Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 40

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 40

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 40: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 40. Yana kawo wutan screen ya ?auke saboda babu chargi, a hanzarce ta mi?e ta…

3,284 words

Yana kawo wutan screen ya ?auke saboda babu chargi, a hanzarce ta mi?e ta koma saman sofa dake kusa da switch, chagern Sharifat ta ?auko ta sanya wayar.

Tana sawa kuma ta kunna shi, kawo wutan screen ?in ya yi. Wayar dake saman bedside drawer ne ya fara ?ara, irin emergency phone ?in nan ne. Da farko kamar ba zata je ta ?auka ba, sai kuma dai ta ce tun da Sharifat bata nan bari ta je ta ?aga ta ji wanenen? Dan tasan iya ?an cikin gidan ne kawai suke amfanai da wayar.

Hannunta na kerma alamar a tsorace take haka ta ?auki wayar tare da karawa a kunnenta tana fa?in hello. "E lallai ya tabbata kin zama yar gida kenan, wato har kin ma iya ?aukar call na emergency wanda ya kamata ace ?an gida ne kawai suke picking ko? To maza ki fito main parlourn ki ?auki abincin su Bilal ki kai masu tun da Sharifat bata nan". Sautin muryar Ummie ce ta daki dodan kunnuwarta da wa?an nan maganganu.

Wani irin dukan uku uku da ta ji kirjinta ya yi ne yasa bata san lokacin da ta yi saurin ?aura hannunta a saman saitin zuciyarta tana sauke numfashi ba. Murya a raunace ta amsa da. "Okey Ummie gani nan zuwa". Kit ta ji an katse kiran ba tare da an sake yin magana ba.

Wani irin fargaba ne ya dira a ranta na tuna yanayin su Bilal, ita shiyasa ko zuwa gashesu ta duba jikin Ramish ?in ma bata yi, ko Sharifat ta ce su je sai ta ?a?alo wani uzurin wanda zai sa dole Sharifat ta tafi ita ka?ai, sai ga shi yau Sharifat ?in bata nan dan dole ta je part ?in nasu, kai amma wannan abin bai yi mata da?i ba sam, jikinta sai kerma yake yi ta mi?e ta nufo waje, sai kuma ta baro wayar tata a saman hannun sofa.

Kai tsaye ta nufi main parlourn, Allah ma yasa bata cire kayan jikinta ba, gyalenta ma yana kanta, a shirye take. Kirjinta sai dukan uku uku yake yi har ta kai bakin kofar parlourn. Dab zata shiga ciki Ummie da Hajiya two seater suka danno kai zasu fito. Karo Leesharh ta yi da Ummie dan ita ce a gaba, wani irin baya baya ta ja tana layi.

Dama kun san haushinta Ummien take ji, ai kuwa bata yi wata wata ba ta dallah mata wani irin mari wanda ya sanyata dafe ?uncinta a hanzarce, ita ta sara me ta yi wa ?an gidan nan kumatunta yake shan marika daga wajaje daban daban...... Abin da baku sani ba a nan shi ne, Hajiya two seater kawar Ummie ce sosai, yanzu Ummien ta kirata ne a kan tazo su yi shawara a kan zargin Abbie da take yi na yana son Leesharh, shi ne dalilin zuwarta gidan a yau. Shawarar suka yi, hajiya two seater ta bada shawarar Ummie ta ?atar da Leesharh daga doron duniya kawai, idan ba haka ba irinsu yara ne masu mugun shiga rai, kuma idan Abbie ya aureta idanunta suka bu?e wlh Ummie bakin ciki ne zai kasheta, cewar Hajiya two seater kenan, shi ne suka tsayar da magana a kan lallai dole a san ta yadda za'ayi a fitar da Leesharh daga gidan a ?atar da ita a shafe babinta, kun fa san larabawa da shegen iya bakin kishi, to Leesharh dai ta shiga uku, tana tsaka mai wuya! Can ga masu nikaf, nan kuma ga Ummie......... Su da basu da tabbacin Abbie sonta yake yi ko tausayinta ya ji, amma suke batun a shafeta daga doron duniya kamar su suka halicceta, kai jama'a, bakar zuciya dai ko a ina take sai ta nuna kanta!.

Amma ni ina da tantanma, tantamata a nan shi ne! Idan baku manta ba Leesharh ta ta?a cewa wannan Hajiya two seater da take zuwa wajen ummie tabbas ita ce wadda ta ?aukota daga gidan AAJ, to idan ko haka ne kunga kenan da biyu hajiya two seater ta ce Ummie ta ?atar da Leesharh a shafe babinta, zasu jefi tsuntsu biyu ne da dutse ?aya...... Kai jama'a mutun abin tsoro, Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu kawai, amma ta kan iya yiwuwa ba ita ?in ba ce wancan hajiya two seater daban, dan da wuya ace mutun ?aya ce dukka, idan mutun ?aya ce kenan Ummie ma munafuka ce? Munafurtansu take yi? Ko yaya ake son ce mana?!!. Tab?ijam!!.

?an siraran hawaye ne suka fara bin ?uncinta. Tsawar da Ummie ta daka mata a kan ta bata hanya ne yasa ta ja baya da sauri jiki na kerma.

Wucewa Ummien ta yi, bata san da cewa akwai hajiya two seater a bayanta ba, dan haka tana na wucewa ta sa kai zata shige cikin parlourn, wani irin baya baya ta yi ta fa?i ?asa saboda karo da ta sake yi da giwar mata wato hajiya two seater, wannan ai doke mutun ya fa?i ?asa idan ya yi karo da ita, idan kun yi karo mai kyau ma sai ka ji komai ya tsaya ma, ka yi tunanin da trailer ka yi karo ba mutum ba saboda ?iba irin nata, tsokoki ta ko'ina.

?an kawar da kanta hajiyar ta yi kamar wata maras gaskiya ta tsallake Leesharh ?in ta wuce abinta. Mi?ewa ta yi tana hawaye ta ?arisa cikin parlourn tana waigen Hajiyar. Da kyar ta iya ?aukar trayn abincin su Bilal ?in, trayn ya yi mata girma, haka ta nufi part ?in nasu. Tana ta jan kafafu har ta isa, fargaba kamar zai kasheta.

Sanya kai cikin room ?in ta yi, bata san cewa a saman dining table ?insu na parlourn part ?in nasu zata ajiye masu ba, ita kam kai tsaye ta wuce emergency room ?in nasu. Tana sanya kai Bilal da ya kai Sharifat gidan King Badeen ya dawo ba jimawa ya sako kai zai fita domin ya ?ebowa Dr Raj wasu allurorin da zai yi wa Ramish.

Karo suka ci tray ?in abincin ya fa?i ?asa a kan kafarsa, gaba?aya kayan abincin suka tarwatse, suka ?ata ko'ina jaga jaga. Cikin fushi ya cire hannu zai mareta, dai'dai lokacin ta ?ago face ?inta dan ta ga waye ta yi karo da shi a karo na biyu kuma? Ita dai ta shiga uku kawai take fa?a a cikin zuciyarta, duk ta ru?e har ta ji kamar fitsari na ?o?arin zubo mata a wando.

Yana ?ago hannunsa ita kuma ta ?ago face ?inta, cak ya tsayar da hannun nasa bai kai ga sauke mata marin ba, kallon tsab ya yi wa face ?inta na ?an sakani kafin nan slowly ya mayar da kallonsa ?asa ?an kafafun nasa, ya ga ?arnanar da ta yi masu, ta ?ata masu waje kaca kaca, dan fa kayan abincin ya watse ta ko'ina a cikin room ?in, kayan fruits duk sun watse.

Dama already da hawayenta na marin da ta sha a wajen Ummie ta shigo cikin room ?in, dan haka sai hawayen suka tsananta gudu a saman face ?in nata, jikinta na kerma ta zube gwiwowinta a ?asa ta shiga furta kalmar sorry. Dr Raj dake zaune kusa da Ramish ?in ne ya zuba masu idanu yana kallonsu, yana jiran yaga me ?an uwan nasa zai yi mata, dan yasan Bilal sarai ba baya ba wajen saurin ?aukar zafi, akwai zafin rai ga shegen fushi da fusata.

Abin mamaki sai bai yi mata komai ba, sai ma hannun da yasa ya ?agota daga zubewa da ta yi a saman gwiwowin nata. Ai tsabar mamaki da kallon kwakwab Dr Raj bai san lokacin da alluran da yake ri?e da shi yana ha?awa Ramish ?in ta cake shi a hannu ba, ya ga abin da bai ta?a zato ba.

Yana ?agota ya ra?a gefenta ya fice daga ?akin abinsa. Ita kanta ta sha madarar mamaki kuma ta sha jinin jikinta, dan kuwa Sharifat tana yawan bata labarin zafin rai irin na Bilal da Ramish and Dr Raj, basu da saukin kai ko ka?an, Rizwan ne dai ya fita zakka a cikinsu, yana da saukin kai da kirki sosai.

Kawar da kallonsa daga kanta Dr Raj ya yi tare da ?aukar cutton ya goge jininsa dake zuba in da ya cakawa kansa allura a wajen ganin gulma.

Turus ta tsaya ta rasa me ma zata fara yi a wajen. Har Bilal ?in ya ?auko sauran alluran ya dawo tana tsaye in da ya barta, ga jiki sai kerma yake yi. Mi?awa Dr Raj alluran ya yi tare da zama a gefen Ramish ?in ya zuba mashi idanu tamkar zai ti mashi kwallah, Allah ya gani yana kaunar ?an uwan nan nasa fiye da kansa.

Ta kai almost 30 mins a tsaye ta rasa abin yi, su kuma sai aikin gabansu suke yi ba wanda ya sake bi ta kanta, da alama ma sun manta da ita a wajen.

Sai da suka gama abin da suke yi ne Bilal ya mi?e zai fita waje, zai je ya yi wanka a room ?insa ne. Yana juyowa suka ha?a idanu da ita, dan sai kallon shi take yi, ita dai wlh tabbas tasan ta ta?a ganinsa a wani waje, kuma tabbas bayan fitowarta daga gidan AAJ ne, hakan yasa duk in da ya yi take binsa da idanu ta kasa tuna a in ta ta?a ganin nasa.

Suna ha?a idanu ya sake yi wa face ?inta kallon tsab kamar ba lafiya ba, bai ta?a ?aga idanu ya kalleta ba sai yau, ga shi kuma ya zo yana ta yi mata kallon tsab, anya kuwa lafiya?.

My people's kallo me kuke tunanin BILAL yake yi mata?.

"Just leave it here and go". Bilal ?in ya fa?a mata hakan, ya yi maganar tare da nuna mata kayan abincin da yatsarsa, tamkar ba shi ya yi maganar ba, dan ba zaka yi zaton ya motsa lips ?insa ba, a hankali ya yi ta.

Abin mamaki baya ?arewa a duniya, wai yau Bilal ne da yi wa wata saukin kai? Anya kuwa ba wata a ?asa? Abin da mamaki, daga kallon farko, gaskiya kamar dai zan saka ayar tambaya a nan.

Ai a dubu ta juya ta fice daga ?akin, kai tsaye ?akinsu ta nufa, tana zuwa ta fa?a saman gado. Waya Bilal ya ciro ya kira number Ummie a kan ta turo a gyara room ?in, sannan ta ha?a masu wani abincin tun da wannan kam ya zube. A takaice ta ce mashi me ya faru da wancan abincin da ta ha?a masu yanzu?.

Shiru ya ?an yi kafin ya ce ya kifar da shi by mistake, dan haka ta ha?a masu wani. Okey ta amsa mashi da shi tare da ce mashi zata aiko Leesharh ta gyara room ?in, ita kuma bari ta shirya masu wani abincin.

A ?an dakile ya bata amsa da Leesharh ai ba ?ar aiki bace bare ace ta zo ta yi gyara ?aki. Daga haka ya katse kiran. Ummie ta saba da halinsu, dan haka sai ta kira phone dake cikin kitchen dan ta kira ?ar aikin da ta aminta da ita ta je ta gyara masu room ?in, emergency room ?an aiki suna iya shiga gyara shi, can cikin ainahin part ?insu ne basu shiga.

Tamkar a mafarki ta fara jiyo vibrate ?in wayarta. A razane ta mi?e zaune a tsakiyar gadon. Kai tsaye wayar ta nufa, wani irin dukan uku uku da kirjinta ya yi ne yasa sai da kanta ya sara mata. Kiran masu nikaf ne ya shigowa wayar, hakan zai tabbatar maku da lallai nemanta suke kamar hauka.

Da farko zama ta yi a gefen hannun sofa taki ?aukar kiran, amma abinku da shai?an suna kiranta na huku sai ta ji tana son ?agawa ta ji me zasu ce mata.

?auka ta yi murya na rawa ta furta. "Assalamu alaikum". Daga ?ayan ?angaren namiji ne ya amsa mata sallamar tata. A hanzarce ta ciro wayar daga kunnenta ta duba ta gani shin da gaske su ?in ne? Ta saba yin magana da mace, yau kuma ta ji muryan namiji? Dole ta shiga ru?ani.

"Aisha Aliyu Haidar". Namijin ya furta.

Muryarta tsananta kerma ya yi a in da ta amsa mashi da na'am. "Ina son ki saurarin wannan da kyau ki ji kafin nayi magana da ke". Kai ta gya?a mashi alamar to tamkar tana a gabansa.

"Innalilahi wa inna ilahir rajiun, bayin Allah dan girman Allah me na yi maku? Su waye ku? Kada ku kasheni, wlh ina da yarinya, kuma ni ka?ai ne gatanta, da ni ka?ai ta dogara, ku dubi girman Allah ku tausayawa maraicinta, wlh idan ma ku?i kuke so a wajen mu wlh bamu da shi, mu talakawa ne! Dan Allah kada ku yanke mun.........." Kit ya katse voice record ?in da suka kunna mata ?in, wannan shi ne maganar dake fita daga cikin voice ?in. Da larabci shi ma na cikin voice ?in ya yi maganarsa.

Ai a wani irin haukace ta mi?e tsaye, ko mutuwa zata yi ta dawo ba zata ta?a manta voice ?in babanta ba, tabbas shi ne, wasu irin hawaye tamkar hanyar ruwa ne ya bu?e suka fara gudu tsere a saman fuskarka, da yake bata san voice record suka kunna mata ba, ta yi zaton baban nata ne a wajen, hakan yasa cikin ?aga murya tana kuka ta fara ambatar. "Baba bazaka mutu ba, tabbas zan yi abin da suke so dan su sakeka, na shiga uku!........."

Tsawar da mutumin ya daka mata ne yasa ta ha?iye kukan nata ba dan taso ba, tsit ta nutsu tana zare idanu. "Ki saurareni da kyau ki ji abin da zan ce maki, mu ba ke ko babanki muke da bu?atar kashewa ba, Ramish muke da bu?ata, ki bamu ha?in kai mu same shi sai mu kuma mu baki babanki ku tafi duk in da zaku je". Cewar mutumin, da kausasshiyar murya tamkar na ?an shaye shaye ya yi maganar.

Tsabar zufa dake tsastsafo mata har face ?inta ya ji?e sharkaf, ga kuka, majina ha?i da yawu dukka, ta sanya hannunta ta toshe bakinta dan ma kada sautin kukanta ya fita wani ya jiyota. Sai ha?e word's take yi, murya a sarke ga kuka ta ce. "Wai me zaku yi wa Ramish ?in? Meyasa sai ni kawai zan yi maku aikin? Ku nemi wata mana! Me nayi maku da kuke azabtar da ni ta hakan?". Tana kai karshen maganar ta zube ?asa a saman gwiwowinta tare da kifa kanta a saman sofa ta saki wani irin kuka mai azabbabben ciwo da kuna.

Kai tsaye ya ce mata. "Fasa kirjin Ramish muke son yi mu tsinko zuciyarsa, mu cinyeta a ?anyarta, batun aiki kuma ke muka ga damar sanyawa, ki yi ko kuma mu shafe babinki a doran duniya!!". Cikin fushi ya yi maganar yana ?aga murya, da alama ransa ya yi mugun ?aci sosai da jin kalamansa.

Kamar zata yi hauka, cikin wata iriyar murya da bata fita sosai ta furta. "Ni na yarda ku kasheni kawai, ku yi wa girman Allah ku kasheni, dan hakan sai ya fi mun sauki a kan in tallafa maku wajen kashe bawan Allah da bai ji ba bai gani ba, ba zan iya yin wannan aikin ba, wlh na yarda ni ku kashe ni, amma ku sake mun babana ya koma gida, ku dubi girman Allah ku tausaya mun".

Wani irin shu'umin dariya mutumin ya saki mai sautin da ya ratsa dodan kunnenta da kyau, hakan yaja ta ?an sassautan kukan da take yi tana sauraron she?anin dariyar nasa.

Sai da ya yi mai isarsa sannan ya dakata cak, cikin wani irin shu'umin murya ya furta. "?an'matan ki tabbata wannan shi ne jin sautin muryar babanki na karshe kenan a duniya, dan kuwa Aliyu Haidar zai fuskanci ukubata yanzun nan, daga yau ya fara fuskantar masifa da bala'i kenan har izuwa ranar da zai mutu, ki sani kullum sai na cire mashi wani abu daga jikinsa, kullum zan yanki wani abin daga jikinsa in jefawa karnikana su cinye, a haka zan kashe shi, adadin join da suke jikinsa adadin rayuwar da zai yi cikin azaba da jin ciwon duk in da nake yanke mashi babu magani har ya mutu kenan.........." Yana kai karshen maganar kit ya katse kiran.

A zabure ta mi?e tsaye, cikin ?aga murya ta fara furta. "Dan girman Allah kada kayi haka, na amince zan yi duk abin da kuka ce, wlh na yi alkawari kawai ku bani umarni". Tana magana tana kewaye ?akin ta ?aura hannu ?aya a kai kamar mahaukaciya. Duk wanda ya ganta a wannan hali sai ya zubar mata da kwallah

Jin ba'a yi magana bane yasa ta ciro wayar daga kunnenta. Ganin sun katse kiran ne yasa ta furta. "Lahhh shikenan sun katse wayyo babana na shiga uku na". Kamar fa ta zare. Ta kai karshen maganar tare da sakin wayar ya fa?i ?asa ya gangara ?asan sofar dake wajen, ihun sunan baban nata ta fara yi tare da cire gyalen da yake a kanta ta yi jifa da shi gefe, tamkar wata zararriya haka ta watsa gashin kanta, kai tsaye ta nufi jikin bangon ?akin, buga kanta da karfi karfi ta fara yi tana kiran sunan baban nata.

A hankali jini ya fara bulbula daga gaban goshinta, sai bugawa take yi da karfi karfi tana kiran sunansa, sosai jinin ya ?alle daga wajen, da karfi yake zuba kafin wani lokaci ta zube ?asa bata numfashi...................

Tab a gaskiya Leesharh kina cikin wani hali, kina tsaka mai wuya, ke baki ma san koda kin taimaka masu hakansu ya cinma ruwa suka cinwa burin nasu ba barin ki ke da baban naki zasu yi ba, wannan wace iriyar masifa ce? Fatan mu dai Allah ya ku?utar da ke daga sharrinsu.

______________________????

GIDANSU KHADIJAH.

A hankali wani sautin murya ya fara yi mata yawo a cikin dodan kunnenta, wani irin jiri take gani daga kwance.

Bayan sallar asuba ne, sun yi sallar sun idar, Zainab ta yi ?o?arin tambayarta me ya sameta daren jiya ta rin?a amai? Sai dai Khadeejerh bata bata damar hakan na, ta ?aure fuska ta haye gado ta kwanta, taki sakewa bare Zee ?in ta kusanceta har ta kawo mata wani maganar na daban.

Ganin haka yasa Zee ?in ta mi?e ta haye gadon ita ma, haka suka kwnata shiru. Kafin wani ?an lokaci barci ya kwashe Zee. Ita kuwa Khadeejerh shiru ta yi tana tunanin.

A hankali wani sautin muryar ya fara dokan dodon kunnuwanta, datse idanunta gam ta yi tare da fara tunani yadda mai wannan murya ta cutar mata da rayuwarta, a hankali sautin yake tashi a cikin kunnuwanta in da take fa?in.

"Dr ka tabbatar da cewa wannan injection ?in zai cire mata cikin nan da yake jikinta? Dan fa na bata kwayoyi kala kala har bleeding ta yi, amma cikin yaki fita, bana son kowa ya san da wannan maganar ne"........ Ya ilahi ya lillahi wasu irin zafafan hawaye ne suka fara bin ?uncinta.

Waro idanunta waje ta yi tare da mi?ewa ta nufi toilet. Tana shiga ta datse kofar da key, a saman gefen jacuzzi ta zauna tare da kifa kanta da jikin bango, kuka ta fara rerawa tare da toshe bakinta da hannu ?aya, wani irin ra?a?in azaba da zuciyarta take yi mata tamkar ta kashe kanta take ji........ Innalilahi wa inna ilahir rajiun, my people's me yake faruwa da Khadijan kenan? Hasbunallah wani'imal wakil!!.

Ta sha kuka tun da da?in rai har ta fara jin numfashinta na fita sama sama tamkar zata sume, jin hakan yasa ta daure ta mi?e daga wajen, hannunta da ta toshe bakinta da shi ne ta ciro ta fara goge hawayen da suke ta ?ar tsare a kumatunta. Gaban wash hand base ta nufa, kunna ruwan ta yi ta sanya hannunta dukka biyu ta taro ta fara wanke face ?inta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull