Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 44

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 44

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 44: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 44. A takaice dai yau a tare suka wuni wajen kiwo, sai yamma suka dawo gida, yau…

3,370 words

A takaice dai yau a tare suka wuni wajen kiwo, sai yamma suka dawo gida, yau dai basu ci abincin rana ba, saboda babu wanda zai yi girkin. Mahreen fa sai da ta ta?a gashin Jaish ?in kamar yadda ta fa?a, yana zaune a ?ar?ashin bishiya shi da bappa ta zo ta shafa gashin nasa. Ai a ?ari ya ?ago yana kallonta, ko a jikinta ta cigaba har da mur?a mashi gashin nasa, da yake a yanzu gashin nasa yana da tsawo zuwa bayan wuyansa, kun san larabawa da gashi, sannan kuma ga shi ya kai almost 3 to 4 months a kauyen bai yi aski ba, sai gashin ta kara tsawo sosai, hakan yana ?aya daga cikin abin da yasa suke ce mashi aljani, dan yadda gashin nasa ya yi tsawo, sannan kun san yadda gashin larabawa yake, akwance ga tsantsi da sheki, ku kanku ku kwanta yadda fatar jikinsa yake fari tas kyakkyawan gaske, ga uban bakin gashi mai tsawo da sheki ai dole ku ?an tsorata da kyansa, sai ma ya zaro idanun.

Yau wuni Mahreen ta yi tana mummur?e mashi gashin kai kamar an aiketa, tana fa shakkarsa, amma tsabar ita ?in in ta fa?a sai ta cika, sai da ko ta cika, tun yana mamaki har ya dai'na, kuma sam bai nuna alamar kamar ya ji haushin abin da take yi mashi ba, bappa ma bai hana ta ba, dan shi kansa yana son su rin?a jan Jaish ?in da maga ko Allah zai sanya watanara bakinsa ya bu?e ya yi masu magana, ya gaya masu daga ina yake dan su samu su mayar da shi in da ya fito.

Duk ta watsa mashi gashi, ta bi ta mummur?esa ya zama kamar indomie, yau ya sha aikin Mahreen manyan ?asa

Time da zasu koma gida da ya yi sam bata ji da?i ba, ranta bai so ba, ta so ne Jaish ya cigaba da zama a wajen tana mur?e mashi kai har gobe, ita fa bata gajiya in dai tana tare da shi.

Haka dai suka koma gida, wanka Mahnoor ta yi suka shirya zuwa wajen Ar?o. Jaish dai ya nuna ba zai je ba, da kyar bappa ya lalla?ashi suka tafi. Jama'a duk sun hallara, kowa sai baya baya yake yi da bappa, sauran manyan dattawan kauyen ne kawai suka ?an yarda suka gaisa da shi, su ?in ma sai ?ari ?ari suke yi, shi kam Jaish dama bai nemi su yi mashi magana ba, dama ko sun yi mashi ma ba kula su zai yi ba, dan haka tsayuwarsa a gefe ya yi yana kallon gefen da babu mutane.

Sai gulmarsa jama'a suke yi ?asa ?asa, masu satar kallonsa suna yi, masu rufe idanu wai suna tsoron ganin maye suma suna yi, haka dai suka tsaya har lokacin da Ar?o yasa su gwaggo suka banka maganin mayu a wuta hayaki ya fara balbalowa, jama'a basu da masaniyar hakan kawai unexpect suka ga hayaki yana bulbulowa. Nan take dayawa daga cikinsu suka fara tari mai sautin gaske, gwaggo bakar muguwa har da dumbulo maganin cikin hannayenta dukka biyu ta sake bankawa a cikin wutar, dan a cewarta idan Jaish maye ne ma ya ji azaba sosai......... Wato mutun dai ko ya mutu sai an ?aure shi!!.

Sai tari jama'a suke yi shi kuwa Jaish yana tsaye yana binsu da kallon mamaki, bappa ma bai yi tari ba, haka su Mahreen ma. Kan kace me ainahin masu aljanu a kai sun fara fa?uwa ?asa suna ihu, nan take wajen ya hargitse da masu aljanu da almatsotsai dukka, ihu sautin muryoyi kala kala ne suka fara kara?e kauyen gaba?aya.

Mahnoor kam gam ta ?an?ame bappa jikinta na kerma, shi kuwa Jaish da ba mayen bane sai ma har?e nannaye a saman faffa?ar kirjinsa ya yi yana ta kallon ikon god. Duk shakkarsa da Mahreen take ji bai hana ta ri?o hannunsa tana tambayarsa menene wannan ba?. Kallonta ya yi tare da yi mata alama da hannu a kan shi ma bai sani ba, hakan yasa ta yi shiru tare da ?an kwantar da kanta a hannunsa tana binsu da kallo, bata ta?a ganin irin hakan ba, dan da wayonta dai ba'a ta?a kama mayya ko makamancin haka a gabanta ba!.

Sai da gaba?aya masu almatsotsai a kai ?in suka sume a ?asa sannan Ar?o ya fito. Ba ?aramin tsorata ya yi ba a lokacin da ya fito ya ga Jaish a tsaye a kan kafafunsa, abin ya ru?ar da jama'a dayawa, wanda suke zaton shi ne mayen sai ga shi a tsaye cak a kan kafafunsa, wan?an da basu ta?a zato ba kuma sune suka zube ?asa matsayin masu lalurar. Abin ya ?aure masu kai, ya kuma jefasu cikin ru?ani, a maimakon su yarda da cewa Jaish fa mutum ne kamar su, amma ina sai ma suka sake kai abin gaba, a in da suka fara cewa ai Jaish shi ne shugaban mayun duniya gaba?aya, wai shi ne sarkinsu, dan haka wannan magani ya yi mashi ka?an ne shiyasa bai fa?i ?asa ba, sai sun nemo magani mai karfin gaske, dan haka dole su shiga kauyukan Cameroon wajen ?an uwansu sullu?awan fulani su nemo magani, sam sam su ba zasu ta?a yarda cewa shi ?in mutun ne ba, dan kyau ?insa fa daban yake, ga shi ya mari yaro ya fara ciwo kamar zai mutu.

Bappa dai da yake ya yarda da Jaish ?in ko a jikinsa, sai ma cewa da ya yi su wuce gida, ?acin ran kalmar da suke jefar Jaish ?in da shi ne yasa ya wuce gida ya manta bai ce da Ar?o a yi wa su Mahreen tsakani da su Salisun ba, ya mance suka wuce gida.

Da Ar?o ya dawo cikin gida ya gayawa su gwaggo Jaish fa shugaban mayu ne, wannan maganin ta yi mashi ka?an, wani irin tsoro ne ya ?ara kamasu, haba kan kace me sun shige cikin ?aki har suna rige rige, Innar Mahnoor ?in ce kawai bata gudu ba, kowa ya ?ara tsorata da lamarin aljanin Mahreen sosai. Shi kuma bawan Allah da Allah yasa ba jin fulatancin sosai yake yi ba, sam bai san me suke ciki ba, a tunaninsa ma wani al'ada ne nasu na banka haka?i a gari su saka mutane tari har da suma, shi bai ma san wasu halitta wai su mayu ba a duniya, tunani ma yake yi a kan wace iriyar al'adance wannan ta cutar da mutane da hayaki har su suma?........ Babbar magana, to jama'ar ruga shi fa Jaish bai ma san kuna yi ba bayin Allah, sai ku kara himma wajen banke kowa da hayaki kuna tonawa kanku asiri, ku yi maza ku kashe kowa sai naga waye zai gaji kauyen, yau ance wasu dayawa ne mayu a maimaikon Prince Jaish namu, gobe kuma sai a ha?a da Ar?onma mai gaba?aya..........??

Duk wani mayen da ya suma a wannan wajen Ar?o ya ce kashe shi za'ayi har lahira tun da su mugaye ne, nan fa kauye ya ri?ice, kowa sai cewa yake yi a'a wlh nasa ba maye bane, kawai ya suma ne, sun ki yarda a kashe masu ?an uwan nasu, nan fa Ar?o ya ce dole a kashesu, dan kuwa basu da amfani a cikin al'umma.

Su Mahreen dai gida suka wuce abinsu, Mahnoor ta je ta hau yi masu girkin dare da zasu ci. Nenne dai ta zama yar gidan Ar?o yanzu,............. A gaskiya Jaish kana wuta a kauyen nan, duk ka sanya jama'a bala'in tsoronka, mata sun bar gidan mazajensu sun koma gidan uba kamar babu mutuwar a can gidan baban nasu, duk saboda kai?..... To ni dai bari na le?a wani ?angaren.

__________________________??????

DARK WORLD????

Washegari da safe Ronnie ya tafi school, a tare da Floris Sweetie ta wuni, sai hira su ke yi, a nan Floris ta bata labarin iyayenta da suke a cikin birnin, sosai Sweetie ta sha madarar mamakin irin halin Ronnie, kawai ka ?auko ?ar mutane ka ajiyeta a nan haka ake rayuwa, su iyayen nata ai rashin addini ne duk ya ja haka, idan ba rashim addini ba yaushe zaku ?auki ?arku budurwa ku baiwa Ronnie ya dawo da ita cikin empeir ?in ya ajiye fisabilillah?. Ko da yake suna a ?ar?ashin ikon Black Tiger ne dole su bi ra'ayin Ronnie su bashi ?a.

Sai around 1:30 Ronnie ya dawo daga school, kai tsaye room ?in Sweetie ya nufo, a lokacin ta shiga cikin toilet dan yin alwala, Floris kawai ya isko a kwance saman gadon. Tana ganinsa ta mi?e zaune.

?ariso ciki ya yi, ?an rungumarta ya yi tare da bata sumbata a kumatu kafin ya zauna a gefen bedside drawer. "Hiran me kuka yi yau?". Ya fa?a murya a kasale.

Kashe mashi ido ?aya ta yi kamar yadda ya saba yi mata, da alama akwai abin da suke ?oyewa. Jinjina kai ya yi kamar mai sauraren wani abin mai da?i. Dai'dai lokacin Sweetie ta fito ta ?auro alwala. Kamar yadda ta saba yin sallah haka ta tsaya ta tada sallah ba tare da ta ce da Ronnie ?in ko uppan ba.

Binta da kallo shi da Floris suka yi, sun kasa iya cigaba da hiran da suke yi, sai kallonta suke yi har ta idar da sallar, addu'oi sosai ta yi tare da shafawa, sannan ta mi?e ta dawo kusa da Floris ta zauna. "Welcome Ronnie" . Ta fa?a a sanyaye.

"Queen of beauty ya naga kin ?ara kyau ne yau?". Tamkar bai san motsa lips ?insa ya yi maganar, sai ka ji tamkar shagwa?a yake yi, saboda a gajiye yake, ga kasala........... Ni kam nace ai dole ta ?ara kyau, dan kuwa ta samu hutu, ga Ac na bugata, sannan ga sabulai masu tsada, kwanciyar hankali ne dai kawai bata da shi, hankalinta gaba?aya yana kan ?ar uwarta Pretty and Kamran, amma ta samu abin da take fata kam dukka saura wannan.

Mi?ewa ya yi ya nufi waje tare da ce masu yana zuwa, dama Sweetie yake ta marmarin gani yasa yana dawowa daga school ya zarcu nan. Da sauri Floris ta mi?e ta bi bayansa suka bar Sweetie ita ka?ai.

Shiru ta buga tagumi tana tunani rayuwarsu a baya ita da su Kamran, har yau har gobe son Kamran yana nan a cikin zuciyarta, shi take buri da muradin gani, ance so mugun wasa, so tabarmar kaya, idan ka iya zama kaji da?i, akasin hakan kuma ka ji a jikinka.

Tana zaune a wajen bata motsa ba har Ronnie ya dawo hannunsa ?auke da trayn abincin kamar yadda ya saba kullum. Yau tracksuit ce a jikinsa daga wandon har rigar, launin ash color mai ?an duhu, ya yi wa kayan kyau, ya ?aure korean up white hairn sannan sai ya baro wani mai ?an tsawo ka?an a gaban goshinsa, ya ilahi, ni kam naga madarar kyau da ban ta?a gani ba a nan, Koreans fa akwai madarar kyau matu?a.

In da ya saba ajiye abincin ya je ya ajiye, tun da ya shigo take kure mashi kallo, har ya ?ariso gabanta, kamar dai kullum yatsunsa ya kyasta mata a saitin face ?inta ha?e da sakar mata lallausan murmushi mai narkar da zuciya.

"What are you thinking?". Ya yi maganar yana wani karyar da murya tamkar budurwar da ta shirya yaudarar saurayi ta kar?e mashi ku?i.

Macewa ta kara yi da kallonsa, ta rasa meyasa shi wannan Ronnien kome zai yi sai ya burgeta, abin ya fara bata mamaki, komansa gwanin birgewa da shiga rai, ga shi da shegen salo kala kala, yanzu idan ya yi maka wannan, to fa anjuma wani daban zai yi maka, sai ka rasa daga ina yake koyosu.

Ganin bata yi magana bane yasa ya matso kusa da ita tare da ciro tsadaddiyar ha?a??iyar wayarsa, ya saita camera ha?e da saita fuskokinsu ya ?aukesu a hoto yana fa?in. "Bari na ajiye tarihi, a duk cikin wa?an da yaya yake kawowa cikin empeir ?in nan dan bu?atar Spender daga wajensu babu wadda na ta?a kulawa ma bare mu yi hoto, gaskiya ke you're the best my queen". Ya kai karshen maganar tare da zama a gefenta yana jin wani irin burgesa da take yi yana ratsa zuciyarsa.

