Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 48

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 48

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 48: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 48. "Okey ayi mun kwalliya sosai yanzu bai wuce saura 5 mins mu sauka a gida ba,…

3,332 words

"Okey ayi mun kwalliya sosai yanzu bai wuce saura 5 mins mu sauka a gida ba, kece burina da nake son fara yin tozali da kyakyawar face ?inta kafin kowa, dan haka ki shirya mun sosai". Wani irin tsallen murna ta buga tare da ?an yin kara ta ce. "Wayyo Allah da?i, Yah Rizwan ni kai'na burina na yi ido hu?u da kai, kada ka cinye mun lokacina, bari na yi maka kwalliya na musamman ka ji?". Kana ganin face ?inta zaka fahimci cewa tana cikin tsantsar farinciki mara misiltuwa, sai murmushi take yi baki ya ki rufuwa.

Shi kansa sai murmushi yake yi uncle Jahiz na ta tsokanarsa, dan a tare suka taho, jirgi daban daban suka hau, amma kusan tare suka sau?a, sai dariya uncle ?in yake yi yana cewa Allah ya yi Rizwan ya fara soyayya, saura su Ramish, sai dai shi kansa uncle Jahiz ?in bai san da waye Rizwan ?in yake waya ba, shi dai ya gane da mace ce, kuma soyayya suke yi.

Okey ya amsa mata da shi tare da katse kiran. ?aura wayar a saman bed ?in ta yi, da gudu ta nufi toilet tana murna. A hanzarce ta shirya wankanta mai kyau, ta fito, cikin wani dandatsetsen doguwar riga mai matu?ar kyau launin purplish red, kayan ya yi matu?ar zama a jikinta, da yake calar tana da ?an duhu sai hasken fatar ya ?ara fitowa sosai, umbrella gown irin na ?a?an sarakuna ne, haka ta ?auko wani tsadadden alkyabbarta da ya sha kwliyar duwatsun gold, abaya ne na musamman wanda uncle Rahab ya saya masu ita da Auta iri ?aya, yana da bala'in tsada saboda gold ?in da yake ji, sai kyalli yake yi yana ?aukar idanu, shi ta sanya a jikinta saman doguwar rigar tata.

Wai my people's nace ba? Shin kunga chuchu a cikin wannan ha?a??en alkyabbar kuwa? Ya ilahi, kyau kam ya fita tsantsar fita, ta zuba perfume ?in nan tamkar anyi ?arinsa a jikinta, simple make up ta yi wanda zai ?ara fito mata da natural beautynta, lips balm ta sanya ba jan baki ba, hakan sai ya ?ara fito mata da pink lips ?inta tamkar ta sanya jan baki.

Cover high heel ta ?auko kalar alkyabbar tata wato golden color ta sanya a kyawawan kafafun nata, ya ilahi ta yi kyau my people's, Chuchu ta cika ?ar wankar kuwa da gaske, ba dan ba dan ba da sai in ce tafi Guyson ?inmu iya ?aukar wanka, sai dai Guyson ?in ma fa ba baya ba, gwanine number ?aya.

40 mins ta ?ata wajen yin wanka da shiryawa haka, da yake ta saba yi sai bata wani ?ata lokaci ba, idan baka saba bane zaka ?auki lokaci mai tsawo, amma ita ?an mintuna sun isheta.

Jama'a ita da kanta ta san ta ha?u, kai duk wanda ya ganta sai ya kai zuciya nesa zai iya tsalle fa?awa tarkon sonta. A gaban dressing mirrornta ta tsaya, ta juya ta nan ta sake juyawa ta nan, sai dubawa take yi ina ne yake neman gyara ta ?ara gyarawa. Ganin ko'ina ya zauna dai'dai ne yasa ta ?auko wayarta zata fara aikin ?aukar hoton da ta saba, zuciyarta na can wajen masoyin nata wato Yah Rizwan, tunaninsa kawai take yi, tana son zuwa suga juna, amma ta tsaya ?aukar hoto da yake abin ya zame mata jiki.

Wajen hotuna kala goma ta kashewa kanta. Bayan ta gama hoton ma sai da ta sake ?urawa kanta idanu a cikin mirror, sai ?an jujjuya face take yi dan ta ?ara tabbatarwa da kanta yes ta yi kyau.

Daga bayanta wajen room door cikin sanyin murya ta ji ya ce. "Jannat kin yi kyau har kin gaji da kyau, please kallon mirrorn nan ya isa haka kada ki kwashe mana kyan naki gaba?aya".

Lallausan murmushi ta saki. "Kai Yah Jawad ka barin na kalli kaina da kyau, dan kada na bar wani waje bai gyaru da kyau ba ya rage mun kyauna ko ma ya ?ata gaba?aya". Ta yi maganar tare da juyo da kallonta a kansa cikin wani irin salo na rigima da yanga mai jan hankali. Bawan Allah ba da gangan ta yi mashi irin wannan salon ba, kawai rigima da yanga ce saboda ta ?auki wanka. Shi kuwa wannan kallo da yadda ta juyo da yangar nan ne ta kara ru?ar mashi da ?wa?walwarsa, ga shi ta yi kyau iya kyau, haba me Yah Jawad zai yi? Ai sai suman tsaye ya yi tare da ?ura mata idanu sosai.

(Na ce ban gane ba! Yah Jawad ya da haka? Komai Chuchu zata yi wa Yah Rizwan sai ka riga shi sani da gani?? watarana ma ka wani shiga tsakaninsu suna waya ka dakatar ka sanya chuchu katse kiran, nace ya ne? Yanzu ta tsara mashi kwalliya a matsayinsa na mijinta ka zo ka wani rigashi gani a kan menene wai??? Rai na ya fara ?aci da abin da kakewa Yah Rizwan namu na zamani fa?? kabarsu su shana tun da kai ka ?oye naka soyayyar haba mana, ko ya kuka ce my people's, sai ya rin?a wani shiga tsakaninsu haka ake yi ne? Yanzu dai ga shi ya riga Rizwan ganin wannan tsadaddiyar kwalliyar, wannan abin ya sakani kuka????)

Ganin ya kafeta da idanu ya kasa yin magana ne yasa ta ?age dara daran idanun nan nata sama tare da yin wani irin fari da su mai ?aukar hankali tana fa?in. "Yah Jawad wai kyau na yi maka ne da ka tsare ni da idanu haka?".

Shiru bai amsa ba, dan baya tare da ita, ganin face ?inta kawai yake yi yana hasaso gasu sun yi aure shi da ita........ Tab gaskiya da matsala idan har bai aureta ba, wlh idan aka hanashi ita da matsala, har wani hasasowa yake yi an ?aura masu aure, toh gaskiya akwai matsala.

Jin still bai amsa mata bane yasa ta sauko da idanun nata a kansa. "Yah Jawad!". Ta ambaci sunansa tamkar zata yi mashi kuka.

Wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da kawar da kallon nasa daga kanta izuwa ?asa, ingazashi kawai zuciyarsa take yi a kan ya gaya mata abin da yake ransa kawai, dan a gaskiya yau ya ji ba zai iya hakuri sai ta ?ara girma ba, wani ?angare na zuciyarsa ne ta ce mashi a'a ya bari ba'a irin wannan lokacin ya dace ya gaya mata ba, ya bari sai ya ?auketa sun fita yawo sannan ya sanar da ita, hakan zai fi ?aukar hankalinta. Aminta da hakan ya yi sannan ya dawo da kallonsa a kan nata, sai tura baki take yi wai yaki kulata dan haka ta yi fushi.

"Jannat ke ?in duniyar kyau ce, sannan ta musammance kuma ta daban". Ya fa?a can ?asan ma?oshinsa ta yadda ita kanta bata ji me ya fa?a ba.

Ganin sai turo mashi baki irin ta yi fushin nan take yi ne yasa ya tambayeta me ya faru?. Kin yi mashi magana ta yi, sai ma ?an murgu?a mashi baki cikin yanga tare da juya mashi baya da ta yi ita a dole ta yi fushi.

A hankali ta ji saukar hannunsa a saman shoulders ?inta, ya ?an rage tsawonsa tare da saita fuskokinsu suna fuskantar mirror, ta cikin mirrorn suka kurawa juna idanu babu ko kyaftawa. Gera guda ya ?aga mata tare da kashe mata ido ?aya. Ai bata san lokacin da ta manta da fushi ta saki ?ayatatcen murmushi ba. Shima ?an siririn murmushin ya sakar mata.

"Sarkin rigima kawai, yanzu me na yi maki da kika yi fushi?".

?an turo baki ta yi tare da juyowa ta shige jikinsa da kyau kafin ta ce. "Ina ta tambayarka na yi kyau ko ban yi ba kaki ka kulani, shiyasa na yi fushi".

Matso da ?an bakinsa saitin kunnenta ya yi, can ?asa ?asa ya fara yi mata ra?an kalamai masu da?in gaske kamar haka. "Am sorry my sister, ke kanki fa kin san ke ?in makura ce wajen kyau, meyasa zaki ?ata bakinki wajen tambayar kin yi kyau ko baki yi ba? Kin san cewa a kan kyanki fa?ema ?atawa ne amma sai ki rin?a sanya mutun ?ata komai, babu wasu kalamai a duniyar nan da suka isa su zayyana yanda kyanki yake, duk abin da kika ji ana fa?ensa to bai kai bane, abin da ya kai babu wasu kalaman da zasu iya zayyana shi, dan haka ke makura ce my lovely sister".

Mata mu da shegen son a yabemu tuni wani irin farinciki na musamman wanda bata ta?a jinsa ba ya cika mata zuciya tab, hannu tasa ta rungume shi sosai tana murmushi. Bawan Allah duk ta sanya ya susuce kamar ba shi ba, tsabar iyashege kuma wai bata fahimci cewa sonta yake yi ba, ta ?auka kaunace ta tsaknin yaya da kanwarsa, akwai matsala kam babba.

Kasa yin wani kata?us ya yi, kwantar da kanta a saman kirjinsa ta yi, ?asa ?asa ta ce. "Yah Jawad duk cikin yayyunmu Allah nafi sonka, kana da kirki sosai".

Nisawa ya yi, ya ?asa iya magana, saboda shi ka?ai yasan halin da yake ciki.

Cigaba da yin maganarta ta yi. "Yah Jawad ina son kasancewa a tare da kai kullum, idan muna tare in jin da?i sosai, kafi su Yah Rizwan sosai, kasan me?".

Shiru bai amsa mata ba, hakan kuma bai hana ta cigaba da cewa. "A duk lokacin da muke tare sai in rin?a jin kamar ba'a duniya nake ba, ko guduwar lokacin bana iya gani, kana ?auke mun komai a duk lokacin da muke tare, ina manta kai'na da kai'na saboda farincikin Allah".

Da kyar ya iya jan dogon numfashi tare da sau?ewa a hankali, yatsansa guda ?aya ya ?aura a saman lips ?inta, alamar ta yi shiru, saboda ba zai iya cigaba da sauraren kalamanta ba, hakan yana kara jefa shi cikin yanayi, dama a kullum yana addu'ar Allah ya tsareshi kada ya wuce gona da iri idan suna tare, Allah yasa kada ya yi abin da zai sa ta dai'na ganin girmansa, shiyasa baya son jin kalaman nata, saboda da?insu suna ratsa ?ashi da ?argonsa.

Ita kuwa da bata san a wani hali yake ciki ba, sannan a yaya mafi soyuwa a gareta ta ?auke shi, sai ta bu?e baki ta sanya hakwara ta kama yatsan nasa tana ?an cizawa a hankali.

Ai bai san lokacin da ya furta wash da karfi ba, da sauri ya rabata da jikinsa, lumshe idanu ya yi kamar wani mara lafiya, kasa iya ri?e kansa a tsaye ya yi, dan jikinsa tamkar wadda aka zarewa laka, dan haka sai ya koma saman bedside drawer ?inta ya zauna yana cigaba da lumshe idanu tare da sha?ar dadda?ar kamshin perfume ?inta da ya gauraye ko'ina a ?akin.

Yana zama kuma Momma tana shigowa cikin room ?in nata, Allah ya taimakesa, da kuwa yau zai sha fa?a a wajen Mommar, dan kuwa dama ta gaya mashi yanzu ya sani son Jannat da aure yake yi, dan haka ta tashi daga kanwarsa, duk wani rungume rungume da suke yi na oyoyo tsakanin yaya da kanwa to ya dakatar da shi, in kuma ba haka ba ba zai ga da kyau ba, sosai dai ta yi mashi fa?a, amma bai ji ba, to dai Allah ya rufa mashi asiri yana raba jikinsu Mommar ta shigo.

Ganinsu a tare yasa Mommar ta fasa yin abin da ya kawota, dama wajen Chuchun tazo zasu yi magana a tsakanin uwa da ?a, amma da ta ganshi a ?akin sai kawai ta juya, dama room nata zata wuce ta biyo nan, daga parlon King take.

"Momma lafiya?". Da kyar ya iya jefa mata tambayar, muryarsa sai sarkewa yake yi. Jin yadda ya yi maganar yasa Mommar yi mashi kallon tsab kafin ta ce. "Babu komai, Jannat idan kin gama ki zo kin ji?". Tana magana tana kare mashi kallo. Ya fahimci ta gane wani abin, dan haka sai ya kawar da kallonsa daga kanta kawai, tunani ya fara yi a kan yau zai sha fa?a a wajenta in suka ha?u, dan bashi da kalaman kare kansa, sai dai fatansa Allah yasa kada ta yi wa Jannat ?insa fa?a.

"To Momma". Chuchun ta amsa. Wucewa ta yi ta fita, ita kuma Chuchun ta zauna a saman mirror chair ?in tana sakarwa yayan nata murmushi.

"Ina zaki je ne ma da kika yi irin wannan kyalliya mai tsayawa Jawad a zuciya?". Ya fa?a yana ?aure fuska alamar kishi ta motsa.

"Yah Rizwan zan je in yi wa oyoyo".

Ba tare da tunanin komai ba ya ce. "Shi ne sai an ?auki irin wannan kwalliya haka tamkar zaki je neman saurayi ko mijin aure? To ban yarda ba, canza kayan nan ki sanya normal kayanki na gida, kuma ki saka hijabi, shi ne cikar mace ta gari". Fuska a ?aure ya yi maganar.............. (My people's kun ji Yah Jawad da karfin hali, shi ya ganta da irin shigar da ta yi ?in amma wai bai kamata kowa ya gani ba, yau ga ikon Allah.)

Turo baki ta yi kamar zata yi kuka ta ce. "Yah Jawad na sha wahala fa wajen tsara wannan kwalliyar, please ka bari mana".

?ara ?aure fuska sosai ya yi tamkar bai ta?a yin dariya ba, alamar babu wasa fa. "A'a ban yarda ba, ki cire kayan ni sai na tayaki yin wani dressing ?in".

Sam bata san yin ja in ja da shi, dan tana jinsa a ranta sosai, kuma tana respecting ?insa sosai, hakan yasa tana tura baki ta nufi dressing room ?inta. Mikewa ya yi ya bi bayanta yana fa?in. "Ni zan za?a maki kayan da ya dace ki fita da su". Sarkin kishi ba, yaga ta yi kyau sosai ne a cikin kayan shi ne bari yasa ta canza dan ma kada ta burge wani.............. Yah Rizwan ka yi sauri ka zo ga nan Yah Jawad zai ci amanarka ya yi maka kwacen mata.

Wata simple gown wanda babu kwalliya a jikinta ya za?a mata, rigar mai tsada ce sosai, amma babu wani kwalliya da zai ja hankali a jikinta, ita ya bata dan ta sanya, sannan ya zari mayafin rigar ya mi?a mata. Ba dan ranta ya so ba ta kar?a ta wuce toilet, shi kuma ya koma saman bedside drawer ya zauna.

Jim ka?an ta fito, da yake ita ?in kyakkyawace sosai kuma munafikin jiki ke gareta mai ?aukar kowani irin kaya ya yi mata kyau, sai kayan ya yi mata kyau sosai. ?an dafe kansa ya yi tare da cewa. "Sister har yanzu dai kin yi kyau sosai, kamar kada na barki ki je nake ji".

Turo bakin nan ta yi, a shagwa?e ta ce. "Kai Yah Jawad wai ni kam me matsalarka da idan na yi kyau kada na fita ne?". A takaice ya ce mata. "Saboda ina kaunarki mana, dole na kula da ke".

Da yake ya saba cewa yana kaunarta sai ta ?auka yau ma irin dai kauna ta tsakanin yaya da kanwa ne, bata kawo komai a ranta ba sai ma cewa da ta yi. "Nima ai ina kaunarka".

Wani irin sanyi ya ji ta ratsa mashi ?ashi da ?argon jikinsa, mi?ewa tsaye ya yi. "Zo mu je to in ?an rakaki dan zan je wajen Aunty MieMie ce, ta ce nazo yanzu na sameta a part ?inta mu tattauna, nace mata a'a sai naganki naga da kika cire kayan Fanan ?in wani irin kwalliya kika yi".

Guntun murmushi ta saki tare da ?arisawa gabansa, hannunta ya ri?o suka nufi waje, har cikin ransa yake jin da?in lallausan hannun nan nata yana ratsa shi. A dai'dai tsakanin part ?in Momma da Mama ya saki hannun nata tare da manna mata sumbata a goshi, sannan ya ce. "To a gaishe da Yah Rizwan".

Da okey ta amsa mashi, daga haka suka raba hanya, shi ya yi wajen Aunty MieMie ita kuma ta nufi wajen Yah Rizwan ?in.

Sai zumu?in son ganinsa take yi, baki a ?auke da ?an siririn sallama ta shiga part ?in uncle Abbas. Babu kowa a parlour, dan haka sai ta nufi part ?insu, already ta san a in da part ?in yake.

A bakin kofar shiga parlonsa ta tsaya ta yi sallama. Shiru ba'a amsa mata ba, sake yin sallama ta yi a karo na biyu, nan ma shiru ba'a amsa mata ba. Hakan yasa ta kutsa kai ciki kawai. Babu kowa a parlourn nasa face sanyi Ac ha?i da kamshin perfume dake tashi. Ajiyar zuciya ta sauke tare da nufar kofar master room ?insa.

Dab zata shiga shi kuma yana fitowa manne da waya a kunne yana waya, ya ji alamar kamar anyi sallama a kofar parlour ne yasa ya fito dubawa. Karo suka ?an yi ya ja baya ka?an da sauri. Ita ma bayan ta ja a hanzarce tana sunkuyar da kanta ?asa ha?i da ce mashi sorry.

Subhanallah tsayuwa ya yi tare da zuba mata idanu yana kallonta, ya manta yana waya ne, ashe a hoto bai ga komai ba, yanzu ne ya ga madarar kyau, wai a hakan ma Jawad ya sa ta canza kwalliyar farko, da se yaya kenan?.

"Yah Rizwan sannu da zuwa, ina wuni?". Ta fa?a kai a ?asa.

Subhanallah, ai ?asa iya amsa mata ya yi, sai ma fitowa parlon da ya yi yana kare mata kallo da kyau da kyau, da yake yasan halinta da shegen son ace mata ta yi kyau, nan fa ya hau yabon kyanta da ya sanyata farinciki da annashuwa.

Da hannu ya nuna saman sofa tare da cewa. "Zo ki zauna". Kamar wata bakuwa haka ta zamto, ba karya zuciyarsa ya kamu da matu?ar sonta.

Zama ta yi sai faman ?oye fuska take yi, haka kawai take jin kunyarsa sa?anin Yah Jawad da suke ?urawa juna idanu suna karewa juna kallo. Saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna while ita tana saman mai zaman mutun ?aya, sai satar kallonsa take yi, ya yi kyau cikin arab jallabiyar tasa, da alama bai jima da fitowa daga wanka ba, dan kuwa ga shin kansa da sauran danshin ruwa, alamu sun ya nuna wanka ya yi ya biya basussukan sallolin dake kansa.

"A fili kuma kunyata kike ji my Jannaty?". Ya yi maganar idanunsa a kanta babu ko kyaftawa.

?ara ?oye fuska ta yi tana ?an murmushi ta ce. "A'a kawai dai na ji ba zan iya ha?a idanu da kai bane".

Ajiyar zuciya ya sauke. "Yanzu nake cewa zan shirya ya je part ?in dad in sameki, idar da sallah na kenan".

"Ai ba zan iya jiranka ba, ina marmarin ganinka, dama nasan zakazo ai shiyasa na yi saurin rigaka". Ta bashi amsa ba tare da kallon in da yake ba.

"Wow ashe my wife ta girma sosai fa! Kai shi ne na tsaya yin sanya salon wani ?an sarkin ya mun kwace, gaskiya da na yi shirme babba". Seriously ya yi maganar.

"Kai yaya Rizwan ni fa yarinya ce". Ta fa?a a shagwa?e.?an le?o face ?inta ya yi yana fa?in. "E wato yau dai ba za'a ce mun my husband ba kenan ko?".

Girgiza kai ta yi alamar a'a tare da cewa. "Zan kira mana"

"To shikenan a kirani in ji".

Hannayenta dukka biyu tasa ta rufe fuska tana murmushi ba tare da ta kira ?in ba.

"Kin gani ko? Ai nasan a waya ne kawai aka iya yi mun wannan soyayya, yanzu gani nan an ?oye mun fuska, a barni naga kayana ma an hanani ni da fuskarta, kuma naga alama a iya waya kawai ake mun shagwa?a yanzu ba za'ayi ba ko?".

"Kai Yah Rizwan ni fa ban hanaka ganin face ?ina ba". "To meyasa aka rufe mun shi?".

Zame hannayenta daga saman face ?in nata ta yi tare da fa?in. "To ga shi nan na bu?e shi ka gani". Ta yi maganar tana ?an turo baki alamar shagwa?a.

Habawa nan take ta ?ara tsunduma shi cikin gogin kaunarta. Zuba mata idanu ya yi yana rakon Allah da ya kara mallaka mashi ita, a gaskiya yana yi mata wani irin son da bai ta?a yi wa wani abin ba, yana jinta har cikin ?ar?ashin zuciyarsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull