Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 17
Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 17: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 17. A masallacin unguwar aka yi walima ranar yini da…
3,326 words
A masallacin unguwar aka yi walima ranar yini da yamma inda aka cika aka ɗakko malama juwairiyya ta yi wa,azi a kan biyayyar gidan aure, sai magriba aka tashi, duk da Aliya ta so Abba ya bari an yi bidi,a a bikin amma ina, don kafin ma a tafi walimar an sha hotunan amare da angwaye da kuma abokai da ƙawaye. Aliya tana ganin ta fi Jidda yin kyau amma dai kowa da irin nasa kyan.
Amare sun shirya tsaf sai ƙamshi suke, sun shirya cikin fararen laffaya mai goldin ɗin flowers sun yi kyau har sun gaji, Abba ya musu nasiha a kan biyayya da kauda kai a kan komai mutum ya ji kamar bai ji ba ya gani kamar bai gani ba. Umma sai hawaye take sharewa na rabuwa da yaran a fili amma a baɗini kukan rabuwa da Aliya take yi, sanna kuma tana kukan takaicin Jidda za ta tafi gidan jin daɗi da hutu.
Kasim ya kawo mutoci guda huɗu a inda motocin ɗaukan Jidda sun fi ashirin motoci ne na alfarma, sannan Abba ya ce a tare za a tafi idan aka kai ɗaya sai a wuce a kai ɗaya. Jama,a sun shiga motoci inda mota ɗaya aka saka amare a ciki sai iyaye guda biyu don amaren ne a tsakiya, Jidda tana kukan rabuwa da gidan a gefe ɗaya tana kukan tunano iyayenta musamman da ta kalli gidan da suka rayu da mahaifanta amma kuma yanzu gashi za ta tafi ɗakin miji ba tare da suna duniyar ba rayuwa kenan.
Motoci sun miƙa a kan titi suna tafiya a laye inda amare suke ta kuka abinsu. Gidan Jidda aka nufa inda yake unguwar GRA a ƙofar wani tanfatsetsan gida motocin suka fara tsayawa horn ɗin da aka saki a kusan tare-tare shi ne ya ankarar da Aliya da take zaune ta haɗa kai da gwiwa tana kuka wanda ya zama kuka biyu na rabuwa da Umma da na baƙincikin Jidda. Matan cikin motar ƴar uwar Umma da Abba ne suka haɗa baki wajen faɗin
"Kai jama'a wannan gida tamfatsi, tamkar ba a nigeri,a ba wannan ai shi ne aljannar duniya!". Aliya wacce maganar ta su ta saka ta faɗuwar gaba mai ƙarfi bata san lokacin da ta ɗago da kanta ba, don wannan furucin ya tabbatar mata gidan Jidda aka fara zuwa, domin ta san da gidanta ne ba za a faɗi haka ba, ɗago kan da za ta yi ya yi daidai da wangale get da mai gadin ya yi, motocin suka fara shigewa ciki a jere, a inda Aliya da ta ɗago ta sauke a kan wani haɗaɗɗan gida na masu aji kuma masu hannu da shuni, wanda ko ita bata taɓa tunin za ta shiga ba bare wata Jidda baƙa mummmuna!.
Ganin gidan ya sa hankalinta ya tashi irin tsaruwarsa da yadda wasu kyawawa fitilu suka masa ƙawanya, tana ganin hakan ta cikin laffyar da ta lulluɓa ita kanta bata san lokacin da ta cire lulluɓin ba, babu zato da tsammani ƴan cikin motar suka ji ta ce
"Wayyo Allah na shiga uku!!!".
MAMAN AFRAH
09025576222
https://chat.whatsapp.com/DNhoKsIb9qP8PlVQdpQ4BW?mode=ems_copy_c
*RUWA CIKIN COKALI*
(Ya ishi mai hankali wanka)
NA
MAMAN AFRAH
. *Daga marubuciyar*
*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*
*09025576222*
BOOK 1
PAGE 1️2️⃣
*SADIYA*
Tun da ta zauna take ambaton innalillahi wa inna ilaihi raji'un, tashin hankalinta ruɓanya yake idan tana tuna cewa Nasir ba ya son haihuwa kuma ko ɗazu yana nannagon ta , sannan tun yanzu tana ita kaɗai da ɗa guda ɗaya yana nuna gajiyawa da ɗaukan ɗawainiyarta bare kuma aka ce ta sake haihuwa, mutumin da yake batun ta kama sana,a don take tallafawa a cikin gidan bayan kuma ko ciyarwa ƙauro yake sai abin sa ya ga dama zai bayar.
Hannu ta ɗaga idanunta yana zubar da hawaye ta ce
"Ya Allah kai kake bayarwa, kuma kai ne kake hanawa, wasu bayinka suna neman haihuwa baka basu ba, ina godiya da ka bani kuma ka ƙara min, ya Allah bam gajiya da kyauta da ƙarin da ka min ba,ya rabbi ka sassauto da zuciyar Naasir kar ya wulaƙantani a kan cikin nan" Tana gama faɗar hakan ta koma ta jingina da jikin kujera tana ta saƙa da warwara kan cewar ta sanar da shi ko kuma ta ƙyale shi, idan ra sanar da shi ba tira za ta yi daga matsalarsa ba sannan idan ta ƙyale ɗin ma akwai ranar ƙin dillanci tun da shi ciki ɗan duba ne duk daren daɗewa, zai bayyana kansa!.
Bayan kwana biyu bata faɗa masa ba, tana nan tana ta nuƙu-nuƙun sanar da shi tana tsoron abin da zai biyo baya, saboda haka ko yana gidan idan ta ji amai yana yunƙuro mata sai ta yi ta dannewa tana addu'ar Allah rufa mata asiri kar ya gane, saboda idan ya sani a ɗaya za a yi biyu ko dai ya sake ta ko kuma ya ringa ƙuntata mata a cikin gidan. Bayan sati guda da sanin tana ɗauke da ciki har lokacin Nasir bai san wainar da take toyawa ba, ita kaɗai ta san tana da ciki sai kuma ƙawarta, amma duk wani laulayi da take fama da shi dannewa take duk ta yi baƙi ta rame. A wata ranar alhamis ne bayan ya fita dama yau bata ga ya yi shirin fita kasuwa ba, zuwa can sai ta ji daga windown ta da yake ta waje ana cewa daga nan za a ajiye bulo, da siminti ta yi mamakin masu ajiyewar don bata ji muryar Nasir ba hakan ya bata tabbacin ko dai wasu ne suka kawo ajiya.
Bayan kamar awa guda ta ji ƙaran babbar mota, motar bata tsaya a ko ina ba sai ta ji ƙaran tsayawarta a ƙofar gidan, motar yashi ce don haka tana ji aka juye yashin motar ta tafi. Muryoyin mutane ta ji sai kuma ta ji muryar Nasir yana cewa su kwaɓa yashin da siminti sai kuma ta ji an turo ƙofa wasu matasa suka yi sallama sai ta ji Nasir tana cewa su shigo da shi, tana ɗaga labule ta ga bulo ne suke ta shigowa da shi, hakan ya bata tabbacin ginin ɗaya part ɗin ne za a tada da alama auren nasa ne ya kusa.
Bai sanar da ita cewa za a yi aiki ba, don haka sai take saka hijabi idan za ta fito tsakar gidan, haka ma,aikata suka fara aikin ƙarasa ginin nan tuƙuru ita dai babu wanda ya ce mata ita ma kuma bata ce ba.
Cikin sati ɗaya aka gama komai na ɓangaren, an saka ƙofofi an yi fenty hatta wuta an ja ɓangaren, da yake har da ɗakin Nasir ɗin mai bayi a ciki, ɗayan kuma ciki da falo ne da banɗaki a ciki. Ita dai bata ce komai ba tana ganin ikon Allah.
Ranar wata juma'a da safe tana zaune haka kawai ta ji tana jin amai ta yi iya ƙoƙarinta na ta dakatar amma abin ya ci tura, haka ya sa ta fita da sauri ta shiga sheƙa aman, kamar an jefo Naair sai ganinsa ta yi ko riga babu ya zo ya tsaya yana wani zazzare idanu ko aman bai tsaya mata ba ya buɗe baki cikin hargowa ya ce
"Wai aman mene ne kike yi bayan lafiyar ki ƙalau?" Tambayar ta kiɗima ta haɗe da ruɗa mata ciki don ta ji tsoro sosai don da alama ko ya fahimci wani abu dangane da ita. Sai da aman ya tsagaita mata ta wanke bakinta da fuskarta a famfon wajen duk ta galabaita a daidai lokacin ne ya sake jefo mata wata tambayar tamkar zai hau ta da duka.
"Sadiya na ce aman uban mene ne kike yi?" Idanu ta ɗaga tana kallonsa ƙirjinta yana dokawa da ƙarfi, ta san dai ko da a ce cikin ne ai ya san ba a waje ta samo ba, tun da sh ne maijinta kuma shi ne mai yawan buƙata kullum abu ɗaya, sannan ai ita ba za ta hana ubangiji ikonsa ba.
Bakinta ne ya yi nauyi tana tunanin ta ina za ta fara, kafin ta samu ƙarfin gwiwar amsa masa, don a ganinta baƙin alƙalami ya bushe, kawai ya kamata ta sanar da shi in ma yankata zai yi to gwara ta faɗa ta fita daga zulumin da take kwana take tashi da shi tamkar wacce ta yi cikin shege!.
A hargitse ya ce
"Idan baki faɗa min ba wallahi na lahira sai ya fiki jin daɗi in har ya yi aiki mai kyau!" Cike da karkarwar baki ta ce
"Lafiyata ƙala...Tun kafin ta ƙarasa faɗa ya katse mata hanzari da faɗin
"Yanzu ba lafiyarki nake tambaya ba aman mene ne?" Kamar zuciyarta za ta fasa ƙirjinta ta fito haka ta ji ganin yadda yake zare ido, a take ta fara tunanin cewa dama haka wasu matan suke fuskanta idan mazajensu basa son haihuwa? Kuma ya kasance macen ta samu ciki haka suke shiga fargaba da tashin hankali?.
Maganarsa ta katse mata tunanin inda ya ce
"Wai ba magana nake miki ba Sadiya? Wato kin mayar da ni kare in yi ta haushi?" Cikin inda -inda ta ce
"Ci...ci...ciki ne da..." Wata wawiyar tsawa da ya doka ita ce silar tashin Kalifa da ya koma baccin safe sai kukansa ta ji,
Nasir ya ce
"Wato kin samu ciki shi ne kike ƙunbiya-ƙunbiya baki faɗa mini ba, wato ga Nasir ɗangote ko Nasir A A Rano shi ya sa za a ke mini haihuwa a kai-akai tun da ni me dukiya ne ko? Ɗan rufin asirin da Allah ya mini kike so sai kin kwantar da ni Sadiya ki tara min ƴaƴa tsufa ya hau ni, a zamana bani da kataɓus sai ƴaƴa to wallahi baki isa ba!" Ya faɗa yana nunata da yatsa, fitowar Kalifa ya sa ya kalli Kalifan yana sakin wani wawan tsaki, shi kuma Kalifan da sauri ya kauce daga hanyar da Nasir ɗin yake tsaye ya yi wajen Sadiya yana ɗan kuka tare da murza idanu.
Fuuuu ya juya tamkar zai tashi sama, ɗaki ya shiga jim kaɗan sai gashi da rigar a hannu haɗe da singlet, a ƙofar ɗakin ya saka singlet ɗin ya ɗora rigar hannunsa riƙe da waya ko maɓallin rigar bai ɓalla ba hatta takalminsa tana gani a baibai ya saka, ƙofa ya nufa sai jin rufowar ƙofar gidan ta yi gararaf!.
Kalifa ta kama ta tsayar a gefe ta wanke wajena ta ɗakko shi suka nufo ɗakin, tana zuwa ta zauna a kan kujerar Kalifa yana kan cinyarta, bata ankara ba sai ta ji hannun Kalifa a kan fuskarta yana share mata hawaye, kallonsa ta yi tare da rungume shi, tana jin son ɗan nata har ciki ranta, tana rayawa a ranta ta san komai daren daɗewa za ta fita daga cikin wannan uƙubar, sannan tabbas ta san Nasir ranar nadama tana zuwa zai gane shayi ruwa ne, amma dai a juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe, don rayuwa tana cike da darasi ne sai dai mutum bai ga damar ɗauka ba, amma a kowane sakan a kowace awa akwai abubuwan da mutum zai koya kuma ya gane sai dai ruwansa ne ya yi aiki da shi ko kuma ya watsar amma dai shi ubangiji mai yin hisabi ne a kan komai!.
Wajen ƙarfe goma ta ji an turo ƙofa, sallamar Hajiya ce ta fara tashi a cikin gidan, cike da ladabi Sadiya ta amsa, sai dai fitowarta daga ɗakin domin yi wa Hajiya iso lokacin Kalifa yana biye da ita dama wanka ta masa tana shafa masa mai. Gabaɗaya fuskar Hajiya a haɗe take tamkar an faɗa mata mutuwa ko wani mugun abu, amma sai Sadiya ta daure ta ce
"Sannu da zuwa Hajiya bismillah ki shigo" Wani kallo ta jefi Sadiyar da shi ta ce
"Ba abin da ya kawoni ba kenan, ko an ce miki zama na zo idan zaman nake son yi in zauna a gidana a ɗakina mana, kin san dai ai kujeruna sun fi naki komai sau miliyan" Sadiya ta ji babu daɗi a ranta amma sai ta danne ta yi murmushin yaƙe wanda iyakarsa leɓe ta ce
"Haka ne sun fi nawa " Wani kallon ke kika sani Hajiya ta mata ta ce
"Nasir ya je mini da wata maganar banza wai ciki ne da ke" Abin ya yi wa Sadiya ciwo wato cikin sunna ne ma maganar banza hakan ya sa ta ce
."Eh gaskiya ne" Hajiya ta ɗan yi mamakin amsar da Sadiya ta bata duba da Sadiyar bata fiya kausasa harshen ba amma amsar tata sai ta ji tamkar dai a fitsarance ta yi amma sai ta ce
"To abin da nake so da ke shi ne, mun yanke shawara da Nasir da ƴan uwansa cewa wannan ciki zubar da shi za a yi" Da sauri Sadiya ta ɗago kai tana kallon Hajiya cike da mamakin kalamanta.
*BABA*
Duk kiran da yake yi wa Sumy tana jinsa amma ta ƙi amsawa hakan ya sa ya fara rafkawa Mama Talatuwa kira, Mama jin kiran ta tunkari ɗakinsa tana zuwa ta ganshi a ƙasa a kwance yana sharɓa uban gumi ta ce
"Subhanallahi Malam lafiya" Baba da ya buɗe baki zai bata amsa jin gudawar ta taho sai ya ji tamkar idan ya buɗe baki kashin zubowa zai yi bai yi wata-wata ba ya sake komawa banɗaki, sai gashi yana tafiya yana ɗan sunkuyawa yana dafa bango yana faɗin
"Wayyo Allah, gaskiya gudawa bata da daɗi ko in ce bata da imani, kalli yadda ta ƙarar min da ƙarfi lokaci guda, ɗan katan daɗi da na ci duk ta saka na kai masai(Toilet ) Haba ai sai na gwammace daman awara na ci don ji ba don idan ban yi gudawar nan ba a wando za ta zubo da ba zan yarda in yi kashin abinci ƴan gayun nan da na ci ba" Tana ta kallonsa har ta samu ya zauna tana son amayar da magana amma tana tsoron masfifarsa sai da ya zauna da sauri ya zame ya kwanta yana cew
"Ni wallahi ina ga mazaunan nan nawa ba za su zaunu ba ma, kai jama,a lokaci guda mutum lokaci guda ba mutum ba"
Mama Talatuwa ta ce
"Dama haka cuta take yanzu mutum yanzu gawa... Kafin ta ƙarasa ya ce
"A bakin ki Talatuwa kuma sai kin rigani mutuwa, ni nan tsawon rai zan yi sai na haifi na miji ko kangararre ne ya taimaka min na san daɗin haihuwa sannan zan mutu" Cike da mamakin maganarsa ta ce
"Allah ya huci zuciyarka dama ni ban maka fatan mutuwa ba, ai cuta ba mutuwa ba ce" Shiru ya yi don jin cikinsa yana kartawa ya ce
"Ki nemo Sumayya ta kawo min maganin gudawar da Habiba ta bata ta saya da safe" Da to ta amsa ta tashi ta fito, ɗaki ta nufa ta samu Sumy ta ce
"Sumayya Babanku ya ce ki kai masa maganin gudawa" Shiru ta yi sai kuma ta tashi ta fita, tana zuwa ɗakinsa ya fara masifa
"Ke saboda ke shegiyar yarinya ce ina wannan halin amma ba za ki kawo min maganin ba?" Tana danne ƴar dariyarta ganin Baban ya yi zuru-zuru don ta tuna matsayinsa na mahaifinta bai nuna tausayawa ba gareta ya bata kuɗin maganin ba sai yanzu kuma zai ce ta bashi hakan ya sa ta ce
"Baba dama fa guda huɗu ne ni kuma duka na shanye" Cike da masifa ya ce
"Si kike dai in fitar da kuɗi ko in banda ma almubazzaranci a ce magani biyu ma bai isa ki shanyw ba sai kin sha huɗu" Bata yi magana ba ya ce
"Ai kuwa da in banda hamsin ko ɗari a siyo min maganin gwara na zauna gudawar da kanta in ta gaji da fitowa ta tsaya min"
Haka Baba ya yi ta gudawa har dare amma bai sha magani ba, sai da ya ga yana dab da rasa ransa sannan ya bada naira hamsin aka siyo masa ya sha.
Washe gari ma haka gudawar ta dawo don haka ya galabaita ma, sai masifa yake yana cewa ƴaƴansa basu da amfani da a ce maza ne da yanzu sun kai shi asibiti Arfat ce ta lallaɓa lokacin baccin wahala ya ɗauke shi ta je ta auno shinkafa kwano biyu ta ɗora ta dafa ta lallaɓa aljihun rigarsa ta ɗauki dubu biyar ta yi miya har da naɓa don dama mahaifiyarta ce da girki.
Aka dafa shinkafar nan har dare kowa yake wadaƙa da ita ya ci ya ƙoshi don dama cikin wacce ya noma ce da ya jibge sai kayan abinci sun yi tsada zai fito da ita ya sayar, shi ma da ya tashi haka Mama Bilki ta kai masa shinkafa da miya da nama ya karɓe ya ci yana ta saka albarkar cewa ashe tana son sa tun da har bakin girkinta tana sayen abinci ta dafa kowa ya ci lallai yana alfahri da ita.
Ko kaɗan bai san cewa abincinsa ba ne kuma a aljihunsa aka samu kuma a aljihunsa kuɗin cefanan ma ya fita, yana da halin da zai wadata iyalansa amma ya gwammace ya musu ƙwauro ya ce kowacce ta je ta nema ba ya musu kallon su mata ne kuma ba ya tsoron hakan ya zama hanyar lalacewarsu.
*JIDDA*
Daga ita har sauran wanda suke kusa da su na motar kallon Aliya suke, hatta direban motar sai da ya taka wani uban birkin da sai da wanda yake bayansa ya kusa buga masa tasa motar, Allah ya rufa asiri ma lokacin ba wani gudu ake yi ba tun da suna ƙoƙarin kutsa kai cikin gidan Jiddan ne. Kowa ya hau tambayar ko lafiya, shi dai direban ƙarasawa ya yi ciki ya yi parkin don duk girman gidan sai da gabaɗaya motocin suka shiga ciki.
Ƴar uwar Ummar ce ta ce
"Lafiyarki Aliya mai yake damunki" Aliya da shigowarsu cikin get ɗin gidan ya sa ta sake susucewa hankalinta ya ɗuguzuma da tashi, ganin gidan da ƙwayaye tarrr ya haske ko ina kamar rana ga motoci ne tamkar wajen aiyar da su suna gefe a lulluɓe, hakan ya sa ta ji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu. Ita ma ƴar uwar Abban ta ce
"Ko dai jifa aka yi wa yarinyar nan ne a kan aure in ba haka ba yanzu nan take lafiya ƙalau amma kuma a ce ta gigice haka?" Ƴar uwar Umma wacce ranta gabaɗaya ya ɓaci na ganin gidan Jiddan ta ce
"Allah ne ya san karatun kurma" Jidda kuma duk ranta ya sosu ta ce
"Aliya mene ne ?" Aliya ji ta yi da Jidda ta yi magana tamkar ta ɗauki wuƙa ta daɓawa Jiddar ai dai dole idan Jiddar ta mutu Ibrahim ya aure ta, ta zauna a wannan gidan mai kyau wanda a ganinta kowacce mace za ta yi buri da mafarkin samu!.
Direban ma gabaɗaya ya maido hankalinsa kansu shi da abokinsa na gafensa, Aliya kuma da sauri ta danne abin da take ji ta tattaro nutsuwar ta ta buɗi baki tana mai miƙa hannu wajen ƙafarta ta ce
"Wani abu ne na ji ya cije ni a ƙafa ta" Ƙofofin motar aka buɗe suka suka fito sauran jama'a kuwa da basu san mai yake faruwa ba duk sun fito daga motocinsu suna shige ciki suna son ba idanunsu abinci domin su kashe ƙwarƙwatar idanunsu, haske-haske aka shiga yi ƙasan kujerun amma ba a ga komai ba, har ma ana tunanin ko kunama ce amma ta ce ba kunama ba ce. Ƴar uwar Umma ce ta kama lafayar ta rufa mata tare da riƙe hannunta, a inda ƴar uwar Abba ta kama Jidda wacce duk ta shiga damuwa da yanayin da ta ga Aliya.
Ƙofar sa za ta sada su da ainihin cikin gidan suka nufa mata sai sakin guɗa ake yi, amma Aliya suna dab da shigewa ƙofar ta ja ta tsaya ta ce
"Aunty ni ba zan shiga ba" Ƴar uwar Umma ta ce