwa fuska, idan ya fita waje tamkar wani zaki haka yake, sai ya tur?une fuska over, kowa ka tambaya zai ce maka bai ta?a ganin dariyarsa ba sai wa?an nan mutane biyun yanzu da Sweetie uku.
Wasa aka fara bugawa jama'a sai murna suke yi, dama kowa ya rigada yasan team ?in su Ronnie ne zasu yi nasara, dan in baku mantaba shi ne zakaransu a empire ?in. Haka kuwa aka yi, su suka ?auke cup ?in wannan wasan, jama'a ihu suke kurmawa sosai kamar ba daga cikinsu ihun yake fita ba saboda sautinsa. Master Devil dake zaune a saman ha?a??iyar kujerarsa ne ya ce yau dole ayi shagali a case dan kwana biyu ba'a yi ba. Jin furucinsa yasa jama'a suka kara kurma ihun suka ru?e da murna.
Master Devil fa ya ?auki Ronnie kamar ?an cikinsa ne, dan shi ne horonsu ya yi dai'dai, yana ji da shi sosai......... Sai da daddare suka shirya partyn da master ya ce.
Tsala tsalan ?an'mata wa?an da suka iya taka rawa sosai ne aka kira, sun iya rawa da har idan suna takawa ma zaku ga tamkar basu da ?ashi a jikinsu, su yi wani irin lankwashewa kamar macizai, su uku ne matan gasu kyawawan gaske........ To ni dai na ce a gaskiya rashin addini dai bai yi ba, idan ka bar addinin musulunci wlh ka shiga uku ka lalace.
To su dai haka suka shirya partynsu, ga kwalaben giya gana dreaks kala kala, saniya da ra?umi aka gasa tun da rana, shagali iya shagali suke yi idan master ya shirya masu party, ga rawan da suke yi innalilahi ba'a magana, sai ma idan Ronnie ya shiga filli yana rawa, guy ?in nan ya kware kam, in dai rawa ne to daga kansa an rufe kofa, dama ga jikinsa ?an dai'dai ya taka son ransa babu nauyin jiki bare ciwo.
Kowa yana zazzaune a saman chairs ?insa, ki?a kawai ake jira sai a fara takawa, shi kuwa mai sakin ?i?an wato Dj yana jiran ne Master ya bada umarni aci a sha sannan a sha giya a yi tatul ta yadda zasu ji da?in casunsu a buge, su haukata kansu su yi ta rawa kamar wa?an da aka zarewa duk wani hankali da sani.
Ai kuwa master na bada umarni ba wanda bai kwankwa?i wine kwalba biyu zuwa sama ba, wasu iyayen rashin hankali kam ma giyar zallarta ba'a sirka ba suka sha har kwalba uku zuwa biyar, duk kuma abin da suke yi Black Tiger yana ganinsu, dama shi baya hana a cashe, su yi duk abin da suke so, shi ma idan ya tashi yana yi masu son ransa ne.
Sai da suka bugu iya buguwa saura Master da Ronnie, su basu shan wine, sai dai su sayawa masu sha, Floris da Delisha ma basa sha, Ronnie ya hanasu, dan shi ?in ?alibin lafiya ne. Dukka ?an Wrestling nasu da kuma dakarun yakinsu ma Black Tiger ya hanasu shan wine, dan in suka shata nan take zata yi masu mummunar illar, saboda kullun cikin yin training suke, zasu mutu a banza in suka ce zasu ha?a hanya da ita.
Matan da zasu yi rawan ma fa sai da suka kora rabin kwalabe, lokacin da Dj ya saki waka ya subhanallah, idan kuka gansu yadda suke cin uban rawa sai kunce kun godewa Allah da ya yo ku a musulmai.
Lokaci da Ronnie da master suka fara rawa, basu fili aka yi ana ihu ha?e da tafi, masu fito suna yi, sai dai fa komai rashin son rawanka idan kaga yadda Ronnie yake rawa sai ya burgeka, ya kware iya kwarewa, wannan da zai shiga gasar rawa na duniya shi zai zo na ?aya.
Yana tsaka da rawa ya tuna cewa dole ya ?auko Sweetie su yi rawa a tare, zai koya mata idan ma bata iya ba, dan haka bari ya ?aukota ita da Floris, dole ya ro?i Black Tiger ya barta su taka rawa yanzu kam tun da a cikin gida ne ya barta ta fito su taka............... Tab Sweetie da rawa, e lallau kinga ta kanki, Ronnie dai anyi ?an duniya wlh.....??
To na dai barku a nan bari mu le?a wani wajen mu dawo kafin nan kila Black Tiger zai aminta Sweetie ta fito ta taka rawan.
___________________??????
DUBAI
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 16/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
E23
DUBAI_____??????