Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 12
Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 12: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 12. Ta jima a gidan sai la'asar liss sannan ta musu…
3,288 words
Ta jima a gidan sai la'asar liss sannan ta musu sallama ta fito za ta tafi lokacin Meenal tana ta aikin munfurci ita kuma Hajiya tana yaba mata a nata ganin taimakawa Momi take. Bayan tafiyarta suka zauna suna ta tsara yadda abubuwan za su kasance idan Meenal ta shiga cikin gidan.
Hajiya tana fita daga nan gidan da ta tari napep sai gidan Sadiya, Sadiya tana tuƙa tuwo lokacin Kalifa yana wasa saboda ya ɗan ji ƙwarin jikinsa ta jiyo Hajiya tana kwaɗa sallama, amsawa ta yi tana mai tasowa daga bayan ta rufe tukunyar dama ta gama tuƙa tuwon. Tun da ta shigo take yi wa gidan wani kallo na rainin wayo tana wani tattaɓe baki Kalifa kuwa kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kai shi kuwa da yake ba wani shaƙuwa ya yi da ita ba wasan sa yake ko wajenta bai nufa ba.
Sadiya cike da ladabi ta ce
",Sannu da zuwa Hajiya" Bata amsa ba ta ce
"Ke dai Sadiya ki ji tsoron haɗuwarki da Allah"Sadiya tana kallonta tana jiran ƙarin bayani don ita bata ga abin da ta yi da za a mata wannan furucin ba a nata ganin ita ce ya dace da ta jefe su da wannan kalmar. Hajiya bata jira cewar Sadiya ba ta ɗora da faɗin
"In banda shegen son kuɗi kike ɗorawa yaro jinya ga yaro nan yana wasa amma har kina ikirarin kai shi asibiti wannan da maraya ne Nasir ba na raye kika aure shi da ya taɓa ya ji gabaɗaya sai kin talautashi a shegen kawo buƙatun naki!" Sadiya kai ta sunkuyar ƙasa ta rasa ma abin da za ta ce mata amma duk da haka sai ta yi ƙarfin cewa
"Wallahi bashi da lafiya ai shi Abban nasa ya...
Hannun da Hajiya ta ɗaga mata ne ya saka ta haɗiye sauran maganar da ta guntso a bakinta. Hajiyar ta ce
"Ai komai ya kusa zuwa ƙarshe zai auro mace mai ladabi da tsoron Allah, mai tattala masa dukiya wacce ta san darajar dangin miji wacce za ta ɗaukeni tamkar ni ce silar zuwanta duniya" Idanu Sadiya ta ɗaga ta kalleta ta haɗiye ɓacin ran da ya ziyarci zuciyarta, don ta ji ba daɗi da ta lissafa abubuwan kenan duk waɗannan abubuwan ita bata da shi, ta ce
"Hajiya ki shiga ɗaki mana baki zauna ba kina tsaye" Baki ta taɓe ta ce
"Ai tuni aka bani wurin zama a inda aka san darajata, aka bani ruwa ana girmamani ai in sha Allah shekara ba za ta rufa ba sai Meenal ta tare a gidan Nasir!" Tana faɗar hakan bata jira komai ba ta juya ta fice daga gidan ta bar Sadiya tsaye tana maimaita sunan Meenal a zuciyarta ita dai Meenal ɗaya ta sani ƴar gidan ƙawar Hajiyar don ta taɓa zuwa gidan ma ita da su Husna lokacin tana amarya suka zo.
Juyawa ta yi ta nufi wajen tukunyar tuwonta, a ranta tana mamakin mutum nawa take aure, Nasir ya ci zarafinta ƴan uwansa ga kuma mahaifiyarsa su basu ma san auren ya fice mata a rai ba don bata da yadda za ta yi ne.
*GIDAN BABA*
Wajen ƙarfe goma na safe Baba ya fito daga ɗaki yana gyara zaman babbar rigarsa ya janyo ƙofar ɗakinsa ya rufe ya kalli Mama Habiba da take wanki ya washe baki ya ce
"To mu fa Allah ya yi aure da marar kwabo za mu tafi na san yau dai ɗari biyar ɗina da nake sayan awarar rana ta huta" Ɗagowa ta yi daga wankin da take tana masa kallon rashin fahimta ta ce
"Yau ɗumaman tuwon safen ne ya ƙosarka sosai da gar ba za ka buƙaci abincin rana ba?" Wata dariya ya yi irin ta ba za ki gane ba ne ya ce
"Ana ga yaƙi ke kina ga ƙura!. To Baban abokin abokina ne ya rasu kuma gidansu masu mugun kuɗi ne wato uban ya bar tarin dukiya kin san kuwa wajen zaman makokin za a ci jar miya, ni ban ma taɓa ganin wanda Baban nasa ya mutun ba kawai dai labari abokina ya bani cewa jiya sun yi ciye-viye da suka je gaisuwa shi ne na masa Allah annabi ya rakani in yi gaisuwa, kin ga gwara mu tafi tun da wuri da zafi -zafi ake bugun ƙarfe sannan da sanyin safiya ake kama fara" Duk abin da yake faɗa matan gidan da suke cikin ɗaki kowa yana jinsa kasancewar shi ba ya magana a hankali, fitowar Sumy daga ɗaki ne ya dakatar da Mama Habiba daga maganar da take son yi ta ce
"Baba don Allah ka bani kuɗi zan saya maganin guduwa kwana na yi ina yi" Kamar wanda ta watsa masa wuta a take ya fitittike yake masifa annurin fuskarsa ya dishe ya ce
"Ah uban gudawa kike ba gudawa ba Sumayya, ku babu dama ku ga mutum sai ku ringa jero masa buƙatunku, shin ina uwarki ma take ko ni kaɗai na haife ki? Wallahi shi ya sa kullum nake fatan Allah ya bani ɗa namiji ko kangararre ne duk tsiya ya taimaka mini amma a ce ƴaƴa mata kitika-kitika sun cika mini gida har baba gane su tsakaninsu da iyayensu mata to duk sun girma sun yi kwantai kowa sai dai ya kawo maka buƙatu ba zai taimaka maka ba...
Mama Habiba ta ce
"Haba dan Allah, yanzu ina amfanin wannan maganganun da kake" Baki sake yake kallon Mama Habiba kafin ya juyo bayansa cike da gatse ya ce
"To uwata Habiba ai sai ki min hukuncin duka" Ɗan baya ta ja tana faɗin
"Ni ban ce zan dake ka ba amma dai wasu maganganun basu da amfanin faɗa ƴaƴa mata ai rahma ne" Wata harara ya jefa mata ita kuma ta ɗauki ƙaramar jakarta da take ajiye a gefe ta buɗe ta ɗakko naira ɗari ta ba Sumy ta ce ta je ta saya maganin.
Juyawa Sumy ta yi tana wani taɓe baki a ɓoye tana aikawa Baba harar ƙasan ido ta koma ɗakin. Malika ce ta fito daga ɗaki sanyi cikin doguwar rigar dakakken leshi mai tsada sai ƙaramin mayafi da ƴar jaka ta yi kyau abinta ganin Baba sai da gabanta ya faɗi don ita da ta jiyo muryarsa lokacin tana shiryawa tunaninta fita ma ya yi dab gidan. Gabanta yana faɗuwa amma sai ta ji ya ce
"Ke ina za ki je haka?" Ya faɗa yana kallon shigar jikinta duk da ya san mahaifiyarta bata da kuɗin da za ta saya mata kayan sannan iya ma yarinyar haka amma ba zai tuhume su inda suke samun komai ba shi dai ɗawainiyarsu ce ba zai ɗauka ba in ya suke samu ma wannan ba damuwarsa ba ce
Cike da ɗan jin kunya ta ce
"Wani Alhaji ne yake jirana a waje" Wani irin washe baki ya yi ya ce
"Allah sa ya miki maganar aure" Ɗan shiru ta yi sai kuma ta ce
"Eh ya ce aure lokaci ne amma dai da shirin aure ya zo"
Baba ya ce
"Haka nake so, akwai kati a wayarki? Ina so na yi waya bani da kati" Kai ta gyaɗa masa tana mai cire pswrd ɗin cikin hanzari ta yi saurin fita daga wtsapp ɗin don ta ga tana ma cikin acc ɗin Alhajin inda suka gama hirar banza da ture-turen hotunan banza, tana fitowa ta bashi wayar ya karɓa ya fito da tasho wayar ya kwafi lambobi ya danna kira ya kara a kunne, abokinsa ya kira yana faɗa masa ya shirya shi kuma ya faɗa masa inda za su haɗu su wuce gidan makokin. Wayar ya kashe zai miƙa mata sai ya ga hoton kan wayar hoton ta ne da wani mutumi Babban mutum suna cikin mota a zaune ta ɗora kanta a gefen kafaɗarsa suna dariya, jim kaɗan ya yi yana kallon hoton ita kuma gabanta yana dukan uku-uku sai dai kuma sai ya ga hakan ba komai ba ne tun da ba wani abu ya gani ba sannan ya tuna ta ce zai aure ta don yana tunanin shi ne Alhajin da ta ce yana jiranta a waje.
Yana bata wayar ta juya ta fita, Mama Habiba tana jifansa da kallon Allah wadaran naka ya lalace, a ce wai kai baka sayawa yaro sutura ba baka saya masa waya ba amma kana ganinsa da abubuwan da sun fi ƙarfin ya mallake su ba za ka tsawatar ba ko ka tuhume shi a kan abun.
Yana baza babbar riga ya juya yana nufar hanyar ƙofar gidan ba tare da ya yi wa sauran matan sallama ba ya ce
"To mu sai Allah ya dawo da mu" Mama Habiba ta ce
"Allah tsare" Ko amsawa bai yi ba ya nufi ƙofar yana sauri so yake ya cimma Alhajin da Malika ta ce yana jiranta a waje ya je ya masa maganar aurr cewa ya fito za a yi aure.
Malika ko da ta fita ta samu Alhajin yana jiranta a mota tana wani yauƙi da rawar kai gaɗe da girgiza jiki domin yanzu ta gane hakan ne yake ɗauke hankalin maza ƴan iska har su kai ga bata kuɗi ta magance matsalarta, Alhajin kuwa wanda ya haife ta ya washe baki haɗe da miƙo hannu ya buɗe mata ƙofa ta shiga yana mata kallon ƙwaf tana magana tana iyayi ya ce
"Sai ina?" Kallonsa ta yi cike da masa wani kallo ta ce
"Sai inda muka saba zuwa" Haɓa ya sosa yana sakin shu'umin murmushi domin ya gane Hotel za su je, yana ƴar dariya ya ce
"Baki da dama Baby Malika" Suna cikin haka ta hango Baba ya taho yana ɗaga babbar riga da sauri ta ce su bar wajen, haka Alhajin ya ja motar Baba sai ƙurar ya tarar a ransa yana faɗin
' Za ka dawo ka same ni wataƙila ya je siya mata cakuleti ne, dole ka fito a yi aure kuwa ka ɗauki ɗawainiyarta' Ya faɗa yana kama hanya domun ya je wajen abokinsa su tafi.
Alhaji tun da ya ja motar suka tafi suna hirarsu, Malika tana jin yanzu ta samu sabuwar rayuwa ta huta da zama da yunwa ko kuma ɗauka ɗawainiyar kanta na abubuwan buƙata na rayuwa, tun da yanzu za ta bada mutuncinta a bata kuɗi a kuma mata duk abin da take so, shi kuma Alhajin yana ganin ya samu yarinya ɗanya sharaf tabbas a nasa tunanin ya tsinci damu a kala sai dai yana tuya yana mantawa da albasa wato akwai ranar ƙun dillanci domin duk abin da mutum ya yi wa ƴar wani shi ma sai an yi wa nasa ƴaƴan, shi yana ganin ya killace nasa ƴaƴa ya zo yana lalata da ƴaƴan wasu duk da su ma wanda ake lalatar da su da laifinsu don su suka siyar da mutuncinsu suka zubar da kima da darajarsu na ƴaƴa mata, domin ai sai bango ya tsage ƙadangare yake samun waje shiga!.
Baba tun da suka je gidan makokin basu samu ganin abokin abokin nasa ba, kaaancewar yana cikin gidan wajen wasu baƙi da suka zo haka suka samu waje a rumfa suka zauna suna ta hira ana zuwa ana gaisuwa. Har wajen sha biyu sannan suka samu suka ga abokin inda ya nuna jin daɗinsa da karamcin Baba na zuwa yi masa ta'aziyya duk da basu da wata alaƙa, bai san cewa cin banza ne ya kawo Baban ba wai gaisuwar Allah da annabi ba.
Har aka kira sallar azahar ba a kawo abinci ba, Baba sai doguwar hamma yake, idanun nan sun kaɗa sun yi jawur don hatta tuwon safe kaɗan ya ce yana tunanin abubuwan daɗin da abokin nasa ya faɗa cewa tun da ya je wajen gaisuwar ake sauke kayan motsa baki. Amma dai shi ban da ruwan roba da ya ga ana ta wadaƙa da shi a wajen bai ga komai ba, tun zuwansu daga an ɗan jima sai a fito da ruwan roba masu sanyi ana rabawa, mai raba ruwan ko da ya zo zuwan farko ya ba su Baba haka Baba ya karɓa ajiye a tunaninsa idan an fara kawo kayan daɗin zai sha ruwan idan ya ci tun fa lokacin babu komai a cikinsa ba ya jin ruwan ma zai samu wuri.
Sawu na biyu ma wani ya ƙara miƙo musu Baba ya karɓa ya ajiye suka zama biyu a gabansa, yana jiran tsammani, a rabo na uku mai rabawar ba miƙawa yake ba ajiyewa mutane yake a gaba ai kuwa ya zo ya ajiyewa abokin Baba yana shirin ajiyewa Baba ai kuwa Baba ya yi farat ɗaya ya ce
"Haba bawan Allah, ruwan nan kun kawo, kun sake kawowa tsakani da Allah dai ko shanaye ne mu ruwan da aka raba ya isa a ce ya kashe mana ƙishirwa, tun da muka zauna a wajen nan muke karɓar gaisuwa ana Allah jiƙansa muna cewa amin amma ku babu aikin da kuke sai ku shiga cikin gida ku jido ruwa kuna ba mutane, bakwa duba yadda idanun jama'a ya yi zuru-zuru haba ku tsagaita da bada ruwan nan tun da shi kaɗai za ku raba, in ba haka ba ni dai kar ka ƙara tunkaroni da ruwa na gabana ma ya isheni" Tun da Baba ya fara magana abokinsa Malam Lurwanu yake danne dariyarsa gudun kar ya saki dariya a wajen makokin a ce bai damu da mutuwar ba, duk da dai wajen dama gefe ne suke zaune kuma ana ɗan hayaniya ba a lura da abin da yake faruwa ba.
Mai raba ruwa cike da mamaki yake kallon Baba, hakan ya sa ya ɗauki ruwansa ya bar wajen, Baba wanda ya kauda kai gefe yana muzurai, babu abin da yake tunowa sai abubuwan da abokinsa ya bashi labari da kuma abin da ya faɗawa Mama Habiba amma gashi dai wankin hula yana son kai shi dare.
Ko da aka tashi yin sallar azahar abokinsa yana masa dariyar ƙeta a ɓoye, aka idar da sallar da yake ba masallaci aka je ba a nan wajen aka yi jam'i shi kuma abokin da aka yi wa mutuwar suna can suna ta karɓar gaisuwar jama'a. Ko da aka idar da sallah Baba yake yi wa abokin masifa wai sai sun tafi gida a nan ya ce masa su dakata wataƙila ko an yi jinkirin kawo abincin ne, ana jimawa aka fara kawo abinci da nama kala -kala Baba ya zage ganin banza ta faɗi ya ci abinci musamman naman da ya ci ya yi yawa, lemuka ma sai da ya saka biyar a aljihu fanta, cola, mirinda nutrimilk lacasera. Duk a aljihun babbar riga ya zunduma su daga an miƙo masa lemo sai ya karɓe bakin nan washa-washa da sai wangale shi yake. Sai da ala'sar sakaliya suka yi wa wa wanda suka je dominsa sallama, abokin Baba sai jin Baba ya yi da za su masa sallama yana faɗin
"To Allah jiƙansa, Allah sa kwanciya hutu ce sai goben idan Allah ya kaimu da abin aro za mu dawo" Amsa masa aka yi ana musu godiya.
Lokacin da Baba ya dawo gida ya nufi ɗakinsa ya ajiye lemukan nan, sai dai ciwon ciki yake damunsa tun a hanya ya fi zaton ko naman da ya ci da yawa ne ya saka masa ciki.
Wani murɗawa da cikinsa ya yi sai banɗaki yana can ya fito ya sake komawa zuwansa uku Sumy da take ɗakin Mama ta ji yana zabga mata kira yana faɗin
",Sumayya kawo min maganin gudawar nan da kika siya da safe"
*JIDDA*
Suna can ita da Salama suna ta hira abinsu, Kasim kuwa tun da ya faɗawa Ummarsa cewa ga yadda Babansa ya ce haka ta bashi baki a kan cewa ya yi haƙuri ya bar maganar don ya san cewa Babansa kaifi ɗaya ne ba zai lamunci wani abu ba bayan wanda ya yanke hukunci a kansa, sannan zai ga kamar ƙarya ce idan aka ce sai an kai a mota.
So yake ya sanar da Aliya halin da ake ciki amma kuma yana tsoron abin da zai biyu baya, saboda ya san sai ranta ya ɓaci amma duk da haka ya san ai umarnin mahaifinsa gaba yake da nata, hakan ya sa ya koma ɗaki ya kwanta yana ɗan jin fargaba yana fatan kamar yadda ta yi farincikin kayan saka rana wannan ma ya faranta mata rai fiye da wancan lokacin!.
Aliya dai ta gaji da zumuɗi ta ɗaga waya ta kira Kasim, Kasim ganin kiranta sai da gabansa ya faɗi da ƙarfi har kiran ya tsinke bai samu zarafin ɗagawa ba, kiran ya shigo a karo na biyu har ya tsinke bai ɗaga ba, sai faman kallon sunan ta da yake a saman wayar. A karo na uku ya yi ta maza ya ɗaga yana ɗagawa ya tsinci muryarta cikin farin ciki tana faɗin
"Hello" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, sai lokacin ya ji hankalinsa ya kwanta wannan alama ce ta nasara wato ranta bai ɓaci ba sanadin kai kaya a baro bayan ya mata alƙwarin kai kaya a mota kamar yadda ta buƙata, kuma da alama kayan ma sun birgeta hakan ya sa cike da ƙarfin gwiwa ya ce
"Barka da wannan lokaci amarya kuma sarauniyar zuciyata" A can ɓangaren Aliya ta murmusa lokacin da suke wayar suna saman wani katakonda suka taka ita da Amatallahi a ɗakin Umma suna window suna jiran ganin masu kaya don su ganewa idanunsu.
Cike da farinciki ta ce
"Na'am sarakin zuciyata" Ji ya yi kamar ya taka rawa don murna. Suna magana Amatulllahi tana musu tsiya wai basa kunyarta a daidai nan ayarin masu kawo kayan Kasim suka yi wa gidan su Aliya tsinke!. A kan idon Aliya mai tura baro mai ɗauke da akwari biyu da ƙaramin kit ya taho inda mutanen suna biye da shi, wani ihu Aliya ta saki wanda ya ɗauki hankalin Amatullahi ta juya ɓangaren da ta ga Aliyar ta kalla a take ta yi arba da abin da Aliya ta gani, Kasim kuwa ihun da Aliya ta yi sai da ya cika masa kunne ya fara tunanin mene ne wannan wanda ya saka ta farinciki lokaci guda kafin ya gama wannan tunanin muryar Aliya ta dawo da shi daga tunanin ta hanyar faɗin
"Kayan Jidda a baro aka kawo akwati biyu da kit" Take faɗa tana tuntsurewa da dariya, mamaki al'ajabi da kuma tsoro suka ɗarsarwa Kasim a zuciya mamaki na farko shi ne shin dama abu iri ɗaya suka ti shi da mijin Jidda da yake ganinsa bashi da wani hali sannan kuma shi ma a baro ya aika lefen ko kuwa? Tsoron da ya ziyarce shi kuma yana tunanin shin kenan ita Aliya bata ga nata lefen ba dama, kafin ya samu wannan amsar tambayar da yake yi wa kansa sai ya ji Aliya ta ce
"Kasim ina zuwa za mu yi magana an jima akwai gwarama" Kafin ya bata amsa ƙit ya ji ta kashe wayar.Zaman dirshan ya yi a saman katifarsa yana jin wani faɗuwar gaba yana fatan dai kar idan ta ga nata kayan ta ce ta fasa aurensa, tun da dai ya ga gashi nan tana yi wa Jidda dariyar an kawo mata kaya a baro.
A ƙofa mai baron ya tsayar da baron inda su kuma masu kawo kayan su Abba suke musu marhabin, a daidai lokacin wannan da Amatullahi da Aliya suka diro daga saman bencin da suka taka suka fito tsakar gida a sukwane suna haɗa baki wajen faɗi
"Umma wallahi kayan Jidda a baro aka kawo, kuma akwati biyu da kit" Daga Umma har ƙawayenta guda biyu wata guɗa suka saki a tare sai bayan sun yi suka tuntsure da dariya har da tafawa, kafi suka yi ayari suka shige ɗakin tare da su Aliya, domin su ƙyaƙyata dariya son ransu gudun kar su Abba suke jiyo tsegumin da za su yi.