"Ronnie kai ?in kyakkyawa ne ajin farko". Ta fa?a kamar mai ra?a. Da sauri ya juyo da kallonsa a kanta, gera guda ya ?aga yana murmushi tare da ?an ?aga kansa sama, shi kansa yasan shi ?in kyakkyawa ne, amma idan kyawawan fararen tattabaru irinsu Sweetie suka fa?a cewa yana da kyau sai ya ji da?i sosai.

"Ronnie ina Floris?". Ajiyar zuciya ya sau?e tare da dakatar da murmushin da yake yi ya bata amsa da. "Floris ta tafi wajen wasa". Shiru ta ?an yi tana tunanin akwai wani abin a ?asa da yasa baya zama tare da ita da Floris waje guda, idan suna tare da Floris da zarar ya shigo Floris ?in zata yi dabara ta zulle ta bar wajen, idan shi ne yake tare da ita da zarar Floris ta zo zai mi?e ya fita ya ce yana zuwa, daga haka ba zai sake dawowa ba sai Floris ?in ta fita, kuma ita dai tasan da cewa ba fa?a ya yi da Floris ?in ba, to meyasa basu ha?uwa su uku su zauna su yi hira?. Ta jefawa kanta wannan tambaya da bata da amsarsa.

Ganin alamun ta shiga duniyar tunani ne yasa ya ce mata. "Come let's eat food first before you continue what ur doing, thinking thinking lady kawai".

Siririn murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Am okey, we eat together with Floris since 12:30".

?an lumshe idanunsa ya yi kafin nan ya sake warosu a kanta. "Ban yarda ba, let's go kawai my Queen, if not ba zan ci abincin ba nima". A shagwa?e sosai ya yi maganar har yana ?an turo baki.

Habawa shagala ta yi da kallonsa, in ya yi wannan shagwa?ar a gaskiya yana kifar da Gwamnatin mata da maza dake kallonsa.

Ta shagala da kallonsa bata ankara ba sai jinta ta yi a sama ya ?auketa cak, kai tsaye sai wajen da ya ajiye abincin ya direta. ?asa ?asa ya furta. "Meyasa kike son saka gown ne ke kam? Ki rin?a sanya kaya irin na beb Floris mana".

"Addinina bai aminta da irin wa?an nan kaya ba, addininmu ya ce mu suturta ko'ina na tsiraici a jikinmu, mu rufesa mu killacesa, dan duk abin da yake a bu?e ba abu bane mai daraja, mai daraja shi ne wanda ake rufe shi ruf babu wanda zai kallah sai mamallakinsa".

Shiru ya ?an yi yana tattauna maganganun nata, can kuma sai ya ?auko spoon tare da fara zuba abincin yana fa?in. "No ba haka bane, duk abin da yake bu?e ana ganinsa dole za'a fi sonsa, saboda kinga za'a ga kyansa har aji ana sha'awarsa, abin da yake ?oye kuwa ai ba wanda zai gani bare ya ji sha'awarsa"............. A wannan magana ta Ronnie fa idan kuka mayar da hankali da kanku zaku fahimci darasin da yake ciki, dan kuwa ya bu?e maku gaskiya ce a fili. Cewa ya yi abin da yake bu?e shi jama'a suke kallah har su ji sha'awarsa, me yake kawo zinace zinace? Amsar ita ce sha'awa, kenan kunga wani lokaci mu da kanmu muke jawo irin su fya?e a'a saurayi ya yaudari yarinya ya lalata da dai sauransu, ya ce abin da yake rufe babu wanda zai kallah ma bare ya yi sha'awa, na san nan kun gane ma da kanku ba sai na tsaya dogon bayani ba, dan haka duk macen da ta suturta kanta a ko'ina daraja ne da ita, Allah dai yasa mu gyara laifukan da muke yi na fili da na ?oye ya kuma yafe mana kura kuranmu. Amin.

Kawo mata abincin da ya ?eba a spoon ?in ya yi saitin bakinta. Bu?e bakin ta yi ya zuba mata, sannan ya tsareta da idanu yana kallon yadda take taunar abincin a hankali cikin nutsuwa. Sai bayan ta ha?iye ne ta bashi amsar sa da cewa. "Duk abin da jama'a zasu gani su yi sha'awarsa su kuma yi rububinsa kai kuma a matsayinka na mai zuciya me zaka yi da shi? Ai babu wata daraja a wajen abin da kowani shashashan kare da doki zai gani ya ji ya burgesa, wanda ya kai da wanda bai kai ba duk ya ji ta burgesa kenan? Hakan na nufin baka cika na daban ba kuma baka cika zakara a cikin empeir ?in nan ba kenan?!".

?ura mata idanu sosai ya yi har ta kai karshen maganar, nazari ya fara yi a kan maganganun nata. Cigaba ta yi da cewa. "Idan har kai ?in zakara ne ko kuma kai na musamman ne to kamata ya yi komai naka ya fita na musamman, kamata ya yi ka nunawa jama'a da banbanci a tsakaninku, kamata ya yi ka zama cewa abin da kake so babu wanda ya isa ya gansa bare ma har ya so ko ya ji sha'awarsa".

Ban da kallo babu abin da yake binta da shi, kalamanta kamar sun yi tasiri a cikin zuciyarsa. Ganin ya nutsa cikin kogin nazari da tunanin yasa ta kai hannu ta kar?i spoon ?in hannun nasa. Nisawa ya yi tare da ?an kawar da kallonsa daga kanta alamar ya dawo cikin hayyacinsa kenan. Abincin ta cigaba da ?ebawa tana kai mashi saitin bakinsa, a hankali yake kar?a yana tauna.

Tabbas ta lura da yanayinsa gaba?aya ya canza, abincin ma taunarta kawai yake yi, amma ga dukkan alamu bata yi mashi ba.

Ta yi nisa cikin ciyar da shi ?in da take yi ta ji sautin dadda?ar sexy voice ?in nan nasa ya daki dodan kunnenta a in da ya ce. "Waye ya koyar dake abin da kika gaya mun ?in nan?".

A takaice ta ce da shi. "Addinina". Adadi ya maimaita kalmar, jinjina mashi kai ta yi alamar tabbatarwa ba tare da ta yi magana ba. Shiru ya yi suka cigaba da cin abincin har suka ?oshi sosai, bai sake yin magana ba.

Mi?ewa tsaye ya yi jiki ba kwari ya ce. "Ba zan gaji da rokan yaya da ya barki muje wajen wasa ba, yanzu ma bari na je na ro?esa ya barki mu je fili ki ga wasana da zan buga, zan ji da?in hakan". Yana kai karshen maganar ya nufi waje ba tare da ya jira amsarta ba.

Da kallo ta bi bayansa tana mai cigaba da yabawa tsantsar madarar kyau da Allah ya yi mashi, ga tsawo da fa?in kirji irin nasu na ?an Wrestling. Tana zaune a wajen har ya je ya dawo. Fuskarsa a ?auke da annashuwa, da alama yau dai ya yi nasara sosai.

Yana zuwa ya ja hannunta da nufin su tafi. "Ka tsaya na gyara ?akin mana". Ta fa?a a hanzarce.

"No ki barshi za'a gyara". "To ka bari in ?auko wani abin na rufe gashin kaina". Nan ma a'a ya ce mata, daga karshe ma sai ya ?agata cak, shi fa da alama yana jin da?in ?aga ?an'mata kyawawa sama.

Kai tsaye wajen wasa ya nufa, yau wasan takalmin taya zai buga, su shiddane dai'dai zasu yi gasar, dukkansu sanye suke da tracksuit masu bala'in kyau da tsada, sai dai na Ronnie ya fi nasu kyau, dan shi na musamman ?in na musamman ake buga mashi, tun daga company design ?insa daban dana kowa, babu kuma wanda ya isa ya sa ayi masa irin nasa ya sanya, idan ya yi hakan zai fuskanci mummunar hukunci daga hannun Black Tiger, hakan yasa ba wanda ya ta?a kwatantawa ma.

Gaba?aya ?an wasan jikin kayansu wajen cikinsu an rubuta number, kowa da numbersa, na Ronnie shi ne number one, shiyasa yau kuka ga ya ?aure gashin kansa, dan ya ji da?in gudu.

Yana sako kafarsa a filin aka fara ihu ana tafi ha?e da fito, a kujeransa da yake zama kallon wasa ranar da ba zai buga ba ya zaunar da ita, Floris tana gefen master Devil tana aikin yin tapi jaruminta Ronnie ya shigo fili.

Takure jikinta waje guda Sweetien ta yi, ba komai yasa hakan ba kuma face master Devil da ta gani, tana bala'in tsoronsa, bare ma kirar jikin nan nasa dole aji tsoronsa, shekaru da dama yana Wrestling, yanzu kuma ya dawo horar da ?an Wrestling ?in, ai kunga dole ya razana du?ata, dole hantar ciki ta ka?a da ganinsa!!.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull