Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 51

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 51

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 51: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 51. Wani irin sanyi ta ji a ranta, burinta ya cika, a tunaninta Jaish irin gama…

3,350 words

Wani irin sanyi ta ji a ranta, burinta ya cika, a tunaninta Jaish irin gama gari banzan nan ne, wanda bashi da gata bashi da galihu, shirinsu shi ne su sanya bappa ya yi wa Jaish ?in nasa ?akin daban can gefe da su idan aka yi auren, bappan kada ya taimaka masu da abinci da komai, su barsu su sha wahala su sha gararin rayuwa, wato dai shi mugu fa kawai ka yi addu'ar Allah ya rabaka da shi shi ne kawai mafitarka, wannan ma jini ?aya suke duka, amma ku dubi muguntar da take ta bibiyar ?ar tahali?ar nan da shi fisabilillah.

Hira suka cigaba da yi, bappa bawan Allah ya ma mance da cewa ya yi wa Mahnoor ?in baiko da Hammanta Faisal, duk abin da Nennen ta ce sai ya aminta da hakan kawai, ya manta da cewa bai fa san wanene Jaish ?in ba, basu san asalinsa ba, kawai dai alamu sun nuna maganin gwaggon Nennen ne yake aiki ba shi ba.

Sai tsara yadda abubuwan zasu kasance Nennen take yi, duk kuma zallar zalinci take tsarawa babu tausayawa, dukka kuma bappan ya aminta, har da wani cewa gobe suna idar da sallar asuba za'a ?aura auren kamar yadda ta bu?ata, shi ya yafewa Jaish ?in ma sadaki, ma'ana zai biya mashi kenan, daga Jaish ?in har ita Mahnoor basu san me yake faruwa ba, Nenne ta shirya komai har da cewa Jaish ?in ya tafi garinsu da Mahnoor ?in ma idan ya tashi tafiya dan tsabar mugunta, a ?aramin tunaninsu da wautarsu sun ?auka idan ya tafi da ita garinsu shikenan ba zai sake dawowa ba, a shirmensu wai shikenan sun rabu da ita rabuwa ta har abada sun huta, wato idan aka ce maku mutun jahiline kawai ka barshi a yadda ka gansa, jahilci kanin hauka kenan.

Shi dai bappa umarni kawai yake kar?a abinsa. Hakan kuma aka yi kamar yadda ta bu?ata washegari suna idar da sallan asuba bappa ya sanar da liman aka ?aura auren, abin ya yi mugun bawa Jaish mamaki jin sunansa na Hamman a bakin liman, sai dai bai yi wani yunkuri ba, sai ma mi?ewa da ya yi ya nufi waje abinsa, sai gida ya nufa.......

Allah sarki Faisal bawan Allah yana jin wannan magana ya yanke jiki ya zube ?asa sumamme a cikin masallaci, shi kansa kawun Mahnoor ?in kanin mahaifiyarta wato Ibrahim sai da ya girgiza da jin maganar, Ar?o da bappan su Faisal babu wanda bai razana ya kuma yi mamaki ba, fa?i suke yi bappa ya haukace ya aurawa ?arsa maye.

Ai Ar?o bai yarda ba, bai yi ?asa a gwiwa ba yasa a kama mashi bappa a kai mashi gida, wai dole a ?auresa a yi mashi magani dan ya haukace, fa?i ?an uwan Inna suke yi wlh ko zasu mutu sai dai su mutu amma Jaish bai isa a aura mashi Mahnoor ba, an gaya mashi bata da gata ne? Ko bata da ?an uwa mahaifiya ne? Wlh ba zasu bawa wani bare ?arsu ba, wani irin hatsaniya ne ta kacame a masallacin, tuni labari ya kara?e kauyen, shi dai Jaish yana gida bai san wace waina ake toyawa ba. Nenne kam tambaya take yi shin an ?aura auren ko ba'a ?aura ba? Amsar ne burinta a yanzu.

Akwai wani kanin Inna mai bala'in ?abilanci da zafin rai, ai kuwa ya ce idan bappa ya isa Allah ya tsine mashi, sune dangin uwar yarinyar nan, basu ga uban da ya isa ya ?auketa ya bawa baren banza ba wanda ake zargin maita a tattare da shi, dole Mahnoor Faisal zata aura, idan ba haka ba ayi ambaliyar ruwan bala'i a kauyen,

Haka ya ha?a matasa a kan su je su yi wa Jaish ?an banzan dukan mutu su ?aukeshi su fitar da shi daga cikin ?auyen....... To fa tashin hankali, cikin ?an?anin lokaci Nenne ta haddasa boom a cikin ?auyen, da alama kuma tashin boom ?in nan sam ba zai yi kyau ba, zai yi mugun munana, kai mata mata Allah ya shiryamu shirin addinin musulunci, ji fa cikin minti ?aya ta rikita gari guda.

Tana gida sai fargaba take ji kamar zai kasheta, sai safa da marwa take yi a tsakar gida, burinta kawai ta ji an ?aura auren nan, tana fargabar ace ba'a ?aura ba, duk wani shirinta zai lalace.

Mahnoor kuwa suna can suna shirin bin bappa kiwo, dan kuwa basu san me yake faruwa ba, basu san Ar?o yasa a capke bappansu an ?aure shi da sunan ya haukace ba, dan kawai ya ?aura mata aure da bare ko in ce maye da suke kiransa, shikenan shi ma ya haukace sai ?auri, kai ?auye duniya ne jama'a.

Gungun matasa da a kallah zasu kai su 20 ne suka nufo gidan bappan, kowanne rike yake da sanda, ?anin Inna ya basu umarni su tabbatar sun fasawa Jaish jikinsa ta ko'ina kafin su fitar da shi daga cikin ?auyen nan, su kai shi can su jefar, sai wani tayar da kura suke yi a hanya suna tafiya, da ganinsu kasan wa?an nan sun ?unso ?unshin mugunta, fuskokinsu babu alamar imani, sai wani haki suke yi kamar wa?an da suka ci uban gudu suka ?oshi, suna wani muzurai da idanu kamar ka arta a guje idan ka gansu. Shi kuwa bawan Allah Jaish da bai ma san me yake faruwa ba, fitowa tsakar gida ya yi hannunsa ri?e da sandar kiwon bappa, fita waje yake son yi ya je wajen dabbobin nasu ya tatso nono kamar yadda yaga bappan yana yi, bai ta?a kwatantawa ba sai yau ya ce bari ya yi, kuma ya yi alkawarin dama daga yau shi zai rin?a tatsanwa bappa yana rage mashi wahala.

Ganin ya fito yasa Nenne ta yi maza ta shiga cikin ?aki ta cigaba da safa da marwanta har tana ha?a uban gumi yadda kuka san wadda take gudanar da wani aiki na alkhari, gaba?aya a ru?e take, tsantsar rashin gaskiya ne tab a saman face ?inta, a hakan ma bata san me yake faruwa a cikin ?auyen ba, bata san babanta ya sa an ?aure bappa ba, da ta sani kam ina ga ru?ewar da zata yi sai Allah ne ka?ai ya sani.

Bokitin tatsar nonon ?in ya ?auka, shi dai baya ?aga idanu ya kalli kowa, haka zalika fuska kamar hadari kullum a ?aure tamau, ga iya shariya, aikin gabansa kawai yake yi, sai ka rantse ma babu shi a gidan idan ba ganinsa ka yi ya fito ba!.

Yana ?aukar bokitin ya juyo zai nufi waje kenan wa?an nan matasan suka banko labulen buhun kofar gidan, tsundum suka afko cikin gidan gaba?ayansu, sai ka?a sandunar kiwon nasu sama suke yi.

Da gudu Nenne da su Mahnoor ?in suka fito waje jin irin wannan hayaniya.

Gaba?aya matasan suka rufa kansa da gudu ha?e da ?age sandunarsu da nufin fara kai mashi jibga ta ko'ina................. TASHIN HANKALI, A GASKIYA NENNE DA GWAGGO HEGU NE, JI LOKACIN ?AN?ANI SU HARGITSA KAUYE GABA?AYA, DAMA AI ABU NE DA BA ZAI YIWU BA ?AN UWAN MAMAN MAHNOOR ?IN SU YARDA DA WANNAN ABIN, AKWAI GAGARUMIM RIKICI A WANNAN ?AUYE, GA SHI DAI BAPPA MAI SHIGARWA JAISH ?IN FA?A TSAKANINSA DA ?AN KAUYEN MA AN ?AURESA DA SUNAN MAHAUKACI, MY PEOPLE'S AKWAI BALA'I BA KA?AN BA, NA BARKU LAFIYA NA TAFI KINGDOM OF POWER, KAFIN MU DAWO WATA KILA SUN GAMA KASHE JAISH ?IN.

_____________________?????

KINGDOM OF POWER??????

Jim ka?an ya fito daga cikin room ?in nasa, saman sofar da ya tashi ya koma ya zauna hannunsa janye da katuwar echolac mai bala'in kyau da tsada. "Before I came, before I actually see your face I already knew that my wife is gorgeous, beautiful and Pretty, you're a so special my Jannaty". Ya yi maganar kallonsa a kanta babu ko kyafta idanun.

"I never thought there is a woman who will make me fall in love at this moment, I was so surprised, one time like a dream you stole my heart, wow my Mammien is special, ta iya za?e gaskiya, dole na yi mata gagarumin kyau"........ Duk ya ru?e ne, ya susuce kalaman kauna kawai yake ta zuba mata.............Haki?a a wannan wajen ?ai zuciyata ta karaya my people's, dukkansu suna bala'in kaunarta, ya zasu yi a lokacin da zasu san cewa mace ?aya suke so? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, waye zai hakura kenan? A gaskiya Mammie bakar muguwace kuma silent killer ce ta gasken gaske wlh, wato da bata da hanyar da zata bi ta kashesu ne yasa ta ha?a masu tarkon da ciwon zuciya zai kashesu gaba?aya, domin kuwa dole ?aya ya hakura ko kuma dukkansu biyu King ya hanasu dan ya raba gardama, kai koda an bawa ?aya ya aureta ba zai ta?a jin da?in zama da ita ba, saboda zai rin?a jin ra?a?in cewa ya auri abin da ?an uwansa yake kauna, dole zuciyarsa ta yi ta yi mashi zogi, kai Allah ka rabamu da masu bakar zuciya irinsu Mammie.

Sai sakin cool murmushi take aikin yi, tana mayar mashi da amsa cikin jin kunya. Sun jima suna hira kafin ta ce mashi zata je Momma na kiranta, dama zumu?in son zuwa ta gansa ne yasa bata fara zuwa kiran Mommar ba. Okey ya amsa mata da shi sannan suka mi?e a tare.

Da hannu ya nuna mata ta yi gaba mana, ba musu ta wuce gaba ya rufa mata baya. Suna fitowa parlour suka isko Mammien and Aliyah suna zaune, har ?asa ta tsugunna ta gaida Mammien, sai wani uban washe masu baki na munafurci take yi.

Gera guda ya ?agawa Mammie tare da cewa. "Mammie bari na raka Queen ?ina in tabbatar ta shiga ciki lafiya ina dawowa mu yi magana". Cike da kaunar Mammien ya yi magana.

Kara fa?a?a murmushinta ta yi tare da amsa mashi da okey ya kula da ita dai sosai kamar da gaske take yi.

Gaba chuchun ta yi da sauri dan kunya da ya lullu?eta, bayanta ya bi yana yi mata dariya wai tana kunyar Mammie.

Suna fita Aliyah ta dubi Mammie ta ce. "Aunty ina na ji kincewa Mama Jawad ne yake son Jannat? Ko dai ba Jannat ?in bace wannan? Dan ni ?a?an King ?in nan ru?ar da ni suke yi, kamanninsu kusan ?aga, duk da shi suke kama da kuma wannan hegiyar tsuguwa mai idanu manya manya kamar na mujiya, wlh banson tsohuwar nan, haushi take bani". Ta kai karshen maganar tana kwa?e fuska kamar an naushi kashi.

My people's nace mu gayawa Aliya gaskiyar wacece Akka ne ko dai mu yi shiru Akka ta bayyana mata wacece ita? Ana bala'i a kingdom of power, wai tana son King ya aureta amma bata son Akka, kam balai'n can, e lallai kin ?auko dala ba gammo hajiya Aliya, dan kuwa Akka kam mai sonta ma bata so shi ba bare marasa sonta, ai duk bala'in ki a tafin hannun Akka ki ke, ita ?in wandon robace dai'dai da ?ugun kowace maras kunya, ita gobara ce daga kogi wanda kasheta sai dai lillahi, dakalin majina a hau a zame, kai Akka bala'i ce, Akka duniya ce, zaki sameta daram yarinya, zata cire maki hayakin da kanki yake fitarwa, su Mama jiga jigan mata ma ya suka kare da ita bare ke tsutsar masai?.

Wani irin ?aure fuska Mammie ta yi kafin ta ja dogon tsaki. "Ita ce Jannat ?in dai, Jawad yana sonta ni kuma na cusawa Rizwan kaunarta, kinga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ?aya, daga karshe dukka zasu yi mutuwar kasko, kinga babu wanda zai ce da sa hannuna, ina da tabbacin dukkansu biyu King ba zai basu aurenta ba, dan kuwa shi King adalin mutun ne, idan yasan suna son mace ?aya zai hanasu dan ya kwatanta adalci, kinga ciwon zuciya ce zata nakastasu". Ta kare maganar tana sakin wani ?an iskan dariya kamar wata mai motsi a kai.

Wani irin shu'umin murmushin ta saki. "Shegiya Aunty gaskiya kin iya plan, amma nasan mama ce ta shirya komai, dan ke baki da irin wannan ?wa?walwar........"

Cak ta tsaya da dariyar tare da ?aure fuska ta wurga mata wani matsiyacin harara wanda yasa ta ha?iye maganar. Zata yi magana kenan Rizwan ya shigo bakinsa a ?auke da sallama.

Tsabar iya munafurci a wajen mammie har da wani cewa. "Kai har ka fara kamshin ango, wai ma me ka sayawa amaryar ne cikin katon echolac haka?".

Hegeya Aliya ita ma har da wani sakin murmushin munafurci tana fa?in. "Yah Rizwan wlh har wani kyalli face ?inka ta fara yi, e ango, wai yaushe ne ma abin?".

Zama ya yi kusa da Mammien yana murmushi, aka ce rashin sani yafi dare duhu, Allah sarki da kansa ya zauna kusa da makashiyarsu shi da marayan kanin nasa.

"Mammie bafa yanzu bane auren, zan barta ta kammala junior secondary school kafin nan na yi wa daddy magana......"

Bata bari ya ?arisa zancen ba ta tari numfashinsa da cewa. "A'a ban yarda ba, zuwan nan naka za'ayi komai a gama, ni da bani da burin da ya wuce ku yi aure shi ne kuma Allah ya kawo lokacin kana ?o?arin ka kawo mana wani zancen da ba shi ba? Shekara nawa ina dakon jiran wannan rana? Ko so kake na mutu da tsumayin zuwan ranar aurenka a raina". Fuska a ?aure ta yi maganar.

Aliyah ce ta capki zancen da cewa. "Gaskiya kam nima ban yarda ba, kawai ka shigo mun da Auntyta". Tana magana tana tur?une fuska yadda kuka san da gaske suke yi bayin Allahn nan, amma tsagwaran iya makircine da munafurcin ne kawai, idan ka fa?a tarkonsu ba zaka ta?a tunanin ba sonka suke yi ba hegu.

Fuska ?auke da ?ayatattcen murmushi ya ce. "Kai mammie Jannat fa yarinya ce, zan bari kafin ta kammala dai zata kara girma, kinga hakan zai fi".

Girgiza kai ta fara yi. "A'a ban yarda ba, idan wani ya yi saurin shigowa ya ?auketa fa? Kasan ?a?an sarakuna nawa ne suke rububinta? Jannat fa ba mace kamar sauran mata bane, ta fita daban, shiyasa na za?a maka ita dan kaima na daban ne, dan haka ka gayawa daddynku, zai ma fi kowa murna, jumma'ar nan a ?aura aure kowa ya huta".

"Haka kike so our Mammie?". A hanzarce ta gya?a kai. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce. "An gama, bari zuwa dare zan sami dad a part ?insa, kafin nan kinga daddy ma jirginsu zai dira, kinga shikenan sai ayi komai ko?".

Murmushin makirci suka saki a tare ita da Aliya. "Kwarai kuwa, ai ka yi kyan kai, ka je ka kwanta ka huta, na san a gajiye kake, saboda nasan tun ?azun hira ake yi da surukata kuma ?ata". ?ara fada?a murmushinsa ya yi tare da mi?ewa. "Our Mammie kamar kin sani, yanzu ma ban gaji da hira da ita ba, itace dai ta ce mun zata koma, shi ne yasa na kyaleta sai zuwa anjuma da yamma zan sameta a cikin gidan".

"Eyyye wato kai baka kunyata ko?".

Kai yasa ya nufi part ?insa yana fa?in. "Mammie kunyarki na me zan ji? Ke fa kika za?a mun ita, ai daga nan kunya ma ta kare, bari dai na yi barci na tashi zan zo ki tayani zabawa ?an uwana rabin jikina mata, dan kin iya za?a". "Kai ai Jawad baya son batun aure, gara ma kada ka yi mashi yanzu, ka kyalesa sai gaba"... ......Munafuka ta fa?i hakan ne dan kada ya je ya ce zai yi wa Yah Jawad maganar aure har su fahimci mace ?aya suke so, ba'a yanzu take son su fahimci hakan ba, ta fi so sai ranar auren ko kuma sai an bawa Rizwan ?in Jawad ?in ya san da hakan, daga nan komai na kwa?e, shiyasa ta yi saurin dakatar da shi.

Da yake yana bala'in kaunar kanin nasa, kada ku manta shi ka?ai garesa, kunga kuwa dole ya kaunacesa, sam baya son ?acin ransa, sai ya ce. "A'a ba sai ya ?ata rai ba, na kyalesa ya yi rayuwarsa, idan ya kara girma shi da kansa zai bu?aci yin auren". Yana kai karshen maganar ya shige ciki abinsa. Ya manta Yah Jawad ya ta?a ce mashi ya samu matar aure.

Wani irin murmushin mugunta suka yi tare da mi?ewa a tare suka wuce room ?in Mammie, dan su je su cigaba da kullah tuggunsu kada ya jiyosu.

___________________?????

A can cikin gida kuwa, sai can dare King Zuhair ya dawo, kai tsaye master room ?insa ya shige. Momma na jin labari ita da Akka suka yi maza suka garzaya izuwa room ?in nasa.

Tsaye yake a tsakiyar room ?in, ya har?e hannayensa ta bayansa, daga ganin yanayinsa zaka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali, damuwace a kewaye da shi, kamar ma zai fa?i kasa sabdoa ?acin rai, ba dan Allah ya tsare yana da taurin zuciya ba da ba abin da zai hana shi fa?uwa.

Tun daga ganin yanayinsa su Momma suka san ba lafiya ba, hakan yasa suka ha?a nutsuwarsu waje guda. Akka ce ta fara tambayarsa menene yake faruwa?.

Wani irin yawu mai ?aci ya ha?iye tare da furzar da wani irin isaka mai tsananin zafi daga bakinsa, sannan ya ja dogon numfashi, a hankali ya sauke. A hanzarce Momma ta ?auko mashi ruwa, hannunta har yana ?an kerma wajen balle marfin bottle water.

Tana mika mashi ya sa hannu ya kar?a, tun da ya kafa a bakinsa bai cire ba sai da ya shanye tas, karbar robar Momma ta yi. A hankali ya fara sauke numfashi mai tsananin zafi!.

A karo na biyu Akka ta sake tambayarsa meyake faruwa?.

Ajiyar zuciya ya sake saukewa, da kyar ya iya furta. "Akka babu Spender, sun ?aukesa daga gareni"....... Tashin hankali, ai wani irin jirine ya ?ebi Akkan, tafiya ta yi luuuu zata fa?i ya yi zafin namar tarota ta fa?a saman kirjinsa. Ita kanta momma ta shiga tsananin tashin hankali na wuce misaltawa, har wani juya mata kanta ta ji yana yi.

A saman gadonsa ya kwantar da Akkar tare da zama a gafenta yana mai bata hakuri tare da yi mata alkawarin tabbas koma a ina Spender yake dole zai kwato kayansa ya dawo da shi.

Me ala?ar King da Spender ne wai?. To ku bu?e kunnenku ku ji, Spender dai mallakin King Abdul Malik ne wato mahaifin su King Zuhair mijin Akka kenan, a yanzu da baya raye kunga kuwa mallakin ?a?ansa ne wato King Zuhair, uncle Abbas and uncle Jahiz, nasan kowa zai so jin menene wannan Spender, amma mu je zuwa zaku ji komai a hankali, sai dai kuma abin tambayar a nan shi ne, King Zuhair da yake babban sarki da kowace kujerar mulki a fa?in ?asar Tunisia take ?ar?ashin tasa kujerar, suna da karfin iko da isa, kada ku manta ko gate ?in masarautarsu babu wani mahalukin da ya isa ya nuna da ?an yatsa, jarumai ne wa?an da akewa maya?ansu ma la?abi da dangerous warriors, amma duk da haka ya aka yi Spender ta bar hannunsu take hannun Pretty? Akwai bala'i gaskiya, wai ni ina mummyn twin's ?in ne ma kam? Tana raye ne ko ta mutu? A ina ta samu Spender har ta nasu? Kai mu je dai zuwa, dan wa?an nan tambayoyi ma kara jefa mun ?wa?walwata cikin zafi zasu yi.

Tana daga kwance tana ganin jiri ta fara fa?in. "Zuhair kada ka yarda ka fitar da zancen Spender ya ?ata saboda abokan gaba, kawai ku nemosa ta ?ar?ashin ?asa".

Hannayenta ya ri?o cikin nasa tare da yi mata alkawarin aiwatar da hakan cikin ?an?anin lokaci.

A takaice a cikin wannan dare ya bugawa duk wasu amintattun cikin fada busar gayyata, sai hidimar gyaran masarautar ake yi saboda yakin da aka buga.

Yana buga masu busar gayyatar ba'afi minti biyu ba suka hallara a cikin meeting room ?insa, zama ta sirri ya gudanar a tare da su, ko ni kai'na basu bani damar jin abin da suka tattauna ba bare na kawo maku labari, sai dai ga dukkan alamu sun gamsu da tattaunar tasu, dan sun tashi taron fuskokinsu ba yabo ba fallasa, dama dai kunsan su ba dariya suke yi ba, musamman ma commander Zafar, ai shi wannan fuska kamar hadari take kullum.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull