Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 49
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 49: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 49. "My Jannaty". Ya ambata a hankali. ?an ?ago da kallonta a kansa ta yi, karaf…
3,367 words
"My Jannaty". Ya ambata a hankali. ?an ?ago da kallonta a kansa ta yi, karaf suka ha?a idanun. Nisawa ya yi kafin ya fara magana. "Ina sonki my Jannaty, ina kaunarki sosai da sosai, da ban yi niyar maganar aurenmu a yanzu ba, ganinki kawai na zo yi, nace zan barki ki kammala secondary sannan na yi wa daddy magana, amma ganinki yasa na ji ba zan iya hakuri ba, gara kafin na koma na sanar da dad abin da yake a tsakaninmu, in yaso idan kin kammala koda Jss 3 ne sai ayi auren mu koma Dubai ki cigaba da karatu a can, please promise me that ba zaki bar wani ya shiga mun cikin zuciyarki ba, wlh ina sanki da dukkanin zuciyata..........". Dakatawa ya yi da yin maganar ba dan abin da zai gaya mata sun kare a bakinsa ba sai dan ya ji amsar da zata bashi kafin ya ?aura mata da wasu maganganun. Har lokacin kallonsa naa kan face ?inta.
Ita ma bata kawar da kallonta daga kansa ba, sai dai bata kallon cikin idanunsa sosai, cikin sanyin murya ta ce. "Ina sonka Yah Rizwan, ina sonka sosai nima, kuma na yi maka alkawarin ba zan kula kowa ba, kuma ai kasan daddy ma baya barin wani ya zo wajen mu, ni bani da wanda nake so sai kai, kuma In ba zan ta?a son wani bayankai ba".
Ji ya yi Dr Raj da suke waya da shi ya katse kiran, idan baku manta ba ya fito manne da waya a kunnensa yana magana, to ya mance da wayar ya afka duniyar soyayya, sai yanzu da Dr ya ji zancen nasu fa ba mai karewa bane ya katse kiransa abinsa.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da mi?ewa tsaye. "Wait for me ina zuwa". Ya kai karshen maganar tare da nufar kofar room ?insa. Sai a lokacin ne ta samu damar ?aga idanu ta bishi da kallon tsab, bashi da wata maraba sosai da Yah Jawad, kana ganinsu zaka san ciki ?aga suka fito, sai dai Jawad ya ?an fisa hasken fata, kuma ya fisa tsawo duk da yake shi ne ?arami. Ba karya tana jin son Rizwan ?in sosai a ranta, ya iya kalamai masu kwantar da hankali........
Ni ma na iya yi wa my people's kalamai masu da?i, ko me Rizwan zai yi a cikin ?akin da ya wani shige, to ni dai bari na le?a Jimeta Yola wata kila kafin mu dawo ya ?auko abin da zai ?auko ya dawo mu zo mu ji kalaman kauna!.??
_________________________????
NIGERIA________________JIMETA
Wasa wasa dai haka rayuwar Jaish ta cigaba da kasancewa a cikin wannan ?auye, jama'a sai gudunsa suke yi, shi kuma ko a jikinsa, Mahreeh tana cigaba da tsula tsiyarta sosai, Jaish kuma kullum sai ya shigar mata fa?a in dai ta tsokalo, baya gajiya saboda bappa.
A hankali saboda shegen son fa?arta yana shigar mata yasa sha?uwa ta fara shiga tsakaninsu, ya zama kullum in dai yana zaune sai ta zo ta zauna ta yi ta faman mur?e mashi arab hairnsa, bata gajiya, shima kuma bai ta?a hanata ba, har ta kai ta kawo idan bata ta?a mashi gashin nasa bama sam baya jin da?i, ya saba da hakan sosai.
Ita ma Mahnoor a yanzu ta dai'na tsoronsa, sai dai shakkar yi mashi magana kawai take ji, Mahreen kuwa har hira take yi mashi duk da baya gane ina take dosa a maganar tata har ta karesa.
Hakika bappa ya yi farinciki sosai na sabon Mahreen da Jaish, dan kuwa ko ba komai a ganinsa zata sanya watarana ya bu?i baki ya yi magana.
Nenne har yau har gobe tana gidan Ar?o, suna can suna ta faman shiryawa Mahnoor mugunta, a cewar Nennen idan ta dawo gidan sai Mahnoor ta mutu ko kuma ta ?atar da ita.
Ita kuwa baiwar Allah a kullum safe da yamma sai ta je ta gaisar da Nennen.
Kamar kullun yau ma suna wajen kiwo, Mahreen da Mahnoor suna bakin kogin da suka tsinci Jaish suna wanke kayan sakawarsu, sai ti?ar wanki Mahnoor take yi ita kuma Mahreen ta zauna a bakin ruwa tare da tsunduma kafafunta a cikin ruwan tana wasa.
"Adda Mahnoor kin san.........
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 25/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
28
"Adda Mahnoor kin san me?".
Girgiza kai ta yi tana mai cigaba da matsan kayan da take wankewa.
Sai wasa da ruwa take yi ta ce. "Su Hamma Salisun gidan Inna Rabi ne suka tareni ?azun da zan je kwaso kayanan wankina a gida, wai sai sun dakeni, ni kuma na yi masu aljanun karya, kin ga yadda na yi wa su yayan Abu a hanyar islamiya ranar ko? Har kika yi ta kuka kamar zaki mutu kina cewa na tashi ba?...........". Ta dakata da yin maganar tana dawo da kallonta a kan Mahnoor ?in, dan ta ga shin tana sauraronta ne ma ko dai ta shareta kamar yadda ta saba.
Aikuwa hakan ce, ta shareta kamar yadda ta saba tana cigaba da dirzan kayan nasu tana ?aurayewa da ruwan gudu.
"Adda Mahnoor wai meyasa kike yi mun haka ne?". Ta fa?a tana ruro baki. Ba tare da ta kalleta ba ta amsa da. "To me nayi maki kuma?". "Sai mutum yana yi maki hira sai ki yi banza da shi".
"Mahreen wai kunne ne yake jin magana ko ido da baki?" Still dai bata ?ago ta kalleta ba, aikin da yake gabanta kawai take ta faman yi ta yi maganar, sai ha?a uban gumi take yi saboda hasken rana da yake haskasu.
"Kunnene yake saurara". Ta bata amsa tana tur?une fuska. "To masha Allah da kika fahimci kunnene yake ji, dan haka ki yi maganarki ina jinki".
Mi?ewa tsaye ta yi tare da cewa. "Na fasa gaya maki ma, kuma wlh yanzu zan kai ki kara wajen Hamma, kin san cewa ni nafi son idan ina magana a rin?a kallona ana amsa mun da e e e haka, amma ke kullum sai ki mayar da mutun ?an iska ya yi ta yin magana shi ka?ai baki ko ?an cewa e ina jin nan, sai ki wani ce ai kunnene mai ji dan haka kina jina, da ga yau ba zan sake yi maki hira ba". Tana kai karshen maganar fuuuuuu kamar wata kumfa ta wuce izuwa wajen su bappa.
A hanzarce ta mi?e tana ihun sunant Mahreen!! Mahreen!! A kan ta dawo zata saurareta kada ta kai ta kara, amma ina fuuuuu ta wuce. Ganin ta rigada ta tafi ne yasa ta koma ta zauna tare da cigaba da abinda take yi.
Jim ka?an sai gata ta dawo hannunta sar?afe a cikin na Jaish, dole dole ta je ta takura mashi a kan ya zo yaga kogin garinsu yaga yadda suke wanki.
A tunanin Mahnoor kararta ta kai wajensa shi ne ya zo rama mata, hakan yasa ta mi?e tsaye da ta gansu, sai uban gumi take ha?awa, kuma taki yarda ta cire hijabin jikinta, dan kada a kalla tana da tula tula, kullum tana kakabe da hijabi ba dare ba rana kamar wata mai takaba.
Tana ?ago kai suka ha?a idanu da Jaish ?in, ?an zuba mata idanun ya yi yana kallon yadda gumi ya wanke mata fuska kamar wadda aka watsawa ruwa, ga wasu sai tsastsafo mata a gefe da gefen face ?inta suke yi. Mayar da kallonsa a kan tulin kayan da yake gabanta ya yi, mamaki ne ya kamashi a kan wankin nata, lokaci guda kuma ya ji duk sun bashi tausayi, irin wannan aikin wahala da suke jibga, sau da dama idan ya fito da sassafe haka zai sameta tana tikar aiki komai sanyin safiya, abin da ya yi ta bashi mamaki da tausayi kenan, gata yar karama da ita amma bata da son jiki ko ka?an, saboda tun tana karama aka horar da ita, jiki ya saba da wahala har in bata yi bama bata jin da?i.
Cikin rawar murya ta ce mashi. "Ka yi hakuri Hamma, wlh sharri Mahreen take yi mun ni ban yi mata komai ba, kuma nace tazo zan saurari hirar tata amma taki ta yi tafiyarta". Baiwar Allah a tunaninta ?ararta Mahreen ?in ta kai, bata san cewa Mahreen kam tana zuwa da ta ga Jaish ta mance da cewa ?ara ta kawo bama, sai kawai ta hau zuba mashi rigima da shagwa?a.
?an jinjina mata kai kawai ya yi, alamar ya ji me ta ce, daga haka ya mayar da kallonsa a kan ruwan dake ta gudu. Sau da dama Mahreen tana ce mashi ya zo ya shiga cikin ruwan amma sai ya ki, sai dai ya tsaya a bakinta yana ganin irin nisan tafiyar da take yi.
Komawar da ta yi ta fara tikar wankin nata, sai shi kuma ya dawo da kallonsa a kanta yana mamakin ?o?ari irin tata. Sosai ya jinjina mata.
"Hamma kazo mu shiga cikin ruwa ka ji?". Cewar Mahreen sarauniya a son shiga ruwan kogi ta yi bulel.
Kai ya girgiza mata alamar a'a shi ba zai shi ga ba. Turo baki ta yi kamar zata yi kuka ta fara yi mashi magiya. Kin yarda ya yi dan shi ruwar ma kyama take bashi, dan ma dai ruwan gudu ce kawai, ita ruwan gudu ai bata da datti.
Zare hannunta daga cikin nasa ta yi, sannan ta sau?o daga saman dutsen da suke, dan akwai tudun dutse tsakanin bakin kogin da gonakin mutane wanda idan baku manta ba a baya na gaya maku hakan.
Da kallo ya bita yana jiran yaga me zata yi. Aikuwa tana zuwa bata yi wata wata ba ta daka tsalle ta afka cikin ruwan abinta. Tana afkawa ta lume ?asa tare da toshe hancinta da bakinta wanda hakan ya yi sanadiyar dan dole Jaish ?in ya bita cikin ruwan, dan a tunaninsa ruwan ya tafi da ita ya kuma fi karfinta ne, bai san cewa ita ?in gwanace wajen shiga ruwa ba, ta saba, ruwan kuma ta can tsakiya tsakiya akwai zurfi sosai, ta baki baki in da suke wanki ne babu zurfi, amma can ta tsakiya ya kai tsawon Jaish ?in a zurfi. Ku kanku kun san ruwan da zai kawo Jaish wannan gari ba karamar ruwa bace ba.
Wani irin dariya ne ya so kubcewa Mahnoor lokacin da ta ga Jaish ya tsorata ya bi bayan Mahreen a dubu dan kada ta mutu. A zuciyarta ta furta. "Ai in dai Mahreeh ce watarana sai ta sanyaka shiga cikin wuta ma ba tare da ka sani ba, ka?an daga aikin wannan yarinya ?ar albarka".
Shi kuwa bawan Allah haka ya zunduma tsulumdum cikin ruwan ba shiri, tana jin alamar ya tsundumo cikin ruwan ta ?ago kai a ?ari tana fitar da numfashi sama sama kamar zata mutu ?ar ?aniya. ?an sakanni ta ?auka tana jawo numfashinta da kyar da kyar, sai da ta dawo dai'dai ne ta daka tapi da ?an tafukan hannayenta tana fa?in. "Na yi nasarar sanya Hamma shiga cikin ruwan nan".
?atsake ya tsaya yana kallon ikon Allah, Mahreen zata iya mayar da mutum ana yi mashi kallon mahaukaci bayan yasan shi mai hankali ne, ita dai Mahnoor ta ?oye fuska ne tana yi masu dariya, shi ma bappa da tun kafin Mahreen ta fa?a cikin ruwan yake tsaye a bayansu yana kallonsu dariya ya shiga yi masu, Mahreen da karfi da yaji tana son mayar da Jaish irinta, in dai zai cigaba da biye mata tsab watara za'a kirasa da abin da ya fi maye a wannan ?auye.
Haka nan ya fito tsamo tsamo daga cikin ruwan ya yi sharkaf yana zuban ruwa, sai dariya bappa yake yi mashi, ita ma Mahnoor ta ?oye fuska dan kada su ha?a idanu ko ya ganta tana yi mashi dariya, ita kuwa hajiya Mahreen tamu a bayyana take yi mashi dariyar tana murna tare da fa?in ta yi nasarar sanya shi shiga cikin ruwan.
Yana fitowa gida ya nufa ba tare da ya yi wajen bappan ba, dakatawa da yin dariyar da yake yi bappa ya yi, dan ya lura kamar ran Jaish ?in ya ?aci, sai dai kafin ya yi mashi wani magana tuni ya sa kai ya wuce.............
Abin da baku sani ba my people's, Jaish ?in nan fa ba Jaish da kuka sani bane, yes hakance kamar yadda kuka ji hakan dai na fa?a, ku kanku kun san Jaish na King Zuhair dai ba zai yi irin wannan abin da su Mahreen yana cikin hayyacinsa ba, to ya abin yake ne?.
Wannan Jaish ?in dai ga shi nan ne, shi kansa bai san wanene shi ba, rayuwa dai yake a tsakanin mutane da kuma mutuwa, a halin yanzu dai iya cema ku zan yi bai san wanene shi ba, baya iya bu?e baki ya yi magana, ga dai shi nan babu wanda ya san hakikanin abin da yake damunsa, saboda babu wata asibitin da aka kaisa bare a san damuwar da take cikin kwakwalwarsa, kawai dai yana rayuwa ne. Sai dai kuma akwai ?abiunsa da dama wanda har yau har gobe suna a tare da shi, which means da su aka haifesa kenan, irinsu kyamar abu, rashin son magana, shariya, halin ko in kula, izza, isa da ta?ama, da dai sauransu, bayan su duk wasu dabi'un da ya ?aurawa kansa daga baya ya watsar da su.
To me ya sameshi? Meyasa baya magana? Meyasa har yau har gobe idanunsa da suka kasance fararetas kamar madara an lalatasu izuwa jajir kamar wuta? Meyasa suka ki washewa idanun? To mu je dai zuwa, alkalamina zai warware maku komai, amma wannan littafin akwai cakwakiyar da ni kai'na suna sanya ?wa?walwata ?aukar zafi, sai na yi da gaske wlh, amma idan ba haka ba kowani ?angare da rikicinsa mai zafin gaske, mai kuma bala'in ?aure kai.
Bayansa bappa ya bi, dan ya lura sam bai ji da?in abin ba, sau da dama idan Jaish ?in ya yi wani abin bappa yana yi mashi kallon kamar jinin sarauta ne shi ?in, saboda su basa ?uya, a jininsu izza take, hakan yasa bappa yake yi mashi kallo duk yadda aka yi ya ha?a ala?a ta jini da sarauta, ba'a haka ?ai watarana idan izzansa suka motsa yake zuba masu mulki ba, bappan baya hana shi ko ya ce mashi ya rin?a sassautawa, dan yasan su fa a jininsu abin yake, ko ya yi mashi magana ba dai'nawa zai yi ba, sai dai ya wahalar da kansa a banza kawai..............
Dama da ni da ku kam my people's ai mun san halin Jaish namu na gaskiya, watakila laluran da yake ciki ne ma yasa ya yiwa su bappan saukin kai wallahu ahlam, amma dai mu je zuwa koma menene zamu sani ai.
Dap bappa zai shigo gida ita ma Nenne tana shigowa, da mamaki cike a ransa yake kallonta, da bakkwan kayanta da komai ta tattaro ta dawo, sai dai da ganin face ?inta zaka iya fahimtar akwai abin da take tafe da shi, da alama akwai zantuka a bakinta.
Sannu da dawowa kawai bappan ya yi mata, tsabar makirci irin na mace har da tsugunnawa ta yi ta kwashi gaisuwa ha?e da bada hakuri. Kai mata duniya ne, muna shagalinmu wlh, mu dai ?uwawune dole a zauna damu ko anki ko anso..........????
Mamaki ne ya kara kama shi, amma bai kawo komai a ransa ba, bawan Allah ya kar?i kayan hannun nata da take tafe da su suka shiga ciki yana ta yi mata sannu da dawowa.
Ha?i?a bappa ya kaunaci maman Mahnoor a rayuwarsa fiye da tubaninku, su bama ha?asu aure aka yi ba, soyayya suka yi har zancen ya kai ga iyaye, Nenne ba ita ce za?insa ba, amma rashin maman Mahnoor ?in yasa ya hakura ya kar?i Nenne, dan gara mashi ita a kan bare, yana kaunar Mahnoor sosai, dan idan ya ganta tana ?ebe mashi kewar mamarta, hakan yasa ya yarda ya kar?i auren Nennen, dan a tunaninsa zata kula mashi da ita tunda ?ar ?ar uwarta ce, bai san ya makaro ba, dan kuwa kamar yadda iyayensu wato su gwaggo basa shiri basa zaman lafiya haka su ma Nenne da maman Mahnoor ?in ma basa shiri, dan kowacce tana taya mahaifiyarta kishi, tun suna ?an'mata ake buga gaba, kunga kuwa Nenne zata iya sauke haushin mamarta da take ji a kanta, matsalar ta samo asaline daga irin zaman kishin da ake yi a gidan Ar?o, shi ne yasa babban kuskure ne ku yi zaman kishi a gaban ?a?anku suna gani, hakan ba ?aramin gur?ata masu tunani da tarbiya zai yi ba, zaku zo ku aurar dasu da nufin hankulanku da nasu ya kwanta ku samu nutsuwa, amma sai ku gaza samun hakan, saboda irin zaman da kuke yi ya gur?ata masu tunani, to dan Allah ku rin?a sassautawa a gaban yara ko dan gobensu ya yi kyau, ku aurar da su ku samu kwanciyar hankali da nutsuwa, suma su ?auki duniya da sauki, yanzu dai kunga aya illar yin irin wannan zama a kan Nenne da mahaifiyar Mahnoor, aka ce idan gemun ?an uwanka ya kama da wuta sai ka yi maza ka shafawa taka ruwa, Allah yasa mu dace!!.
Suna shigowa ?akinta ta wuce, da alama dai har yau har gobe akwai tsoron Jaish a ranta. ?aki bappa ya bita da kayan, bayan ya ajiye mata ya wuce nasa ?akin izuwa wajen Jaish ?in, ko sannu bata sake ce mashi ba bare ta tambayi ina zai je, dan magana ta gaskiya ita ma bappan ba shi ne za?inta ba, tana da nata saurayin, suna tsaka da soyayya aka rabasu wai dan ta auri bappa ta kula da Mahnoor, kunga kuwa ko dan haushin rabata da saurayinta ma ba zata bar Mahnoor ?in ba, ta dinga azabtar da ita kenan dan ta huce, kun san shi fa so mugun abu ne wani lokaci, sai ya iya saka ka yi kisa a kan abin da kake so ba tare da ka sani ba.
Da kallo ta fara bin ?akin nata da shi. Duk tsawon lokacin nan da ?auka bata nan wlh kullum sai baiwar Allah Mahnoor ta share mata ?akin ta gyara shi fes, abin har ?an mamaki ya bata, amma da yake kishi da bakar zuciya sun rufe mata ido da kuma zugin gwaggonta, ga ?an banza jahilci a cike da kai, dan ita ko karatun addinin ma bata samu ba, gwaggonta mayyar son ku?i ce, tun tana yarinya bata barta ta samu ilimin addini ba, yara rabi duk su tafi islamiyya amma ita kuma da sauran yaran da iyayensu ke son ku?i sai a ?aura masu tallar nono su tafi, haka ta taso kan fanko babu komai sai shirme da wauta, shiyasa da zarar gwaggon nata ta kitsa mata wani abin tsab zai shiga kunnenta ya yi kane kane ya yi tasiri.
Ba abin da take tunani face kudirin da ya dawo da ita gidan, a burinsu na son suga sun ?untatawa Inna kakar Mahnoor ?in zasu je su jefa kansu ga halaka.
Shi kuwa bappa nasa ?akin ya shiga, kwance ya isko Jaish a saman gado ya yi flat tare da ?aura hannu ?aya a saman face ?insa tamkar mai yin barci, sai dai idanunsa biyu, ya canza kaya ne ya kwanta.
Kusa da shi bappa ya zo ya zauna tare da fara ambatar sunansa da Hamma Hamma kamar yadda su Mahreen ke kiransa. Kada ku manta shi kansa bai san wanenen shi ba bare har ya sanar da su sunansa, so sai kawai suka sanya mashi Hamma!.
Shiru bai motsa daga in da yake ba, dama idan jiji da kan mulki jinin sarautar tasa ta motsa sai ayi ta yi mashi magana yana ji amma ba zai motsa ba bare ya nuna alamar ya ji me suka ce, hakan yana ?aya daga cikin abin da yasa bappa yake zargin ko dai shi ?in jinin sarauta ne, ya iya miskilanci da shegen izza na karshe.