Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 64

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 64

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 64: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 64. Wato da Hausa cewa ya yi. Bana sonta dan uwana, kawai ina tausaya mata ne,…

3,243 words

Wato da Hausa cewa ya yi. Bana sonta dan uwana, kawai ina tausaya mata ne, kuma a cikin zuciyata nake ji kamar kanwata ce. Yaya ka yi hakuri ka barmu a tare da ita.

Shi ne maganar da ya fa?a ta ?arshe, daga haka wannan mutumi ya riki?e ya koma haskensa kamar yadda ya shigo tun farko, waje ya nufa ba tare da ya sake yin yunkurin wani abin ba.

Yana fita ita ma kujerar da ya zauna a kanta ta ?ace ?at!.

Kifa kai a saman mattress ?insa ya yi tare da sanya hannu ya fara dukan jikin mattress ?in kamar wanda bashi da cikakken hankali.

Da karfi ya furta. "Why nae hyeong?". Wato meyasa ?an uwana?.

Wato dai Black Tiger yaki sauraronsa a kan batun Sweetie, ya ce mashi ya mance da ita a rayuwarsa tamkar bai ta?a saninta ba, domin kuwa in dai bata basu Spender ba babu abin zai hanashi kasheta already ya rigada ya da san haka, so ya daina wahalar da kansa a banza, dan yasan dai shi bai ta?a ?udurta yin abu kuma ya janye ba, so ya kiyaye!.

A can waje kuwa, bayan Master Devil ya isar da wa?an nan Robbot ?in wajen da ya dace da su, sai ya koma bakin aikinsa, ba ko'ina bane bakin aikin nasa ba face azabtar da ?a?an mutane, to mu je dai mu gani me ake ciki.

TRAINING HALL????

Shi ne sunan da aka rubuta a jikin katafaren gate ?in shiga wajen, duk a cikin empeir ?in yake, yana ta kusa da wajen buga basket ball ?in su Ronnie.

Katafaren waje ne yadda kuka san stadium na kwallon, duk wasu kayan training na ?an Wrestling da maya?a akwaisu a wajen.

Yadda kuka san kung fu place, haka wajen yake, yara ne birjik a wajen, matasa ne masu ji da rai da lafiya wa?an da daga 20 years ya yi sama side ?insu daban, akwai masu daga 30 years up, daga masu shekaru 40 suka tsaya, Black Tiger baya sanya wa?an da suka haura 40 a sahun warriors ?insa, daga 40 ya yi ?asa yake shiryawa a cikin dakarun yakinsa.

Duk wanda ka ?aga idanun ka gani a wajen sai ka razana, master ya iya bada horo, sun horu kam ba karya. Sun cika zakarun maya?a

Daga wani waje mai girman gaske, sannan wajen yana ke?ene, yara ne ?anana a wajen wanda a kallah zasu kai su 100, dukkansu babu wanda ya haura 10, sai dai kuma babu wanda yake da ?asa da 5 years.

Mafiya yawa daga cikinsu idan kaga fuskokinsu sai ka zubdar masu kwallah, dan dayawansu busassun hawaye ne a kan fuskokinsu, idanu sun yi jajir, wasu ma idanun sun kumbura saboda kuka. Bayin Allah basu saba ba, dama idan baku manta ba shi Black Tiger idan kika haifo ?a namiji a cikin birnin ko wani shayar da shi ba za'a bari ki yi ba za'a kar?esa.

Allah sarki su yara ba wani samun nonon uwa suke yi ba, ga bakar horo tun suna ?an shekaru uku a duniya ake fara lallankwashe masu ?asusuwar jiki kamar wasu ?a?an Chinawa, tun suna ihun neman taimako har su ha?ura su fawwalawa Allah komai, har su zo su saba, suna tasowa suna tashi da wannan horo a jikinsu, da zarar sun kai 15 years fa to wlh duk ranar da basu yi training ?in bama basa jin da?i, duk sai su ji duniyar babu da?i.

Haka zasu taso babu tausayin uwa bare na uba, ko iyayensu sun zo ganinsu basa jin kamar iyayensu ne ma, saboda basu saba da su ba, master shi ne zai zama kamar iyayensu, sai sun fi tausayinsa fiye da yadda zasu ji na iyayensu, wani ma idan horon ta ratsa shi wlh da za'a bashi izini ya yi wa iyayensa wani abin tsab zai yi masu, gara ma iyayensu mata, ko yaya suna jin iyayensu mata a ransu ba kamar maza ba, uwa ko bata shayar ba ta wuce wasa, ita soyayyarta a jini yake, abin ya wuci tunaninku.

Haka dai suke tasowa, wani ko ance mashi ga mamarsa ta zo ganinsa kai tsaye zaku ji ya ce bashi da lokaci yana training ko yana yin wani abin makamancin haka. Wannan shi ne babban cuta kuma babban tabo da ya yi wa mutanen birnin da bazasu ta?a mancewa da shi ba a rayuwarsu, ya cuta masu matu?a, raba uwa da ?a wlh ba wasa ba, zunubinsa daban ne, kina ji kina gani ki haifi yaron, kuma kuna waje guda da shi amma baki da iko da shi, sai dai ya bi tsarin wani, ko ganinsa zaki yi sai da izini, wani lokaci ma ace ki tafi yana aiki ki dawo anjuma ko gobe, abin da matu?ar takaici na wuce misali ga ban tausayi da ta?a zuciya!.

Abin dai babu da?i sam, Black Tiger ya kai azzalumi ta wannan ?angaren kam, ba karya yana cutar da iyaye da dama, wani irin fargaba da balai'n tsoro mutanen birnin suke yi na su haifo ?a namiji. Kai har ta kai ta kawo idan mace ta fahimci tana da ciki, tun daga ranar da ta san da cikin tana cikin tashin hankali da fargaba ga azababben tsoro, kullum haka zata kasance cikin addu'ar Allah yasa mace zata haifa ba namiji ba, ba wai dan basa son ?a?a maza ba, dan dole yasa suka tsanesu, dolen dole aka cusa masu tsanar maza, dan dole suka koyi addu'ar idan ?a namiji ne a cikin cikin nasu to gara cikin ya zube kafin su haifesa, ko kuma idan sun haifo najimi ya mutu a lokacin da ya fa?o duniya!.

Kun san uwa da ?a, da a rabata da shi a turasa yaki gara mata ya mutu ko kuma cikin ya zube tun ba'a je ko ina ba.

Sai dai kuma kash gaba?aya mutanen birnin sun fi haifar ?a?a maza a kan mata, sai ku tarar mace ?aya zata haifo maza 8 mace 1, idan ya yi yawa ne ma mata 2, haka suke, sun fi haifar maza, shiyasa Black Tiger yake alfahari da su, yake kuma da tarin gayyar warriors and ?an Wrestling masu ?ebe masa kewa su sanya shi nisha?i.

Wato shi Black Tiger ayi Wrestling a kashe wanda ya fa?i a zubar da jini shi ne yake sanyashi nisha?i, gaskiya yacika azzalumi, da gaske RAWANIN ZALINCIN ce a kansa. (Zan so ganin wanda zai cire wannan RAWANIN ZALINCIN gaskiya akwai bada?ala ba ka?an ba.????)

Wani irin katafaren ruwa ne mai matu?ar zurfi a farfajiyar wajen horon nasu, ruwace mai bala'in sanyi, har da ice a cikinsa. Wasu yara da ba zasu wuce 8 years a duniya ba, tsaye suke a gaban ruwan jikkunansu na kerma, kana ganin face ?insu alamar tashin hankali da firgicice sosai a ?wance.

Idanunsu gaba?aya ya rena fata, a tsananin tsorace suke, fighter uniform ce a jikinsu, yanayin kayan nasu yaso ya yi kama da kayan maya?a, sai dai su nasu hular ta roba ce, and nasu kamar over roll suke, wato a ha?e rigar take da wando suke kamar kayan Spider-Man.

Kowani yaro a jikin hularsa akwai sunansa da sunan babansa complete a rubuce a jiki.

Dukkanninsu sun ri?e hulunar nasu a hannunsu dake ta faman kerma tamkar hulunar zasu fa?i ?asa, babu takalma a kafafunsu, gaba?aya yanayin kamanninsu iri guda ne kamar yadda nace maku mutanen birnin suna kamanceceniya.

Master Devil yana tsaye a gaban ruwan ta ?ayan side ?in suna fuskantar juna da yaran, ya har?e hannayensa a saman wannan bu?a??iyar kirjin nasa, fuskar nan a ?aure tamau, ga wani ?an iskar gashin bakinsa kamar na bunsuru da ya tara, idanunsa jajir kamar jini, bashi da imani ko miskala zarratin.

Da wannan bu?a??iyar fasasshiyar muryar tasa ya fara ?irga from one to three. Yana kaiwa three ko yaro ?aya bai rage a bakin ruwan nan ba, duk wannan firgici da tashin hankali da yake a saman face ?insu bai hanasu yin azaman fa?awa cikin wannan ruwan ba, ji kake zundum sun afka ciki!.

Abin tausayi ba su iya iyo a cikin ruwan ba, sai lumewa ?asa suke yi suna ?ara ?agowa sama, duk in suka lume kuma sai sun sha ruwa sosai kafin su iya ?agowa su sha?i kamshi duniya wato numfashi.

Nan take idanunsu ya ka?a ya yi jajir, sun sha ruwa tamkar cikinsu zai yi bindiga, sun kasa iya yin iyo su kai ba?in ga?a su fita, suna nan a in da suka fa?a basu motsa ba sai ?asa da suke yi suna ?agowa.

Wlh yadda kuka san mutum mutumi ne ba mutum ba haka master yake tsaye yana kallonsu babu ko tausayi bare imani, tamkar karfe ce a kirjinsa ba zuciya ba, yara ?anana haka, ina ma laifin ace manya ne? Ai da da sauki, amma su wa?an nan abinci ma yaushe suka gama iya ci sosai bare wannan horon mayakan, abinci ma har yanzu sai an nuna masu yadda zasu ci da kyau, wasu har yau na tabbata cusa hannunsu a baki dukka suke yi a yayin cin abinci, amma saboda shi master dama sunansa na she?an ne mai gaba?aya babu imani a ransa, shi kuma Black Tiger ina ga ma uban shai?an ne mai gaba?aya a zallar mugunta.

Wani shirgegen katon maya?i ne ya shigo cikin wajen. Kai tsaye in da master yake tsaye ya nufo, yana tafi har wani amshi ?asa take yi.

Sanye yake da kayan warriors a jikinsa, sai dai bai sanya hularsu ba, daga ganin face ?insa kasan ?an cikin birnin ne shi ma, a kallah zai kai 35 years haka.

Kusa da master ya tsaya, cikin dakiya da katon murya kamar engine ni?a ya fara magana kamar haka.

"Na gama bincikena, duk tsawon tarihi ba'a ta?a yin wata masarauta mai ji da karfin iko da jaruman maya?a ba biyun wannan KINGDOM OF POWER, masarauta ce a gaba?aya fa?in ?asar Tunisia babu irinta, kujerace da kowani sarki zai ci burin ?ale kanta, in takaice maka labari ?agun kansu yafi na wannan empeir ?in, suna ji da kansu, King Zuhair shi ne sarkinsu, mutum ne mai kafiya, jajircewa, jarimta, karfin iko, isa, ta?ama, karfin fa?a aji dole, sannan kuma adalin sarki ne, yana kuma da zaratan jaruman ?a?a ha?e da wani bujumin namijin zakin commander maya?ansu mai suna Zafar wanda ya kware wajen sanin duk wasu dabarun yaki, yana da wani yaro guda ?aya mai suna Hoorain, namijin gaske ne mai firgita hantar manya manyan sarakuna wannan yaron, a yadda bincikena ya nuna mun da wuya ko in ce zamu sha bakar wahala kafin mu iya tankwarasu su dawo ?ar?ashin ?afafamun kamar yadda muke yi wa sauran masarautun da suke kawo karfi a idon duniya". Ya kai karshen maganar cikin jarumta babu alamar jin ?ar ko wani fargaba a tattare da shi.

Idan baku manta ba a baya na gaya maku a cewa duk wata masarauta da Black Tiger ya ji labarin suna da karfin iko to fa sai ya san ta yadda ya yi ya shirya dakaru ko ta halin ?a?a su je su yakesu, su kashe sarkin, sannan su kwaso mashi maya?an dake masarautar su kawo mashi master ya ?ara masu horo su zama nasa, yana amfani da karfin sihirinsa wajen control na ?wa?walwar duk wani maya?i da zasu kamo daga wata masarauta, yana juyar masu da kwakwalensu yasa su mancewa da tsohon masarautarsu ya zama nasa kingdom ?in kawai zasu tuna, fatan yanzu kun tuna?.

To a wannan karon kuma idanunsa sun kyalla sun kyallo mashi kingdom of power, ya ji labarin suna da karfin iko fiye da tunaninsa ne yasa a ?ara bincika mashi da kyau, duk da cewa ya ga karfin ikon nasu a cikin ruwan tsafinsa, amma duk da haka yasa aka ?ara bincika mashi dan ?ara tabbatarwa, yanzu a shirinsa kingdom of power zai ya?a, a hakan ma bai san cewa King Zuhair shi ne mamallakin Spender ba, ina ga da ya sani ai da a yau ba sai gobe ba zai ce aje a kifar da su a shafe tarihinsu a doron duniya...... Tashin sense, akwai gwarama wlh ba ka?an ba!.

Amma wani hanzari ba gudu ba, my people's shin kuna ganin a gwabzawar Black Tiger and King Zuhair waye zai yi nasara? Shin Black Tiger zai iya yakar Kingdom of power? Me zai faru a tsakanin wa?an nan masarautu biyu masu ji da balai'n karfin iko dukkansu? Ga Queen Zarina a gefe! Sai dai Black Tiger ya fisu arziki nesa ba kusa ba, bazama a ha?a ba, su kuma sun fishi kwararrun dangerous warriors masu lafiya renon Commander Zafar, shi kuma ya fisu da Robbot masu ha?ari, sun fishi da ayar Allah, shi kuma karfin tsafi, ya kuke tunanin wannan wasa zata kaya? Su waye masu nasara? Daga karshe waye zai kasance mammallakin Spender? Akwai gagarumin cakwakiya, masarautu uku zasu fara farautar junansu kamar hauka, dan kun dai san King Zuhair ba zai kyale Queen Zarina harin da ta kawo masu ya tafi a banza ta ci bulus ba, ta ?etare iyakokin yaki, a dokikin yaki yanzu suna da damar mayar mata da martani dan ta ketare iyakarta, akwai tashin hankali.

King Zuhair zai yaki Queen Zarina, shi kuma Black Tiger zai yaki King Zuhair, su kuma turawan yamma suna shirin ya?ar Black Tiger ?in dan su kwashe mashi arzikin Daula, shin ya kuke tunanin wannan game ?in zata kaya? Ya kuka hango wannan cakwakiya? Muje zuwa, yanzu wasan zata fara da zafi zafinta ko in ce da tafasarta. Dan haka ku gyara zama, mu je zuwa, yanzu ne zaku ji ainahin da?in shan maratu ni kuma na sha Maltina mai sanyi ina suburbu?o maku update!!.

Master Devil.

Suna tsaka da yin maganarsu da wannan mayakin kwatsam ba zato ba tsammani master ya ji an cukumi ruyar rigarsa.

Wani irin zaro idanu wannan warriors ?in ya yi, saboda ko da gigin wasa bai ta?a ganin wanda ya yi wa master magana cikin ?aga murya a cikin birnin nan bama bare har a kai ga nuna mashi matsa, sai ga shi yau an cakumi wuyar rigarsa?! Abin dole ta tashi hankalin kowa.

Shi kansa master ya girgiza da ganin cakumar wuyar rigar nasa da aka yi tun ma kafin ya ?ago idanu ya kalli wane? Yasan cewa Black Tiger ne kawai zai iya yi mashi hakan a cikin birnin nan, bayan shi kowa mahaukacin tsoronsa yake ji.

Zuciyarsa tafasa take yi tamkar an?aura dalma a wuta, jikinsa sai wani irin tsuma na ban mamaki yake yi, gashin jikinsa duk sun mimmi?e, duk wata alama ta zarra na cikakken namiji ta bayyana a jikinsa a wannan lokaci, tamkar wanda ya ci uban gudu ya ?oshi haka yake huci ha?e da ha?a uban gumi, idanun nan sun ka?a sun yi jajir da su kamar wuta, tamkar ba Ronniensu Floris ba.

Da kyar ya kawar da tunaninsa ya furta. "Ronnie are you out of your sense? Am I your mate?!". Cikin ?an ?aga murya ya fa?a.

Ronnie da ya gama fusata, zuciya ta zo har wuya, ransa ya gama jagulewa, jikinsa na wani irin zafi, ya rasa hukuncin da ya dace ya yi wa master a yau, dan dama ya jima yana tara mashi ne, master ya jima yana shiga harkarsa sosai, yau kam ya ?uresa ba zai iya ?aga mashi ?afa ba.

Ganin haka yasa wannan mayaki da ya kawo rahoto a kan Kingdom of power ya salalla?a ya gudu ya bar wannan waje, domin yasan fa?an na manyan kai ne, duk cikin birnin nan banda Black Tiger babu wanda ya isa ya ce zai saka baki a wannan fa?a wane ?aniyarsu.

Zuciyarsa na tafasa, da kyar ya furzar da iska mai zafin gaske daga bakinsa, cikin ?aga murya ya ce. "Akan me zaka je ka yi mun karya? Ni nace maka ina son Sweetie?! Me yarinyar nan ta yi maka da zaka ja mata irin wannan hukuncin? Shin ta cancaci haka daga gareka ne ko ni na cancanci hakan?!". Ya ?are maganar yana wani irin huci, ran maza ya ?aci!. Tamkar bai ta?a yin shagwa?a a rayuwarsa, kamar ba Ronniensu Floris mai zuba masu shagwa?a idan suna a tare ba!!.

Rai a ?ace ya bashi amsa da. "Awww kai ta yarinyar kenan ma kake yi?! Kai baka kishin yayanka? Baka masa fatan burinsa ya cika? Baka son mu samu Spender mu cinma burinmu? Saboda yanzu zuciyarka ta mutu shi ne kake bin bayan mace a kan yayanka?........"

Tsawar da ya daga mashi cikin fushi da kausasshiyar murya ne yasa ya dakata da yin maganar ba dan ya kai in da yake son dasa aya ba.

Da kausasshiyar murya mai amo ha?e da zafin rai ya fara magana kamar haka.

"Kai har ka isa kace ni bana kishin yaya? Ka isa kace zuciyata ta mutu? Har yau har gobe nine zakarar Black world!! Ba'a ta?a yin namijin da ya kaini ba kuma ba za'ayi shi ba!! Ra'ayi nane na yi magana a kan Sweetie or not, daga yau kada ka kuskura ko da sunan wasa ka sake ce mun zuciyata ta mutu a kan mace!!".

Zaro mashi wa?an nan jajayen idanun nasa master ya yi. Shi ma cikin ?aga murya ya ce. "Ronnie na gaya maka ka zama rago mai matatccen zuciya a kan mace!! A kan yarinyar da baka san asalinta ba, ka haukace a kan abin da ba zai taimake ka ba, ka zubarwa da y............".

Azababben marin da ya dallah mashi cikin fusata ne yasa ya dakata da yin maganar, al'ajabi da mamaki ne suka kusa sanya shi sumewa a wajen, bai ta?a tunanin Ronnie yana da gwanin gwiwar da karfin zuciyar iya ?aga mashi murya bama a rayuwarsa, duk da yasan cewa tabbas ya fisa matsayi da komai da komai, amma bai ta?a kawowa a ransa ya yi ?as?ancin da zai iya ?aga hannu ya dallah mashi mari ba, abin da mamaki.

"Master kada ka jawa kanka bala'in da ba zaka iya ?auka ba, kada ka ?ureni! Kada ka ?ata mun rai! Kai kanka kasan ?acin raina girgizan rugugin aradu ce ga birnin Black world! Kada ka ja na kasheka a nan kuma na kashe banza karen farauta!!..............".

Bai iya kai karshen maganar bane sakamakon zuciya da ya yaudari master ta ja shi ya ?aga hannu da nufin ya kai mashi mari, hakan yasa ya dakata da yin maganar tare da kaucewa marin.

Shi kansa mastern bai san ya aka yi ya yi yun?urin marin nasa ba, ya san duk abin da yake fa?a gaskiya ce, ?acin ransa rugugin aradu ce ga birnin, amma aka ce zuciya bata da ?ashi, sai ta ingiza shi a kan kada ya bari ?an yaron nan yana gaggaya mashi ba?a?en maganganu hakan zai sa mutumcinsa ya zube ya kuma sa jama'a su rage jin tsoronsa.

Ransa ne ya ?ara ?aci, wato yanzu master har zai iya cire hannu ya ce zai maresa? E lallai dole yau su cire raini a tsakaninsu, dole kowa ya san matsayinsa, hakan yasa cikin fushi ya jijjiga wuyar rigar master da karfin gaske, da hannu ?aya ya jinjigasa sai da gaba?aya jikinsa ta girgiza, sannan ya ?an yi baya tare da ?aga kafarsa ya takashi da karfi a kirji sai da ya tafi ta baya da karfi ya fa?a cikin wannan ruwa da yaran suke ciki suna ta faman ?irkar ruwa, wasu daga cikinsu ma sun sha ruwa ta yi masu yawa har sun sume a ciki master yana can suna tafka fa?a da Ronnien, yara abin tausayi.

Wani irin daka sufa Ronnien ya yi tare panjamawa cikin ruwan. Fa?a suka farayi a matsayinsu na zaratan zakaru masu ji da rai da lafiya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull