Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 55
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 55: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 55. Sarai maman Hanif ?in ta lura da ru?ewar da ta yi daga tambaya, hakan yasa ta…
3,335 words
Sarai maman Hanif ?in ta lura da ru?ewar da ta yi daga tambaya, hakan yasa ta ji zuciyarta ya tsinke, addu'a ta yi a cikin ranta Allah yasa ba abin da take zargi bane ya faru da ?ar ?an uwan nata, da sun shiga uku sun lalace.............. Ai kuwa sai dai ki fara kukan kun shiga ukun, dan kuwa abin da kike zargi ne in ji ni princess Teema!.......????
Zuciyarta a tsinke ta ce. "Khadija naga jikinki ne wani ?anye ?anye ban gane ba, kamar mai ?aramin ciki kamar kuma period ne, menene yake faruwa?". Ta jefa mata tambayar kirjinta na dukan uku uku, fargabar abin da zata tono ne yake neman kasheta.
"Gwaggo nima ban sani ba". Ta fa?a tamkar zata rushe da kuka, wani irin ?ululun bakinciki mai matu?ar bala'in tsaci ne ya tokare mata ma?oshi, wani lokaci ji take yi kamar ta kashe kanta kawai ta huta, Zee ce take ce mata ko ta kashe kanta bata huta ba, hasali ma a lokacin da ta kashe kanta a lokacin ne babin wahalarta mai lasisi zai bu?e, dan kuwa duk wanda ya kashe kansa dai yasan makomarsa, to gara mata azabar duniya da ta lahira, tun da Allah ya ?addara basu da rabon duniya to su tsaya su nemi lahira kawai kada su yi biyu babu, wannan maganganu na Zainab suke sanyawa ta daure ta fasa kashe kan nata. Ban da haka wani lokaci har wu?a take ?auka ta ce zata kashe kanta!.
"Anya kuwa Khadija? Ko dai mu je asibiti ne? Dan gaskiya alamar mai ?aramin ciki ne a tattare da jikin nan naki".
Zaro idanun nata da rama suka kara masu girma ta yi, nan take wani irin fa?uwar gaba ya dira mata, da kyar ta ha?iyi yawun wahala a wahalce, sannan ta ce. "A'a gwaggo ni bana jin komai wlh".
Shiru ta ?an yi kamar mai tunanin wani abin, can kuma sai ta ce. "To shikenan ta shi ki je".
A hanzarce ta mi?e har kamar zata kifa ?asa, duk saboda saurin ta bar wajen kada ma gwaggon nata ta sake jefo mata wata tambayar da ?wa?walwarta ba zai iya jura ba.
Da kallo ta bita har ta shige cikin kitchen ?in, ajiyar zuciya ta sauke, a fili ta furta. "Ya tabbata baki da gaskiyar Khadija, wlh akwai abin da kike ?oyewa, ya Allah gamu gareka, ka dubemu da idanun rahma, ya Allah kada ka sa abin da nake zargine yake a gaske, ya Allah ka kare mun mutumcin dangina". Tana magana idanunta ne suka ciko tab da kwallah, zuciyarta yana yi mata wani irin suya, yau da bata yarda da Allah da Manzonsa ba da ta shiga uku ta lalace, irin wannan jarabawa sai mai karfin imani zai iya ?auka, duk rintsi duk wuya my people's kada ku kaucewa Allah, kowace irin hali zaku shiga kada ru?u da tashin hankali yasa ku manta Allah ne ka?ai zai iya fitar da ku.
Duk abin da ya faru a kan idanun Zee dake bakin kofa tana ?o?arin fitowa ya faru, zata fito ne ta taya Khadijah ?in aiki ne dama, jin suna magana da maman Hanif ?in ne yasa ta tsaya tana sauraro, wani irin bugawa da zuciyarta ya yi na jin abin da gwaggon nasu take zargin ?ar uwarta da shi.
Da karfi ta dafe saitin zuciyarta tare da furta. "Ciki? Kuma Khadija gwaggo kike zargi? Innalilahi wa inna ilahir rajiun, na shiga uku ni Zain........." Bata kai karshen maganar ba ta yanke jiki ta fa?i ?asa, idan baku manta ba dama tana da ciwo a zuciya baiwar Allah, sai hakan ya fama mata ciwon ya ja mata wata bala'in. Kuma ha?i?a ta yarda da zancen gwaggon nasu ne ya ja mata wannan matsalar, dan dama ta jima tana zargin Khadija na ?oye mata wani babban al'amari dangane da ita, sai dai bata kai abin har ga ciki ba gaskiya, amma da gwaggon nasu ta yi magana sai ?wa?walwarta ta tariyo mata komai da ya rin?a faruwa a tsakaninta da Khadija.
Na farko tun da Khadija ta dawo bata ga ta yi fashin sallah ba wato period, sannan sau da dama tana kamata a cikin toilet tana kuka, idan ta tamnayeta sai ta ce ta tuna baba da mama ne, kuma tasan karya take yi mata, dan bata saba yinsa ba, idan ta yi dole a ganeta, amma duk da haka bata nuna cewa ta gane karya take yi mata, sai ta yarda kawai a wuce wajen, to yau ga gaskiya ya bayyana innalilahi wa inna ilahir rajiun wannan wace iriyar bahaguwar ?addara ce?.........................
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 29/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
E30
A guje maman Hanif ta mi?e ta yi kanta, sunanta take ambata babu kakkautawa cikin tsananin tashin hankali take!.
Jin tana ihun sunan ?ar uwar tata yasa Khadija ?in fitowa daga cikin kitchen ?in da gudu a kuma ru?e, haka zalika ita ma Hauwa a guje ta fito daga nata ?akin.
Kansu Khadija ta yi tana ambatar sunan Zee ?in, ita kuwa Hauwa ganin cewa Zee ce ta suma ba wata masifar da ta zata bace sai ta ja birki ta tsaya a tsakiyar parlourn tana binsu da kallon wala?anci.
A ru?e Khadijar ta bar kan nasu ta juya da nufin ta je ta ?auko ruwa su zubawa Zee ?in, tana juyowa suka yi karo da Hauwa dake tsaye a tsakiyar parlourn tana yi masu kallon rashin mutuncin.
Bangajeta Hauwar ta yi har sai da ta yi baya ta fa?i ?asa, hakan yaja hankalin maman Hanif ta juyo da kallonta a kansu.
Yun?urawa ta yi ta mi?e tsaye, a tsiyace ha?e da wala?ance ta ce. "Ke amma dabbace ko? ?wa?walwar ki ta jakuna ce da alama".
Da yake jahilar ce bata ma san zafin abin da Khadija ?in ta fa?a ba, sai bata wani ji zafin maganar ba, amma saboda a cewarta Khadijar ta rainata da zata yi mata magana ba respect haka sai ta cire hannu zata dalla mata mari.
Kaucewa ta yi marin bai sameta ba, cikin fushi ta ?ago kai, dama ga cikin nata ya mayar da ita mafa?aciya. Kanta ta yi da nufin ta daddallah mata maruka, dan kuwa duk yadda kake kai zuciya nesa sai Hauwa ta kureka, duk yadda take dannewa ta kawar da kai yau sai da ta kure ta, sam bata so wani abin ya sake ha?asu ba, amma Hauwa muguwar ?ar shisshigi ce.
A hanzarce maman Hanif ta ri?eta tana fa?in. "A'a Khadija ki rabu da ita, jeki ki kawo ruwa mu zubawa ?ar uwarki kin ji?".
Wani irin hucin da ta fara fitarwa ne zai sa ku gane lallai yau ranta a matu?ar ?ace yake, ta zo har wuya.
Zata wuce Hauwar ta danko rigarta ta wajen shoulder ?inta tana fa?in. "Dawo nan dan ubanki! Da kenan fa?a da ni zaki yi ko? To bismillah, ba kin san abin da uwarki ta sani ba? Ai dole ki ce zaki yi fa?a dani ina matsayin uwarku a cikin gidan nan". Ita fa Hauwa a dole dole so take yi su yi fa?a ta samu wani abin ta buga mata yadda zata raunatata.
Aikuwa a wannan karon Khadija tana juyowa ta ?auketa da wani irin gigitattacen mari mai rai da lafiya. Ihu ta saki kamar wata mai motsi a kai, cukumo wuyar rigar Khadija ?in ta yi da nufin ta lakka?a mata dukan tsiya.
Kunsan dai tana fama da kanta, ba wani karfin kirki bane gareta, ba ci a ?oshi ga ciki, hakan yasa Hauwar ta jefar da ita ?asa, tana ?o?arin hayewa kan ruwan cikinta ta yi mata dukan kawo wu?a.
Aikuwa maman Hanif ta ce ba'a haifi uwarta ba, dankota ta yi, hanka?ata ta yi sai da ta tafi ta kifa a kusa da sofa two seater. Bin bayanta ta yi ta hau jibgarta kamar ba gobe, dama ta jima da takaicin Hauwar nan a ranta, kullum idan ta ganta sai ta ji tamkar ta kasheta kowa ta huta, to yau dai Allah ya yi ta samu dama jibgar banza.
Dukar takaici ta rin?a kaimaya ta ko'ina tana sauke numfashi mai kama da huci, ihu mai sauti Hauwar ta fara fitarwa dan jama'a su kawo mata ?auki, kunsan akwai ?ai?aikun ?an zaman makoki a waje da suka yi saura.
Jin ta dameta da ihu zata iya tara masu jama'a yasa ta dunkule hannunta ta dakarkare ta danna mata naushi a bakin nata.
Habawa kan kace me sai jini ya ?arke, duka ta ko'ina take sauke mata tamkar wadda aka yi wa wahayin duka.
Lalla?awa Khadija ?in ta yi ta mi?e tsaye, baiwar Allah har wani irin jiri jiri take gani.
Kai tsaye kitchen ta wuce tana ?an dafa bango, ruwa ta ?ebo a bowl ta zo ta fara yayyafawa ?ar uwarta, bata sake bi ta kansu maman Hanif ?in ba.
A ru?e Zee ta farka, kuka ta shiga yi hawaye bibbiyu ha?e da sambatu wadda sai ka yi zaton yaren China take yi, ko ita kanta bata san me take fa?a ba, surutu kawai take bar?ate da yaren da bana mutane ba, kamar wadda ?wa?walwarta ya samu matsala.
Rungumota Khadija ?in ta yi a kirjinta, wani irin tausayinta ne ya kamata, ji take tamkar ta fasa ihu mai sautin dode jin kowa ko zata huta, wannan shi ne rana zafi inuwa ?ona.
"Zainab dan Allah ki daina wa?an nan surutan haka ya isa, dan Allah kada ki bari wani abin ya sama mun ke, kada ki manta ke ka?ai ke gareni, ko kina son wani abin ya sameki zuciyata ta buga na mutu ne?". Tana magana tana matsar kwallar da suka cika mata idanun, abin gwanin ban tausayi.
Ina ai Zainab kamar ta samu matsala fa a ?wa?walwarta, dan kuwa duk bata jin me ?ar uwar tata take fa?a ba, cigaba da sambatunta kawai take yi. Abin idan ka gani sai ka matsa masu kwallah.
Khadija ta rasa ina zata sanya ranta ta ji sanyi, rarrashinta ta shiga yi tana ruwan hawaye tamkar ruwa ya fasa hanya ya ?allo.
Ita kuwa maman Hanif da zuciya ya ?ebeta sai da ta ga Hauwa ta daina wani motsin kirki ga jini da yake bulbula daga bakinta, bakin ya sunduma sum, sannan ne ta kyaleta tana sauke numfashi da sauri sauri, haki ta shiga yi yadda kuka san wadda ta tiki uban gudu ta ?oshi.
Kan su Zainab ?in ta koma, kama hannun Zee ?in ta wajen shoulder ?inta ta yi, ?agota ta yi suka koma saman sofa.
"Khadija jeki ki kawo mata magungunanta da sauri". Ta yi maganar har lokacin tana haki sosai, dan fa ba karya ta jibgi Hauwa iya jibga, wannan shi ake cewa dukan huce takaici.
Da gudu ta watsa cikin ?akin, jikinta sai kerma yake yi ta kwaso magungunar ta fito.
"Zainab ?in ta ci abinci ne?". Cewar maman Hanif.
Girgiza kai ta yi, tana kuka sosai ta ce. "A'a bata ci komai ba".
Shiru maman Hanif ?in ta yi tana tunanin ya zasu yi kenan? Dan babu komai da ya danganci abinci a cikin wannan gida, ga shi ita bata da ko sisin kwabo.
"Gwaggo dan Allah ki bata maganin mana". Cewar Khadija da voice baya fita.
"Khadija ba ta yadda za'ayi ta sha magani ba tare da ta sanya komai a cikinta ba, maganin ba zai yi mata wani amfani ba, dan haka dole mu nemo mata wani abu mai ?umi wanda zai ?umama mata ciki ta ci".
Zaro idanu ta yi, jikinta sai kerma yake yi, ta gaza tsayuwa waje guda, kamar zata fa?i tana ta tangal tangal. "Na shiga uku na ni Khadija, Zee dan Allah kada ki mutu, kowa sai mutuwa yake yi yana barina, baba ya tafi ya barmu da kewa, yanzu kuma Hajiya ta tafi, ke kam Zee ki tsaya da ni, ko kuma ni gara na tafi na barki". Tana magana tana mai cigaba da tangal tangal.
Ba kara ?aga hankalin maman Hanif suka yi ba, ga abin tausayi marayun Allah. Ta ru?e sosai a in da take ta fa?in. "Khadija ya isa kukan nan ki yi shiru, Zainab ki yi wa Allah ki daina sambatun nan, kinga kin jefa ?ar uwarki ita ma ta fara sambatu ko? Kin ?aga mana hankali sosai, dan Allah ki yi shiru". Ita kanta da take maganar kwallah ne a cike tab a idanunta, dan kuwa dole su bawa mutum tausayi.
Kamar daga sama suka tsinkayo muryarta tana fa?in. "Gwaggo wlh na yarda ciki Khadija take da shi, tana yawan yin amai a toilet, ga yawan barci da fa?a, idan na yi mata abu ka?an zata hau zagina abin da a baya ko da sunan wasa bata ta?a yi mun ba, sannan ga kukan da take ?uya tana yi, na sha kamata tana yi a cikin toilet, innalillahi wlh tun da ta dawo gidan nan dama na ?asa gane mata". Cewar Zee mai sambatu.
Jin zantukan Zee ?in yasa maman Hanif da tashin hankali ya kusa yin ajalinta ta mi?e tsaye, a razane take kallon Khadija dake tsaye tana layi.
?urawa cikinta idanu ta yi, duk da hijabi ne a jikinta amma tabbas cikin ya bayyana, ga alamar ya fara girma. Ai maman Hanif bata san lokacin da ta ?aura hannu bisa kanta ta kurma ihu mai sautin gaske wanda ita kanta bata san ya aka yi ta yi shi ba.
Ihun ya yi sanadiyar bu?ewar idanun Zee ?in. Wani irin bugu da karfi karfi zuciyarta ya fara yi, ita ma da take gwaggonsu kenan, yau da ace babansu yana raye ina da tabbacin wannan mummunar labarin ce zata zama ajalinsa, dan kuwa yana da kishin familyns matu?a.
Zubewa ?asa ta yi a saman gwiwowinta, dan kafafunta ya kaza iya ?aukar gangar jikinta, ita ma maman Hanif ?in zubewa ta yi a saman nata gwiwowin tare da rushewa da kuka mai sauti, tamkar wata ?aramar yarinya ta shiga rera wi wi wi gwanin ban tausayi.
An rasa waye zai rarrashi ?an uwa, Hauwa dake kwance magashian tana numfashi sama sama ne kunnuwanta suka tsinkayo mata wanna bakin labarin. Ai bata san lokacin da ta waro idanunta waje ba, fa?i take a cikin zuciyarta ta samu damar korarsu daga cikin gidan, a cewarta yanzu maman Hanif ?in ce kawai ta rage ta yi maganinta shikenan komai ma baban Zee ya zama nata, yanzu dai shirin korarsu daga gidan zata yi, dan dama ta jima tana tunanin hanyar da zata bi ta aiwatar da hakan, ta ?asa iya kashesu.
Abin da baku sani ba, sau biyu tana shirya masu gadar zare Allah yana tsaratar da su, taso salwantar da rayukansu, ko kuma ta turasu waje mai nisan da ba zasu iya dawowa ba, amma duk ha?arta bai cinma ruwa ba, to yanzu dai da alama ta sami abin da take so, a tunaninta zata iya cinma burinta..... To fah!! Akwai matsala, amma dai mu je zuwa ni ina ma zarginta a kan mutuwar Hajiya, dan wannan Hauwar a kan duniya babu abin da ba zata iya ba.
"Khadijah wanenen ya yi maki wannan abin? Waye ya cuceki ya kashe mu innalilahi wa Inna ilahir rajiun........". Cewar maman Hanif. Yadda take magana wlh sai ta ?agawa bawa hankali, saboda wani irin kuka take yi mai tsuma zuciya, tamkar ranta zai fita take ji, hmmmm da mamaesu na nan ta sami wannan labari da sai yaya kenan? Ina ga ita ma shi ne zai yi sanadiyar rayuwarta. Zata gwammaci gara mata zaman prison ?in.
Kuka ita ma Khadijah ?in take yi tamkar ranta zai fita. Da kyar ta iya fa?in. "Gwaggo nima ban san shi ba, ban sansu ba, kawai ?aukata suka zo suka yi a kofar gidan nan, daga nan suka wuce dani ?asar Brazil, a can na yi wata ?aya da sati biyu cikin wani irin gida da ban isa in fita ko nan da parlonsu ba, kuma wlh gwaggo daga ni sai shi ne ka?ai a cikin gidan, ko parlonsa bana iya kai kaina saboda yanayin tsarin gidan, kofofin gidan dukka sai da password suke bu?uwa, kuma shi ka?ai yasan password ?insu, bana fita ?akin da ya ajiyeni, haka na shafe wannan lokacin, daga nan kuma sai ya ?aukeni muka je wani gari ne ko wace ?asa ce ban sani ba, sai da dai muka hau jirgi........."
Dakatawa da yin maganar ta yi tana tari mai sauti, irin tarin nan mai kwarzane kirji, mai zafin gaske.
Sosai ta yi tarin, tun tana tsugune kan gwiwonta tana yi har ta zauna dirshan mai gaba?aya. Maman hanif bata da za?in da ya wuce ta matso ta ri?eta dan ta tallafa mata, ita ma Zee da sauri ta sau?o ?asa daga saman sofar, rungumarta ta zo ta yi.
"Zee kawo mata ruwa". Cewar maman Hanif ?in.
A guje ta mi?e, sai dai kuma ta ?asa yin gudun, saboda ba lafiya ne da ita ba, dan dole ta hakura ta ja kafafunta a hankali ta nufi kitchen, ga?o?inta duk ciwo suke yi mata.
Ruwa ta ?ebo a cup ta kawo. Kar?a maman Hanif ta yi ta sanya mata a saitin bakinta, a hanzarce ta kar?a ta fara sha ba kakkautawa, Allah sarki har ma?oshinta ya bushe ne saboda tashin hankali.
Tas ta shanye ruwan kafin ta cire kai, kifa kan nata a saman shoulder ?in gwaggon nata ta yi tana mai cigaba da kuka ?asa ?asa.
"Ban san ?asar da ya sake tafiya dani a karo na biyu ba, shi ma Brazil ?in abin da yasa na san a ?asar nake shi ne, a lokacin da jirginmu da ya ?aukomu daga Nigeria ya sau?a a airport ?insu, a nan ne na ga kasar da muke, to ?ayan ?asar da muka je ?in kuma lokacin da muka sau?a ina barci, sai dai bu?e idanuna na yi na ganni a wani ?aki na daban, babu kowa a cikin ?akin, sai dai hayaniya da na ji a wani ?angare na cikin gidan, hakan yasa na mi?e da nufin in je in ga su wanene? Ko da na fito na rasa hanya, haka na yi ta bin daga in da sautin hayaniyar yake tashi har Allah ya kaini main parlon ?asa na gidan..........". ?an dakatawa ta yi tana mai jan numfashi, kuka yana neman cin karfinta.
"Wanene shi Khadijah?". Cewar gwaggon nasu, a ?age da son jin amsar ta yi tambayar. "Kin san shi ne? Aina kuka ha?u? Meyasa zai ?aukeki? A ina yake yanzu?". A cikin tsananin fargabar amsar da zata ji ta jefa mata tambayoyin nan.
"Gwaggo ban sani ba, wlh ban ta?a ganinsa ba sai ranar da wa?an da suka ?aukeni suka kaini gidansa, bani da wata ala?a ta kusa ko ta nesa da shi, yanzu haka ban san a wace ?asa yake ba, ban san ?an wace ?asa bace, ni sau ?aya ma na ta?a jin sautin muryarsa, ranar da zamu rabu, a ranar ne ya ta?a yi mun magana, ba komai kuma ya ce mun ba face na kula da kaina sosai sai ha?uwa ta gaba idan Allah ya ?addara, shikenan abin da ya ce mun, daga haka ban sake sanin komai ba, tsawon sati ina sume, bayan na farfa?o da kwana uku aka dawo dani Nigeria, kuma ko da na farfa?o ban gansa ba, boys ?insa ne suka dawo dani kamar yadda suka zo suka ?aukeni".
"Har kofar gidan nan suka dawo dani, sannan suka bani ku?i suka ce oga ya ce na rin?a cin abubuwa masu da?i, kuma na tabbata ya bani wa?an nan ku?a?en ne dan a tunaninsa cikin jikina ya fita kamar yadda suka yi yun?urin zubar da shi tun farko, so shi ne yasa ya bani ku?in dan na yi jinyar kai'na......" Ta kai karshen maganar tana sake rushewa da kuka mai sautin gaske.