Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 56

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 56

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 56: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 56. Wani sabon kuka maman Hanif ta ?arke da shi, da yake Zee tasan wacece ?ar…

3,321 words

Wani sabon kuka maman Hanif ta ?arke da shi, da yake Zee tasan wacece ?ar uwar tata sosai, sai ta iya gano cewa tabbas karya take yi, duk yadda aka yi ta san uban cikin nan, wlh ta san komai dangane da shi, watakila tasan ba kaunar cikin ake yi bane yasa ta ?oye dan ma kada maman Hanif ta ce zaa je wajensa har yasan da cikin ya yi yunkuri yi mashi wani abin, amma ba ta yadda za'ayi ace mutum ya ?auketa tsawon wata biyu suna tare, kuma ya yi mata ciki sannan ta ce bata san shi ba, karya take yi, dole ta san shi! To a ina ta san shi? Ita dai Zee bata yarda da wannan magana ba, dan idan baku manta ba Khadijah ?in ta yi mata karyar cewa bata san in da aka kaita ba har da ce mata tun da aka kaita a sume take tsawon wata biyu nan, har da ?arawa wai ?asar Russia aka kaita, kunga kuwa ai dole ta karyatata a yanzu ma.

Sai dai abin da Zee ?in bata sani ba a nan shi ne, wlh maganganun Khadeejerh a wannan karon kam zallar gaskiya ce, duk abin da ta fa?a hakance ta faru, dama da farko taso ?oye abin ne shiyasa ta yi wa Zee karya, to yanzu da komai ya tuno kansa me amfanin ?oye gaskiya? Ai kunga babu, to wlh gaskiya ta fa?a, shi dai uban wannan ciki bata san shi ba, hasalima ba a nan Nigeria yake ba, ?an Nigeria ne ko ?an waje ne duk bata sani ba.

Ko a ina ya santa? Wannan ne abin tambaya, yanzu kuma a ina zata gansa har ta kai mashi ?ansa ko yarsa idan Allah yasa ta haife? Sannan ?an wani ?asa ne uban? Ina yake a halin yanzu? Shin yasan tana ?auke da cikinsa? Wacece wadda Khadijah ?in take yawan tunano muryarta tana ?o?arin zubar mata da cikin? Ya tabbata kenan kamar yadda Zee take hasashe ba'a kaunar wannan cikin kenan? Tun da ga shi har alluran zubar da shi aka yi mata! Lallai akwai cakwakiya sosai, ha?i?a akwai abin da Khadijah ?in ta rage bata sanar da su ba, dan kuwa bayan rayuwar da ta yi daga ita san uban cikin nata tabbas ta yi wani rayuwa da wata na ?an lokacin, dan in baku manta ba bata tuna uban cikin nata kamar yadda take tuna sautin muryar wannan mata da zata zubar mata da cikin, ta ?oye wannan labarin baya gaya masu ba. To wacece wannan mata?.

Ni kam na ce amma lallai wannan uban ciki na Khadijah anyi ?an duniya na bugawa a jarida, tsabar isa da iskanci kawai kasa a ?auko maka yarinyar mutane, ka ?irka mata ciki ba gaira ba dalili, sannan ka yi yun?urin zubar da ciki, ka kuma sakota a jirgi a dawo da ita Nigeria kamar yadda ka ?auketa, wai ma a ina ya santa? Da alama guy ?in ?an balai ne, fata nama dai ni kam Allah yasa musulmi ne ba kafuri ba, amma dai wannan ya kai duk in da ?an iska dan duniya ya kai wlh, anya yana da iyaye ma kuwa? Daga gani da wuya idan yana da mafa?a gaskiya!.

?an rungumuta maman Hanif ta yi tare da shiga rarrashinta sosai.

After some minutes, da kyar suka samu ta yi shiru, bayan ta yi shirun komai ya lafa sun kudundune waje guda ita da Zee.

Kallonta da kyau maman Hanif ?in ta yi, cikin sanyin murya ta ce. "Khadijah to me zai hana mu je asibiti a zubar da cikin nan, kinga sai ki fito da miji kawai ki yi aure ki hutawa ranki".

Zaro idanu waje sosai ta yi, tamkar zata sa kuka ta ce. "A'a gwaggo, ina son cikina, idan na zubar da shi me ribana? Mutumin nan ya zalunceni, ya cuceni, ya lalata mun rayuwata, sannan da ya fahimci ina da ciki shi ne yasa a zubar mun, yanzu a tunaninsa an zubar da cikin, da alama babban mutum ne wanda baya son sunansa ta lalace na ya haifi ?an shege, shi ne yasa ko ta halin ?a?a a zubar mun da cikin, ba abin da basu yi ba sai dai jinina ya zuba, amma cikin yana nan, tun da kika ga haka cikin nan yaki fita gwaggo to tabbas akwai wata aya da Ubangijinmu yake son nuna mana, kuma ni kai'na ina son haifar cikin, ko dan na ?auki fansar abin da suka yi mun".

"Kullum mama tana yi mana nasiha, hakan yasa ta ja na yi wa ?an shege muguwar tsana, sai ga shi yau ni ce da kai'na zan haifi ?an shegen kuma a cikin gidanmu innalilahi wa inna ilahir rajiun....." Wani sabon kuka ta fashe da shi.

Shiru maman Hanif ta yi tana jinjina wannan al'amari a ranta, tabbas Khadija tana da gaskiya, tun da ba abin da ba'ayi wa wannan ciki ba yaki fita to gara kawai su barshi kada su ja rayuwar yarinya ya salwanta a banza, sannan kuma kamar yadda ta fa?a ne, tun da uban cikin baya son ?an har ya yi yun?urin zubar da ciki to tabbas yana da kyau ta haifi ?an, idan ma uban nasa babban mutum ?in ne ta yi amfani da wannan dama shi ma ta rusa mashi farincikinsa kamar yadda ya lalata mata tata, dan haka ya cancanci a bar wannan ciki ta haifesa, kuma cikin ma ya wuci munzalin zubarwa a yanzu, dan ya kai ?a......... Tir?ashi ana yinta a RAWANIN ZALINCIN!!.??

Wunin yau cikin tsananin rashin da?i suka yi shi, duk suna cikin damuwa, walwala ya kau daga tattare da su, Hauwa kuwa ta ja jiki ta kai kanta hospital dan ta jibgu ba karya.

Sai da aka yi kwana bakwai da rasuwar Hajiya sannan maman Hanif ta koma gidanta, maman Haidar dai shiru bata ba labarinta bata san mamansu ta rasu ba.

Allah sarki, time da maman Hanif take tare da su a gidan Khadija taga kula sosai irin wadda kowace mai ciki zata bu?ata, tana komawa gidanta kuma suka fara fuskantar matsala da Hauwa, da maman Hanif tana nan sam bata shiga harkarsu, dan kuwa tana tsoron ta sake cin jibga, da farko ?an'sanda taso kirawa maman Hanif ?in, sai kuma ta fasa, dan bata son case ?in ya zama babba, saboda tana son maman Hanif ta koma ita kuma ta fara gallazawa su Khadija har sai sun gudu da kafafunsu sun bar gidan, shi ne shirinta, sannan tana son yi wa maman Hanif ?in wani mugun abin dan ya zama ita ce ka?ai zata cinye dukiyar bb Zee, shiyasa bata kira ?an'sanda ba, dan idan ta yi mata abin ya faru ?an'sanda zasu iya shiga case ?in, idan suka shiga kuma za'a iya bukatar wa?an da suka ta?a sa in sa da maman Hanif ?in dan bincike, kunga a nan asirinta zai iya tonuwa, shi ne yasa ta hakura bata kirasu ba

Ai kuwa ha?arta yana son cinma ruwa a wannan karonma, dan kuwa da alama burinta zai iya cika, saboda kuntata masu da take yi tana shiga harkarsu ta yi ta lalata masu abubuwa idan suka ajiye, idan suna girki ta zo ta zuba omo ko ta juye kedar gishiri a ciki, da kyar da su?in goshi suke samun abin da zasu sanya a bakin salati, sai suna girkawa ta lalata masu.

Wani lokaci haka suke kwana su wuni da yunwa, hakan yasa Khadija ta fara bawa Zee shawara a kan su je Kaduna su nemo su Sadiq, daga nan su nemi aikin yi wanda zasu rin?a yi dan su rufawa kansu asiri, yunwar nan ta yi yawa.

Da Zee ta ce. "To Aunty khadina baga ku?in da kika dawo da shi ?in nan ba, ki fitar mu fara sana'a da shi".

Girgiza kai ta yi tare da cewa. "Zee ki bar batun wannan ku?i, ina tanadinsu ne domin in ?auki fansa a kan wannan mutumi, jira nake yi na haifi cikin tukun nan, dan mu gwabza shari'a, shiyasa bana son ta?a ku?in". Tana magana tana shafa cikin nata da a yanzu ya kai almost 6 to 7 month. Ashe dai tasan da zaman ku?in ba mantawa ta yi da su ba, ashe tanadinsu take yi dan gwabza fa?a ta kwatarwa da kanta ?anci, akwai cakwakiya kenan, muje zuwa, da alama Khadija zata ?auki dala ba gammo, idan babban mutum ne kuna tunanin zata tona masa asiri kamar yadda take tunanin nan kuma ta zauna lafiya? Ya zuba idanu yana kallonta?. Hmmmm akwai matsala gagarumin ma kuwa!!.

"Haka ne kuma, nima zanso ki ?auki fansa a kan wannan bakin shai?ani azzalumin". Cewar Zee.

"Yauwa ashe kin gane, yanzu kinga mu shirya mu sa ranar tafiya Kadunar nan, dan na gaji da zaluncin Hauwa, banda RAWANIN ZALINCI da mugunta babu wani abin da yake kanta, gara mu tafi wajen kawu sai ya fi mana, kinga ba iyawa da ita zamu yi ba, ni bani da karfi a halin yanzu, ke kuma baki da lafiya, ba zamu iya da ita ba, gara kawai mu bar mata gidan.

Na'am da zancen nata Zee ta yi. "To amma Aunty khadina ku?in motar zuwa fa? Sannan a ina zamu ga su kawun?". Tana magana tana ?an zaro idanu alamar ta shiga ru?ani.

"Ku?in mota kam zan ?auka mana a cikin ku?in da na zo da shi, su kuma su kawu In Sha Allah zamu gansu". Ta kai karshen maganar tare da karkatawa ta kwanta a saman gadon ta tada kai da laps ?in Zee.

Duk wa?an nan maganganun da suke yi a kan kunnuwar Hauwa suke yinsa, ta yi masu la?e tana jinsu, burinta kawai ta ji sun fa?i a in da suka ajiye ku?in, dan ta sha alwashin sace ku?in nan ko ana ha maza ha mata, Allah Allah take yi wani tsautsayi ya ja su fita daga cikin ?akin ta shigo ta kwashi ku?in abinta. Bakar mugu ba, to ta Allah ba taki ba, In Sha Allah ba zaki gansu ba bare har kwashe.

Shafa kan Khadijah ?in ta farayi suka cigaba da yin hira a in da Zee take ta yi mata magiya a kan idan mace ta haifa dan Allah ta yi mata takwara. Alkawari ta yi mata a kan za'ayi haka, koda ta mutu idan yarinyar ta zo da rai to ta rin?a kiranta da Zainab.

Girgiza kai ta yi tare da cewa ba zata mutu ba, In Sha Allah ita zata shayar da ?ar tata. Amin kawai ta amsa da shi, amma ita a jikinta bata jin zata cigaba da rayuwa mai tsawo...........

__________________________??

DUBAI??

Leesharh, kwance take a saman bed ?insu tana fuskantar saman celling, ta yi shiru da alama duniyar tunani ta lulu?a, wayarta ce ta fara ringing, ba wayar da masu nikaf suka bata ba, a'a, wayar da Bilal ya saya mata ita da Sharifat iri ?aya, jiya ya sayo masu wayar ya kawo masu, akwai sim card da komai a ciki.

Ganin sunan my brat ne yasa ta yi saurin picking. Sharifat ce.

"Hllo Bloody". Daga ?ayan ?angaren Sharifat ?in ta fa?a. "Naam Brat". Ta masa mata tana mi?ewa zaune, ta kara kyau sosai, har ?an cika ta yi, ta yi kumari saboda kwana biyun nan ta rabu da su annoba wato masu nikaf, tun da ta jefa wayarta a cikin echolac bata sake bi ta kansa ba.

"Bloody ki zo ?akin Abbie yanzu". Cewar Sharifat ?in.

Da okey ta amsa tare da mi?ewa zaune tana katse kira , wandon jeans fari ne a jikinta, daga ta sama kuma riga ce black color mai karamar hannu iya daidai shoulder ?inta, kanta babu ?an'kwali, ta saki gashinta da yake shan gyara sosai a hannun Sharifat, sai kyalli yake yi.

Kasa ta sako, mayafinta mai ?an girma ta ?auko, yafawa ta yi tare da ?aukar wayar tata, ta sanya parlourn sillpers masu kyau da laushi a kafafunta, sannan ta fito.

Kai tsaye part ?insa ta nufa, tana kan tafiya ne massage ya shigo cikin wayar tata, ?ar kara wayar ta yi, haka yasa ta kunna wutar screen ?in dan ta duba sa?on wanene?.

Tana yi tana cigaba da tafiya, bata ankaraba dab zata shiga parlon Abbie shi kuma yana fitowa, karo suka ci a in da dukkansu wayoyinsu suka fa?i ?asa, shi ma yana tafiya ne yana latsa waya kamar dai ita, shiyasa suka ci karo ba tare da sun farga ba.

Wani irin tsoro ne ya kamata, tsoron ?agowa ta kalli wanenen ma ta ji, ?asa motsawa daga in da take ta yi. Hakan ba ?aramin haushi ya bashi ba, ta buge mashi waya kuma ta ?asa tsugunnawa ta ?auko ta bashi hakuri? Lallai yarintar nan da me take ta?ama? Ya jefawa kansa tambaya.

Ai ko da wuta take tafiya a bakinta sai ta san yau ta ha?u da Ramish ya fa?a a ransa. Wani irin marin da ya dalla mata a kumatu ne yasa ta dai'na gane komai, ji ta yi kamar ba a duniya take ba, duk da take chocolate color sai da yatsun hannunsa suka fito a saman face ?inta, alamar ta maru kenan, har wani jiri ne ta ji yana ?o?arin ?ibarta, hankalinta sai da ya gushe na wucin gadin.

Bilal da yake bayansa da suka fito a tare ne ya ce. "Ramish yau kai ne da sanya hannunka a jikin mace? Abin da mamaki, what kind of sadness did you feel da har ka mareta?". Yana magana yana kallon ta ta yi mutuwar tsaye, ko motsawa ta kasa yi.

Dr Raj dake bayan Bilal ?in ne ya amsa da. "Dole ya mareta mana, kana gani ta buge mashi waya amma taki tsugunnawa ta ?auko ta bashi hakuri!"............ Aka ce so so ne amma sonkai ya fi, karo fa suka yi, ba ita ta buge shi ba, duk suna kan latsa wayar ne suka bugi juna, amma sun ?aura mata laifi sun bi bayan ?an uwansu, sun ha?i?ance itace ta buge mashi waya.

A tare suka fito daga ?akin Abbien nasu, gaishesa suka je suka yi.

Tsugunawa Bilal ya yi ya ?auko wayoyin dukka biyu, ya dam?a mata nata a hannunta tare da kama hannun nata ya turata cikin parlourn, sannan ya mi?awa Ramish ?in ma nasa yana fa?in. "Sorry bro".

?an binsa da kallon mamaki Dr Raj ya yi. "Amma Yah Bilal ni kam me ha?inka da wannan aljanar yarinyar ne?". Kasa hakura ya yi sai da ya tambaya, dan abin yana bashi mamaki yadda Bilal ?in yake yi mata mugu mugun saukin kai, ko Sharifat baya yi mata irin hakan.

Wucewa Ramish ya yi ba tare da ya kar?i wayar tasa ba, bayansa suka bi Bilal yana fa?in. "Dr tausayi take bani kawai". Ya fa?a yana cusa wayar Ramish ?in a cikin aljihunsa, dukkansu shigar Arabs jallabiyas ne a jikkunansu.

Ta jima a tsaye a bakin kofar parlourn ta gaza motsawa daga in da take, ra?a?in marin nasa ne yake ratsa tsoka da jijiya har izuwa ?argon kashin jikinta, bata ta?a jin mari mai zafin wannan ba, kai ko marin gandurobobin gidan yarin AAJ bai kai ko rabin nasa a zafi ba, ko marin su Omaid da suke twins bai kai nashi zafi ba, har ta ji duniya ya canza mata.

Sautin muryar Ummie da ya daki dodan kunnuwanta ne yasa ta farga ta dawo cikin hankalinta, firgita ta yi tare da zaro idanun, ba komai Ummien ta ce mata ba face me ya kawota part ?in mijinta?.

Murya na rawa ta ce. "Sharifat ce ta kirani wai na zo". Da hannu ta nuna mata hanyar barin parlourn ba tare da ta yi magana ba. Da sauri ta juya har tana ha?awa da ?an gudu gudu. Tamkar zata kifa ?asa, a haka ta wuce ta koma ?akinsu.

A saman gado ta kwanta tare da kunna wutar screen ?in wayar tata. Ajiyar zuciya ta sauke ta sanya hannunta guda ?aya a saman kumatunta in da ya mareta, ?asa ?asa ta ce.

"Mugu azzalumi Allah zai saka mun, ashe haka kake bakin mugu, ai dole ne ma jama'a su nemi kashe ka, daga gani ka zalunci mutane dayawa ne, sai Allah ya saka masu, idan ka yi wasa ma makiya ne zasu kasheka a kan titi, daga ?an yi karo da kai kawai ka sauke mun wannan hannun naka kamar na samudawa, Allah ya isa na". Tana surutan tana cire password na wayar dan ta duba massages ?in da ya shigo cikin wayar tata ?azun kafin su yi karo da shi.

A wani irin zabure ta mi?e zaune, wani irin razana ce ta bayyana a saman face ?inta lokacin da ta ?aura idanunta a kan sa?o. A ru?e kuma a fili ta furta. "Who give them my number? A iya sanina only Sharifat ce kawai take da numberta, ko shi Yah Bilal da ya saya mana wayoyin bana tunanin yana da number.

Mamaki ne ya kusa kasheta, har ta kasa karanta sakon, wani irin fargabar abin da zata ji dangane da sakon ne ya kamata, yau kuma dame suka zo? Infact a ina suka samu contact ?inta?...... Idan kun fahimci wani abu my people's, masu nikaf fa basu da wani za?i ne da ya wuce dole su sake nemanta, dan itace kawai ta samu damar da babu wata da ta?a samun makamancinsa a gidan, babu yar aikin da aka ta?a yantawa sai ita, sun san yanzu ta zama yar gida zata ?ara kutsawa cikin family sosai, ta samu wajen zama, yanzu ne ma aikinsu zai tafi yadda suke so cikin farinciki, dole su nemota su lalla?ata, shiyasa suka sake yi mata text a kan zasu sanyata aiki na karshe wanda ba mai wahala ba ne, amsa kiran waya ce kawai zata yi idan lokaci ya yi, daga wannan aikin amsa call ?in da zata yi shikenan zasu bata babanta su kuma mayar da ita kasarsu.

Jin hakan yasa ta mi?e zaune, wani irin gumi ne ya fara tsastsafo mata daga gefe fuskarta. Tunani ta fara yi a kan in dai amsa call ne kawai ai gara ta yi masu su bata babanta.

To amsa kiran me? Magana zata yi da wani? Leesharh ta kasa gane cewa yanzu fa time ?inta ne, ta kasa fahimtar cewa yanzu fa sai dai ita ta juya masu nikaf ba dai su su juya taba, yanzu Allah ya ara mata dama, tana da damar da zata iya ce masu idan basu yi mata kaza ba ita kuma ba zata yi aikin ba, ba su da za?i kuma ba yadda zasu yi da ya wuce dole su yi abin da take so, dan kuwa ita ka?aice zata iya yi masu wannan aiki, dole su lalla?ata idan suna so, amma duk bata gane hakan ba, bata gane cewa yanzu ita fa abin su lalla?ane idan suna son aiki, ba wai su rin?a yi mata barazana ba, da yake tun farko da tsoronsu a ranta, sun rigada sun sanya mata tsoro azzalumai sai ta ?asa gane komai.

Shiru ta lulu?a duniyar tunani, bata san da shigowar Sharifat ?akin ba sai tsinkayo muryarta ta yi tana fa?in. "Bloody me ya sameki a kumatu? Waye ya mareki? Kuma ya baki zo kiran da Abbie ya yi maki ba?".

?ar firgita ta yi alamar mutum yana cikin tunani, a hanzarce ta shiga sharce gumin dake saman face ?inta.

Da mamaki ?auke a fuskarta Sharifat ta ce. "Bloody lafiya kike kuwa? Gumi fa naga kike yi? Ko dai gudun Acn ne ya yi maki ka?an ko baki da lafiya ne?".

Duk tana ru?e, hannunta har yana kerma wajen fita daga kan massages ?in ta kashe wutar screen ?in, murmushin dole ta ?a?alo tare da fa?in. "Brat babu komai fa, kawai ina tunanin mamata ce, Abbie kuma kin san har yau bana iya gane wasu hanyoyi na cikin gidan nan, na fita zanje wajen nasa sai na rasa hanya".

Ajiyar zuciya ta sauke tare da zama a kusa da ita. "Allah sarki my bloody, da na yi zaton wani abin ne ya sameki, kada ki damu ki rin?a yi wa mama addu'a Allah yasa tana cikin rahmarsa".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull