Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 52
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 52: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 52. King bai iya kwanciya barci ba har sai da ya samu matsaya a kan ta yadda zasu…
3,280 words
King bai iya kwanciya barci ba har sai da ya samu matsaya a kan ta yadda zasu nemo Spender!. Sannan ne ya yi wanka ya samu ya sanya ha?arkarinsa a gado.
Haka ita ma Momma sai da ta samu tabbacin mijin nata ya samu nutsuwa ya dawo cikin hankalinsa sannan ta iya kwanciya.
Kafin King ya dawo uncle Abbas da ya yi isowar yamma ya zo dan su gaisa sai bai samesa ba, shi ma Rizwan ya zo da nufin ya sanar da shi batunsa shi da Chuchu a lokacin bai dawo ba, hakan yasa ya wuce part ?in Momma suka sha hira da chuchu, Jawad kuma yana tare da uncle Abbas a lokacin, sai tsokanarsa daddyn nasa yake yi yana tambayarsa ina Jannat? Sai ya wani kafe wai shi bai san in da ma take ba dan bashi da wata relationship da ita.
____________________________?????
Washegari da safe, uncle Abbas and uncle Jahiz sai Akka suka zauna zama ta sirri, sai dai King bai iya sanar da su cewa Spender ta ?ata ba, dan in ya gaya masu za'a samu matsala, Akka ta hana ma ya sanar da su, sun dai yi zama na tattaunawa a kan ?atar Jaish da sauran matsalolinsu.
Mummyn Gimbiya Chuchu ce ta bu?aci King da ya yarje mata zata shirya gagarumin walima na dawowar Guyson kamar yadda ta yi alkawarin kuma kamar yadda take shiryawa duk wanda ya dawo daga cikin ?a?an nasu, sai dai wannan karon zata ha?a da walimar nasarar yakin da suka ci, da yake ita bata san da batun ?acewar Spender ba yasa ta bukaci hakan, su suna cikin jimami ita kuma murna ma take yi, ko da yake dole zata yi murna dan a ganinta sun ci nasara a yaki ai abin murna ne.
Da farko King ya so hanata shirya walimar, amma sai Akka ta yarje mata, ta yi mata hakan ne kuma dan kada a fahimci batun ?atar Spender, dama a duk lokacin da suka ci nasara a yaki sukan shirya walima da manya manyan masarautu zasu halacta, duk wani mai ri?e da mu?ami zai hallara, suci su sha, su yi kyaututtuka, ayi abubuwa dai na bajinta da taimakawa talakawa, to kunga idan ba'ayi ba wannan karon dole jama'a zasu ce akwai wata a ?asa, hakan yasa Akka ta ce mummyn ta yi.
Kan kace me aka hau shirin walima. Shi kuwa Yah Jawad yau tun da sassaqfe ya shirya dan yana da gagarumin aiki a office, jiransa ma ake yi, sai kiransa a waya suke yi, sun takura mashi.
Jiya a tare da Rizwan ya kwana ?aki ?aya, kamar zasu cinye juna saboda so, ko shirin tafiya office da ya yi yanzu sai da Rizwan ?in ya taimaka mashi saboda kauna.
Yana fitowa daga part ?in daddyn nasu ya nufi part ?in King dan ya gaishe da su Momma kafin ya wuce office. Yau kingdom of power a cike take da baki, su uncle Jahiz sun zo, Guyson tun da suka zo yana tsakanin mummyn Gimbiya Chuchu da mommarsa, shi fa irin mutanennan ne mai ?ulafucin uwa, sai dai suna mugu mugun shiri da mummy, badan kaunar da yake yi wa mummyn ta musamman bace bama da ba zai iya motsawa daga kusa da mommarsa ko nan da can ba, amma yana kaunar mummyn, dan tana da farar zuciya tana kuma kaunarsa.
Duk girmansan nan, yana da kanne uku a duniya, amma tsabar shagwa?a da kulafucin uwa a ?akin momma saman gadonta ya kwana, bai san da batun dawowar King ba, tun karfe 8 ya yi barci abinsa, a saman cinyarta ma ya kwantar da kai ya yi barci, sai da ya yi barcin ne ta lalla?a ta kwantar da shi ta tafi wajen King.
JAWAD
Dab zai shiga ?akin Momma ita kuma tana fitowa, karo suka yi a in da kanta ya bugi faffa?ar kirjinsa.
Baya ta ?an yi tare da sanya hannu t........
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 28/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
E29
Baya ta ?an yi tare da sanya hannu tana murje gaban goshinta, da alama ta ?an ji zafin karon da suka yi. From toe ya fara kallonta yana ?agowa har izuwa face ?inta, da sanyi safiyar nan har ta tsantsara kwalliya, kai Chuchu duniyar kwalliya, idan ka ji mutum ya ce make up bata burgesa to fa bai ha?u da na Chuchu bane, ita ?in duniya ce.
Har ta tashi ta yi wanka, tsantsara kwalliya ta yi dan Yah Rizwan ?inta, wandon jeans doguwa ce sai riga zuwa gwiwarta a jikinta, a takaice dai Pakistan dressing ta yi, mayafin kayan babba ne yana ja mata har a ?asa, ga shi kuma net ne da ya ji flowers, ha?i?a kayan sun yi mata kyau sosai, gata fara kayan launin maroon and milk, abin ba'a magana.
Shakar dadda?ar kamshin perfume ?inta ya yi tare da lumshe idanunsa, a hankali ya sake warosu a kanta.
"Ina kwana Yah Jawad?". Ta fa?a a sanyayye.
Kawai kura mata idanu ya yi babu ko kyaftawa tamkar idan ya rufe idanun zata ?acewa ganinsa.
Sake maimatawa ta yi. "Yah Jawad ina kwana?". Hannu ya kai saman kansa ya ?an shafa arab hairnsa tare da sauke ajiyar zuriya.
"Jannat ki na yi mun son ranki a gidan nan". Ya yi maganar ce a zatonsa a cikin zuciya ya yi, sai da ya ji ta ce. "To ni Yah Jawad me kuma nayi maka?". Tana magana tana turo baki. A san nan ne ya fahimci ashe a fili ya yi maganar ba'a ?oye ba.
Girgiza mata kai kawai ya yi tare da cewa. "Babu komai, yanzu dai da kika yi wannan tsantsararren kwalliya ina zaki je? Kuma yau ba school ne?".
Tana ?o?arin yin magana sai ga Momma ta fito daga cikin room ?in. Shiru ta yi shi kuma ya ?agawa Mommar gaisuwa.
"Office zaka je yau ?in nan hakan zata yiwu kuwa?". Momma ta tambaya.
"Yeah Momma, sai kirana ake ta yi ne, wani aiki ne da muka yi apply since last two months ago sai yanzu fa daddy ya sanya baki aka sakar mana aikin, shi ne zan je in saka hannu".
"Tom shikenan ka kula sosai, dad ?inku dai ya ce su Jannat su zauna yau kada su je school saboda wannan yaki da aka yi, su dakata tukun nan zuwa kwana biyu komai ya koma normal". Tana magana tana kallon shi.
Sa kai Chuchu ta yi zata wucesu, dan ta lura hiransa da Momma ba karewa zai yi ba. Cikin sauri ya ri?o hannunta yana kawar da kallonsa daga kan Mommar. Harara Mommar ta watsa mashi tare da sa kai ta wuce abinta.
Tana wucewa ya matso kusa da ita. "Ina zaki je bamu gama magana ba? Ko kallonki mafa ban gama yi ba". Cike da so da tsantsar kaunarta ya yi maganar.
Cigaba da turo mashi baki ta yi bata yi magana ba. "Lafiya naga kin ?ata rai kuma? Yanzu fa face ?inki ?auke da ?ayatattcen murmushi amma daga Momma ta fito ta wuce shikenan kika dai'na murmushi why?".
Girgiza kai ta yi tare da cewa babu komai. ?ara matsowa kusa da ita sosai ya yi tare da rage tsawonsa ya ?an rankwafo kanta ka?an. ?asa ta yi da kai tare da ?an ja baya ka?an, dan har sautin numfashin juna suna ji, hakan yasa ta ?an matsa.
"Menene ya faru? Fa?a mun kin ji ko?". Ya fa?a murya kamar mai ra?a. Still dai girgiza mashi kai ta yi tare da cewa babu komai.
Hannayensa da ya har?esu a saman kirjinsa ne ga saukesu, ?aya ya ?aura a saman handle ?in kofar Mommar, ?ayan kuma ya yi kamar zai ?aura a saman jikin bango, sai kuma ya sauke shi a bayanta tare da janyota ta fa?a jikinsa, bai cire hannun nasa ba ko da ya janyota, sai ya kara ?an haura da shi sama daga mazaunanta izuwa tsakiyar bayanta. ?ara rankwafo kanta ya yi, a dai'dai saitin kunnenta ya fara yi mata ra?a.
?an zaro idanun nan waje ta yi. Dukan wasa ta kai mashi a kirji bam tana turo baki tare da fara ?o?arin ture shi, hannunsa na saman handle ya sauke tare da ha?awa ya rungumeta da kyau yana murmushi.
"Ni Yah Jawad ka kyaleni ko na je na gayawa Akka!". Tana magana tana ?ara ?aure fuska kamar wadda aka yi wa wani abin.
"Da gaske?". Ya fa?a kamar mai ta?a.
Kai ta gya?a mashi alamar e. "Okey tom yanzu dai a gaya mun meyake faruwa ko dai na aiwatar da abin da na gaya maki a cikin kunne zan yi".
"Please my sister, gaya mun me ya sameki kin ji?". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar.
Kwanciya a jikin nasa ta yi tare da fara magana a shagwa?e. "To Yah Jawad ba kai bane". "Ni kuma?". Kai ta gya?a mashi alamar e. "Menayi to?". "Ba kai ne kullum sai nace zan bika office ?inka sai ka ce mun a'a ba, to yau Allah na ?ata da kai, ni nasan Allah da Yah Rizwan ne nace zan je office ?insa zai tafi da ni".
Nan take face ?insa ya sauya, kishi ta motsa, sai dai kuma bai bari sai?an ya yi tasiri a ransa ba, ya yi ?o?arin kawar da hakan a in da ya ?a?alo murmushin dole, sannan ya ce. "Am so so sorryyyyyyy my sister, jeki shirya ki zo mu tafi, amma kada ki gayawa kowa har Auta ma, dan bana son dad ya samu labarin kin bini, bama dad ba kada kowa ya san kin bini, dan kinga dad ya ce kada kuje school yau, kada ku fita ko'ina duk dan saboda yakin nan da aka yi, dan haka kin ga ba zai ji da?i ba idan na fita da ke, so kada ki bari kowa ya sani kin ji?".
A hanzarce ta ?ago daga kirjin nasa, murmushi ne ya bayyana a saman face ?inta, da?i kamar ta zuba ruwa a ?asa ta sha, dama kunsan basu fita daga kingdom ?in, kullum suna ciki, idan aka ce zasu fita sai su yi ta murya tamkar wa?an da zasu je aljanna.
Haka kawai ya ji shai?an yana raya mashi da akwai wani abin a tsakanin Rizwan da ita, saboda idan suna magana tana yawan sanyo zanjen Rizwan a ciki, abin ya fara jefa shi cikin tunani, amma yana ta ?o?arin koran shai?an dake faman zugasa, fa?i yake bai kamata ko zai yi kishi da kowa ya yi da Rizwan ba, domin kuwa irin kaunar da yayan nasa yake yi mashi ya wuci tunaninku.
Wata ?angare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da ai koda da gaske Rizwan yana sonta ma ya cancanci ka bar mashi ita. ?ayan ?angaren zuciyar tasa ta ce mashi ina hakan ma ba zai yi wu ba, ba wata ala?a a tsakaninta da Rizwan face ala?a ta yaya da kanwa, shakuwa ce kawai dan yana kyautata mata.
Ha?i?a dai yanayinsa ya sauya, ga dukkan alamu ya shiga damuwa sosai, dan har bugawar zuciyarsa ta canza daga yadda take da, amma dai yana ?o?arin ya kawar da tunani, sai da ya sanya a ransa idan suka je office zai tambayeta me a tsakaninta da Yah Rizwan? Idan ta gaya mashi sa?anin abin da yake zargi to tabbas a yau zai bayyana mata soyayyarsa, idan kuma ba haka ba........ Hmmmm akwai matsala kuwa!!.
Ta lura da canjin da face ?insa ya yi, ta lura da damuwa ta bayyana a tattare da shi, dan haka sai ta ce. "Yah Jawad tunanin me kake yi?".
Ajiyar zuciya ya sauke tare da sakar mata murmushi kafin ya bata amsa da. "Ina tunani ne a kan yau zaki ga budurwata abar so na, kina son ganinta ko?". Ya jefa mata tambayar yana kura mata idanu, dan yana son gane shin ita ma tana son shi ne ko dai kawai sha?uwa ce a tsakaninsu? Zuciyarsa sai harbawa da sauri take yi, yana fargabar amsar da zata bashi.
"Dama kana da burdurwa da gaske kamar yadda su Aunty Sarina suka fa?a?". Ta jefa mashi tambayar tana ?an tur?une fuska.
"Yeah Jannat, ina da budurwa kyakkyawa sosai fara mai kama da dad ?ina, yau idan mun je office zaki ganta ai". Har lokacin fargabar jiran amsarta yake yi.
?aure fuska sosai ta yi kamar ba ita ba. Murya ?asa ?asa kamar wadda bata son motsa bakinta ta ce. "Tom shikenan mu je".
Ya lura da ita sosai, sam ranta bai so jin zancen nasa ba, da alama ma hankalinta ya tashi, murmushi ya kau daga saman face ?inta. "Jannat lafiya kuwa?". Ya fa?a yana le?o face ?inta, dan ta sunkuyar da kai ?asa.
Idanunta ne suka cicciko tab da kwallar da ita kanta bata san na menene bane, haka ?ai ta ji komai ya canza mata, har sara mata kanta ta ji yake yi mata, nan take ta ji kamar zazza?i ne yake son kamata, duk sai ta ji bata ma son sake ganin face ?insa, kishi ne ?aro ?aro ya bayyana a tattare da ita, tabbas kuma ya lura da hakan, ya lura da kishinsa ne fal a tattare da ita, abin ya yi mugu mugun yi mashi da?i, ransa ta yi sanyi sosai, zuciyarsa har wani irin sanyi ne ya ratsata, ya samu abin da yake so.
Ita kuwa da yake kishin fa a jininsu yake, abin nasu na gado ne tun daga kan King Abdul Malik, bala'in kishi ne da kakan nasu, haka ita ma Akka, tsabar bala'in kishin Akka yasa King Abdul Malik duk zafinsa bai iya yi mata kishiya ba, dan yasan duk wanda ya auro wlh kishin Akka ba zata ta?a barin ?ar mutane ta zauna lafiya ba, shiyasa ma bai fara ba, an san sarki da mata hu?u cif, amma ban da King Abdul Malik, duk kuma saboda kishin bala'i da suke da shi, so ku sani abin nasu na gadone, a jininsu yake, kada ku ga laifin Chuchu, gado ta yi, sai dai ko a cikin nasu ma na wani ya fi na wani zafi kishin.
"Jannat lafiya kuwa? Menake gani a idanunki kamar hawaye?". A ?an ru?e ya yi tambayar, dan bai ta?a tunanin kishinsa zai sanyata kuka ba. Yana magana yana wani waskewa kamar bai san me take yi wa hakan ba.
Ra?awa ta jefensa ta yi zata wuce da gudu, dan ta ji ta gaza tsayuwa a wajen ne, ba zata iya ba. A zafafe ya ri?o hannunta tare da jawota jikinsa. "Jannat menene?". Ya fa?a still yana ru?e.
"Ni Yah Jawad ka sakeni!". Ta fa?a da ?an ?aga murya. Ajiyar zuciya ya sauke tare da ?aukarta cak sai saman shoulder ?insa. Kuka ta fara yi mashi sosai tana bubbuga bayansa a kan ya sauketa sun ?ata kowa ya kama kansa, bai kula ta ba sai saman bed ?inta ya sauketa tare da duba watch dake manne a hannunsa, kirar Rolex deepsea wadda a ?alla darajar ku?inta ya kai dollars 10,000, naira kuma ta kai naira million dubu goma sha biyar.
"Tashi ki shirya mu tafi kin ga lokaci yana ta kurewa". Kuka take yi sosai wanda ita kanta bata san dalilin yin sa ba, da kyar ta iya cewa. "Ni Yah Jawad babu in da zan je, ka yi tafiyarka kawai". Tana kai karshen maganar ta kifa kanta a saman pillow ta cigaba da rera kukanta.
A can wajen su Mummy kuma sai shirin yin walima ake yi, da misalin karfe hu?u za'ayi walimar.
Ya janyowa kansa rigima, dole kuma ya kashe wutar da ya kunna. A hankali ya zauna a gefen gadon, hannu biyu yasa ya ?agota daga kan pillown, a kirjinsa ya manta, sai ?o?arin ture shi take yi, idanu a datse gam take fa?in. "Ni ka kyale ni, ka tafi kawai, kuma ni bana son ganin burdurwar taka, kuma ba zan ta?a zuwa office ?in naka ba, na tsani zuwa, ni ka barni". Sai sambatu take yi idanu a rufe.
Dariya ce ma taso kubce mashi, su Jannat ma ansan kishi, Allah mai iko, ji yadda take kuka kamar wadda aka cewa mummynta ta mutu, ta ha?i?ance sai zabgar kuka take kamar ba gobe, yanzu da zaka tamnayeta dalilin yin kukan nata ba ta da amsa.
"Yanzu dai na ji zan tafi, amma kafin nan sai wannan kyakkyawar tawa ta gaya mun me nayi mata take wannan kukan?". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar.
A fa?a ce ta ce. "Ni ba kyakkyawa bace, budurwarka ce kyakkyawa ko ka manta haka kace a bakin kofar Momma? Har da cewa kyakkyawace sosai, wato ta fini kyau ko?........" Ta ?an dakata da yin maganar saboda jan numfashi da ta yi irin na mai kuka.
"Kuma kai ne ka ce nafi kowa kyau a duniya ranan a parlon dad, ashe kenan Yah Jawad kai ma kana fa?ar magana biyu ko?". Tana kai karshen maganar ta sake rushewa da kuka mai sauti.
Yau ga ikon Allah yana gani, ji yadda ta ha?i?ance tsakaninta da Allah take murzan kukan nan nata, Chuchunmu mai abin mamaki, ko ina ta baro soyayyar Yah Rizwan da take kishin Yah Jawad a nan kuma? Yau muna ganin ikon god.
?asa sosai ya yi da voice ?insa a in da ya kawo bakinsa dai'dai saitin kunnenta, magana ya fara yi mata cikin sigar rarrashi ha?e da tsantsar so da kauna.
"Am so so sorryyyyyyy my Jannat, wlh ba da wasa nake yi maki ba, kuma ni ba mai magana biyu bane, kamar yadda na gaya maki a idanuna wlh babu wata mace da ta fi mun ke kyau, kyanki ke ka?ai ce babu mai irinta kin ji ko? Dan Allah ki dai'na kukan nan haka ya isa".
Hannu ta ?aga ta fara kai mashi dukan wasa a kirji tana fa?in. "Koma me zaka ce tun da kana da budurwa babu ruwana da kai........."
Katse mata maganar ya yi da cewa. "To meyasa? Meyasa zaki ce babu ruwanki dani dan ina da budurwa? Ko dai kina sona ne?".
A hanzarce kuma ta fara girgiza kai tana fa?in a'a bata son shi. "To baki sona kuma ki ce kada na yi budurwa? Ke zan aura ne?".
Kai ta girgiza alamar a'a. Shiru ya ?an yi kafin ya ce. "To tashi ki je ki shirya mutafi ko?". Ya kai karshen maganar tare da ?ago ha?arta ya shiga goge mata hawayen face ?in nata da white handkerchief da ya ciro daga aljihunsa.
Shiru ta ha?iye kukan nata a in da ita da kanta ta shiga tambayar kanta kukan me ma take yi ne kam? Ina ruwanta da budurwarsa? Ita da take da Yah Rizwan meyasa zata ji babu da?i dan shi ma yana da budurwa?. Haka ta rin?a jefawa kanta tambayoyin da babu amsarsu, daga ni sai ku my people's muka san wannan amsa ko ba haka ba? Mu mun san kishinsa take yi, dan a ?ar?ashin zuciyarta akwai kaunarsa da bai taso izuwa saman zuciyar tata ba, hakan kuma bai faru bane dan bai bayyana mata nasa son ba, da zai gaya mata tabbas nata ma zai bayyana. Ita fa bata san menene son soyayya ba, ba kuma ta iya banbanta so da son ?an uwantaka ba, tabbas tana son Yah Rizwan haka zalika tana son Yah Jawad ?in ma, sai dai banbancin son da take masu a nan shi ne, Yah Rizwan da?a?an kalamansa yasa take jinsa a ranta, ya kuma ha?u da jini, sannan kuma akwai son ?an uwantaka.