Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 39

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 39

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 39: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 39. Izuwa yanzu Leesharh ta yi mugun sabo da Sharifat sosai, sun zama kamar ya da…

3,365 words

Izuwa yanzu Leesharh ta yi mugun sabo da Sharifat sosai, sun zama kamar ya da kanwa, har Abbie yana batun saka Leesharh ?in a school ?in su Sharifat, sai dai a nan matsalar take, dan dai da ni da ku munsan takardunta dai na karya ne, kuma hakikanin malamai idan suka ga takardun nan dai zasu gane gaskiya, matsala ta biyu kuma bata kammala secondary school ba a gaske, a takardu kuma ta kammala, yanzu Abbie magana yake a kan zata shiga jami'a fa kenan, jamb zata rubuta yanzu....... Babbar magana!!.

Tab?ijam! Dan ma tana da ?wa?walwa yarinyar da lallai za'a shiga babban makaranta da dolanci, dan kuwa ba wani abin kirki ta iya sosai ba, matsala ta uku 15 to 16 years take da shi kada ku manta, gata ?a mace, a wannan zamani a ?an shekarun nan nata ake son ta goga da manyan mata ?an jami'a, ita da ba wayewa ne ke gareta ba, ba ishasshen ilimi ba, da alama Abbie yana son ?aukar dala ba gammo, domin kuwa kamar yadda masu nikaf suke beating na brain ?inta da wuya idan ta shiga jami'a manya mata bazasu kwatanta beating na brain ?in nata ba suma, koma su yi mata wayo su ?ata mata rayuwa, ga maza sosai, tsab wlh zasu mata wayo su bu?e mata idanu, dan ba ?arya ta yi ?an?anta, ga shi ba uwa kusa bare uba, Ummie dai kun ga bata sonta, bata ko kulata bare ace zata maye mata gurbin uwa ta rin?a bata ?ar shawarwari ta jata a jiki.

Sannan ga dukkan alamu Leesharh bata taso da uwa kusa ba, saboda yanayin yadda take gudanar da rayuwarta zai tabbatar maku da cewa ba shakka ta jima bata a tare da mahaifiyarta, duk macen da ta taso a tare da uwa ba zata yi irin shirmen da take yi ba, ga ?wa?walwar dai tana da shi, amma an rasa wanda zai sarrafata ta hanya mai kyau har ?wa?walwar tata ta amfaneta, kuna gani dai yadda take ta fama a kan tunanin masu nikaf, sai ta yi kamar zata ?ago gaskiyarsu sai kuma ta sake komawa ruwa, sai ta yi tamkar ta gane gaskiya, sai kuma ta sake fa?uwa, gaba?aya gata gatan nan kawai, tana da bu?ata uwa ko kuma mai irin zuciyar uwa wanda zai cike wancan gurbin.

Shi kansa Abbie yanzu da ya jawota a jikinsa sosai ya fara lura da cewa da wuya idan wannan yarinya ta kammala secondary, sannan yanzu ya ga ?an?antar shekarunta a yanayinta da ta matso kusa da shi, sai dai bai wani ?auki wannan tunani nasa da mahimmanci ba, daga karshe ma ya watsar da tunanin a in da ya umarce Dr Raj ya tsaya mata ya yi mata duk abin da ya dace!!.

Yah Rizwan and Omar wato Guyson sun shirya komawa ?asar Tunisia a yau, shi Yah Rizwan batun aurensa da Gimbiya Chuchu zai kaisa sai kuma Akka da ta ce lallai lallai ya zo, dan tana zargin Jaish ko Jawad ne suka yi mata wancan tsiyar, shiyasa ta ce Rizwan ?in ma ya zo, a cewarta shi ne uwarsu ?aya da Jawad, dan haka kome za'a yanke a gabansa za'ayi, Su King basu ta?a rabe ?a?ansu ba shi da uncle Abbas, amma Akka tsab take rabasu, ba wani ha?esu da take yi da sunan family, wani lokaci idan gigin tsufan ma ya bugota sai ta kira Yah Jawad da Abbas ?in ma mai gaba?aya, wannan tsohuwa dai sai dai muce Masha Allah, rigimamma ce number ?aya.

A ?angaren Yah Ramish kuwa, Dr Raj ya sha matu?ar wahala a kansa, Bilal ma ba'a magana, har rama bawan Allahn nan ya yi, ya shiga matsanancin damuwa sosai, baya fita office, baya samun ishasshen barci, haka zalika baya nutsuwa ya sanyawa cikinsa wani abin kirki, sai gayyar coffee or cappuccino, idan ya ?an gaji da su ne sai ku ga ya sha cold brew, aikin kenan kullum, ya rasa ina zai sanya ransa ya ji sanyi, suna kaunar junansu ne, in short Ramish ?in dake kwance yana jinya ma ya fisu kumari da kyan gani, sai jigila suko suke yi suna going up and down a kansa.

Idan baku manta ba dama harbi biyu aka yi mashi, dukka biyun kuma sun ?an ta?a yi sosai, ?ayan kam ma a gefen cikinsa ne bullet ?in ta fasa, ?ayan kuma a hannunsa wajen damatsansa, na hannun nasa kam Alhamdulillah ba laifi an shawo kan wannan matsala, na cikin ne dai aka samu matsala saboda abin da ya sha kafin harbin ?ille ?in. A iya binciken da Dr Raj ya yi a cikin jininsa ya gano an bashi wata magani ne mai suna arm bars an kwa?a shi da joins locks da wani shegen magani mai karfin iya ?acewa a cikin jini wanda ya ?asa iya gane wanenen, duk iya binciken da ya yi ya kasa ciro maganin, shegen magani ne mai wuyar ganewa idan ya ratsa jini, da ace ba Ramish aka ha?awa wannan ba, kai ace ba wani na jikin Dr Raj ?in aka yi wa hakan ba tsab zai iya bincika ya gane wani irin magani ne.

Amma ?an uwansa da suka sha?u aka yi wa hakan, baya cikin ishasshen nutsuwa da zai iya yin wani dogon bincike, yana tafiya ma tamkar zai kifa saboda tashin hankali, aikin nan yinta kawai yake yi dan tabbatar da ?an uwansa ya ku?uta daga ha?ari, amma a wahalce yake bawan Allah.

A ?angaren Leesharh tun ranar da masu nikaf suka katse mata kira a kan ta ce su ha?a ta da babanta, to tun ranar basu sake kiranta ba, ba wai kuma basu nemanta ?in ba ne, nemanta ma suke yi kamar hauka dan su tambayeta shin Ramish ya mutu ne ko kuwa harbin bata same shi a in da ya kamata ba? Kun san idan ba ita da take cikin gidan kuma hawan da su Ramish ?in suke ba da wuya masu nikaf ?in su san halin da ake ciki ta wajen wasu, dole sai ta wajenta, dan idan baku manta ba a baya sun fa?i cewa suna da ma'aikata a gidan, amma ba'a can ciki ba, har suka kara da cewa Leesharh yarinya ce za'a barta ta yi aiki a can ciki, to shiyasa suke nemanta dan su samu rahoton meke gudana a cikin gidan.

Sai dai kash a yanzu ko sun kirata wayar baya shiga, ba komai yasa hakan ba kuma face sun koma kwana ?aki ?aya da Sharifat, gudun kada asirinta ya tonu yasa ta kashe wayar mai gaba?aya ta cusata cikin wani aljihun wandonta ta danna a can kasar echolac ?inta, ta yadda hankalin Sharifat ba zai kai wajen ba.

Abin da Leesharh bata sani dan gane da masu nikaf a nan ba shi ne, a wannan rana da ta zubawa Ramish wannan maganin da suka bata, da Ramish ya mutu tamkar yadda suka shirya ko sun kamashi sun tafi da shi kamar yadda suke so, to da ba shakka ba zasu sake nemanta a waya ba, aikinsu da ita ya ?are, zasu san ta yadda zasu yi ne a cikin gidan su tona mata asiri ta yadda Abbie zai binneta da ranta, ko kuma su Yah Bilal su kasheta su mi?awa karnika namarta, sannan su kuma su kashe babanta dake hannunsu, kunga sun rufe babinta kenan, a tunaninsu asirinsu a rufe hankalinsu a kwance dan sun san bata san komai dan gane da su ba bare ta tona masu asiri.

Da Allah yasa bata da hakkinsu, Allah ba azzalumin bawansa bane, sai Allah ya nufa burinsu bai cika ba, Allah ya aiko Bilal ya ceci ran ?an uwan nasa, Ramish bai mutu ba!! Wannan dalilin yasa yanzu suke neman Leesharh ?in kamar hauka, dan kuwa kunga idan ya kasance Ramish bai mutu ba dole su nemota ta koma bakin aiki, dan su fa sun kwallafa rai a kan sai sun ga bayansa, ba gudu ba ja da baya, wannan abinfa ba iya masu nikaf bane kawai, akwai manyan jiga jigai daga sama wa?an da su suka ?addamar da contract ?in, dan haka Leesharh rayuwarta yana cikin gagarumin ha?ari, tabbas idan ta yi sanadiyar mutuwar Ramish kamar yadda suka tsara, to su ba zasu fitar da ita daga gidan Abu Abdussalam ba, a nan zasu tona mata asiri su Bilal su ji da ita, su kuwa kunga a tunaninsu dama bata san face ?insu ba bare idan suka tona mata asiri ita ma ta ce zata tona masu.

Gaskiya akwai gagarumin cakwakiya zallarta, dan kuwa Leesharh tana tsaka mai wuya ne, saboda wannan aiki da aka bata jiga jigai manyan kai a ?asar ne suka ?addamar da shi........ Ni dai fatana a nan shi ne kada Leesharh ta sake ta kunna wayarta, dan dole ta nan zasu sameta, idan bata kunna ba ai shikenan, Allah yasa kamar yadda ta kashe wayar ta manta da ita shikenan a tafi a hakan kawai mugayen mutane kawai, zasu zalinci marainiyar Allah!.

Yau ta kama Friday sai murna Sharifat take yi idan aka sauko masallacin sallar jumma'a Abbie ya aminta za'a kaita gidan King Badeen ta wuni sai dare a dawo da ita, ba yadda bata yi ba a kan Leesharh ta zo su je, amma ina ta ce wlh ba zata je ba, kuma tun farko Sharifat ?in ce ta ja ta ce ba zata je ba, dan tana zaune a tsakiyar gado daga ita sai kayan barci, basu jima da tashi daga barci ba, Sharifat ta tafi gaishe da Abbie, a nan ta tambayesa zata je gidan kakan nasu, ya ce idan an sau?o daga jumma'a za'a kaita, shi ne ta shigo room ?insu da gudu tana murna ta ce. "Leesharh ki shirya Abbie ya yarda za'a kaimu gidansu abokan fa?arki wato su Omaid sarakan zuciya".

Ai daga jin sunan su Omaid ta ce wlh har ta mutu ba zata je wannan gida ba, sai godiya ga Allah dama take yi da Allah yasa ba'a gidan nan suke da zama ba, sun tafi nasu gidan, kawai rana tsaka Sharifat ta wani ce mata tazo su je gidansu? A kan wani dalili? Ai ba wannan magana, shi ne ta ce ba zata je ba.

Magiya sosai Sharifat ?in ta rin?a yi mata tana gaya mata ai basa nan suna school, ina ai taki yarda, ta ce wlh ba wannan zance. Daga karshe dai Sharifat ta ha?ura ta shirya ita ka?ai. Gidan Abu Abdussalam a manne yake da katafaren masallacinsa da ya gina a waje, a nan suke yin sallar jumma'a, amma fa saboda girman gidan sai sun shiga mota daga cikin gida izuwa mallacin.

Haka suka shirya, su Sharifat sun yi kyau a cikin black abayn da suka sanya, sunyi rolling mayafan abayan a kansu, kayan ya fi kar?ar Sharifat sosai, saboda ita farace tas, Leesharh kuma kunga ai chocolate ce, kalar fatanta ya ?an saje da kayan, sai bata wani haska sosai can ba. Ga shi suna son saka kaya iri ?aya, Yah Rizwan ne kafin ya tafi Tunisia suka je ya saya masu kayayyaki komai iri ?aya, shiyasa suke saka kaya iri ?aya yanzu. Abbie yana jin da?in ganinsu a shiga iri ?ayan kenan, idan ya ga Leesharh na murmushi har wani sanyi yake ji tana ratsa ransa, ya rasa dalilin hakan, amma ya danganta hakan da cewa, dan yana jin da?i ya sanya marayun Allah farinciki ne, bai san abin ya wuci haka ba, tabbas yana matu?ar jin sanyi a ransa idan ya ganta, Hakan na matu?ar ?onawa Ummie rai, sanadiyyar haka har shai?an ya samu matsuguni a cikin zuciyarta in da yake sa?a mata cewa tabbas Abbie son Leesharh da aure yake yi, idan kuma Ummie ta yi sake to nan ba da jimawa ba zata ji diran kishi ?ar cikinta a cikin gidan, wannan dalilin yasa ta kara tsanar Leesharh ?in fiye da tunaninku.......... Tashin hankali, tab lallai gidan Abu Abdussalam zai kama da boma bomai ma kuwa, jama'a kun ji wata lukutar masifar da Ummie take tunani? Tana son tasa su Bilal su yi wa karnikansu kilishi da namar jikin Leesharh, ai idan suka ji Abbie zai kara aure ko da babbar mace ma zai aura akwai yaki ba ka?an ba bare Leesharh da Sharifat ma ta fita a shekaru, lallai ummie ta zo da babban al'amari, amma kuma fa tun da ta fara tunanin hakan kila akwai kamshin gaskiya, dan fa mai ?aki shiyasa wajen da yake yi mashi yoyo, ta san halin mijin nata in and out, lamarin abin dubawa ne.

(Ni kam nace da kuwa abin zai bada citta, kash wayaga Leesharh ana buga kishi da Ummie?? wayaga ta ce kai Ramish zo kayi driving ?ina muje shopping ?? yau zan kwana cikin farinciki dan za'a samu mai saukewa ?an gidan dukka jijida kansu na jinin sarauta, haba idan Leesharh ta aure mana Abbie da takalma zamu rin?a shiga parlon muga uban da zai hana mu?? mu kaka yaro kneel down???? uhmm babu ruwa dai.)

A motar Bilal Sharifat da Leesharh suka shiga dan zuwa masallacin, sai bata labarin yadda gidan king Badeen yake Sharifat take yi, tana ta kwa?aita mata son ta ce zata bita gidan, amma ina ta ce ai koma menene a gidan ba zata je ba, ita ai bata fatan ta sake ha?uwa da su Omaid a rayuwarta.

A haka suka nufi masallacin, ?a?an larabawa sai kallon Leesharh suke yi, dama last week ma da suka zo da ita Sharifat taga idanu a kansu kam har ta godewa Allah, tun bata magana har ta gaji ta kira securitynsu guda ?aya ta sanar da shi cewa kallon da jama'a dake cikin masallacin nan suke yi masu ya isheta, dan haka a taka masu birki.

Haka kuwa aka yi, securitys suka ja masu layi tare da daka masu warning, sai ya zamana a sake suke satar kallonsu, basu fitowa kai tsaye su kallesu bare a kamasu su sha hukunci. To wannan satin ma haka suke ta faman kallon Leesharh ?in, tabbas ba dan komai suke kallonta ba face kyanta, gata dai chocolate color, amma kuma za'a iya cewa duk ?an'matan dake cikin musque ?in ta fisu kyau nesa ba kusa ba, shi ne abin yake ta basu mamaki, basu yi zaton za'a samu kyawawa a bakake fata ba, da sun ?aukemu kamar a kanmu aka sauke muni gaba?aya.

Motocin Abu Abdussalam yana shigowa cikin masjid ?in sai da gaba?aya jiniya ya kara?e ko'ina, yau Bilal bai jira Abbie ?in nasu bane, kawai ya ?auko su Sharifat sun yi gaba, sai yanzu su Abbie suka iso, motocin a jere sun kai guda 10, daga gida zuwa masallacin kawai, Allah sarki Ramish yau jumma'a na biyu kenan za'ayi sallah ba tare da shi ba, abin tausayi, a gaskiya masu nikaf ?in nan bakaken mugaye ne, sun dagula mashi jini sosai da makirin maganin nan nasu, da kyar aka iya shawo kan jinin aka sarrafata, yanzu dai ikon Allah kawai ake jira, kila ya farfa?o ko akasin haka, su Dr Raj kam dai sun gama nasu aikin.

Mata kenan, mu ?in ?an albarka ne, kowa da abin da yake yi a cikin masallacin kafin a tada hi?ama, wasu ?an'matan suna latsa waya a cikin masjid ?in ma, sam ba zasu hakura ayi askar ba, ayi karatun Alkur'ani a bar wayar sai an koma gida kuma, kwana shidda a week ana tare da waya ana latsawa, amma tana ?aya, a ranar ma ?an awannin biyu zuwa uku kawai ake da bu?ata ka ware dan samun falala da lada, amma a'a, sai dai anyi abin da ba shi ba, ya Allah ka rabu da sharrin waya ka ha?amu da alkhairinta, kasa ya kasance mune zamu moreta ba itace zata moremu ba.

So wasu suna latsa waya, wasu sun ha?u suna ta hira maras amfani, wasu suna ri?e da Alqur'anin basu bu?e ba suna ta kallon mutane, kuma wlh wannan ?abiar dayawan mata ne, haka suke yi, meyasa zaku bari shei?an ya hanaku samun wannan gara?asa mai girma da daraja haka? Please mu daina bari shai?an yana zugamu yana hanamu aikata aikin da ya dace damu, yasa muna zuwa muna aikata aikin da bai dace da mu ba, kowani wayewan gari ki tabbata kin tuna mutuwa fiye da yadda zaki tuna rayuwa, hakance zata baki damar gina lahirarki mai kyau, Allah ka bamu dacewa.

Alqur'anin mai girma Leesharh ta ?auko daga wajen ajiye Alqur'anai, tana ?o?arin dawowa mazauninsu Sharifat ta nuna mata da hannu a kan ta ?aukomata ita ma, komawa ta yi ta ?auko. A tare suka bu?e suratul Maryam suka fara karatu, Sharifat ta yi mamaki sosai na jin yadda Leesharh ta iya karatu sosai, da kamar zata tambayeta a ina ta iya karatu nan, sai ta fasa ta ?oye mamakinta suka cigaba da karatu har liman ya fara ?o?arin tada kabbara, sannan suka mi?e suka fara kikkimtsawa yin sallah.

Tun daga masallaci bayan sun idar da sallah Sharifat ta ce da Abbie daga nan a wuce da ita kawai, ita ko gida ba zata koma ba, saboda murna yau an barta ta je, tana fin wata biyar haka wani lokaci bata samu daman ko le?a waje ba idan ba school ba, shiyasa idan aka bata damar zuwa gidansu uncle Rahab ko dai gidan kakan nasu mai gaba?aya ba ?aramin da?i take ji ba.

Saka Bilal Abbie ya yi a kan ya kai masa ita can, sannan ya yi umarni da motocin securitys da dama su raka su. Haka kuwa aka yi Bilal ya wuce da ita, ita kuma Leesharh Abbie ya ce tazo ta shiga nasa motar. Sosai Sharifat ta ?an yi mamaki, dan kuwa Abbie ba zaka ta?a ganin wani a cikin motarsa ba, ko ita da take ?ar cikinsa sau biyu ta ta?a binsa a cikin motarsa, yau rana tsaka kawai ya ?auki Leesharh, abin da mamaki.

Shiru ta ?an yi shai?an ya fara raya mata anya babu kamshin gaskiya a zargin Abbie da Ummie take yi na yana son Leesharh da aure kuwa? Dan kuwa yana yawan lalla?a Leesharh ?in sosai, wani abin idan ya yi ma sai ka zaci Leesharh ?in ce yarsa ba Sharifat ba, abin da mamaki kam.

Dannewa ta yi ta shiga motar Bilal, shiru ta yi tanata sa?e sa?e har suka bar gidan, dama Ummie ta sha gaya mata tana zargin Abbiensu da soyayyar Leesharh a ransa, har ta ce mata ta daina janta a jiki, ita kuwa taki fir, ta ce ai Abbie ba zai ta?a yin haka ba, yana da ?a mai 25 years a duniya ai ba zai ce zai ?ara aure ba, bata san a nata wautar bane hakan, dattijo mai yaro mai shekaru wajen 40 ma ya kara aure bare Abbie, nawa yake?....... Ni dai na ce akwai tashin hankali gaskiya ba ka?an ba a gidan nan my people's, bala'in can kai jama'a!!.

Ummie ma fa ta zo masallacin, dan haka tsarin gidan Abu Abdussalam yake, sai dai ita ma a nata jerin gwanon motocin ta zo, haka zalika da zata koma, bata lura yau Leesharh ta shigar mata motar miji ba, da yau anyita kuwa.

Bayan sun koma gida ma a elevator ?aya Abbie ya haura sama da tare da Leesharh ?in, ya ri?e hannunta ?aya da hannunsa ?aya, ya kuma ri?e wannan sandar girman tasa da hannu ?aya, yana dake cikin alkyabbar nan nasu na larabawa, kansa ya sha na?i da rawani ya fita sosai. Sai kamshi ha?a??e ne yake tashi a cikin elevatorn.

Suna haurawa parlourn sama suka fito, Abbie ya wuce part ?insa yana cewa Leesharh bye bye, ita ma nata room ?in ta shiga. Tana zuwa ta haye saman gado ta kwanta tana tunanin rayuwa, yau da Sharifat bata nan sai gaba?aya ta ji gidan babu da?i, hakan yasa ta mi?e ta fara tunanin me zata yi dan ya ?ebe mata kewar Sharifat kafin zuwa dare.

Sai a lokacin ne tunanin wayarta ya dawo cikin kwakwalwata, dan ba abokiyar hira sai tunane tunanen banza, a haka ta je ta afka tunanin wayarta ko nace barazana ga rayuwarta. A hanzarce ta mi?e ta ?auko wayar dan ta kunna ta gani, sai a lokacin ne ma ta tuna da abin da ya kawota gidan, babanta ya fa?o cikin ranta, nan take zuciyarta ta karaya jikinta ya yi sanyi sosai, har kerma hannayenta suke yi wajen kunna wayar tata.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull