Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 62
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 62: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 62. Yana kai karshen surfa masifar tasa ya ja hannunta suka koma cikin hall ?in.
3,349 words
Yana kai karshen surfa masifar tasa ya ja hannunta suka koma cikin hall ?in.
Ba zaka ta?a fahimtar a wani irin hali Hoorain yake ciki ba, bakinciki ne ko farinciki ne Allah masani, cikin takun jarumta ya bi bayansu izuwa cikin hall ?in, suna tafiya tana juyowa ta kallesa, har suka shige ciki.
Ko da suka shiga cikin ma idanunta na'a kansa, shi kuwa gani take yi baya kallonta, alhalin kallonta sosai yake yi kamar zai cinyeta da ido.
Sai gudanar da party ake yi cikin tsantsar girma, harkar ta manya ce. Ba Chuchu ba Jawad a wajen.
_______________________????
A hankali ya furta. "Ke dai Jannat kin cika tsoro, jibi yadda eyelashes ?inki suke ?ari kamar ba lafiya ba?".
"Ni Yah Jawad yanzu budurwarka kawai nake son gani". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.
Raba face ?in nasu ya yi yana sauke ajiyar zuciya, idan bai nuna mata kanta ba ba zata barshi ya sarara ba, kai mata kishinsu sai su.
"Tashi mu je in kaiki in da take".
Da sauri ta waro idanun tare da sauka daga jikinsa, sai dai kuma ta ?aure fuska sosai, sai kunkuni take yi ciki ciki wadda ba zaka iya jin me take fa?a ba, da alama tsinewa budurwar tasa ma take yi.
Mi?ewa shi ma ya yi, sarai ya lura da kunkunin da take yi, ta wani cunkushe rai, ta ha?e jeran sama da na ?asa, bai ce mata uppan ba.
Tafukan hannayensa ya kai ya rufe mata idanunta da su, a hankali ya ce. "Let's go".
Fara tafiya ta yi tana fa?in. "Yah Jawad to sai anrufe mun idanu ne za'a nuna mun ita?".
"Yeah, saboda ita ?in special ce da babu irinta a duniya, dole na rufe maki idanu, a gabanta zan bu?e maki idanun naki sai ki fara yin tozali da kyakkyawar face ?inta".
Shiru ta ?an yi suna cigaba da tafiya. Can kuma ko me ta tuna sai ta ce. "Wlh nama san mummuna ce budurwar taka, duk yadda aka yi kanta ?ato ne".
Yana jinta dai bai tanka ba. Gaban mirror dake cikin office ?in ya dakata.
"Get ready". Ya fa?i hakan a saitin kunnenta na dama.
"Ni a shiryena nake". Da alama ranta a ?ace ta yi maganar.
"Gaskiya beb ?in ta kyakkyawa ce sosai Jannat? Ki shirya wanke idanunki da kyanta yau, dan nasan da wuya yau ki yi barci matu?ar kin ganta".
"Wlh nama tsani ganinta, ni Yah Jawad na fasa ganin nata sakeni na koma office ?inka". Tana kai karshen maganar tana ?o?arin juyawa har da ?an ture shi.
Da ?an kasasa murya ya ce. "Ki nutsu!".
Ba dan taso ba ta dakata tare da nutsuwa tsit.
A hankali ya zame hannunsa daga saman idanun nata, cikin zumu?i da son ganin wacece mummuna ce budurwar tasa ta waro idanunta.
Subhanallah zaro ido ta yi, she was shocked and so surprised na ganin kanta kuma, hannu ta kai saman face ?inta a fujaje ta fara murje idanunta dan ta tabbatarwa da kanta abin da take gani.
Ganin da gaske fa ita ?in ce yasa ta kai kallonta a kansa ta cikin mirror, cool murmushin da ya sakar mata ne yasa ta tabbatar da gaske ne.
Tafukan hannayenta tasa ta rufe fuskar tata tana sakin cool murmushin da bata ta?a yin irinsa ba....... Ni kuwa nace Chuchu ban da cin amana, shi kuma Yah Rizwan ?in ina zaki kaisa dan gidanku?.
Hannunsa ya sanyo ta saman shoulders ?inta, a hankali ya ri?o hannayenta dake saman fuskar ?in tata, janyesu ya fara ?o?arin yi dan ya samu damar ganinta da kyau.
Juyowa ta yi ta fa?a jikinsa tana dariyar da sautinsa yake fita a hankali hankali, wani irin kunyarsa ta ji ya kamata, kenan yanzu duk zagin budurwar nan tasa da ta rin?a yi kanta ta zaga? Ta manta da zancen Yah Rizwan ta wani shige jikinsa.
Rungumeta shi ma ya yi, cikin wata iriyar sigar soyayya dake fusgarsa ya fara zuba mata uban tulin kamalan da ya tarasu a cikin ransa na tsawon shekaru, yadda yake magana sai kaji kai ma ka kamu da kaunarsa. Cikin sanyin murya ga magana one by one ya fara fa?in............
Ba dai zasu ji me ya fa?a yau ba sai gobe?????? su maman Yasmin, Mumcy, Sumy sarakan gulma da sauran my comments section grp in kunji babu da?i ina gidanmu kuzo ku sameni?? ba za dai ku ji wasu irin kalamai zai kashe Jannat ?insa da su ba??
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 1/11/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
E33
Rungumeta shi ma ya yi, cikin wata iriyar sigar soyayya dake fusgarsa ya fara zuba mata uban tulin kamalan da ya tarasu a cikin ransa na tsawon shekaru, yadda yake magana sai kaji kai ma ka kamu da kaunarsa. Cikin sanyin murya ga magana one by one ya fara fa?in.
"My Jannat i don't know how can i tell you the way i love you, your love has been in my heart for a long time, it melted and made me feel the lump inside my heart, no person in this world that can remove it, is something that will never be possible, unless i will die with it, your love has melted and mixed with the blood that circulates in my body, know that every beat of my breath is beating with your name, a kowace rana na kwanta ?ayan biyu ne, dole sai na yi mafarkinki ko kuma tunaninki ya hanani barci, zuciyata ta jima tana azalzata a kan lallai na isar da sa?onta a gareki, please tell me with your mouth, I want to hear the sound of your sweet voice when you say that you love me?". He asked the question full of fear of the answer she would give him, even though he knew that she will love him, but he found himself afraid of what would come out from her mouth in this moment.
"Yah Jawad, I can't talk right now, leave it until after some hours, I can't tell you what kind of situation I'm in right now, just leave me alone". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.
"Na ji zan barki, amma har sai kin furta mun abin da nake son ji, ko dai kina son in shiga tashin hankali ne?".
Kai ta fara girgizawa alama a'a bata so.
"Okey to ki gaya mun, kina sona?".
A shagwa?e ta ce. "Yah Jawad ni bana sonka, ina da wanda nakeso, sai dai ba shakka na ji da?in sona da kake yi, kada ka damu idan na yi aure na haifi yaro namiji zan saka mashi sunanka, kaga kenan na baka cukuicin son da ka yi mun ko?". Ta kai karshen maganar with full confidence a voice ?inta, yadda kuka san da gaske take yi.
Ai a fujaje ya sauko da kansa a kanta yana ?o?arin raba jikinsu dan ya kalli face ?inta da kyau.
?ara ?an?ameshi ta yi, taki bari ya raba jikin nasu, ta ?ara kwantar da kanta a saman kirjin nasa luff. Wani irin bugu da ta ji kirjinsa na yi da sauri sauri ne yasa ta yi hanzari ?ago da kanta ba dan ta so ba, a tsorace ta kai kallonta kan face ?insa.
Wani irin razana ta yi na ganin a take har kalar idanunsa sun sauya, lallai da ita ce ta yi ta mashi irin wasa da hankali da ya rin?a yi mata ?azun na yana da budurwa ashe da zuciyarsa zata buga, ha?i?a ta yarda ba karamin so yake yi mata ba.
"Yah Jawad ka yi hakuri ka ji, ni idan ban soka ba waye kake tunanin ni Jannat zan so? Dole kai ne mana". A shagwa?e sosai ta yi maganar, tana kai karshe kuma ta mayar da kanta saman chest ?in nasa ta kwanta.
Wani irin dogon ha?a??en numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, ?asa ?asa tamkar zai yi kuka kamar kuma mai ra?a ya furta. "Kin gama yi mun komai my Jannat, ban san da me zan biyaki ba, tun bayan da na yi wayo nasan cewa a duniya bani da mahaifiya, tun daga lokacin farinciki kaso hamsin da biyar cikin ?ari na rayuwata babu shi, ina rayuwa ce bisa farincikin cewa ina son Allah da Manzonsa, bayan haka sai farincikin sanin cewa ga family na, amma a yau ina da farinciki kaso tamanin cikin ?ari saboda ke, i really love you...........".
Shiru ya yi sakamakon hannunta da ta ?aura a saman face ?insa tana lalu?ar lips ?insa, so take yi ta ce ya yi shiru, kalamansa suna neman fasa mata kai, ru?ar da ita kam sun jima da yi.
?asa ?asa da wata iriyar murya wadda za'a iya kiranta da raunatatcen murya ya furta sunanta. "Jannat". yau cikin wani irin tsantsar farincikin da yake ciki har wani kyalli face ?insa ta fara yi, baki ya yi ka?an ha zayyana yadda yake ji a yau, kawai ga shi nan ne.
Ita kanta baki ba zai iya zayyana abin da take ji a kansa ba, kamar yadda yake kaunarta ita ma haka Allah ya sanya mata matu?ar kaunarsa a ranta sosai.
Shiru ya yi tamkar mai tunanin wani abin, kamar a mafarki ya ji sau?ar hawayenta mai ?umin gaske a jikinsa, hakan ya ja ya yi hanzarin ?ago da ha?arta tare da ?an raba jikinsu.
"Subhanallah Jannat menene ya faru kike kuka a maimaikon farinciki kuma?". A ru?e ya yi maganar, ta ?aga hankalinsa ne sosai kukan nata.
"Yah Jawad ni ma ban san meyasa nake hawayen ba, kawai zuba yake yi, ina matu?ar murna da farinciki, yau burina ya cika, ina sonka Yah Jawad, ina sonka sosai, ban ma san ya zan gaya maka ba, kawai ka barni na cigaba da yin kukana ko zan samu sassaucin abin da nake ji a raina".
"No Jamnat, ba kuka zaki yi ba, addu'a zaki yi mana tare da godiya ga Allah kin ji?".
Kai kawai ta gya?a mashi, handkerchief ya ciro, wanda ya goge mata hawaye a gida kafin su zo ne, da shi ya sake goge mata hawayen a yanzu ma.
Komawa jikinsa ta yi ta kwanta shiru tana mai matu?ar farinciki sosai yau, da alama ta mance da cewa suna soyayya da Yah Rizwan.
Shi kuwa Yah Rizwan bawan Allah kayan make up ya je saya mata a shopping, dan a ?an zaman shi da ita ya fahimci akwai abubuwa da dama da take balai'n so wanda bai saya mata a cikin tsarabarta ba, dalilin zuwansa shopping kenan yau.
Yana yi yana jin fa?uwar gaba, hankalinsa ya gaza kwanciya har sai da ya kira number Jawad ?in, yana son ya ji ko yana lafiya, saboda idan baku manta ba dama yana zargin bashi da lafiya kafin ya fita daga office ?in nasa, so sai ya ta'allaka fa?uwar gabar nasa da ?an kanin nasa abin soyuwa a garesa............. Ni kam nace baka san amanarka suke ci ba, soyayya ?an kanin naka yake zubawa da matar da kake burin aura, wlh wani tsiyar sai a RAWANIN ZALINCIN.....??
A lokacin da kiran ta shigo suna manne da juna yana ta zuba mata kalaman da suke sanya ta kuka sosai kamar ?aramar yarinya, yana sake aikin goge mata hawayen kuma.
Jin wayarsa tana ringin ne yasa ya ambaci sunanta a hankali.
?ago kai ta yi tare da kai kallonta kansa. Wani irin sar?afewa idanunsu suka yi cikin na juna, yau burinsa ya cika, wani irin kallo yake binta da shi mai wuyar fassaruwa, ji yake yi idan bai mayar da ita cikin cikinsa ba ba zai samu nutsuwa ba, yana yi mata wani irin soyayya wanda bai san iyakarta ba....... E lallai soyayyarku daga Allah ne mutanennan.
Shigowar call na biyu ne yasa suka ?an farga da kallon juna da suke yi, da sun macewa juna basa gane komai.
Juyo da ita ya yi suna fuskantar mirror. ?asa ta yi da kai, sai yanzu ta ji ba zata iya ha?a idanu da shi ba. ?ayatatcen murmushi ya sakar mata tare da ?an rage tsawonsa ya sureta sai saman shoulder ?insa, luf ta kwanta tana wani irin jin da?i na musamman.
Wajen table ?in suka koma, zama ya yi da ita a jikinsa, a saman cinyarsa ya ?aurata, sannan ya ?auko wayar tasa dake ta rurin neman agaji, Yah Rizwan ya gaza samun kwanciyar hankali shi ne yake ta kiransa.
Dai'daita nutsuwarsa ya yi tare da gyara voice ?insa, sannan ya yi picking. Daga ta cikin wayar yana iya jiyo sautin wani irin ajiyar zuciya da ?an uwan nasa ya sauke alamar ya ji matu?ar da?in ?aga call ?in da ya yi.
"Yah Rizwan lafiya kuwa?". Ya jefa mashi tambayar idanuwansa suna a kanta babu ko kyaftawa, ta wani yi ?asa da kai kamar mai ?aukar darasi gaban malami.
"Lafiya lou, kawai kewarka na yi ne yasa na kiraka, hope kana normal cikin amincin Allah?".
"Da izinin Allahn ina cikin amincinsa kuma ina cikin ?oshin lafiya fatan ?an uwana ma hakan ne?". Yadda ya yi maganar zaku fahimci ba shakka suna masifar kaunar juna.
"Da izinin Allah nima ina nan cikin ?oshin lafiya, ka kula mun da kanka ka ji?".
Gya?a kai ya yi tamkar yana a gabansa, sannan ya ce. "In Sha Allah ?an uwana, kai ma ka kula mana da kanka, muna kaunarka sosai, kana da mahimmanci over a cikin rayuwarmu".
Murmushin kawai ya saki. "Sai mun ha?u a gida ko?".
Okey ya amsa da shi tare da ciro wayar daga kunnensa. Kit Rizwan ya katse kiran tare da dakatawa da za?ar kayan da yake aikin yi, tunani ya fara yi a kan to wai meyake faruwa ne yake jin irin wannan fa?uwar gaba? Shi dai yasan a kan Jawad ?in kawai yake fuskantar irin wannan fa?uwar gaba, amma ya aka yi yau Jawad yana cikin amincin Allah da ?oshin lafiya amma still yake jin fa?uwar gabar nan?.
Abin ya bashi mamaki matuka, sai kuma ya fara tunanin bai ta?a jin voice ?in ?an uwan nan nasa cikin tsantsan farinciki haka ba, amma bai kawo komai a ransa ba, ya cigaba da ?aukar kayayyakin da yake da bu?ata, sai dai kuma ya zama wani sukuku da shi saboda rashin samun kuzari da kwanciyar hankali, wannan fa?uwar gabar ta haifar mashi da kasala sosai. Kada ku manta dama tun zuwansa office ?in yake zargin Jawad ?in, shei?an kuma da shegen son ha?a bomb sai ya ?ara ingiza zuciyarsa!.
Shi kam Yah Jawad cigaba da zibewa juna madarar kalaman soyayya suka rin?a yi, tamkar zasu cinye juna da hira.
Sai around karfe 11 Momma ta kirasa a waya dan ya tambayesa ina Jannat?. Dan tasan shi ne wanda ta gani last a tare da Jannat ?in, wato da safe kenan, kunga a tare ta barosu a kofar room ?in.
Yana picking ta fara fa?in. "Meyasa ka fita da Jannat?".
"Sorry our Momma". "Sorry for what? Kadai san idan daddynku ya ji labari ba zai ji da?in hakan ba ko?".
Sake ce mata sorryn nan dai ya yi. Shiru ta ?a yi kafin ta ce to su dawo da wuri ba sai sun kai lokacin da yake dawowa ba, dan kada kowa ya farga cewa Chuchun bata gidan.
Da okey ya amsa mata. Amma sai misalin karfe 8 na dare suka koma, ya biyewa Chuchun suka zauna sai hira suke yi manne da juna, bai fargaba sai gani ya yi karfe 8 ta yi, ko sallar mangariba ba su yi ba, hankalinsa ya tashi sosai, tunanin yadda zasu kwashe da Momma ya fara yi, a ransa ya ce ai ina yau ba zai je part ?inta ba.
Ko da suka komo gida har angama walimar jama'a sun watse, an sha kyaututtuka na girma kam ba'a magana.
Part ?insa ya wuce da sauri dan kada ma Momma ta kama shi, ita kuma Chuchun part ?in Momma ta wuce. Tun da yamma mummynta take nemanta, ta ?aga hankalinta sosai har sai da Momma ta ce ai ta aikesu ita da Jawad, sannan ne ta samu natsuwa.
Da yake da Momma ta saba tana dawowa bata nemi kowa ba ta wuce wajen Auta dan ta fa?a mata yau Yah Jawad ya ce yana sonta, kun san dai ita da Auta hanta ne da jini, ba'a rabasu.
Ko da Momma ta ganta bata ce mata ko uppan ba, dama dai saboda tsaro ne yasa take yawan yi masu magana. Wanka ta tsara tare da tsala kwalliya, ?akin Auta ta nufa domin su ga juna daga nan su je wajen mummynta.
Kwance ta iskota tana latsa waya, da alama tana cikin farinciki sosai, dan sai sakin murmushi take yi wanda yake ?ara mata kyau sosai, dimples ?inta suna lotsawa, duk yadda aka yi chatting take yi da wanda yake sanyata farinciki.
Hayewa saman gadon ta yi tana kaiwa Autar duka a baya.
A fujaje ta ?an ?ago kai, ganin ita ce yasa ta ?an turo baki. "Kai Aunty Chuchu sai yanzu Yah Jawad ?in ya dawo mun dake?".
"Ke duk ba wannan ba, zo ki rakani wajen mummy idan mun dawo sai na baki labarin abin da ya faru yau".
"A'a Aunty Chuchu ni babu in da zanje, ki je kawai, yanzu ma ni wajen uncle Jahiz zan je, ya ce idan na yi sallar mangariba na zo, kin ga kuma lokacin sallah saura ?an mintocin da basu fi 15 ba". Ta kai karshen maganar tana mi?ewa zaune.
"To shikenan jeki, ni ma dai zan je duba uncle Abbas, dan bamu gaisa ba yau, idan mun yi sallar isha'i mu ha?u a part ?in Akka".
Da okey ta amsa mata, a tare suka fito waje, ita ta nufi part ?in mummynta, Auta kuma ta nufi part ?in uncle Jahiz kamar yadda ta fa?a, sai dai kuma ba can ?in ta je ba, hanyar baya na sirri ta je dubawa, hanya take nema ta yadda zata fita da daddare idan kafa ta ?auke, ko ina zata je?.
After some hours. Bayan sun yi sallah sun ci abinci, kowa ya wuce part ?insa. Room nata da yake part ?in Akka ta nufa, dan ta ce su ha?u da Auta a wajen.
Wayarta ta ?auko suka fara chatting da Yah Rizwan ?in da bata san matsayinsa a gareta ba yanzu, tabbas bata dai'na jin sonsa a ranta har yanzu.... E akwai cakwakiya kam.
Ita kuwa Aura fitowa ta yi daga nata room ?in, kayan barci wando da riga launin pink ce a jikinta, kayan sun yi mata kyau, ta sanya hular barci a kanta.
Kamar wata maras gaskiya haka ta wuce ta fara san?o, tana yi tana juyowa. Karaf suka ci karo da uncle Taheer da ya fito daga wajen King zai koma part ?insa.
Wani irin zabura ta yi, a take ta yi ?asa da kai, rashin gaskiya ce zalla ta bayyana a tattare da ita.
"Baby ina zaki je kike tafiya haka kina waige waige kamar maras gaskiya?". Ya yi magana yana bin bayanta da kallo ko zai ga mai biyota da yasa take irin wannan waige waigen.
Babu kowa da yake zuwa.
Murya na sar?afewa ta ce. "Wajen dad zan je".
?an zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda ta yi wa kayan barcin nata kyau matu?a.
"Uncle Taheer in tafi?".
Ya shagala da kallonta ne muryarta ya daki dodan kunnensa. Kai kawai ya gya?a mata alamar e. A hanzarce ta wuce har kamar zata kifa ?asa saboda sauri.
Da kallo ya bita, sai faman waigowa take yi, duk in ta waigo sai su ha?a idanu, dan yana tsaye yana kallonta, dan dole ta shiga part ?in dad ba dan nan zata je ba, sai dan bata da za?i yana tsaye yana kallonta.
La?ewa ta yi a bakin kofar ta ciki tana le?arsa har sai da taga tafiyarsa, sannan ta fito da sauri ta nufi kofar bayan.