Kenza eBookz

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 67

Rawanin zalinci 2 Complete - Chapter 67

Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 67: Rawanin zalinci 2 Complete Chapter 67. "Tom shikenan, ni na manta ma ban gaya maka ba, batun neman Prince Jaish mai…

3,368 words

"Tom shikenan, ni na manta ma ban gaya maka ba, batun neman Prince Jaish mai martaba ya ce a barshi yayyunsa suna aiki a kansa a kimiyance, dan haka mu maida hankali a kan neman Spender kawai, ka shirya gobe akwai in da zan aikeka kafin nan mu fara shirin mai da wa Queen Zarina martani, kada ku kyaleta idan kuka je, ku tabbatar sai ta fito daga cikin fadarta ta zube gwiwowinta a gabanku ta bada hakuri a fatar baki a kuma rubuce a takarda ku dawowa da King da shi, matar nan ta ketare duk wasu iyakoki, duk wasu dokokin yaki ta takesu ta kawo mana hari ba gaira babu dalili, dan haka yanzu a dokar yaki muna da damar yi mata duk abin da ya dace, ku ladabtar da ita, lastly ka da ka mance da ri?e addu'a dan kai kanka kasan in da zaku dosa". Ya kai karshen maganar tare da ?an kawar da kallonsa a kansa......... Da alama wannan karon ba tare da shi za'a fita yakin ba.

Ni kuwa nace rashin sani yafi dare duhu, da kunsan balai'n da yake tinkaroku na harin da Black Tiger yake son kawo maku wlh da ba zaku ?ata warriors ?in yakinku, ku wahalar da su, ku jigatar da su a kan wata Queen Zarina karamar kwaruwa ba, ga babban she?ani ifiritu mai shafe Daula duk girmanta daga doron duniya, ya rufe babinta a manta da an ta?a yin irin ta a duniya nan yana dinfaroku! Zaku wani tsaya biyewa Queen Zarina! Ai kawai fara shirin gagarumim yaki na a mutu ko a rayu kawai zaku yi! Hmmm akwai dai gagarumim matsala sosai gaskiya.

Jinjina kansa ya yi alamar ba matsala ya ji zantukan baban nasa, daga haka suka yi sallama, commander ya fita ne kawai amma ba dan ya so hakan ba, saboda yana son sanin me yake damun ?an nasa.

Yana tafiya kamar da minti biyar haka sai ya ?auko holarsa ya mayar kansa, sannan ya ce da ita ta zo ya mayar da ita dare yana kara yi.

A hanzarce ta fito daga cikin toilet ?in, yana tsaye ta ?ariso gabansa.

Kansa a ?asa ya nufi hanyar fita daga ?akin!. Bayansa ta bi da sauri, ita kanta izuwa yanzu a tsorace take kada a nemeta a cikin gida, ga kuma uncle Taheer da ya biyo bayanta tasan za'a iya samun matsala.

Bu?e kofar ?akin nasa ya yi tare da fara fitowa, ya yi mata alamar ta tsaya bari ya duba ko akwai wani motsi a wajen!.

?an wawwaigawa ya fara yi domin dubawa.

Ganin babu kowa ne yasa ya yi saurin, yi mata alama da hannunsa a kan ta fito. A hanzarce ta fito, jikinta har kerma yake yi ?ar ?aniya, hannunta ya ri?o suka nufi hanyar komawa. Kamar wasu marassa gaskiya a duk in da suka ga mayaki na shawagi sai su la?e a wani wajen har sai kafa ta ?auke ta wajen sannan su cigaba da tafiya.

A bakin kofar bayan nasu ya dakata, da hannu ya nuna mata hanya a kan ta wuce kenan ba tare da ya furta kalma ba.

Da sauri ta wuce ita ma bata furta kalma ba, dan a tsorace take. Zuba mata idanun ya yi yana kallonta har ta shige ciki ta rufo kofar. Ya ?an jima tsaye a wajen kafin daga bisani ya ?an matsa ka?an.

Ita kuma tana shiga ta hango King ya fito daga part ?in Mommarta zai shiga na mama, tasan ita yake nema hakan yasa dabarar guduwa part ?in Akka ya fa?o mata, tasan idan ta shiga part ?in Momma to zai gano ta fita, saboda ai ya duba wajen da farko bata nan, shi ne yasa ta gudu wajen Akka ta haye gadonta ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda wasu kattin gani kasheni suka biyo ta sha da kyar.

To kun ji yadda aka yi, mu cigaba da labarinmu.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...???????

?angaren Jawad kuwa, yau kusan a ?akin Chuchun ya kwana, domin kuwa lokacin da ya ha?e bakinsa da nata, ya kasa iya aikata abin da yake da niya wato kissing ?inta, ya kuma ?asa iya rabata da jikinsa, shiru suka tsaya ita tana jiran ta ji me kuma zai yi mata, shi kuma Allah ne ka?ai yasan me a ransa.

A dai'dai wannan lokacin King ya yi knocking na kofar ya zo neman Auta. Ba ?aramin razana suka yi ba, domin kuwa dukkansu sun san dole King ?in ne, idan ba shi ba babu wanda zai zo a cikin wannan dare ya buga mata kofa.

Tuni Yah Jawad ya dawo cikin hayyacinsa, kamar dai yadda ya yi ranar yau ma hakan ya yi, cikin toilet ya shige ya ?uya, ita kuma ta haye saman gado da sauri ta shige cikin bargo tana zare idanu kamar antare ?era a tarko, yanzu kam ta yarda ba mafarki take yi ba ?ar ?aniya.

A karo na biyu King ya kara yin knocking jin na farko shiru ba'a amsa ba.

Shiru ta lume a cikin bargon har da rufe kanta irin idan ma ya shigo ya ce barci take yin nan, kai Chuchu ma fa ?ar duniya ce wlh, tasan komai kawai shiru take yi.

A karo na uku ya sake knocking, shiru da ya ji ba alamar motsi ne yasa ya mur?a handle ?in kofar ya tura ya shigo.

Daga bakin kofa ya ?an tsaya yana kallonta, kowani ?ansa yasan kalar perfume ?in da yake amfani da shi, saboda yawan zaman da suke yi a tare da shi, so ya ji mamakin jin kamshin perfume ?in Jawad a cikin ?akin, ga shi kuma ya ga Chuchun barci take yi.

A ransa ya furta zan kamaka ne, da ni kake yi Jawad, wato idan mun ce maka kana son Jannat sai ka ce mana ba haka ba, ko jiya mun yi maganar nan da Abbas, shi ma ya kafe a kan lallai son Jannat kake yi, in muka yi maka magana kuma sai ka ce mana bahaka ba, amma ka iya zuwa mun ?akinta cikin dare ku sha hira ba? Ina nan lokacin yin maganinka ya yi, Allah ya kaimu da safe.

Karisawa ciki ya yi yana zancen zucin nasa, cike da so da kaunarta ya haye saman bed ?in, tana jinsa ya fara tofa mata addu'oi kamar yadda ya saba yi masu kullum. Bayan ya kammala a fili ya furta Allah ya yi masu albarka ya cigaba da basu kariya.

A cikin zuciyarta ta amsa mashi da amin. ?asa ya sauko ya nufi waje.

Yana fita Jawad ya fito, a saman bedside drawer ya zauna tare da fa?in. "Gaskiya ya isheni wasan ?ar tsere da nake yi da dad, dole na ?auki mataki a yanzu, dole kawai na gaya masu gaskiya dan su mallaka mun ke na huta ki huta".

Shiru ta yi bata amsa mashi ba, ta yi kamar ta yi barci da gaske. Hannunsa ya kai ya yaye bargon da ta kudundune a ciki. Idanunta a datse kamar mai barcin gaske, sai dai kuma shi barcin karya asirin mutum tonuwa yake yi ida ya yi shi.

"To kaunaty sai ki bu?e idanun naki ai, bama ki iya barcin karyar ba, ji yadda eyelashes ?inki suke kerma". Can ?asan ma?oshinsa ya yi maganar.

Turo baki ta yi, ba tare da ta bu?a idanu ba ta furta. "Kai Yah Jawad me haka ne wai? Na yi barci na kazo ka tasheni".

"Tom shikenan ayi hakuri, cigaba da barci ni ma bari na je nayi nawa barcin".

Jin ya furta kalmar tafiya ne yasa ta yi saurin waro idanu tare da mi?ewa zaune. "Kai Yah Jawad dare fa bai yi sosai ba, yanzu karfe 12 ma bata cika ba ne zaka tafi?". A shagwa?e ta yi maganar.

Cikin zolaya ya ce. "Awww dama a duniyar mafarki ma akwai time ne? Ko dai yanzu kam kin gane ba mafarki bane?".

Hannu tasa ta rufe fuska na rashin kunya tana ?an sakin murmushi, kumatu a kumbure cike da iska data hura ta ce. "Kai Yah Jawad nasan ba mafarki bane yanzu, kuma ni ka dai'na tsokanata".

"Eyyeeee Jannat matar Jawad, dan ni aka haifeki, kin ma ji sunanmu kusan iri ?aya, Jannat and Jawad". Yana magana yana murmushi cikin sigar zolaya.

"Kai Yah Jawad ni ban san yaushe ka zama haka na".

?an matsowa kusa da ita ya yi. "Tun lokacin da Jannat ?ita ta fara girma na zama hakan". Kamar mai ra?a ya yi maganar.

Pillow ta ?auka ta jefa mashi a fuska tana ?an dariya maras sauti sosai.

Bai bari pillown ta sau?a a face ?in nasa ba ya ri?eta tare da ?an kara matsowa kusa da ita.

"Idan kina turo mun wannan ?an bakin kina sakawa na ji ina bu?atarsa, kwanta ki yi barci sai da safe". Yana kai karshen maganar ya mi?e tsaye.

"Yah Jawad meyasa zaka tafi yanzu?". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

"Saboda dare ya yi". Ya bata amsa a takaice.

"Tom shikenan ka kula mun da kanka, sannan ka yi mafarkina".

Jinjina mata kai kawai ya yi alamar to ya ji, baya son sake yin magana dan kada ta tsayar da shi. Kwanciya ta koma ta yi ya ja bargo ya rufa mata izuwa wuyarta, sannan ya tofa mata addu'oi kafin ya manna mata sumbata a goshi.

Kofar fita ya nufa ba tare da ya sake furta kalma ba, da kallo ta bishi har ya fice ya rufo mata kofa.

Yana fita ta mi?e ta ?auko remote daga cikin drawer bedside, kashe wutar ?akin ta yi, ta koma ta kwanta bayan ta ajiye remote ?in.

Yana shiga room ?insa shi ma ya haye saman bed, sai dai kuma ya ?asa iya yin barci, tunaninta ya tsaya mashi a rai. Kamar yadda ya ga rana haka ya ga dare......... To asuba ta gari malam Jawad namu na zamani jikan Akka tamu ta amana.

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...???????

Shirye suke cikin uniform ?insu gaba?aya ?an'matan, suna zaune a saman dining table chairs dake part ?in King, su momma kowa yana zaune, Akka ma tana wajen, yau sun ha?u fa, ga uncle Jahiz and uncle Abbas.

Sai kallon uncle Jahiz mammie take yi tana ayyana yadda zamansa zai kasance shi da Aliya bayan an ha?asu aure. Ita kuwa Aliyah ayyanawa a ranta take yi yadda zamanta zai kasance da King Zuhair.........E lallai wa?an nan sun yi nisa, akwai cakwakiya gaskiya.

Cikin nutsuwa suke cin abincin nasu, gaba?aya room ?in tsit kake ji, babu abin da yake tashi a cikin face ?arar spoons. Kuyanga Zubaida sai aikin serving ?insu take yi, duk wanda yake da bukatar zai ?ara wani abin haka zata ?ara mashi.

Guyson dai yana zaune kusa da Mommarsa, har da wani ?an kwantar da kansa a saman shoulder ?inta, kamar kullum ya dauki wannan kwalliya tasa mai ru?ar da masu kallo su yi ta santin kyansa, kansa sanye da hular sanyi mai gashi sosai a jiki, ya yi shiru baya ma cin abinci, shagwa?a kawai yake ta aikin zubawa Mommar tasu tana biye mashi, dan son da take yi mashi na daban ne, musamman ma yadda ta sha wahala a kan na wannan ciwon cikin nasa, shiyasa yake manne mata, saboda ya saba idan ta je Dubai ciwonsa ya tashi to wlh duk girman nan nasa yana saman jikinta, ko lafiyarsa lau ma yana jikinta kullum abinsa.

Yaki cin abinci wai sai anjuma around 9 zai yi breakfast sai ya sha magungunarsa, dan dole suka ha?ura suka kyalesa, amma sun so ya yi breakfast a lokacin.

Rizwan yana cikin room ?insa yana zuba barci, bai fito ba, dama shi baya cin abinci a tare da su, shi kansa Jawad idan baku manta ba tafiyar Jaish yasa ya fara shiga cikin iyayen nasa suna ci a tare domin ya rage kewar ?an uwan nasa.

Shirye cikin wani irin luxury pea long coat, daga ciki kuma tuxedo shirt ce mai bala'in kyau fara tas, ?asa kuma blue jeans ne kalar pea coat ta sama. Ya shigo wajen, sai tashin kamshi yake yi kamar anyi ?arin perfume a jikinsa, bakinsa a ?auke da cikakken sallama, cikin nutsuwa ya shigo.

King and Uncle Jahiz har suna ha?e baki wajen amsa mashi sallamar. Sai a lokacin da ta gansa ne ma Akka ta tuna da dalilin da yasa ta kira su uncle Jahiz su zo, wannan yakin da aka yi yasa ta manta da dalilin, amma yanzu ma da ta tuna bata yi maganar ba, dan yanzu suna cikin tashin hankali na ?atar Spender daga hannunsu, yanzu ta Spender take yi ba tsayawa wani shirirta ita da jikokinta ba.

Tun da ya shigo take ta aikin satar kallonsa, ya yi kyau sosai, da alama office zai tafi, shi kuwa da yake ba kunya ne garesa ba, tun da ya shigo idanunsa a kanta, sai kallonsa King and Uncle Abbas suke yi ko a jikinsa.

Kusa da uncle Jahiz ya zauna yana ?agawa King gaisuwa, bayan sun gaisa sai ya dagawa uncle Abbas sai uncle Jahiz, sannan ya gaida Akka, da yake tana cikin tashin hankali sai bata tsaya wasa da shi ba, kawai ta amsa gaisuwar a takaice. Ya yi tunanin ko dai gigin tsufarta ce yau ma ya tashi take share mutane, hakan yasa bai wani damu da ganinta so silent ba, ya cigaba da gaisawa da iyayensa.

Gaba?aya jikokin nata sun sha madarar mamakin ganin yadda yau ta amsawa Yah Jawad gaisuwa kai tsaye kuma cikin sanyin murya ba tare da sun kai ruwa rana ba, abin da mamaki sosai gaskiya, a cikin jikokin nata kuma babu wanda yasan da batun ?atar Spender, bama su san menene shi Spender ?in ba.

Dannewa ya yi ya ?agawa su momma nasu gaisuwar, sannan suka yi musabaha da uncle Taheer.

Umarni ya yi wa kuyanga Zubaida a kan ta zuba mashi abinci da sauri dan zai fita ne.

Uncle Abbas ne ya ce. "Jawad ina Rizwan?."

"I think bai tashi ba daddy". Ya bada amsar yana ?auko spoon ?aya daga cikin wa?an da kuyanga Zubaida ta jeresu a wajen.

Cikin nutsuwa ya fara cin abinci, sai satar kallonsa take yi, shi kuwa tsaboda tsokana sai ya fara yi mata abin da ya saba yi mata idan suka zauna saman table, wato ya yi ta ta?a mata kafafunta da nasa kafar ta ?asan table ?in.

Duk abin da suke yi wlh King yana ganinsu tsab, kuma ya ci alwashin yin wani abin a kan hakan, jira yake yi su gama cin abinci zasu je su tattauna da uncle Abbas and uncle Jahiz a kan hakan, daga nan sai su yanke hukuncin da ta dace.

Sai da suka kammala cin abincin ne ya mi?e da nufin ya tafi office, dan sauri yake yi.

"Zauna ina da magana". Cewar King Zuhair.

Komawa ya yi ya zauna.

"Gaba?aya ku bani hankalinku a nan". Cewar King again.

Gaba?ayansu nutsuwa sosai suka yi, suka tattara mashi hankulansu ha?e da kallonsu a kansa.

?an gyaran murya ya yi tare da gyara zamansa, cikin ?asaita ta jinin sarautar ha?e da a dake ya fara magana kamar mai bada umarni.

"Sarina, Fanan and Aneesa ku shirya zuwa yamma zaku yi baki". Ya yi maganar idanunsa a kansu dan yaga reaction ?insu.

A fujaje Sarina ta zaro idanu, kamar zata yi kuka ta ce. "Dad baki kuma? To su waye?".

Fanan da Aneesa kuma kallon kallo suke fara yi wa juna ha?e da bin fuskokin iyayen nasu ma da kallo.

Cigaba da yin magana ya yi ba tare da kawar da kallonsa daga kansu ba.

"Na samu takarda daga masarautu daban daban a kanku, ?a ga sarkin Sudan ya turo mun sako yana neman wa ?ansa alfarmar a bashi dama yana son Sarina, a taron da aka yi jiya suka samu damar ganinku, so sun nemi alfarmar zuwa su ha?u da ku".

Ya ?an dakata da yin maganar yana kallon fuskokinsu gaba?ayansu har da iyayensu mata.

Duk cikin room ?in face ?in mama, Mammie and uncle Jahiz ne kawai suka nuna alamar basu ji da?in maganar ba. Shi uncle Jahiz abin da yasa bai ji da?in hakan ba shi ne, a ganinsa an yi masu sauri, wai basu girma ba, Sarina almost 20 to 21 years take da shi a yanzu a duniya, amma haka yake cewa basu girma ba, dan kawai shi boko tafi arabiya yawa sosai a kansa, kuma shi girman cikin turawa ne ba larabawa ba sai yake ganin aibun hakan.

Ni kuwa nace to yau dai su Omaid basa nan waye zai taya Sarina koran wannan ?an sarkin da zai zo? Akwai matsala to! Za dai muga ya zasu kaya, dan dai da alama ba zata so shi ba tun da ta fara da complain tana ?aure fuska.

Cigaba ya yi da cewa. "?a?an sarakuna ne mabanbanta suka nuna sha'awarsu na son ha?a danganta da mu, sai dai sai da na za?i wa?an da suka dace ne na basu izinin su zo ku gansu su ganku ku tattauna a tsakaninku, dan haka sai ku shirya".

Dawo da kallonsa a kan Momma ya yi, ba tare da ya basu izinin yin magana ba ya ?aura da cewa. "Rahilarh kema fa aiki ya ganki sai ki shirya".

?an zaro mashi idanu ta yi tare da cewa. "Aikin kuma? To aikin me?".

Tsayar da kallonsa a kanta ya yi. "Aiki a kan shirya Autata mana, a sa?on ai harda ita, ?a ga sarkin Egypt wai ya ganta kuma yana so".

Kun tuna guy ?in da ya bisu lokacin da ta fita daga cikin taro ita da Hoorain? To shi ne ya matsawa babansa a kan a nema mashi izinin ganawa da ita ha?e da aurenta, ya bi ya matsa shi da gaske yake yi har sai da aka yi mashi abin da yake so ya sakar masu mara suka samu damar yin fitsari.

Ai uncle Abbas bai san lokacin da dariya ta kubce mashi ba, wai ?ar Autar nan ce da yanzu take kirgan dangi ne wani zai wani turo ya ce a nema mashi izinin ?ansa na so?. To me zai aura a nan? Ita Auta yanzu yaushe ma tasan wani aure bare soyayya fisabilillahi?.

Ni kuwa nace tab aikuwa ba yaran yanzu ba, dan ku kuna can kuna wasu tunaninku na banza Auta kam ta jima a cikin kogin kaunar Hoorain ma idan baku sani ba, ai yaran yanzu da sanin komai ake haifarsu ato........??

Uncle Jahiz kuwa bakincikin ne ya hanasa furta kalma, dan sai ya ga abin nasu ma kamar da rai'nin hankali a ciki, idan ba rai'nin hankali ba yaushe yarinya kamar Autar nan zasu wani ce suna neman izinin aurenta fisabilillahi? Abin sai ya bakanta mashi rai, kawai dai baya son yawan magana ne yasa bai tanka su ba, dan idan ya ce zai bu?e baki to babu wanda zai ji da da?i a wajen, kuma shi da alama ya fi King and uncle Abbas ?aukar zafi da wuri, da alama shi ne ya ainahin gadar King Abdul Malik, wato marigayi babansu kenan.

Yah Jawad da ransa ya ?aci shi ma a kan batun autar ne ya ce. "Dad Auta kuma? Amma dai wannan bashi da hankali ko?".

Uncle Taheer da ya gama zuwa har wuya da ?acin rai ne ya ce. "Dad ga dukkan alamu bashi da hankali ko dai babu ?wa?walwa ma a cikin kansa mai gaba?aya, idan ba dabbanci ba yaushe Auta ta isa aure? Kuma ko ta isa aure ma sai aka ce mashi bata da masu sonta ne da zai wani gwada mana shi ya isa?".

Sarai Momma ta fahimci maganganun uncle Taheer akwai wata a ?asar zuciyarsa, shi kansa King ya fahimci haka duba da yadda uncle Taheer ?in ya wani harzu?a ya hayayya?o da masifa kamar anfa?i wani abin da ba dai'dai ba, daga tambayar aure ai ba bashi aka ce za'ayi ba yake wannan surfen masifar.

Shi ma Yah Jawad ya fahimci ina uncle Taheer ?in ya dosa, shi kuwa uncle Jahiz da ra'ayinsa baya son auren wurin sai ya yi tunanin kawai halinsu ne yazo iri ?aya da uncle Taheer ?in, bai kawo komai a ransa ba!.

Su Sarina da suke zaune shiru ne Mummy ta ce su tashi su je abinsu, su tafi kada lokacin tafiya school ya wucesu su yi latti, su dai su sani suna da baki da yamma kamar yadda dad ?insu ya fa?a.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull