Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 57
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 57: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 57. Da amin ta amsa tare da ?an runtse idanunta, tunanin Jasrah ce ya fa?o mata a…
3,357 words
Da amin ta amsa tare da ?an runtse idanunta, tunanin Jasrah ce ya fa?o mata a cikin ?wa?walwarta, Allah sarki baiwar Allah, yadda Sharifat take bata shawara a kullum, yadda take nuna mata girman Allah a kullum sak yadda Jasrah take yi mata, suna yi mata kamanceceniya, ga shi bama su san juna ba bare ta ce suna da ala?a ta jini, haka kawai Allah mai halitta sai komai nasu yana zuwa kusan iri ?aya, wani lokaci idan Sharifat ta yi magana sai ya yi mata tamkar Jasrah ce a wajen take magana, tana yawan yi mata addu'a a kullum, dan tasan yanzu ?an watanni ne da basu wuci biyar zuwa shidda ba suka rage a yanke mata hukuncinta, a ratayeta a kashe, innalilahi wa inna ilahir rajiun.
A wani ?angaren na zuciyarta kuma wani tunani ne ya fa?o mata, shiru ta yi tana tuna lokacin da mahaifiyarta take magagin mutuwa ga wu?a a saman tsakiyar ruwan cikinta, ya fasa fatarta ya shiga har can ciki, fa?i take. "Leesharh ki yafe mun, ki yafe mun duk abin da na yi maki, nasan na cutar dake na ?auki alhakinki, duk abin da kika yi a duniyar nan ba laifin kowa bane laifina ne, na yi danasani a lokacin da na rigada na san lokacin ta kure mun, amma dai ina sa ran zaki yafe mun, idan kin ha?u da Abbanki ki ce ya yafe mun, ha?i?a na cutar da ku, sai magana ta karshe kuma shi ne........". Wani irin zabura ta yi tare da furta.
"Hakan ba zai yiwu ba mama, ni ba zan ta?a yarda da wa?an nan kalaman naki ba".
Tsoratar da Sharifat ta yi tare da mi?ewa zata gudu ne yasa ta farga ashe a duniyar gaske ta yi maganar ba'a duniyar mafarki ba, hakan yasa ita ma ta mi?e tsaye tana fa?in innalilahi wa inna ilahir rajiun.
Ta lura idan bata yi hankali ba watarana tunanin mahaifiyarta zai iya sanya a ce mata tuburar mahaukaciya.
"Bloody zaki sa na gudu, tunanin me kike yi haka har zancen zucin naki ya fito da karfi?".
Komawa ta yi ta zauna tana wani irin sauke numfashi kamar wadda ta ci uban gudu ta ?oshi, dafe saitin zuciyarta ta yi tana huro iska daga bakinta, bata iya amsawa Sharifat amsarta ba saboda ru?ewa.
"Bloody yakamata ki dai'na yawan tunani, kinga a yanzu tunani ya fara sanyaki kin fara surutai da karfi a bayyane, na ce maki addu'a zaki rin?a bin mama da shi, ni tashi mu je mu yi breakfast ma, amma kafin nan ki rakani na kaiwa su Yah Ramish abincinsu, mu dawo mu yi namu breakfast ?in, Abbie kuma yana kiranki a kan result ?inki ne, dan ya ce yana son week ?in nan ki fara zuwa school".
Shiru ta ?an yi kafin ta amsa da. "Ni dai Brat ba zan je wajensu Yah Ramish ba, sannan ni breakfast ?in ma mu yi namu a nan ba sai mun je main parlourn ba, sai ki rakani wajen Abbie ?in daga haka na amsa kiran nasa".
"Oh oh oh yanzu na gane dalilinki na kin zuwa amsa kiran Abbie kika wani fake da cewa baki gane hanyar ba, dama naji ne kawai amma ban yarda ba, wai bloody sau nawa zan gaya maki ki dai'na ?oye mun abin da Ummiena take yi maki? Dama na yi tunanin yadda ta baro room ?in Abbie ?in nan da wuya idan baku ci karo ba, ban yi tunanin zata fita a lokacin bane shiyasa nakiraki nace ki zo, nasan ita ta hanaki shiga ko?". Ta kai karshen maganar tare da komawa ta zauna.
Girgiza kai ta fara yi. "A'a ni Ummie bata yi mun komai ba, kuma bata hanani shiga ba, ban ma ha?u da ita ba, kawai dai hanyar ce ta ?ace mun". Ta yi maganar kai a ?asa.
"Bloody kenan, watanninki almost 6 a gidan nan amma ki ce wai hanyar zuwa ?akin Abbie daga nan ne ba zaki gane ba? Anyway yanzu dai zo mu je mu kaiwa su Yah Ramish abinci, kin ma san me nake tunani ne?".
Girgiza kai ta yi alamar a'a, a cikin zuciyarta kuwa ta furta Alhamdulillah da Allah yasa zata canza masu topic na hira.
"Addu'a nake yi Allah yasa Yah Bilal ya kamu da sonki, kinga ina son Yah Ramish sai kawai a ha?a aurenmu, matsalar ma ke ?in nan wawiya wawiya ce, sai ki rin?a cewa kina jin tsoronsu, ba fa abin da zasu yi maki, dan kuwa su ?in basu dukan mata, Yah Ramish ya ce me abin duka a jikin mace? Wai idan ya ce zai daki mace mutuwa zata yi, shiyasa baya farawa, nima idan na yi masu laifi harara ta kawai suke yi a wuce wajen, dan haka ki dai'na tsoronsu kema kin ji?".
Kai kawai ta gya?a mata alamar to, amma batun ta dai'na jin tsoronsu kam babu shi bai taso ba, dan fa dole a ji tsoronsu, zaratan samari irin haka ai dole hantar ciki ta ka?a idan ta gansu.
"Yauwa my gurl, ki rin?a tsara kwalliya idan zamu je wajensu, Ummie na ta ce in dai ina son shawo kan Yah Ramish har ya fara ?aga idanu yana kallona to sai da hakan, dan haka kema ki ?aura ?amayar sace zuciyar Yah Bilal saboda mu auri yaya da ka?in zan yi farinciki da hakan".
Okey nan dai da shi kawai ta bita, dan kuwa dai ba ?aukar shawarar nan tata zata yi ba, ita ka?ai tasan abin da ya kawota gidan, ba auren ?an gida ta zo yi ba, dan haka babu ruwanta da su, yanzu ma jiran ranar da masu nikaf zasu ?auketa kawai take yi, dan tasan dole zasu ?auketa kamar yadda suka kawota, ta san suna kewaye da ita, duk wani motsinta suna samun information a kai, ga shi yanzu ma daga saya mata waya jiya har sun sani sun kuma samu number.
"Yanzu gaskiya ki yi wanka ki canza kayan nan mu je kai masu breakfast, sai mu zauna mu ?an yi hira a wajensu, dan ma dai Yah Rizwan baya nan, shi ne abokin hirana, su sauran basa magana, sai dai ki zauna shiru kina kallon film". Ta kai karshen maganar tana mi?ewa tsaye.
Okey nan dai shi ta sake amsa mata da shi tare da mi?ewa ita ma, har ga Allah bata so binta part ?insu ba, dan ita bata son hanya ma yana ha?ata dasu ba batun zuwa in da suke ba ma tukun nan.
Sharifat fa wayayyiyar yarinya ce sosai, idanunta a bu?e suke, gata da iya soyayya dan mayyar kalle kalle film ?in turawa ce, kada ku manta na gaya maku tana da yawan karance karance da bincike bincike, ta iya bada shawarar yadda za'a sace zuciyar namiji, amma ita kuma ta kasa sace zuciyar Yah Ramish ?in nata, ko kallon ma bata ishe shi ba, dan shi ?in wani irin bahagon mutum ne ba mai iya mashi sai Bilal and mamarsa, ko King Zuhair wani lokaci hakuri yake yi kawai ya kyalesa, ita maman nasa kawai ya san girma da darajar mahaifiya ce yasa baya musa maganarta komai ?ankanta, hakan yasa ake ganin kamar ita ce kawai take iya mashi, ba wani nan, kaunarta yasa hakan.
Shi kuma Bilal shakuwar da take a tsakaninsu da tsananin kaunar juna yasa idan ya ce yana son Ramish ?in ya yi abu to yana yi dan kauna, suna iya sadaukarwa juna da abubuwa sosai, hakan yasa ake ganin kamar Bilal ?in yana iya mashi, kaunace kawai shi ma.
Toilet Sharifat ta nufa, wanka ta yi, yau da kanta ta ciro masu kaya masu shegen kyau, Italians gown ta fitar masu, kayan daidai yake da shape ?in jikinsu, yana ?aya daga cikin kayan da suka sayo lokacin da Bilal ya kai su shopping.
Ita ma Leesharh wanka ta yi suka tsara shirunsu, yau Sharifat ?in ce ma ta yi wa Leesharh kwalliya, wai duk dan ta sace zuciyar Bilal, ni kam naga ikon Allah, ita ta kasa iya sacen zuciyar nata masoyin amma tana tsarawa wata yadda ita kuma zata saci zuciyar wani, abin dariya wai yaro ya tsinci hakwara.
Ba karya sun yi kyau kam matu?a, kayan ya bi shape ?in Leesharh sosai, dama na gaya maku tana da shape mai tafiya da imanin duk wani lafiyayyen namiji, mata ma idan suka ganta sai sun sake juyowa sun kalla bare maza.
Ha?i?a Sharifat ?in ta ?an ji wani abin a ranta na ganin duk kayan da zasu sanya sai ya fi zama a jikin Leesharh tamkar dan ita aka yi, kuma komai na kayan iri ?aya, amma sai ya fi bin shape ?in Leesharh ya fita zat, ta kasa yarda cewa Leesharh ta fita good bye and welcome, da alama Sharifat tana da kishi sosai gaskiya.
Amma bata bari hakan ya yi tasiri, tana kore tunani, yanzu ma kore tunanin ta yi tare da ri?o hannunta suka nufi waje, kamar wasu taurari haka suke haskawa........... Eyeee my people's yara sun shirya sace zu?atan zaratan samarin Abbie, gaskiya ne!! To dai mu je zuwa muga su zasu yi nasara ko dai samarin Abbien ne zasu yi nasara.( Ni dai na ce Leesharh Sharifat zata kai ki ta baroki ar To????)
Kayan abincin nasu Sharifat ta ?auko, a parlon suka isko Ummie and Abbie suna yin breakfast, cikin girmamawa ta ?agawa Abbie gaisuwa, da yake shi ba mutun ne mai fara'a ba, kamar dai Mommar Zunaira yake shi ma, bashi da fara'a sai wa?an da yake kauna sosai yake sakarwa fuska, hakan yasa face ba yabo ba fallasa ya amsa mata gaisuwar tata tare da zuba masu ruwan albarka.
Amin suka amsa da shi, sannan suka juya, Leesharh ta ?agawa Ummie gaisuwa, ita kuma Sharifat ta ?an yi gaba da kayan abinci.
Rai a jagule ta amsa a takaice da lafiya, da alama amsar ma bata kai zuciya ba, saboda Abbie yana wajen ne ma yasa ta amsa.
Bayan Sharifat ta bi suka nufi part na samarin Abbien. Yau a parlon ta samesu dukkansu, sun sauya shigar da yake jikinsu daga jallabiya izuwa ?ananan kaya. Bilal and Ramish suna sanye da hoodies dan ana ?an sanyi sanyi, shi kuwa Dr Raj t-shirt and Jeans ne a jikinsa.
Ramish yana ri?e da cup mai ?auke da cappuccino, yana tsaye a tsakiyar parlourn, ga zura hannu ?aya a aljihun wandon jikinsa.
Bilal yana tsaye wajen center table, ya ?aura kafarsa ?aya a saman center table ?in tare da ha?e hannayensa dukka biyu waje guda ya zubawa Ramish ?in idanu, shi kuwa Dr yana zaune saman two seater yana binsu da kallo, da alama magana mai mahimmanci suke tattaunawa.
Sallamarta yasa suka dakata da maganar da suke yi, dama Dr Raj ne yake magana a lokacin. Da kallo Dr ya bi Sharifat ?in, shi kuwa Ramish da kallonsa yake a kan Bilal bai yi mashi kamar ma mutane ne suka shigo cikin parlourn ba, ko gezau bai motsa ba.
Bilal ma dai satar kallonsu ya yi dan gulma.
"Hakan ba mai yiwuwa bane, is better for you to look for another way". Ramish ne ya yi maganar a sanyayye, har lokacin kallonsa naa kan Bilal.
Mamaki ne ya kama Leesharh na jin maganarsa, tamkar ba muryan maza ba, ba kuma muryan mata ke garesa ba, da yawan maza suna da ?aton murya, muryarsu a fashe yake, amma shi muryarsa tana da sanyi sosai ga da?i sauraro sai kaifi irin na King Zuhair.
Ajiyar zuciya Sharifat ta sauke domin wani sanyi ta ji a ranta na sauraron voice ?insa, baya da yawan magana, ko kana tare da shi zaka jima baka ji maganarsa ba, muryarsa mai tsada ce.
A saman table ta ?aura masu abincin nasu tare da nufo saman sofa kusa da Dr Raj ta zauna tama murmushi. Turus Leesharh ta tsaya a wajen table ?in, already Sharifat ta wuce gaba ta barta, ita kuma tana tsoron ?arisawa wajen nasu ita ka?ai, sai kawai ta tsaya turus a wajen.
Bilal da tun da suka shigo yake satar kallonta ta wutsiyar idanunsa ne ya juyo da kallonsa mai gaba?aya a kanta, ta tsaya kamar wata sakarya tana raba idanu.
Kamar zai yi mata magana sai kuma ya fasa, saboda Dr Raj ya saka mashi idanu a kanta, sai ya basar kamar bai ga tana tsaye ba.
Ganin tana tsaye yasa Sharifat ta ce. "Leesharh ki zo ki........". ?asa ?arisa maganar ta yi saboda idanun masoyin nata da ya sauka a kanta, maganar da ta yi ne yasa ya kawar da kallonsa daga kan Bilal izuwa kanta, kaifafan idanun nasa suka sa ta kasa idasa maganar tata, Sharifat tana da abin dariya sosai, yayanta ne, gidansu ?aya, tana bala'in sonsa amma tana bala'in tsoronsa, ko cikin idanunsa bata iya gani, ko maga take yi idan ya kalleta sai ta ha?iye maganar, ni kam zan ga ta yadda za'ayi wannan soyayya, na tausaya mata, dan kuwa shi dai Ramish bai san tana yi ba, infact yama tsani mahaifiyarta, ita ?in ma albarkacin Abbiensu take ci ya barta tana zuwa part ?insu, ku kunsan yadda ya tsani Ummien nan da wuya idan zai yarda da wani zancen sonta, sai dai idan dole Abbien zai yi mashi, kuma wlh shi ba kunya ce da shi ba, dan ya zauna ya gayawa Abbie baya sonta ?aramin aikinsa ne, mutum ne mai magana kai tsaye, ba ruwansa da abi da maganar zata haifar, shi dai zai fa?i san ransa ato, ga shi idanunsa babu kunya ko ?igo, a bushe suke.
Jin takasa ?arisa maganar yasa tun basu ganta ba suka gane Ramish ya kalleta kenan, dan kuwa ba ita ka?ai ba ko jami'ansa idan suna magana da zarar ya sauke idanunsa a cikin nasu sai sun sha jinin jikinsu su ?an daga ta da yin maganar, sai daga baya su cigaba, yana da idanu masu kaifi ne sosai.
Ta wutsiyar idanunsa Ramish ya kalli Leesharh ?in jin Sharifat ta ce ta zo ta zauna, shi ne bari ya ga wacece ma?. Ga mamakinsa sai ya ga yarinyar da ya mara ?azun ne, tunani ya fara yi a kan wacecec ita ?in? Dan lokacin da Abbie ya ?antata ai kunga yana sume.
Wata zuciya ce ta ce mashi bai wuce kwashen ?an uwan Ummie bane, tuna hanan yasa ya nufi saman table ?in dan ya yi breakfast abinsa, a cewarsa dik abin da ya shafi Ummie bashi da lokacinsa.
A hanzarce Sharifat ta mi?e, fuska a ?auke da ?ayatattcen murmushi, tana murna ta ce. "Yah Ramish bari na yi serving ?inka". Allah sarki soyayya kenan, har wani nisha?i take ji a duk lokacin da take yi mashi hidima, da?i sosai take ji, shi kuwa tamkar gunki bai san tana yi ba.
Yana isowa kusa da ita ta datse idanu gam, tun da ta ji marinsa ta ?ara jin tsoronsa sosai. Kamar bai ganta a wajen ba ya wuce ya zauna a saman chair, cike da murna Sharifat ta fara serving ?insa.
Zama Bilal ma ya zo ya yi a chair dake kusa da shi yana fa?in. "Lil zuba mun nawa abincin sai ki ?auki sister nan taki ku tafi".
?an turo baki ta yi tana satar kallon Ramish. "Ni Yah Bilal hira nazo taya ku".
Sarai ya kalleta tana satar kallon mashi ?an uwa, a ransa ya ce zaki yi ki gaji ki bari.
Ita dai Leesharh tana tsaye shiru, Dr Raj kuwa shiru ya yi yana nazarin maganganun da suka tattauna, da alama ba zai yi breakfast yanzu ba.
Zuba masu abincin ta yi, cike da class suka fara ci, ita kuma sai ta zauna a saman chair ?aya tana ta aikin satar kallon shi.
Shi kuwa Bilal duk ransa bai so tsayuwar Leesharh a tsaye ba, duk ya takura, yana cin abinci ne amma hankalinsa kacokam yana a kanta, ya rasa sukuninsa, amma kuma baya son kulata bare ya ce ta samu waje ta zauna, Dr Raj ya saka mashi idanu, haka dai ya daure ya danne yana ganinta a tsaye ba yadda za'ayi.
________________________????
JIMETA YOLA NIGERIA.
Gaba?aya matasan nan kansa suka nufa, suna zuwa da nufin su hau jibga mashi sandunar nasu yasa hannu ya kwace sandar mutun ?aya tare da rage tsawonsa sandar da wani ya zo buga mashi ta wuce fiw bata same shi ba.
Cikin ?acin rai ya fara jibgarsu da sandar hannun nasa da ya kwata yana kaucewa nasu dukan da suke kawo mashi, su da suke kiwo ma sun san ta yadda zasu daki mutum bare shi da yake renon Commander Zafar? Ai wlh lilis ya dakasu kamar ai aikosa, yana dukansu yana tunanin me ya yi masu suka zo jibgarsa haka?.
Tsurewa Nenne ta yi har ta ji cikinta ya mur?a, nan take ta ji tana son shiga ban?aki, wani tunani ne ya fa?o mata a ranta na cewa anya kuwa ba garkuwa ma ta ha?a Mahnoor da shi ba kuwa? A tunaninsu bashi da karfin iya nemo masu abinci da zasu ci ma bare har ya bata kulawa, sai ga shi ya jibgi matasa wajen guda 20 shi ka?ai, kuma ya iya kauce dukan da suka rin?a kawo mashi bai ta?asa ba, gaskiya da sake, in dai haka ne wannan zai iya zamawa Mahnoor babban garkuwa ma kuwa, ba zai bari ta wala?anta ba.
Nan take Nennen ta ji ina dole a raba wannan aure idan ma an ?aura, dan su ba garkuwa suke neman mata ba, wanda zai wala?antata suke neman mata...... Lallai akwai cakwakiya babba ma kuwa, tab?ijam!!.
Mahreen dake tsaye a bakin kofa ita da Mahnoor suna kallonsa ne ta daka wani irin uban tsalle tana fa?in. "Hammana jarumin namiji ne! Adda Mahnoor kina ganin yadda ya yi masu bahagon makahon duka! Wayyo da?i kasheni, Hamma dan Allah ka koya mun irin wannan fa?ar ka ji? Ina son in ga nafi kowa karfi a garin nan, dan na rin?a dukan kowa a garin nan". Tana kai karshen maganar ta watsa a guje ta nufi she babu ko tsoro a tatare da ita.
Tana zuwa ta daka tsalle.
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 30/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
E31
Kash! Kullum sai kun mun magana Pretty and Kramer, har da masu ce mun ko na manta da su ne, ta ya za'ayi na manta da su? Bayan ni na zauna na ?ir?irosu! Suna nan labari ne kawai bai juyo ta kansu ba, kunga lanarin part part ne da dama, so ko wanne kuma ina tafiyar da shi ne bisa ga yadda na tsara kayana tun farko! Komai zai zo maku daki daki, me kuke ci na baka is falling down? Calm down my people's duk wanda story ya juyo ta kansa zaku ji labarinsa dallah dallah, dan haka let's go kawai!!.
Tana zuwa ta daka tsalle ta haye jikinsa tana murna. Jefar da sandar hannun nasa ya yi tare da sanye hannu ?aya ya tallafeta da kyau dan kada ta fa?i, ya gyarata izuwa saman kirjinsa fuskar nan kamar wadda aka cewa Mommarsa ta rasu.
Karo na farko a rayuwarsa yau ya ?ago idanu ya kalli Nenne dake tsaye a bakin kofar nata room ?in. Ya kalleta ido cikin ido
Ai a ?ari da sittin ta shige cikin ?aki tana fa?in. " Hasbunallahu wani'imal wakil, innalilahi yau na yi gamo".
Dariya sosai Mahreen ta ?alle da shi, mayar da kallonsa a kan Mahnoor dake tsaye ya yi, ?asa da kai ta yi ta fara ?an kame kame kamar maras gaskiya.
Muryar Mahreen ?in ne ya kara?e kunnuwansu a in da take fa?in. "Hamma Nenne fa tsoronka take ji, ka jita har da cewa hasbunallah, ni kam ban san meyasa suke tsoronka ba, ni kuma kyau kake mun wlh".
Tun da ta fara maganar ya dawo da kallonsa a kanta, while ita ma Mahnoor ?in sai ta dawo da kallonta a kansu.