Kenza eBookz

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 8

Ruwa cikin cokali complete hausa novel - Chapter 8

Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 8: Ruwa cikin cokali complete hausa novel Chapter 8. NA

3,362 words

NA

MAMAN AFRAH

. *Daga marubuciyar*

*Ci* *ma zaune, malamin* *bogi, ƙazamin* *miji* *Bonono, ruɓaɓɓiyar igiya, ƴan adaidaita sahu, ƙara'in inna delu, jalli* *joga, Beelal, ƴar zaman wanka, ungozoma* *da* *sauransu*

*09025576222*

BOOK 1

PAGE 7️⃣

*MAMY*

Da kallo ta bi bayan Mubin har ya ɓacewa ganinta tana jin babu daɗi a ranta, Zalika ce ta dawo da ita daga ƙaramin tunanin da ta tafi ta hanyar faɗin

"Mamy ki yi haƙuri kawai amma dai Baffa ba ya kyauta mana, tun muna yara bamu san daɗin hira ko zama inuwa ɗaya da mahaifinmu ba, gashi har mun girma abin yana mana ciwo amma hakan bata sauya zani ba"

Mamy ta ɗan nisa ta ce

"Zalika kin san na yi iya ƙoƙarina wajen ganar da mahaifinku kuskurensa amma ya ƙi fahimta ko ya gane bare har na saka ran cewa zai yi aiki da shawarata, kin san da yawa wasu mazan suna ganin mata basu da tunanin sannan kasancewar an ce mace tana ƙasan namiji haka ya sa wasu mazan suke ganin mace ba za ta basu shawara ba su ɗauka, bare shi da yake ganin kawai duk abin da zan faɗa ma labarin ƙanzon kurege ne don shi a tashi fatawar idan ya ba ƴaƴa abinci da biya musu dukkan buƙatunsu shikenan ya sauke haƙƙi!"

Suna cikin tattaunawa suka ji mai gadi ya buɗe ƙofa, jim kaɗan sula ji shigowar mota wacce sun tabbata Baffa ne ya dawo domin lokacin dawowarsa ya yi.

Zalika ce ta miƙe tsaye da sauri, Mamy ta riƙo hannunta ta ce

"Ina za ki je?"

Zalika ta ce

"Ɗaki zan je"

Mamy ta ce

"Mai ya sa?"

Zalika ta ce

"Kin san yanzu Baffa zai shigo ni kuma ba na son yake wannan ɗaure fuskar" Jin furucin ta sai Mamy ta sakar mata hannu abin da ya ba Mamy mamaki da sassarfa Zalika ta bar falon tamkar wanda take gudun kar wani abun tsoro ya afka mata.

Karaf ƙaran buɗe ƙofar falon ya ziyarci kunnuwa Mamy wacce ta yi tsuru kamar mai jiran tsammani. Kamar yadda ta tsammata ɗin hakan ce ta kasance domin yadda ya turo ƙofar kamar wani kumurcin zaki haka ya shigo ran nan nasa a ɓace kamar an faɗa masa mutuwa, ko arziƙin sallama ba a samu ya yi ba, ƙofar ya mayar ya rufe sai da ya zo tsakiyar falon ya ja ya tsaya yana ƙarewa ko ina kallo. Har lokacin Mamy bata ɗago ta kalle shi ba.

Takowa ya fara yi sai dai ya zo falon sannan ya nemi waje ya zauna bayan ya ajiye ledar da ya shigo da ita, kallonta ya yi ya ce

"Baki ganin mutum ya shigo kika watsa yina?" Sai da ta yi yaƙi fa zuciyarta ganin bata faɗa masa wata magana da za ta ƙona masa rai ba, a hankali ta buɗe dashashshiyar muryarta ta ce

"Sannu da zuwa"

Kallo ɗaya ya juya ya mata ya ga ɓacin rai kwance a saman fuskarta sannan daga hakan ma ya fahimci tana cikin damuwa don yanayinta ya sauya kuma yana iya hango sawun hawayen da ya zuba a idanunta.

Sai dai kasancewarsa ba ya cikin mutanen da suka damu da damuwar iyalansu ba sai ya juya ya nufi hanyar da za ta sada shi da part ɗinsa, Mamy ɗago kai ta yj tana bin bayansa da kallo ji take kamar ta janyo shi ta buɗe kunnuwansa ta faɗa masa cewa ya gyara halayyarsa sai dai ta san wannan ba mai iyuwa ba ne.

Bayan tafiyarsa da mintina kaɗan ta tashi ta goge fuskarta ta bi bayansa duk da ta san bin bayan nasa ba ƙaramin matsala ba ne amma dai tana ƙoƙarin sauke nauyin haƙƙinsa da ya rataya a wuyanta matsayinsa na miji a gare ta.

Tana zuwa ta ɗan yi kamar minti uku a bakin ƙofar kafin ta tura ƙofar, taa shiga ta mayar ta rufe, Baffa da yake ɗaure da towel a ƙugunsa ya juyo ya ce

"Lafiya dai?" ,Duk da ba wannan ne karo na farko ba da ya jefa mata tambayar ba amma dai ta sosa ranta. Cikin sanyin murya ta ce

"Lafiya ƙalau, dama ruwan wanka zan haɗa maka"

Baki sake yake kallonta kafin ya ce

"Ikon Allah na zaune ya faɗi, yanzu akwai ruwa a famfo a banɗaki da komai sai an biyoni" Jin furucinsa sai ta juya cike da takaici ta fita, ledar da ya ajiye ta ɗauka ta adana kayan bata san wane irin miji ne shi ba ko ta ce bata san wace irin zuciya gare shi ba da babu ruwansa da iyalansa.

Bayan an yi sallar magriba ya shigo gidan dawowarsa daga masallacin magriba kenan, sai da ya yi kamar minti uku da shigowa sai ga Mubin ma ya shigo don dama ta san ba zai bari ya bishi ba irin na ɗa da uba sai dai kowa ya yi tafiyarsa da ban. A kujera ya yada zango ya ɗauki remote ya sauya channel ya ɗan ƙara volume.

Ko da Mubin ya shigo bai tsaya a falon ba, tun da ya yi wa Baffa sannu da zuwa ya amsa dakyar a ciki-ciki sai ya wuce ya tafi ɗakinsa ya kwanta yana danna waya. Zalika ma da ta idar da sallah ta zo ta ce

"Baffa barka da dawowa, an dawo lafiya"

Baffa ya amsa a taƙaice da

"Yawwa" Sum-sum ta koma ɗakinta a kan sawunta. Mai aiki ta shigo ta jera kayan abinci a dining kamar ba gobe, Mamy ta ɗaga waya ta kira Zalika da Mubin a kan su zo a ci abincin dare duk da cewa ana cin abincin ne kamar a gidan makoki amma babu wani raha ko nuna kulawa a tsakanin iyalan, don shi wanda shi ne ginshiƙin gidan bai bada damar hakan ba.

Kusan a tare suka shigo falon, lokacin Baffa yana waya da wani abokinsa duk ya cika falon da karaɗin wayar da yake bakinsa a washe kamar an biya masa kujerar makka, yana magana yana dariya har da ƙyaƙyatawa. Daga Mamy har yaran sai suka mayar da shi TV domin su sai su manta ma da ganin fuskarsa a sake sai dai idan ya bar gida ko yana waya ko a kasuwa wajen shagunansa ki ga yana ta raha da jama'a, haka ake yabonsa cewa mutum ne mai fara'a da sanin darajar mutane amma su dai iyalansa basu san wannan ba.

Yana gama wayar ya haɗe rai kamar bai taɓa wani abu dariya ba, lokacin da Mubin da Zalika sun koma kan dining sun zauna.

Cike da izza ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya mayar da hankalinsa kan TV ransa a haɗe kamar ba shi ne yake dariya da ƙyaƙyatawa a waya ba.

Sun jima zaune kan dining ɗin amma Baffa babu alamar zai taso, Mamy ma ta je ta ja kujera ta zauna, sai kallon kallo suke a tsakaninsu. Cike da takaicinsa ta ce

"Baffan yara kai muke jira fa" Ta faɗa tana kallonsa, kamar ba zai furta komai ba sai dai ya ƙara tamke fuska ya ce

"Zan zo ai" Ganin haka sai Mamy ta shiga zuba musu abincin, farfesun kifi ne, wani fulas ɗin soyayyan naman kaza, ɗayan farfesun kayan ciki, abinci ma kala biyar dambun kuskus, soyayyar taliya, sinasir, funkaso, ɓarjen alkama, drinks ma iya ganinka sai wanda kake so, kallon kwanukan da Mamy ta bubbuɗe tana zuba musu abincin Mubin ya yi ya ga, ga komai amma kuma babu farinciki!.

An zubawa kowa har Baffa amma har lokacin babu alamun zai taso shi ko kaɗan bai san cewa iyalinsa suna buƙatar kulawarsa fiye da kayan more rayuwa da zai wadata su da su ba.

Kowa sai juya cokali yake a ciki, tausayin yaran ya sa Mamy ta ce

"Baffan yara abincinka fa zai huce na zuba"

Buɗar bakinsa sai ya ce

"Ki ɗakko nawa abincin ki kawo min nan ba na sha'awar cin abinci a kan dining yau" Kamar wanda ya zuba mata ruwan dalma a kunne haka ta ji yayin shigar maganarsa, idanu ta runtse don bata son ganin fuskokin yaran. Mubin da Zalika kamar wanda suka haɗa baki sai kowanne ya tashi riƙe da plate ɗin abincin sa a hannu, ƙaran buɗe ƙofa shi ne ya ankarar da Mamy ta buɗe idanunsa sai kuwa ta ga wayam gabanta babu yaran sun bar wajen, mayar da idanu ta yi kan dining ɗin sai kuwa ta ga duka babu plate ɗin kowanne a cikin su.

Juyowa ta yi ta mayar da kallonta kan Baffa tana so ta ga ya zai yi tun da dai ta san ya san cewa yaran sun tashi daga wajen ne saboda ba zai ci abinci da su ba.

*SADIYA*

Sai da ta kama Kalifa ta ɗago shi sai ta shiga duba jikinsa a matuƙar kiɗime tana son ganin inda ya ji ciwo, kamar daga sama ta ji muryar mai mashin ɗin yana faɗin

"Tsorata ya yi ne da ya ji ƙaran horn, Allah ma ya kiyaye ban lura da shi ba ya taho" Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke har lokacin tana jin sanyin da ƙafafunta suka yi. Gefe kawai ta matsa tana jijjiga Kalifa don bata da ƙarfin halin furta masa komai, shi kuma ya ce

"Allah ƙara kiyayewa ake kula da yara" Yana gaɓa faɗar hakan ya ja mashin ɗin, jakarta ta koma ta ɗakko daga inda ta ajiye don ita dama wayar tata ma ko caji babu domin bata ma riƙe caji sosai shi ya sa bata tarki kiran Nasir ba, bare ma ta san ba ɗauka zai yi ba in ta kira sai in ya ba dama.

Tana nan tsaye a ƙofar gidan lokacin an fara kiran magriba wani mashin da ya karyo kwanar ta gani kamar daga sama ta hangi Nasir a bayan mashin ɗin, sai da suka zo har ƙofar gidan ya sauka daga mashin ɗin ya ba mai mashin kuɗinsa mai mashin ya ja ya bar wajen, Kalifa ne ya hau faɗin

"Abba, Abba, Abba" ,Kallo ɗaya Nasir ya musu ya ɗauke kai mukulli ya fiddo daga aljihunsa ya buɗe ƙofar gidan ya shige har da ɗan turo ƙofar, wani abu ne ya tokarewa Sadiya a maƙoshi saboda abin da ya yi wa Kalifa sai ta ji duk abin da ya mata bai mata ciwo ba kamar wanda ya yi wa ɗansa , abin na matuƙar damunta ita a nata tunanin ko da a ce da Kalifa ta zo gidansa bai kamata yake yi wa yaron haka ba, bare kuma ɗansa na cikinsa. Haka ta daure ta taka matakalar ƙofar gidan ta saka hannu ta tura ƙofar ta shigo gidan ita tsabar bata da nutsuwa ma ta manta da wani abu wai sallama haka ta shigo gidan kamar wanda dama Nasir yake jira sai ji ta yi ya ce

"Ke! Babu manya a gidan ko? Na ce manya sun ƙare a gidanku, idan ma akwai manyan to basu bada tarbiya ba gskiya tun da kike shiga gida babu sallama" Maganar ta mata ciwo sai abin ya zame mata zafi biyu wato ga mari ga tsinka jaka, saboda bai san darajarta ba ya barta wuni guda a titi amma ya zo yana ƙara mata wasu maganganun mararsa tushe.

Daurewa kawai take amma kuka neman ƙwace mata yake, sauke Kalifa ta yi don yanzu hankalinta ya fi karkata ga yin sallolin da suke kanta hakan ya sa da ta sauke Kalifan kawai ta yi gaba don yin alwala, shi ma Kalifan kamar ya san mai yake faruwa sai ya ja ya tsaya a ƙofar falon ya raɓe yake leƙen Nasir ɗin.

Inda ta cika butoci ta je ta ɗauki ɗaya ta yi addu'a ta shige banɗaki ta turo ƙofar, ta tsugunna tana kama ruwa kawai sai ji ta yi an banko ƙofar har sai da ƙofar ta gwaru da jikin bangoda sauri ta tashi tsaye don dama ta gama kama ruwan.

Juyowa ta yi tana kallonsa a tsorace ganinsa a fusace tamkar wani fusataccen zaki, kafin ta furta wani abu ya ce

"Wato ga ɗan iska ko saboda kin rainani ina faɗa shi ne kika yi tafiyarki kika barni in yi ta zuba ko?" ,Cikin sanyin murya da kuma ƙarfin da yunwa ta cinye mata ta ce

"Ka san dai a waje muka wuni ban yi sallar azahar ba bare la'asar kuma yanzu ana kiran magrib... Tun kafin ta ƙarasa ya katse ta da faɗin

"To ina ruwana da sallarki, in ban da rashin tarbiya ina magana ki tafi wannan daga gani babu tantama gida kika ɗakko halayyar rashin tarbiya, dama ai an ce tarbiya daga gida take farawa, in ba don ni ba wa zai kwasa iyayenki ma da kin ishe su da Allah annabi Babanki ya sa na aure ki, don na ɗauke masa ɗawaniniya saboda yana so ya kawar da ke, ina faɗa a ko ina ban aure ki don ki zama abokiyar rayuwata ba na san aurena da ke ƙaddara ce baƙar ƙaddara ma kuwa, a yau idan na ga dama zan yanke igiyar aurena da ke kuma in auro wacce ta fiki komai don ke baki cika mace ba!."

Kallonsa take yadda yake magana cikin ɗaga murya, idanunta suka fara tara hawayen da take ta ƙoƙarin maƙale suka fara ambaliya a dakalin fuskarta, a take maganganun da ƙawarta Noor ta faɗa mata suka fara dawo mata, wanda take faɗa mata cewa take kataɓus wajen rama abin da Nasir ɗin yake yi wa iyayenta na cin mutunci tun da iyaye ai sun fi ƙarfin wasa tun da shi bashi da mutunci bai san shi ba. Jin kalamnsa kuwa ai ta tabbatar iyayen nata yake faɗawa magana, ai kuwa ta fara takowa daga cikin banɗakin sai da ta zo gab da shi ta tsaya ta ce

"Nasir" Da mamaki yake kallon ta jin ta kira shi a wani gadaranci ko dai ya kira hakan da muryarta cike da fitsara.

Baki ya saki yana kallon ta ta ci gaba da faɗin

"Duk abin da za ka yi ka tsaya iya kaina amma iyayena ba sa,anninka ba ne da za kake faɗa musu abin da duk ya zo bakin ka ba zan ɗauki haka ba"

Haɓa ya riƙw cike da mamaki ya ce

"To mai za ki iya idan an sako iyayen naki ko kina da matakin ɗauka ne? Iyayen naki da basu damu da farin ciki da baƙin cikin ki ba ni fa a wajena baki da maraba da wacce aka min tallar ta ko aka bani sadaka"

Ita ma a harzuƙe ta ce

"Ko ma ya suke iyayena ne kuma ko ma ya suka ɗaukeni wannan tsakaninmu da su ne, ni dai gargaɗina na ƙarshe da kai kar ka sake cin mutuncin iyayena"

Idanu ya ƙanƙance ya ce

"Gargaɗi? Sadiya ni Nasir ne kike yi wa gargaɗi kamar wanda bakin uwa ya kamani har wata mace za take faɗa min magana"

Bata bi ta kan tambayarsa ba ta ce

"Ni da sakakkiya a gidan nan banbamcin mu kaɗan ne, ko kaɗan baka darajani, tsakani da Allah kana gani na amma ka tafi bayan ka san gidan a kulle na wuni a titi ni da ɗanka ko kishin iyalinka baka yi, duk namijin da ya san darajar kansa da ta iyalinsa ba zai wofintar da su su wuni a titi b...

Wani gigitaccen mari ya ɗauke fuskarta da shi, da yake marin ya je mata ne a bazata sai ta ji tamkar ba da hannu aka mare ta ba, marin da Kalifa ya gani ne ya sa ya ruɗe ya fashe da wani kuka ya yi kanta ya je bayanta ya ƙanɗame ta har lokacin yana kuka, bata kula Kalifa ba duk da kukan nasa yana taɓa mata zuciya. Tana dafe da kumatun da ya mara ta kalle shi idanunta taf da hawaye ta ce

"Ni ka mara Nasir?"

