Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 45
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 45: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 45. Fili Ronnie ya nufa, bayan ya tsaya a bayan red line dake zane a gaban…
3,287 words
Fili Ronnie ya nufa, bayan ya tsaya a bayan red line dake zane a gaban dukkannin ?an wasan ne ya ?ago da kansa tare da ?ara ?aure fuskarnan tamau tamkar bai ta?a yin dariya ba a rayuwarsa. Kallonsa ya kai kan Sweetie dake ta kallonsa tamkar zata taso ta zo ta manna mashi hut rumguma, ji take kamar ta ganta a gabansa kawai.
Kashe mata ido ?aya ya yi fuska a ha?e, hakan wani irin cool murmushi ya sanyata saki ba tare da ta san lokacin da ta saki ?in ba, saura ka?an ta sanya shi yin murmushin shi ma, sai kuma ya sake dakewa ya ?aure fuskar tamau.
Wannan abin da suka yi kuwa a kan idanun master Devil suka yi shi, hakan yasa master ya jinjina kansa tare da fara tunanin Ronnie yana son ji?a masu aiki, dan kuwa in dai suka barsa ya saba da Sweetie to tabbas ba zasu samu abin da suke so cikin da?in rai ba, dan ba zai barsu su azabtar da ita har sai ta bu?i baki ba, zai rin?a shiga tsakaninsu ya yi ta yi masu kuka har sai sun hakura sun rage mata azabar da suke kan tanada mata idan bata basu Spender ba, hakan yasa master ya mi?e ya nufi cikin gida, da alama wajen Black Tiger zai je.
Shiryawa ?an wasa suka yi, wasu irin hut luxurious taya shoe aka kawo masu, na Ronnie ya fita daban da nasu, dama na gaya maku ai shi kayansa daban da na kowa. Sanyawa suka yi a kafafunsu tare da yin ready.
Commissionern wasannin yana hura usir suka tashi a guje kamar zasu fasa kirazansu saboda karfin gudu.
Nan take jama'a suka ?auki tafi ta ko'ina ha?e da fito, sai watsa flowers a sama jama'a ke yi, wasu sai rawa suke yi suna ile, kowa ihun sunan jaruminsa yake yi, amma a gaskiya ban ji sun ambaci sunan kowa ba face sunan Ronnie mai tarin uban masoya ta ko'ina.
Gudu suke yi tamkar masu gudun cetar rai, ga tayan takalmar nasu ba'a magana.......
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 22/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
26
Gudu suke yi tamkar masu gudun cetar rai, ga tayan takalmar nasu ba'a magana.......
Mi?ewa tsaye Floris ta yi tare da ha?e hannayenta dukka biyu ta ?aura a saman kirjinta ta lumshe idanu tana fa?in Jesus yasa Ronnie ya yi nasara.
Da kallo Sweetie ta bita tana mamakinsu, ita dai bayan addinin musulunci bata san yadda ake yin kowani addini ba, sauran addinan ma mum ?inta ta basu labarinsu a lokacin da take koyar da su karatun Alkur'ani mai girma, a lokacin tana basu tarihin annabawa da yadda magabata suka sha gwagwarmaya duk da cewa gobenmu ta yi kyau, ta hakan tasan cewa akwai wasu addinai na daban bayan musulunci, amma bata san ya ake yi sun ba.
Kowa da yake cikin wannan fillin addu'a yake yi a kan Ronnie ya yi nasa, duk da sun san cewa kullum shi yake zuwa na ?aya, har yau babu wanda ya kai kusan shi ma, amma abin ya zame masu jiki yi mashi addu'a a ya yin da yake buga koma wace iriyar wasa ce.
Number one dai shi ya zama number ?in kamar kullum, ihu da fito a wajen jama'a ba'a magana, tamkar ma?oshinsu zai ?alle. Ita kam Sweetie nata idanu kawai..........
Kamar daga sama ta ji an ri?o hannunta, a hanzarce ta ?ago kanta dan ganin wanenen?. Wani irin razana ta yi ha?e da zaro idanu waje sosai, mutumin da ta fi tsoro a rayuwarta wato master Devil shi ne ya ri?o hannunta tare da yi mata alamar ta tashi su tafi.
Da sauri ta juyar da kallonta izuwa kan Ronnie da yake tsaye a saman wani irin shinfi?a mai kyau za'a sanya mashi tambarin zakara a wuya, shi dai a rayuwarsa yana matu?ar kaunar wasanni, yana kuma bugasu son ransa, Allah kuma ya bashi, kowace wasa zai buga shi yake zama zakara.
Tamkar zata ce ba zata bi master ba, sai dai tsoro ya hanata ko motsawa ma, jikinta har kerma ya fara yi, ta gaza iya sake juyowa ta kalli face ?insa, addu'a kawai take yi Allah ya juyo mata da kallon Ronnie a kanta, dan tana ganin cewa shi ka?ai ne zai iya dakatar da master daga ?aukarta su tafi.
Sai dai har ya jata suka fita daga wajen hankalin Ronnie bai juyo kanta ba, yana can yana kar?ar lambobin yabo kala kala, ga wata ha?a??iyar box mai girma da Black Tiger ya aiko mashi da shi a matsayin gift ?insa, sai yaba kyan box ?in yake yi duk da bai san me a cikinta ba, abi da ya sani kawai shi ne wajen box ?in ta yi mashi kyau.
Sai tafi jama'a suke yi, da sauri Floris ta sau?o izuwa cikin filin. Kai tsaye wajensa ta nufa, sam ita ma bata lura da cewa master ya tafi da Sweetie ba. A gefensa ta zo ta tsaya aka fara ?aukarsu hoto, sam yaki yarda a ?aukesa hoto da sauran ?an wasan da suka buga a tare, da Floris kawai ya yarda su ka yi hoton.
Tana zuwa da aka fara ?aukarsu hoto sai ya ?ago da kallonsa zuwa in da Sweetie take zaune da nufin ya kirata ita ma tazo su yi.
Wayam ya ga kujerar da take ?in babu kowa, zaro korean eyes ?in nan nasa ya yi yana kallon filin da kyau.
Wata ha?a??iyar tattabara ?ar siririya fara tas da ita zubin bebs ?in Dark world ?in take da shi ita ma. A gabansa ta zo ta tsaya, wasu kyawawan fararen ?an'mata su biyu ne a gefe da gefenta hannunsu ?auke da aword plate gift. Suna isowa gabansa matar ta kai hannu ta ?auko wani kyakkyawar aword towel ?an siririr mai tsawo, a wuyarsa ta nufo da nufin ta rataya mashi abin, ya fita tsawo sosai, kuma high heel sosai ta sanya a kafafunta, amma ina hannunta bai iya kai wuyarsa ta rataya mashi abin ba.
?an du?a mata ka?an ya yi ya rage tsawonsa dan ta sanya mashi, yana yi hankalinsa a kan jama'ar dake kusa da in da ya ajiye Sweetie, one by one yake bin mutanen wajen da kallo ko zai hangota, sai dai wayam bata ba alamarta. Wannan mata tana ?o?arin sanya mashi gold na girma wanda ita ce gold na winner wajen na 35 da ya ci a ?an shekarun nan nasa, awajen takalmin taya kawai ya ci 15, haka a sauran wasanin irinsu foosball da sauransu, ya tara ?anyen gwalgwalai dayawa, harta takalmar da yake sakawa wajen buga kwallo ta ?anyar gold ce wanda Black Tiger ne ya yi mashi gift ?inta lokacin da ya ?auki cup.
Bai bari ta sanya mashi wannan gold ?in ba ya sanya kai da sauri ya wuce tare da cire wanda ta sanya mashi a wuyar tasa ma ya ri?e a hannu. Kai tsaye wajen da ya zaunar da Sweetie ya nufa, sam hankalinsa baya jikinsa ita kawai yake tunani.
Sosai Floris ta yi mamaki, yau Ronnie ne ana karrama shi ya tafi ba tare da ya jira an gama ba? Kai abin da mamaki, to ina zai je?. Tambayar da take ta jefawa kanta kenan. Ganin ya nufi cikin gida ne yasa ta yi saurin barin wajen ita ma, bayansa ta bi zuwa cikin gidan.
Yana shiga ciki room ?inta ya nufa kai tsaye. Sai dai ko da ya je bata ciki, ai bai san lokacin da ya yi wurgi da gift dake hannunsa a tsakar ?akin ba, a hanzarce ya nufo waje. Yana fitowa suka ci karo da Floris da ta biyo bayansa.
"Beb what happened? Naga ka bar wajen taron lafiya?". Cikin sanyin murya ta yi maganar, dan ta lura tamkar hankalinsa a tashe, ta kuma san halinsa sarai, wlh idan ya fusata ransa ya ?aci ko master Devil ya bashi hanya a zafin zuciya, kun dai ga yadda yake rayuwa dasu so simple ga shi so silent, amma kada ku ga ?ayar zuciyarsa ta ?acin rai kenan, a wannan lokacin bashi da kyan gani, kun dai ga yadda ya ?a??allah Delisha duk da take ?awarsa, to wlh a haka ransa bai ?aci ba, da ya ?aci ina mai tabbatar maku Delisha ba zata rayu ba.
Sam bai amsa mata maganar tata ba, da alama kamar bai ji abin da ta ce ba, kai yasa zai wuceta. Da sauri ta sake cewa. "Beb are you okay? What's going on? What are you looking for?". A wannan karon a ru?e ta yi maganar.
A karo na biyun ma bai amsata ba, cikin zafin nama ya nufi part ?in Black Tiger kai tsaye, har wani irin zafi ya ji zuciyarsa tana yi mashi, ya saba da Sweetien sosai, ba zai ji da?i ba idan aka rabasu, kuma yasan tabbas Black Tiger ne ya ?auketa, dan kuwa idan ba shi ?in ba ba'a haifi mutumin da zai iya ?aukar ta ba, kai koma ba'a cikin empeir ?insa take ba, ko a iya cikin birnin take wlh babu wanda ya isa ya fitar da ita ba tare da izininsa ba, kada ku manta komai da suke yi a tafin hannunsa suke yi, Ronnie ya fi kowa sanin hakan, shiyasa ma bai tuhumi kowa ba ya nufi yayan nasa kai tsaye, yasan ko master Devil bai isa ya gwada mashi sani a kan black tiger ba, duk cikin birnin shi ka?ai ya san shi.
Abin da baku sani ba shi ne, duk wanda ya yi kuskuren shiga wannan ?akin da Ronnie yake shiga da sunan ?akin Black Tiger, duk wanda ya yi kuskuren shiga wannan ?akin shikenan an shafe babinsa, magana ta gaskiya in dai ka shiga wannan ?akin to fa ka tafi kenan har abada, wlh mutum baya rayuwa, Ronnie kawai yake iya shiga kuma ya fito lafiya lou, wani lokaci ya fito da farinciki idan ya shiga, wani lokaci kuma ya fito fuska a ?aure, idan abin ta yi tsamari ma har da hawaye yana iya fitowa idan abin tafi karfinsa, duk da haka baya ?aukar good 5 hours ba tare da ya ziyarci cikin ?akin ba, to me a cikinta kenan?.
A yanzu ma bai kula Floris ba kai tsaye ya nufi wannan ?akin, da yake ita Floris ?in tasan me tsarin wannan ?akin sai ta ja da baya tare da nufar parlon dan ta jira shi a can.
A wannan karon ya jima a cikin ?akin, ya ?auki a kallah awa ?aya da rabi kafin ya fito, fuskar nan tasa a ?aure tamau kamar hadari, kai tsaye wajen part ?in ya nufa.
A parlon ya isko Floris sai safa da marwa take yi tana jiran fitowarsa....... Yana fitowa ko kallon in da take bai yi ba ransa a matu?ar ?ace ya nufi nasa room ?in.
Da sauri ta rufa mashi baya, sai dai kafin ta iso ya banko kofar ya murza key ta ciki. ?asake ta tsaya a wajen tana mamakin abin da bai ta?a yi ba yau ya aikata, to me yake damunsa har haka? Ta jefawa kanta tambaya. Ganin babu mai bata amsa ne yasa ta ja ?afafuwanta, jiki duk a mace ba kwari ta nufi hanyar nata room ?in............
To fah me ya ?atawa Ronnie rai har haka? Me aka yi mashi? Ina aka kai Sweetien? Me zasu yi mata? Da alama nasu game ?in yanzu zai fara, sai ku gyara zama my people's, amma ni dai bari na le?a wani part ?in kafin mu dawo kan wannan cakwakiyar, dan su sai anyi masu shiri na musamman.
____________________??????
DUBAI
Sanyin Acn da yake a ?akin ne ya fara ratsa ?ashin jikinta har izuwa cikin ?argo, hakan yasa ta fara motsawa, kyawawan yatsun kafafunta dake motsawa ne ya ja hankalinsa.
A hankali ya furta. "I will call you back uncle". Yana kai karshen maganar ba tare da ya jira amsar da za'a bashi ba ya katse kiran.
Kusa da gadon da take kwance ya matso, three cuter and t-shirt mai laushi na shan iskace a jikinsa, ya yi kyau sosai, arab hairnsa ya sha gyara matu?a, sai tashin kamshi yake yi.
Number Dr Raj ya danna, short sms ya rubuta mashi tare da tura mashi, sannan ya zauna a gefen bed ?in yana kallon face ?inta.
A hankali yatsun hannunta ma suka fara motsawa, tamkar wadda aka dannawa allura da karfi ya karye a cikin jikinta haka ta waro idanunta da suke jajir kamar wuta waje, idanun nan nata a kumbure sosai saboda kuka, gaba?aya from head to toe idan ka ganta sai ka tausaya mata, duk da tana sume kallo ?aya zaka yi mata ka fahimci lallai ba shakka a birkice take, sam bata da nutsuwa ko na second ?aya.
Mai da idanun nata ta yi ta datse su gam tare da fara fa?in. "Wlh zan yi, zan yi kome kuke so, kada ku cutar da rayuwata, wlh ni marainiya ce, ku ji tausayin maraicina............"
Shiru ya zuba mata idanu yana sauraron sambatun nata, ga dukkan alamu baya son ta?ata ta daina sambatun, kamar akwai abin da yake son ji. Sallamar Ummie a cikin room ?in yasa ta dakata da surutan da take yi, kai kallonsa kan room door ?in ya yi. Ummie ce da Sharifat suka shigo a tare. Da farko Ummie ta ce ba zata zo ta dubata ba, amma da Sharifat ta matsa mata sai ta hakura ta zo. Ummie fa har da launin fatar Leesharh da take chocolate yasa ta tsaneta ba iya dan tana zargin mijinta yana sonta ba, kun san wasu larabawan dama da tsanar bakake fata ba gaira babu dalili.
Zame ha?a??en white glass dake face ?insa ya yi, a hankali ya mai da kallonsa a kan Ummie dake ?o?arin zama a saman ha?a??un kujerun dake room ?in........... Da sauri Sharifat ta dawo kusa da ita, a hankali ta fara ruwan hawaye tana fa?in. "Leesharh ki tashi dan Allah, tun jiya fa nake ta kiran sunanki amma kin ki tashi............" Dakatawa da yin maganar ta yi sakamakon hannu da ya ?aura mata a saman lips ?insa alamar ta yi shiru.
A da?ile Ummie ta ce. "Ya jikin nata Bilal?". Shiru ya kafeta da idanu ba tare da ya amsa ba, dan kuwa mugun zarginta yake yi sosai, dama da shi da Ramish sam basu shiri da ita, shi Ramish dama baya shiri da kowa kamar wani aljani, gara Bilal ?in sau dubu.
Ganin bashi da niyar amsa mata ne yasa ta mi?e ta nufi waje, sai ?ari ?ari take yi, dan kuwa yadda taga ya tsareta da idanun nan tasan akwai wani abin a ?asa da yake zargi, nan take ta ru?e, tunanin kashe Leesharh ?in da suka shirya ita da hajiya two seater kawai ta fara yi, tasan su waye su Bilal ?in sarai, ita ta renesu, za?wa?uran jami'ai ne masu aiki da ?wa?walwa, tun da suka sanya hannunsu a kan Leesharh is better for her da ta janye ?udurinta, idan ba haka ba zata jawa kanta balai'n da dukka danginta babu mai iya tare mata, dan idan abin nasu ya motsa wlh ko maganar Abu Abdussalam basa saurara bare ta sa ran zasu ?aga mata kafa, ta san pata pata zasu yi da ita, bare ma Ramish da dama shi ba wani jin maganar mutane yake yi ba, idan ya tsara abu fa to sai ya yi shi, idan ya tsara abu yasan cewa King Zuhair ba zai aminta ba to wlh baya ta?a yarda ya yi magana da King ?in a lokacin har sai ya kammala abin da zai yi ?in sannan ya nemi daddyn nasa haka yake wannan tafiyar, a duniya mamarsa ce kawai take yi mashi magana ?aya baya bata hakuri bare ya ce zai kwatanta yin wannan abin, da zarar ta ce Ramish ka bar wannan abin bana so, to fa a lokacin zai share wannan abin daga ?wa?walwarsa ya ce ya barta har abada, ita ka?ai take yi mashi magana ?aya ba ?ari kuma ya bi cikin hanzari, uwa uwace, yana girmamata sosai.
Amma King idan ya ce mashi baya son abu ya rin?a takura mashi kenan har sai ya kyaleshi ya yi.
Ummie na fita Dr Raj na shigowa, saura ka?an ma su ci karo. Sannu ya yi wa Ummien tare da ?arisowa ciki ba tare da ya jira amsarta ba. Sanye yake da kaya irin na jikin Bilal ?in sai!.
A gaban gadon Leesharh ?in Dr ya zauna.
Kallon Sharifat dake ruwan hawaye Bilal ya yi. "Little tashi ki je room ?inki". Ya fa?a a sanyaye.
Mi?ewa tsaye ta yi tare da nufar wajen da Ramish yake kwnace, bawan Allah ya yi wani irin haske sosai a kan wanda yake da shi, ba shakka wannan magani da Leesharh ta bashi yana da tsananin karfi sosai, ya sha wahala sosai ?an tahali?in nan, ga shi sun ?oyewa King Zuhair abin da yake faruwa, saboda sun san King yana matu?ar kaunar ?a?an nasa, idan ya ji labari komai zai iya faruwa, shiyasa suka ?oye mashi, dama idan baku manta ba a baya ya bu?aci su Ramish ?in su je, kunga a kan washegari zasu tafi ne wannan abin ya faru, shi ne Bilal ya sanar da King ?in anyiwa Ramish kiran gaggawa a wajen aiki ya tafi, dan haka sai ya dawo zasu zo, to a haka suka rabu da King ?in lafiya, basu je sun duba jikin Mama ba har ta warke. Sai dai abin da basu sani ba shi ne tabbas King ya san komai da yake faruwa dangane da su, dan kuwa yadda yake bibiyar rayuwarsu yana kula da su tabbas ko kansa baya kula da shi haka, duk wani abin da suke ciki yana sani, ya sanya masu kula da matakan tsaronsa a matsayinsa na uba na gari, su sam basu san da hakan ba duk da suke jami'ai, shiyasa wanda ya haifeka fa komai iliminka komai baiwarka da wayonka sai dai ka gwadawa wasu ba dai shi ba, dan kuwa shi dai a tsirara yake kallonka ato, gara ma mutun ya san da hakan.
King yasan komai, yana da niyar yi masu dirar mikiya a Dubai ?in ne ma wannan yaki ya riskesu, da zuwan bazata zai masu, a tunaninsu sun ?oye mashi.
A kansa ta ?an tsaya tana kallon face ?insa, har cikin ranta take bala'in kaunar Ramish, mafarkinta a kullum su yi aure, Allah sarki shi kuma bai ma san tana yi ba, bashi da ma wata kusanci da ita, yasan dai yana da kanwa mai kawo mashi abincin, sannan autarsu a gidan, shikenan, ba kaunar uwarta ma yake yi ba bare ace ita ma zai kaunace ta, uncle nasu kawai suke so ?an albarka.
Dr Raj ne ya ce mata. "Little zaki iya tafiya ba wata damuwa kin ji?". Jinjina kai ta yi tare da nufar waje da gudu saboda wani irin kuka da ya kubce mata. Duk abin da ya faru a kan idanun Leesharh da tun ?azun ta dawo cikin hayyacinta ya faru. Tabbas tasan da cewa Sharifat na son Ramish, ta gaya mata tun lokacin da suka koma kwana ?aki ?aya, a lokacin ne ta fara nadamar abin da ta yi wa Ramish ?in, saboda ba karya Sharifat ta nuna mata kauna na wuce misali, idan ta cutar da Ramish tamkar ita ta cutar, a yadda ta kaunacetan nan kuma wlh tasan idan ta cutar da ita Allah ma ba zai kyaleta ba.