Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 43
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 43: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 43. ?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ?????…
3,258 words
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
25
A guje matasan wajen suka watse yau aljani ya mari wani ya suma.
Kan kace me zance ya baza kauye ai aljanin gidansu Mahreen ya mari yaron Inna Rabi ya suma, abin ku da kauye nan take suka canza mashi suna daga aljani zuwa maye, dama can kun san ba yarda da shi suka yi ba, to ga abu kuma ya zo ya faru, kun san kauye da iya champa abu, take suka champa shi (champi), sai dai kuma duk kauyen babu mai iya tinkarar Jaish ?in ya ce mashi ya bar garin ko wani abin makamancin hakan, dan tsoronsa suke ji, sai gangami ake yi ana kaiwa Ar?o complain a kan shi a matsayinsa na Ar?on kauyen ya ?aukar masu mataki a kan Jaish, su sun kasa.
Shi kuwa Jaish ?in bai sauke Mahreen a ko'ina ba sai a tsakar gidan nasu, sai dai kafin ya sauketa sai da ta ta?a mashi gashin kansa, dan ta jima ita da Mahnoor suna gulmar arab hairn nan nasa, suka ce ba gashi bane, to yau da ya ?auketa sai da ta ta?a ta tabbatar gashi ne, kyallin da gashin yake yi ga shi bakin kirin da shi ne yasa suke ganin kamar ba gashi irin na mutane bane da shi, Mahreen kam da hankali ya yi mata yawa ma har da cewa ai roba ce ba gashi ba, Mahnoor kuwa ta ce a'a gashi ne amma ba irin na mutane ba, na aljanu ne, to yau dai ta ta?a ta ji bana aljanu bane na mutane ne.
?akin bappa ya shige bayan ya sau?eta, binsa da kallo ta yi har ya ?arisa shigewa ciki, ajiyar zuciya ta sau?e, wasa wasa fa ita Mahreen ta fara son shi, tun asali kun san dama tana sonsa, lokacin da kowa yake gudunsa ya ce aljani ne a lokacin ita da bappa kawai suke kusantarsa, kunga kuwa idan tace tana sonsa ma bata yi laifi ba!.
Bappa kuwa da yake dattijon arziki ne sai da ya kira matasan da suka watse ?in ya sanyasu suka kama yaron Inna Rabin suka nufi gida da shi. Da kafafunsa kuma ya taka izuwa gidan Inna Rabin dan ya bata hakuri, idan kuka lura da yanayin bappa zaku ga shi mutun ne mai son zaman lafiya, baya son yin hayaniya da kowa, haka zalika baya son ?atawa kowa rai, shiyasa baya ganin cewa shi babba ne yake bawa kowa hakuri, har yara matasa ya kan basu hakuri idan suna fa?a, shi bai ?auki bada hakuri a bakin komai ba face tubali ko ace makulli na zaman lafiya.
Da kyar ya iya shawo kan Inna Rabi ta yi shiru, da kuka take ta yi, dan tana tsoron Jaish ?in ita ma.
Allah da ikonsa kuwa tun marin da Jaish ?in ya yi wa yaron sai Allah ya rabbeshi da wani irin ciwon ciki mai tsanani wanda yasa jama'ar kauyen suka kara tabbatarwa da cewa Jaish fa mayen gaske ne, hakan yasa suka fara shirya ta yadda zasu koresa daga garin, sai dai suna tsoro, Allah ya bawa yaran Momma kwarjini sosai, komai zafin da ka ?ebo da nufin ka yi masu fa?a ko ka ga ya masu sun yi maka ba dai'dai ba, to kuna ha?a ido ko kana ganinsa zaka ji ina ka kasa, duk sai ka nemi kalaman bakinka ka rasa, wasu irin su Mama gani suke yi tamkar asiri Momma ta yi wa ?a?an nata suka kasance a haka, bata san daga Allah bane kwarjinin nasu.
Ai Nennen da ta ji wannan labari haukacewa ne kawai bata yi ba, ta ce wlh ba zata koma gidan bappa ba, dan ita bata shirya mutuwa ba, haka kawai ta je Jaish maye ya cinyeta, wlh ba zata sa?u ba, shi kansa Ar?o mahaifin nata cewa ya yi ya fara tsoron Jaish gaskiya, dole su bulbula hayakin mayu a kauyen, gobe za'ayi gayya na jama'ar kauyen dukka izuwa kofar gidan Ar?on, dan shi ne Ar?on kauyen gaba?aya, kamar ace sarkin kauyen kenan gaba?aya, to Ar?on ya sanya sanarwa gobe da yamma kowa ya hallara a kofar gidansa, dole za'ayi turaren mayu, duk kuma mayen da aka kama wlh kashe shi za'ayi.
Yadda Ar?on ya rin?a nanatawa bappan kwairaga a kan lallai ya tattare gaba?aya jama'ar gidansa ya zo da su ne yasa Bappan ya fara tunanin ko dai Ar?o ma ya yarda da maganganun ?an kauye ne da suke zancen cewa Jaish maye ne?. Da yake bappan mutun ne mai ?an wayewa saboda tafiye tafiyen da yake yi kasashen daban daban, shiyasa bai yarda da duk abin da suke fa?a ba, dan kuwa yasan da Jaish maye ne ko wani mugun to da shi zai fara cutarwa, dan a ?aki ?aya suke kwana, su wuni a daji wajen kiwo tare ba abin da yake yi mashi, sai ma tallafa mashi sosai da yake yi, dan ko jiya da suna wajen kiwo bappan yana zaune a ?ar?ashin bishiya wata kunama ta zo kusa da shi ba tare da ya sani ba, saura ka?an ta harbesa Jaish ya ganta, da hannunsa yasa ya kamata ta harbesa a hannu, bappan ya sanya mashi maganinta, to da shi mugu ne ko mayen da suke fa?a da ba zai taimakesa daga harbin kunama ba, sai dai ma ya kara mashi wasu kunamun, amma da yake su kauye sai a hankali akwai karanci wayewa ga karanci addini shiyasa.
Ai Nenne dai ta koma gidan Ar?o da zama, ta ce wlh sai randa Jaish ya bar gidan zata dawo. Ar?o fa mutun ne mai zafi sosai, amma a wannan karon dole ya hakura ya bar Nennen a gidansa ta cigaba da zama, dan kuwa gwaggo ta hayayyako mashi da ruwan bala'i a kan ?arta ba zata koma gidan bappa maye ya lashe mata kurwa ba, idan ana son ta koma ?akinta dole mayen nan ya bar gidan.
Yaron Inna Rabi dai tun daga aka kaisa gida cikinsa ke matsanancin ciwo tamkar ba zai rayu ba, idan cikin ta wani irin mur?a mashi har wani irin sandarewa yake yi yana mi?ewa kamar ransa ta zo fita, abin gwanin ban tausayi, sai kuka Innar take yi baiwar Allah.
Da daddare misalin karfe 9 suna zaune a tsakar gida da bappa da Jaish a saman tabarmar da Mahnoor ta shinfi?a masu, abinci ta kawo masu, yau dai Jaish ya nunawa bappa alamar baya son cin nama, bappan ya ce mashi to me zai ci, ko dai zai iya cin irin abincinsu ne?. Hakika bappa ya ga ?o?arinsa ma na juriyar cin nama na tsawon lokaci haka da ya yi, dan ma dai bai da yawan ci ne, bai wani cin abincin rana, wata rana ma sau ?aya yake cin abinci a rana, shiyasa namar ma bata yi saurin ginsarsa ba.
Cikin harshen larabci bappa ya tambayesa me zai ci?. Shiru ya yi kansa a ?asa, baya yarda ya kalli face ?in bappan a lokacin da yake kallonsa, sai ya kauce, idan ya kauce kuma sai ya yi ta kallonsa yana jinjinawa kyawawan halayensa da tarin alkairansa, da zarar ya juyo da kallonsa a kansa kuma zai yi maza ya kawar da nasa kallon, abin ma wani lokaci gwanin ban dariya.
Shiru ya yi bai amsa ba. A karo na biyu bappan ya sake tambayarsa me zai ci? Kai ya ?an girgiza alamar shi ba zai ci komai ba.
"A'a ban yarda ba dole ka ci wani abin, da safema fa kaki cin komai, kai haka zaka yi ta horar da kanka da yunwa?". Cewar bappa.
?ara yin ?asa da kansa ya yi ba tare da ya yi magana ba. Mi?ewa bappan ya yi yana fa?in. "Akwai wata kauye a gabanmu can su suna da shago, bari na je na duba maka ko suna da fanta da bread ne na saya maka sai ka sha". Kunsan fulani da kallon darajar bread and fanta...........?? (To fulani masu karanta book nan ayi hakuri amma gaskiya na fa?a, kuna daraja bread and fanta ??????)
Mi?ewa shi ma Jaish ?in ya yi tare da nunawa bappan alamar a'a kada ya fita, shi ba zai ci komai ba, a daren nan ya tafi har wata kauye kai gaskiya a'a ya barshi kawai.
"A'a ka bari na sayo maka, dan ba zan iya barinka da yunwa ba, kai bakona ne, dole na kula da kai, kamar yadda ba zan iya barin su Mahreen su kwana da yunwa ba haka kai ma ba zan iya barinka da yunwa ba, dan haka ka zauna dai bari na zo".
Rike hannunsa Jaish ?in ya yi ya shiga nuna mashi alamar a'a shi dai bai yarda ba, ya yi hakuri ya bari shi baya jin yunwa. Kuma ha?i?a yana jin yunwar, kawai baya son wahalar da dattijon nan ne, saboda yana hidima da su sosai, ya gaji da cin nama, ga shi babu wani abincin, tunani yake yi a cikin ransa ko dan ya faranta ran bawan Allah nan bappa, ya rage masa wahala dole ya koyi cin irin abincinsu ko da fura da nono ne kawai, idan ba haka ba wahalar da bappan da yake yi ta yi yawa, kullum sati sai an yanka mashi kaji guda goma, ai abin ta yi yawa, shi bai ta?a tunanin akwai irin dattijawan arziki irin bappa na, gaskiya mutum ne mai farar zuciya sosai.
Da kyar bappan ya yarda ya koma ya zauna. Mahreen and Mahnoor ne suka fito daga nasu ?akin suka ?auki abincinsu, a kusa da bappan suka zauna dan su ci. Sai le?en Jaish Mahreen take yi, ga hasken wata tankar tana haska shi, ya sunkuyar da kai tamkar mai tunanin wani abin ko kuma mai ?aukar darasin karatu.
Sallamar da Hamma Faisal ya yi ne yasa suka kai kallonsu a kan kofar shigowa. Kusa da Jaish ya zauna tare da mi?a mashi hannu kamar kullum. Kin bashi hannu su gaisa Jaish ?in ya yi, har yau har gobe bayan su bappa mugun kyamar jama'ar kauyen yake yi, baya ta?a yarda ya gaisa da kowa, dan zai yi amai, su bappan ma ba karamin fama ya sha ba wajen ?o?arin cire kyamarsu a ransa.
Already Faisal ya saba da cewa Jaish baya yarda su yi musabaha, amma kullum yana gwada bashi hannu idan suka ha?u, dan a kullum gani yake yi tamkar zai yarda ya bashi hannun nasa su gaisa, sai dai ba wani canji, bai da ko alamar niyar gaisawa da kowa, ko bappa baya musabaha da shi sai dai ya nuna mashi alamar gaisuwa kawai idan suka tashi da safe. Faisal baya jin tsoron Jaish, dan kuwa tun da yaga bappa bai guje shi ba, kuma Jaish ?in ma bai cutar da bappan ba sai ya share zancen mutanen kauye shi ma.
Hira sosai suka fara yi tsakanin bappa da Faisal Jaish ya yi shiru kai a ?asa yana sauraronsu, ita kuwa Mahnoor ta je ta ?aukowa Faisal ?in abinci, ta zo suka gaisa sannan ta ?auki abincinsu tare da cewa Mahreen su wuce cikin ?akinsu. Ba musu ta mi?e dan su tafi ?in, saboda idan baku manta ba dama Mahreen ba shiri suke yi da Faisal ba, dan haka basu ha?a inuwa sam sam, shiyasa ma ta yarda ta bi Mahnoor cikin ?aki ba dan ta so ba, saboda bata gajiya da kallon Jaish.
Suna shiga cikin ?aki Mahreen ?in ta ce. "Adda Mahnoor kin san me?". Kai ta girgiza mata tana ?o?arin kawar da fitillar kwai dake wajen da suke zama su ci abincin nasu.
"Allah Adda Mahnoor da Hamma aljanina ?in nan ya ?aukeni ?azun sai da na ta?a gashin kansa naji, ashe ba roba bace, gashi ne mai laushi kamar namu, kawai dai dan nashi ya fi namu baki kuma kinga yana she?i shi ne kawai banbancin".
?an zaro idanu Mahnoor ?in ta yi tare da cewa. "Haba da gaske?". Kai ta gya?a mata. "E da gaske, kuma gashin nasa wlh kamshi yake yi, akwai da?in ta?awa".
Harara ta wurga mata tare da cewa. "Ke Mahreen dama ai komai na Hamman da?in ta?awa yake yi maki, haka fa kika rin?a ta?a mashi kumatu a gidan nan har sai da kumatun nasa ta kunbura ta yi ja, to dan Allah kada idan yana barci ki je ki yi ta ta?a mashi kyakkyawan gashin kan nasa har kisa ta fara muni tana zamowa ja ko kuma ma dai yawan ta?awan naki yasa gashin duk su cire, dan Allah ki bar masa kayansa kin ji yar kanwata?".
Turo bakin nan ta yi, a shagwa?e ta ce. "Gaskiya a'a, Allah Adda Mahnoor idan dai na samu dama sai na ta?a, in yana barci zan rin?a ta?awa, idan yana zaune da bappa ma sai na ta?a, dan in bappa yana nan ba zai yi mun komai ba, ke dan baki ji laushin gashin nasa bane shiyasa kike cewa kada na ta?a". Ta kai karshen maganar tana tur?une fuska irin na shagwa?a.
Shiru Mahnoor ta yi, dan kuwa tun da ta ce sai ta ta?a gashin nan to fa ba makawa sai ta ta?a ?in, kome za'a ce sai ta ta?a, kai ko Jaish zai daketa sai ta ta?a, bare ma sun san ba zai dakesu ?in ba, ai shikenan.
Suna cin abincinsu suna hira gwanin birgewa, har suka kammala, sannan suka mi?e Mahreen ta tattare komai ta gyara wajen, sannan ta haye saman gado ta kwanta. Ita kuma Mahnoor sai da ta yi wanka kafin ta kwanta, saboda zafi da ake yi, kuma ita ta saba yin wankar dare kafin ta kwanta, Mahreen ce randa ya gameta ta yi wankar daren, ran da bai gameta ba kuma wankar da ta yi da rana ma ya wadatar. Amma fa duk ranar da ta yi wanka da daddare to tabbas sai ta yi kwalliyar nan nata na aljanu, ta mammaka kwalliyar sannan ta kwanta......... Ni kam na ce ai wannan kwalliyar kawai ya isa idan aljanu masu yawo tsakar dare suka zo giftawa ta ?akin nasu suce ga ?ar uwarsu a nan a kwnace bari su ?auketa su tafi da ita........??
Washegari da safe kamar yadda ta saba ta tashi da aikin gyaran gida ha?e da girki. Bayan ta gama komai tsab kamar kullum, sai ta ?auki hijabinta ta nufi gidan Ar?o. Gaishe da su ta je ta yi a lokacin ita kuma Mahreen ta shiga wanka, dan ta ce wlh ba zata je gidan ba, dan Ar?o ya ce Jaish maye ne, dan haka tun da suka zagar mata Hamma aljaninta wlh ta raba gari da su, kowa ya yi ta kansa, Mahreen manyan ?asa.
Tana dawowa a hanya, sai bitar karatunta da Inna Rabi ta kara mata take yi, cikin nutsuwa take tafiyarta, kwatsam taga mutane a gabanta kamar wasu aljanu. Zaro idanu ta yi tana kallon su ?aya bayan ?aya, yaran Inna Rabi guda biyu ne sai abokansu. Murya na rawa ta ce "Hamma Salisu ina kwana". Yaron Inna Rabin kenna, kanin wanda Jaish ya dallawa mari.
Sandar kiwon dake saman shoulder ?insa ya sauke ?asa tare da ce mata. "Yanzu ina mayen naku mai rama maku duka idan anyi maku?".
Narai narai ta yi da idanu, dan tasan yaran Inna Rabin da shegen zuciya ga fa?a, saboda zafin zuciyarsu yasa wancan yaron da Jaish ?in ya mara ya yi saurin kaiwa Mahreen duka a maganar da bata kai ta kawo ba, suna da saurin hanu wajen duka ga fushin bala'i.
"Kayi hakuri Hamma Salisu". Ta fa?a kamar zata yi kuka. "Ba hakuri na ce ki bani na ai, kin ganmun nan ramawa Hammanmu abin da mayen gidanku ya yi mashi muka zo yi a kanki, sai ki kira mayen naku mu gani, ya zo ya hanamu in ya isa".
Wani irin fa?uwar gaba ta ji, dan ita wlh bata son abin da zai ta?a mata lafiyar jikinta, kwana biyu Nenne bata ta?a mata lafiya ba dama, sai bin sandar hannunsa da kallo take yi, addu'a take yi Allah ya hana hannunsa ?aga sandar nan har ya ce zai buga mata shi, ?an hannayenta sai kerma suke yi, alamar ta tsorata, ga manyan idanun nan nata sun fara cika da kwallah.
Daga ta bayansu kamar daga sama suka ji muryan wani dattijo ya ce. "Kai Salisu me kuke yi a wajen?". A hanzarce suka kai kallonsu wajen, mahaifinsu ne. A da?ile Salisun ya ce. "Bappa ba komai......". Bai ?arisa maganar ba Mahnoor da ta ga sun juya suna kallon bappansu haba ai sai ta watsa a guje, ta samu hanya kafa me naci ban baka ba? Sai hanyar gida.
Da gudu suka rufa mata baya, sai kwala ihun sunansu bappan nasu yake yi, amma ina basu tsaya ba. Gudu take yi da iya karfinta. Da karfi ta nufi kofar gidan tana ?o?arin banke buhun kofar gidan ta shiga Salisun ya capko hijabin jikinta da nufin ya janyota baya kada ta shiga gidan, dan su samu su daketa koda sanda uku ne su yi mata kafin su sake ha?uwa da ita a wani wajen sai su ?auki fansa na gaske, dan sun ce wlh ba zasu barta ba ita da Mahreen, ko dare ne sai sun bi su rama abin da aka yi masu, dan a cewarsu su Mahreen ?in ne silar da yasa mayen ya kama masu ?an uwa......... Kenan yanzu idan Allah ya kar?i rayuwar yaron su ma fa haka zasu ce zasu kashe su Mahreen dan rashin ilimi da hankali, kai wato wani lokaci mutane masu zuciyar gado ma fa basu yi ba a rayuwa, dan irinsu basu yafiya kuma basa manta gaba wlh.
Yana damko hijabinta while tana ?o?arin shiga cikin gidan suka ci karo da Jaish da bappa da suke ?o?arin fitowa, sun gama cin abincin safe zasu fita zuwa gona. Da karfin Salisu ya ja hijabinta ta yi baya, bayan da ta yin nan kuma a tunanin Jaish ?in fa?uwa ?asa zata yi saboda karon da suka yi, sam bai lura da su Salisun a bayanta bane, hakan yasa ya kai hannu da sauri ya ri?o hannunta.
Sai da ya ri?e hannunta ne ya ji daga bayanta ana jan hijabin jikinta, sun sha?e mata wuya kan nata ya yi sama. Hakan yasa ya ri?eta da kyau take da fitowa wajen.
Subhanallah, ai suna ganin Jaish ?in suka saketa tare da watsawa a guje suka bar wajen, ashe rashin kunya suke ji da shi, balai'n tsoron Jaish ?in suma suke ji.
Da kallo ya bisu kafin ya dawo da kallonsa a kan face ?inta, ruwan hawaye take yi saboda shake mata wuya da hijabin nata da suka yi. Sake mata hannunta ya yi tare da sa kai ya wuce gaba abinsa. ?arisowa wajenta bappa ya yi da sauri, tambayarta ya fara yi a kan meya ha?ata da su Salisu? Ya yi maganar yana goge mata hawaye!.
Bata ?oye mashi ba ta sanar da shi duk abin da ya faru. Shiru ya ?an yi yana tunanin wannan rikicin kuma tab, shi yasan halin mutanen nasu, tun da suka fara hakan ba barinta zasu yi ba, sai sun ?auki wannan fansa da suke ikirari, tabbas dole ya san abin yi a kan hakan kada wannan matsala ta girma, kar ya yi sake a illata mashi ?a?a, hakan yasa ma ya ce yau ba zai barsu a gida su ka?ai ba, gara ya tafi da su gona, in yaso idan sun je wajen Ar?o da yamma ya gaya mashi a yiwa su Mahreen tsakani da su Salisu, dan baya son abin da zai ta?a mashi lafiyar ?a?ansa.