Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 47
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 47: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 47. Alhamdulillah kingdom of power dai ta yi nasara a wannan yakin, sai dai sun…
3,303 words
Alhamdulillah kingdom of power dai ta yi nasara a wannan yakin, sai dai sun rasa mayaka a kallah guda ?ari, amma gaskiya sun yi namijin ?o?ari ba ka?an ba, dan kuwa irin wannan yakin da aka shammacesun ai ba wanda ya yi zaton ma zasu yi nasara, sun ?in jajirtattune na ha?i?a gaskiya.
Bayan komai ya lafa ne kowa ya fara neman ?an uwansa, mayan?an Queen Zarina da suka kama kuma sai suka watsasu cikin gidan yarin masarautar sai King ya zo ya yanke masu hukuncin da ya dace da su. Commenters and Hoorain suka ja ragamar duba mayakan da suka rasa da kuma ?an uwan su wanenen, suka yi wa kowa adalci, suka ja ragamar har aka shirya mayakan aka kaisu makwancinsu na gaskiya.
Commenters and Hoorain suna da ?o?ari sosai, ga jajircewa matu?a, duk suka juri ?awainiyar kowa, wa?an da aka ?arnatar masu da duniya ma sun tarasu waje guda a kan idan King ya fito duk zai fito da dukiya a mayar masu da abubuwan da suka rasa cikin aminci.
A can ciki kuwa, sai da komai ya lafa sannan suka fito, Momma ce ta ja ragamar kula da su ita kuma, Akka dai ta ce a barta ta fita ta yi yaki, Momma ta rin?a bata hakuri. Amma fa Aunty MieMie da mijinta sun gwabza, Allah kuma ya tsare babu abin da ya samesu, yanzu da komai ya lafa ne suka shigo family part, dai'dai lokacin suma su momma suka fito waje, duk a ru?e suke saboda ganin Auta da suka yi da ciwo a jikinta, sannan an tambayeta ina su Yah Jawad da suka je nemanta? Ta ce ita bata gansu ba, me ya ji mata ciwo in kuma ta je? Nan kuma taki bada amsa, anyi anyi ta fa?i ina taje taki fa?a, da suka matsa mata ma sai ta ce masu ai daga part ?in uncle Abbas ta fito, tana ?o?arin dawowa nan ne wasu mutane suka tareta zasu kasheta sai wani mayaki ya taimaka mata, taki yarda ta kawo ko alamar sunan Hoorain a cikin maganar tata ma bare har ayi zargin wani abin, sai ta yi ma kamar bata san da wani Hoorain a duniya ba.
Uncle Taheer kanin mamane ya fara duba hannun nata zai yi mata ?inkin wajen, sai kuka take yi, Momma kuwa ficewa ta yi daga part ?in King da suke ?in ta nufi fada dan ta duba mijinta, da sauri Aunty MieMie ta bi bayanta, dan ita ma daddyn nata kawai take son gani a halin yanzu.
Mummyn Gimbiya Chuchu ne ta ce da uncle Taheer. "Attaheer ina su Jawad da chuchu ne?". Sai a lokacin suka farga suma basu dawo ba. Ita ma Momma ta je fada King bayanan, babu shi babu labarinsa. Ai idan hankalinta ya kai dubu to gaba?aya ya tashi, nan take ta shiga ru?u. Dakarun dake gadin fadan ta umarta da su kira mata commander Zafar yanzun nan.
Aunty MieMie da yake irin matan nan ne masu zubin halittar ru?ani, nan take ru?anin nata ya ninninka na momman, kun san akwai masu irin zubin halittar ru?ani, wanda ko hankalinsu a kwance idan suna magana sai ku gansu kamar a ru?e suke, akwai su sosai a cikin mutane, to ita ma haka zubin halittarta yake.
Commander na zuwa Momma ta gaya mashi dalilin kiransa. Cikin tashin hankali ya ce mata ai shi kwata kwata basu ha?u da King ba a wannan yakin, ai shi bai ma san King ya fito ba da ba zai barshi ya gwabza yaki ba. Nan take hakalin masarauta gaba?aya ya tashi, ba'a ga sarki ba ai kunga ba zaman lafiya.
