Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 46

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 46

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 46: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 46. Idanunta ne suka cike tab da kwallah, ta ji matu?ar tausayin Sharifat ?in…

3,347 words

Idanunta ne suka cike tab da kwallah, ta ji matu?ar tausayin Sharifat ?in matu?a, mayar da idanunta ta yi ta datse su, zafafan hawayen da suka cika idanun ne suka fara bin gefen ?uncinta da ?uminsu, ta rasa mafita, idan ta juya gefe guda babanta, idan ta juya zata aiwatar da aikinta dan ta ceci baban nata kuma sai ta tuna Sharifat dake da tsohuwar soyayya a zuci, in ta ja Ramish ya mutu ya Sharifat ?in zata yi? Tasan zata cutu matu?a. In ta juyo ta wani gefen kuma Abbie bawan Allah ya nuna mata kauna, shi take tunawa, duk sai ta ji tamkar ta kashe kanta kawai ta huta, ta gaji da wannan azaba, kullum bata cikin nutsuwa, zuciyarta cike da ciwo matu?a, kullum tana cikin tashin hankali da fargabar asirinta zai tonu!.

Kallon Dr Raj Bilal ?in ya yi. "Dr i think Ummie ce ta azabtar da yarinyar nan, dan a sambatun da ta yi lokacin farkawarta tana ambatar aji tausayin maraicinta a kyaleta, kaga kuwa hakan na nufin wani daga cikin gidan nan ne ya yi mata wannan aika aikan!"............. Tab tashin hankali, wato shi Bilal ma zargin Ummie yake yi a kan ita ta fasawa Leesharh kai? E lallai kuwa, Leesharh tana zarginsa a kan yana tare da masu nikaf, dan yanzu ta gane cewa wlh shi ta gani a gidan masu nikaf, wlh shi ne ba kama ba, domin kuwa farfa?owar da ta yi jiya kafin ta sake suma ta ga kayan da ya sanya ya je gidan masu nikaf shi ya sanya a jikinsa jiyan, ya fito a sak yadda ta gansa, sannan yana da zanen kunama a wuyarsa, kuma ta ga zanen, kai wlh shi ne ya je wajen masu nikaf, kunga ita tana zarginsa a kan da sa hannunsa wajen kashe Ramish, shi kuma yana zargin Ummie wajen cutar da ita, tab akwai cakwakiya, idan kuwa haka ne an samu babbar matsala ba ka?an ba!

Amma meyasa duk zafin rai da zafin kai irin na Bilal ?in daga kallonta a karon farko ya yi mata saukin kai? Meyasa ya za?i ya taimaka mata bayan su da basa yarda wani ya ra?esu? Su da basu yarda da kowa ba?! Har ma yake zargin Ummie a kanta! Meyasa ya ?auketa da mahimmanci lokaci guda haka?. Sannan kuma ta wani ?angaren idan har yana son cutar da Ramish meyasa zai taimaka mashi a lokacin da suka zo kashe shi? Meyasa ya shiga damuwa sosai na rashin lafiyar Ramish ?in? My people's akwai matsala fa, wannan cakwakiya ta kusa sanya ?wa?walwata ta ?auke ?if na wucin gadin.

Mu koma baya ka?an dan jin abin da ya faru. Abin da baku sani ba Bilal ne ya shiga ?akinta dan ya yi magana da ita ya ganta kwance cikin jini, shi da tun da Allah ya yi Sharifat a cikin wannan gidan bai ta?a taka kafafunsa ya shiga ?akinta ba sai jiya wai yana son ganin Leesharh, shi ne ya je, idan baku manta ba a lokacin ta baro part ?insu ba jimawa masu nikaf suka kirata, to ya biyo bayanta kenan, yana shigowa ya sameta kwance a ?asa cikin jini, kanta a fashe saboda bugasa da bango da ta rin?a yi, a hanzarce ya ?auketa cak zuwa room da Ramish yake kwance, a nan ya sanya Dr Raj ya bata taimakon gaggawa, da yake kanta ta rin?a bugawa sai yasa jinin nata ya yawaita zuba, a jiyan ta farfa?o ta sake sumewa, dan ciwo a kai ba karamin abu bane. Wannan shi ne abin da ya faru, tsayuwa tsayin daka a kanta Bilal ?in ya yi har sai da Dr Raj ya kasa danne hakurinsa ya ce mashi wai ko ya san yarinyar nan ne da ya tsaya tsayin daka a kanta haka? A'a ya amsa da shi tare da ?aurawa da cewa kawai tausayi take bashi.............. To mu koma kan labarinmu tun da mun ji ya aka yi Bilal ya taimaki Leesharh!.

Siririn tsaki Dr Raj ya ja tare da sanya hand gloves a hannunsa ya kwaso wasu allurai da nufin ya ha?a ya yi mata, dama jiran farfa?owarta suke yi ya yi mata allura.

"Dama kai Yah Bilal ka yarda da Ummie kenan? Ai ko dan wa?an nan shashashun friends ?in nata da suke zuwa gidan nan ita ba abar a yarda da ita bane, tsab zata iya cutar da ?ar mutane, kasan dai babu wata maikaciya a gidan nan da zata yi wa wannan yarinyar irin wannan rauni, dole Ummien ce mana".

Shiru ya yi kamar mai nazarin wani abin. Kamar daga sama idanunsa suka sau?a a kan Ramish, a hankali ya ga yatsun hannunsa suna motsawa, a lokacin kuma Dr Raj yana ?o?arin yiwa Leesharh allura, ai tana jin za'ayi mata ta waro idanunta waje, da a tunaninsu barci ma take yi shiyasa suka tsaya suna hiran Ummie a wajen, ashe basu san ta ji komai ba. Tana bu?e idanu sai kan alluran hannun nasa idanunta suka sau?a. A ?ari ta yunkura zata tashi, dan tana tsoron allura kam sosai.

Da kallon mamaki Dr ya bita tare da daure fuska sosai kamar ba shi ba, dama dan dole Bilal ya sanyasa kula da lafiyarta. "Gyara na yi maki". A dake ya yi maganar, irin babu wasa a tartare da shi ?in nan. Jin ya yi magana yasa Bilal dawo da kallonsa a kansu, sai gani ya yi Leesharh ta manne da bango dan bata son ayi mata alluran, ga shi kuma ba zata iya mi?ewa ta gudu ba, jikinta dukka tamkar an ?aure mata shi da igiyoyi.

Motsawa ga??an jikin Ramish suka cigaba da yi, nan take bugawar zuciyarsa ta fara aiki daidai wa dai'da, sautin numfashinsa ya fara dai'daituwa, hakan yasa duk suka kai kallonsu a kansa jin na'urorin dake wajen bed ?in nasa sun fara ?ara. Cikin zafin nama Bilal ya fara isa wajensa, shi ma Dr ajiye alluran hannunsa ya yi suka nufi ?an uwansu. Ajiyar zuciya Leesharh ta sauke, dan a tunaninta sun fasa yi mata alluran ne.

Suna isa Dr ya fara aikinsa, shi kuwa Bilal cikin ?aguwa da tsananin kaunar ?an uwan nasa ya fara ambatar sunansa a hankali a cikin kunnensa. Kamar daga sama a hankali ya ji Ramish ?in ya amsa da. "Yes blood".

Wani irin annashuwa ne ya bayyana a saman face ?insu, wani irin sanyi suka ji, tsabar da?i Dr bai san time ?in da ta furta. "Yes, oh my god, Allah Alhamdulillah, Alhamdulillah!".

Shi kam Bilal matsowa ya yi ya rungumi Drn, dan ya rasa ina zai tsoma kansa saboda murna. Sautin muryar Ramish ?in yasa suka raba jikinsu da juna suna sauraron me zai ce dasu. Girgiza kai ya fara yi a hankali, idanunsa a rufe ruf ya fara fa?in.

"Bilal don't let this people's to go anywhere, kill them all, the hut me to much.............." Bai ?arisa maganar ba tari ta kwacemashi wanda ya yi sanadiyar waro idanuwansa da suke kamar wuta waje. A hanzarce ya mayar da idanun ya datsesu, saboda wani irin haske da ya kashe mashi idanu, ya jima idanun a rufe ruf shiyasa, ga idanun sun kumbura sosai sun yi jajir kamar ba wa?an nan idanu kyawawa irin na King ba.

Da sauri suka yi kansa, Dr yana ce mashi ya yi shiru kada ya yi magana, shi kuwa Bilal yana gaya mashi ai bai bar mutanen sun tafi ba, ya kamasu dan haka ya kwantar da hankalinsa ya yi shiru kada ya sake yin magana dan kada ya ja wani ciwon ta tashi kuma.

A hankali ya sake gwada bu?e idanun nasa. A wannan karon ma haske ne ta kashe mashi idanun, sai dai bai rufesu ba, ya barsu a bu?e har lokacin da haske ya ?an washe, sannan ne ya fara iya ganinsu Bilal ?in.

Yana ?aura ganinsa a kan Bilal ?in ya sauke wani nannauyar ajiyar zuciya, har cikin ransa ya ji wani irin sanyi ta ratsa shi na ganin ?an uwan nasa, Dr Raj fa shi ne ?aninsa da suke uwa ?aya, amma ga dukkan alamu ya fi kaunar Bilal, bai yi farincikin ganin Dr kamar yadda ya ji wani irin sanyi lokacin da ya ?aura idanun a kan Bilal ba.

Hannunsa dake ?aure da drip ya bu?ewa Bilal ?in. Da sauri ya kai hannunsa saman hannun Ramish ?in suka ha?a hannu, saman shoulder ?insa Bilal ?in ya damko tare da ?an jijjigasa alamar ya cigaba da kasancewa da jarumtarsa, jinjina kansa Ramish ?in ya yi alamar In Sha Allah jarumta a jininsu take, Dr Raj dai ya zama ?an kallo, ya tsaresu da idanu kawai yana kallonsu.

Ita ma Leesharh tv ta mayar da su, wani irin abu ta ji a kan Ramish ?in, kura mashi idanun sosai ta yi tana kallon yadda yake magana ?asa ?asa da Bilal, wani irin jiri ne ta ji ya wani ?ebeta, ta rasa gane irin wannan wahalallen cakwakiya, kenan shi Ramish yana bala'in kaunar wanda yake neman rayuwarsa fiye da ?an uwansa da suka fito ciki ?aya ba tare da saninsa ba? Anya kuwa hakan zai yiwu? Ko da yake mutun fa ko ya mutu sai an ?auresa, Allah dai yasa mufi karfin zu?atanmu.

Nan take Dr Raj ya hau kiran ?an uwansu a waya yana sanar da su ?an uwansu ya farfa?o kuma ya farfa?o ba tare da wata matsala ba, sai dai jikin ne da za'a cigaba da kula da shi har ya ?ara warwarewa. Murna a wajen su Yah Rizwan ba'a magana, Abbie yana jin wannan labarin ya baro office ?insa ya dawo gida, kan kace me gida ya cika tab da family, su uncle Rahab duk sun zo, Sharifat sai kuka murna ake yi masoyi ya farfa?o.

Duk wanda ya zo gidan sai ya tambayi wacece Leesharh? Tun Abbie nacewa Allah ne ya kara mashi kyautar ?a bayan Sharifat har ya gaji da basu amsa. Mahaifiyar mommar Gimbiya Zunaira wato uwar gidan King Badeen ce da ta samu labarin Leesharh ta ce a kawo mata ita zata ri?eta, dan ita a yanzu babu wata ?a a gabanta, su Obaid and Omaid ne kawai suke gabanta, su kuma kunga suna school, sai an yi hutu suke dawowa, ko sun dawo kuma Tunisia suke tafiya yin hutunsu, basu wani zama da ita, dama tana neman yarinya mace dan su rin?a zama a tare tana ?ebe mata kewa, idan baku manta ba Momma ce kawai yarta mace dama.

Nan fa Abbie ya ce shi dai a'a bai yarda ba, a barmashi ?ar marainiyarsa ya ri?e abarsa, ba yadda ba'ayi ba ya ce ina Leesharh shi zai ri?eta. Yadda ya kafe a kan babu in da zata je ne yasa Ummie ta ?ara tsananta zarginta a kansa, wani irin bakinciki ne ya rufeta, fa?i take wlh ko zata mutu sai ta san ta yadda zata yi Leesharh ta bar mata gidanta.

A takaice dai Leesharh ta yi tarin masoya, da alama tana da farinjini sosai, kowa son ?aukarta yake yi Abbie ya hana, Ummie ce dai ka?ai bata sonta.

Kwana uku a jere family suna tururuwar zuwa duba jikin Ramish, a kwana na ukun ne ya tashi, dan ya ce kwanciya ta ishe shi, ya ?an samu karfi ya tashi, yana tashi kuma ya fara shirin komawa bakin aiki, ba yadda basu yi da shi ba ya ce ina dole ya koma bakin aiki, dole a koma bakin rai bakin fama. In takaice maku dai dole suka ha?ura suka kyalesa, dan sun san kome zasu ce sai fa ya koma kamar yadda ya yi niya.

Leesharh kuwa ta samu lafiya sosai, dan Bilal yasa Dr Raj ya bata kulawa sosai. Daga haka suka koma bakin aikinsu kamar yadda suka saba, batun zuwa ?asar Tunisia dai sun shafeshi, sun ji labarin harin da aka kaiwa King, amma jin cewa daddyn nasu ya yi nasara sai suka ce to ai ba sai sun je ba, suka cigaba da abin da suka saba yi............????

_________________________________??

KINGDOM OF POWER.??????

Mu koma mu duba yadda aka yi Hoorain ya fita daga cikin gonar nan bayan an kai masu hari!!.

Fafatawa ya fara yi da mayakan nan, yana kashesu wasu suna shigowa, abin mamakin kuma duk wani warriors da zai shigo wajen Auta kawai yake hara, ita ka?ai suke son kamawa, abin tun bai dami Hoorain ?in ba har ya fara ?aure mashi kai, meyasa shi basu kawo mashi hari sai ita? Ya jefawa kansa tambaya. Wani maya?i ne da ya kusa cin galaba a kanta a in da ya zo datse mata wuya Hoorain ?in ya kare mata da nasa takobin, amma duk da haka sai da wukar ta ta?ata a saman shoulder ?inta, ya yanketa sosai, hakan yasa ta kurma ihu mai sauti, kan kace me jininta ya fara bulbula daga wajen.

Haba idan ran Hoorain ya kai dubu to fa ya ?aci a wannan lokaci, wani irin tafasa da zuciyarsa take yi mashi ne yasa a tsananin fusace ya ?aga takobin nasa ya raba wannan warriors ?in gida biyu, nan take ya fara yi masu yakin a haukace, kashe su kawai yake yi tamkar mai kashe karnika ba mutane ba, ransa ya kai kololuwan ?acin rai.

Da suka ga ya haukace masu kisa kawai yake yi babu kama hannun yaro sai suka fara yin ta kansu, kowa ya fara gudun cetan ransa. Bai bi ta kan Autar ba ya raka warriors ?in da gudu yana yi masu kisan ?as?anci da wala?anci, pata pata ya rin?a yi masu ?aya bayan ?aya sai da ya tabbatar ba mai sha?ar iskar numfashi a cikinsu, sannan ne hankalinsa ya dawo jikinsa.

Jefar da takobin nasa ya yi ya nufe ta da gudu, tana zube a saman gwiwowinta, ta ri?e in da aka yanketa ?in tana kuka hawaye tamkar ruwa ya ?alle hanya ya fita, kunsan a guje zai fita ai, haka hawaye ke tsere a saman face ?inta. A guje ya taho, yana zuwa ya zube gwiwowinsa a ?asa a gabanta tare da kai hannunsa ya ri?o hannun nata.

Yadda jininta ke zuba ba ?aramin ?aga mashi hankali ya yi ba, jikinsa har wani tsuma yake yi ya kai hannu zai rago rigar jikinta ya ?aure mata hannun nata. Ai a ?ari ta ri?e rigarta da ?ayan hannun nata tana girgiza mashi kai a kan bata so kada ya yaga mata riga, dan an fara kirgan dangi kar ya kalle mata kayanta. Bai yi mata musu ba ya sake mata rigar tata tare da mi?ewa ya ?auketa cak suka nufi saman kujeran King, zaunar da ita ya yi, sannan ya kama sket ?inta zai yaga, nan ma a hanzarce ta ri?e ta hana shi.

Mi?ewa tsaye ya yi, ya shiga tashin hankalin da ta haifar mashi da ru?u, ji yake ana caka mashi wu?a mai kaifi a ?awon zuciyarsa, ita aka yanka da wu?ar amma zuciyarsa tafi tata jin ra?a?in hakan. Matsawa daga in da take ya yi, can gefe in da ba zata iya ganinsa ba ya nufa, yana jinta tana kuka tana fa?in. "Hoorain kada ka tafi ka barni, dan Allah ka dawo tsoro nake ji".

Sam bai kulata ba, ya tafi abinsa, zuciyarsa na ?una. Sai da ya tabbatar ya ?urewa ganinta sannan ya dakata a bayan wata bishiya, cire rigar mayaka dake jikinsa ya yi ya ajiye a gefe, nan take wani farar single ta bayyana a kakkarfar kyakkyawar surar jikinsa, tamkar yanzu ya ?are single ?in daga ledarta, haka ya cirota ya ajiye a gefe, sannan ya ?auki kayan yakinsa ya mai da jikinsa. Single ?in ya ?auka ya koma in da take.

Farar single tas haka ya sanya cikin wannan jini nata ya ?aure mata hannun, saboda zubar jinin ya yi yawa, sai kallonsa take yi tana kuka, sam yaki yarda ya ?ago su ha?a idanun, duk jikinsa jini shi ma, dan ya yi kisa ba karya.

Yana gama ?aure mata ya mi?e ya nufi gate ?in gonar, still dai a rufe. Haurawa ta saman katanga ya yi ya dira baya ya barota a ciki. Wani jibgegen dutse ya ?auko, kwa?on dake jikin gate ?in ya zo ya fara duka da wannan dutse yana son ?alleta. Duk wasu warriors a wannan lokacin suna harabar Kingdom ?in, hakan yasa har ya ?alle kwa?on ba wanda ya gansa. Allah ma yasa kwa?o guda ?aya suka sanya, sauri yasa basu rufe gate ?in da kyau ba, da kwa?i 6 ake rufe gate ?in da su, sannan a sanya mashi kuba, to tsabar sauri ko kubar ma basu sanya ba saboda sauri.

Ya yi sa'a yana ?alle kwa?on gate ?in ta bu?e, godiya ya yi ga Allah, sannan ya nufi in da take. Yana zuwa bai yi magana ba ya sa?eta sai saman shoulder ?insa, da alama yana cikin matsanancin ?acin rai, dan yadda yake taku ma zaka fahimci ran maza fa a ?ace yake.

A hanyarsa ta nufa cikin kingdom ?in ma sai ha?uwa yake yi da warriors ?in Queen Zarina, abin da ya kara kona mashi rai ya sanya shi fafata yaki cikin fushi kenan, duk mayakin da ya kama wani irin kisan wala?anci yake yi mashi na ?in karawa. Da kyar da su?in goshi ya iya samun dama ya ?ariso kusa da cikin harabar kingdom ?in da ita, a maimakon ya bi ta hanyar da zata sada shi da cikin harabar, sai ya kauce hanya, da yake kingdom ?in tana da girma kuma tana da kofofin sirri sosai a cikinta, sannan a matsayinsa na assistant commander kuma wanda ya yi wasan kasansa a cikin kingdom ?in ba wata hanya ta sirri da bai sani ba, dan haka sai ya ?ad da kafa.

Yau har cikin family part ya shiga da ita amma ta kofar baya. Yana shigowa ta kofar baya ya hango King Zuhair yana fita ta kofar gaba, wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da yiwa Allah godiya da Allah yasa babu wanda ya kamashi ya ta?a jikin Gimbiya har ma ya ?auketa, da sun yi katari da King ai shikenan kwanansa ta kare, dan da ya shiga ?ari uku ba uku ba.

Ciki ya shigar da ita, a dab kofar underground ?in ya sau?eta, sai shesshekar kuka take yi.

Hannu yasa ya kwance mata single ?insa da ya ?aure mata hannu da shi, sannan ya ce.

"Ranki ya da?e ki je ciki su momma suna wajen, nan shi ne mazauninsu a duk lokacin da aka kawo mana hari irin haka". Ya fa?a cikin kunar rai, har wani huci yake yi, da kyar ma ya iya yin maganar.

Kura mashi idanu sosai ta yi, ya kawar da kallonsa bai san su ha?a idanu. Fa?awa saman faffa?ar kirjinsa ta yi tare da ce mashi. "Nagode sosai Hoorain, ba zan ta?a mantawa da kai ba a rayuwata, dan Allah kazo mu gudu wajensu momma tare kada ka je mutanen nan su kasheka ka ji?".

Hannu yasa ya cireta daga jikinsa, yana tsaye kyam cikin jarumta. "A'a ranki ya da?e, ki je kawai kekam, nima zan je wajen Abbona, In Sha Allah babu abin da zai faru, amma dole na fita yaki kam!".

Kuka ta saka mashi mai sauti a kan ita ba zata yarda ya je yakin ba, dan kada a kashe shi a banza. Lallashinta dan dolensa ya fara yi, hankalinsa duk ya tafi wajen Abbonsa, da kyar ya samu ta yarda zata shiga ciki. Matsowa ya yi da kyar ya iya cire tiles dake wajen ya bu?e mata kofar sirrin da idan ba a cikin family kake ba ba zaka iya sanin wannan waje akwai kofa ba, shi ma dai kasancewarsa zakara abin alfaharin KINGDOM ?in ne yasa King ya yarda da shi sosai haka har yasan duk wasu kofofin sirrin dake masarautar.

Tana kukan bata son rabuwa da shi haka ta shige ciki, tsayuwa ya yi yana kallonta, tana tafiya tana waigoshi har ta kurewa ganinsa, sannan ne ya mayar da tiles ?in ya rufe bayan ya rufe kofar cikin kenan, ya mi?e tsaye cikin zafin nama, jininsa na tafasa ya nufi waje.

A nan ne fa ya je ya ?arawa maya?ansu kwarin gwiwa a in da suka shiga fillin daga gadan gadan har ya taimakawa Abbonsa. TO KUN JI ABIN DA YA FARU, MU KOMA KAN LABARINMU.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull