Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 53
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 53: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 53. Shi kuma Yah Jawad, na farko akwai sha?uwa mai karfi a tsakaninsu, sannan…
3,371 words
Shi kuma Yah Jawad, na farko akwai sha?uwa mai karfi a tsakaninsu, sannan akwai son yaya da kanwarsa da take yi mashi na daban, dan ko Bilal da suke uwa ?aya bata yi mashi son da take yi wa Jawad ?in, sannan akwai soyayya mai karfi ta aure da take yi mashi wanda ita da kanta bata san hakan ba, so ta yi ?an?anta iya banbance wa?an nan abubuwa, shiyasa zaku ga zata nunawa Rizwan so ta kuma nuna kishi a kan Jawad, dan a cikin duhu take ita yanzu, babu mai iya kunna mata haske ta fita daga cikin wannan ru?ani sai Jawad ?in, shi kuma ya biyewa gur?ataccen tunanin da zuciyarsa take sanya shi, ya tsaya kallon ruwa kwa?o zata yi mashi kafa.
Raba jikinta da nashi ta yi, sannan ta sau?o ?asa ta nufi dressing room ?inta, jim ka?an ta fito ri?e da wasu kaya a hannunta, toilet ta nufa. Da kallo ya bita yana jin wani irin sanyi tana ratsa shi, ko ba komai yau ya san yadda Jannat ta ?aukesa, yasan yadda take jinsa a ranta, irin wannan kishi haka ai sai wanda ake matu?ar kauna ne zai samu haka.
Wayarsa ya ciro ya shiga amsa kiraye kirayen da ake ta yi mashi, jiransa ake yi yazo ya sanya hannu, tun wuraren karfe 6 bakin nasa suka zo, suna ta jira yasa masu hannu a takarda su mayarwa minister, amma ya zauna biyewa Chuchu.
Wanka ta yi ta shirya cikin wandon jeans white and t-shirt pink, ta yi wa kayan kyau sosai, sai ta ?aura after dress a saman kayan, ta yi rolling gyalen after dress ?in a kanta, a cikin toilet ta kammala shirin nata tsab, sannan ta fito.
Tun da ta fito ya kura mata idanu babu ko kyaftawa, tana kallonsa amma sai ta yi kamar bata gani ba. Dressing room ?in ta koma, simple make up ta ?an yi da yake akwai kayan make up a ciki, sannan ta sanya lips balm a ?an bakinta, ta ?auki high heel ta sanya a kafafunta, kun santa da iya zuba perfume, haka fa ta zuba sosai. Sai da ta gama fesa perfume da Momma ta bata ne idanunta suka sau?a a kan kwalbar perfume da Mammie ta bata, ji ta yi ai da shi ta fesa, kamar zata ?auka ta ?an fesa sai kuma ta ce kamshin zai yi mata yawa over bari ta barshi sai ta yi wanka da daddare......... Tir?ashi!! My people's akwai kallo! Kuna tunanin perfume ?in Allah da annabi Mammie ta bata kuwa?! Muje dai zuwa.
Fitowa ta yi yana zaune yadda ta bar shi, zuba mata idanu ya yi har ta ?ariso gabansa, tana tafiya tana wani yauki kamar hawainiya rai a ?ace, sai tura baki take yi dan tsabar kishi.
Mi?ewa tsaye ya yi tare da ri?o hannunta yana fa?in. "Jannat duniyar kyau, haba akwai wanda ya isa ma ya ce akwai wadda ta fiki kyau ne? Wane mutum! Ke ?in ta daban ce".
Shiru bata amsa mashi ba, dan har yanzu kishi ne yake cin mata ?ar?ashin zuciya, bata son yin magana da shi, idan ta ce zata yi magana kuka ne zai kubce mata. Mata kenan, mu ai daban muke da kowacce halitta ato, manzon Allah (S.A.W) ya ce a karkace muke babu wanda zai yi dai'dai damu, sai dai a lalla?a a bimu yadda muke a karkace ?in dan a samu zaman lafiya. Wasu malamai suka ce kamar aljanu muke.......????
Jin bata yi magana ba sai bai wani damu ba, dan yasan me take yi wa fushi, burinsa kawai su je office ?in ya nuna mata wacece budurwar tasa dan ta samu kwanciyar hankali ta kuma koma cikin farincikinta kamar ?azun, yau ransa tas, duk wani fargaba da yake ji na tana son shi ko bata son shi yau ta kau daga zuciyarsa, dan ya tabbatar so mai karfin gaske ma take yi mashi.
Suna fitowa waje ya saki hannunta tare da ce mata ta yi gaba ta jirasa a wajen motarsa, baya son a gansu a tare ma bare ace shi ya fita da ita in ba'a ganta ba. Wucewa ta yi ba tare da ta yi mashi magana ba, sai wani shakar dadda?ar kamshin perfume ?inta yake yana lumshe idanu, har wani barci barci yake ji saboda da?i.
Da tafiyarta kamar da minti biyar sai ya bi bayanta, a lokacin su Akka suna meeting a kan Jaish, so sai bai je in da suke ba ya nufi office kawai.
Bai yi sallama da Rizwan ba, tsabar hankalinsa yana a kan Chuchunsa, burinsa kawai su tafi office ?in ya je ya yi ta tsokanarta tana ?ata rai, yau dai ya samu damar ?a?aicewa da ita su wuni a tare, yana matukar farinciki da hakan.
Tana fitowa motarsa ta nufa, securitys suna ganinta suka rufa mata baya, suna isa wajen da take ta ce masu su bu?e mata motar. Cikin girmamawa ?aya daga ciki ya ce mata key baya hannunsu sai dai su jira shi ya zo.
?aya daga cikin securitys ?in ne ya sake ce mata. "Ranki ya da?e ko kina bukatar wani abin bayan bu?e kofar motar kafin ya zo".
Kada ku manta da larabci fa suke yin magana, dukkansu larabawa ne har securitys ?in.
Da yake dai izza a jininsu take sai ta girgiza mashi kai kawai tare da ?aga masu hannu alamar zasu iya tafiya bata bukatar komai, ta yi hakan ba tare da ta yi magana ba, ko kallon in da suke ma bata yi ba, sai kawai ta jingina bayanta da jikin motar ta hau latsar waya. Chat ta shiga yi da Rizwan dake kwance a saman bed ?in Jawad daga shi sai short and single.
Har ya iso in da take bata sani ba, dadda?ar kamshin perfume ?insa da ya cika mata hanci ne yasa ta ?ago kai, ya har?e hannu a saman chest ?insa tare da zuba mata idanu yana ganin yadda take sakin murmushi, hankalinta na a can Rizwan yana zuba mata kalamai tana sakin murmushi, massage na karshe da Rizwan ?in ya tura mata shi ne ta kawo mashi breakfast yana ?akin Jawad a part na King Zuhair kenan, sai dai bata ga wannan massage ?in ba, dan a lokacin ta dawo da kallonta kan shi. Tana sauke idanu a kansa ta ?aure fuska kamar ba ita ce ke murmushi a yanzu ba, kalamar Rizwan suna yi mata yawo a cikin kwakwalwarta.
"Sarkin buga game and ?aukar hoto, meyafaru kike ta murmushi haka? Sannan me na ha?a fuska daga ganina?". Ya fa?a tare da cire hannunsa daga saman chest ?in nasa, gently ya tako izuwa gabanta. Securitys ?in da suka biyosa da ganin fitowarsa ne suka tsaresu da idanu, su kansu sun ga dacewarsu a matsayin mata da miji ba yaya da kanwa ba.
"Ni babu abin da nake yi, kuma ni dama can face ?ina a ?aure take". Cikin fushi ta yi maganar.
Ajiyar zuciya ya sauke. "Haba my sister! To shikenan dai muje ko?".
Jin ya ce muje yasa da sauri wani katon dakakken arabs man daga cikim securitys ?in ya matso ya sanya hannu ya ?alle kofar motar back seat. Da hannu ya nuna mata ta shiga.
?an murgu?a baki ta yi a tunaninta bai ganta ba, sarai kuma ya ganta, sai dai ya yi kamar bai gani ?in ba. Ciki ta shiga tana tura baki kamar wadda aka yi wa dole zuwa office ?in, bayan kuma ita ta ce zata bisa.
Tana shiga ta matsa can jikin ?ayar kofar, rufa mata baya ya yi, a maimakon ya zauna a kusa da nasa kofar, amma sai ya matso kusa da ita. Wannan securityn ya rufe kofar sannan ya shiga driving teas ya zauna.
Sauran securitys da a kallah zasu kai goma da hanzarin suka juya zasu nufi nasu motocin Jawad ?in ya ce da drivern nasa ya dakatar da su, dan yau baya da bu?atar gayya.
Da sauri securityn ya risinar da kansa alamar ya kar?i umarni, sannan ya isar da sakon kamar yadda ya fa?a.
Juyawa suka yi suka koma muhallinsu.
"I'm late dan haka ka taka motar nan da kyau dan mu isa da wuri". Ya fa?a yana duba agogon dake hannunsa, ga uban miss calls da suka cika mashi waya na ana jiransa.
Haba ai a dubu ya taka motar suka nufi gate one.
"Yah Jawad yanzu ita budurwar taka a companynka take aiki ne?".
?an satar kallonta ta wutsiyar idanu ya yi, wani irin sanyi ya ji a cikin zuciyarsa, wato har yanzu batun yana cinta a cikin zuciyarta, Allah ya gani yana jin da?in wannan kishi da take nunawa a kansa.
"Yeah a can take". Ya bata amsa ba tare da ya kalleta ba.
Har?e hannayenta a saman kirjinta ta yi.
"To Yah Jawad yanzu idan muka je zan ganta kenan tana aiki?".
Gya?a kai ya yi tare da tabbatar mata da hakan. Switch off na wayarta ta yi mai gaba?aya sai kace wayar ce ta yi mata laifi, sannan ta ?aure fuska kamar hadari.
"Yah Jawad kuma idan muka je dole sai na ganta ne?".
"Kwarai kuwa, zaki je har office ?inta ki gaisheta tun da Auntynki ce". A dake ya yi maganar tamkar da gaske yake yi, yana yi yana satar kallonta, yadda ta ha?e rai kamar wata jagaba, ita a dole kishinsa take, daga ta cikin zuciyarsa dariya sosai yake yi mata, da kyar ya iya danne dariyar na fili dan ya samu damar cigaba da ganin turo wannan ?an bakin kamar ya yi kissing ?insa.
"Yah Jawad please ka mayar dani gida dan kai'na yana yi mun ciwo, ni na fasa zuwa". Ta fa?a tana dawo da kallonta a kansa.
Da yake dukka yare ?aya suke yi sai ya zamana driver yana jin duk abin da suke fa?a, mamaki Chuchun ta bashi na yadda take da wannan kishi haka, sannan abin ya so bashi dariya yadda Jawad ?in yake yi mata yawo da hankali.
Shi ma juyowa ya yi suka kalli juna ido cikin ido, nan take dukkansu wani irin sa?o na musamman daga zuciya izuwa zuciya ya isan wa zu?atansu a lokaci guda, a wani irin yanayi na tsananin ?ishin ruwan son kallon juna suka tsinci kansu, kurawa juna idanu suka yi kowannensu da abin da yake tunawa a ransa.
Shi hangosu yake yi a matsayin mata da miji cikin ?an ?an?anin lokaci, ita kuma tunanin yadda zata ga budurwar tasa kawai take yi, tsabar kishi har haskowa take a idanunta ga shi a tare da wata a cikin office nasa suna kashe juna da hira, ita ina zata sanya ranta yau? Ta jefawa kanta tambaya.
Jin sun yi shiru yasa wannan securityn ya fara satar kallonsu ta cikin mirrorn motar, ha?i?a sun yi matu?ar burgesa, har ya ji dama ace shi ne, ji yake da zai samu dama tabbas yadda suka mace da kallon junar nan sai ya ?aukesu hotuna, amma ina babu damar yin hakan, dan bai isa ba, bashi da wannan dama da kwarin gwiwa.
Ya dai'na ganin hanya sosai, ya koma kallonsu ta cikin mirror, ya ga madarar kyau sun ha?e waje guda.
Dukkansu sun mance da in da ma suke, sai da driven ya taka wani irin birki wanda yasa suka yo gaba, ta tafi zata buga kanta da jikin kujerar motar yasa hannunsa a tsakanin kan nata da kujerar, hakan yasa kan nata ya sau?a a kan hannunsa, abin gwanin birgewa, duk da accident suka kusa yi amma shi hankalinsa yana a kanta, tabbas soyayyarsa a gareta ba ta wasa bace.
Dawo da ita saman kirjinsa ya yi tare da juyo da kallonsa a kan drivern domin ya tambayesa me ya sanya zai ja irin wannan birkin?.
Suna ha?a idanu tun bai yi magana ba drivern ya shiga bashi hakuri, ya je yana satar kallonsu ne ta cikin mirror har motar tasu ta kauce daga kan hanya tana ?o?arin sauka daga titin, shi ne da ya farga ya taka wannan irin burki mai rikitarwar.
Ita kuwa da ta gama tsorata ta kwantar da kanta luf a saman chest ?insa tare da datse idanu kam tana sauke numfashi, ta wani ?an?ame jikin rigarsa kamar ya ce zai gudu ya barta.
Jin ya fara bashi hakuri yasa sai bai yi magana ba, da hannu ya yi mashi nuni a kan ya tada motar su tafi. Haka kuwa aka yi, a hanzarce ya yi mata key, da gudun gaske ya bar wajen.
Dawo da kallonsa a kanta ya yi, ta tsorata sosai, kamar zai ambaci sunanta, sai kuma ya fasa, dan ya tuna ashe fa?a suke yi, gara ya kyaleta har sai sun isa kawai.
After 10 mins.
A marking space na katafaren Companyn nasa drivern ya yi parking. Jin motar ta tsaya ne yasa ta bu?e idanu a hankali tana jin tsoron abin da zata gani.
Like wow a cikin zuciyarta ta furta, ashe haka Companynsa take duniya guda, gaba?aya ginin glass and tiles ne, ba shakka dukiya ta yi kuka a wannan wajen, ta yi mubaya'a.
Da sauri drivern ya fice waje ya barsu a cikin motar, a dai'dai lokacin kuma wasu jiga jigan securitys dake Company suka ?ariso wajen motar, dakatar da su drivern ya yi a in da ya ce kada su bu?e motar dan yau yallaboi a tare da madam suke, dan haka su dakata, sai ka ce an ce mashi madan ?insa ce ko kuma ita yake son aura, shi dai tun da yaga sun dace mashi sun kuma birgesa shikenan ya ?aura masu aure a ?angarensa.
"Jannat ta shi mu je ko? Ana jirana". Ya fa?a tamkar mai ra?a.
"Yah Jawad ni fa bana son ganin budurwar nan taka, ka ce kada ta zo in da nake, kuma ni ma ba zan je in da take ba".
"But why?". Ya yi maganar yana ri?o hannunta da yake saman kirjinsa ta ?ar?ame rigarsa saboda tsoro.
"Ni dai babu wata dalili kawai bana sonta ne". Tamkar zata rushe da kuka ta yi maganar.
"Jannat baki son abin da nake so?".
A takaice ta ce. "Ina son duk abin da kake so amma ban da budurwarka". Tana kai karshen maganar ta raba jikinta da nashi tare da juyawa zata bu?e door ?in side ?inta.
Hannunta dake sar?afe cikin nasa ne ya dakatar da ita daga yun?urinta na bu?e kofar ta fita. ?an juyo da gefen face ?inta ta yi tana kallan hannun nata.
"My Jannat uwar rigima, to dai yanzu komai zai wuce mu je, za dai ki ga budurwar nan tawa yanzu". Ya kai karshen maganar tare da sakar mata hannu.
Bata sake ce mashi uppan ba ta bu?e motar ta fito. Ganin ta fito yasa securitys ?in har suna rige rigen bu?e door ?in side ?insa. Cikin izza ya zuro kafafunsa waje kafin ya fito gaba?aya. Wani irin ?aure fuska na musamman ya yi, cikin isa da izza ya fara takawa ya kewayo ta side ?in da take, tana tsaye shiru.
Hannunta ya ri?o ba tare da ya yi magana ba, ciki suka nufa, kai tsaye sai wajen ha?a??iyar elevatorn da zata sada shi da office ?insa ya nufa.
Tunda Allah yasa suka sako kafafunsu cikin companyn duk wasu ma'aikata suka fara binsu dana mujiya, ga wasu rika??un securitys dake gadi tun daga farkon corridor da elevator yake saukesa wajen office ?insa kenan har izuwa bakin door office ?in, dukkan securitys ?in sanye suke da pea suit, ga wani uban black glass kamar dai yadda kuka san dressing na securitys, dukkansu arabs mens ne, farare kal da su.
Kafin ya kai ga wajen elevator ransa ya gama ?aci, dan kuwa yaga idanu iya idanu a kan Chuchunsa, sai kallonta suke yi, kishinsa ta motsa shi ma. Wasu suna yi masu kallon suna kama, wasu kuma suna yi masu kallon mata da miji, wasu su ce sun dace, wasu kuma da yake duk wanda ya kwana ya tashi a Companyn yasan Jaish sai su ce ai da Jaish ta fi dacewa, wasu kuwa su ce daga gani wannan kanwar Jaish ce dan sun fi kama da shi, kowa dai da abin da yake fa?e, tamkar zasu cinyeta da idanun.
Sai tambaya suke yi wai master ya yi aure ne? Da yake master suke ce mashi.
Duk in da zai wuce sai securitys sun girmama shi ha?e da sara mashi, gaba?aya ma'aikatan wlh tsoronsa suke ji, dan yadda suke bashi girma mugu mugun shakkarsa da tsoro suke ji. Duk wani ma'aikaci ya zo wucesa sai ya gaishesa cikin tsananin girmamawa, abin ya yi mugun bata mamaki, bata ta?a tunanin haka yake da girma sosai a waje ba, ga shi ya wani ?aure face no respect.
Bata tashi shan ainahin madarar mamaki bama har sai da suka hau elevator ta kai su hawa na hu?u in da office ?insa yake. A nan ne taga abin al'ajabi, yadda ?an wannan hawa suke girmama shi jiki na kerma, yadda kuka san yana dukansu ko yana basu hukunci mai tsanani. Ga company nasa duniya ce guda, number one ce, a kallah ba'a ?asara ba ma'aikata zasu kai dubu goma da suke aiki a ?ar?ashinsa.
Duk securitys dake wajen wani irin girmama shi na musamman suke yi, bata gama tsinkewa ba har sai da ta kalli office ?insa, a ranta take fa?in. "Ashe Yah Jawad haka yake a waje? Ji yadda kowa yake bashi girma matu?a, amma a gida na mayar da shi abin wasa na?". Abin ya bata mamaki sosai.
Yana shiga waiting room ?insa wata matashiyar budurwa ta iso wajen cikin kerman jiki, dama waiting room ne a farko kafin office na P.Ansa sannan sana shi ne a canciki.
Sanitizer ne mai kyau da tsada rike a hannunta, a gabansa ta tsaya cikin girmamawa, while shi ma ya dakata da tafiya, tafukan hannunsa ya bu?e mata, matsa mashi sanitizer ta yi.
Cike da class ya murje hannun nasa da kyau, sannan ya ri?o hannun ita ma Chuchun ya bu?ewa yarinyar tafukanta ta matsa mata a ciki. Da kansa ya murza mata shi, sannan suka wuce ciki, sai binsa da kallon mamaki yarinyar take yi, ita kuma Chuchu sai banka mata harara take yi kamar ba lafiya ba.
Suna shiga ta hango P.A a hakimce a saman kujera, sai juyi take yi a saman kujerar, ga sanyin Ac na bugata, ita ma da take P.A office ?inta ba ?aramin girma bane da shi, akwai komai a ciki har da toilet.
Tana ganinsa ta mi?e tsaye tare da fara kwasan gaisuwa ha?e da yi mashi sannu da zuwa.
?aure fuska sosai Chuchu ta yi, dan a tunaninta wannan ce budurwar tasa, dan taganta a office.
"Barkanki da zuwa ranki ya da?e". Cewar P.A ga Chuchu.
Wani irin kallon ?as?anci da wala?anci ta bita da shi ba tare da ta amsa gaisuwar ba.
"Yah Jawad ina ne office ?inka? Dan ni wucewa can zan yi".
Yadda ta yi maganar sai ta baka dariya, kishi kiri kiri, ko waye ya ce mata ita ce budurwar tasa? Kai Chuchu ikon Allah. Ita kanta P.A ta lura da balai'n kishin da yake kwance a cikin idanunta, hakan yasa ta fahimci duk yadda aka yi Chuchu matar ogansu ce ko kuma wadda zai aura, ?aya cikin biyu, dan haka sai ta kama kanta kada ta ci duka, a cikin ranta fa?i take. "Shiyasa master baya ?aga idanu ya kalli mutane kenan? Allah mai iko, dama kana da wannan ha?a??iyar beauty flower yaushe zaka kalli wasu matan? Yanzu kenan master a maza fa yake kallonmu, dan idan irin wa?an nan mata suna a gabanka a maza zaka rin?a kallon sauran mata, ni kam yau ina Rashidah take ne? Ita sarkin ji da kyau har tana ikirarin zata iya sace zuciyar oga da wannan ?an guntun kyan nata, to yau ta zo ta ga kyau a nan, ai tana zuwa kusa da wannan zata zama kamar namiji, Allah ya yi halitta a nan, ga iya ?aukar gayu, ji yadda kayan jikin nan nata ya zauna mata da kyau kamar dan ita aka yi su, master ban ga laifinka ba na kin ?aga idanu ka kallemu, dole ka ru?e a nan gaskiya, ashe a maza muke a gabaka, yau ina Rashidah ne". Sai sambatu take yi a cikin zuciyarta, da alama wannan P.A ?ar iska ce, dan har da fa wani lashe baki take yi tana karewa Chuchunmu kallo.