Kamar zai kai mata wani marin ya ce

"An mare ki fitsararriya ko za ki rama ne? Har ni za ki ce ban san darajar kaina ba, kuma wallahi sai na faɗawa wannan uban naki ya gargaɗe ki don zai iya zuwa ya ga gawarki matuƙar baki yi wa bakin ki linzami daga furta min kowace kalma ta zo bakinki ba" Yana gama faɗar hakan ya juya ya nufi falo, Kalifa ta ɗauka har lokacin yana kuka da alama tsorata ya yi da marin da aka mata tana ɗaukansa ya maƙalƙale wuyanta bata san lokacin da ta fashe da kuka mai sauti ba. Ta jima tana kuka mai cin rai kafin ta yi shiru ta goge hawayen, jin Kalifa ya yi shiru ya kwantar da kansa a kafaɗarta, sai ta duba sai ta ga ya yi bacci haka ta kawo shi falon ta kwantar da shi a kan kujera ta koma ta yi alwala ta zo ta kabbara sallah.

Lokacin Nasir yana bedroom, sai da ta yi azzahar da la'asar tana yi tana hawaye duk sujadar da ta kai sai ta faɗawa ubangiji damuwarta a kan ya magance mata, tana shirin miƙewa ta yi mageriba sai ga Nasir daga bedroom ɗin kamar an jefo shi, gabanta ya zo ya tsaya yana riƙe da wayarsa da take ringing da alama wani yake kira don wayar a handsfree take ma.

Kamar daga sama sai jin muryar Baba ta yi yana cewa

" Assalamu alaikum malam Nasiru mutumin kirki" Wani murmushin gefen baki Nasir ya yi kafin ya haɗe rai kamar Baban yana ganinsa ya ce

"Ni wallahi Baba ba na cikin yanayin da zan amsa sallama gabaɗaya raina a ɓace yake"

Buɗar bakin Baba sai ya ce

"Sadiya ce ko? Wannan yarinya mai ya sa bata jin magana wai, haka fa ta kwaso jiki wai wuni ta zo gidan nan na korata ɗakinta da tsakar rana shi ne kuma da ta dawo ta ɓata maka rai" Sosai Sadiya ta ji duk ta muzanta dole Nasir yake mata abin da ya ga dama saboda mahaifinta shi yake bashi kowace dama, shi yake zubar da kima da darajarsa, shi ya sa ba ya siya mata mutunci bata san wane irin uba ne ta samu ba.

Nasir ba yabo ba fallasa ya ce

"Ai Sadiya bata san darajar miji ba ko kaɗan, ban da zagi da baƙaƙen maganganu babu abin da take a gidan auren ta, yanzun nan ta gama cewa ban san darajar kaina ba da ta iyayena" Ya faɗa cike da ɓacin rai, Sadiya jin har da ƙarya ya shirga bata yi mamaki ba da ya yi haƙuri ma in dai Baba ne a kan a samu matsalar da za ta koma masa gida ba sai da ƙarya zai mata faɗa ba.

Baba ya ce

"Bata wayar" Wani kallo Nasir ya mata yana wani ƙanƙance ido irin na fitsararru ya miƙa mata wayar tana ƙoƙarin danna wayar Nasir ya katse ta da faɗin

"Kar ki kuskura ki cire min waya a handsfree ki bari in ji, idan ma shi yake ɗaure miki tsantsa ki rainani" Yana gama faɗar haka ya koma kan kujera ya zauna tare da harɗe ƙafafu.

Baba ya ce

"Sadiya wallahi ki fita idona in rufe, mijin da ya rufa miki asirin kike zagi, shin wuta balbal kike son shiga Sadiya?" Kallonta ta mayar kan Nasir da ya kaɗa kai alamar ta dai ji rufa mata asiri ya yi.

Kafin ta samu zarafin furta komai Baba ya ci gaba da cewa

"Wallahi idan ba so kike in zo har gidan in saɓar miki ba ki masa biyayya ko wuta ya ce ki faɗa ba dole ki shiga ba Sadiya tun da mijinki ne aljannarki tana ƙasan ƙafafunsa, kin samu Allah ya tarfawa garinki nono kin yi aure amma kike tada fitina da dai ban san ki da haka ba ko ƙawaye kika samu suke hure miki kunne?" Jin Baban ya dakata ta gane kamar ya bata damar magana hakan ya sa ta ce

"Baba tun da na dawo yana ganina fa ya tafi da mukullin a titi muka wuni sai yanzu ya dawo kuma bani da damar da zan nuna ban ji daɗin abin da ya yi min ba sai ya kai min hannu? Marina fa ya yi Baba yana ta faɗa wa iyayena maganganu... Cike da faɗa Baba ya katse ta ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba yana ta ɗora mata rashin gaskiya a ƙarshe ya ce idan ya ƙara jin wata magana ta ɓullo sai ya saɓar mata.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull