Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 65

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 65

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 65: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 65. Abin mamaki abin al'ajabi, master dai shi ya bawa Ronnie horo, shi ya koya…

3,362 words

Abin mamaki abin al'ajabi, master dai shi ya bawa Ronnie horo, shi ya koya mashi komai, amma sai ga shi Ronnie ya bashi kashi, ya sha kashi a hannun ?alibinsa, da kyar da makyarkyata ya iya kwace kansa yana haki ya samu ya fito daga cikin ruwan, kamar zai mutu ya fara ?o?arin gudun cetar ransa, dan ya wahala, Ronnie ya kama kansa ya danna a cikin ruwar almost 10 mins yana ta shan ruwa, dama Ronnien yasan suna da horon iya ri?e numfashinsu har na tsawon 5 mins a cikin ruwa, shiyasa kuka ga yana ?o?arin koyawa wa?an can yaran irin wannan ne yasa ya jefasu cikin ruwan, su sun samu wannan horon ne kuma daga wajen master ?in tun suna yara, shiyasa ya danne shi har ya kai 10 mins a cikin ruwan, kunga ya wuce adadin da ya iya.

Sai shan ruwa yake yi yana fafutukar neman numfashi, ashe shi ma Ronnie ya iya mugunta, haka yasa karfi ya dannesa yaki bashi wata damar da zai iya sha?ar numfashi!.

Ya sha ruwa kam babu karya, har idanunsa suka kara wani uban ja kamar wutar dake ruruwa.

Gudun cetar ransa ya fara yi. A fusace Ronnien ya fito daga ruwan, a fujaje ya bi bayansa, shi kansa ya yi mamakin yadda aka yi ya iya dukan master har haka, mutumin da ba wanda ya ta?a iya ja da shi a fagen fa?a ne ace yau shi da yake matsayin ?alibinsa kuma kusan ?an cikinsa ne ya dakesa har haka? Abin da mamaki! Power da ya samu a jikinsa yanzu ta bashi mamaki ba ka?an ba, bai ta?a zaton hakan yake ba....... Ran maza ne kawai ta ?aci!.

Bayan master ?in ya bi domin har izuwa yanzu bai huce ba, sai ma ?ara tafarfasa da zuciyarsa take yi.

Basu zame ko'ina ba sai cikin main parlourn, a lokacin Floris tana zaune a saman sofa ta buga uban tagumi, ga busassun hawaye a face ?inta alamar ta ci kuka ta ?oshi.

Da gudun gaske master ya haura sama yana haki kamar numfashinsa zata ?auke, jikinsa dukka sai ?igar ruwa yake yi.

Ronnie na danno kai da dugu Floris ta mi?e tsaye, da gudu ta nufesa, yana wani irin huci zai nufi sama ta yi saurin fa?awa jikinsa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Kowani mutum da rauninsa, shi kuma Ronnie kyawawan ?an'mata ne rauninsa, yana matu?ar son ganinsu cikin farinciki. Na gaya maku baya zina, kuma bai ta?a yi ba, amma dai yana kaunar kyawawan mata a kusa da shi kam ba karya.

Wannan kuka nata yasa ta ?an ta?a mashi zuciya, hakan yasa dan dole ya dakata da bin master da yake da niyar yi, ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya.

A saman shoulder ?inta ya kwantar da kansa yana jin kamar zai ha?iye zuciyarsa ya mutu. Ita ma kuka take yi sosai, dan ta yi kewarsa over, yau ya yi mata abin da bai ta?a kwatantawa ba ko da sunan wasa.

Jin kukan nata na ta?a mashi zuciya ne yasa ya ?auketa can jikinsa duk ruwa suka koma saman sofa suka zauna. Goge mata hawayen nata ya fara yi tare da fara aikin rarrashinta.

Cikin ?an?anin lokaci ta yi shiru, da yake ya kware a fannin sanin me mata suka fiso, ya iya rarrashi da kalamai irin na soyayya masu sanyaya zuciya, sai dai shi ba soyayyar yake yi ba ?an albarka...........??

Ya dai zuba masu kalaman ya kwantar masu da hankali, yagansu a gefensa suna murmushi, shikenan fa.

"Beb yunwa nake ji". Ta fa?a cikin muryar kuka.

Ba tare da ya sake furta kalma ba ya mi?e ya ?auketa suka nufi dinning room.

Shi kuma master ko ina ya yi? Yau Floris kyakkyawar tattabara ta cecesa. Me kuke tunanin Black Tiger zai ce a kan wannan fa?a nasu? Kun dai san yana ganin komai! Shin zai yi shiru ne ko dai zai gayawa kowa matsayinsa ne?! Hmmmm mu je dai zuwa!.

_P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A__???????

JAWAD and CHUCHU?????

Murya a ?an ru?e ta furta. "Yah Jawad kai ne da middle night ?in nan?". Ta yi maganar tare da mi?ewa zaune cikin sauri, ta zuro kafafunta ?asan gadon sannan ta mi?e tsaye.

Har?e hannayensa da kyau ya yi a saman chest ?insa, sannan ya jingina da jikin door room ?in. A hankali ya lumshe idanunsa ya sake warosu a kanta.

"Mekike yi baki yi barci ba har yanzu?". Tamkar mai magagin barci ya yi maganar, kana jinta kasan yana tare da kasala sosai.

"Nakasa yin barcin ne". A shagwa?e ta yi maganar.

Wani irin yanayi ya ji ta ratsa shi tun daga tafukan kafafunsa har izuwa tsakiyar kansa. "Jannat kina mun son ranki kam, yanzu dai meyasa kika kasa yin barcin?". Ya kai karshen maganar tare da ?aga mata gera guda alamar yana jiran amsa!.

"Yah Jawad na kasa yarda cewa wai kai ne kake sona, abin ya tsaya mun a rai'na, idan na rufe idanuna kalamanka ne kawai suke neman fasa mun kai'na, jin abin nake yi tamkar a mafarki, na ?asa yarda gaskiya ce, na kasa samun wanda zai mareni na farka daga wannan dadda?ar mafarkin, ina ma na farka naga gaskiya ce ba mafarki ba, da kuwa sai na yi azumi guda biyar ina godiya ga Allah". Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar.

Gently ya fara takowa izuwa in da take tsaye, tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki yake tafiyar.

Tana tsaye ya ?ariso gabanta, cike da tsananin kaunarta ya furta. "Har yanzu gani kike yi a mafarki kike?".

Kai ta gya?a mashi alamar e ba tare da ta yi magana ba.

A hankali ya sauke hannunsa daga saman kirjin nasa, jikinsa duk a wani irin mace sosai kamar mai jin barci, komai a kasalance yake yinta.

Hannunsa ?aya ya kai saman waist ?inta. ?an zaro idanu ta yi sakamakon wani irin shock da ta ji tamkar wadda aka jonawa wutar lantarki.

Iskar bakinsa mai tsananin kamshin mouth perfume deference type and toothpaste ne ya hura mata a cikin kwayar idanun da ta zaro mashi ?in.

A hankali ta lumshesu tana turo baki alamar shagwa?a. "Kai Yah Jawad me hakan to?".

?asa sosai da voice ?insa ya yi wajen furta. "So da kauna mana".

Wani dadda?ar ajiyar zuciya ta sauke, a fili ta ce. "Yah Allah kasa ba mafarki nake yi ba, Allah kaga zuciyata ina son Yah Jawad so mai tsanani, Allah ?asa gaskiya ce ba a mafarki ya zo ya ce yana sona ba, Allah ka cika mun burina ka mallaka mun shi a matsayin miji". Tana magana nan take idanunta suka cicciko da kwallah.

Hannunsa dake saman waist ?in nata ya fisgota da shi ta fa?a saman kirjinsa. Wash ta ?an furta sakamakon fa?awa da ta yi babu excuse ta buga kanta a dai'dai saitin ribs ?insa.

Hannu ta zura ta bayansa ta rungumo waist ?insa ta baya, shiru ta kwantar da kanta a saman kirjin nasa tana addu'ar Allah yasa kada ta farka daga wannan mafarki a yanzu sai gobe.

Rankwafo da kansa a kanta ya yi. Cikin wani irin salon soyayya mai jan hankali ya fara magana kamar haka.

"My kaunaty har yanzu baki farka daga mafarkin bane?".

Tana daga kwance ta gya?a kai alama e, sai ta ?aura da cewa. "Yah Jawad ka bari kada ka tasheni, kaga a zahiri ka cika yi mun fa?a da bada punishment, amma a mafarkinka da nake yi kullum soyayya kawai kake nuna mun, ina sonka my melody".

Hannu ya ?aura saman bayanta yana ?an shafawa a hankali kamar mai rarrashinta. Cikin sigar soyayyarta da ke wani irin fiagarsa ya fara fa?in. "My kaunaty ki bu?e idanunki, tabbas ba mafarki kike yi ba, ni ?in ne da gaske, amma bari na yi maki abin da zai sa ki yarda".

Shiru bata iya amsa mashi na, sakamakon wani irin kaunarsa dake ?ara ratsa fata, nama izuwa ?ashi da ?argon jikinta, duk wasu kofofi na jikinta sun bu?e suna kar?ar soyayyarsa da salonsa dake ratsata, duk sai ta ji wani iri da?in da ya rufe mata baki, ta ?asa iya furta kalma, sako kawai take ?ar?a yana ratsata. ?ara yafe mashi a jiki ta yi kamar mage.

Sai kiran layinta Yah Rizwan yake ta sake yi, amma basu ji ba, da yake wayar tata yana vibrate ne kuma tana kan gado pillow ya ?an danneta.

"My kaunaty please talk to me nown, kin san yadda nake marmarin jin voice ?inki a kullum kuwa?".

"Ni Yah Jawad ka barni please". Tamkar zata yi kuka ta yi maganar, a salon irin shagwa?a mai kara fisgar zuciyar masoyi ta yi shi.

Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali. Hannu ya kai ya ?an ?ago ha?arta yana mai cigaba da ?an shafa tsakiyar bayanta.

"Wahalar dani kike son yi ne kaunatyna?". Idanunsa a ?an limshe ya yi maganar.

Waro nata idanun ta yi, nan take suka sar?afe juna da kallon so mai tafiya da imani.

Almost 5 mins idanunsu sar?afe cikin na juna, a hankali ta hura mashi iskar bakinta a face ?insa wanda hakan yasa ya ?an limshe idanun nasa, soyayyarta ce kawai ke wani irin fisgarsa tamkar zai sa hannu a kai ya yi ta zunduma ihun da?i.

?an turo baki ta yi, shagwa?a mai kara rikita mashi ?wa?walwa ta fara zuba mashi tana tur?une fuska.

"Ni Yah Jawad ka kura mun idanu duk ka kwashe mun kyau ?ina, yanzu idan na farka daga wannan mafarki sai naga kyauna ta rabu..............".

?asa ?arisa maganar ta yi sakamakon saukar kyawawan lips ?insa da ta ji a saman tata, ta rikita bawan Allah sosai ne, shiyasa.

Suman tsaye ta yi tana jiran ta ji me zai yi mata da ya ha?e lips ?insu waje guda.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A__???????

AUTA ZUNAIRA?????

Ga duhu ga toshe baki sai abin ya matu?ar daga mata hankali tare da bata tsananin tsoro, a ru?e ta fara ?o?arin kwatar kanta dan ta samu ko ihu ne ta kurma ko za'a kawo mata ?auki.

Saukar zazzakar voice ?insa a cikin kunnenta in da yake cewa. "Ki nutsu ni ne". Yasa ta nutsu tsit, amma jikinta na kerma, saboda ta rigada ta tsorata tun farko.

A hankali ya zame hannunsa daga bakinta tare da saketa ya ?an yi baya ka?an kamar taku biyu daga kusa da ita.

Bata iya ganinsa sosai, amma ta samu nutsuwa matu?a da jin voice ?insa.

?asa ?asa ta ce. "Hoorain me kake yi a nan? And meyasa ka rufe mun baki ka jawo ni wajen duhun nan?".

A maimakon ya amsa mata tambayar tata sai ya jefa mata nasa tambayar shi ma.

"Ina zaki je a daren nan? Meya fito dake?". Da alama ransa a ?an ?ace ya yi maganar, saboda ba da irin muryar da ya saba yi mata magana bane ya yi ta.

"Sai ka amsa mun nawa tamnayar tukun nan ni ma zan amsa maka, domin ni na fara tambayarka ai". A ?an shagwa?e da irin muryar da take yi wa Yah Omar ?inta magana ta yi mashi.

Dadda?ar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Afuwan ranki ya dade, tuba nake yi bisa jefo maki tambaya da nayi ba tare da na baki amsar wanda kika tambaye ni ba, rai'na ne a ?an ?ace, amma ki yi hakuri". Wayyo shi dai kullum muryarsa cikin sanyi da nutsuwa, sam babu hayaniya abinsa, very gentle guy.

"Ba komai, yanzu dai ka gaya mun me kake yi a wajen nan?". Ta yi maganar da alama son jin me yake fito da shi da daddare haka, meyasa shi ba zai je ya kwanta ya hutawa ransa ba? Ta damu sosai a kan hakan, tana tausaya mashi sosai.

Shi kansa ya fahimci cike da damuwa sosai a tattare da ita ta jefa mashi wannan tambayar, ya kuma ji matu?ar da?i a ransa na yadda ta nuna damuwarta sosai a kansa, sai dai kuma bai bari hakan ta yi wani tasiri a cikin zuciyarsa ba, dan shi yasan da wacece yake tare, yanzu haka ma idan aka kamasu ai ya shiga dubu ?ari uku bama uku ba, so baya barin duk wani abin da zai shafeta ya ratsa fatarsa ma bare har ya fasa tsoka da ?ashin jikinsa ta shiga mashi cikin zuciyarsa, Allah sarki har ya bani tausayi ya kuma ta?a mun zuciya bawan Allah.

"Gadinki nake yi shiyasa kika ganni a wajen".

Allah sarki ya bata amsa, bai iya yin karya ba, baya iya samun nutsuwa a kullum, sai ya fito kusa da part ?insu ya zauna dik dan saboda ita, Hoorain sam bai iya karya ba, yanzu haka da commander ya tambayesa ina yaje lokacin da aka kawo masu hari kai tsaye ya gaya mashi gaskiyar komai na cewa yana tare da ita ne a lokacin, sosai baban nasa ya ja mashi kunne tare da daka mashi warning a kan ya kula kuma ya yi baya da ita. Amma dik da haka baya iya janye jikinsa daga in da yasan tana wajen, ko barcin kirki baya iya samun yi, shi kansa bai san me yake damunsa ba.

Wani irin sanyi taji ya ratsata, ha?i?a ta yi matu?ar farinciki na jin cewa saboda ita yake kusa da part ?insu, tsabar da?i sai ta ji tamkar ta daka tsalle ta rungumesa, amma sai ita ma ta danne ta ce.

"Yanzu saboda ni kake tsayawa a wannan waje? Meyasa to?". Ta gefa mashi tambayar idanunta a kan face ?insa duk da bata ganinsa sosai saboda duhun wajen.

"Babu komai, kawai zuciyata ce take kasa samun nusukuni idan har ban kasance a dik in da nasan kina wajen ba". Ya bata amsa kansa a ?asa. Shi dai ya ji da?i baya karya kuma bai iya bama, kun ji ya bu?e mata gaskiyar dake cikin zuciyarsa.

Ai wani irin da?in da ta ji ne yasa bata san lokacin da ta matso ta fa?a jikinsa tana murmushi ba.

Bai so barinta a jikin nasa ba dan gudun kada a gansu, amma kuma ya ?asa iya rabata da jikin nasa, sai ya tsinci kansa da jin da?in hakan.

"Ke kuma baki fa?a mun me ya fito dake a wannan daren ba?". Kamar mai ra?a ya yi maganar.

Hannunta ta zura ta ?ugunsa izuwa ta bayansa ta rukunkumesa, ta kwantar da kanta a saman lion chest ?insa.

"Kai mana na fito gani". A shagwa?e ta bashi amsa.

Wani irin yanayin da ya tsinci kansa a ciki na farinciki ne har bai san lokacin da ya sanya hannayensa dukka biyu ya rungumeta da kyau ba. Yaji matu?ar da?i over, ashe shi ta fito nema dan ta gansa.

Ta fahimci ya ji da?in maganarta, dan haka sai ta ?aura da cewa. "Na ji ina son ganinka ne, sannan kuma ka bani wancan rigar taka idan ba haka ba ba zan koma cikin gida ba, a wajen nan zan kwana". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

Da kyar ya iya bu?ar baki ya furta. "Meyasa zaki zo ganina? Kina son su Prince Jaish su hukuntani ko?".

"Babu wanda zai hukuntaka, ai ba kai ka kirani ba, ni da kai'na nazo". Tana magana tana ?an motsa hannayenta dake saman bayansa.

Hakan da take yi ba ?aramin rikitar da shi take yi ba, tana ?ara jefasa cikin yanayi, bare ga shi ga yadda yake dama, kunga mutane masu shiru shirun nan, idan kuka kuskura suka bu?e baki sai kun gudu, sannan ga yanayin aikinsa aiki ne wanda kullum jinin jikinsa yana cikin busy, bai san wani rauni ko gazawa or sanyin jini ba, jininsa a tafashe yake sosai, irinsu sai an bisu a hankali idan ba haka ba ayi ?atacciya.

Shiru bai iya furta kalma ba, ya kasa koda motsawa saboda wani irin bakon yanayi mai ra?a?in da?i dake ratsa shi.

"Hoorain ina tambayeka........". Bata kai karshen maganar ba a fujaje ya rufe mata baki da hannunsa dake saman bayanta.

A hanzarce ta ?ago da kallonta izuwa kansa, ganin yana kallon wani wajen yasa ta kai kallonta nan, inuwar mutum ta hango kamar uncle Taheer.

Wani irin dum dum ta ji kirjinta ya bada bugu, ya biyo bayanta kenan? Hakan na nufin yana ankare da ita kenan? Yanzu me abin yi?.

Ta lulu?a duniyar tunani sai jinta ta yi a saman shoulder ?insa, cikin san?a ya matsa da ita gaba, dan wannan inuwa mai kama da uncle Taheer ?in yana tinkarosu kamar ance mashi tana wajen, ko da yake kamshin perfume ?inta ya bi, da shi ya yi amfani ya iso in da take.

Ganin da gaske yana cigaba da biyosu ne yasa ya dakata tare da sauketa ?asa. A cikin kunne ya ra?a mata. "Kina da vest a ciki?".

?an zaro idanu ta yi, ganin babu lokacin tsayawa ta ce zata yi mashi shagwa?a ko gardama ne yasa kawai ta gya?a mashi kai alamar e tana vest a ciki.

A hanzarce ya kai hannunsa saman ma?allan rigar barcin jikinta. ?allesu dukka ya yi ya rabata da rigar, ya rage saura white vest na ciki kawai.

Sauri sauri ya tsugguna ta haye bayansa, bayan bishiyar mangoron dake karshen wajen ya la?e, yana ganin uncle Taheer ?in yana tafiya cikin san?o har ya iso in da suke.

Har zai rufe mashi fuska da rigar tata sai kuma wani tunani ya fa?o mashi, tunawa ya yi da idan ya kuskura ya rufe mashi fuska da rigarta fa to ba shakka zai gane cewa Autar tana wajen, dama ya yi niyar ya ?aure mashi fusa da rigar tata ne sosai sai su gudu, kunga kafin ya samu ya kwance face ?in nasa ya bisu ma sun kurewa ganinsa sun yi nisa, amma sai ya tuna to ai zai gane rigarta ce, in hakan kuma ya faru to fa tabbas yau ba zaman lafiya a wannan masarauta, tabbas sai hankalin kowa ya tashi.

Tuna hakan ne yasa ya fasa kudurin nasa, a hankali ya fara san?o da ita a bayansa suka bi ta bayan bishiyar, uncle Taheer yana ta gaba su kuma suka bi baya, cikin dabara ya samu ya bar arear wajen.

Suna fita kuma ya rasa ina zai yi da ita, ga ko'ina da haske tamkar rana, maya?a suna ta shawagi, idan aka gansu a tare kawai ma ya shiga uku bare kuma a ganta goye a bayansa.

Duk ya ru?e hankalinsa a tashe bawan Allah, sam bai ma san lokacin da ya wuce room ?insa da ita ba, ba zai iya sauketa a wajen ya ce ta tafi ba, dan babu riga a jikinta, ?an banzan kishi ba zai iya barinsa ya yi hakan ba, zai ga ai kowani mayaki idan zai wuce zai ganta kafin ta isa cikin part ?insu, idan kuma ya ce zai tsaya sanya mata rigarta to fa tabbas za'a iya ganinsu, dan maya?a masu gadi suna ta going up and down a cikin harabar kingdom ?in dan tabbatar da tsaro.

Suna shiga ?akin nasa ya banko kofa tare da murza key, a hanzarce ya sauko da ita daga bayan nasa, jikinsa har tsuma yake yi wajen mi?a mata rigarta dan tasa yasan ta yadda zai yi ya mayar da ita cikin gida.

Yana jiyowa da nufin ya mi?a mata rigar idanunsa suka sau?a a kan ha?ad?en lallausan surar jikinta, fata kamar na jarirai.

Ai a dubu ya kawar da kallonsa while ita ma ta yi ?asa da kai. Mi?a mata rigar tata ya yi ba tare da ya sake juyowa ba, da kyar ta iya kar?a ita ma saboda kunyarsa da ya kamata, ga shi vest ?in jikin nata a dai'dai cibiyarta ya tsaya mata, ya kalle mata plat tummynta da sauran sassan jikinta.

Mayar da rigarta jikinta ta yi, wani irin yanayi na tsananin kunyarsa ta tsinci kanta a ciki.

"Muje na rakaki ko?". Ya fa?a ba tare da ya juyo gareta ba.

?akin nasa ta fara bi da kallo tana mamakin irin tsabtarsa, komai nasa kamshi yake zubawa, ga ?akin nasa ?an dai'dai, sai dai akwai komai da duk wani ?an adam zai bu?ata a cikin bedroom dan more rayuwa, bed ?insa dake shinfi?e da up white bedsheet ne ya yi matu?ar burgeta, ashe dai ya iya aikin mata.

Kallonta ta kai saman zabgegiyar takobinsa dake rataye a jikin bango, abin ya burgeta.

Can ta hango wani hoto dake saman bedside drawer ?insa cikin frame, an ?awata shi sosai da kwalliyar flowers masu ?aukar hankali.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull