Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 66
Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 66: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 66. Dawo da kallonta a kansa ta yi tana mamakin hali irin nasa, idan ka gansa a…
3,233 words
Dawo da kallonta a kansa ta yi tana mamakin hali irin nasa, idan ka gansa a dake cikin jarimta kamar bashi da wani shaukin a kan soyayya, ashe ?akinsa harda kwalliyar flowers, ashe dai ya san love kawai dai jarumta ce ta fi soyayyar yawa a jinin jikinsa har ta riki?ar da shi har haka, da zai samu wadda zata farfa?o mashi da soyayyar tuni zai taso da tasa, irinsu ne idan suka fara zuba love sai ka rasa ta ina suka koya.
Ra?awa gefensa ta yi zata wuce dan ta je ta ?auki hoton taga su wanene? Ta dai hango har da ?aramin yaro a cikin hoton, ga kuma mace da namiji wanda idan ba gizo idanunta suke yi mata ba sai taga kamar commander Zafar ne lokacin yana ?an matashi matashinsa, to waye ?aramin yaron kenan?. Ta jefawa kanta tambaya, taso amsar ya kasance Hoorain ?in nata ne dai, hakan yasa ta nufi hoton da sauri dan ta tabbatar, sai dai bai bari ta ?arisa wajen ba ya yi saurin ri?o hannunta.
A hanzarce ta juyo da kallonta a kansa, da sauri ya kawar da idanunsa daga kanta dan baya son su ha?a ido.
"Hoorain ka bari mana, hoton can zan je na kallah". Kamar zata yi kuka ta yi mashi maganar.
Jin ta ambaci hoto yasa ya yi saurin kai kallonsa kan hoton, ai kuwa a fujaje ya saki hannunya ya je ga ?auke hotonsa da nufin ya ?oye.
A hanzarce ta ?ariso wajensa tana yin ?an kukan shagwa?a a kan ya bata ta ga su wanene?.
Kin bata ya yi saboda baya son ta gansa yana yaro, ga shi a hoton mamarsa ta ha?a shi da nama a hannu ta kuma cusa mashi wani a baki bai gama ha?iyewa ba, duk dan ya yi shiru a ?aukesu hoto, kuka yake ta yi, hakan yasa kumatunsa suka kumburo a hoton, abin gwanin ban dariya, shiyasa baya son ta gani.
Kuka ta fara yi mashi tare da fara ?o?arin kwatar hoton daga hannunsa.
Hannun nasa ya ?aga sama kafin ya ce. "To ki kwata ki gani mu gani idan kina da tsawo".
Tsalle ta fara yi tana son kwata sai dai ina ta kasa, dan kuwa komai tsallen da zata yi bata kusa kamawa ma.
Dakatawa da yin tsallen ta yi tare da juya mashi baya ta har?e hannayenta a saman kirjinta a dole ta yi fushi.
Ganin haka yasa ya sauke hoton, a hankali ya dawo ta gabanta ya zamana suna fuskantar juna. Hoton ya mi?o mata ba dan ya so ba sai dai fushin da ta yi bai so hakan ba, cikin sanyin murya da sigar rarrashi ha?e da tausasawa ya ce. "Am so so sorryyyyyyy ranki ya da?e, tuba nake yi, ga hoton nan ki gani".
Yadda ya yi maganar da ka jita zaka san bata kai har cikin zuciyarsa ba, saboda baya son ta gani gaskiya.
Ba tare da ta ?ago da kallonta a kan hoton ba ta furta. "Dukkan abin da my hero zai ce baya so to nima bana bu?ata, dan haka na fasa ganin hoton ka ajiye shi kawai".
Maimaita sunan my hero da ta fa?a ya yi a cikin zuciyarsa, ha?i?a ba yau ta fara ce mashi jaruminta ba, amma na yau da ta fa?a sai ya ji sunan ya yi mashi wani irin daban.
"Da gaske nake yi ranki ya da?e ki ?ar?a ki gani kin ji? Dan Allah ki dai'na yin wannan fushi ko?".
Cool murmushi ta sakar mashi tare da dawo da kallonta a kansa, tamkar wata babbar mace tasa hannu ta kar?i hoton, ba tare da ta kallah ba ta nufi saman drawer ta ajiyeta, a hankali ta juyo garesa, murya mai cike da kulawa ta furta. "Wani lokaci idan na zo zan kalli hoton, yanzu dai bani rigar taka na tafi". Tana magana tana matsowa in da yake tsaye, kallonta kar a kan face ?insa.
Ajiyar zuciya ya sauke, yau jin kansa yake yi tamkar ba'a duniya yake ba, ya kasa yarda cewa yau Gimbiya Zunaira ce a cikin ?akinsa, abin ya tsaya mashi a rai, anya zai iya rintsawa yau kuwa? Ya jefawa kansa tambaya.
Ya shagala da tunani bai san lokacin da ya kafeta da kallo har cikin ba, sai dai jinta ya yi ta sanya tafukan hannunta cikin nasa tana fa?in. "Tunanin me kake yi kuma kallon me kake mun?".
Nisawa ya yi tare da bu?e baki zai yi magana kenan suka jiyo knocking na kofar ?akin da karfi.
A tare suka wani irin zaro idanu kamar kwayar idanun nasu zai fa?i ?asa.
My people's wa kuke tunanin ya buga masu kofa? Me zai faru a wannan dare?.
A can cikin gida kuwa, nemanta King Zuhair yake ta faman yi a ?akunan ?an uwanta, dama kunsan yana zuwa yi mata addu'a a kowani dare, to ya je room nata zai yi mata addu'a ne bai sameta ba, ya je ?akin Mommarta bata nan, ya le?a na Chuchu bata nan, izuwa yanzu hankalinsa ya fara tashi, ga shi Guyson ma yana ?akin Mommarsu bare ace suna tare, sarkin kwalafucin uwa ba, yaka manne da ita yaki matsawa.
Me kuke tunanin zai faru idan King bai ganta ba? Akwai cakwakiya gobe, ni dai suna yi ina shan Maltina mai sanyi, to me yafi rai'na?.
??KADA KU MANTA WANNAN DADDA?AR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE????
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH ????
??RAWANIN ?? ZALINCI ????
????????????????
FATEEMA ZAHRA MUSA ????? ??A-K-A ???????????????? ????????????
?????????? 6/11/2024.....??????
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
?????????? ????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ???????? ?????????? ??????? ????? ????????? ??????? ??? ?????????? ????? ????????? ????? ???????????? ??????? ??? ????????????? ??????? ??????? ?????????
??ZANGO NA BIYU....??????
35
A tare suka dawo da kallonsu a kan juna, sun kasa motsawa daga in da suke, dukkaninsu fa?awa suka yi duniyar tunani.
Ita kanta Autar ta yi matu?ar tsorata, zuciya da iya shegen jefa mutum cikin mugayen tunani da sa?e sa?e, musamman idan mutum yana tsorace da abu to wlh zuciya ta rin?a kara mashi tsoro ta hanyar jefa mashi munana tunane tunane.
Tunani ta fara yi a kan idan Yah Jaish ne ya zo fa? Ta shiga uku ta lalace! Ita da kanta ma kenan, ina kuma ga shi? Kamar ba yanzu ta gama ce mashi ba mai hukunta shi ba, ta yi mashi da?in baki, ashe dai ita da kanta ta san bakar zuciyar ?an uwanta, tasan idan hakan ya faru ta ja mashi babbar aiki ne da kaf kingdom of power babu wanda zai iya tare mashi, a gaskiya ta tafka babban kuskure wanda sai a yanzu ta fahimci hakan, addu'arta ?aya shi ne Allah yasa Yah Guyson ?in ta ne idan ma ?aya daga cikin ?an uwanta ne, shi ne kawai a gaba?aya familyn nasu wanda tasan zai iya fahimtarta ya kuma rufa mata asiri ba zai gayawa kowa ba, bayan shi wlh ko Gimbiya Chuchu da suke tamkar chewing gum ba barinta zata yi ba, sai ta sanar da King, dan ita ma bata wani sonta da Hoorain ?in, bata son ganinsu a tare.
Sake buga kofar da aka yi ne yasa suka dawo cikin hankalinsu, dawo da kallonsa daga kan kofar izuwa kanta ya yi, while ita ma shi take kallo, sun rasa mafita, yadda suka tsaya a tsakiyar ?akin sai sun baka tausayi ga kuma abin dariya na yadda suke kallon juna sun rasa mafita.
"Zan ?uya a cikin toilet ?inka kai kuma sai ka duba wanenen ka ji?". Ta yi maganar ?asa ?asa kamar mai yin ra?a.
Kai kawai ya gya?a mata, da alama jikinsa duk a mace, bashi da wani kuzari, dan kuwa shi ba ?an uwanta ne ma suka damesa ba, idan sun kamashi karkari dai bai wuce su kashe shi bane kawai, shi damuwarsa yadda Abbonsa ya ja mashi kunne a kanta, ya yi mashi fa?a, sai a ce mashi yau an kama shi da ita a ?akinsa a irin wannan daren? Ya kuke tunanin commander zai ji a ransa? Shi ?acin ran mahaifin nasa ne baya so, gara mashi su kasheshi idan suna so amma kada Abbon nasa ya sami labarin hakan, yasan zuciyarsa ba zata iya ?auka ba.
Wato commander yana balai'n kaunar ?an nan nasa ?aya tilo a duniya, shiyasa duk abin da zai zama mashi matsala a rayuwarsa yake saurin taka mashi birki a kan abin, kunga yasan kasancewarsa kusa da ita zai haifar mashi da matsala ne yasa tun wuri ya daka mashi warning a kan, amma bai ji ba, ko da yake ba laifinsa bane bawan Allah.
Tun da yake bai ta?a sallake ko A a maganar da Abbonsa zai gaya mashi ba, yana yi mashi biyayya sosai, yana gudun ?acin ransa sosai, da ya yi abin da zai ?ata mashi rai gara mashi ya yi kwana biyar a ?aure babu ruwa babu abinci, a kanta ne farkon fara tsallake maganar commander, a hakan ma kullum yana cikin danasani tare da ?o?arin nesanta kansa da ita, amma ya ?asa.
Kofar ?akin ya nufa ita kuma da sauri ta shige cikin toilet.
"Wanene?". Ya fa?a muryarsa tana sarkewa. Ya yi tambayar cike da tsoro da fargabar muryar wanda zai bashi amsa. Kirjin maza yau sai dukan uku uku yake yi dan tsoron kada ace Abbonsa ne, Allah sarki shi commander ne ma kawai a ransa.
Daga wajen ya amsa da. "Lafiya yau ka kulle kofar Hoorain?".
Wani irin sauke nannauyar ajiyar zuciya ya yi, to fah ya zai yi kenan? Abin da yake gudu dai da alama shi ne yake shirin faruwa.
"Babu komai Abbo". Ya bashi amsa tare da sanya hannunsa dake ?an ?ari saboda tashin hankalin da ta jefasa a ciki, da kyar ya murza key ?in ya bu?eta.
Commander ne a tsaye cikin wannan irin tsayuwar tasa ta manyan jiga jigan jaruman, hannunsa ri?e da kayan abinci cikin wani babban tray.
Hannunsa dake ?ari ya kai ya kar?a mashi abinci yana fa?in. "Sannu da zuwa Abbo".
Mi?a mashi abincin ya yi a tare suka ?arisa cikin ?akin commander ya rufe kofar. A saman gefen bed ?insa ya zauna yana fa?in. "Hoorain wani irin kamshin perfume ne wannan?".
Wani irin dukan uku uku ya ji kirjinsa ta bada, Abbonsa akwai kaifin ?wa?walwa, wai yanzu har ya iya tantance cewa akwai wani kamshi na daban da ya shigo ?akin?. Kai shi ma dai ya iya sa ido gaskiya.
"Kamar wani kamshi fa?". Ya yi tambayar cikin dakiya, yadda kuka san bai san me commander yake nufi ba.
"Na ji kamshin perfume irin na mata ne a ?akin, kuma tamkar kamshin perfume ?in princess Zunaira ko Jannat, su ne suke amfani da irin wannan turaren". Ya kai karshen maganar tare da mi?ewa ya sau?o ?asa saman dadduma ya zauna.
Tun da ya fara magana kirjin ?an nasa take harbawa pat, pat, pat da karfi karfi, addu'arsa ?aya kada ya titsiyesa a kan sai ya ji dalilin zuwan wannan kamshi ?akin, bawan Allah duk yana cikin firgici da tashin hankali, Auta tana neman jefashi cikin bala'i, da yake bai ta?a aikata hakan ko da sunan wasa bane sai tsoron nasa ya tsananta.
"Zo nan na baka abinci yau barci da wuri nake ji". Abbon nasa ya katse mashi tunanin da yake yi.
Wani irin ajiyar zuciya da ya sauke ne yasa Abbon nasa ?agowa ya zuba mashi idanu.
"Hoorain ya na ganka tamkar a ru?e haka? Lafiya kake kuwa?".
Da sauri ya furta. "E a'a e". Ya yi maganar ma murya na sarkewa alamar rashin gaskiya, wlh bai iya karya ba, ga shi wane shi ya ce zai fa?i gaskiya a yau, zai jawa kansa bala'i ne, amma kuma ya rasa ta ina zai fara yin karyan dan kare kansa, shi ne yasa ya ru?e yake ta fa?in eh kuma a'a.
"E a'a kuma?". Ya sake jefa mashi tambaya.
A karo na biyu ma cewa ya yi e a'a e ya sake yi.
Zuba mashi idanu sosai ya yi yana son karantarsa. Ganin hakan yasa sai ya yi saurin mi?ewa, a ru?e ya nufi toilet duk dan ya kaucewa zargin da yake gudun Abbon nasa ya fara jefansa da shi.
Da kallo ya bisa har ya shige cikin toilet ?in, bai kawo komai a ransa ba, sai ma tunani da ya yi a kan ko dai toilet da yake son shiga ne ya rikitashi har haka? Ko da wasa bai bashi wani zargi maras kyau ba, dan yasan da wuya Hoorain ya aikata wani abin rashin gaskiya, yasan irin tarbiyar da ya bashi.
Jim ka?an ya fito daga cikin toilet ?in ya dawo ya zauna, sai a lokacin kuma ya rage kayan jikinsa, ya kuma cire wannan hula tasu, ya zauna a gaban Abbon nasa, zaman cin abinci da kyau.
Abinci commander ya zuba masu da kansa, a tare suka fara ci suna tattaunawa a kan rayuwa, haka suke yi kullun, commander yana bala'in kula da ?an nan nasa, baya yarda Hoorain ya ci abinci har sai ya zo sun ci a tare, shiyasa baya barinsa ya ci shi ka?ai.
Duk abinda suke yi tana jiyosu daga cikin toilet ?in, sun yi matu?ar burgeta, uba da ?a ne kamar wasu abokai haka abin da birgewa matu?a.
Hira commander yake ta zuba mashi amma hankalinsa baya a tattare da shi, yana can ya tafi duniyar tunanin yadda za'ayi ya mayar da ita cikin gida.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...???????
Sosai hankalin King ya fara tashi, sai yanzu yake danasanin saba mata da zuwa kowani ?aki ta kwanta da yake yi, kun san tana kwana da Chuchu ko su Sarina idan ta yi ra'ayi, sannan tana kwana wajen Momma, har part na Jaish tana kwana da shi idan tana so, yau dai King ya yi nadamar hakan.
Bai sanar da mommarta ba, ya nufi part ?in Akka domin dubata a can, a jikinsa yake jin bata cikin arear wajen, saboda bata ta?a wuce wajen su Mommarta ba, in ta ?an yi nisa ne room na Jaish, yasan bata zuwa wajen mama and mummy, amma haka ya je can ya duba, duk dan kawar da zargi.
Duk wasu ?akuna da suke part ?in na Akka sai da ya shiga, wayam babu kowa, yau ko su Sarina ma basu kwana a part ?in ba, har ?akin uncle Jahiz dake cikin part ?in sai da ya duba, wayam bata a ciki, uncle Jahiz ?in ne kawai kwance yana zuba barci cikin kwanciyar hankali.
Tsayuwa ya yi a main parlourn part ?in yana tunanin ina ta shiga a wannan dare? Baya son shiga ?akin barcin Akkar dan kada ya tasheta ko wani abin makamancin hakan.
Tunani ya fara yi ta ina zai fara nemanta a daren nan? Ina ma taje? Yasan dai babu wanda ya isa ya shigo part ?in nan nasu har ya ?auketa ya fita da idan ba dai aljani ba, domin masu tsaron wannan part ?in ko ?uda idan zasu gani ba zasu barshi ya giftasu har ya wuce ciki ba, so idan ma bata nan to wlh da kafafunta ta fita ko kuma wani daga cikin family ya fita da ita!!.
A hankali ya juya zai bar part ?in, amma sai ya ji zuciyarsa ta ?asa yarda da hakan, ya kasa samun sukunin aikata hakan, damuwa mai tarin yawa ce take cunkushe a cikin zuciyarsa take ?o?arin taso mashi izuwa ma?oshinsa.
A hankali ya juya ya nufi ainahin bedroom na kwanar Akka, bai so shiga ba, amma haka ya tsinci kansa da le?a wajen dan ya samu damar cewa babu in da bai duba ba a gidan.
Ba karamar madarar mamaki ya sha ba na ganinta kwance a kusa da Akkar, idanunta a rufe alamar barci take yi, shi dai yasan bai ta?a samunta a wannan part ?in da sunan zata kwana ba, tana shiga, amma banda batun kwana kam.
A hanzarce ya ?arisa cikin ?akin domin ya tabbatar ba kaunarta ce take sa take yi mashi gizo ba.
Kamar zai kunna wutar ?akin domin ?ara tabbatarwa, sai kuma ya fasa dan kada Akka ta farka, wutar lamps ?in ma sun wadatar ya iya hango face ?inta.
Tana kudundune a cikin bargo, sai zuba barcinta take yi abinta. Ina ai duk da haka bai yarda ba sai da ya hau saman bed ?in ya ta?ata dan dai ya kara tabbatarwa da kyau.
To shi ma kenan da bai san cewa ta fita ba ya sha madarar mamakin ganinta a saman bed ?in Akka, to ina kuma ga mu da muka san tana a tare da Hoorain, wai me ya faru? Ya aka yi ta dawo room ?in Akka?. To mu koma baya ka?an mu gani.
Bayan sun kammala cin abinci ne commander ya bu?aci da su yi hira, a nan shi kuma ya nu?e ya ce barci yau yake ji, sosai commander abin ya bashi mamaki, domin kuwa tun da yake da Hoorain yau almost 26 to 27 years bai ta?a ce mashi Abbo ina jin barci ba, hasalima shi ne yake matsa mashi a kan ya kwanta ya yi barci, amma sai ya ce a'a shi bai ji.
Tun yana ?arami haka yake baya son yin barci dare, gara na rana ma yana ?anyi bisa ga na dare.
Amma sai bai kawo komai a ransa ba, saboda yarda da ya yi da ?an nasa, bai kuma sake ta da batun kamshin perfume ?in Auta da ya ji a ?akin ba, saboda ya yi tunanin ai Hoorain mai kula da lafiyar ta ne, ta yiwu basu jima da rabuwa bane, hakan yasa ya yi shiru bai sake tada maganar ba.
A ?angaren shi kuwa Hoorain addu'a kawai yake yi Allah yasa mahaifin nasa kada ya jefa mashi wata tambaya ko kuma wani magana, dan bashi da amsa ta karya da zai iya bashi, bai iya ba.
Sai dai kuma ya gudu bai tsira ba, sai da Abbon ya ce. "Baka da lafiya ne Hoorain?".
Kai kawai ya girgiza alamar a'a, yau yaki yarda su ha?a idanu da shi, ya kuma ki yarda ya bu?i baki ya yi magana sosai.
"Hoorain me kake ?oye mun ne? Alamu sun nuna akwai abin da ka ?oye mun ko dai baka son na san baka da lafiya na tashi hankalina ne?". Kallonsa na'a kansa babu ko kyaftawa ya yi maganar.
Tunani ya shiga yi a yanzu idan ya yi karyar bashi da lafiya ma ya ?ara ?aure kansa ne, dan kuwa Abbonsa zai ce ba zai fita ya barshi shi ka?ai a ?akin ya kwana ba, sai dai su kwana a tare, dan kada jikinsa ta tashi da tsakar dare, dan haka karyar bashi da lafiya ma bata taso ba, dole ya nunawa mahaifin nasa cewa lafiyarsa lou dan ya samu ya tafi ya barsa shi kuma ya mayar da ita cikin gida.
"Abbona lafiyana lou, yau na gaji dayawa ne, barci sosai nake ji". Kana jin yadda ya yi maganar zaka fahimci ba'a cikin nutsuwarsa yake ba, bawan Allah abin da bai ta?a kwatantawa bane, ko tuna hakan a ransa bai ta?a yi ba Auta ta ja mashi, shiyasa ya ru?e, kuma ga dukkan alamu Hoorain baya magana da mata, bai saba ba, bare kuma ace ya kawosu cikin ?akinsa, kai bai ta?a, da akwai bayi mata masu hidima sosai a cikin gidan, amma shi baya daga cikin layin masu yi masu magana gaskiya, dan ru?ewar da ya yi wanda ya saba kasancewa da mata sam ba zai ru?e har haka ba!!.