Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 50
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 50: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 50. Lallashinsa tare da bashi hakuri sosai bappan ya fara yi, dan ya fahimci…
3,290 words
Lallashinsa tare da bashi hakuri sosai bappan ya fara yi, dan ya fahimci tabbas ransa ne ya ?aci, wato fushi yake yi yanzu kenan.
In short bappa ya ?auki almost 40 min a wajen yana yi mashi magana, amma ?an tahali?in nan yadda kuka san mutum mutuminsa ne aka sassaka a wajen, ko ?agowa ya kalli bappan yaki, duk da dama can baya yarda su ha?a idanu da shi, amma ko motsawa daga in da yake yaki yi.
Sai da bappan ya gaji dan kansa ya hakura ya rabu da shi, amma ransa bai so hakan ba sam sam, shi da burinsa a kullum Jaish ?in ya saki jiki da su, ya zama kamar jini ?aya suke kawai, amma sai ga shi yau Mahreen ta ?ata komai, abin ya ?ona mashi rai matu?a.
Mi?ewa ya yi ya nufi waje, wlh idanun Jaish biyu yana jinsa, kawai ransa ne a ?ace, baya son ya yi wa dattijon nan wani abin da babu da?i ne yasa ya danne zuciyarsa ya kuma ri?e harshensa, yasan yadda zuciyarsa take tafasa in bai yi da gaske ba wlh tsab zai iya dallawa bappan maruka, ku da kun san halinsa, to shiyasa ya kwanta shiru ya danne zuciyar yana jiran har ta sau?a, kun ji dalilinsa na share bappan, ya yi kokari matu?a gaskiya na iya danne zuciyar tasa.
Gona bappan ya koma, kai tsaye wajen Mahreen da Mahnoor ya nufa, sai hira suke yi suna wanki gwanin birgewa. Yau karo na farko a rayuwarsa da ya fara yi wa Mahreen fa?a dan kawai ta sanya ran ba?onsa ya ?aci.
Tsabar mamakin hakan yasa Mahnoor mi?ewa tsaye tana tambayarsa meyake faruwa?. Bai ?oye mata komai ba ya gaya mata Mahreen ta ja Jaish ya yi fushi sosai, mamaki ne sosai ya kama ta sosai baiwar Allah, ita dai tasa wlh ko Ar?o Mahreen ta yi wa laifi bappan nasu baya ta?a yi mata fa?a, amma yau akan bare da basu san saga ina yake ba yake yi mata fa?a? Lallai wai wani irin kauna bawan Allahn nan yake yi wa Jaish ne? A gaskiya yana kaunarsa over, ku duba ku gani, kun san yadda fulanin daji suke kaunar dabbobinsu sosai, amma a haka bappa yake zubar da dabbobin nan nasa yana yankesu wa Jaish, a gaskiya ya nuna mashi kauna sosai, ya cancanci a jinjina mashi, yau a kansa aka yi wa ?ar gabar goshi, ?ar Auta, kuma ?ar zinarinsa fa?a? Lallai Jaish ya ciri tuta. Wlh haka yaran Momma suke da shegen farinjini da shiga rai, shiyasa ya shiga ran bappa sosai.
Ita ma fushi ta yi da ya yi mata fa?an, fuuuuu ta wuce gida abinta, cikin raunin murya Mahnoor ta ce. "Bappa kaga ta tafi gida fa".
Rai a ?an ?ace ya amsa mata da. "Kyaleta ta tafi ?in, yau wata da watanni ina ta shan wahala wajen ganin bakon nan nawa ya bu?i baki ya samu lafiya sosai, amma na lura Mahreen tana neman ta lalata mun komai, yanzu idan ta sanya yana shiga ?acin rai komai ya zo ya lalace ya take son nayi?".
"Ka yi hakuri bappap In Sha Allah zata dai'na". A sanyayye ta fa?a. Albarka ya sanya mata tare da juyawa zai koma cikin gonarsa, har ya fara tafiya sai kuma ya juyo. "Nennenku fa ta dawo". Ya fa?a fuska ba ya bo ba kuma fallasa.
?an zaro idanu waje ta yi tare da cewa. "Kai masha Allah, amma ba zata sake tafiy ba ko?".
Wallahu a'alam ya amsa mata da shi tare da wucewa in da ya nufa.
Cigaba da yi wankinta ta yi har izuwa azahar, ta kammala ta je ta shanyasu a farar yashin dake gefen kogin, sannan ta ?auro alwala ta nufin in da bappan nata yake.
Ga mamakinta sai ta iskoshi a tare da Mahreen suna ta zuba hira kamar ba ita ce ta yi fushi ta tafi gida ba, yanzu ta dawo, abinci ma ta kawo masu Nenne ta yi girki mai rai da lafiya yau, sai mamaki bappa yake ta yi, ita kanta Mahnoor ta sha madarar mamaki na ganin Nenne ta yi girki, ta kai tsawon shekaru 5 bata girki kamar matar aure a gidan, Mahnoor ?in ce ke yi, yau rana tsaka ta yi girki abin da mamaki, amma duk basu kawo komai a ransu ba, suka ci suka sha, suka yi sallah, sannan suka zauna yin hira kamar yadda suka saba. Nasiha bappan ya rin?a yi masu sosai mai ratsa zuciya, sai kuka Mahnoor ta rin?a yi saboda nasihar ya ta?a mata zuciya sosai, bappa ya iya yi masu nasihar da ya kan sanyasu su ji duniya ma gaba?aya ya fice masu daga ransu, bawan Allah ne sosai, uba ne na gari sosai.
Ita kuwa Mahreen da harkar tsoro baya a tsarinta, idanunta a bushe garau ba ko alamar hawaye, kun san ita harkar jarumta ta tasani, sai kace wata renon Commander Zafar, idanu a bushe, komai nasihar da bappa zai yi masu, zai ratsa zuciyarta, amma hawaye? Tab baya fitowa daga idanun yarinyar nan, sai ka yi zaton ma bata da ruwan hawayen a duniya, amma akwaisu, kukan ne kawai ba za'ayi ba.
Sai karfe uku Mahreen and Mahnoor suka dawo daga wajen kiwo, abin mamaki kuma yau Nenne dai bata yi masu tijarar da ta saba ba, salum alum suka yi wanka, suka ?auro alwala, har da abinci ta basu suka ?ara ci suka ?oshi, sai ?ari ?ari Mahnoor take yi da ita, dan bata ta?a ganin ta yi masu makamancin haka ba, ita dai tasan tsakaninta da Nenne duka, zagi da kuma hantara.
Sai tunani take yi a kan to ko dai yau lafiya Nennensu take? Abin da ?aure mata kai.
Islamiyya suka nufa kamar yadda suka saba, yau bata hanasu tafiya da wuri bama.
Ko da suka tashi daga islamiyyar sai da su Salisu suka biyosu da nufin su dakesu, duk da yayan nasu ya sami sauki saboda bakar zuciya sunki hakura sai sun ?auki fansa.
A hanya suka taresu, suka sha gabansu sun hanasu hanya. Mahnoor dai hakurin nan da ta saba shi ta shiga basu da wannan sanyayya muryar tata.
Ita kuwa Mahreen Mahnoor na tsaka da basu hakuri kamar wata zararriya ta zunduma ihu tare da bajewa a ?asa ta fara birgima tana watsi da wulli da kafafunta sama. Zaro idanu gaba?ayansu suka yi, da sauri Mahnoor ta tsugunna a gabanta, murya na rawa ta fara tambayarta me yake damunta?.
Sam bata kulasu ba, ihun ta ta cigaba da yi tana birgima, sai da ta babbatar zu?atansu sun gama tsinkewa, sannan ne ta wani irin girgiza jikinta yadda kuka san wata bujumar saniyar da aka zubawa ruwan sanyi, kunsan zai karka?e jikinsa ya yi wani irin girgiza ai? To haka ita ma ta yi tamkar mai wani motsi a kai.
Zaro idanu suka yi suna cigaba da kallonta, da wani irin murya kamar na ?an shaye shaye da suka jima a harkar murya ta gama lalacewa ta ce. "Kai Salisu zo nan gabanmu!!".
Tun da Mahnoor ta ji haka ta gane iskancin da ta saba yi wa wa?an da suka fi karfin ta iya dukansu ne ta yi masu, dama idan ka fi karfinta, ta san cewa zaka iya dukanta sai ta yi masu aljanun karya, a haka take kwatar kanta a koma inane, lafiyar jikinta ne ba zata bari a ta?a mata ba yar albarka.
Da farko Salisu dai an gwada jarumta, nunawa ya yi kamar baya tsoro har da wani ?aure fuska sosai. "Ba zanzo ba, idan ma kai aljani ne to ka fito ina dai'dai da kai, ba kana ganin da safe kasa mun gudu ba? To yanzu aradun Allah babu in da zanje har sai na ci uban yarinyar nan".
Wani irin zaro idanu waje ta yi tare da sake yin wani irin girgiza, sannan ta kara kausasa murya tare da yun?urawa a haukace zata tashi tana fa?in. "To jiramu gamu nan zuwa!!".
Habawa ai tana yun?urowa da karfinta a guje Salisu ya watsa sai hanyar gida har wando na fa?uwa, takalma kam ba'a maganarsu, tuni ya watsar da ?an banza, hege ko waye ya ce mashi barno a gabas take, ai Mahreen ba taya baya bace, kuma she's know how to act well well ?ar albarka, ji yadda ta taso fisabilillah har da wani cewa gamu nan zuwa, oh ni princess Teema ina ganin rayuwa wajen wannan yarinya, ko da yake jikar gwaggo ce fin haka ma idan ta aikata ba abin mamaki bane, dan fa?a dai kun gani da idanunku a jininsu yake, gwaggo ce ko bala'i, ga Nenne ma ta gado.......... Ni kam na ce to da ta tason nan in da Salisun bai gudu ba ya zata yi kenan? Ita dai tasan ba iya dukansa zata yi ba? Amma dai koma me yarinyar akwai bala'in karfin hali tare da sanyawa ranta koma me itace da nasara, bata tunanin ?acin rana sam sam............ Na ce ba Allah ya ha?a mun ita da Obaid and Omaid, ?an amin ku ce amin......??
Tana ganin sun gudu ta mi?e tsaye tare da buga tsalle tana fa?in. "Gobe ma ku dawo mana, na fiku iya shan kunun tsiya". Tana magana tana karka?e kasan da ya ?ata mata jiki saboda kwanciyar da ta yi a ?asan.......... Oh ni ?ar mamata, har da kunun tsiya ma Mahreen take sha? Allah mai iko!.
Ko sannu Mahnoor bata ce mata ba suka nufi gida, sai addu'ar neman shiriya a wajen Allah Mahnoor ?in take ta yi wa ?ar kanwar tata a cikin zuciyarta.
Suna shigowa suka isko bappa a tsakar gida yana gyaran harawa, sam basu ji da?in rashin ganinsa a tare da Jaish ba, da alama kenan har yanzu zuciyar tasa bata sau?o ba, kullum a tare suke komai da bappan, amma yau yana ?aki yana kwance shiru, sai tafarfasa zuciyarsa take yi mashi. Shi kansa bappan zuciyarsa zafi take yi mashi na fushin da Jaish ?in yake yi, haka ya shiga gyara harawansa shi ka?ai yana zubawa awakansa da suka kusa haihuwa ya tsamesu daga cikin sauran ya dawo da su cikin gida.
Wajensa Mahreen ta nufa, ita kuma Mahnoor nonon da suka tatsa da safe suka ajiye shi a ?akin bappa ya yi bacci dan ya yi kauri ta shiga ciki ta ?aukowa. ?asa ?asa ta yi sallama cikin natsuwa, yana kwance ko gezau bai yi ba.
Wucewa ta yi ta ?auko kwaryar nonon ta fito, dama haka suke yi kullum, idan ta ?auko sai ta damawa Jaish, tun baya iya sha har ya koya dan dolensa, da idan ya sha sai ya yi ta amai tamkar zai akayar da komai na cikinsa saboda karninta, amma yanzu lafiya lou yana sha, rayuwa kenan, wuya mai koyawa mutun abin da yake ikirarin bai iya ba kuma ba zai yi ba, sai ga shi dai yau kun gani a kan Jaish, duk wanda ya ce bai iya kuka ba to ku ce mashi mahaifiyarsa bata mutu bane, tana mutuwa dole ya yi dan gidansu!!.
Dama mashi fura da nonon ta yi ya damu sosai, ha?i?a Mahnoor yarinya ce mai abin birgewa, dan kuwa a kullum ta san kowani aiki da ya rataya akanta, ku duba ku gani ko ina ta je tana dawowa dallah dallah zata fara yin duk abin da ta san aikinta ne baiwar Allah, ba sai ta jira an ce ta yi ba, fatan Allah ka shirya mana ?a?anmu da jikokinmu.
Bayan ta kammala ta mi?e ta ?auko mashi ?an ?aramin kwaryarsa mai kyau ta zuba a ciki, sannan ta zubawa bappa da Nenne, ta bar masu sauran ita da Mahreen a cikin wannan babban kwaryar, ta ?auki paipai ta rufewa kowa nasa, ta ?auki na Jaish ta nufi cikin ?akin bappan. Tana shiga ita kuma Mahreen ta zo ta ?auki na bappa ta je ta mi?a mashi, kar?a ya yi ya ajiye a gefensa ya cigaba da aikinsa. Sannan ta ?auki na Nennen ta kai mata, sai ta ?auko wani ludayi ta zo ta zauna tana jiran Mahnoor ?in ta fito su sha a tare.
Ihunta da suka ji daga cikin ?akin bappan ne yasa suka kai kallonsu a bakin kofar, da sauri Nenne ta fito daga cikin nata ?akin dan tsabar gulma. Da gudu bappa ya ajiye harawar hannunsa ya nufi ?akin nasa, da gudu ita ma Mahreen ta rufa mashi baya, Nenne kuwa a bakin kofar nata ?akin ta tsaya tana jiran ta ji menene? Sai addu'a take yi a kan Allah yasa kashe Mahnoor ?in ma Jaish ya yi kowa ya huta.
Turus suka tsaya a tsakar ?akin suna ganin abin da yake faruwa, gaba?aya Mahnoor ?in jikinta ya sha wanka da furar da ta kawo mashi ?in, tana tsugunne a gaban gadon nasa. Abin da ya faru shi ne, ta saba idan ta kawo mashi furar ko da yana kwance ne zata zo gabansa ta tsugunna ta mi?o mashi, wani lokaci har hannu take sawa ta ?an bubbuga katifar ta ce ya tashi ga furarsa. To yau dai da ta zo ta yi mashi na farko bai motsa ba, sai ta yi zaton bai ji bane yasa bai motsa ba, dan ta san dai in ta yi mashi magana yana ?aga mata kai kawai alamar ya ji, yau sai taga akasin hakan, kuma idanunsa biyu ba barci yake yi ba.
Shi ne ta sake buga jikin katifar ta maimaita abin da ta fa?a da farko, ita gaba?aya ta manta cewa da safe ya fusata. Nan ma bai motsa ba, ganin hakan ga idanunsa biyu sai yasa ta kai hanni ta ?an ta?a hannunsa zata yi magana kenan a fusace ya kai hannu zai dallah mata mari, zaro idanun da ta yi ta sha jinin jikinta tare da kamewa waje guda ne yasa ya fasa marin nata ya sauke haushinsa a kan furar a in da ya yi fatali da shi, ya yi mata wanka da shi, gaba?aya jikinta ya ?aci, har face ?inta, hakan ya ?aga mata hankali har ta yi kara, dan bata ta?a ganinsa a irin wannan yanayi ba, Allah ya ceceta, wlh da ya sauke mata wannan marin da ya yi niya in da yake cikin fushin nan in bata mutu ba zata sume, amma sai ya danne, tun safe yake ta ?o?arin danne zuciyar nan nasa na Modarawa, amma abin ya ci tura bawan Allah. Ba laifinsa bane, zuciya gadon modarawa ne kowa yasan da hakan!.
Bappa yana ?aura idanunsa a kansu ya fahimci abin da ya faru, hakan yasa ya ce mata ta je ta canza kaya ta wanke jikinta. A hanzarce ta mi?e, sarki tsoro jikinta har kerma yake yi ta fito waje a tsorace.
Tana fitowa Nenne ta dakatar da ita a kan ta gaya mata me ya faru a cikin ?akin?. Murya na rawa ta bata labarin abin da ya faru, wani irin murmushin mugunta ta saki tare da juyawa ta shige cikin ?akinta.
Bayan Mahnoor Mahreen ?in ta biyo tana bata hakuri. Shi kuwa bappa rarrashin Jaish ?in ya shiga ya fara yi. Da yake ya ?an samu ya yi wa Mahnoor patali da furarta sai ya ?an ji zuciyar tasa ta yi sanyi, hakan yasa ya kara zagewa wajen dannar zuciyar har ya iya amsawa bappan ta hanyar jinjina kansa alamar ya ji. Sosai bappa ya ji da?in hakan tare da sanya mashi albarka.
Shi ma ya ji da?i da Allah ya taimakesa wannan bakar zuciya tasa bata ja mashi ya cutar da bappan ko ya yi mashi wani abin da ba dai'dai ba, godiya ya yi ga Allah. Kiraye kirayen sallar mangariba da yara suke yi ne yasa ya ce mashi lokacin sallah ya yi ya fito su tafi masallaci. Alamar wanka zai yi ya nunawa bappan. To ya amsa mashi da shi tare da fitowa ya umurci Mahnoor da ta sanya mashi ruwa a wuta.
Baiwar Allah haka ta tafasa mashi ruwan tare da surkawa dana sanyi, ta kai mashi ban?aki ta fito. Yana fitowa da nufin ya shiga wanka da ita suka fara ha?a idanu, kawar da kallonsa daga kanta derect ya yi tare da satar kallonta ta wutsiyar idanu, sai ya ji bai kyauta ba abin da ya yi mata, ta mashi alkhairi ya sauke haushin laifin da ba nata ba a kanta, dama idan baku manta na yana jin tausayinsu ita da Mahreen.
Toilet ya nufa yana aikin satar kallonta, ita kuma a tunaninta baya kallonta sai ta tsare shi da idanu tana ta kallonsa har ya shige.
After some minutes. Bayan sun yi sallar mangariba da isha'i sun dawo, zaune suke a tsakar gida kamar yadda suka saba, sai hira suke zubawa abin gwanin birgewa, bappa, Mahreen and Mahnoor ne suke yin hiran, Jaish dai shiru yana sauraronsu, Hamma Faisal bai rigada ya ?ariso ba.
Fitowa daga ?akinta Nenne ta yi, a kusa da bappa ta zauna, ko wanka matar nan bata yi ba tun da ta dawo, da alama dai akwai wata ?asa. Cikin rawar jiki bappa ya ce. "Kin fito ne?".
Kai ta gya?a mashi hasken fitullun kwai na haska su, da dayake wata ta ?an yi nisa.
"Wata magana nake son yi da kai". Ta fa?a da wata iriyar murya kamar masoyiyarsa ta gaske, da alama wani makircin zata ha?a.
Jin ta ce tana son yi magana da shi ne yasa Mahreen and Mahnoor suka mi?e tare da shiga kitchen suka ?auki abincinsu suka wuce nasu ?akin.
Shi kam Jaish mi?ewa ya yi ya nufi waje mai gaba?aya, a karkashin bishiyar kofar gida ya zauna yana ganin yadda mata da maza suke zirganiya tamkar ba dare bane, kowa da firillar kwai a hannunsa yana haskawa, ?ananan yara sai yawo suke yi a tsakanin gidan makota.
Dawo da hankalinsa kacokam a kanta ya yi tare da ce mata yana sauraronta. Gyara zama ta yi tare da lankwashe kafafunta ta juyo suna fuskantar juna. Cike da makircin ta ce. "Wani alfarma nake nema idan ba damuwa?".
A takaice ya ce. "Ba damuwa ki fa?a ina jinki".
Sai da ta sakar mashi murmushi kafin ta fara kora mashi jawabin abin da take bu?ata. "Ina son in ba damuwa ka aurawa wannan bakon namu Mahnoor, nasan zata samu kulawa daga wajen shi, ai kama fini sanin halinsa, kuma.........."
?aga mata hannun da ya yi ne yasa ta dakata da yin maganar.
"Ba sai kin ?arisa ba, duk abin da kike so shi kowa zai yi a gidan nan". Ya fa?a a sanyaye.
To fah, a gaskiya Nenne muguwa ce ko kuma in ce gwaggo bakar muguwa ce, wai dan ance Jaish shi ne sarkin Mayu shi ne suka zauna ita da gwaggon nata suka shirya ta yadda zasu rufe bakin bappa ya aurawa Jaish ?in Mahnoor dan ya cinyeta, sun yi imanin shi ?in mugu ne na karshe, burinsu kuma ta wahala sosai, a tunaninsu idan aka aura mata shi zata zama abin tausayi koma ta mutu, shi ne har da zuwa kauyukan Cameroon suka samo magunguna da zasu rufewa bappan baki ta yadda zai yarda da maganarsu kai tsaye, su dai kawai suga sun sanya yarinyar nan cikin wahala, sai dai basu san cewa boom suke shirin ha?awa kansu ba, dan kuwa da ni da ku dai munga soyayya a tsakanin Mahreen da Jaish ?in, akwai sha?uwa, ya zasu yi kenan a lokacin da Mahreen zata ce masu idan ba shi ba sai mutu? Mu dai mun san jinin Modarawa jinin Akka wato Jaish namu ba maye bane, kunga kuwa ai baya cinye Mahnoor ko ya azabtar da ita ba, in da tsawon kwana muna nan Mahreen zata kara girma kuma sha?uwa ta kara shiga tsakaninsu, a wannan lokaci ni kam zanga ya zasu yi, akwai matsala wlh babba, idan zaka gina ramin mugunta dai ka gina shi dai'dai kai, dan watan watarana kai zaka afka a ciki, Allah dai ya kyauta ya kuma sa mu dace.