Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 59

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 59

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 59: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 59. Slowly ya ?ago da kallonsa, saman face ?inta ya sauke kallon nasa. Kana ganin…

3,347 words

Slowly ya ?ago da kallonsa, saman face ?inta ya sauke kallon nasa. Kana ganin face ?inta zaka san a firgice take baiwar Allah, tana son ta tambayi bappa meyasa za'a aura mata shi? Amma kuma kunya ya hanata, ita ba shi take so ba! Hamma Faisal shi ne za?inta, shi ne ta bu?e idanu ta kallah a matsayin masoyi, tsawon shekaru 5 kenan suna tare a matsayin masoya, tun bata fi ?ar 9 years ba kenan, kawai rana tsaka a zo a canza mata da wannan mutumi da take tsoro? Kai gaskiya abin da sake.

Amma dai haka ta daure tana tunanin wa kanta mafita. Ha?i?a Jaish ya ga wasu abubuwa kwance a cikin idanunta, sosai ta bashi tausayi, shi ba yana tausayinta dan auren da aka yi masu aka rabata da Faisal bane, a'a, yana tausaya mata halin da take ciki a cikin gidan, dama Allah ya gani ba shi yake yi wa?an nan ayyuka da take yi ba, amma wlh ganinta kawai yake tana aikin ya gaji, wlh ya gaji da ganinta tana bautatuwa da tsabar bakar wahalar da take sha.

"Hamman Mahreen". Bappan ya ambaci sunansa. Dawo da hankalinsa ha?e da kallonsa a kan bappan ya yi, sai dai side ?insa ya kalah, ya ki yarda su ha?a idanu.

"Baka amsa mun ba, ka kar?i amanar da na baka? Zaka ri?e mun ita da amana?".

Shi kam me bappa zai nema a wajensa da zai ki yi mashi? Irin yadda bawan Allahn nan ya nuna mashi kaunar da iyayensa ne kawai zasu iya nuna mashi irinta a duniya, ai koma me ya yi bai biyasa ba, kuma koda bai ce mashi ya ri?e mashi ?a da amana ba wlh dole zai ri?eta, saboda shi tun ainahi ma ai ba maci amana bane, babu cin amana a jinin Modarawa.

Dan haka sai ya gya?a kansa sama kawai alamar zai cikawa bappan maganarsa. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke, koba komai ya ji sanyi a ransa, kuma a yanzu duk duniya ba wanda ya kaishi sanin wanene Jaish ?in, yasan yana da zuciya mai kyau.

Sake hannayen nasu ya yi, da sauri ta juya zabar ?akin dan wani irin kuka da ya zo mata, tun bayan kukan rashin mahaifiyarta da take dirza sai yau ne ta ji kuka mai zafi irinsa ya zo mata, duk azabar da Nenne take yi mata ko ka?an baya ta?ata kamar idan ta tuna rashin uwa a duniya, yau kuma ga rashin masoyin da ya sota tun tana ?ar shekara biyu a duniya, an ha?ata da wani mutum mutumi kawai.

"Waru ha?o (zo nan)". Bappa ya fa?a cikin sanyin murya. Ba musu ta dawo ta tsugunna a gabansa.

Mi?ewa Jaish ya yi ya fice waje. Hannunta bappa ya ri?o, cikin sanyin murya ya fara bata hakuri tare da yi mata nasiha a kan ta kar?i kaddararta, ta dage ta ci jarabawarta, sannan ta sani Jaish ya fi Faisal nagarta da komai da komai, in ta yi hakuri a hankali komai zai dai'dai ta, sai magana ta karshe kuma shi ne. "Duk da nasan kina da kula da takatsantsan, amma ina son ki kara kulawa sosai, ki mayar da hankalinki wajen ganin kin gujewa abin da baya so, kin san cewa yana da zafin zuciya, kuma nasan ita ce ka?ai zata rin?a kawo sa?ani a tsakaninku, yana da zuciya da zafin nama, jininsa a tafashe yake, baya son abu sanyi sanyi da ?ata lokaci, ke kuma kina da sanyi over, dan haka sai ki kula, ki guji abin da zai sanya ransa ya ?aci, dan idan zuciyarsa ta matso kusa komai yana iya faru, nasan kin san hakan, ina kara tunatar dake ne kawai, ki kula sosai, na mai tabbatar maki zaki ji da?in zama da shi".

Kanta a ?asa, ban da aikin kuka babu wani abin da take yi, ita dai Allah ya gani Faisal take so, bayan shi bata jin zata so kowa.

Rarrashinta bappan ya rin?a yi, a haka Mahreen ta shigo ta samesu, ta dawo daga aikan da Nenne ta yi mata gidan Ar?o.

Ganin ?ar uwarta tana kuka ne yasa ta fa?o cikin ?akin da sauri tana tambayar ba'asi.

Rungumo juna suka yi tana gogewa Mahnoor ?in hawaye tana mai cigaba da tambayar bappa waye ya dakar mata ?ar uwa yaga tijara yau!!.

"Babu wanda ya daketa Mahreen, nasiha nake yi mata shi ne take kuka, ku tashi ku tafi ?akinku Allah ya yi maku albarka".

Da amin Mahreen ta amsa, sai ta ?aura da cewa. "Bappa ina Hammana?".

"Ya fita waje".

Mi?ewa ita kuma Mahnoor ta yi ta nufi waje da sauri tana mai cigaba da dirzan kukanta. Da sauri Mahreen ta bi bayanta, suna shiga ?aki ta kwanta a saman gado tare da ?ara rushewa da wani sabon kukan.

Sai aikin rarrashinta Mahreen ta fara yi, bata kulata ba kukan nata kawai take yi. Can kuma ko me ta tuna sai ta mi?e zaune a zabure. Da sauri ta diro ?asa ta nufi waje tana goge hawaye.

Bokiti ta ?auko ta juyo ruwan zafin dake saman wuta a kitchen, ta ?ebo na sanyi daga randa ta surka, sa hannu ta yi ta ta?a ya yi dai'dai. Ta ?auka sai cikin toilet, tana ajiyewa ta fito da sauri. Already kunsan akwai hijabi a jikinta kullum dama, dan haka sai ta nufi waje kai tsaye.

Yana zaune a ?ar?ashin bishiyar kofar gida kamar yadda ya saba zama, gabansa ta ?arisa, cikin girmamawa ta ce. "Hamma ga ruwan wankan can na kai ma, ka yi hakuri na manta ne yasa tun ?azun ban kai maka ba".

Tun da ta fara magana ya kafeta da idanu yana kallonta, bai san meyasa yau ya ji kamar ta yi mashi kama da wata wadda ya sani ba, sai yake jin kamar ya ta?a rayuwa a wata duniya ta daban, kansa ya ji tana ?an sara mashi a hankali hankali,

Magana ta gaskiya a lokuta da dama yana jinsu kamar Gimbiya Zunaira ce, baya cikin hayyacinsa, amma tabbas soyayya da yake yi wa kanwar tasa a jinin jikinsa yake, sau da dama yana jin kamar yana da wata wadda yake matukar kauna, yafi yawan ganin Mahreen a wannan matsayi shiyasa yake yawan sake mata, yau kuma sai ya ga hakan a tattare da Mahnoor, musamman ma yadda ta yi magana a kusa da shi, sai ya ji tamkar sun ta?a yin wata rayuwa a wata duniyar da ita, a zahiri ba da ita bane, da Zunaira ce.

Jin ya yi shiru bai ko motsa ba ne yasa ta ?ago da kallonta dan taga me yake yi. Tana ?agowa suka kalli juna ido cikin ido.

Gabanta ne ya bada ras a hanzarce ta yi ?asa da kanta. "Hamma in tafi?". Muryarta ya daki dodan kunnuwarsa.

Mi?ewa tsaye ya yi ya wuce gaba ba tare da ya yi mata magana ba. Da sauri ta mi?e ta bi bayansa. Kai tsaye cikin toilet ya nufa ita kuma ta wuce ?akinsu.

Yau dai abincin dare turasa kawai baiwar Allah ta yi, amma ba dan da?i ta ci shi ba, tunanin Hamma Faisal ?inta ne kawai a ranta, abin ya yi mugun sosa mata rai.

Haka baiwar Allahn nan yau sam bata rintsa ba, kamar yadda taga rana haka taga dare. Sai dai ba ita ka?ai bace bata rintsa ba, bappa kwana sallah ya yi yana rokon Allah da yasa Jaish ba mugu bane zai ri?e masa ?a da amana, Allah Ubangiji ya bashi lafiya, sosai ya yi masu addu'a, shi kuwa Jaish yana ta barci abinsa.

Nenne ma bata yi barci ba, kwana ta yi tana tsinewa tunanin gwaggo na ce wa a ha?a Mahnoor and Jaish aure, ga shi yanzu tun ba'a je ko'ina ba ya fara tare masu fa?a, a kan Mahreen ya daki Faisal da safe, to ina ga kuma Mahnoor da take matsayin matarsa? Zai iya kisa a kanta kenan?. Abin ya tsaya mata a rai matu?a, duk sai ta ji kamar ta kashe kanta, sai tunanin ta yadda zata bi ta ruguje wannan aure take yi, ta yi wa kanta alkawarin ko ana ha maza ha mata wlh sai ta ruguje wannan aure ta mayar da yarinya ?aramar bazawara ko 15 years bata cika ba, sannan ta ?untatawa rayuwarta, shi ne next plan ?inta.

Washegari da safe daga bappa har Nennen idanunsu a kumbure suka wayi gari, saboda rashin samun barci, gara ma shi bappa a kan dadduma gaban Ubangijinmu ya kwana, ita kuma fa? A tawagar shai?an ta kwana?

Idanun sun yi jajir. Mahnoor da bata samu barci daren jiya bane na asuba ya ?auketa bayan sun yi sallah, kun san shi fa barci ba'a cin bashinsa, idan ka ci sai ka biya a time ?in da baka yi zato ba, aikuwa tana sallah tana gyangya?i, da kyar ta iya samu ta daidaita nutsuwarta ta gabatar da sallarta dai'dai.

Daga nan ta ?ige da barci, tana tsaka da barcin ne ta ji saukar duka a jikinta ta ko'ina da bulalar itaciyar gwaiva.

A razane ta mi?e, bama ta yi ihu ba dan tasan wanenen mai dukan nata, waje kawai ta fita da gudu. Nan take hawaye suka cika mata idanu tab da kwallah. Aikinta ta fara yi tana sharar kwallah da ya fara bin saman ?uncinta.

Karfe shidda ne dai'dai a lokacin. Tsintsiya ta ?auka ta fara ?o?arin share gidan tas. Ita kuwa Nenne ta koma ?aki bata ko kalli in da Mahreen take ba, saboda ?arta ba ?ar wahala bace a cewarta, ?ar gata ce ta sha barcinta.

Bayan ya gama sharar sai ta kwashe dattin cikin wani marfin langa ta nufi bayan gida zata je ta zubar a can wani rami wajen dabbobinsu bayan ta gama sharan kenan, dama a nan suke zubar da shara kullum, tana yi ma tana kuka baiwar Allah, ga yunwar safe da take ji, idanunta ita ma a kumbure saboda rashin barci jiya, jikinta duk babu kuzari, zuciya a raunace, tana tafiya tana jan kafafu kamar zata kifa ?asa. Garin yana ha?e bakin kirin da hadari, yau da alama ruwa zasu sha ba ka?an ba.

Tana zuwa ta juye sharar a ramin, juyowarta ke da wuya ta ci karo da shi a in da ta buga kanta a saman kirjinsa, baya ka?an ta ?an yi dan ta samu damar ganin face ?insa.

Ko yaushe ya tashi barci har ya fito ya zo cikin dabbobin zai tatso nono? Ta jefa wa kanta tambaya. ?asa ta yi da kanta tare da cewa. "Hamma ina kwana?".

Bai motsa ba bare tasa ran ya jita, hannunsa ri?e da bokiti wanda ya tatsi nonon a ciki. Kyawawan yatsun hannunsa ya ?ago ya ?aura a saman kumatunta a in da ya nuna hawayen face ?inta tare da yi mata alama da hannun na meyasameta da sanyin safiyar nan take kuka haka?.

Ta gane me yake nufi, dan haka yake tambayar Mahreen ma idan ya ganta tana kuka, dama dayawan lokuta tana kukan yunwar safe idan ba'a gama abinci da wuri ba, ai Mahreen manyan ?asa ne.

Girgiza mashi kai ta yi alamar babu abin da ya sameta. Zuciyarsa ce ta zarga mashi Nenne, dan yasan ita ce mai sanyata aikin sassafe kuma tana zazzaga mata masifa. Wucewa ya yi izuwa cikin dabbobin ba tare da ya sake bi ta kanta ba.

?an binsa da kallo ta yi tana mamakin hali irin nasa, wani irin mutun ne a mur?e haka? Abin dai sai a hankali, shi baya tambaya sau biyu, idan ya yi ?aya ba'a amsa ba shikenan kai ka jiyo, gaskiya yana da abin mamaki.

Sa kai ta yi ta wuce, a hankali take tafiya tana goge hawayen nata. Tana shigowa ta sami Nenne a tsakar gida, a lokacin kuma bappa ya tafi gidansu Hamma Faisal ya je duba jikinsa.

Wani irin tsawa da Nennen ta daga mata a kan ta je ta jima ne sai da yasa ta ji duk wani kasala da yunwa da take ji sun gudu, nan take jikinta ya soma kerma.

"Uban me ya tsayar dake daga zuwa zubar da shara?!" Shi ne tsawar da ta daka mata.

Murya a sar?afe ta furta. "Hamma na tsaya gaisarwa". Har lokacin hawaye suna cigaba da gudu a saman face ?inta.

Gadan gadan ta tinkarota da nufin ta fara aikin da ta saba na jibgarta, dan a cewarta wato yanzu ta yi girman da har zata iya bata amsa idan tana magana, kuma dai kuna ji ita ta tamnayeta me ya tsayar da ita, ta bata amsa kuma abu ya zama bala'i, wato dai idan mutun mugu ne kawai ka barsa, dan kome zaka yi mashi sai ya gallaza maka.

Wani tray irin na kwano na mutanen da ?in nan ta rarumo a fujajan zata maka mata a kai dan tsabar bakar zuciya irin na matar nan, ga jikin tray ?in duk a farfashe ya yi lamba, wanda kuma kun san lambar jikinsa tsartse ne da yana iya fasa fatar jikin mutun ya shiga cikin nama, yana yi wa mutum illah sosai.

Amma tsabar mugunta sai ta rarumo shi zata rafka mata a kai, ita kuma tana tsaye baiwar Allah, da yake tasan ko ta gudu ma ba tsira zata yi ba, sai dai ta kara wa kanta wani bala'in, dan idan ta gudun ma dole a gidan zata dawo ta kwana, idan ta dawo kuma ninninka mata azaba zata yi, so is better for her to stay kawai.

Da iya karfinta ta ?aga trayn zata buga mata, runtse idanu ta yi gam tare da sanya hannu ta tare kanta da fuskarta tana jiran saukar trayn a kan nata.

Shiru bata ji an rafka mata ba, hakan yasa ta ?an motsa zara zaran eyelashes ?inta tana son bu?e idanun ta ga me yake faruwa bata ji anfasa mata kai na?.

Aikuwa tana bu?ewa cak ya ri?e hannun Nenne da tray ?in gaba?aya. Tsabar tsoro yasa Nennen ta yi suman tsaye, yau ga aljani ya ri?e mata hannu ko in ce maye da suke ce mashi.

E lallai ba shakka yau Nenne taga bone, maye ya ri?e mata hannu ba kanta, me kuke tunanin zai faru a wannan ?auye? Ya kuke ganin zamansu zai kasance a yanzu? Shin Nenne zata iya samun nasarar raba wannan aure kamar yadda ta shiga ta fita ta ha?a kuwa? Me makomar Jaish? Shin zai yarda ya zauna da Mahnoor matsayin mata kuwa? Dan ni dai ban ga alama ba!. Akwai cakwakiya fa sosai, yanzu muke ?o?arin afkawa cikin littafin mu gadan gadan, ku gyara zama akwai......... Ba sai ma na fa?a ba, muje dai zuwa. ________________________????

FRANCE????

Hakimce yake cikin katafaren office ?insa, ya ?aura kafa ?aya bisa ?aya, sanye yake cikin shigar ?ananan kaya wandon jeans milk color and flannel shirt coffee color masu bala'in kyau da tsada, ya ?aura denim jacket a saman kayan nasa, dan kowa yasan ?asar faransa suna da balai'n sanyi mai dusar ?an?ara, mai daskarar da abu, sai da jackets manya manya ma kuwa. Ya fito a ainahin Smart ?insa, ko mai kiyayyarka da shi sai ka amincewa ranka shi ?in smart ne, komai ya yi guy ?in nan dai'dai take tafiya da shi.

Jiga jigan jami'ai ne ta ko'ina suke ta shawagin shige da fice, wani irin sanyin Ac da kamshin office perfume ne yake tashi a office ?in. A ainahin office ?insa yake ba'a ma'aikatan ha?a nuclears ?insa ba, nan yana bakin aikinsa ne.

Wayarsa dake saman desk ?in gaban nasa ne ta fara ruri alamar shigowar kira. Yana tsaka da yin aiki ne ba kama hannun yaro. Jajirtattun jami'ansa guda ?ai ?ai ?ai har guda shidda ?asar America ta kama masu a matsayin ?an le?en asiri ?asa da ?asa, kuma hakance, le?en asiri suka je yi Allah ya bawa American dama suka kamasu, sun jima suna yi mata le?en asirin kamar yadda ita ma take yi masu, sai dai Smart hege ne na karshe, maye ne a basira, duk wasu ma'aikatansa ya zuba masu matakan tsaro na na'urori, harta na'urar ?adda kafa yana da shi wanda shi da kansa ya ?ir?ireta, amfaninta shi ne ba'a isa a bibiyesa a lamuransa ba, komai bala'in ?asa haka zata gansu ta barsu.

Da su da America fa ana mugun tare, kawaye sosai, amma dukkansu basu yarda da juna ba, suna le?ar asirinta ita ma tana le?ar nasu, kunga duk suna munafurtar juna ta ?ar?ashin ?asa kenan, a fili kuma idan suka ha?u sai kuga kamar zasu cinye juna saboda so, amma American ce ta fara le?ar asirinsu shiyasa suma suka koya, sai dai America ?in ko ta le?i asirin nasu bata samun komai, duk min karfin na'urar da zata yi amfani da shi bata iya hango komai daga sararin samaniyarsu, har tauraron setline system suka sanya dan su le?i asiri amma ina basu iya ganin komai, hege Smart ya juyar masu da kwakwalen kai.

Hankalinsu ya gaza kwanciya dan suna ganin kamar tabbas yadda Allah ya baiwa Smart wannan basira daddynsa ba zai barshi haka ya tafi a banza ba, suna zargi lallai lallai yana amfani da ?wa?warar nan tasa suna gina ?asarsu, shi ne yasa suke le?e le?e ko zasu iya ganin ko da ?ir?ishin makami ne haka irin abin zargin nan.

Sai dai basu san Smart ya wuce tunaninsu ba, duk ya rufe komai abinsa.

Sau da dama jami'an Smart ?in suna zuwa la?ar asiri ba'a ta?a kamasu ba sai yau, dama ai ba kullum ake kwana a gado ba.

Yau dai an kamasu shi ne ya ?aga hankulan sauran jami'an, dukkansu jira suke yi suga matakin da zata ?auka a kan jami'an nasu, kansa ya ?au zafi, sai aiki yake yi tukuru dan ya yi amfani da basiransa wajen kwato jami'an sa cikin sirri, baya son maganar ta baza duniya.

Mummynsa ce take ta kiransa a kan ya zo gida da wuri akwai ?an ?aramin party da suka shirya, yau iyayen Heleena sun zo daga ?asar England, shi ne suka shirya party, ba komai ne kuma ya kawo iyayen Heleena ?in ba face sun zo ne domin ayi maganar aurensa da Heleenar....... Babbar magana, har sun bani bazawarar dariya ??

Abin da baku sani ba shi ne, Heleena zaman Smart take yi a cikin gidan, tun da ta yi wayo ta san menene soyayya, ta san kanta take fama da son shi, ta kafe shi take so, tana bala'in tsoronsa sannan tana haukar sonsa, iyayenta sun san da zancen, shi ma mummynsa ta sani, shi da daddynsa ne kawai basu san da zancen ba, dan su fa idan daddy ya san abu to tamkar shi ne ya sani, idan kuma shi ya san abu to tamkar daddyn ne ya sani, yadda kuka san twin's wlh, kuma wai uba da ?a, ko da yake sha?uwa ce ta yi yawa.

Mum ta ?asa iya gaya mashi Heleena fa shi take jira, shi take so yasa ma ta yarda har yanzu take tare da su, tana tsoron gaya mashi ne kada ya tayar mata da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali, tasan a duniya ya tsani mutum maras kunya, ita kuwa Heleena badan badan bama sai ace ita ta kawo rashin kunya duniya, tsabar bata da shi ko ?igo, shiyasa ya tsani ganinta kamar ba gobe, sam basa shiri.

Sun gama shirin komai shi da daddynsa kawai ake jira su zo a tattauna a tsayar da magana, daddy ma yana office yana ta tikar aikinsa bisa gaskiya da amana, yana ta ganin call ?in mum ?in amma yaki ?agawa, dan yasan ita fa idan bata je office ?inta ba bata da aiki da ya wuce ta zauna ta ?aura kafa ?aya bisa ?aya ta yi ta danna masu kira a kan su dawo suma su ha?u su jibge a gidan suna kallon juna, ba aikin fari bare baki da zasu yi mata, kawai su zauna suna ta ganin juna, ai mummy duniya ce.

To da suka gane mata ne sai basu wani cika ?aukar call ?inta idan bata je office ba.

Wani call ?in ne ya sake shigowa cikin wayar a karo na biyu, sai dai ba call ?in mum bace.

Bluetooth dake kunnensa ne ya isar mashi da sa?on cewa ga number dake kiransa. Jin bana mum bane yasa ya yi picking.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull