Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 54
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 54: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 54. Ta kai karshen zancen zucin nata bata san lokacin da dariyar mugunta ya kubce…
3,334 words
Ta kai karshen zancen zucin nata bata san lokacin da dariyar mugunta ya kubce mata ba, ba dariyar komai kuma ba ne ya kubce mata face dariyar Rashidah da take jiji da kai ita kyakkyawace, to ashe dai a namiji ma Jawad yake kallonta, shi ne abin da ya bawa P.A dariya.
Ganin Chuchu ta dalla mata harara ne yasa ta yi cak ta tsayar da dariyar. Shi kuwa ko kallon in da table ?in P.An yake bai yi ba, kamar bai ji ta yi dariya ba
"Fuck dirty girl!". Chuchun ta fa?a a bayyane.......... Ni kuwa nace ashe dai Chuchun mu ta iya fa?a, ashe ba'a iya gayu aka tsaya ba har da tsiwa, kunji ta kama zagin mata ba gaira babu dalili, sai kace ance mata ita ce budurwar yayan nata.
"Jannat lafiya?". Ya fa?a a sanyaye yana kallon face ?inta dake ?aure kamar hadari.
"Ni dai ka nuna mun office ?inka kawai". Kamar zata sa kuka yi maganar.
Cigaba da tafiya ya yi suka shiga cikin nasa office ?in. Suna shiga a maimakon ya wuce saman kujerarsa, sai ya zauna a saman ?aya daga cikin sofars set dake cikin office ?in, a saman three seater ya zauna.
Yana zama sai ga wani matashi da ba zai wuci 20 years ba, a gabansa ya zo ya tsugunna ya hau cire mashi takalma izuwa sock.
Bayan ya kammala ya mi?e ya kaisu ma'ajiyarsu, sannan ya fice, shi ma mi?ewa ya yi izuwa saman nasa kujerar ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.
"My Queen zan iya samun ruwan sha?". Ya fa?a yana kallonta, ta zauna saman sofa tana ta aikin tur?une fuska.
Shi fa duk abin da take yi yau kara sanyayya mashi zuciya take yi, dan kishin da take nunawa a kan nasa ma ya ja sonta ya ?ara ninninkuwa sosai a ransa.
Mi?ewa ta yi ta isa gaban freezers dake cikin office ?in. Bu?e ?aya ta yi ta ciro ruwan, ta dawo wajen kyakkyawan show glass da ta gani a ta kusa da shi, a shake yake da cups and small plates kala kala for snacks. Guda ?aya ta ?auko mai kyau, a gabansa saman table ta ajiye mashi da nufin ta juya.
Hannunta ya ri?o, da sauri ta juyo, saman laps ?insa ya nuna mata a kan ta zauna. Babu musu ta zauna tana mai kallon face ?insa.
"To zuba mun ruwan". Yana magana yana ?aga kansa izuwa kallon pop.
?aukar robar ruwan ta yi tare da fara ?o?arin bu?ewa, kasawa ta yi hakan yasa ta ajiye tana fa?in. "Yah Jawad ya yi tauri sosai ba zan iya bu?ewa ba, amma ka kira budurwar nan taka ta zo ta bu?e mana, dan naga ita lukuta ce kirar adawa ko sumudawa zata iya".
A ?ari ya sau?o da kansa ha?e da kallonsu izuwa kan ?an bakin nata, wato dai a fakaice ita a dole ta zagi P.A da take yi wa kallon budurwarsa ce, ba shakka Chuchu ita ma akwai fa?a kam.
?aukar ruwan kawai ya yi tare da bu?ewa ya zuba a cup ?in bai ce ko uppan ba. Sosai ya sha sannan ya cireta daga bakinsa.
Kawo mata saitin bakinta ya yi, dama ita ma tana bu?atar shan ruwan, dan haka sai ta bu?e baki ya sanya mata. ?an dai'dai tasa ta cire baki.
Tunani ya fara yi ta yadda zai bayyana mata soyayyarsa a gareta, can dabara ya fa?o mashi ya ce ta rufe idanu sai ya kaita gaban mirror dake cikin office ?in, sannan ya ce ta bu?e idanu taga budurwarsa, tana bu?ewa sai taga kanta a cikin mirror hakan zai ?ayatar.
Na'am ya yi da wannan shawara da zuciyarsa ta basa, yana ?o?arin yi mata magana aka yi knocking na kofar.
Shiru ya ?an yi na na ?an sakani kafin ya ce wanene?.
Daga waje P.A ta e ita ce. Izinin shigowa ya bata, a ?ari Chuchu taso barin jikinsa ya yi saurin ri?eta yana kallon face ?inta.
A gaban table ?insa ta ?ariso, cikin girmamawa ta ce. "Sir daman wa?an nan bakin namu ne suke jiranka a meeting office". Tana magana tana aikin satar kallonsu, sun yi mugun dacewa sun kuma tafi da imaninta sosai.
Kai kawai ya jinjina mata alamar ya ji ba tare da ya yi magana ba. Juyawa ta yi ta tafi tana mai ?an waigowa ta saci kallonsu. Muguwa tunanin Rashidah ce kawai a ranta, tana ta faman dariyar mijinta ta ciki, su Rashidah masu kyan sace zuciyar oga.
"Jannat ban aran minti biyar ina zuwa ko?". Ya yi magana yana kallonta.
Okey ta amsa tare da barin jikin nasa.
Mi?ewa ya yi a hanzarce ya fice. Yana fita ta koma saman chair ?in ta zauna.
Shiru ta yi tana tunanin Yah Rizwan ?inta, a haka har ya dawo ya sameta, ya je ya sanya hannun.
Yana zuwa ta mi?e ta bashi waje, zama ya yi tare da mayar da ita saman laps ?in nasa.
"Yah Jawad wai ina budurwar taka ne?". Ta fa?a kamar zata yi kuka.
Tausayinta ne ya ji ta kamashi, wato har yanzu abin yana cinta a rai, hakan yasa ya ji gara ya gaya mata abin da yake ran nasa kawai, dan ya saukaka mata abin da take ji na zafin kishi.
Juyowa ya yi tare da matso da face ?insa daf da tata har suna iya jiyo sautin numfashin juna, wani irin ?urawa juna idanu suka yi, jiran amsarsa kawai take yi, shi kuwa ya zubawa kwayar idanunta ido yana kallon tsantsar soyayyarsa dake kwance a cikinsu.
Sa?o na musamman zuciyoyi suka shiga aikawa juna, a hankali ya ha?e face ?insu waje guda, wani irin duniya na daban ya tsinci kansa a ciki.
?asa ?asa cikin salo mai matu?ar jan hankali ya furta. "My Jannat".
Sar?ewa muryarta ya yi a in da ta kasa amsawa da na'am ?in, saboda yadda ya ha?e fuskokinsu ya jefata a cikin ru?ani da fargabar me zai biyo baya.
"My Jannat bani da kalaman da zan iya bayyana maki abin da nake ji a yanzu, baki bai isa ya fa?i abin da suke tare cunkushe a cikin zuciyata ba, ba abin da zan iya cewa face in ce maki..............".
Knocking na kofar da aka yi ne ya sanya ya dakata da maganar bai iya kai karshenta ba.
Cikin wani irin kasala ya ?an yi baya ka?an ya raba fuskokinsu ya koma ya jingina bayansa da jikin chair ?in.
Kasa jurewa ta yi da sauri ta kwnatar da kanta a saman kirjinsa tana sauke numfashi a hankali hankali, ?azun ta rasa ina hankalinta ya shiga da har ta iya tsayuwa tana kallon cikin idanunsa ya kuma ha?e fuskokinsu waje guda, har yana ?o?arin kamar zai yi kissing ?inta kuma duk tana kallon cikin kwayar idanunsa, abin ya bata mamaki, soyayya yasa tama mance a wace duniya take.
Da kyar ya iya motsa lips ?insa wajen furta. "Come in". Dan yasan P.A ce.
Turo kofar ta yi ta shigo, a karo na biyu ta same Chuchun kwance a saman kirjinsa, abin dai ya yi matu?ar ?ayatar da ita, sai ta ji ina ma ace ita ce, sai dai matsalar ita ?in hajiya one seater ce a ?iba, ai kunji ma Chuchun ta fa?a da bakinta ?azun, tana da ki?a sosai.
Idanunsa a lumshe ya ce. "Lafiya?". "Sir dama sir Rizwan ne yake neman iso".
Ai da jin sunan Rizwan bai san time ?in da ya waro idanunsa waje na. A ?ari ita kuma ta ?ago kanta daga saman kirjin nasa, kai tsaye face ?insa ta kai kallonta, while shi ma juyo da kallonsa a kanta ya yi.
P.A dai mamaki suka bata, daga jin sunan Rizwan duk sun ru?e kamar marasa gaskiya, shi Jawad tunani yake yi ya za'ayi ya bari yayan nasa ya kamashi da ita a nan? Ai sai ya ce dama ya saba. Ita kuma tunani take yi shikenan ya zo sai su yi hira.
"Zan iya tafiya sir?". P.A ta katse masu kallon juna da suke yi, dan ta lura kamar sun manta da ita.
Kai kawai ya gya?a mata, a hanzarce ya ce wa Chuchun ta shiga ?asar table ?insa ta ?uya, tun da in ta shiga babu mai iya ganinta sai shi da yake ta wajen, wa?an da zasu shigo daga baya ba zasu ganta ba.
A hanzarce ta sau?a daga jikin nasa ta shige ?asan table ?in, dan ta lura ba da wasa yake yi ba, so kada ta ja ransa ya ?aci a banza.
Tana shigewa shi kuma Rizwan ya shigo, ?ananan kaya ne a jikinsa, ya yi kyau fresh da shi.
Tun da ya ?aura idanu a kan kanin nasa ya fahimci akwai wani abin, dan har lokacin a ?an ru?e yake, Yah Rizwan ya ?ata mashi komai, ya so gaya mata abin da yake ransa, ya kuma yi kissing nata kamar yadda ya yi niya, amma idan ya kama shi yana aikata hakan ko ya kamashi da ita a tare a nan ai ya shiga talatin............
My people's shin me kuke tunanin zai faru a cikin wannan companyn yau?
________________________??????
GIDANSU KHADIJAH.????
Ya ilahi, my people's Khadijan ta koma tamkar ba ita ba, kullum ?oye kanta a cikin ?aki take yi ta murji kuka kamar me, tun Zainab na tambayarta me yake damunta har ta hakura ta daina tambaya, taki yarda ta sanar da kowa abin da yake faruwa, cikin nata kuwa ya kusa isa level ?in da ba'a isa a ?oye shi ba, dan ma cikin fari ne, bashi da girma sosai ita ma bata da babban ciki, kuma Allah ya rufa mata asiri bata laulayi sosai, sai uban fa?a da tsanar mutane ta iya, ko Zainab dan dole suke tare da ita, dan ba yadda zata yi ne, amma ta tsani ganinta a kusa da ita sosai, ga dukkan alamu duk yadda aka yi uban cikin nan mafa?aci ne sosai, dan kuwa abin da baku sani ba shi ne a ciki akwai ilimi biyu zuwa uku da ba kowa ne yake iya gane hakan ba sai wanda ya kasance mai ilimin addini sosai, domin kuwa fa?ar Allah ne wannan ba fa?ar bature ba, amma a hankali zan warware maku komai In Sha Allah.
A ?angaren malamamin makarantarsu kuwa, kullum sai ya zo, amma Khadijan ta ki yarda ko da sunan wasa su ha?u, kwata kwata ma ta dai'na fita, saboda matsa mata da samari suke yi, tamkar abin ba lafiya ba sai da abin nan ya faru da ita ne suka fara tururuwar zuwa neman aurenta.
Sannan makudan ku?a?en da ta dawo da su ko naira bata sake ta?awa ba, tun da ta cusasu a bayan gado ta fita harkarsu. Yau tun safe basu ci komai ba daga ita har Zee ?in, Amma bata fito da ku?in dan ta saya masu abinci ba, da alama ta mance da ku?in.
A yau ne kuma suka tashi da mummunar al'amari na rasuwar Hajiyar su baban Zee wato kakarsu kenan, Hajiya lokaci ya yi, sai dai mu ce Allah ya jikan musulmi.
Kakarsu ta wajen uwa wato Hajiyar su Sadiq kam ma basu san a wani hali take ciki ba, tun da Sadiq ya tsallake ya bar Kano ba su sake jin ?uriyarsa ba, Zee ta nemo waya a ma?ota wajen wani mai shago ta kirasa numbersa a kashe, kusan kullum sai ta kira shi domin ya zo ya kawo masu ?auki a kan wannan wahala da suke ciki, amma ina basu samunsa, sun kira number kakar tasu ma a kashe.
Yanzu haka wani irin cin kashi Hauwa take yi masu, Khadeejerh mai iyawa da ita ?in kunga tana fama da kanta, ita kuwa Maman Haidar tana can tana hidima ta yadda zata yi ta fitar da ?anta daga halin da yake ciki, bata da nutsuwa, hankalinta a tashe yake sosai, bata ma garin, tana can Abuja wajensa, zuwanta na biyar kenan yanzu ana hanata ganinsa, har yau bata samu damar sanyashi a idanunta ba, bata san a wani hali yake ciki ba, duk ta firgice, ta rame kamar ba ita ba.
Ta zama kamar mai cutar ?anjamau, rasuwar Hajiyar tasu ma ita bata da labari, tana can tana up and down, sai bin manya take yi duk dan ta samu mafita, ta samu ko da sau ?aya ne taga ?an nata, sai ta je wajen wannan ta sha bakar wahala wajen sati tana bi?ar ganinsa, idan ta samu da kyar ta gansa sai ya ce mata case ?in a sama da shi yake, ya fi karfinsa, dan haka ta kara gaba zuwa sama ko zata dace, haka dai take ta fama, ta sayar da gidan mijin nata, dan kuwa shi ka?ai ne kadarar da suka mallaka, shi kuma mijin kunga ga shi ne ga kalarsa, in dan ta shi ne Haidar ?in ya mutu a can ba ruwansa, ita ce dai ta tsaya tsayin daka wajen ganin ya fito. Ta juri rana, ruwa, iska da zafi dukka!!.
In takaice maku ku?in gidan da ta sayar wajen 10 million ?in ma ta kusa cinyesu a neman ganin manya, duk in da ta je sai ta bada ku?in goro kafin ma ta samu a ha?ata da P.An wanda ta je nema, shi ma P.A ya kwashi rabonsa, gata wawuya ba ilimi ba, sai ayi ta cutarta, wani ma karya yake yi mata ya ce zai ha?ata da wanda zai fitar mata da ?an nata amma sai ta biya, haka zai kar?e mata maku?an dubbanin ?aruruwa ya gudu ya barta, sai dai ta yi ta jan Allah ya isa.
Wani abin da wani ya yi mata sai da ya sanyani kwallah, dan kuwa sati tana bibiyarsa, ta je office ?insa ya fi kafa talatin, yana ciki amma sai P.A ya ce mata baya nan, haka mai gadi zai ce kada ta zauna a ciki dan tana wari, sai dai ta fito waje ta zauna, komai zafin rana haka take zama a tsakar ranar, uwa kenan, komai lalacewarta dai daban take da kowa.
Ko ruwan sama ake yi haka zata zauna, ta gama cin bakar wahala, ta basu ku?i kamar ba gobe, P.A ?in ma mugu ne sai ya yi ta kar?ar mata ku?i yana kuma ce mata ta dago gobe ogansa baya nan, abin dai ba da?i, koda baka kaunarta sai ka tausaya mata a wannan ga?ar.
Daga karshe randa Allah ya nufa ta samu damar ganin mutumin ya fito daga cikin mota zai shiga office, tana ganinsa ta ruga da gudu ta nufesa, securitys ?insa suna tare ta kada ta isa garesa ta bangajesu ta isa gabansa, har ?asa ta zube gwiwowinta tana kuka tana ce mashi dan girman Allah ya ceci yaronta.
Mutumin nan ba kunya bare tsoron Allah har a kai ga tausayi yasa ?afa ya ham?areta ya wuce gaba fuskar nan kamar na shanu, har da dakawa securitys ?in nasa tsawa a kan su fitar mashi da wannan almajira da talauci yasa ta sami ta?in hankali a nan hai, sai warin datti take ta cika masu waje, ya ce kada a sake barinta ta doso mashi office baya da bu?ata. Ya bi ta kan yatsun hannunta ya takesu ya wuce, yatsun nata sai da suka fashe suka fitar da jini, saboda takalmar kafafunsa masu ?arfin gaske ne.
Haka securitys ?in suka kamata suka jefa waje, sai kuka take yi......... Yanzu wa gari ya waya fisabilillah?. Da ace sun yi zaman mutunci da su Sadiq, da shi ka?ai bai isa ya tsaya mata ya yi iya bakin ?o?arinsa har a samu Haidar ?in idan yana da rabon fita ya fito ba?! Wlh da Sadiq yana nan ba sai ta zo nan tana shan wannan bakar wala?anci da kaskaci haka ba, da tana gida zai yi komai, amma ga shi nan tana ganin illar mugunta ai, su ba tsayayyen namiji suke da shi a cikin familyn ba, ga rashin ilimi da rashin wayo, kowa ya ce mata ku?i ta ?eba ta bayar, sai ma ta tambayesu nawa zata kawo, mugaye su suke yanke nawa zata kawo, ita kuwa ta cire ta mi?a, Allah sarki ita dai ?anta kawai take son ya fita, duk da haka ko ta bada a wala?antata, yanzu duk ta yi yaushi ta rasa ina zata sanya rayuwarta ta ji sanyi.
Duk wannan halin da take ciki kawarta hajiya Hauwa tana gida ta baje tare da ?aura ?amarar cin dukiya da gasken gaske, idan ta yi crossing leg ?in nan nata a saman sofa, ta tasa su kaji gassasu and yogurt a gaba tana cin duniyarta da tsinke babu wanda zai takura mata, ga shi Hajiyar tasu ma rai ya yi halinsa, gidan babu wani tsayayye, Hauwa kam duniya sabuwa abinta.
Zata yi saye sayen kayan da?inta, su Khadeejerh suna ji suna gani zata ci ko a gabansu ko ?an?ane bata yi masu.
Allah ya rufawa Khadeejerh ?in asiri ma cikin nata bashi da kwa?ayi kuma baya za?e, ai da ta wahala ?ar tahali?ar nan a hannun Hauwa.
Hajiyar tasu da ta rasu ma ba wanda ya sani a tsawon awanni, su Khadijah suna ?aki kamar kullum, ita kuma Hauwa sai abin da hali ya yi, ta fita ya kai sau uku tana zuwa unguwa ta je ta dawo, ta kuma yi girki amma duk da haka bata san cewa surukartata ta rasu ba tsabar bata da albarka.
Sai da Maman Hanif ta kawo masu ziyara gidan ne ta iya ganewa, ta zo ne dan ta ji ko ya labarin ?ar uwarta maman Haidar ake ciki, sai kawai ta tadda bakar labari na rasuwar Hajiyarsu. Ta yi matukar ki?ima tare girgiza, hankalinta idan ya yi dubu ya tashi!.
Duk da ba shiri su Khadija suke yi da kowa a gidan ba ha?i?a sun sha kuka na rasuwar Hajiyar. Hauwa kuwa wani irin da?i ta ji, fa?i take gara ya karun mata, jin da?i babu tsayawa, ita fa ga dukkan alamu bata tuna akwai ranar tafiya gidan gaskiya, anya jahilcin Hauwar nan ma ya barta ta yarda da lahira kuwa? Akwai matsala, wannan wutarta daban yake idan bata tuba ba, Allah baya yafe laifin wani, ko ta tuba a ina zata ga baban Zainab har ya yafe mata abin da ta yi mashi, dan shi ta cutar da shi cuta mafi muni a rayuwa, duk wannan abin shi ta yi wa, ta ja Hajiyarsu ma ta rasu saboda bakin cikin abin da ya faru ne yasa hawan jininta ya tashi har zuciyarta ya kumbura, yanzu rai ya yi halinsa, rayuka biyu Hauwa ta salwantar wa?an da basu ji ba ba kuma su gani ba. Innalilahi wa inna ilahir rajiun, ga maman Zee a can prison tana kar?ar azabar laifin da a kan Hauwa yakamata ya rataya.
Haka maman Hanif ta kira jama'a aka yi kira mai wankar gawa ta yi wa Hajiyar tasu, daga haka aka je aka rufeta a gidanta na gaskiya.
Bayan rasuwarta da kwana uku ne Maman Hanifa tana zaune a parlour, ta buga uban tagumi tana tunanin rayuwa. Fitowa daga cikin ?akinsu Khadija ta yi, ta zo wucewa zata shiga kitchen, idan baku manta ba dama kitchen ?in a parlour yake.
"Zo nan Khadija". Ta fa?a tana kallonta sosai, da alama tana zargin wani abin.
Ba musu ta juyo ta zo, dan koba komai maman Hanif tana nuna masu so, tana kuma tausaya masu.
A saman sofa ta zauna kusa da gwaggon nata. "Gwaggo gani nan". Da kyar muryarta ya iya fita har ta furta hakan, saboda kukan da ta rin?a sha, ga kukan cikinta da take ?uya a cikin toilet kullum dare ta ?irka, ga kukan rasuwar kakar tasu, ga shi bata san a wani hali kawunsu mai kaunarsu Sadiq yake ciki ba, hakan yasa yanzu sai dai ka kalli bakinta ka fahimci me take fa?a, muryanta kam sam baya fita.
"Khadija me nake ganin nan? Ya naga jikinki haka?". Maman Hanif ta fa?a da mamaki a saman face ?inta!.
Wani irin dukan uku uku kirjinta ya bada, nan take ta nemi nutsuwarta ta rasa, tsuru tsuru ta yi da idanu, duk da muryar tata baya fita zaka iya fahimtar muryar tata tana sarkewa, da kyar ta furta. "Me kika gani gwaggo? Me jikin nawa ya yi?".