Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 60
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 60: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 60. Yana ?aga kiran daga ?ayan ?angaren a ru?e wani fasashen murya ya fara fa?i.…
3,320 words
Yana ?aga kiran daga ?ayan ?angaren a ru?e wani fasashen murya ya fara fa?i. "Sir remain s few minutes, the bomb went off". Ba tare da ya amsa ba ya mi?e tsaye, cikin nutsuwar nan tasa ya nufi waje wayar na'a hannunsa.
Kai tsaye wajen wata F-15E Strike Eagle ya nufa, ?aya ne daga cikin jiragen da air force suke amfani da shi, shi ba air force bane amma yana amfani da irin jirgin a duk lokacin da yake son isa waje cikin gaggawa, dan jirgin tana da mugun gudun gaske.
Yana sa?o kafarsa waje wasu irin jiga jigan zaratan maza ne suka fara aikin sara mashi, tamkar zasu bauta mashi saboda biyayya.
Ba tare da ?ata lokaci ba ya bar headquarters ?in nasu cikin wannan eagle ?in.
Bai jira a ko'ina ba sai a lotus forest, gaba?aya wajen harta bishiyoyin dake kewaye da wajen snow na mamayesu except wajen da jirgin nasa ta sau?a. Wajen ana tsabtace shi ba'a barin snow a nan.
Already an rigada an shirya komai shi ka?an ake jira, jami'ai ne da dama cike a wajen, dukkansu fararen fata ne tas.
Suna ganinsa a guje suka nufosa, jami'a,i zasu kai goma karti da su, haka suka nufosa, wasu daga cikinsu suna ri?e da bomb hand gloves, wasu kuma bomber jacket.
A tsananin zafafe suka fara sanya mashi bomber jacket and hand gloves ?in, sauri sosai suke yi domin bomb ?in saura ?an mintuna ya tashi.
Cikin nutsuwa yana taku a hankali ya nufi wajen, ji jami'an suke yi tamkar su janyoshi da sauri su ?arisa da shi wajen, dan rayukan ?an uwansu ne yake a ha?ari, kuma shi ka?ai zai iya cetansu, sai dai ?an banzan jan ajine da shi na masifa.
Wayarsa ce ta fara kara, call ?in mum ne, dan ya tsokaneta sai ya yi picking, bai bari ta fara jefa mashi tambayoyi ba ya ce. "Mum i am near the bomb, I will remove it from some of our officers, so i will call you later".
Habawa ai mum tana jin wannan labari ta mi?e tsaye, duk da tasan wanenen shi ?in a kan aikinsa, amma ita wannan batu na bomb yana ?aga mata hankaki sosai,........ Ni kam na ce dan ma baki san har nuclear ?an albarkar ?an nan naki yake ha?awa ba kenan! Da kin sani sai yaya kenan?.
A ru?e ta fara fa?in. "My baby, take care of yourself, don't let something to happen to you, take care".
Katse kiran kawai ya yi tare da tura wayar a aljihunsa, dama dan ya tsokaneta ya yi hakan.
Jami'ansa tsabar ?aguwa da son ya zo ya ceci rayukan ?an uwansu har kamar su kai hannu su janyo shi izuwa wajen bomb ?in, tsabar isa da jan aji shi kuma ya tsaya yana waya. Abin abin takaici
Nasan zasu ce wani bomb ne akewa haka? To dai sai gobe zaku ji komai........????
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 31/10/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
E32
Jami'ansa tsabar ?aguwa da son ya zo ya ceci rayukan ?an uwansu har kamar su kai hannu su janyo shi izuwa wajen bomb ?in, tsabar isa da jan aji shi kuma ya tsaya yana waya. Abin abin takaici.
Kowannensu zuciyarsa sai bugawa yake da sauri sauri, a cikinsu akwai jami'in da duk jarumtarsa kuka ya fara yi, idanunsa sun cika tab da kwallah, saboda akwai yayansa a cikin jami'ai shidda da suke sarkafe da rigar boma boman, shiyasa ya fara kuka, dan Smart ya ?aga masu hankali, baya abu da sauri dan iskanci, saboda yasan shi ka?ai ne zai iya, dole a jirasa idan ana da bu?ata.
Gabansu ya ?ariso, shi kansa ya girgiza da ganin jami'an nasa, gaba?ayansu ?aure suke da rigar bomb, jami'ansa da ?asar America ta kama ne, da Smart ?in ya bu?acesu a hannunsu ne suka yi masu wannan abin, duk suka sar?afesu da boma boman da koda minti goma aka baka ka kashe bomb ?in har ya tashi ba zaka iya sanin me yakamata ka ta?a a jikinsu dan kashe su ba.
Ga shi su dukka shiddan aka ?aurawa, bayan haka dukkansu time na tashin bomb ?in nasu lokaci guda ne, kafin ya cire na wasu na wasu zai iya tashi, wannan dalilin ya ?aga hankulan sauran jami'an da suke wajen, shiyasa kuka ga wancan jami'in ya fara kuka, sai dai dukkansu sun san in dai Smart ya ce zai cire, to ?an sakanni sun isheshi, dan yana ha?a boma boman da suka fi wa?an nan ha?ari.
A gabansu ya tsaya dukkansu suna zaune saman chairs da sauran jami'an suka kawo masu. Tsabar suna cikin ha?ari ma a jiragen Rockwell B-1B Lancer aka turo su, sun ki sanyasu a normal jirgi, saboda gudun fashewar bomb ?in.
Calmly ya furta. "Jack come and remove all the camera's that have installed for them".
Zaro idanu suka yi, fuskokinsu ?auke da mamaki, kallon kallo suka fara yi wa junansu, gaskiya Smart ya cika ?an baiwa, sun duba jikunan jami'an nan nasu tas su basu ga wani abin ?aga hankali a tattare da su ba, shi daga zuwa ya ga an sanya masu camera a jiki, wato dole dai America tana son kama shi da komai kan?antar abar zargi, kunga idan ya cire ko ya kashe masu wannan bomb na jikin nasu cikin ?an?anin lokaci, in America ta ga da gaske shi ya cire ta hanyar wa?an nan camerorin to fa zasu ce wlh duk yadda aka yi yana ha?a irin boma boman, tarko suka ha?a mashi.
Cikin sauri suka fara ciccire masu camera's ?in, shi kuma yana nuna masu in da suke, irin ?ana?nanan cameran nan ne wa?an da ake ?atar dasu a jikin botrin riga, sai ka cika mai kaifin basira zaka iya za?ulosu.
Gaba?aya bombs ?in saura five minutes su tashi, jikin wasu jami'an har kerma yake wajen cire camera's ?in, dan tsoron kada ya tashi da su. Shi kuwa yana tsaye yana aikin shafa lallausan hair ?insa.
Bayan sun gama cirewa ne ya ?an rage tsawonsa ?a?an ya fara aikin kashe bombs ?in, bai yi yunkurin cire masu ba, kasheta ya yi kawai, dan cirewa zai ja lokaci.
Na karshe da ya zo cirewa saura one minute ta tashi, boma boman da kafin ka ciresu a matsayinka na kwararema sai sun ?aukeka sama da ten minutes, amma shi ya ciresu dukka in less than five minutes tsabar ya kware a iya ha?asu, kuma yana da tsananin nutsuwa ne, irin wannan aikin kuma dama tana bu?atar nutsuwa sosai, ga misali ma kun gani, jami'ansa da yake suna cikin tashin hankali kunga ai basu ga camera's dake jikinsu ba, shi kuwa kunga ai yana zuwa ya gani.
Umarni ya basu a kan su kwashi jami'an izuwa hospital ?insu na headquarter. Allah sarki har sun cire rai da rayuwa, dan basu ta?a tunanin za'a cire masu wannan bombs ?in ba, sun jigata sun sha bakar wahala, kafin ya sanya daddynsa ya yi magana da America ta sakar masu jami'an wlh sun azabtar da su ba ka?an ba, da kyar ma suka samu aka sakesu.
Sai da daddy ya ratse masu ba le?en asiri jami'an suka je yi ba, da yake suna matsayin kawaye sai ta hakura zata basu su, amma mugun munafurtar juna fa suke yi, dukkansu suna yi wa junansu kallon wawaye, a duniya idan kana raye babu abin da ba zaka gani ba wlh. Smart dai da daddynsa sun zama ?an duniya, wato sun iya siyasa ne na bugawa a jarida, yanzu sai su saka mutum a kwana.
Sai da ya tabbatar antafi da jami'an cikin aminci, sannan ya kwashi boma boman da ya cire masu bayan ya kashe ?in ya nufi eagle ?insa.
Office nasa ya koma, a can ya ajiye boma boman a kan idan ya samu time zai dubasu, daga haka ya wuce gida, dan mom taki barinsa ya huta, sai kira take ta danna mashi babu kakkautawa.
Ni dai securitys dake tsaron gidan nan nasu suna ?aga mun hankali har bana son zuwa ?auko maku labarai, wa?an nan ganinsu kawai ya isa ya sanya mutum sakin fitsari a wando, dan ma dai na ri?i Allah ina da kwarin zuciya ne, kuna ganinsu wasu jiga jigan turawa, sai dai kyawawa ne kuma duk da fuskokinsu babu alamar annuri bare imani, ga su ta ko'ina tun daga farko titin ketowa unguwar har izuwa cikin gidansu, ai kunsan yadda gidan shugaban ?asa yake, ba'a wasa da tsaro!!.
Yana shigowa main parlourn ?asa wani irin ?aure fuska na musamman ya yi, ya cunkushe rai dan kawai ya ga ba?i a gidan nasu.
Ko kallon in da suke bai yi ba bare su sa ran zai ce masu sannu, kai tsaye ya nufi elevator domin ya wuce room ?insa.
Da sauri mom ta mi?e tana fa?in. "Baby come here".
Wani irin kallo ya wurga mata, irin kallon nan na mom kin fara ko. Mayar mashi da makamancin irin kallon ta yi na e ?in na fara maza zo nan. Abin gwanin birgewa da ban dariya.
Tsayuwa ya yi kusa da elevator ba tare da ya ?arisa in da take ?in ba, ?arisowa gabansa ta yi tana fa?in. "Baby don't you see ur uncle? Come and greet them".
"Mom i have a lot to do now, you just go and greet them for me". Ya yi magana ba tare da ya kalli in da suke ba, yana kai karshen maganar ya haura sama. Haushinsu yake ji dan ba yadda dad ?insa bai yi da su a kan su musulunta ba sunki, a haka kuma suke son ha?a ala?a da shi, tab lallai kuwa!.
Bin bayansa izuwa saman ta yi, already har ya shige toilet dan yin wanka, a gefen bed ?insa ta zauna dan ta jirasa, ita kanta kirjinta bugawa yake yi da sauri sauri, tana jin tsoron bayyana mashi maganar da ta zo da shi, tasan ba wanda ya tsana biyun Heleena a gidan, baya son ganinta sam, tana fargabar yadda zasu kwashe da shi, ita ma kenan da yake matu?ar kauna yake kuma jin maganarta, ina ga ace uncle ?in nasa ne zai yi mashi maganar, me kuke tunanin zai faru?.
After 40 mins
Bathrobe ce a jikinsa fara tas ya fito daga toilet ?in, da yake tsakanin in da bed ?insa take da toilet ?in akwai nisa saboda girman bedroom ?in, sai bai san tana cikin ?akin ba, ya yi zaton tana parlourn, duk da ta san password na bu?e kofar room ?in nasa dan ba iya fingerprint bane kawai da kofar, zaka iya bu?ewa da password ma, duk da yasan tasan password ?in bai yi tunanin zata biyo bayan shi ba.
Dressing room ya shiga daga toilet ?in, girman room ?in nan ba'a magana, gaba?aya show glasses, transferred glasses su ne cike a ciki, kowani irin kaya da glass wardrobe ?insa, daga waje kana iya ganin duk wasu kayan da suke ciki kowanne, ba sai ka sha wahalar neman in da ma'ajiyinsu take ba, part na set ?in takalma daba, abubuwa dai sai wanda ya gani.
Shiri ya yi cikin denim short mai bala'in tsada, and white single, da alama kwanciya zai yi. Ya zuba wani ha?a??en perfume ?insa mai kamshin kwantar da hankali a jikinsa.
Cikin room ?in ya nufa bayan ya kammala shirin nasa. He was so surprised ganinta da ya yi a zaune a bakin bed ?in.
?an kara cukule fuska ya yi, dan yasan takura mashi kawai ta zo yi.
Ganin ya kara cukulewa yasa ta saki murmushi tana binsa da kallo from down to up.
Haye gadon ya yi da nufin ya kwanta, cikin sanyin murya ya ce. "Mom what are you doing here again?". Ya yi maganar yana sauke kansa a saman lallausan pillownsa.
Juyowa ta yi garesa da kyau, cikin sigar rarrashi da lalla?a mutum ta fara magana. "My baby please come and greet ur uncle and ur aunty, i will be happy if you do thet". A marairace ta kai karshen maganar.
Yana cigaba da cukule fuska ya ce. "Mom i want to sleep, because am feeling to much of sleeping, if they're here, they haven't left, by the time I wake up we should say hello". Yana kai karshen maganar yaja katuwar lallausan duv ?insa ya rufe harda face ?insa gaba?aya dan ma tasan da gaske barcin yake ji....... Smart wato idan kun lura shi fa jan ajin nan kamar a jininsa take, komai sai ya ja aji a kanta kafin ya aikata kamar ba gobe.
Mi?ewa tsaye ta yi, sam bata ji da?in hakan ba, amma kuma farincikin ?anta yafi mata komai, wannan barcin da ya ce yake ji to ya yi sa ya fi mata auren ma gaba?aya, tana kaunarsa sosai.
Parlourn ta iskosu suna zaune, hakuri ta shiga basu tare da gaya masu cewa ai ya dawo a gajiye ne shiyasa, yanzu ma haka ya yi barci, su yi hakuri sai ya tashi.
Baban Heleenar ne ya nuna ?acin ransa a kan hakan, ya ce dan Smart ?in yaga Heleena tana haukar sonsa ne zai na yi wa mutane wala?ancin? To su wlh sun ma fasa ba zasu ha?a wannan aure ba.
Nan fa Heleena dake zaune tana cikin wani irin tantirin shiga nasu na turawa ta fara fa?in wlh baban nata bai isa ba, ita Smart take so, shi take son yin rayuwa da shi, dan haka dole su jirashi kuma su yi duk abin da yake so, bata son ma su ?ata mashi rai....... Idan kana raye dai babu abin da ba zaka gani ba, kuma su fa hakan a wajensu normal ne ?a tasa iyayenta dole su nema mata soyayyar wadda take so, su kuma kaunar ?a?an nasu ne yake rufe masu idanu ya kaisu ga halaka.
Hakuri mom ta basu a in da ta ce musu shi fa Smart bai ma san Heleena tana son shi ba, infact bai ma san me ya kawosu gidan a yanzu ba, dan haka su bi a hankali, gaya mashi batun auren ma sai an bishi a hankali.
Ta?e baki baban Heleenar ya yi, yana mamakin irin son da suke yi wa ?an nan nasu, shi baya laifi, komai ya yi daidai ne, ita kuwa mum Heleenar bata ji komai ba, ita burinta yarta ta samu abin da take muradi.
Haka suka yi ta zaman jiransa har barci ya ?auki mum Heleenar. Dad kuwa shi ne bai dawo ba sai can da yamma, shi ma a tare da manya manyan bakinsa ya dawo.
Mom ta sha mamakin ganinsa da baki, har ?asa hakuri ta yi sai da ta tambayesa wa?an nan kuma daga ina? Taga mace da namiji masu kama ?aya, kuma ga dukkan alamu dangin gidan sarauta ce, sarauta ma mai karfin iko duba da yanayin shigarsu, sun ha?u sosai, da alama ma?udan dukiya ta yi masu mubaya'a, domin kuwa sun ji?u da dukiya ba ka?an ba, shi namijin ma takalmar sarauta dake kafarsa ta zallar madarar gold ce.
Shi ma dad he was so surprised na ganin iyayen Heleena a gidan nasu, da izinin mom kenan suka iya ketowa cikin gidan, dan babu wanda ya isa ya keta arearsu ba tare da izinin ?aya daga cikinsu ba bare har ya iya shigowa cikin gidan, koda kuwa securitys ?in sun san kasan mutumin to fa dole sai ka sanar da su zai zo zasu bashi hanya bayan sun gama cajesa in and out tsab!.
Gaisawa suka yi cikin mutunci da mutunta juna, sannan ya wuce izuwa sama bayan ya damka amanar bakin da ya zo da su a hannun mom ta kula mashi dasu bari ya duba Smart sai ya yi wanka ya zo su tattauna.
Lokacin da ya shiga ?akin ?an nasa barci ya iskosa yake yi, har lokacin bai farka ba, a hankali ya lalla?a kamar wani ?arawo ya fito waje, wai duk dan kada ya tashesa daga barcin.
Nasa room ?in ya nufa, a nutse ya yi wanka, ya shirya cikin hoodie, kyakkyawa ne dad ?in nan fa sosai.
?asa ya sauko, a lokacin already mom ta sa masu aiki sun tashi kan bakin dad da kayan abinci masu rai da lafiya, president food ma ta sa suka shirya masu, wato irin abincin da dad ?in yake ci, na gaya maku mom mutuniyar kirkice mai zuciyar zinari, musulunta ne dai har yanzu taki yarda ta yi.
A rest parlourn suka ha?u dukkansu bayan bakin sun gama kwasan abinci daidai gwargwado.
A nan dad ya ce da bakin nasa su zo ayi magana, da yake ita ma mom tana son su yi magana da shi da iyayen Heleena sai ta ce duk su ha?u a rest parlourn kawai. A cikin bappan parlourn wannan rest parlourn yake, ya ji komai na more rayuwa, waje ne da suke yawan zama dan hutawa ko su tattauna abubuwa masu mahimmanci.
Saman sofa suka zazzauna, a nan dad ya gabatarwa da Mom bakin nasa, ya nuna namiji tare da ce mata shi ne Prince mai jiran gado na ?asar England, macen kuma babar yayarsu ce, kara gaisawa suka yi cikin mutumci.
?arawa dad ya yi da cewa. "Prince they came for the issue of their sister's marriage which they are asking for Smart to do, saying that the girl is determined that she want him to marry her or she will kills herself".
Prince sun zo ne a kan maganar auren sistersu da suke son Smart ya yi, wai yarinyar ta ce tana son ya aureta ko ta kashe kanta.
______________ Ai tun dad bai kai karshen maganar ba Heleena ta mi?e a zabure.
Su mom kuwa binsa da idanu suka yi tun da ya fara jawabi suna jiran ya direta.
Cikin tsawa Heleena ta ce wlh bata ga ?ar iskar da ta isa ta ce tana son Smart ba, dan ita ka?ai aka yi shi, wlh mace ko da wuta take tafiya a jikinta bata isa ta ce zata aure shi ba, tafi karfin yarinta sai dai uwar yarinyan ita, ba sarauta suke takama da shi ba, ko uban sarauta ne basu isa ba.
Tashin sense! To fa, nan fa kallon kallo ya koma a parlon, shi dai dad bai ta?a sanin wannan zancen na son da Heleenar ke yi ?an nasa ba, yau ake yinta, Heleena zata taro mach, kishi da ?ar sarki, to ni dai ina daga gefe ni da Smart bamu san komai ba.
Yau ga ikon god, ha?a??un chikun turawa masu kama da ?an tsana suna fa?a a kan Smart namu na amana, shi da bai ma san me ake ciki ba, ni kam princess Teema na ce duk mai son Smart a cikinsu to ta musulunta ko ba haka ba my people's? Idan ta musulunta da ni da ku my people's zamu tayasu gaya mashi ko? Har ma tayasu shawo kansa zamuyi, duk tsaurin nan nasa tsab zamu jure mu sadaukar da rayukanmu mu tayasu neman soyayyarsa ba sai sun yi fa?a ba, su kar?i kalmar shahada kawai su ga ikon god!! Ko ya kuka ce???
Dad kam bin Heleena da ido ya yi, ta wani tsaya a tsakiyar mutane tana huci kamar wata zakanya. Mom ce ta ce mata ta kwantar da hankalinta Smart nata ne ita ka?ai.
Nan fa ta dakawa mom ?in ma tsawa wai ta kyaleta, yau sai taga waye uban yarinyar da aka kawota talla wajen Smart ?inta. Kun ji mun karfin halin irin na Heleena, wai an kawo yariya tallah, sai kace ita ma ba tallar kanta take yi ba, abin takaicin ma wajen wanda sam bai san suna yi ba, hasalima tsoronsa take ji ?ar ?aniya, rashin kunyar tata mom and dad kawai take yi wa.