Ba yadda ba'ayi ba Momma ta koma cikin gida kada ta fito wajen fada, amma ina taki yarda. A dokar Kingdom of power Queens wato Momma Mama and Mummy basu fitowa wajen fada, kullum suna cikin family part ko kuma iya fada kawai zasu tsaya, jama'ar da suke waje basa ganinsu, idan ma tafiya wata ?asa ko wani garin zasu yi motor da zasu shiga akwai tinted, sannan daga cikin family part suke shiga mota, babu wadda ta ta?a fita waje a cikinsu.
Amma yau ba yadda commander bai bawa Momma hakuri a kan kada ta fita za'a nemo King ?in ba, amma ina taki yarda, gani take yi kamar ta fi su idanun ganinsa......... A hanzarce ta nufi kofar fita, gaba?aya dakarun dake cikin fadar zaro idanun waje suka yi, dan sun san dokar masarautar, in ta fita tabbas King zai hukuntata.
Dab zata bu?e kofar da zai sadata da wajen ne daga bayanta ta ji ance. "Kada ki kuskura ki yi wannan gangancin Rahilarh!".
Ko bata juyo ba ta san mamallakin wannan muryar. Dan haka ba tare da ta juyo ba ta ce................
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 23/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
27
Ko bata juyo ba ta san mamallakin wannan muryar. Dan haka ba tare da ta juyo ba ta ce. "Gwaggo bayanan fa, bai dawo ba ne".
Akka dake tsaye a bayan nata ne ta sake maimaita mata abin da ta ce tun farko a akan ta koma kada ta kuskura ta fita waje. Rai a matu?ar ?ace, ba dan ta so ba ta juyo, kofar da zata sada ta da cikin gida ta nufa rai a ?ace.
Da kallo Akkar ta bita har ta wuce, sannan ta dawo da kallonta a kan su Commander dake tsaya, umartarsu ta yi a kan su nemo mata ?anta, tana kai karshen maganar ta juya ta bi bayan Mommar.
A parlon King suka isko family, kai tsaye room ?inta Momma ta nufa, bata bi da kan kowa ba, bata jin kamar King ya rasu, infact bata jin kamar wani abin ma ya same shi, tana ji a jikinta yana nan lafiya lou, sai dai a ina yake to? Wannan shi ne matsalar.
Hankalin kowa a tashe, dan sun sami labarin King fa baya fada. Gaba?aya sun ha?e a main parlon har Aunty MieMie dukka. Mommar ma ta dawo parlon ta zauna shiru tare da buga uban tagumi. Akka dai babu ruwanta, hankalinta a kwance dan ta ce ita bata haifi tagwaye ba, dan haka ita jarumin jarumai ta haifa, kuma tana ji a jikinta yana nan dawowa, shiyasa kamar ba ita ta haife shi ba, bata wani damu ba.
A dai'dai lokacin call ?in uncle Jahiz ya shigo wayar Momma dake hannunta, sai a lokacin suka tuna da bayin Allahn nan.
Picking ta yi tare da karawa a kunnenta. Daga ?ayan ?angaren ya ce. "Amarya kullum amarya ce fa bakya laifi". Bata cikin mood mai kyau amma sai da ya sanyata sakin fuska kamar zata yi murmushi.
"Ban san yaushe zaka canza ba Jahiz". Ta fa?a tana kallon Akka. Carap ya capki maganar da cewa. "Babu rana, ba zan ta?a canzawa ba har abada".
?an siririn murmushi ne ya kubce mata, idan baku manta ba ita da su King ?a?an gwaggo da ?an kawune, akwai wasa sosai a tsakaninsu, shiyasa take yawan wasa da Jahiz bama dan kanin mijinta ba, ya ha?u da jini, har uncle Abbas idan kuka ji irin wasan da suke yi sai sun burgeku.
"Momma since one hour ago fa muna airport, sai kiran numbers ?inku muke yi bakwa picking lafiya?". Kai kallonta kan jama'ar parlon dake ta faman kallonta ta yi.
"Wato kenan shiyasa ka fara da amayar bakya laifi ko? Saboda kasan mun yi laifin na barinku a airport, to muna bada hakuri yanzu za'a zo ?aukarku".
Cool murmushi ya saki, da?insa da Momma akwai saurin gane abubuwa. "Tom shikenan ?ar kanwata na yafe maki". Ya fa?a cikin zolaya. "Jahiz Allah ka fita idona, banson yin dogon magana yanzu, ka kyaleni haka, amma kafin nan ka sani ni dai na haifeka ba kanwarka ba".
Kafewa ya yi a kan sam ita sister shi ce, dama sun saba tun kafin King ya aureta, sai ya ce ya fita shekaru, in ya je Dubai a gidansu yake tarewa dan neman magana, ya yi ta tsokanarta kawai, da kin ya aureta sai abin ya kara yi mashi sugar, ya ji da?in yin tsokanar da hujja.
"To shikenan dai ni kam, na yarda ke kanwata ce". Yana kai karshen maganar ya yi maza ya katse kiran dan kada ta ce ita yayarsa ce, hegen son girma ne da shi kamar me, wani lokaci ma sai ya ce uncle Abbas da ka?an ya girme sa, bayan kuma uncle Abbas ?in ya fisa da almost 15 years, shi fa 35 years yake da shi, ko aure bai ta?a yi ba, ga uncle Abbas da yake da Yah Rizwan mai 28 to 29 years, kunga ya kusa haifar Jahiz ?in ma ai, amma sai son girma kamar me.
Kallon uncle Taheer ta yi kafin ta ce. "Attaheer ka jagoranci zuwa ?auko su Jahiz a airport".
A hanzarce Mammien ta capki zancen da cewa. "Sun zo ne dama?". Kai Momma ta gya?a mata alamar e ba tare da ta yi magana ba.
Wani shu'umin murmushi Mammien ta saki tare da wurgawa Aliyah dake zaune kusa da mummyn Gimbiya Chuchu wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, ita dai ta zage sai ta ha?a Jahiz da Aliyah aure kamar dole, Aliyah ta ce King take so ana dolene wai?.
Tunani take yi tayadda zata ha?asu aure kafin ya koma Brazil, dan tasa baya ta?a wuce kwana biyu zuwa uku idan ta yi yawa in yazo.
Jugum jugum suka cigaba da zama a cikin parlourn, Auta ta yi barci saboda alluran da uncle Taheer ya yi mata, kowannensu da abin da yake tunani, uncle Abbas ma yana hanyar zuwa, saboda ya ji labarin abin da ya faru.
Muryar Yah Jawad ne ya kara?e kunnuwansu a in da ya yi masu cikakkiyar sallama ta addinin musulunci. A ?ari kowa ya kai kallonsa kansu, tare yake da Chuchu, tamkar basu san anyi yaki bama, dukkansu biyu sun yi wanka, Chuchu kayan Gimbiya Fanan ce a jikinta, shi kuma Jawad kayansa, da alama akwai in da suka tsaya suka kwana har zuwa wayewan gari.
Mi?ewa tsaye Momma ta yi tana fa?in. "Jawad ina kuka je? Ina kuka tafi kuka sanya mu cikin tashin hankali da jimami, tun daren jiya bamu da nutsuwa, mun rasa kwanciyar hankali da walwalarmu, babu ku babu daddynku".
?arisowa cikin parlourn ya yi tare da sake hannun Chuchu da yake ri?e da shi, da alama ta sha kuka dan ga idanunta nan suna kumbure jajir da su. A gefen Auta ya zauna, a maimakon ya basu amsar da suke dakon ji daga bakinsa, sai ya ce. "Momma menene ya samu Auta?".
Gaba?aya parlon binsa da kallo suke yi, Mammien dai da yake bata so dawowarsu a raye ba sai ta ha?e rai, ta ?asa hakuri da son jin daga ina suke ta ce. "Ana tambayarka daga ina kuke kana sake jefa mana wani tambaya?".
Dawo da kallonsa a kanta ya yi tare da cewa. "Daga part ?inki muke, a nan muka kwana".
Wani irin ?ululun bakin ciki ne ya tokare mata ma?oshi, danasani ta fara yi na barin gate ?in part ?in a bu?e da ta yi, duk sai ta ji dama bata tambayesa ba, yanzu amsarsa ya ?ona mata rai matu?a.
Ha?i?a Momma ta lura da cewa Mammie bata ji da?in bayyanarsu a parlon ba, sai dai bata munana mata zato wajen tunanin ko bata sonsu ne yasa ba ko tana yi masu fatan mutu, sai ta kyautata mata zato ta hanyar cewa kila dan basu dawo da wuri bane sun wahalar da zu?atansu wajen tunani ina suke ne yasa Mammien ta ji babu da?i har alamar jin haushin ganinsu ya bayyana a saman face ?inta.
Mummyn Chuchun ce ta ce. "Kai amma masha Allah, Allah mun gode maka da ka kare mana ?a?an nan namu, Allah ka kara kare mana su da kariyarka a koma ina suke".
Da amin dukka parlon suka amsa.
Kuka Chuchun dake tsaye bata iya ?arisowa cikin ba ta fara yi. Hankali a tashe Jawad ya tambayeta lafiya take kukan? Da kyar ta iya bashi amsa a kan saboda Auta take kuka. Hakuri ya shiga bata tare da gaya mata ai zata samu sauki.
?arisowa wajen Autar ta yi tare da kai hannu tana ta?a kumatunta tana mai cigaba da kwallah ha?e da sambatu ?asa ?asa.
Akka ce ta ce. "Zo nan Jannat!". Da kyar ta iya mi?ewa, kusa da ita ta je ta zauna, goge mata hawaye Akkar ta fara yi ha?e da lallashinta har sai da ta yi shiru.
Mummyn Gimbiya Chuchu ta sake cewa Yah Jawad. "Jawad zama bai kama ku ba ai, domin kuwa daddynku bai dawo ba".
Hankalinsa na'a kan Auta ya amsa da cewa. "Daddy ya tafi fillin kaka ai, mun ha?u da shi a lokacin da muke ?o?arin shiga part na dad".
Momma dake ?o?arin komawa ta zauna ne ta dakata tare da cewa. "Alhamdulillah, Alhdulillah ya Allah, to Allah ya dawo mana da shi lafiya". Gaba?aya suka amsa da amin, mummyn Gimbiya Chuchu har da sakin murmushi, nan take farinciki ya bayyana a saman fuskokinsu.
Akka kuwa cewa ta yi. "Meyakai Zuhair wannan wajen? Shin harin da aka kawowa masarautar nan tana da ala?a da wajen ne?".
A hanzarce Jawad ?in ya amsa da. "Gaskiya akwai ala?a, domin kuwa daddyn ya ce mun saboda Spender suka kawo wannan harin, kinga kenan Queen Zarina ita ma a yanzu ji take yi ta kawo karfin da zata iya kwatar Spender a hannun daddy".
Shiru gaba?aya parlon suka yi, can Mammie ta ce. "Amma dama Spender baya gidan nan ne?". Da wani irin kallo Momma da Jawad suka bita, tambayar tata ya yi kama da na wadda take son a kwace Spender daga hannun King, yadda kuka san ita ce ma ta turo a kwace, dan yadda ta ce dama baya gidan ne ya yi kama da kamar ta gayawa wasu cewa yana gidan ne dama. Sai dai kuma duk parlon Momma da Jawad ?in ne kawai suka lura da ita, ba wanda ya gane hakan. Akka kam ma sai cewa ta yi. "E Spender baya gidan nan, Zuhair ya kawar da shi daga nan saboda irin su King Abdulkarim".
Shiru ta yi kamar mai tunanin wani abin, sarai Yah Jawad ya lura da yanayinta ya canza kamar bata ji da?in cewa Spender baya nan gidan ba, sai dai bai kawo wani mummunar zargi a kanta ba.....
Spender a hannun King Zuhair? Black Tiger ya kama Sweetie saboda bukatar Spender? Queen Zarina ta turo a kwatar mata shi ta karfin tsiya! Me ala?ar wa?an nan mutane da suka ha?e wajen bu?atar abu guda? Ainahi shi Spender na wanenen? Kuma a halin yanzu ina ma Spender yake? Yana hannun wanene? Mu je dai zuwa akwai rikici a gaba!.
Shiru gaba?aya parlon ya yi, can Chuchu ta mi?e tare da fa?in. "Mummy bari na je nayi wanka, kayan Aunty Fanan ?in nan sun yi mun yawa, so nake in ciresu".
?an satar kallonta Jawad ya yi ta wutsiyar idanu, dama ya yi mamakin tun da suka shigo bata wuce nata room ?in ba, dan ita ta takura mashi su dawo cikin ?an uwanta dan ta yi kwalliya ta sanya kayanta, ba dan haka ba bai yi niyar dawowa yanzu ba, ya yi niya sai da rana zasu dawo, ya fi son ya ajiyeta ya yi ta kallonta yana samun nisha?i kawai.
Daren jiya kwana ya yi bai yi barci ba, zama ya yi tana barci yana gadinta, saboda gani yake kamar maya?an Queen Zarina zasu shigo su cutar da ita, shi bama ta kansa yake yi ba, ita yake tunawa, tana barci yana ta kallon face ?inta, Allah ya gani yana kaunarta fiye da kansa, ko ganinta da ido kawai ya yi yana tsintar kansa cikin matsanancin farinciki sosai.
Amsa mata da okey mum ta yi, da sauri ta wuce sai satar kallonta yake yi, shi fa baya gajiya da ganinta sam sam. Aneesa da Fanan ma a tare suka mi?e suka fita waje, suna fitowa Fanan ta ce. "Wai Aneesa ina Yah Jaish ne? Kwana biyu ban sanyasa a idanuna ba, ko ya yi tafiya ne?".
Girgiza kai ta yi tare da cewa. "E to ya yi tafiya sai dai kuma na ji dad da momma suna magana a kan ansamu matsala a tafiyar tasa, in da ya ce zai je an duba baya can, babu kuma wanda ya san in da ya tafi, yana lafiya ko yana da matsala ba wanda ya sani, yanzu haka dad ya ce su Yah Ramish su fara binciken ina yake, momma kuma ta ce a'a ya bari zata sanya yayanta ya nemosa, hakan zai sa cikin ?an?anin lokaci a gansa". Idan baku manta ba na ta?a gaya maku cewa duk wani labari idan kana son sani to ka tambayi Aneesa zaka sami bayani dallah dallah kamar wata aljana, sai ka rasa a ina take samo gaskiyar labarai wa?an da babu alamar karya a cikinsu, komai yadda ya faru take fa?a, yanzu batun ?acewar Jaish daga Momma sai Yah Jawad and Dad ne kawai suka sani, amma kunji ita har ta samu labarin da mamanta ma bata sani ba.
Zaro idanu waje sosai Fanan ta yi, nan take ta yi narai narai kamar zata yi kuka, dan ita fa yanzu da gasken gaske take bala'in kaunar Jaish, bata san kudirin Mammienta na son ha?ata aure da shi ba, abin da ta sani kawai shi ne tana son shi da iya gaskiyarta.
Murya a karaye ta ce. "Innalilahi wa inna ilahir rajiun, hasbunallah wani'imal wakil, ya Allah a duk in da wannan bawan naka yake ka taimaka ka kare mana shi da kariyarka, ya ilahi ya lilliahi, wayyo Allah, dan Allah Aneesa duk halin da ake ciki dan gane da shi ki rin?a sanar da ni kin ji?". Ta kai karshen maganar hawaye na zuba daga face ?inta.
Sake baki Gimbiya Aneesa ta yi tana mamakin Fanan ?in, dan ita bata san da cewa tana dakon son Jaish ?in ba, abin da ta sani dai basu sonsa saboda mugu ne, iyakarta kenan, amma yau ga Fanan har da kwallah dan ance ya ?ata? A baya kuma ba wanda ya kaita zaginsa na cewa shi mugu ne bashi da imani, abin da mamaki.
Shiru ta yi tana kallonta bata bata amsa ba har suka shiga cikin room ?in Fanan ?in, suna zuwa ta fa?a saman gadonta ta hau murzan kuka, mamaki ya hana Aneesa tambayar me ya sameta............
A ?angaren Chuchu kuwa, tana shiga cikin ?akinta wayarta dake saman bed ya fara ruri, a hanzarce ta ?arisa wajen. My Yah Rizwan shi ne sunan da ya bayyana a samam screen ?in. Jikinta har kerma yake yi wajen tsumayar ?aukar wayar, ta yi kewarsa sosai. Picking call ?in ta yi tare da kara wayar a kunnenta fuska ?auke da murmushi.
Cikin sanyin murya ya ce. "Assalamu alaiki my jannaty".
Wani irin cool murmushi ta saki kafin ta amsa da. "My Yah Rizwan wlh na yi kewarka sosai, tun jiya fa ban ji dadda?ar voice ?inka ba". Kamar zata yi kuka ta kai kashen maganar.
Siririn murmushi ya saki tare da cewa. "Am so sorry my Jannaty, ni kai'na na shiga damuwa sosai na rashin jin voice ?inki, amma ayi hakuri kada ayi mun kuka, fatana dai Allah yasa my baby tana cikin ?oshin lafiya ha?e da farinciki?". Cool murmushi ta kara saki kamar tana gabansa kafin ta bashi amsa da. "Ina nan lafiya my noor, bari na yi wanka nazo mu yi hira ka ji?".