Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 58
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 58: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 58. Matasan da ya jibgan ne suka fara motsawa, dama already akwai masu motsawa a…
3,299 words
Matasan da ya jibgan ne suka fara motsawa, dama already akwai masu motsawa a cikinsu, duk sun watsa cikin gidan a garin fa?arsu, sun tumurmushewa bappa harawarsa dukka, gidan dai ya zama kamar bola.
Sallamar Ar?o tare da bappa ne yasa Nenne sake fitowa daga ?akin nata, dan ta ji muryar mahaifin nata.
Mamaki ne ya kamata na ganinsu a tare, Ar?o bai ta?a zuwa gidan nasu ba sai yau. Kawar da kallonsa daga kansu Jaish ya yi, dan baya son ha?a idanu da bappa, kada ku manta kunyarsa yake ji dama.
A hanzarce Mahnoor ta shiga ?akin bappan ta ?auko masu tabarmar sakar mafici, a tsakar gidan ta zo ta tattare abubuwan da suke wajen ta shinfi?a masu.
Zama suka yi idanun bappa a kan Jaish, shi kuma ya yi ?asa da kai, ga Mahreen data ?ale jikinsa ta sa?alo wuyarsa da hannunta ?aya tana shafa mashi arabs hairnsa ta bayan wuya, tana ta zuba mashi surutu, yana gane wasu, wasu kuma sai dai ya ji kawai.
Nasan zaku so jin me ya kawo bappa a tare da Ar?o bayan kuma Ar?on ya ce aje a ?aure mashi shi, to ku saurara.
Kamar yadda ya bu?ata haka aka je aka ?aure mashi bappan, yasa su gwaggo suka kawo mashi garwashin wuta mai ci dan ya yi mashi hayakin kaikayi koma kan mashekiya, dan a cewarsu wani ne nan ya yi wa bappan asiri har ya samu matsala a ?wa?walwarsa, dan sun san yadda suke basa bawa bare auren ?a?ansu, haka kawai Bappa ba zai bada Mahnoor ga Jaish ba duk yadda yake son shi kuwa, shiyasa basu yarda ba dan sun san halinsu su da kansu!.
Ai kuwa hantar cikin gwaggo ne ya ka?a jin cewa Ar?o zai yi mashi hayakin ?ai?ayi, nan take ta sha jinin jikinta, dan tasan idan fa aka yi kashi hayakin nan shikenan maganin da suka yi mashi zai karye, a tsure ta fara ?o?arin dakatar da Ar?on cikin ?issa da kisisina.
Sai dai ina bata yi nasara ba, tana ji tana gani ya banka wannan garin ?ai?ayi a cikin wutar, kan ?ace me hayaki ya bule cikin gidan nasa, dama a cikin gida wajen bishiyar mangoron dake tsakiyar gidan aka ?aure shi, aikuwa Ar?o kam ya banka maganin abinsa.
Nan take bappan ya sume, wani irin zaro idanu sosai Ar?on ya yi a lokacin da ya ga bappan ya sume, hakan na nufin da akwai asiri a jikin nasa kamar yadda suka yi hasashe kenan?.
Gwaggo kuwa tana ganin haka cikinta ya mur?a ta ?ara tsurewa, me zata yi banda ?aukar buta ta nufi ban?aki, zawo ta fara yi cikin ya ?uri ruwa, Allah Allah take yi kada asirinta ya tonu, addu'a take yi Allah yasa kada aljanin da suka turo masa ?in ya fito ya yi magana ya ce su suka sanya shi ya gusarwa da bappan hankali.
Tun da ya shiga ban?aki ta kasa fitowa, sai zata fito cikin nata ya sake mur?awa ta koma, ba komai kuma ya razanata har haka ba face sanin halin mijin nasu, idan baku manta ba a baya na gaya maku mafa?aci ne, yana da tsauri sosai, so tsoron halinsa da sanin abinda zai iya aikatawa yasa hakan.
Sai dai fa Allah ya taimaketa da ?ai?ayi Ar?o ya yi amfani da garin makarin asiri, da da ayoyin Allah ya yi amfani to da babu abin da zai hana aljanun magana, amma wannan hanya da ya bi asirin komawa kan wanda ya yi kawai zai yi, hakan kuwa aka yi, kan gwaggon abin ya koma, dan ita ta ha?a komai ba Nenne ba, Nenne tana gida sai dai aka kawo mata maganin ta zuba mashi a abinci!!.
Bayan ya tabbatar asirin ya koma kan wanda ya ha?asa sai ya bu?aci da a kwance mashi shi a kwarya, matasan da suka ?auresa ?in ne suka kwance sa, ya bu?aci tabarma daga wajen Inna.
Da sauri ta kawo masu ta shinfi?a. A kai suka kwnatar da shi, ruwa ya bu?ata, nan ma Inna ce ta kawo mashi. Kar?a ya yi, sai a lokacin ne ya tofa ayoyin Allah, suratul iklas, suratul nasi and falak sai ayatul kursiyu and amanarrasu. Ya tofa a cikin ruwan sannan ya ?abo ka?an a hannunsa ya shafa mashi a face ?insa.
A lokacin already abin ya koma kan gwaggon. Sanadiyar wa?an nan ayoyin yasa bappan farkawa a nutse cikin kwanciyar hankali kuma cikin hayyacinsa.
Abin da ya basu mamaki ya kuma kara tabbatar masu da cewa asiri aka yi mashi shi ne, da bappan ya farfa?o sai ya kama tambayar me ya kawo shi gidan Ar?o kuma?.
Bayani Ar?on ya yi mashi dallah dallah a kuma nutse, sai da ya tabbatar ya fahimta sannan ya kyalesa. Ru?u iya ru?u Bappan ya shiga.
To kun ji abin da ya faru, Ar?o ya sanar da shi dik abin da yake faru, daga haka suka nufo gida, dan bappan ya ce yana son ganin Jaish and Mahnoor ?in...... To fa, ko ya makomar wannan aure.
Da farko fa musawa bappan ya yi a kan shi wlh ba shi ne ya ce a ?aura auren ba, dan shi ai already ya bawa Faisal ita ta yaya kuma zai sake cewa a aura mata wani? Sai da sirikin nasa ya yi masa bayani da kyau ne ya ?an yarda da zancen.
Mi?ewa suka yi suka nufo gida.
Story
Kusa da bappan Nenne ta ?ariso ta zauna, cikin harshen larabci ya yi wa Jaish kira a kan ya zo su yi magana.
Sauke Mahreen daga jikin nasa ya yi, cikin nutsuwa ya nufesu, sai dai bai kai ga ?arisawa ba sai ga kanin Inna da wasu zugan matasa sun banko cikin gidan yadda kuka san wa?an da aka jefosu daga sama.
Sai wani irin huci kanin Innan yake yi, shi ala dole ba za'a bawa jikarsa bare ya aura ba.
Mi?ewa tsaye bappa da Ar?o suka yi a tare cikin ru?u, ita kam Nenne yau tana ganin bala'i, ta haddasa abin da tun ba'aje ko'ina ba tana tabka danasani mai girma kuma maras amfani.
A guje ta watsa sai cikin ?akinta, ta fasa jin gulmar da ta fito da ita, dama ba ta zauna zata ji me su bappan zasu tattauna ba?. To ganin tawagar Inna yasa ta fasa.
Da farko da zafansa kanin Innan ya shigo, harda wani huci yake yi irin ran maza ya ?acin nan. Yana sauke idanunsa a kan matasan da ya aiko da farko Jaish ?in ya jibgesu sai ya ji tsoro ta ?an kama shi, nan take ya lafa, ya shafawa kansa ruwan sanyi dan samun lafiya.
Bai ma karasa razana ba sai da ya ?aura idanunsa a kan Jaish ?in, yaga dakakke tsayayyen namiji! Ai nan take ya nemi nutsuwarsa ya rasa, sai da hantar cikinsa ta ?a?a.
"Lafiyarku kuwa Shehu?". Cewar Ar?o, ya tambayi kanin Innan.
Jaish kuwa yana tsaye yana binsu da wani irin kallon da duk bala'inka ba zaka iya fassara wani irin kallo bane, sai shi ka?ai da ya yi ta yasan wace iriyace.
?an ja da baya Shehu dai ya yi, dama bai san Jaish ?in ba, sunansa kawai yake ji na aljani da ake mashi ikirari da hakan, wato yau da ya ?aura idanu a kansa sai da zuciyar maza ta karaya, ya tsorata sosai, hakan yasa ya ?ara ja da baya.
Kafin Ar?o ya sake yi masu wata tambaya ma suka juya a hanzarce suka bar gidan, suma matasan dake zube a ?asan, wa?an da suka dawo cikin hayyacinsu sai suka tashi da gudu suka bi bayan Shehun, wa?an da suke kwance basu dawo cikin hayyacinsu kuma suka cigaba da kwanciya kamar wa?an da suka suma.
Komawa su bappan suka yi suka zauna, da yake already sun san su waye ne su Shehun, and sun san a kan me suka zo.
Nunawa Jaish saman tabarma bappa ya yi a kan ya zo ya zauna. Ba musu ya zo ya zauna, a tsanake cikin sanyi da nuna kulawa bappan ya gaya mashi dik abin da yake faruwa, daga karshe ya ce. "Banso hakan ba, kuma Allah ya ga zuciyata Faisal na so ya auri Mahnoor, amma kuma ba zan iya kiran ?ata da bazawara ko kuma in ji wani ya kira mun ita da hakan ba, abin kunya ce babba mu a wajenmu, bani da za?in da ya wuce in..........."
Dakatawa ya yi da maganar bai kai karshenta ba sakamakon sake bankowa cikin gidan da aka yi a karo na biyu. A lokacin Mahnoor tana tattare gidan tana gyara abubuwan da fa?ar da su Jaish ?in suka yi suka watsa komai, ita kuma Mahreen tana zaune kusa da Ar?o ta buga uban tagumi tana tuna yadda Jaish ya yi ta jibgar matasan can, a gaskiya abin ya yi mata mugu mugun da?i kuma ya ?ayatar da ita.
Ba kowa bane ya banko cikin gidan ba face Faisal, kamar wani zararre, yana wani zaro idanun, ga dikkan alamu baya a cikin hayyacinsa, sai wani huci yake yi, ga shi babu ko riga a jikinsa, daga shi sai wando dogo ta wata shadda ko?a??iya, gashin kan nan nasa kamar dambu mahaukaciya ko ace bukka, ya tara gashin sosai, gata da cika, da alama ya yi birgima da gashin nasa a cikin tur?ayar ?asa ne, dan gaba?aya gashin nasa ta zama yadda kuka san power aka zuba mashi, saboda ?asa da ta wankesa.
Jikinsa duk ?asa, kai in takaice maku ya fita a hayyacinsa, ya fita sahun mutane.
Yana shigowa a gaban bappa ya zube gwiwowinsa, yana zaro idanu, ga idanun nasa alamar ya ci kuka ya ?oshi, sun yi jajir gulu gulu da su, haka kamar mahaukaci ya fara sambatu.
"Wlh bappa ina son Mahnoor, kuma kowa ma ya san da haka! Kai kanka ka sani, ba ka bani aurenta ba ma? Dan Allah bappa kada ka ?auketa daga gareni ka bawa wani ?a?o can bare da bai san darajarta ba, ka ji tausayi na bappa, zan iya mutuwa a kanta, aradun Allah ina kaunarta, wayyo na shiga ukuna......."
Yana tsaka da yin maganar ne idanunsa suka sauka a kanta, ta tsaya turus a tsakar gidan baiwar Allah, Allah ya gani tana son Faisal ?in, ita yanzu ma ?o?ari take ta fahimci wani abin, tana son ta san menene ya sanya Hamma Faisal ?in nata ya birkice haka? Ta ji yana fa?in kada a rabasu, to waye zai rabasu? Ta gaza gane kada a rabasu kamar yaya? Bata fahimci komai ba.
A zabure ya mi?e tsaye, hannunta ya zo ya ru?o, ya jata har gabansu bappan, kuka bawan Allahn nan ya shiga yi da hawaye bibbiyu kamar ?aramin yaro, fa?in ya fara yi. "Mahnoor ki gayawa bappa kina sona, dan Allah ki gaya mashi ba bakon ?a?on nan nasa kike so ba, ki gaya mashi kada ya rabamu kin ji?". Yana magana hawaye da gudun gaske suka cigaba da wanke mashi fuska, ya ha?a uban gumi, fuska kamar wanda aka watsawa ruwa saboda gumi, jikinsa har kerma yake yi, tsikar jikinsa duk sai tashi suke yi, wlh sai ya baka tausayi idan kaga yadda ya mace a kanta.
Daga Ar?o har bappan an gaza samun mai kwarin gwiwar iya yi mashi magana, ko ya taushesa, sun zuba mashi idanu kawai.
?o?arin kwace hannunta daga nasa ta yi, dan ta gudu izuwa cikin ?aki, baiwar Allah ba zata iya tsayuwa wannan rashin kunyar ba, yanzu ta fagimci batun aurenta kenan ake yi, sai dai ta gaza gane da waye a cikinsu ake batun auren nata? Me kuma yasa Hammanta kuka?.
Mahreen ce ta mi?e tsaye tare da ?arisowa in da suke, hannu tasa ta fara ?o?arin taya Mahnoor ?in kwace hannunta daga ri?o da ya yi mata, da yake kunsan ita fa bakinta baya shiru, kuma kun san ba shiri da Faisal ?in suke yi ba dama sai ta ce. "Kai Hamma Faisal ai dama bama sonka, dama Adda Mahnoor ba zata aureka ba, dan ni bana sonka, ka sake mata hannu........."
Bata ?arisa maganar ba ya ?auketa da wani irin gigitattacen mari wanda yasa sai da ta yi baya baya ta fa?i ?asa. Zuciyarsa tafarfasa yake yi tamkar an ?aura dalma a wuta, dama shi ma yana da zuciya har haka?. Yana ji da tsananin bakinciki tazo tana sake gaya mashi mai ?aci, ai dole ya dallah mata mari.
Yadda kuka san zuciyar Jaish zata fashe, yadda kuka san shi ya mara ba Mahreen ba, a wani irin zuciye ya mi?e tsaye, nan take ransa ya ?aci, da hannu ?aya yasa ya pincike rikon da ya yi wa Mahnoor ?in, wani irin mari mai tsananin zafin da ya sauke mashi a saman ?uncinsa ne sai da yasa shi ganin wasu irin taurari masu hasken gaske suna gilma mashi, sake ?aga hannu ya yi a karo na biyu zai ?ara mashi wani marin.
Da saurin bappa ya mi?e ya ri?e hannun nasa ta baya, a fusace ya juyo tare da damko wuyar bappan ba tare da ya lura cewa shi ?in bane, a tunaninsa wasu ne irin su Faisal ?in.
Ya juyo da kyau da niyar ya karya hannun wanda ya rikesa ?in, duk da ?acin rai da zafin zuciya da ta rufe mashi idanu hakan bai sa ya gaza gane cewa bappa ya sha?e ba. A hanzarce ya zame hannunsa daga wuyar nasa yana sunkuyar da kansa ?asa, ransa ya ?aci ne na Mahreen da Faisal ?in ya yi wa mutuniyar tasa.
A hankali ya sakar mata hannunta da ya kwace daga cikin na Faisal. Yana saketa ta kwasa a guje sai cikin ?akinsu tana sauke numfashi.
Hannunsa ya mi?awa Mahreen dake baje a ?asa tana kuka. Da sauri ta ri?o ta mi?e tsaye. ?akinsu ya nuna mata da ?ayar hannun nasa alamar ta je.
Ai da gudu ta wuce. Shi kuwa Faisal da ya yi suman tsaye ko motsi bai yi ba ne bappa da Ar?o suka ?ariso kusa da shi, bappa nasa hannun ya ta?ashi kawai sai ga Faisal ya tafi luuu sai ?asa, da karfi ya furta. "Shikenan ni Faisal na mutu".
Yadda ya yi maganar gwanin ban dariya gwanin ban tausayi, ya ji marin manya ne yasa ya zama kamar ya zare, kamar ?wa?walwar ta samu matsala, shiyasa zaku iya jin abin da ya fi wanda ya fa?a yanzu ma, ba laifinsa bane, ya ji hannun jinin Modarawa ne.
Cikin harshen fillanci Ar?o ya ce da bappa wannan magana ta batun auren nan a barta sai komai a daidaita, sai a san abin yi, yanzu dai su ?auki Faisal a sama mashi magani ya samu lafiya, dan da alama hankalinsa ta gushe ?wa?walwa ta ta?u.
Na'am da zancen sirikin nasa bappa ya yi, matasa suka nemo aka ?auki Faisal ?in zuwa gidan Ar?o, a tare suka wuce da bappan, amma kafin su tafi sai da suka zubawa sauran matasan da Jaish ya jibga wa?an da basu farfa?o ba ruwa.
Baya sun farfa?o ne suka tasasu a gaba suka tafi. Nenne tana can cikin ?aki tana ciza yatsa tammar zaga yi hauka, ban da nadama da danasani babu wani abin da yake ranta, ta yi babban danasani na sanyawa a ha?a wannan aure......... Ni kuwa nace danasani tun daga yanzu Nenne? Kada ki bada mata mana! Ai bai kamata ki fara danasani tun yanzu ba! Yana da kyau ki kara ?aura ?amara ne hegiya!. Ai duk wanda ya gina ramin mugunta to ya jira ranar afkawarsa ciki! Ai baki ga komai bama tukun nan. Dama ke kin ta?a gani ko kin ta?a jin zalinci ta ?aure ne? To jama'a sai a kula, komai yana da iyaka yana da karshe musamman ma zalunci!!. Aka ce idan jemun ?an uwanka ya kama da wuta?? Ku ?arasa mun!!.
Baiwar Allah Mahnoor tun da ta shiga ?aki kuka take yi sosai har Mahreen ta shigo ta sameta. A gefenta ta zauna suka cigaba da kuka a tare, ba mai rarrashin ?an uwan.
Shi kuwa Jaish da ko a jikinsa, shiryawa ya yi ya fito ya ka?a dabbobin bappan ya tafi kiwo abinsa, yau bai ma jira bappan ba, dan ya ji lokacin da suka ce zasu je su nemawa Faisal magani, dan haka sai kawai ya tafi abinsa.
Bai dawo ba sai can yamma kamar yadda suka saba, bappan har lokacin bai dawo gida ba, dan kuwa Faisal dai a maimaikon sauki sai abin ya kara gaba sosai, kamar ya zare ne fa!.
Lokacin da ya dawo daga kiwon babu kowa a tsakar gidan, ?akin bappa ya nufa dan ya ?an huta sannan ya je ya yi wanka.
Yana shiga ita kuma tana fitowa, baya ta ?an ja dan ta bashi hanya ya wuce. Ta sunkuyar da kanta ?asa ta mannu da jikin bango.
Shiru bai wuce ba ya tsaya a bakin kofar. Ganin haka yasa ta ?an ?ago idanunta dan ta saci kallonsa ko me ya hana shi wucewa?.
Tana ?ago kai suka yi four eyes, dan kuwa idanunsa yana kanta, ba komai yake gani ba kuma face hawayen da yake saman face ?inta ga idanunta a cike tab da wasu zafafan hawayen.
?asa ta sake yi da kai tana ?an kame kama kamar maras gaskiya.
Hannu ya kai ya ?ago ha?arta, wani irin dukan uku uku kirjinta ya yi, wiki wiki ta fara yi da idanu kamar an tare ?era a tarko.
Da hannunsa ?aya ya yi nuna mata alamar meyasameta take kuka?.
Kai ta fara girgiza mashi alamar babu kenan. Tabbas yaga tsoro a kwance a cikin idanunta hakan yasa ya yi tunanin duk yadda aka yi Nenne ce ta daketa, shiyasa ma taki fa?a, saboda tana tsoron bala'in Nennen.
Shiru ya ?an yi yana tunanin irin rayuwar nan tasu, shi dai kunga ya taso ya samu King matansa har uku, kuma kowacce da ?a?anta, amma basu yin irin wannan zaman kishi na cutar da ?a?an nasu haka, su ba ruwansu suna kaunar ?an uwansu, ba ruwansu da uwa daban daban suke, su dai sun san ubansu ?aya, ba ruwansu da kishin da iyayensu mata zasu yi, amma a nan ya rasa me matsalar Nennen nan, dan ba ke kika haifi yarinya ba sai ki yi ta gallaza mata? Ke kika halicceta ne?.
Zame hannunsa daga ha?ar tata ya yi tare da shigewa ciki. Bappa da yake tsaye a bayansu tun ?azun yana ganinsu ne ya fara zubawa Allah godiya a cikin ransa da Allah yasa aka ?aura auren nan, a cewarsa soyayya suke yi da ya gansu a tsaye haka, bai san cewa shi Jaish tun da yake ma bai ta?a shigar mata fa?a ba, kai bai ma ta?a matsowa kusa da ita kamar yau ?in ba, yana dai shigarwa Mahreen fa?a, dan ita kunga ai mutuniyarsa ce, amma Mahnoor gaskiya babu wani abin da ya ta?a ha?asu ko da sunan wasa.
Yana sake ha?ar tata ta nufo waje da sauri, karaf suka ci karo da bappa. Gaisuwa ta ?aga mashi tana goge hawayen face ?inta.
Hannunta ya ri?o suka koma cikin ?akin. Yana zaune a bakin bed suka isko shi, ya kurawa yatsun hannunsa idanu yadda kuka san yana son tuna wani abin.
Kusa da shi bappa ya zauna tare da sanya hannu ya kamo nasa hannun da ya kurawa idanun. Ita dai tana tsaye tana ganin ikon Allah, tana jiran ta ji me bappan nata zai ce?.
Bu?e tafukan hannun Jaish ?in ya yi tare da matso da ita ya ?aura nata hannun da ya ri?e a kan nasa. Cikin harshen larabci ya yi mashi bayanin cewa ga amanarta nan ya bashi ya ga dai marainiyar ce, ya dubi girman Allah ya ri?e mashi ita amana, kada ya kuntata mata, kada ya zalunceta, yana da tabbacin Mahnoor yarinya ce mai biyayya, kuma In Sha Allah zata yi mashi biyayya fiye da yadda yake tunani.
Shiru bai ce komai ba, sai ma sunkuyar da kansa ?asa da ya yi, bashi da wata damuwa da wannan aure, dan bai san wanene shi ba ma.